You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya d'ago kan shi, yana kallon umma sannan yace.
"Ina haka ma ya kinyi magana Umma nasan ba zaki tab'a taya Anum kishi ba, tunda
kece kashin bayan aurena da Hajjon, don Allah kiyi hakuri"

Sai taga no matter how, ta tsaya tana fada da surukinsa, mutum min da ya kasa
tsayuwa ya daidaita kan shi da ita, haka ya bata girmanta na Uwa, murmushi tai
sannan tace.
"Ayi ta hakuri wata rana sai labari!"
Daga haka tayi mishi sallama, tana komawa gida ta kira Abubakar tace maza ya nimo
mata masu furniture azo a gyara na Anum.

Yace to suna zuwa..
Tunda ya shiga cikin gidan, da kan shi ya fara gyara falonta wanda zaka rantse ya
shekara dari babu gyara, tana share kwalla tana gyara cikin d'akinta, zuwa ban
d'akinta, babu inda ba a shiga ba a cikin dakin, bata kuma kuka ba sai da ta ga an
mata wulakancin na fitar hankali kayan akwantinta na aure da na fadar kishiya an
watsa mata ruwan b3t cikin shi ta zuba gwiwar ta a kasa tana kuka.. har yana jin
muryanta.
Shigowa yayi kowa wani zani ya d'aga ya sai ya rididige.

Haka ya maida ya rufe yana bata hakuri, sallamar ya Abubakar yasa shi fita, suka
shigo aka duba kujerun, tare da kayan kallonta da aka kona, anan Ya Abubakar yayi
fada sosai, da sassarfa ta fito daga dakin ta,

Da sauri ta isa gare shi tana kuka, tare da gaya mishi abinda aka
mata, hatta kayan sawarta sai da aka lalata su. Anan Abubakar ya fara fada, wallahi
karku ga yadda hankalin maude ya tashi.

Nan ya shiga bashi hakuri, dukda maude kusan sa'an Aunty Binta ne, amma haka ya
saukar da kanshi yana bawa Abubakar hakuri, bayan tafiyar su, ya tattara
lalatattun kayan ya kai dakin shi, sannan ya fito.

Dakin hajjo ya shiga..tana barci bata san ma Anum ta dawo ba, dan a tunaninta
ta tafi kenan..
Jan kafarta yayi take ta bude idanunta.

Ganin yadda fuskar shi a tanke, tashi tayi zaune.
"Hon...."
"Daga Ni sai ke a gidan nan, waye ya lalatawa KHADIJAH kayanta?"

"Ni....Ni...Ni.."
"Tambayar ki nake?" Ya daka mata tsawa,
"Wallahi sharrin shaidan ne!"
"Toh tattara ki koma gidan ku, zan nime ki. Iyayen Khadijah sune suka tsaya min na
aure ki, yau kayan Khadijah kika lalata, hatta frij ɗinta, meye yayi zafi shi ba
wuta ba?

Mijin ta kika aura zaki nuna mata kishinki yafi nata, ban da dalilin me ƙarfi ce
miki aka yi ina sonki ne? Itace macen da na fara so? Ko wadanda na bari babu wacce
na aureta da sunan kaunarta kawai na auri kowacce ne da sunan zab'in iyayena. Ita
kuma zab'in raina ce, zoki fita min a gida."

Kuka ta saka tana bashi hakuri ya fita, dawowa dakin Anum yayi, ya same ta
tana kuka sosai, shi yana zaune a cikin gidan bai tab'a sanin anyi wani mugun abu
ba, asalima hankalin shi baya kan kome. Dan haka ya yi ta bata hakuri ko zata wuce.
D'ago kanta tayi tare da zuba mishi ido. Sun jima kafin ta dauke kanta bata yi
mishi magana ba, ta mike tare da cire kayan jikinta, yaga yadda bulala suka kwanta
a jikinta, tasowa yayi tare da rike hannun ta, kukan da ta saka ne ya sashi
sassauta rikon da yayi mata, yana kallon hannunta, wanda ya kumbura sosai. Rike
wuyar hannunta yayi....
🤔🤔 Anya ba zamu saka a gurguje ba? Dan na gaji wallahi....
#Mai_Dambuje
[2/4, 10:23 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA TALATIN
"Ka rabu dani, tunda aka iya zuba min ruwan b3t a kayana gaba Ni ce za a nemi
kashewa,"

Tana fadar hakan ta mike zuwa ban daki, ta sake fashewa da kuka ganin yadda aka
lalata mata kome nata, babu abun amfani.

Tunda ta shiga ban dakin yake kallon kofar, ya rasa yadda kome ya lalace
haka, mik'ewa yayi tare da shafa kanshi ya nufi waje ya sami Hajjo a tsaye tana
kuka, ita a tunanin ta wani farraku aka musu, ita da shi. Bayan tabargazar da suka
yiwa Anum hatta firj ɗinta babban su da aka fasa silindar gas din, anyi mata barna
ga satar da aka mata.

Bayan ta fito ta kuma gyara d'akin, tsaf sannan ta shiga store ta ga
kayan da aka kawo mata, durkusawa tayi ta fara kokarin ajiye kome a muhallin shi,
sannan ta dibo dankalin turawa, ta fere. Tare da doya tayi aikin su.

Namar da malam ya kawo mata, ta yanyanka a choping bot, tana gamawa ta wanke
kamar yadda taga umma ta dibo kayan kmshi da albasa ta gyara sanan ta zuba bayan ta
kunna gas din.

Ta daura miyar ta, bayan ta duba taga akwai kayan miya, idan ya sayowa hajjo yana
kawo mata na, tana aikin amma kuka take sosai, domin ban da rigar jikinta babu
kayan da zata saka.

Haka hada miyar ganye kuma babu ganyen, komawa d'akinta tayi tare da
niman wayarta ta kira Rulwanu ta gaya mishi tana son ganyen miya, alayahu. Bayan
minti goma sha biyar sai ga Maude da kanshi ya kawo mata, koda ya mika mata kin
amsa tayi tare da dauke kanta, kamar ba zai ajiye ba. Kuma sai ya ajiye mata, ya
saka kai ya fita. Bin bayan shi tayi da kallo, wasu fitinannun kwalla suna kuma
sauka mata.

Bata san me zata yi ba dan maude ya rabu da ita ba, amma tabbas tana cikin
damuwa da tashin hankali. Dan haka bayan ta gama hada miyar ta kuma daura tuwon
shinkafa, tayi kome dan dai-dai, sannan ta yi kunun gyada, tayi abubuwa da yawa, da
jera tare da kaiwa d'akinta ta ajiye. Dan tana gudun kar a sake mata wani abu.

Wanka sallah tayi tana kallon kayan jikinta, bayan ta zuba ta gumi, wani
kaya zata saka. Kwalla ne ya zubo mata, tana jin kamar tayi ta kurma ihu.

Dan haka ta cusa kanta a tsakanin cinyoyin ta, tana kuka kamar ana mata
mutuwa, yana shigowa yaji sautin muryanta. Jikin shine yayi matukar sanyi.

Tsayawa yayi a bakin kofar ta,. Har ya kai hannun shi handle din kofar kamar
wanda aka ce ya juya ya fasa, shiga dakin ya koma falon shi yana me dafe goshin sa
bayan ya kwantar da kan shi a kujeran.

*ANUMULLAH!"
Ya faɗa da dan karfi, ji yaƙe kamar son zuciyar shine ya sanya shi ta faɗa cikin
wannan yanayin. Ajiyar zuciya yayi sannan ya juya yana kallon kofar falonta..
kitchen yana kallon yadda take tafiya a hankali kamar wacce kwai ya fashe mata a
cikin ta.

Nan kuwa zunzurutun zazzaɓi ne da yake damunta, sabida tsamin da jikinta yayi
sakamakon dukar da aka mata, a gurguje tayi gyaran kitchen ɗin sannan ta fito,
hango shi tayi har ya shiga dakinta. Ban daki ya shiga ya sami koma fashe wankar da
da tayi ma da buta tayi, fita yayi tare da kallon agogon d'akinta. Sannan ya fita.

..... Dab za a sha ruwan sai gashi dauke da babban baho wanka da
kayan bukata dai na banɗaki ya ajiye mata, sannan ya kalleta tana kwance, sallamar
almajiri yayi, ya amsa mishi sannan ya fita.

Mika mishi wani katon leda yayi sannan yace.
"Oga maude daga gidan su Anum aka bani na kawo mata."

"Toh kace mun gode." Ya faɗa tare da shafa kan yaron, ya koma cikin gidan,
bude ladar yayi, kayan shan ruwa ne da aka zuba shi a wani katon roba, dan haka ya
shigar mata dashi cikin ɗakin.

Tayi laushe kamar ba zata kai azumin ba, ya isa gurinta. Sannan ya d'aga ta
tare da saka mata pillow ta jingina.
"Anum! Waye yayi miji duka haka?"
"Wanda ka kai ƙara na gurin shi mana"
"A'a Anum ban kai karan ki gurin kowa ba;" dauke kai tayi tare da gyara zaman ta.

Ya bude baki zai magana aka kira sallah, ruwan zafi ya zuba mata a kunun
gyadar kamar ba zata amsa ba, kuma sai ta kai hannun ta zata masa, rike hannunta
yayi suna kallon juna.
Ofco's yaga soyayyar shi d'anye a cikin idanun ta. Amma me yasa take iya boye
soyayyar shi.

Bayan ya ganshi ƙarar a cikin idanunta, sake mata hannunta yayi ta fara sha,
kwarewa tayi yayi maza ya rike hannunta, yana murza yatsun hannunta. Cikin kulawa
har ta daina tarin. Sai da yaga tasha ruwan kafin ta samu ya sha nashi.
"Ina Matarka?"
"Ta tafi gidan su."
"But Why?"
"She deserve."
"Maude! Kasan me kace?"
"Ai nayi English ko?"
"Kwarai kuwa!"
Ta faɗa tana cizon lips dinta, murmushi yayi sannan yace.
"Toh nayi yaki da jahilci, har na kasa karasawa amma ina iya rubutu da tsintar wasu
kalmomin Faransanci da turancin nayi ƙoƙari ko?"
Ya tambaye ta tare da mata alamar da idanun shi,
Murmushi tayi tare da gyada mishi kai. A hankali ya haɗa kunun suna sha suna hira,
cike da kewar juna, duk da tana tsoron abinda haka zai kuma haifar wa, haka suka
gama sannan ya nufi masalacin Sheikh Aminu bakin kura.

Bayan ya idar ya saka kai zai dawo, suka gamu da yayan Hajjo. Gaisawa suka yi
sannan yace mishi.
"Don Allah kayi hakuri, nasan abin da aka yi bai maka dadi bane, tunda har ka iya
zama da yarinyar da kowa yasan bata sonka, aka zauna lafiya. Ita wannan kuma da ka
iya."

"Malam Adam, da ace abinda tai shi Anum take yi min wallahi zan sake ta! Ko ban
sake ta ba, zan turata gidan su. Malam Adam b'arnan da Hajjo tayi min ko Anum da
bata kaunata ba ta min ba, haba jama'a kayan amfanin Kishiyarta ta lalata kasan
asarar da tayi sanadiyar shi kuwa,bayan kayan auren Anum da ta b'ata.

Hatta kayan da iyayen ta suka mata sai da ta lalata su me tayi mata? Kishi
hauka ne? Don Allah kayi hakuri ta zauna zan nime ta da kaina."

Daga haka ya wuce abin shi. Ya bar yayan hajjo cikin damuwa, koda ya koma
gida ya same ta kwance jikinta yayi zafi rau, riko hannunta yayi zuwa falon shi.
Suka zauna duk da ba wani hira suke ba, abinci ya zubo musu, tace ta koshi dan
dankalin da tasoya ta kasa ci. Haka yayi ya mata hira, har barci ya dauke ta,
Shafa kanta yake, yana kallon yadda take barci, kamar wata yar mage.
Yana zaune tare da kallon tafsir din Malam Haifan har aka kira sallah,
kafin ya tashe ta. Shi kuma ya nufi masalacin.

A d'akinta tayi sallar isha da tarawee, tana idarwa a gurin ta bingire da
barci, yana Shigowa ya same ta a kasa rufe kofar gidan yayi sannan ya dawo d'akinta
ya ci abinci, ya koma dakin shi yayi wanka tare da shiryawa cikin kananun kayan
barci, ya dawo falon ya zauna.

--- Ya jima yana kallon tashar gidan tv har karfe sha biyu lokacin yaji
wani irin yanayi na kewar Hajjo, tashi yayi ya nufi dakin shi har ya kwanta ya tuna
bai kuma leka Anum ba, shine ya koma dakin, ya duba ta ya samu tana nishi zazzafar
zazzabi ya tirmushe ta.

Gyara mata kwanciya yayi, sannan ya haura gadon, taimaka mata yayi ya
cire mata kayanta, sannan ya dawo kitchen ya debi ruwan zafi ya je ya goge mata
jikinta, ya kai bahon ban daki.

Gyara kwanciyar ta yayi tare da kwanciya a bayan, yana matsa mata jikinta, a
hankali take mika saboda yadda jikinta yake matsanancin ciki, tausa yake mata har
ta daina, sannan ya cigaba da taimaka mata, bayan awa daya zuwa biyu. Barci yayi
gaba da ita, karon farko tare da Anum suna kwance jiki da jiki.

Shafa kanta yake zuwa bayanta, tare hura mata iskar bakin shi. Gyara
kwanciya tayi a jikin shi har da wani rungume shi tana kara mannewa a jikin shi.
Wani irin nutsuwa ce ta shige shi. Tare da da jin zai iya manta kome da kowa idan
har Anum zata bashi dama sun shimfid'a soyayya me tsafta.

Wanda duk inda ka zaka sai ka magantu akan su,. Da zata bashi damar haka da
sai an tambaye ta wani boka da malam ne yake mata aiki haka, domin zai manta da
past Future's din shi ya zauna da ita, ya manta da duniyar shi ya rungume
duniyarta..

Da ace zata bashi dama, da ya maida Ila cikin ahalin shi ita kuma ya
rungume ta, su boya daga iyayenta babu wanda zai kuma ganin su. Me yasa yake raye?

Saboda kaddarar shi da Anum, sake k'amk'ameta Turai yana ji kamar wani zai
amsa mishi ita, d'ago kanta yayi tare da d'ago kanta.
"Anum! Ina ta gudu! Ina gudun ceton rayuwata, Ina ta boye gobe na, Anum ki bani
damar na gaya miki waye ni. Ki bani dama na shimfid'a kaunar mu, mara iyaka.

Amma, nasan duk yadda naso na kasance dake haka bai zai samu ba,
sabida."
"Maudeeeee!" Tsigar jikin shi ne ya mike wanda ya haifar da mikewar gargasar jikin
shi, a hankali yaji yanayin halittar jikinsa ta motsa, a hankali yake biyar da ita,
tare da gaya mata irin kaunar da yake mata, a nutse yake kokarin gudanar da
sha'anin rayuwar auren su.

"Maudeeeee! Mama tace idan na sake wani abu ya shiga tsakanin mu, Allah ya tsine
min Albarka!" Ta faɗa muryanta na rawa, tare da kifa kanta a kirjin shi tana rizgan
kuka.
"Tabbas babu amfanin zaman mu! Ba zan iya zama dake ba, Kaunar da nake miki gaskiya
ce amma ba zan iya rabaki da Mahaifiyarki ba, Anum"

Rike kanta yayi, yana jin zafin zuciyarshi, itama hannunta ya kai tare da
rungume shi tana kuka, yau gata ga Maude. A sanyayye ya janye tare da saka kayan
shi ya bar mata d'akin, tun daga ranar bai kuma mata magana ba, asalima tana lura
da yawan mishi aikan da Umma take, karshe ta tsare Rulwanu da tambaya.
"Matar shi zai dawo da ita"
Ita a tunaninta ai Hajjo ta tafi kenan, ji tayi cikin ta ya cure guri guda, da
sauri ta juya ban daki. Kuka take irin na zafin kishi, amma sam bata tab'a tunawa
shi ma Ɗan Adam ne kuma yana bukatar nutsuwa da rayuwar shi.

Sunyi haka da kwana biyu, Hajjo ta dawo, lokacin har an gyarawa Anum kayan
falonta, na wutan kuma Maude ya sake mata wasu, deep freezan kuma aka gyara tare da
kawo mata abinta,

Zaman su da Hajjo kadaran kadahar, babu me shiga harkan kowa, maude ya hana
Hajjo shiga falon Anum, shi yake Bin ta d'akinta.

Zaman su babu wani abinda zaka iya gani kace ai ana karuwa, har aka
gama azumi akayi sallah, yan uwan Anum da malam sun mata kaya wanda ya ci Uban na
da, shima maude ya maida mata da kayanta, har yafi nada, a hirar da suke ne ya
tambaye ta gold dinta dan ya gani a wuyar Hafsat. Ta shiga kame kame, karshe yace
mata.
"Kin bawa yar uwarki ba! Kinsan me? Ba zaki gane yadda take cutar ki ba, idanun ki
a rufe suke."

Shiru tayi bata kuma ce mishi kala ba, haka ta fara zuwa inda ake bitar
darasin aikin hajji. Shi yake kaita ya dawo da ita, wani abun da yake bawa kowa
mamaki, idan ya kaita aka tambaye ta mijinki ne? Sai ta ce a'a ya rage mata hanya
ne.

Asalima bata kaunar ta gaya musu waye mijinta, ko maude ne mijinta, ranar
wata talata. Wata yarinya itama an biya mata tana zuwa bita, kawai ta haɗu da Maude
yazo daukar Anum.

"Don Allah ki cewa Khadijah mijinta yazo daukarta!"

Da sauri yarinyar ta shiga cikin jama'a tace.
"Khadijah mijinki yazo daukarki wanda yake kawo ki a mashin"

A kunyace ta mike tare da musu sallama, tana zuwa bata kalle shi ta juya bayan
mashin din ta haura yaja suka fita. Kuka take a bayan mashin din. Kamar wacce aka
zagi uwarta. Har suka isa gidan tana gaya mishi.
"Uban waye yace ta gaya musu, kaine mijina."
Ran shi ya b'aci sosai, kawai ya tsinka mata mari, tare da matse bakinta jikin shi
yana rawa.
"Idan zaki min rashin kunyar ki yarinya ki tsaya a kaina, karki yarda ki tab'a min
iyaye, lusarai sha-sha-sha, wallahi ban da girman Mahaifinki da na Umman ku, da yau
sai na nuna miki yadda nake, Ni ba sakarai bane. Nayi hakuri nayi hakuri, Khadijah
ba dai Arziki kuke nima ba, kije aikin hajjin ki dawo .

Ko kece autar matan duniya na gaji dake, bani da nutsuwa bani da kwanciyar
hankali. Khadijah duk wanda zai miki fatan Alkhairi da na Arziki bayan na wanda ya
jibanci soyayyarki ce, wallahi na rantse, ba zaki tab'a samun irina ba, ba zaki
samu wanda yayi hakuri na ba, Idan ina raye da kafar ki zaki zo niman Alfarma ta, a
lokacin zaki san waye *BANIJARE*" ya tureta tare da tsallakata ya bar gurin.

Cire kai tayi tana kallon su, yadda suka zuba mata ido.
"Karfe uku, kaina na ciwo sosai don Allah kuje zan kwanta gobe Ku zo zan baku
labarin da safe, karfe goma sha biyu, karku tashe ni, dan barci nake ji sosai"

"Kiyi hakuri Aunty Anum, hakkin Maude ba zai tab'a Barinki ki rayu cikin
salama da nutsuwa ba, kai ko da bai sake ki ba, wallahi baki ga kome ba. Yo wannan
rashin Imanin har ina? Mutum da lafiyar shi a hana shi kwanciyar da matar shi,
wallahi ji nake kamar nayi ta dukarki!"
Inji Fa'izah,
"Karki damu, zaki dake ni idan lokacin dukar yayi." Na fada ina dariya, domin gani
nake har yanzun ban zo inda ya dace su fahimci laifina ba.....

*Walle nepa sun kumdume mana wuta 😂Allah Nagode maka da kasa suka dauke wutar 31
Insha Allah gobe ko😂😹😸😺*
#Mai_Dambu....ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA TALATIN DA ƊAYA


Fita suka yi tare da cewa.
"Allah zamu tashe ki, dan jiya kman nayi hauka,. Ina ji kamar gari ba zai waye ba."

"Ai kunga gobe idan Allah ya kai mu sai ku zo da hantsi, zuwa karfe 10 na dare
Insha Allah na gama baki labarin ko?"

Na gaya musu, fita suka yi. Nima na shiga ban daki nayi alola tare da gabatar da
sallar nafilla. Har kusan minti talatin da biyar, sannan na kwanta. Ina kwanciya na
kasa samun nutsuwa, wani irin yanayi nake ji, me cike da faduwar gaba. A hankali
nake jin bugun zuciyata tana kara tsannanin ta, tashi nayi zaune kwalla na zubo
min.

"Wacce ƙaddara ce take kusanto Ni? Ya Allah na tuba, na kuma na tuba, Ubangiji
bani da kowa bani da kome sai wanda ka arzurtani dashi idan ka kuma amsar sauran Ya
Allah niyi laifi, ya Allah ka yafe min, Ni baiwarka ce me wanka cikin zunubai. Ya
Allah na tuba, ya Allah na tuba ya Allah tuba."

Shigowar Shukrah, bai hanani kuka na da tashin hankali, ji nake. Rungume ni
tayi tana kuka nima kukan nake, muna a gurin har aka kira sallah farko. Sannan muka
mike tare da gabatar da sallar raka'atun fijr, kafin muka zauna a gurin har aka yi
sallah asuba. Wani irin zazzaɓi ne ya rufe ni bayan nayi Sallah asuba.

---- karfe goma sha daya dai dai na farka sakamakon saka alerm da nayi, a
hankali na bude idanuna na zuba su a kan su, sun jeru kamar wasu masu niman gafara,
murmusa musu nayi tare da mik'ewa na nufi ban daki nayi wanka da alola, tare da
brush. Koda na fito same su har abin karyawa aka kawo min, bana jin dadin rayuwa
ta, a hankali na zauna tare da ɗaukar mai na shiga shafawa a jikina, ina yi ina ka
musu rai.. My Asadullah ne ya fado min a rai, murmushi na sake. Ina tuna ranar da
yazo ya same ni ina shafa mai, cikin rashin kunyar da ya saba min wai yazo ganin
ajiyar shi. Sauke kaina nayi Ni daya na. Sai dariya nake me hade da kuka.
"Am sorry! Ka yafe min Zakina! Ba zan kuma ba. Aliyu na, na tuba wallahi na bar
duniya da abinda yake cikin ta, ko a daji kake zaune zan zauna da kai, domin kaine
cikon mafarkina."

Badi'ah da tafi kowa ruwan hawaye, kuka take tare da cewa.
"Don Allah, Sadiya jeki dauko min wayana. Zan kira baban Khalid."
Da gaske fa take kuka, tare da kiran a Nimo mata wayarta, Yau tuba ya tashi (😂😹)

Tashi tayi tare da fita, daga d'akin. Ta sami sadiya a waje, ta amshi
wayar, ina jin yadda take kuka bayan ya dauki kiran, murmushi nayi, kai na a kasa,
na share kwalla da yake bin fuskana, tare da ɗaukar kofin tea na sha, har yanzun
ruwa tana maganin daudda, sabida surar nan da take birkita yan maza da gigita
duniyar wasu Mazajen yana nan, hip da Beautiful sexy body dina da yake ruda mutanen
da suka jefa ni cikin damuwa yana nan, kallon Cutie da dina nayi.
Murmushi nayi amma fa inside me, ina jin zafi da ciwon zuciya akan abinda a
jikina yaja min, lumshe idanuna nayi tare da tuna abubuwan da suka faru.

Dawowa nayi ka zauna akan gadon tare da nad'e kafana, sannan nace musu.
"Kun tashi lafiya?"
"Lafiya Aunty Anum."
"Toh mu Cigaba ko"

*Son Zuciya...*
Bahaushe yace son zuciya b'acin zuciya, lokacin da ya fita daga falona, ina jin
shewar Matar shi. Kuka ne ya kwace min tare da kifa kaina, akan babban kujeran
falon, ina kuka.
"Ba dama an kaiwa dodon igala wanda yake tsafi." Tare da fadar wasu maganar banza
akan iyaye na.

Da gudu na ficce daga falon, ta nufi tsakar gidan, na shake yar iska, na fara
dukarta ko nace muka fara dambe, na bura uban bala'i, dukarta nake ina juya ta,
kafin kace me ihunta ya cika ko ina tare da kiran niman taimako.

Babu shiri aka kira Maude, yana shigowa ya ga yadda nake gwara kan matar
shi, zuwa yayi ya raba mu da karfin tsiya, tare da dauke ni da sabon mari, ya
ingiza kai na cikin falona, a wulakance.

Tun daga ranar Maude ya bude babin wulakanta ni, a tunani na da kenan. Amma a
bangaren shi, wulakancin ya buɗewa Matar shi, domin yace mata tunda na iya kamata
da dambe, tabbas akwai abinda tayi min, dake sokuwa ce, fada mishi tai.

Ga baki daya mun hada mishi zafin kai, tsakanina da shi babu wani abu dad'i,
har zuwa lokacin tafiyar su aikin hajji. Allah sarki haka ya dauko U.S dollas. Ana
jibi zasu tashi dan yace matar shi ba zata bi motar da maza suke ja ba. Da kansa
shi ya dauke ta zuwa kano,.bata san me yasa ya nacewa wani irin riga me hula, sai
face mask domin lokacin a kano ake tashin alhazzain jahar Bauchi.

Tunda suka isa, yaki kai ta tashan jirgin saman, kasa hakura yayi, domin kamar
wani maganaɗisu, haka ya makale mata. Wani irin abu yake ji ya cika mishi mara, dan
haka ya matseta yana jin daga wannan yanayin shikenan, ya rasata kenan.

😹

Please Login or Register in order to submit comment