You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fada, ka rage mana aikin saka katin dubu daya
muyi mata fada, Baba ga Anum nan, duk fadin kasar nan da kewayar shi bata da dangi
da suka wuce kai! Bata da Uban da ya wuce kai, bata da uwar da ya wuce kai, Baba
muna niman Arzikin ka mai da Anum cikin iyalinka yadda ba zata yi kukan rashin mu
ba."

Kuka ne ya ɗan so hanata magana sannan tace.
"Baba, iyayen mu suna matukar kaunarta, amma kaunar da suke mata da Asadullah yasa
mun rintsa idanun mu, mun bashi ita. Don Allah Baba idan tayi mishi laifi ya dube
ta a matsayin Kanwar shi, ko kuma yar da zai iya tsawarta mata, ya mata nasiha. Don
Allah kar yayi fushi da ita.

Bata da hankali, ba zata iya gane tashin hankalin da yake ciki ba, amma idan
ya tuna mata nisan gidan da inda take zata Fahimci yadda ake rayuwa, Baba banda
aure da ya kawo ta, har abada ba zamu tab'a shigowa wannan babban zuri'a ba."

Kuka da kewar Anum yasa ta kasa magana, Aunty Rabi ce ta cigaba da cewa.
"Itace yar autar mu, mafi soyuwa a zuciyar iyayen mu, Kanwar da muka fi so, Baba ga
Khadijah nan, zamu tafi mu Barka da aiki da fama, ayi mata Uzuri idan tayi laifi,
dan mun san bata jin magana."

Matan Yayuna suma kuka suke, Sai Rulwanu ne da ya iso inda nake ya
zauna a gaban Liman. Yace mishi.
"Abokiyar faɗa tace, kuma kanwata ce, Shalelen Mama da Malam, Hasken zuciyar
Ummana. Daga karb'an da muka samu, na fahimci Allah ya kawo Kyautar Allah Cikin
Babban Ahali, Baba Insha Allah ba zaka tab'a samun ta da laifi ba, duk da dai ta
kasance mai kan tukunya dan bata jin magana, ta rena ni yanzun zamu ga wanda zaki
mishi renin hankali da tsaurin ido. Baba ga kanwata nan na mika maka amanarta duk
da naji Oga Maude yana cewa yana hanya. Amma haka ba zai hana mu, nuna maka soyayya
da muke mata ba. Ayi hakuri da yadda take Insha Allah. Nan da shekara me zuwa zan
zo suna."

Murmushi Liman yayi, sannan yace musu.
"Wallahi tunda nake ban tab'a ganin yan uwa masu kawazuci ba, gashi kuna ta bani
amanar yar uwarku, nan abu daya nake so da ita, idanunta su zame mata aikin su
gani! Kunnenta ya zame mata aikin shi ji, bakinta ya zame mata faɗan alkhairi,
zuciyarta ya kasance me taushi, idan tayi wannan abun babu wanda ya isa ya takata,
matukar ina raye."

Duk sai kansu ya daure, shi kuma yayi haka ne dan baya kaunar Asadullah ya cigaba
da fuskantar matsala daga matan shi, musamman yadda basu da hakuri, idan suka mishi
abu ya kamata ya samu inda zai tsuma ranshi yaji sanyi.dan haka yayi ta musu bayani
a dunkule.
"Kunga yanayin rayuwa da irin aikin shi na soja,yana bukatar mace me sanyi, ba
wacce zata zame mishi lalura ba, wacce a koda yaushe tana sanyayye domin shi, idan
tayi haka Insha Allah zata iya rike ragamar kome na cikin ahalin nan baki daya."

Haka suka bar shashinsa, a filin waje muka hadu dashi.
"Hajiya Binta! Toh gashi na ce a bari sai gobe ayi muku booking, don Allah kuyi
hakuri gobe ku bar garin nan."
#Mai_Dambu...

ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SITTIN DA HUDU.

*😔 Da Alamu dai wannan labarin so yake sai na kai saba'in Yaushe na fara free book
har haka 😕😒😏*

"Kayya amma dai da kabar mu,munyi tafiyar mu wallahi,ai mun rigada mun gama
kome."
"A'a don Allah, Aunty B karki tafi!"
"Wallahi tafiya zamu yi, ji min munafuka. Kina murnan an kawo ki gidan mijinki,
yanzun muyi"
"Aunty Binta, kinji shi ko?"
"Ko ba Aunty Binta ba! Yarinya anan zamu barki."
Aikuwa na sake kuka, tare da buga kafana a kasa, kallona yake yana rike da Hoor,
sai kallon yadda nake boye fuskana ina kuka.

"Tafiya kan sai gobe, Insha Allah" ya faɗa tare da kafe ni da ido,lekowa
nayi tare da jan mayafina nayiwa Rulwanu gwalo.
"Inji gwiwar tuzuru kafin Gwauro barna!"
"Kutt melesi!ina wasa dake? Ni sa'an kine, Abban Isma'il wallahi zan mata shegen
duka, kafin na bar garin nan."

"Oho dai tuzuru kawai an gaya maka tuzuru." Na fada ina karkada mishi harshe.
Aikuwa yaji haushi, sai gashi wai zai make ni, da sauri na koma bayan Aunty Rabi,ya
kuma biyo ni duk da suna fada, hango wasu kyawawan mata nayi, irin kyan nan suke
dashi me daukar hankalin, suna kallon mu. Garin tsayawa ina kallon a ina na tab'a
ganin su naji yana fadi.
"Aunty Safiya kyale ni na ji mata Kafin mu bar garin nan."
.yadda yayi maganar na fahimci suna tare tare dashi ne,da sauri na koma bayan
Dadda. Tare da buga kafana ina cewa.
"Don Allah boye ni, karka bari ya min kome"

Kasa motsi yayi sakamakon yadda nake kara rike shi ina dariya.
"Don Allah ku shiga cikin gida, ga su A'isha can ki tsaya ku gaisa dasu."
Lekowa nayi ina kallon su,.kafin nace mishi.
" Su din suwaye?"
Sannan na kalli inda suke, ashe ina zuwa bayan shi, su Aunty Binta suka kara
gaba. Fuskar shi babu walwala yace min.
"Mata na ne?"
Gaba nane ya fadi, na kura mishi ido. Shima ni yake kallo, a hankali na zare
hannuna daga cikin na shi, sannan muka jera.
"Kin razana ne da ganin su?"
Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Kai ina kawai dai ina musu kallon kamar na tab'a ganin su."
Har inda suke, muka isa. Ya bude baki zai magana suka yi tafiyar su a fusace.
Sharewa nayi maganar umma tana dawo min, amma kuma da ban mamaki,yadda suka mishi
dan bana ce ni suka yiwa ba. Rakani yayi har inda muke,

Da dare suka kuma rako ni, cikin gidan shi,shi kuma yana can gurin Dattijo,
tunda muka shiga gidan muke sallama babu wacce ta leko, dan haka suka wuce dani
shashina, sannan suka min nasiha, kafin suka sauko.. babu kowa a falon.

Bayan fitar su, ne suka jajjanta abun kafin suka shiga hada kayan su.

Har karfe goma sha biyu babu miji babu dalilin shi, dan haka ban yi
barci ba, na tashi na fara sallar dare, sai karfe biyu ina zaune akan abin sallah
ya shigo ranshi a b'ace, mik'ewa nayi tare da nad'e abin sallah. Sannan ya kalle
ni.
"Hmm! Baki kwanta bane?"
Girgiza mishi kai nayi, sannan nace mishi.
"A'a!"
"Ok mu kwana lafiya!"
Ya fadi haka tare da barin d'akin, bance mishi kome ba, dan bani da abin cewa.

**Washi gari.
Na tashi cikin natsuwa, amma akwai guntun damuwa a raina, kawai na adana abina ne,
na shirya cikin atamfar Vlisco riga da skirt, me ratsin ruwan hanta.

Farin mayafi na yafa sabida kayan akwai farin sirki, nayi karamin kwalliya
mara hayaniya.ina shirin fitowa ya shigo sanye da farar yadin material na maza,
fuskar shi babu walwala ya kalle ni.
"Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillahi! Ya ka kwana kai ma?"
"Masha Allah, Alhamdulillahi." Daga haka ya juya ya fita na bi bayan shi da
kallo,ina tsaye a inda ya bar ni, ya kuma dawowa da kudi CF ya ajiye min, su tuli
guda, sannan ya ajiye min wasu yan dubu dubu na kudin Nigeria.


"Me zanyi da su?" Na tambaye shi,
"Ki bawa yan uwanki mana,!"
Daga haka ya juya ya fita, haka na shirya ya fito, kallon shi nayi shida Daya matar
shi, wacce take kallon kofar dakina, ranta a b'ace.
"Ina kwana?"
"Dan ban kwana ba, zaki ganni!"
Kallonta nayi sannan na sunkuyar da kaina, ina son tuna inda na tab'a ganin su, har
na sauka kasa, kallona shi nayi tare da zuwa inda yake na zauna.
"Dadda!" Na kira sunan shi kamar yadda yaran shi suke kiran shi.
Zuba min ido yayi yana jin sunan har cikin jinin shi.
"Kina kina da matsala ne!"
"Ban da bakin jaraba, ai sai kiyi hakuri idan ya dawo girkinki ba."
"Esha!"
Ya daka mata tsawa, sunkuyar da kaina nayi. Sannan na mike zan fita.
"Anumullah!"
Ya ajiye kofin hannun shi bayan ya kirani.
"Jirani na kai ki, kuyi sallama." Murmushi nayi sannan na tsaya ina kallon yadda
suka juya harshe suna masifa, mai da kaina nayi ina kallon wani african magic,
wanda sune ta harshen faransanci..

Har ya gama abinda yake yazo ya sakani a gaba muka bata su. Tunda na isa
gurin su na zauna na karya, shima ya wuce cikin gidan su. ina karyawa ina kuka, sun
tambaye ne me ya faru bakie magana karshe sai da na basu haushi,kamar zasu doke ni.
Nace.
"Ni wallahi bana son ku tafi ne!"
Sake baki Aunty Binta tayi cikin jin haushi tace.
"Qaniyarki!"
Tayi min dakuwa, dakyar na iya karyawa, domin sun dake sai sun bani a baki, bayan
na gama ne suka kuma kara min nasiha, domin daga yanayin kishiyoyin da na samu, sun
san zanci kaniyar kaina, bayan sun gama min fada suka kuma ɗaukar kayan su, zasu
tafi anan ne nace ban ji ba.

Kuka nake tare da rike Aunty Binta, idan na kasa hakuri na koma kan wannan,
dukda abinda Hafsat tayi min sai da naso da yau zan ganta na yafe mata abinda tayi
min. Gabaki daya na hana su tafiya fa.

Dan shiga motar nayi, na zauna ina kuka. Wiwi.

Sun yi fadan kamar zasu dake ni, karshe suka kuma dawo suna rarrashina, ai
kuwa nayi tsalle nace ban san da haka ba, sai da Yazo gurin, yaga yadda ake yi
dani.
Bai ji haushi ba, domin abinda ya faɗa musu babu wanda bai yi dariya ba.
"Au ku har haushinta kuke ji? Bayan yaushe Anum ta daina kuka daga ita sai yar pant
a kofar gida ba zata ci ciwo ba."

Aikuwa suka saka dariya, dole na fito, tare da fadawa jikin shi ina kuka, kai
hannun shi yayi bayana, yana shafa bayana a hankali. Tare da cewa.
"Ke ko ina sai kin nuna, musu ke yarinya ce!"
"Ina ruwa na, don Allah kace karsu tafi"
"Toh uwar masu hankali, mazajen su da?"
Aikuwa na fashe da kuka, ina kuma rike rigar shi, tare da buga kafana a kasa, ni ba
zan yarda ba sai su tsaya, haka ya samu ya janye daga jikina, suna barin gidan na
saka kuka, kamar zan fasa ihu. Rike ni yayi lokacin da yaga na kifa hannuna akan
fuskana, ina shashekar kuka. Hannun shi ya kai kan cikina, tare da kai bakin shi
kunnena.
"Ki shirya! Domin kuwa aure kika zo yi ba tunanin gida ba!"
Daga haka yaja hannuna muka shige cikin gidan.

Tunda na shiga falon naga suna ta karyawa, tare da min kallon yarinya ce ko
nace yarinya ke damuna, haka na wuce ina kuka.
"Yarinta manyan kai kuma Ya Asad irin wannan ka dauko?"

Bai kula su ba, sai da yaga na haura sama da gudu ina kuka, sanan ya juya ya bar
min gidan, tun daga ranar ban kuma gane mishi ba,.kullum zai ajiye min kudin, dan
wancan kudin rulwanu na mikawa ya basu.

Amma wannan karon kullum sai ya ajiye min, babu batun rayuwar auren mu, zai
shigo ya tambaye ni, daga nan ya juya ya fice a dakin, abinci kuwa. Basu bani.

Gashi ban saba da kowa ba, dan ma Yan uwan shi suna shigowa na basu kayan
tsaraba, sannan muyi hira dasu.

Farisa da Safina, Matan Aasim sun shigo min. Tare da min wuni a ranar,.nayi
hira sosai gashi ban san me zan dafa musu ba, dan babu Kitchen a sama, cikin gidan
suka zo suka amshi abincin suka kawo min, tun daga ranar. Aka fara kawo min abinci.
Ban san me ya faru ba, ya shigo a fusace.
"Akan me zaki na amso abinci a cikin gidan?"
"Kayi hakuri!"
Na fada mishi kai na a sunkuye,sake magana yayi.
"Bana son munafunci da hada husuma, idan girki zaki yi,.ki sauka kasa kiyi mana!
Sai ki na zuwa kina amsar abinci har a kai karana."
"Kayi hakuri ba zan kuma ba!"
Na gaya mishi, kaina a kasa.
Tsaki yayi min tare da barin d'akin,
Ban ce kome ba, amma naji wani irin bakin ciki ya tsaya min a raina.
Washi gari na nufi kitchen zanyi girki na samu a rufe, murmushi nayi domin, kuwa
ban san me suke nufi da haka ba, ban damu ba. Na koma dakina na kwanta, kayan tea
na hada nasha, sannan na shiga kiran yan uwana ina jin ya suka koma, mun sha hira
dasu wanda kusan nasiha ce akan rayuwar aure.

Umma kan ba zan ce kome ba, dan tayi min nasiha sosai.
*** Sai dare ya shigo gidan ina jin motsin shi na sauko kasa da gudu, na fada jikin
shi.
"Ina kewar Rulwanu, ko na kira shi baya dauka. Don Allah ka kira min shi."
Ware idanu yayi yana kallon Sharifa da ta cika dam. Kasala ce ta sauko mishi tare
da wata gajiya mara iyaka, sauke ni yayi tare da cewa.
"Zan tura miki kati ki kira su."
Ya wuce zai tafi na bi bayan shi kamar jela ina sake mishi kananun magana, na niman
rigima between ni da shi. A gajiye ya kalle ni.
"Anum!"
"Dadda!"
Na kira sunan shi,
Share ni yayi, har muka haura zama, zan bi bayan shi naji an finciko ni, ban yi
aune ba sai jin saukar mari nayi akan fuskana.
"Kina mare ni?"
Sake baki nayi ina kallon makirci, kiri kiri.
"Anum!" Ya daka min tsawa,
"Rashin kunyar ki har takai ki marar min mata? Meye tayi miki? Ba tambayar ki nake
ba?"
"Wallahi!"
"Kiyi min shiru! Wuce dakinki"
Haka na juya na tafi ina sheshekar kuka ina rufe d'akina yana kifa mata mari. Ya
kuma kara mata,
"Nayi haka ne domin idan na karya taki a gabanta ba zata cigaba da ganinki da kima
ba, kin manta kofana yana da glass ne, ki mareta ki kuma mata sharri. Kun saka min
doka a gaban iyayen mu, karku tab'a min mata na, domin zaku ji a jikinku."

Kasa magana tayi dan bata dauka zai ga abin ba.
Haka ta sauka, abinda tana jin a ranta sai ta kuma marina,
Koda yayi wanka ina bukatar Anum, amma horon da yake mata yasa ya ajiye bukatrta
ya cigaba da aikin shi da yake a laptop.

--- haka nayi kuka har na godewa Allah,.na rasa waye zan gaya mishi, haka na
kwanta duk sa yunwa da nake ji.
Dakyar nayi barci.
.....
Da safe suna karyawa na fito na nufi kitchen, na fara kokarin niman abinda
zanci.
"Uban me zaki mana a kitchen?"
Shiru nayi tare da kallon ta.
"Ba tambayar ki nake ba?"
"Don Allah ki daina damu na." Na gaya mata tare da hada abinda zan ci. Kawai kashe
gas din sannan ta watsa min ruwa a cikin abinda zan dafa.
"Ya Asad!"
Ta kwala mishi kira,
Kwalla ne ya cika min idanu, yana shigowa cikin harshen buzanci ta gaya mishi
abinda nayi mata.
"Wai Anum me yasa baki jin magana ne?"
"Kayi hakuri!"
Tsaki yayi sannan ya fita, nima fita nayi na same shi ya kasa cin Abincin shi,
kallon shi nayi, sannan na haura sama abuna. Dan ban ga amfanin.....
#Mai_Dambu......
[2/21, 11:15 AM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SITTIN DA BIYAR.

"Ina abincin ta?"
Kafe shi da idanun A'isha tayi, tare da cin abincin ta,
"Ba tambayar ku nake ba?"
Ya kuma daka musu tsawa,
"Ya Asad"
"Tambayar ku nake?"

"Toh waye bawanta da zai mata girki, tunda ta iya kwana da namiji girki ne ba
zata iya ba?" Inji Sharifa,
"Me yasa kuke niman hanyar da zata rena ku? Idan ta fara muku na yarda zan
hukuntatta, amma me yasa kuke azabtar da ita da yunwa?" Ya tambaye su,

Cikin ko inkula suka cigaba da cin abincin su, mikewa tayi ta dauki nashi da tea
din ya bi bayan Anum, tsaki Sharifa tayi da karfi. Cak ya tsaya, kafin ya wuce bai
musu magana ba,

Ina kwance ya shigo d'akin, zunzurutun yunwa, ji nake kamar ba zan iya kara
awa daya ba, ajiye min abincin yayi, sannan ya fita, can sai gashi da tulin kudi ya
ajiye min, ganin har zuwa lokacin ban kalli Abincin ba, ya sashi zama kusa da ni,
ya d'ago ne ni.

Tashi nayi zan bar gurin shi, jiri ya nemi yar sar dani, da sauri ya tare
ni.
Kuka nasa mishi tare da rike rigar shi gam, idanuna a rufe.
"Meye haka?"
"Ka kai ni gurin Umma na, zan mutu da yunwa."

Na fada ina ƙoƙarin mik'ewar, shima mikewa yayi, tare da kai hannun shi dukka biyu
baya na,
"Bana son damuwa, ki zauna kici abincin."
Wani irin kuka ne ya kuma kwace min, ina girgiza kai tare da rike shi gam, ina buga
kafana a kasa, tare da sake shi ina kuka.jirin da ya kuma dibana ya sashi rike ni
sosai,

"Kiyi hakuri kici abincin."
"Don Allah ka kai ni gurinta ba zan zauna ba"
"Toh naji."
Zaunar da ni yayi, tare da mika min tea, kamar mahaukaciya haka na shanye tass,
sannan ya kuma mika min Farfesun kayan cikin rago. Karnin namar ya sani ji kamar
zanyi aman tea din, na ajiye mishi.

"Kici."
"A'a, bana son shi"
"Me zaki ci?"
"Gurin Umma na zaka kai ni."
Na fada tare da sake kuka,
"Baki da hankali ne? Babu inda zaki."

Mik'ewa yayi abin shi ya barni cikin kuka,yana sauka ban san me ya faru ba, sai dai
naga an turo Kanwar shi Rafi'a kirana.
Babban hijab na saka har kasa.

Sannan na nufi gidan, tunda muka shiga babban falon Liman. Naji Sharifah tana
kuka, A'isha kan kasa magana tayi, shine yake magana.

"Liman a nan kuka ce tunda naje can ba zan raba musu kwanaki ba, sai tayi sati
biyu! Naji kuma na dauka, me yasa zasu mata horon yunwa? Sannan kuma idan tazo
girki su tadda husuma? Gidan su ko Gidana ga Sharifah nan da ranta akan idanuna ta"
d'aga mishi hannu liman yayi, Shiru kowa yayi.
"Ai inda ranka kasha kallo, kayi magana ace ana fifiko, ke Khadijah kizo nan kina
amsar abinci, shi kuma ki bar musu shi, ki zubawa Sarautar Allah ido.kiga yadda
karshen munafukai zai kare!" Kakan su Ta faɗa tana yarfe hannunta.

"Dijimah! Danyi hakuri na kammala wannan yanayin." liman Ya fada kallona.

"Kin karya?" Gyada kai nayi,
"Me yasa baki dafawa da kanki?"
Sunkuyar da kaina nayi, duk yadda naso rike kwallar idanuna sai da suka shiga
sauka.
"Khadijah! Ana cutar ki ne?"
Ya kuma tambayana, rike baki nayi cikin kuka nace.
"A'a ina son komawa gida ne?"
"Toh shine kike kuka?"
Gyada mishi kai nayi. Shiru yayi sannan yace.
"A duk lokacin da yaro ya bukaci iyayen shi, toh inda yake yana fuskar damuwa ce,
A'ishah da Sharifa meye kukewa Yar mutane?"
" Liman me zamu mata banda munafunci irin nata, girki ne dai babu shegen da zai
mata." Inji Sharifa,

"Toh yayi kyau!"
Ya faɗa,
Kare mana kallo yayi, sannan yace.
"Daga yau kabawa kowa hakkin shi, karka yarda ka tauye wata dan wata, sannan
karabawa kowa key din kitchen ɗin, idan wata ta miki rashin kirki ki rama, idan ba
zaki rama ba, ki kawo min karar su. Kai kuma ka zama namijin duniya a gidanka."

Daga haka Kakar su ta rike hannuna muka shiga cikin d'akinta, abinci ta
shiga jera min.

Haka na ci na koshi sannan tace min.
"Kin samu ganin Mamar ku kuwa?"
"A'a bai kai ni ba!"
Kura min ido tayi sannan tace min.
"Kamar na sanki? Da jimawa"
Dariya nayi sannan nace mata.
"Tunda naga Sharifa na tuna da mun tab'a haduwa a aikin hajji."

Aikuwa muka balle da hira, a hankali muke hira, tare da gaya mata lokacin ai da
auren shi nazo, bayan komawa muka samu saba'ni, gashi na kuma dawowa rayuwar shi
karo na biyu.
Nasiha tayi min tare da nuna min dole na jajjurce akan mijina ba kuma nuna
mishi nima mace ce, su kuma wadancan lusaran nayi tsayin daka kar a manta da azumi
da sallar dare, tare da azkar. Kar nayi wasa da lahaula!

**
Tunda aka yi magana shi kenan, na sami sauki. Amma a ta bangaren ai babu sauki,
sannan ya raba mana kwana ɗaya rak, haka ya zaga kansu. Ranar da zai shigo d'akina
ya ajiye min kudi yayi tafiyar shi gurin aikin shi.

Ganin baya nan suka kuma ɓullo min da Iskanci, har kofar dakina suke zuwa zasu
dake ne.gasu ba kananun mata ba,.balle na biye musu.

Ban tab'a gayawa kowa nawa ba, amma na barshi sai ranar da Maude ya shiga
hannuna zasu Fahimci dalilin shigowa rayuwar su.
Idan na shiga nayi girki bana fita sai na gama, domin ina kuskura na
fita zan samu an kashe gas ko an zuba min ruwa a cikin abincin. Dan haka babu wani
abun da zanyi dan na rama.

Kallon su kawai nake, ina kwasan ilimin kishi. Sai da yayi sati Uku. Sannan
ranar friday ya dawo.

Dan a tunanina d'akina zai sauka yasa na wuni ina aiki, abin har mamaki yake
basu, yadda nake ta hawa da sauka, Hoor ma ban ganta ba, sai da suka shigo gaishe
ni, sannan nace taje ta kira min Rafi'a. Dake idan nayi girki ina saka musu, su
kaiwa Innarmu.

Shima sai da aka ririta alamarin aka kai karana, gurin Liman, ban san ya akayi
ba, dan shima ina kai musu abincin, sai ji nayi ana sake min habaici da bakar
magana, nazo da asirin Nigeria, na mallake tsoho me adalci.
Ban kula su ba, haka na cigaba da rayuwa na, ina tsaye Rafi'a ta shigo na mika mata
nasu, sannan nace mata.
"Ga nasu Dijimah, zan haura sama da na yayanku ne ko zaki dan jirani na kai na
dawo."

"Karki damu ina jiranki"
Haka na kwashe abincin na haura dashi, sannan na dawo na samu suna fada da
Sharifah, da yaren su.
Dan haka nayi tsam da raina duk yadda aka yi tazo b'ata min abinci ne, dan haka na
kwashe sauran nace mata.
"Ki kai musu naso!"
"Mun gode!"
"Ba kome!"
Ina haurawa na shiga ban daki, ina cire pant naga bako na yazo, shiru nayi, sannan
nayi wanka. Doguwar riga na saka tare da zama nayi kwalliya.

Kallon kai na nayi kawai na cire kayan na saka wani doguwar gown mara
hannu, kallon agogon d'akina nayi, nasan yanzun zai shigo tunda anyi isha.

Fitowa nayi, na kefawa kofar gidan ido, ina jiran shi.
Yana shigowa na sauka da gudu, na rungume shi, tare da sumbatar kumatun shi da
goshinsa.
"Barka da hanya? Ka dawo lafiya!"
"Baki san zaki karya ni ba?"
"Ayya Daddaaaaah bani da nauyi fa!"
"Don Allah da gaske?"
"Sosai kuwa!"
Na fada ina dariya, amsar jakar shi nayi, muka haura sama. Dakin shi na bude naga
ba a kintse ba, juyawa nayi tare da kallon shi.
"Ko zaka bani aron dakinka na minti arba'in! Sai kayi amfani da nawa"
"Toh!"
Haka na kai shi d'akina, bayan na saka mishi ruwan wanka, sannan na fito, sai da
na wanke kome na ban dakin shi na wanke har da gajerun wandon shi, sannan ba kuma
hada zanin gadon na fito dashi, kayan shi na nima mishi masu kyau da rashin nauyi.
..na shigo mishi dashi d'akina,

Yana fitowa daga ban daki kwanciya yayi, yana jirana. A kwance na same shi. Ina
shiga na dauki mai na fara shafa mishi, tashi yayi zaune.
Yana kallon yadda nake kokarin shafa mishi mai,
"Ki gama ki bani abinci yunwa nake ji!"
Da sauri na gama kome na mike tare da jera mishi abincin, sauka yayi ya fara
kallona. Fuskar shi ba a sake ba.

Zuba mishi abincin nayi,.ya fara ci. Sannan na mike zan bar gurin yace min.
"Yaushe kika fara al'adar ki?"
"Yau;"
Dauke kai yayi, ya cigaba da cin abinci juyawa nayi ina duba jikina.
"Ba anan na gani ba? Audugar da kika ajiye na gani,"
Ajiyar zuciya na sauke sanan nace.
"Ai!"
A hankali ya gama ci, Ni kuma na bude show

Please Login or Register in order to submit comment