You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dani yayi tare da zuba min ido.
"Kin sami danginki, kin manta da Ni?"
"Ban manta da kai ba, gani nayi kana da wasu matan zasu iya kome."
"Mata na daban ke daban, Anum bana son kina hana ni sakewa dake, sai nayi ta ganin
ko har yanzun baki sona ne!"
"Ina sonka mana, kawai kar mu wuce iyaka ne!"
"Naga kinyi wanka jinin ya dauke ne?"
"A'a bai dauke ba! Kawai dai na wanke kai nane!"
Daga haka bai kuma magana ba, ya daura min kan shi a kafada na, rike shi nayi.
Sabida yadda yaƙe birkita min lissafi.

Wasa wasa sai da muka raba dare, sannan na bar dakin shi bayan naga barci ya
dauke shi. Ina shiga dakina na samu yaron yana hannun Umma, a sadadde na shigo.
"karki kuma bijirewa bukatar mijinki akan wani dalili can."

Sunkuyar da kai nayi ina wasa da zoben hannuna. Sannan ta mika min Asil na bashi
nono, sannan na kwanta. Washi gari suka gyara min namar da aka yanka tare da
soyawa.

Suka kintsa min gurina, bayan suna suka tattara kome na, sannan, suka
bar kasar da dinbun alkhairin Mijina.

A hankali nake kula da Yarana, tare da samun goyan bayan mijina, dan ma
Aadheen yana gurin Sharifa, karshe shima sai da A'isha tayi dalilin da aka dawo min
da yaron sabida hada su fada da tayi da Aliyu.

Fada sosai, har ya nemi dukarta sai da na shiga tsakanin su, nace mishi.
"Kana niman shekaru hamsin amma har yanzun ka kasa Fahimtar meke faruwa a cikin
gidan ka, sanin kanka Sharifa ba zata cutar da kai ba, balle d'anka.

Kishin da take dani, ban tab'a ganin shi akan Aadheen ba, amma ka d'aga hankalin
ka, ka dawo min da shi, kiyi hakuri Allah zai saka miki."

"Rashin kunya zaki min? Karki ga mun tara yara dake kice zaki min rashin
mutunci, wallahi sai na baki mamaki."
Ganin yadda yake niman kawo mana tashin hankali ya sani baki daya, na ajiye mishi
Yaran shi, tare da ɗaukar kudin da yake bani na hada kayana. Na fara saukowa daga
sama da kayan, ganin da gaske nake, ya sashi rufe kofar gidan,

Aikuwa na tubure mishi, sai na bar gidan, abinda ya daga mishi hankali
kenan, ya rasa wanda zai dakatar dani, karshe ya kira Innar shi, tace babu ruwanta,
ya san inda dare yayi mishi.

Da ya sami Liman shima yace babu wani abinda zai iya, gaba daya suna juya mishi
baya, kamar zai yi hauka, dan haka ya kira Umma, ya gaya mata. Itace ta kira ni
tayi min fada sannan na hakura.

Lokacin da muka cika wata biyar anan ya dauke mu,. muka zo nigeria,
ganin gida. Haka muka zaga dangi da yan uwan, har lakwaja muka je,,

Bayan mun yi sati biyu muka dawo Bauchi, muka je har badara, da Dewu.

Muka yi sati Uku, sannan yazo ya kai mu Umma, muga Hisham, tunda muka isa
gidan su. Dadda ya kasa ya tsare shi nan kar na sake baki nayi ta dariya, sai na
kame kaina ina kallon shi.
Haka koma masaukin mu, ina sauke Asil ya ajiye Asif, nan yaja tare da cewa.
"Na lura har yanzu Ban miki yadda zaki daina kwadayin wancan mutumin ba."
"Kaga ni bana son zargi, waye ya gaya maka ina kaunar Ibrahim banda zuciyarka da
bata maka adalci, ka duba cikin idanuna kaunar kace zalla, amma kullum baka da aiki
sai na korafin wani. Gani ka cinye ni, idan ka sami abinda ya rage ka barni haka."

Sanyi jikin shi yayi tare da rungumo ni, sai lokacin na sami damar sake kuka,
na rasa yadda zanyi da Maude kishin tsiya ne dashi. Tunda yaga na mishi bori ya
kyale Ni haka, yaran kan A gidan Ibrahim muka Barsu, sashe shima yazo wani taron
Ecowas ne dan haka muka yi sati biyu anan Abuja sannan muka dawo Bauchi, anan muka
samu har an wuce min da tsarabar da aka mana,

Kwanan mu biyar muka wuce, Riyadh, gurin Isma'il. Inda na same shi yayi kyau yaron
ya kara girma, kallon shi nake gwanin ban sha'awa. Idan yana Hausa kamar ba
bahaushe ba, larabci ne akan harshen shi, sai da muka zo masauki na rike hannun shi
nace mishi.
"Me kake son nayi maka bayan Alkhairin da kai min Asadullah?"

Murmushi yayi min, sannan ya kashe wutar dakin, ya shiga kashe arna tare da
karatun zungura da raruka.

. bayan mun shiga Makka munyi umra da Isma'il din da yake gaya min ai Dadda
yana zuwa duk karshen wata uku, kallon Shi nake ina mamakin shi, yadda yake rufe
min kome, yayi kai tsaye.

...... Tun lokacin da naga Hafsat zuciyata ta karaya, domin shi alkhairi da
sharri suna tafiya akan turba daya ne, kuma idan suka yi abinda zasu yi suna dawowa
ne, dan haka abinda ka shuka shi zaka girba.

Haka nayi ta mata addu'o'in a dakin ka'aba, bayan mun dawo daga gurin
Isma'il, ina renon Yarana, mijina yana kuma kara sake min ragamar rayuwar shi.

Wani irin kauna yake nuna min , Sharifa kan babu ruwanta dani, dan haka A'isha
face dai ta daurawa kanta damuwa akai na.

** Matar Ahmad ila, yau muka tashi da bakin labarin Allah yayi mata
rasuwa, dan haka. Bayan anyi jana'izar ta a can gurin aikin shi, anan aka yi zaman
makokinta.

Kasancewar Ni nake kula da abubuwa da ake girkawa ya sani fara tsanar kamshin
albasa, da kayan miya ta fashashe, ina jin tiririn shi zan fara kokarin amai.

Lissafin da nayi yarana watan su goma cif, tsoro ne ya kamani, dakyar aka yi
sadakan bakwai dani, ana gama zaman makoki na fara laulayi.

Kuka nasaka mishi ina rokon shi don Allah muje a cire cikin, ya kafe sai na Haifa
mishi. Dan haka na nufi gurin Liman na gaya mishi, shima ya kira Asadullah aka yi
magana yace.
"Tsoho shekaru na hamsin cif, Allah ya dube ni da idon rahama ya bani haihuwa sai a
cire dan kawai akwai wasu a hannun, ba zan zama butulu ba, tayi hakuri gaskiya
gidana babu inda za a dakatar da haihuwa, wallahi banki ace dukkanku uku kuke
haihuwa ba, dan haka kiyi hakuri ki haifa mana shi kinji."

Bayan sun rarrashe ni ashe, har an gama bazani a cikin family na cika haihuwa
kamar akuya. Bayan kwana biyu matar Mubarak ta haihu muka shiga Barka shine nake
jin ana gaya min magana.
"Wasu matan yadda kuka san akuyoyi, sabida dadin aci Arziki ana d'aga bujen su, sai
ciki."
Suka kwashe da dariya, murmushi nayi yadda suke fadar maganar har da A'isha a cikin
su, daura daya ayi akan daya, nace musu.
"Ai dadin gindi yasa kullum bunsurun ku yake barbaran yar akuyar shi, shi yasa wasu
dake gindin su bata da dad'i kuma bata iya fitar da kan d'a ba, suke niman hanyar
kashe yar akuya, so ni bani da damuwa da ku saboda ina da Taure a kusadani kuma ya
iya cin mace a tsanake har sai yayi mata ciki, wasu kuwa sun manta da Allah keyi
shi yasa suka turoni daga saman step dan na zama tarihi, haihuwa kuwa ba zan tab'a
dakatawa ba, sai ba jerawa Aliyu Asadullah yara goma sha biyu cif da Yardan
Ubangiji sannan zan huta meye amfanin gindi idan ban bashi yaci ya kuma min ciki
ba."
.ina fadar haka na mike abuna na Barsu da kallona baki dake...
*Ko ban gaya muku ba, Next page Insha Allah zai zama ƙarshe*
#Mai_Dambu
[2/22, 9:07 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SABA'IN.

Karhe 😜

"Dama yarinyar nan ta iya bakar magana, kaji shegiya mara mutunci. Har mu zata gaya
mana mara daɗi. Wallahi sai mun gayawa Asad yayi mana waje da shegiya" ina nasan
suna yi,

Bayan sallah Isha, kawai ya shigo min yana huci, ko kallo shi banyi ba na
cigaba da bawa Yarana abinci.
"Har ke kin isa kiyiwa mutane gorin rashin haihuwa? Toh bari na kwashe sai ki
cigaba da musu."

Haka yayi ta masifa ban kula shi ba, sai da zai tafi min da yarana nace
mishi.

"Wallahi karka kaiwa ko wacce shegiya kayana, wato ga mara hankali, na zauna na
cigaba da kallon su suna zagina, wallahi ba zan yarda ba ko kai ka zage ni sai na
gaya maka magana, kuma ka ajiye min Yarana tunda a gindinsu fito."
Na fada da karfi, kamar yadda nayi haka ya saka kai ya fice min da Yarana, kam Uban
can.

Haurawa sama nayi tare da dauko hijab dina, na sauko lokacin ya shigo gidan,
kallona yayi sannan yace min.
"Ina zaki?"
"Gidan Mahaifina ka rike Ƴaƴan ka, sabida nasan Rabon sune yake dawainiyya da ni,
zan.."
"Kinga Khadijah bana son tashin hankali idan Ƴaƴanki kike so zan dawo miki dasu
amma ba...."

"Kasan Allah, na gama zama da kai." Wasa wasa har su Sharifa suka fito, juyawa
nayi, zan haura sama yace min.
"Don Allah kiyi hakuri, mu sassanta" ban kula shi ba na haura da gudu, kamar
zautacce ya biyo ni da gudu, haka muka yi ta bala'i a sama, karshe fita yayi ya
dauko kakan shi. Dakyar suka shawo kaina, sannan na hakura.

Yarana aka kawo min su, na cigaba da abinda yake gabana, bawai dan ina da dadin
dandano bane, a'a kawai mun kai matakin da dole a rayuwa mu zauna da junar mu, kuma
ko ba kishiya dole zan zauna da mijina, kuma ya zama wajibi nayi hakuri da halin
shi, balle kuma kishiyoyin da suka zama dole na zauna dasu.

Dama dan shi nake dauke kaina, toh wannan karon da na sami.damar zama a gidan
dindindin. Rashin mutunci nakewa Aishan domin tana yi min zan mata, na kuma gaya
mishi idan zai zauna da Sharifa kishinta a fili yaƙe,

A'isha kuma munafuka ce, bawai na kai tsaguminta bane, kawai ya gaya mishi ne
musamman yadda yake kushe Sharifah. Dan ko yanzun da muke shiri da ita idan kishin
ya motsa mata kiri kiri take gaya min yau bana son ganinki da mijina,

Murmushi nake mata kawai nace mata.
"Yau kishin ya motsa kenan?"
Murmushi kawai take min, idan na ga haka toh bana kuma sakewa na shiga harkanta,
domin tana da zafin kishi wanda sai tayi kwana uku bata min magana ba. Sai idan
abun ya saketa tayi ta niman yadda zamu daidaita..

Koda wasa bai sake min ragamar shugabancin gidan shi ba, amma yana matukar
sauke hakkin mu.

*** Cikina yana da wata hudu, na tashi ina son zan daura abinci, ina saukowa
na gansu cirko cirko. Kallon su nayi sannan na kalle shi yana zaune ya dage
goshinsa.
"Gadanga kusar Yaki lafiya?"

Kallon Center table din gaban shi, nayi naga ai kunun tsamiyar da nayi ne
d'azun na sha kadan sauran akan idan na tashi zan sha. Kai hannuna nayi zan dauka
yace min.
"Ajiye Anum! Akwai kwaya a cikin kunun!"
Kallon A'isha nayi wacce jikinta yake rawa.
"Wai meye ya faru?"
"Hmm! Sharifah ce ta dauki hoton A'isha tana zuba miki kwaya a cikin kunun,da nazo
nace mata meye ta zuba a kunun tace babu kome Sharri aka mata. Anum can you image
maganin zubda ciki, ta zuba a cikin kunun?

Sannan badan Sharifah ta dauko min hoton ba, wallahi da itace zata ce ta zuba
miki, kuma na zarge ta akan itace bata kaunarki. Anum A'isha tayi abubuwa dayawa
wanda na boye miki, amma Sharifah wallahi ina da yakinin ko kyankyaso ba zata iya
kashewa ba.

alhamdulillahi nagodwa Allah da bani na zalince ki ba, kije Allah ya hada ki
da rabonki na Alkhairi, zan zauna da Mata na wanda suka kasance *RABO NA NE*"
Ya mike tare da fita daga gidan, ya sami Kakan su, yayi mishi bayani sannan ya sake
ta zama saura igiya biyu ne, dan haka ya karasa sauran igiyoyin, sannan ya kawo
mata. Kamar Mahaukaciya haka take rokon mu, tare da rike kafar mu.. wallahi duk
yadda kaso ka ɗauke kanka sai kayi kuka sabida tabawa Talatin da takwas baya wajen
arba'in yau ace miji ya sake ki akwai tashin hankali, sanan ya sake ki da tabon
zata zubda mishi cikin matar shi.

Lokaci guda muka shiga hankalin mu, ni da Sharifah, ganin zaman mu baya karan
mu da kome muka shiga islamiyya, wanda ake a cikin masallacin gidan, har da Aishan
muke haduwa nan ta dauki sabon tsanar mu, wai mun hade kai mun saka an sake ta.

Kuma ba kome yaja mata haka ba, sai mugun nufinta.

Bayan na haihu na kuma samun namiji, inda aka saka mishi Suna Abdullahi, a
lokacin aka zaka bikin Rafi'a da Ahmad ila, muka sha biki, bayan nasu da wata shida
nazo na Rulwanu, da wata yar uwan Umma suke Ganjuwa. Sai tsiya suke min wai na
zama uwar maza ga kunika ya amshe ni.
Tunda nazo bauchi naso nayi tsarin iyali amma ban iya yi ba tsabar
tsoron kar wani matsala ya biyo baya, haka na hakura, muna nan muna shan hutu
Alhaji Hamisu Natsira yazo niman yafiya ta, akan abinda yayi min.

Nace na yafe, Mudi kan yana can gidan shi ba a cewa kome,domin yaran da ya
tsafe su, sune suka yi ajalin shi, dan haka Aliyu ya boye Asalin Isma'il. Domin
yadda ya nunawa kowa dan shi ne, idan ka matsa ne zai ce ya aure ni da goyan shine.

Na samu labarin mutuwar Salmanu Adam Firo, ya rasu sakamakon jinyar da
tacinye kafar shi.
Ibrahim da Yaron shi sun zo bikin Rulwanu, zamu tafi dinner haka
Aliyu ya hanani tafiya, ya tattarowa Umma yaran da Maman Aminu, ya kai ni cikin
gidan shi, wallahi sai da nayi danasanin amsa gaisuwar Ibrahim, dan baya kishi da
kowa kamar yadda yake kishi da Ibrahim. Tunda ya sani a daki yake abinda yaso dani.
Da ya bani haushi nace.
"Tsohon kawai,.dalla kyale ni na fita, bana jin dadin jikina ka isheni da jaraba"

Haka ya cigaba da turmushe ni, sai da ya ji dan kanshi sannan ya kyale ni,
anan na kwana Abdul yana gurin Umma na, da safe aka kawo min shi, muna kwance Aka
yi mana sallama, tashi nayi na bude kofar. Hajjo na gani, murmushi nayi sannan na
bude mata kofa ta shigo, sannan na shiga dakin ta taso shi ya fito. Suka gaisa.

Anan suka tab'a hiran yaushe gamo, har take gaya mishi inda tayi aure yaranta
uku yanzun,
"Allahu Akbar! *RABON* Shi ne ya raba mu fa, kinga da Allah ya nufa *RABO NA CE*
Anum gashi har da yara biyar, Dan haka mu godewa Allah da yasa ka babu *rabon
Ajali* a cikin mu sai *Rabon Alkhairi* "

Haka suka yi ta tattaunawa, sannan zata tafi ya dauki kudi ya bata dan ko bata fada
ba tana cikin wahala, washi gari yasa aka kira Mishi mijinta yayi mishi alkhairi
sabida ita, yasa aka saya mishi napep yayi mishi barazana akan koda wasa yaji
labarin ya karo aure zai bashi mamaki dan ya bashi keken ne sabida ita, kuma babu
amfanin bata mora ba.

.haka yasa ya amsa, Mijina mutum ne me yawan alkhairi, dan haka nake godewa Allah
da ya bani shi a matsayin mijina, bayan aikin gwamnati babu abinda zan ce yake sai
kasuwanci sosai yake yi,

Bayan mun gama hutun, muka dawo gida, anan ya kawo min Isma'il, wanda ya
zama ɗan saurayi, ba laifi yazo yayi min kwanaki ya koma.

*** Bayan shekara goma.
Zuba mata ido nayi yarinyar da na haifa yar autana, ji nake kamar na fasa ihu, ta
saka tuwo a gaba tana kuka, yar shekara biyar.
"Wallahi bazan ci tuwon nan ba, idan naci Allah ya tsine min." Tayi kwallon da
tuwon.
Zama nayi ina kallonta, ni dai a shekara goma, na tsani tuwo.

Amma Maman Aminu karama Hauwa ta tsani tuwo, ga shagwaɓe kamar me, idan aka
hanata abu kafewa take zata yi, yayunta maza basu da abinda take yi, asalima suka
tsorona bakamar Abban su da Mame dinsu ba, wato Sharifah.

"Don Allah idan ba zaki bata wani abincin ba ki ce tayi hakuri mana,"
kallon Sharifah nayi sannan nace mata.
"Wallahi bazan bata hakuri ba, dan qaniyarta na kamata sai na fasa jikin ta" aikuwa
haka ta fice da gudu tana ihun Wayyo Allah zan ta mutu, karshe suka haɗu da Jamal
dan gurin Addah Rufaidah ya kaita gurin Innarmu taci shinkafa.

Bata dawo gidan ba sai dare da Babanta wanda ya biya ta dakin Innarmu ya daukota,
tayi barci. Yarana maza takwas, mata biyu. Bayan Abdullahi da Muhammadu Bello, da
Alhassan da Alhussain, na kuma na kuma haihuwar yan biyu, maza, sukan an bar musu
sunan su ne, sai Aliyu d anayi, da Muh'd Aasim, sai auta ta, Ha'uwa.

Wacce muke kiranta Khairat, ina kasuwanci sosai, ake shigo min da kaya ta nan
maradi.

*A'isha tayi wani auren babu dad'i haka tayi ta fuskarta matsala,, nan ta
hanamu sukuni taje can kishiyar tace ita ba zata zauna da kishiya ba, ta tasota a
gaba, sai da auren ya mutu sannan hankalinta ya kwanta, nan ta fara zawarcin mijin
mu, muka ce bamu yarda daba. Tabi wani sarkin ba namu ba.

*** Wato wani abinda na Fahimta a iyakan rayuwa, yarda da ƙaddarorin
masu kyau ko marasa kyau,.nayi hakuri da ƙaddara, domin idan Allah ya haɗaka da
Maman Aminu a matsayin Uwa baka ramin tashin hankali bane, sai gashi na amsheta
hannu bibbiyu, na kuma yi hakuri da ita.

Bayan nan hakkin miji, idan Allah ya tashi kama ka, dashi ba zaka ji da dad'i
ba, wallahi na fahimci duk abinda ya faru dani da hakkin Aliyu, sai hakkin Yar shi.

Sai na gaba bakin Mahaifa, masiface babba, duk wani takadiri a duniya zaka
samu yana tutiya da sawan albarkan Uwa, Ni kuma sai na fuskanci ciwon bakin Uwa,
wanda yaja min watangaririya a rayuwa ta.

Sai wani abu da zan ya kiran shi Na gaba *KAUNA* wannan shine linzamin da na rike
zuciyar Aliyu dashi, ban da shi babu abinda zai ja min Aliyu ya dawo rayuwata.

Addu'o'in mahaifina da tsayin daka da Umma tayi akaina, sune Mabudin
canji rayuwata, wannan yanayin da Malam ya barni da shi Allah ya amshi bakin shi ya
maidani tauraruwa a duniyar mu, ya kuma karawa min daraja a gidan Aurena, wanda
nasan hakuri da juriya suka dawammar dani a gidan mijina.

Idan kayan mata yana hana ayi Iskanci wa mace toh Aliyu shi zai baki, kudi har da
na kayan mata, idan kika yi tasty dayawa yace miki kinyi zaki dayawa, karku kuma
shan maganin, ko idan ya gama rayuwar aure dake yace miki baki yi yadda yake so ba.

Kayan mata ana shan shi ne, dan gyara zama bawai dan kiyi yadda kike so da mijin
ba.

Dan haka karki yarda ki sake mutumin kirki da yazo miki da Alkhairi ki kama
na banza, shi rayuwa akan tsarin Ubangiji yake wani bai isa ya ture wani ba, dan
haka muyi hakuri da abinda yazo mana, Allah yana son mu ne yake bamu dama ta biyu.

Tarbiyyar Umma na samu shi yasa wani shashin rayuwata ya boya ba tare dangin
Aliyu sun san nayi wani mugun abu a waje ba, nayi kokarin koyawa yarana Kaunar
junan su, yadda idan wane baya nan sai an nimo shi.

Ko Khairat ce tayi laifi na make ta, dukkan su suke kuka har Hoor, bana son na
koyawa yarana Irin wahala da nasha a rayuwata, akan makauniyar soyayya..kuma naki
na bar Khairat a matsayin auta na, dan kar na cutar da ita, Uban ne yake kiranta da
Auta.
Rulwanu ma yaran shi uku, idan muka.hadu sai munyi halin...

Mijina ya ajiye aikin soja, yayi kokarin fadawa siyasa, muka hana shi, dan
karya zama bai da lokacin mu, Ashe hana shi da muka yi Alkhairi ce, domin kuwa sai
gashi an tura shi jakadar Nijar a kasar Germany, haka muka tattara muka koma can,
soyayya me tsafta da kaunar juna muke, yarike mun Yarona. Haka kuma Hisham.yana
zuwa min hutu.
Alhamdulillahi
*Adda Ramlat kinji labarina, kuma kinji gwagwarmayar da nayi, wasu abubuwan ma na
manta, masu muhimmancin na iya rikewa, shi yasa da naji ana magana akan Safinah ta
masarautan Jordan tana da daurin kai, dariya suka bani sabida banga taurin kai a
gurinta ba, dan nice matattarar taurin kai, Alhamdulillah gashi na baki labarina
kicewa mutane suyi hakuri haka labarin faru da yar uwansu mace, shi yasa ya tafi a
hankali.*

_Nima Nagode da kika bani damar na rubuta labarinki, Gashi nan salon labarin
😜
anata daukaInji wata wai don Allah tana son Ganin hoton ki da Abban Isma'il_

_Hhhh! Ki rufa min asiri, wallahi mijina yana da kyau daidai misali, ina
tsoron kar yan mata suyi crushing din shi, dan wallahi kishine dani, kice ina musu
fatan Alkhairi 😢Nagode sosai zanyi kewar su_

*Toh mai karatu anan na kawo karshen Labarin ANUM KHADIJAH MUH'D BELLO.... Allah
ya hada mu a wani labarin Insha Allah! Muji wata Chakwakiyyar ce a cikin shi.
Alhamdulillahi Nagode sosai masu daukar salon labarin ku Cigaba bani da salo amma
ina da Chakwakiyya 😜😂 zalla 👌🏼 idan kin shirya mu hadu A Daula biyu*

Masu son sayan Daula biyu... Ga damar shi. Me kike yi har yanzun baki saya
ba....kusan bana Allah ya isa bana zagi.. amma akwai mita 😜Idan kin karanta
masarautan Jordan, Bahaushiyah, Magajin Izzah, Ruwa biyu, Matar so! Wai Casss....
Mu hadu a wata badakalar. Amma don Allah nafi son ku biya ta bank ₦200 babu tsada
bani da VIP.... amma zan baku labarin da ku kanku baku tsammani ba.. Please kuyi
payment ta bank, idan kuma katin mtn 300₦ ne,
Acct: 0472282105
Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK! +2347035133148

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment