You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Haka suka bar unguwar, suka nufi asibitin, inda suka sami Aunty Amina da
Rabi sune a jikin Anum, sai rikici take musu, su kuma suna lallabata, yadda suke
circcira bai fahimtar da su Aunty Aminatu ba, dauka suka yi akan auren suke masifa
dan suma sunyi nasu, kalmar da Hafsat ta furta yasa Aunty rabi zuba mata ido.
"Wasu ai farin ciki suke dan sun san hankalin wasu a tashe shima malam dake an tofe
shi, sai yadda aka yi dashi yasa ya kafe da.."
"Rashin kunyar da kikewa dangin mijinki, zaki mana? Ko ance miki bani da labarin
rashin hankalin da kikewa Umma."

"Rabi, kiyi shiru karki tadda mana hankali a cikin asibitin, Allah ya kyautata
karshen mu." Inji Aunty Aminatu.

Haka suka bar asibitin ransu babu dad'i, cikin kuka tace.
"Don Allah ku kira min Ummana, don Allah kuce Umma taxo, wallahi ba zan kuma ba."
"Wato kina son ki cigaba da janyowa Umma abin fada shi yasa kika sha piya
piya, hankalinki ya tashi yan uwan ki suna zargin Baba ya kore Maman Aminu ne dan
Umma, bayan kuma ba haka bane, kema kanki sheda ce, dan haka muma zamu barki a nan,
kiyi jinyar ki ke daya a daina zagin mahaifiyar mu."

"Don Allah kuyi hakuri ba zan kuma ba, sako XOXO ta turo min wai idan nasha
piya piya aka ga zan mutu a fasa aura min Maude don Allah ki cewa Umma ba da son
raina nayi ba." Ga abin duka rashin sanda, dan haka suka share ta,basu mata magana
ba.

...... A daren ranar Maude yazo dubata, ya samu jikin da sauki. Tana kwance a
jikin Aunty Binta, da take bata ayaba,matar Aminu tana matsa mata kafarta, taki ta
kalli inda yake duk maganar da suke mata. Asalima kifa kanta tayi tare da fara
barcin karya.

Har ya mike zai fita, ya kalle ta, sai lokacin ta d'ago kanta, ta zuba
mishi wani uwar kallon banza, ta dauke kanta, juyawa yayi zai fita suka bangaji
juna da wani mutum.
"Sannu don Allah!"
"Yawwa babu kome!" Ya faɗa mishi,
har ya kai zai fita, yaji mutumin yana faɗin.
"Major General Asadullah Haidar Turab!" Cak ya tsaya,
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! MG Asadullah! Kai ne?"
Juyawa yayi tare da girgiza kan shi yace.
"A'a sunana Maude, ban san wanda kake fada ba."

"Amma wallahi kayi min mugun kama da shi Babban sojan kasar Nijar, wallahi babu
abinda ka bar mishi. Allah sarki!"

Bai ce kome ba, ya saka kan shi ya fita daga asibitin. Shi kuma mutumin sai
jajjanta zancen yake da kamar ya koma gurin Maude ya karya shi.

.... Ajiyar zuciya yayi sannan ya shiga abin hawan shi. Yana nazarin
mutumin da yayi mishi magana. Share maganar yayi tare da wurgata a kwandon shara.
Bayan kwana biyar aka sallami Anum, ta dawo gida. Tunda ta dawo umma kamar
zata yi fushi da ita, sai kuma ta kasa, ta cigaba da kula da ita.
Satin ta daya da dawowa aka kawo kayan lefe. Wanda ya taimaka gurin d'aga mata
hankali. Bayan kawo lefen dake har dasu Hafsat a karb'a. Bayan zasu koma gida ne ta
dauko kudi har dubu uku ta mika mata.
"Ki tafi wani guri ki zauna idan kome yayi kyau sai ki dawo."

"Toh zan yi yadda kike ce" ta ajiye kudin, tana kallon shi har ta fita.
Kasa aiwatar da abinda Hafsat tasata tayi, karshe ta shiga dakin Umma
tana sallah ta zauna har ta idar, ajiye mata kudin tayi..
"Umma gashi wai na gudu, don Allah karki gayawa Malam yayi musu faɗa."

"Wacece tace ki gudu?" Shiru tayi tana wasa da yatsunta.
"Toh ba zaki yi magana ba?"
Kuka tasaka mata.
"Umma kina fushi dani dayawa, bana jin dadin rayuwa na!"
"Toh idan banyi fushi dake ba, KHADIJAH wuka zan burwa cikina? Ke daya tal kin hana
kowa sukuni, sabida ke kullum Mallam sai ya sha maganin hawan jini, sabida ke yan
uwanki suke min kallon na raba auren mahaifanku, gaya min idan banyi fushi ba in
zauna nayi ta dariya sabida kina aikin kwarai?

Wai har kin san kisha madarar piya piya, ki mutu? Toh sai me dan kin mutu?
Wallahi nayi danasanin renon abinda zai kashe ni da bakin cikin rayuwa har na aurar
da su Binta basu saka Ni damuwa ba, Rulwanu da yake namiji bai saka ni damuwa ba,
sai ke Anum? Meye nayi miki da kike azabtar da ruhina?

Mahaifiyarki tana jin zafina! Yayana da na haifa suna jin zafina,.mijina
yana jin zafina kinyi min adalci? Ai dana san XOXO ce ta baki shawaran shan piya
piya, wallahi kinji na rantse da wanda rayuwata da mutuwata take hanun shi ba zan
tab'a kawo miki ɗauki ba. Anum kiyi yadda kike so bani kuma dakatar dake idan na
kuma ni shegiya ce ba yar halak ba.

Yadda kika iya daukar shawarar XOXO nayi imani da Allah idan aka yi auren
haka zaki.dauko shawararsu su. Meye amfanin na zauna ina bata lokaci na akanki?
Anci mutuncina akanki an zarge ni akanki ashe ban cancanci na samu nutsuwa, Anum
idan Aminatu da Rulwanu haihuwa ta suka yi ta hanyar sunnah, ba zan kuma cewa ki
gyara kayanki ba, idan kuwa a kasuwa suka samar dani zan miki magana, ki saka kai
ki ficce min daga cikin d'akina kafin na sab'a miki, duniya ce tafi gabaruwa ji
ma."

Kuka Anum take son yi amma fir yaki zuwa, haka ta makale jikin umma
tana cewa.
"Wallahi mutuwa zanyi idan na saka kafa na fita daga dakinki." Aikuwa ran Umma ya
kai iyakar b'aci, tana tashi ta yakinin ceta a jikinta ta wullar da ita waje ta
datse kofar ta, gashi ana ruwan sama, ihu Anum take tana buga kofar Umma, itama a
cikin dakin kuka take me mugun cin rai, tana jin ina zata iya daukar kasadar rabuwa
da Anumullah ɗinta,

Yarinayr da take ji tun ranar da ta fado cikin uwarta itace ta fara daukarta
tare da rungume ta, sabida an haifeta ta wahala ko numfashi bata yi, domin tayi
kankanta lokacin a tunanin su ma bata cika wata tara ba, duk iya kokarin ganin
yarinyar ta motsa Umma tayi ta daura ta a kirjin Maman Aminu amma ko gizau, sai da
Maman Aminu tace mata.
"Ki sakata a jikinki mu gani, kamar bazata tashi ba."
"Anya zata tashi kuwa?"
"Gwada dai mu gani!"
"Toh Ya Allah, gamu gare ka mun gode maka"
A hankali ta saka Anum din cikin rigarta tare da mannata sosai a kirjinta, ta kuma
dauko zani da bargon Maman Aminu, ta manna Anum din sosai.
*_Fatan Alkhairi Sister Maryam Badam Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi nagode
sosai_*
#Mai_Dambu
[1/31, 11:27 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA...!!
_Rayuwar Aure a Arewacin Najeriya_

Mai_Dambu
Farga daji....
BABI NA UKU
--------------------------------------

Ina jin hayaniyar yan uwana, amma sabida kasancewa ta, mujiya a cikin su, ya sani
kara lafewa a gadona, ina had'iye yawun, sakamakon kamshin soyar namar da ake na
sunan Ikilima matar Ya Abubakar, wacce ta haifi d'a namiji aka sami shi sunan Baba
Malam.

"Mama yar sarki me rigar mutum ba zata fito bane ayi aikin da ita? Wato ga
bayinta su gama mata, ta zauna ta cinye?" Inji Aunty Hafsah, yayata ce da muke ciki
ɗaya.

D'aga labulen Yaya Binta tayi dan ita ce ya ta farko a cikin gidan mu, ta
kalle ni na tashi zubur ina zare idanuna da suke cike da kwalla. A hankali ta sake
labulen sannan tace musu.
"Da bata yi aikin sai ya kashe ku? Hafsat da Safiya kuna bani mamaki. Da akace
karta na yawan shiga damuwa shine bari kuyi ta sirka mata rashin mutunci?

Hmm! Zuciyarta yana tabuwa da abinda kuke mata, idan rayuwarta ce baku so!
Shi kenan, zaku iya Cigaba da abinda kuke."
Daga haka ta wuce dakin Mahaifiyar su. Cikin jin haushi Safiya tace.
"Yarinya ta gama rashin kunyarta tare da mana sanadin mahaifin mu, amma ake ganin
bata yi kome ba, har abada ba zan tab'a yafe mata ba, taji kunci da Baba Malam yaji
lokacin da yake rokonta arzikin da bai mata ba, amma fir taki kula shi."

Haka suka yi ta mita, tare da jin haushin yar autar su. Wato Anum.

... Duk ina jin su, amma bani da ikon fitowa wajen domin ina fitowa zasu min
caaa, dan haka na cigaba da zama a d'akina. Har zuwa azhar da na fito alola, naga
yadda suke kallona, jikina ne ya dauki rawa, kamar zan kifa, dan har tsalleke
abubuwan nake sakamakon tsawar da Aunty Hafsah ta daka min.
"Ke wata irin dabba ce? Kin zo kina niman zuba mana, ruwan butar a cikin abincin da
muke banza akuya, karya k...."

"Hafsat!" Ya Aminu ya daka mata tsawa, cikin jin haushi ta ce mishi.
" Ba ajiyar bace? Ko ba karyar bace? Wallahi har kunyar nunawa kawayena wannan yar
iskar cikin mu daya, sabida yadda ta zama taxi.."

"Kina da ƴaƴa mata, sannan kina zagin yar uwarki ciki ɗaya, sabida ajizanci."
Take kowa yayi mata caaa, ni kam nasan haka zai faru, da bi bango na isa d'akina,
na zauna tare da sake kuka me mugun ciwo, wanda su kansu yan wajen duk sai da suka
ji yo ni.
Kallonta kowa yayi cikin jin haushin abinda ta aikata, sannan suka ce mata.
"Yayi miki kyau!"
Maman su da take jin abin a cikin ranta, share su tayi amma tasan duk abinda
Khadijah Anum tayi ba laifinta kadai bane har da nata,a matsayin ta na Uwa ta gaza
tsawa yar autarta ta zama abin alfahari.

Itace ta gina mata kome na rayuwar da tayi, ita ce ta nusar da ita abinda zata
aikata, ita ta nuna mata kudi da kyau sune cikon muradinta,. Ba lallai sai ta zama
mace ta gari ba, zata iya zama mace mafi daraja indai zata hadu da me daraja.

Haka ta share kukanta a cikin dakin ta, dan bata son yaranta su gani wutar
k'iyayyar da take ruruwa a tsakaninsu ya kuma tashi.

--- bayan sun gama kome, suka shirya tare da barin gidan, suka nufi gidan da
ake taron sunan wanda yake Makara huta, dake garin bauchi. Suna shiga aka shiga
tambayar su.
"Ina Anum? Aunty Hafsah"
Inji wata budurwa wacce ba wuce shekaru ashirin da hudu ba, duk da bata girme Anum
ba, amma kuma zasu iya zama kusan shekaru daya.

"Shukrah, yaushe kika zo daga Kano?" Murmushi sannan tace mata.
"Yau kwana biyu kenan, don Allah Aunty Anum zata zo ne?"
Tab'e baki Hafsat tayi sannan tace mata.
"Ban sani ba, ko zata zo ashe."

Ta wuce Shigowar Mahaifiyar yarinyar ta mike tare da amsar jakarta, tana faɗin.
"Ammih Aunty Khadijah Anum ba zata zo bane?"
Shiru tayi sannan tace mata.
"Kuma na manta da sakonki, Amma Insha Allah zata zo dan naji tana cewa idan kanta
yayi mata sauki zata zo."

"Toh Ammih, Allah yasa kin san yanzun Aunty Anum ta zama wata iri ne tsoro ln
shiga mutane take."
Kallon ta Uwar tayi sannan ta girgiza kai, ta wuce komawa gurin Kawayenta
tayi tana gaya musu, bata zo ba amma Insha Allah idan ta kama suje bakin kura sai
suje.

---
"Toh ishashiya, kowa ya tafi gidan sunan shine ba zaki tafi ba!" Inji Mamarta.
Sunkuyar da kai tayi sannan tace mata.
"Don Allah Mamah ba.."
"Ok shima Zumuncin so kike ki lakata min kashin kaza? So kike a Cigaba da cewa nice
nake hanaki shiga yan uwanki."

"Don Allah Maman Aminu ki bar yarinyar ta samu kanta mana, wannan wacce irin
rayuwa ne, tunda bata jin dadi ta hakura mana!"
"Umma zani Insha Allah. Bari na shirya."
A gurguje na shirya tare da saka wata shaddata, wacce aka mata aikin surfani, sai
hijab me yashi.
Babu wani kwalliya na fito tare da daura niqab nayi musu sallama, ina fitowa daga
cikin gidan na sami Abba K2 yana zaune a bakin shagon Oga Maude, kallona yayi
sannan ya ajiye kofin shayin yana faɗin.
"Uwargida, ina zaki?"
"Zamu gidan Yayana ne ana suna." Na bashi amsa a takaice bai na kokarin barin gurin
su,

Tashi yayi daga gaban shayin, ya shiga keke napep din shi, ya sha kaina da keken.
"Muje ko"
"A'a kaje kaci.."
"Karki damu sabida ke nake aikin da babu ke haka zan cigaba da sara suka, a kashe
ni a banza,.dan haka ki shiga muje."

Ban musanta mishi ba, dan yaran suna bani wani irin girma ne na musamman, gani suke
kamar nice ogan su ma. Har kofar gidan Ya Abubakar ya kawo ni, kuma abinda zai
daure maka kai shine bai dauki kowa ba, sai ni yana ajiye ni yace min.
"Uwargida yaushe zan zo daukarki!"
"Karka damu zan sami motar da zata..."
A birkice ya kalle ni tare da tsuke fuskar shi yace.
"Ina nan ina jiranki duk lokacin da zaki koma sai na koma."
.sake bakina nayi domin kuwa ya bani mamaki, akan me zai zauna,
"Ka dawo bayan isha."

Na fada mishi haka, dan kar ya b'ata lokaci, a gurin zaman gadina, duk da nice
na janyowa kai na, da ace hannun agogo zai dawo baya lashakka zan gyara kuskure na.

Labarina babu abin dauka a cikin shi, domin cike yake da ƙadarorin masu
girma, kowani dan Adam da irin tashi ƙaddarar amma yawa ƙaddarar nice na zanata
wanda har yau na kasa goge shi.
"Laa, Aunty Anum!" D'aga niqab dina ina kallon yar Yayar mu.
"Shuky yaushe a gari?"

Cikin farin ciki da gani na ta shiga rawan jiki tare, da bani amsa, yayuna mata uku
musamman yan dakin mu, tsaki suka yi tare da dauke kan su, duk da yaran su, suna
murnan ganina, isa nayi gaban su na dauki yaran tare da musu wasa.
"Ajiye min Y'ata! Da kin san zafin shi ba zaki sake a tafi da shi wata duniya ba."

Murmushi nayi a karo na farko da naso majin zafin kalamanta, nace mata.
"Zanen ƙaddara ta kenan! Amma haka bai hanani kaunarta ba, kome zaki gaya min ki
min a cikin gidan mu, inda ba zan kulaki ba, nan kuma cikin jama'a ne, zuciya bata
da kashi kina min zan rama." Daga haka na ajiye yarinyar na bar su tsaye cikin
damuwa da mamaki, suna jin haushina, amma kuma halin da nake ciki, ba zai hana su
min rashin mutunci ba.
Gurin mejego na shiga muka gaisa dasu Ya Amina, Ya Rabi, da Ya Bintu, zama nayi ina
narkewa a jikin Ya Maryam.
"Kin san Allah Autar malam, ki rabani da son jiki. Kun hadu da shukrah."

"Eh!"
"Wai zata zo ki mata nasiha akan zaman aure ne. Tazo gurina nace mata bani da
wannan tunanin, tayu ke asamu wani abu daga gare ki, idan mutum ya duba daga
yanayin rayuwar da kika yi."

Tana maganar ne amma kasa kasa, da sauri na d'ago kai nace.
" Kuma kika ce Ni? Amma ai naga rayuwar auren da nayi babu kome cikin shi sai
damuwa da son zuciya!" Na fada a raunane.

"Babu son zuciya cikin ƙaddara, duk da kina da laifi, sai dai ki sani
ƙaddara itace igiyar da ya jaki zuwa ga wannan rayuwar, idan Allah bai zana miki
haka cikin ƙaddarar ki ba, toh babu abinda zai sanya haka ya faru, zanen ƙaddara
kenan, ki same ta naga har da Kawayenta suka zo, ita daya tana shirin aure nan da
sati biyu, daya kuma tana fama da matsalar mijinta da baya iya ciyarwa sai dai
iyayenta su kawo musu, yaci kuma ya kwashe musu albarka."

Kallonta nayi sannan na mike tare da cewa.
"Toh bari na gani."
"Yawwa yar albarka."
Fita nayi suka bini da kallo cikin tausayi da damuwa.
"Wallahi Yarinayr nan tausayi take bani, ga baki daya ta firgice da yan uwanta,
ganin dodanni take musu, don Allah Aunty B kunyi musu wani abu su kyaleta ta huta,
kiga duk fushin Baban Ayman haka ya hakura tunda yaji zuciyar ta zata iya bugawa
sabida damuwa, ku wanda kuke akan shi yayi tafiyar shi ai sai ku kyaleta haka."

Tattaunawa suka yi tayi, har zuwa wani lokaci, kafin suka share batun.

Ina fita ta mike muka shiga wani falon da babu cunkoso mutane, zama muka yi suna
kallona, nima kuma kallon su nayi kafin Shuky tace min.
"Aunty Khadijah, sunan ta, muna kiranta da Anum, kyautar Allah.!" Jan fasali tayi
tare da nuna musu ita, sannan tace mata.
"Mu nan, Kawata ce zata yi aure shine muka je gun Aunty Salamatu, wai muzo gurin."

Shiru nayi tare da nazarin ta inda zan fara musu bayanin.
"Wato shi Al'amarin aure girma ne dashi tare da fadin gaske, duk yadda mutum zai
gwada muku matukar bai tab'a shiga wannan bangaren ba, toh babu abinda zai gaya
muku sai hakurin. Abu na farko da zaku fara shine kuyi auren ku da Kyakyawan
niyya,karki yarda kiyi auren dan yana da kuɗi! Karki yarda kiyi auren da yana da
kyau! Karki yarda kiyi auren da shi wani ne! Karki yarda kiyi auren dan zai miki
lefen kece reni! Kuyi auren domin bautar Ubangiji, haka zai sanya ku rabauta, karki
yarda ki aure shi dan samun Freedom! Babu yancin da yafi ki bautawa Allah a cikin
zamantakewar aurenku!

Karki yarda ki aure domin ya cancanci haka ne, a'a ki aure shi domin Allah
kuma kiji a ranki koda shi gwamna ne ko shugaban kasa, zaki zauna dashi ne a
matsayin miji da mata, a karkashin kulawar Addininki!
Rayuwar Aure yayi ne! Domin babu rayuwar da yafi rayuwar aure dad'i, a
rayuwar aure babu, abinda zaki yi bai zama lada da Alkhairi ba, amma a wannan
lokacin rayuwar aure ya zama niyasu, sabida yadda muka sake addinin mu da Ibadar
mu, da ace mutanen baya sun san da haka toh bazasu tab'a barin mu,. Haka ba sai sun
mana addu'a akan zamani, sabida a lokacin su ana girmama auren fiye da kome a
duniya, amma a wannan lokacin auren ma wulakanta shi ake, da zaka tambayi wani dan
me zaka yi aure? Zai ce maka kawai zai yi ne sabida ya dace da haka, ko kuma zai
yine sabida Yarinayr zata kawo mishi kayan daki da Gara, har hada suke da junan su.
Da zaran anyi auren sai kaga kwanaki ƙalilan an fara samun matsalolin
rayuwa, ka rasa ta ina aka fara, bayan daga mune abin ya fara, karki yarda mutumin
kirki ya subuce miki bayan kina sane da shine zai ririta alamarin ki, karki yarda
da wanda zai zauna kullum yana gaya miki yayi mafarkin ki, bayan ba aurenki zayi
ba.

Shukrah karki yarda wani ya baki damar da zaki ki auren Mutumin kirki, bayan
kema kinyi imanin mutumin kirki ne, irin su ƙalilan ne muke dashi a cikin al'ummar
mu. Toh Alhamdulillahi anzo fagen aure, kowa zai ce miki kiyi hakuri halin maza sai
su, tun kafin ki isa gidan mun gama razana ki da mabanbanta Halayyar maza, da fadar
wasu munanan halayen su.

Shin kin tab'a tambayar Mamanki wani irin halin Mahaifinki yake dashi? Toh ai
idan halin shi mugun nufi ne, haka kuwa tayi hakuri da shi ta zauna a haka dashi,
idan halin shi na kwarai ne, haka zaki zauna da naki, duk duniya babu wanda ya isa
ya baki shaidan zuciyar mutum sai Allah, dan haka kiji a ranki zaki zauna dashi ne
da zuciya daya. Anzo fagen aure!

Anyi aure, an haihu daya biyu uku, wai sai kiji matsala ya dame ki, kina
kukan ya zaki yi,kece Posting a grp na Whatsp! Kece kaiwa IG, kece kaiwa Facebook.
Kin tab'a zama kinyi nazarin zaki magance wannan matsalar? Wadannan Groups da kike
Turawa 75% na cikin su Yan mata ne da suke niman mijin aure kin dauki damuwarki kin
kai musu! Shin akwai wani bayan Allah ne? Babu tabbas babu, akwai me magance miki
matsalar ki ce? Babu tabbas babu, Amma akwai Allah, Tabbas akwai shi. Kin tab'a yin
azumi domin Allah ya yaye miki damuwa? Toh indai har kinyi wallahi zaki iya akan
damuwar mijin, kin dauki Matsalarki kin gayawa mutane, sannan sun ce miki gaskiya
ki rabu da mijinki nan baya sonki da zuciya daya, shin kin tab'a ganin matar auren
da ta shekara goma a gidan mijinta ta bawa wata mace shawarar ta kashe aurenta?
Sabida duk lalacewar auren shine kimarta, bari na gaya muku wani abu, yan fashi da
manyan masu laifi, wallahi suna da matan su na sunnah kun tab'a ganin matar su tafi
toh tace mijinta dan fashi ne? A'a ba zata tab'a barin kowa yasan halin mijinta ba,
sabida boye sirrin shi.

Amma zaka samu mijinki yana zuwa kasuwa, domin niman na kanshi daga karshe
zata yi Posting don Allah ku boye sunana, mijina bayi da kirki. Mijina ya cika
masifa, mijina kaza yaushe Hausa Fulani suka koma haka? Wallahi tunda nake yawon
aure aure, ban tab'a kawo kara gida ba, sabida bana son Kowa yasan damuwata, sai
dai idan kunje kuga halin da nake ciki. Ban tab'a ganin zamani ne cike da mamaki
kamar wannan zamanin ba.

Kun mai da rayuwar Freedom kamar yadda kuka tsarawa kanku. Kun mai da aure kamar
takalmi, wai har budurwa zata baki shawara bayan ita bata zauna da namijin ba,
kunsan falalar da Allah yayi mana, toh ku barshi a haka karku what man can do,
Woman can also do it, wannan kamar kunyi fito na fito da yar Allah ce, kina da uwa
kina da Uba, kina da yan uwa, ki zaɓi abokin shawarar ki karki kaiwa kowa kukanki
sabida Akwai Allah.. rayuwar mu da ban mamaki take, wai sai kaji ana ce maka
maganin mallaka, Yes kiyi maganin gyara, amma duk Wanda yace miki, zai baki maganin
mallakar miji, karya yake miki domin ko kin same shi kwana biyu, zai lalace kuma
zai ci Ubanki, karki yarda kawarki ta kawo miki wani abu dan mallakar mijinki,
domin cutar dake zata yi babu wani mallakar shi da zaki yi.

Idan baki mallake shi ba, ita zata mallake shi ta aure miki shi. Kuma a
zauna lafiya, babu yadda kika iya.

Kince baki son kishiya ba laifi amma ki sani dole yayi aure, domin idan bai yi
ba, zai bi matan layi, kuma zai kwaso miki damuwa, babu yadda kika iya.

Uwar mijinki, Allah sarki uwar miji. Har ulcer ake ce miki, zunzurutun
rashin kunya da mutunci, kin mai da mahaifiyar mijinki da yan uwan shi abokan
adawarki, toh my Sister karki manta kema uwace, iya haka ma ya ishe ki, kamar yadda
kika hana shi kyautatta mata, haka d'anki zai auri yarinyar da zata miki, kuma baki
da abinda zaki iya, sabida rashin adalcin da kika nuna mata.

Na rasa gane wani irin kyashi da Hassadar da take damun mu, bamu kaunar muji
mazajen mu zasu kyautata yan uwansu, take kishi da bakin ciki zai motsa kin tab'a
tunanin kema kina da dan uwan namiji abinda kika yiwa wasu shi za a miki, mata muji
tsoron Allah, zamu mutu mu tarar da Ubangiji, mu girmama auren mu, mu cire cutar
kai da hassada mu rike auren mu da kima.
Maza kuma kuji tsoron Allah, baka auri mace dan ta rike kanta ba, wallahi muji
tsoron ganuwar mu da Allah, domin duk wanda ya auri mace yasan ci da shan ta yana
wuyar shi, amma sabida rashin amana ka sauke ƙana jiran danginta su kawo maka ka
cinye kuma kabi yarsu da zagi da cin mutuncin, shin idan aka yiwa Yarka haka zaka
ji dadi? Zaka yi farin ciki? A'a kawai dai ka auro mace kayi ta gana mata azaba,
daga karshe kace kai ba zaka zauna da ita ba, sai ta biyaka kudin da ka kashe, anya
kana tuna bayanka kuwa? Toh idan barci kake ka farka, tuni. Domin kuwa idan ka sake
Allah ya kamaka da hakkin wulakanta aure, sai kayi DANASANI mara amfani.!

Karku manta da wasiyyar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, idan yace
yafita hakkin mu, ya zo

Please Login or Register in order to submit comment