You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babba kamar iya.

"Ta ja hannunta ajinsu, ta Waukko wani Wan kwano ta bata abinci, aikuwa hannu baka hannu ™warya ummi take danna abincin."

"Na'ima ta dubi ummi ta ce ""Ya jikin amma dai kin warke ko?"" Ummi ta Waga mata kai alamar eh."

"""Gashin ya fara fitowa?"""

"Ummi ta saka hannu Waya ta buWe mata kan, Na'ima ta rufe mata ta ce ""Masha Allah, ya fara fitowa, kin wanke kayanki na makarantar boko?"""

"""A'a yaya magaji ya saya mini sabon uniform na makarantar boko"" ta faWa cike da jin daWi."

"Na'ima ta ce ""Alhamdilillah, Allah ya saka masa da alkhairi, na bayar a Winka miki atamfar bikina"""

"Ummi ta kalleta ta ce ""Biki, aure kenan?"""

"Na'ima ta ce ""Eh, aure zan yi ko in tafi da ke gidana?"""

"""Eh yaya Na'ima zan biki dan Allah"""

"Na'ima ta ciro Wan ™aramin tsumma a jakarta da ruwa a jarka, ta bawa ummi ta sha, sannan ta shiga goge mata"

"hannu ta ce ""Zan so ace za a bani ke na tafi da ke ummi, sai dai hakan ba zai yiwu ba, ki je aji idan an tashi ki jirani mu tafi tare, zamu je gidan mansura, an kawo mata takalma daga Kano, idan da wanda zai yi miki, sai na saya miki na biki"""

"Ummi ta ce""Ba zaki tafi da ni ba?"""

"""Ki yi ha™uri ummi, ba zai yiwu ba"""

"""Kema tafiya zaki yi ki bar ni? Mama ma ta tafi ta™i dawowa"""

"Na'ima ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Maza je ki ajinku, ga malam can ya tafi"" ta mi™ar da ummi tsaye, ummi ta tafi ajinsu."

"Naja da take ™awar na'ima, ta ce ""Ke dai ki na son yarinyar nan naima, gashi kin saka mata ran tafiya da ita"""

"Na'ima da hawaye ya taru a idonta ta ce ""Wallahi naja ina tausayin ummi sosai, wallahi da za a bani ita zan Wauke ta,"

"kakarta matsiyaciyar tsohuwa ce, ai babarta uwar Wakina ce, mun yi mutunci sosai, baban ummi ya rasu, ta koma garinsu, Kakarta ta ™wacw ta take azabtar da ita, ko a lahira na ganni gani g matar nan na san ban yi kyakkyawan ™arshe ba"" Duk da a ™ufule Na'ima tayi maganar, bai hana naja dariya ba, saboda maganar ta ta ™arshe ta bata dariya."

"Bayan tashi daga makaranta, tare suka tafi da ummi, hannunta cikin nata suna tafe tana yi wa ummi hira, tana"

"bugun cikinta, dan jin zaman da take yi, sai dai abun babu daWi mussman da ta gaya mata abun da su auwwalu suka yi mata, da aka yi mata aski."

"Na'ima ta ce ""Bakomai Allah ya isanki wallahi, duk wanda yayi nagari kansa,. Ki yi ta ha™uri kin ji ummi, duk tsanani"

"duk yunwar da ki ke ji, kar ki bari wani a mazan gidan ku, manya ko yara, su kai ki wani wuri, su saka hannu a jikinki, kin ji ko?"" Maimakon ummi ta amsa sai ta Waga kai tana kallon na'ima."

"Cikin sauri na'ima ta tsaya ta ce ""Suna yi miki wasan banza ko?"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""A'a"""

"""Ki gaya mini gaskiya, suna taSa ki ko?"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""A'a"""

"""Duk wanda ya saka hannu a cikin jikinki, kar ki yadda kar ki tsaya, ki yi masa ihu ki gudu kin ji ko"" ta jinjina mata kai"

alamar eh.

"""Ko bayan na tafi, idan kina jin yunwa, ki je gidanmu wurin babarmu ta baki abinci"""

"Da haka suka ™arasa gidan mai takalmi, aka yi sa'a aka samu dai-dai ™afar ummi."

"Na'ima ta ce ""Zan ajiye a wurina, ranar bikina in yi miki kwalliya ko?"""

"Ummi ta Waga kai tana murmushi, daga nan suka ™arasa gida."

"Ummi ta shiga gida hannunta ri™e da wani kara tana wasa da shi ""Ke!"" Idris ya kwaWa mata kira a wula™ance."

Ta juyo tana kallon sa.

"""Zo ki sayo mini sukari a kanti"" yayi maganar yana watso mata kuWi."

"Ta dur™usa ta Wauka, ta je ta sayo masa, sai dai ta din ga tuna gargaWin Na'ima na hanata zuwa Wakin su idris."

"Ta nemi wuri ta zauna a ™ofar shiga wurin, ya gaji da jiranta ya fito."

"""Dan ubanki ina aiken da na yi miki?"""

Da sauri ta mi™e tana nuna masa sukarin.

"""Ba zaki shigo ki kawo mini ba saboda baki da mutunci, sai ki nemi wuri ki zauna?"""

"Tayi shiru tana kallon sa, ""Ba zaki kawo mini ba"" ya sake yi mata maganar cikin tsawa."

"Ta ™arasa in da yake cikin jin tsoro, sai dai ya ya haWa da hannunta, ya ja ta cikin Wakin."

"Kuka ta fara yi masa iya ™arfin ta, yau ya samu damar da rabonsa da ita an daWe, amma ta nuna masa tayi wayo"

"yanzu, dan haka ta din ga yi masa kuka da ™arfi, kamar yadda Na'ima ta gama gaya mata Wazu."

"Wawan marin da ya kifa mata ne, ya tafi da ji da ganinta na wani Wan lokaci, ta dafe kuncinta jikinta na wata irin tsuma, tana karkarwa."

"Wata sharSeSiyar wu™a ya nuna mata ya ce ""Ki ka cigaba da yi mini kuka, sai na yanka wuyanki"" kallonsa take yi, kallo mai cike da tsoro da tsana, ya ajiye wu™ar tare da sanya hannayensa cikin rigarta, rigar da bakomai a ciki sai"

teSa dan wannan dai ba nono bane.

"Ba ta karaya ba, ta fara kokowar cire hannayensa daga jikinta, tana kuka mai cin rai, iya ™arfin ta."

"BankaWo ™ofar Wakin aka yi, hakan ya razana shi, dan bai yi zaton zuwan wani a dai-dai wannan lokacin ba."

"""Idris meye haka?"" Hashim yayi maganar yana kallon sa."

"""Kamar yaya meye haka, abun da ka gani"" a fusace ya ™arasa ya hankaWe idiris, ya janye ummi, ya kalli idiris ya ce ""Wani irin banza ne kai, ba zaka girma ba a rayuwarka, da me yarinyar nan za ta ji ne?"""

"Wani uban tsaki idiris yayi, ya ce ""Ka daina shiga sabgata ba ruwanka da ni""."

"""an shiga sabgar taka, wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba, sai na Wauki mummunan mataki a kan ka"""

"""To ka Wauka mana kar ka fasa"" ya sake jan tsaki ya fice."

"Cikin ™unar ran yadda ™aninsa ya raina shi, duk saboda iya na goya masa baya, ya kalli ummi ya share mata hawaye,"

"ya fito da ita daga Wakin, shaidar yastun idiris kwance a kan ba™ar fuskarta, da har idonta yayi taruwar jini."

"Ya zubawa ummi ido, da haryanzu jikinta yake tsuma, ga wata irin nannauyar ajiyar zuciya da take yi, har a lokacin a"

"tsaorace take, kuma hawayenta ya ™i tsayawa."

"""Ummi"" ya kira sunanta, sai dai bata amsa ba, ta sake fashewa da kuka."

"Wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, ya din ga share mata hawayen, ya ri™e hannunta suka nufi sashin iya, tana ta"

dakan fura tana wa™e-wa™e.

"Tana ganinsu tare ta hau bala'in tun Wazu take neman ummi, zata aiketa amma daga zuwa makaranta ta zauna."

"Magaji ya ce ""Iya"""

"""Ya aka yi"""

"""Dan Allah idan ba za a iya ri™on yarinyar nan ba, a mayar wa da uwarta ita, idiris fa na kama yana neman haike mata a Wakinmu, wace irin rayuwa ce wannan, kalli yadda ya mare ta, haba dan Allah"""

"Iya ta dafe ™irji ta ce ""Shi idiris Win? Ita uban me ya kaita in da yake, me ya kaita Wakin ku, ai ita ta kai kanta, amma"

"shima zai zo ya same ni, da ni yake zancen. Kai kuma sai ka ce ba Wan uwanka ba, ka ke Waga murya tona masa asiri zaka yi?"""

"""Iya to zuba masa ido za ayi, idan abun da ba a so ya faru fa?"""

"""Ba abun da zai faru sai alkhairi, jeka zai zo ya same ni, ke kuma canza kayan ki zo ki kai dusar nan gidan lami, ta"

"bawa dabbobina"""

"Hashim ya ce ""Ni bani dusar na kai, kalli yadda take a razane"""

"""Ba wani a razane, da a razane take ai da ba ta kai kanta ba, yarinya ™an™anuwarta da ita, ta san ta je wurin namiji"""

"""Haba iya, me ummin ta sani da zaki faWi wannan mummunar maganar a kanta?"""

"Iya ta ce ""Zaka zo ka kai mini dusar ko ta Wauka ta kai mini?"""

"Ya ™arasa ya Wauki dusar ya fita, zuciyarsa kamar ta tarwatse, tausayin yarinyar na damunsa sosai da sosai."

"Kwanaki biyu tsakanin abun da ya faru, sannan idiris ya shigo sashin Iya."

"Iya ta dube shi ta ce ""Idris, kashedi zan yi maka a kan yarinyar nan, kar ka kuskura ka sake saka yarinyar nan a loko"

"kana lalubeta, wallahi idan ka sake wani abu ya afku ba zan rufa maka asiri ba, kuma ba zaka janyo mini masifa ba, kai gashi ba sana'a ba balle ace ayi maka aure, in huta. Ina yi maka kashedi, wallahi wani abu ya faru ba zan saurara maka ba, na gaya maka"""

"Cikin fushi ya ce ""Me kuma na yi, magaji ne ya zo ya ce na yi mata wani abu?"""

"""A'a ni banga magaji ba, bai gaya mini komai ba, fuskanta kawai na yi"""

Ficewa yayi ba tare da ya sake magana ba.

"Rashin samun biyan bu™atar sa a jikin ummi, ya sanya ya ji ya ™ara tsanar yarinyar, ko son ganinta ba ya yi, ita kanta"

"ummi, har fargaba take yi a aike ta, saboda bayan iya ta yi masa wannan faWan, sai da ya zane ta, saboda a zaton sa ita ta gaya wa Iya."

"Duk wannan cin kashin da ake yi wa yarinyar, daga ´an uwan ubanta da suke ciki Waya, da wanda uba suka haWa da matayen su, babu wanda ya taSa shawartar iya a kan sassautawa ummi azabtarwar da ake yi mata, tamkar ´ar"

tsintuwar da ta faWo daga sama.

"Azumi saura wata biyu, aka yi bikin na'ima, ta yi kuka sosai, ciki har da na rabuwa da ummi, dan har cikin zuciyarta"

take jin rabuwa da ummi.

"Mariya kuwa tun ´an uwanta na ta tata, suna rarrashin ta, suna bata ha™uri, har suka zubawa sarautar Allah ido"

"suka ™yaleta, ta riga dai ta kamu da larurar hawan jini, a hankali kuma ciwon damuwa ya fara addabar ta, kullum tana Waki, daga bacci, kuka sai shiru."

"Yaya Wan lami ya fara tunanin ko ta koma makaranta, amma yanayin da take ciki, ya tabbatar masa da ko an mayar da ita makarantar ba za ta iya mayar da hankali ba."

"Dama labarin haihuwar ta ta ko su iya ba a gayawa ba, dan gaba Waya sun fuskanci sabgar Iya babu Allah a cikinta."

"Yaya Wan lami kuwa da suka ga mariya ta™i sakin ranta, ya ™are mata cin mutunci, tare da tabbatar mata da muddin"

"ta je wurin su Iya babu su babu ita, ´a ce idan ta girma da kanta za ta neme ta."

"Watan azumin ramadana ya kama, wanda hakan ya sake jefa ummi tsaka mai wuya. Ba iya azumi take yi ba, dan"

"haka babu mai kulawa ya bata abinci, haka za ta yi ta gararanba ta wuni a kwance, idan makaranta ta je, tana kallo yara na ciye-ciye, ita ba raSar su take yi ba ma, balle ta yi musu kwaWayi, ko kuWin makaranta ba bata ake yi ba, dan haka bata saba da kashe-kashen kuWi ba."

"Sai an sha ruwa take samu ta ci abinci, sai da hashim ya fuskanci ba ta samun abun da za ta ci da rana, shi ne yake rage mata abincin sa, da safe ya bata, da rana ya sai wani abun ya bata. A haka har aka ™are azumi."

"Da salla kowane Wa cikin kyakywar shiga mai kyau, ummi kuwa kayan bikin na'ima ta saka, da suka fara koWewa, da"

"takalmin makarantar da kawunsu ya saya mata, shi ta koma tana sakawa tayi yawo da shi a gari, saboda ko silifas ba ta da shi, wanda naima ta saya mata tuni ya lalace."

"Yara na ta shiga su na fita, ummi kuwa na ™ofar Wakin mamanta, ta zauna tana wasa da duwatsun wurin."

"Hashim yayi sallama, ummi ta amsa cikin ´ar siriyar muryarta."

"Ya ™arasa in da take zaune, ya ce ""Kin je sallar idi ne?"" Ta girgiza kai alamar a'a."

"""Me ki ke yi a nan wurin?"""

"Ta ce ""Bakomai"""

"""Kin ci tuwon salla kuwa?"""

"Ta ce ""A'a iya dai ta ce zata bani"""

"Ya mi™a mata hannu ya ce ""Taso mu je"""

"Ta saka hannunta a nasa, ya ja ta zuwa sashin mahaifiyar sa."

"Babansa ma, da ake cewa baba sagir, yana zaune yana cin abinci."

"Ummi ta dur™usa ta gaishe shi, ya amsa mata babu yabo ba fallasa."

"Ya ce ""Yaya a zubawa ummi abincin salla dan Allah"""

"Ta ce ""Ga maimuna nan, ya zuba mata"" ta kalli ummi ta ce ""Ke ummi baki da kayan salla ne, ki ka saka wannan"

"koWaWWiyar atamfar?"""

Ummi tayi shiru tana kallon ta.

"Aka kawo wa ummi abinci, ya saka ta wanke hannunta, ta zauna ta saka tuwon sallar nan a gaba tana ci, tana yi tana"

kallon yadda yara suka yi kyau sosai a sababbin kaya.

"Ta gama ci ta hau tattara musu kwanukan wanke wanke, ta share musu tsakar gida."

"Hashim ya dawo sashin, ya tarar da ummi ta haWa kwanukan wanke-wanke."

"""Me kuma zaki yi?"""

"""Wanke-wanke zan yi""."

"""Ke yara na can waje suna tsalle-tsalle, suna wasanni, amma ke kina nan ki na haWa wanke-wanke, ki je ki yi wasanki"

"sa yi wanke-wanken da kan su"""

"""A'a bani da kayan salla, idan na fita tsokanata za ayi, su ce mini ba™a"" tayi maganar tana ™o™arin jan kujera ´ar"

tsuguno tayi wanke-wanken.

"Shiru yayi yana kallonta, cikin tausayawa."

"Yana zaune yana kallonta, gata yarinya ™arama amma ta riga ta saba da wahala, yadda yake wanke manyan kwanukan da aka Sata da miyar abincin salla."

"Wata ragowar miya da ta rage, ta zuba mata ruwa zata zubar, idirisa ya kawo kai ta watsa masa a jikinsa."

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724

Arewabooks ayshercool7724

YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels What's app 08081012143

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

P8

"Tuni ummi ta zabura, ta jefar da kwanon hannunta, jikinta ya hau rawa, a fusace ya ™araso kan ummi, yayi ball da ita"

ta hantsila cikin kwanukan da take wankewa.

"A cikin azama hashim ya ™arasa, ya hankaWe idiris, yana faWin ""Idirs meye haka?"""

"""Ban gane meye haka ba, ba kaga abun da ta yi mini ba? Dabbar ina ce? Ko makauniya ce?"""

"""Kai za a cewa dabba, ya za ayi ka shigo babu sallama, ya za ayi ta san da zuwan ka? Idiris zaluncin da ka ke yi wa"

"yarinyar nan yayi yawa fa"""

"Ummi kuwa karo tayi da ™afar tukunyar ™arfe, fi™arta Waya ta karye, nan da nan bakinta ya rine da jini, kuka take yi sosai, saboda ciwon buguwar da tayi, har cikin kanta take jin azabar ciwo."

"Babarsu da ta jiyo hayaniya ta fito tana faWin ""Wai lafiya ku ke yi mini hayaniya da tsakar ranar nan?"""

"Idonta ya sauka a kan ummi, da yawun bakinta ya gauraye da jini""."

"""Ita kuma wannan meya sameta?"""

"""Ga wanda ya yi ball da ita cikin kwanuka nan"" Hashim yayi maganar cikin takaici, yana nuna idiris."

"Nuna wa mahaifiyarsu kayansa yayi, da ummi ta Sata da miya."

"Hashim bai tsaya jin abun da mahaifiyarsu za ta ce ba, ya ja hannun ummi, ya tafi da ita."

"Sun sha yawo sosai, kan su samu chemist, kasancewar salla ce, aka bawa ummi magani."

"Haka aka gama bikin salla, ummi ba kayan salla sai jinyar baki, da ya sanya ta ciwon kai sosai da sosai."

***

"Mariya na zaune a Waki tana ninkin kaya, fuskar nan kamar wadda aka yi wa mutuwa, tana jiyo hirar da mama, da jimmai ma™wanciyar su suke yi, wadda ´ar ta aka kai gagarawa, suka haWu da balarabe suka yi aure."

"Tana bawa mama labarin ´ar ta mijinta ya samu sauyin wurin aiki zuwa ikko, sun bar gagarawa."

"Mariya ta yi shiru, tana tunanin ya aka yi ba tayi tunanin ta din ga bayar da abu, idan an samu mai zuwa gidan ´ar jummai a kai a bawa ummi ba."

"Sai dai ta tuna ba shiru suke yi ba, dan ´ar gidan jimmai, tana ganin tana auren mai kuWi mijinta Wan sanda ne, idan suka haWu da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta."

"Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa ""Ai nan asalamiyya ke bani labari, ´ar da mariya ta baro,"

"wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ™afarta, na ce ta Wan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun Waukko yarinyar nan"""

"Mama ta ce ""Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ™i, shiyasa muka ™yalesu, ba"

"su da mutunci ko kaWan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ™yale su idan yarinyar ta girma ta nememu"""

"Jimmai ta ce ""Ashsha! To Allah ya kyauta""."

"Mama ta amsa da ""Amin"""

"Mariya ta ajiye ninkin, ta haWa kai da gwiwa ta din ga kuka."

"Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga Wakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce ""Mariya na san kin ji abun da jimmai"

"take faWa, amma ha™uri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini"" shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ™ona zuciya, tana ji a ranta ba zata taSa yafe wa Iya ba."

"An doshi shekaru huWu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake sanya idonta ana"

"mahaifiyarta ba, tamkar baiwa a cikin gidan nan haka take rayuwa, babu gata babu kulawa, wahala ta yau daban ta gobe daban, ga Iya ta tsiri yi mata kunu ranar asabar da lahadi ta kai kasuwar garin, ta sayar mata, har ma wasu su yi abun sayarwar su a gidan su haWa mata."

"Babu yadda Hashim bai yi da iya ba, a kan ta daina Worawa ummi tallar nan, azabar da take sha tayi yawa, amma iya ta zage shi tsab, ta ce idan ya cigaba da yi mata katsalandan, za ta ci mutuncinsa ta tsine masa."

"Babu kunya ba tsoron Allah, Iya ta saka aka Salle ™ofar Wakin mariya, aka kwashe kayanta aka sayar, ta karSe kuWin,"

"wai da su zata tarawa ummi kayan Waki, Wakin ya zama wurin tara itace, hatsi da sauran shirgi."

"Ummi ta dawo daga makarantar boko, takalminta ya kusa rabewa biyu saboda tsufa ™asansa kuwa ya huje,"

"malaman su, sun gaji sun ™yaleta, ™afarta futu-futu. Ta tarar da Iya a tsaye tana jiran isowarta."

"Jiki a sanyaye ta ™arasa in da Iya take, ta ce ""Iya laifi na yi ne?"""

"""Au tambayata ma ki ke yi, saboda tsabar kin shahara, nan gaba makami zaki fara nuna mini, ki yi mini ™wace, kuWina zaki bani da saminu ya zo jiya da daddare, ban gan su ba, kuma daga ni sai ke a Wakin"""

"Gaban Ummi ya faWi, ta girgiza kai ta ce ""Wallahi iya ban Wauka ba, ki sake dubawa""."

"""Ni ki ke gaya wa na sake dubawa? ˜arya zan yi miki kenan? Ki zo ki bani kuWina kan jikinki ya gaya miki"""

"Ummi kawai tayi shiru tana kallon iya, dan ta rasa me za ta ce mata ma, ta san kawu saminu ya bata kuWi jiya, amma"

ba ta san ma a ina ta ajiye su ba.

"""Au saboda kin mayar da ni ´ar iska ki ka tsaya kina kallona, ba zaki bani kuWina ba?"""

"Ummi ta sunkuyar da kai, dan gaba Waya kanta ya kulle."

"Iya ta saSa mayafi ta fice, jiki a sanyaye ummi ta ™arasa cikin Wakin iya, ta hau duddubawa, ko za ta ga in da Iya ta"

ajiye kuWin.

"Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce ""Ka tambayeta ina ta kai mini kuWi, ka yi ta dukanta, har sai ta faWa"" kan ummi ta"

"ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa ri™e da manyan reshen bishiyar darbejiya."

"Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiWa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita."

"Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ™arfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ™afa."

"""Fito mini da ita daga Waki, Sarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a Waki"" a ™asa haka ya"

"din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida."

"""Ga Wakin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuWina"""

"Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a Wakin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe Wakin bisa"

umarnin iya.

"Ummi ta kwanta a ™asa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ™afarsa, tamkar ba a jikinta yake"

"ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata."

"Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin Wakin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su"

"Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuWi dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a Waki."

"Hashim ya ji kamar ya Wora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaWon, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri Waya,"

"saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare."

"""Ummi"" ya kira sunanta, ta Wago ta kalleshi ta sunkuyar da kai."

"""Da gaske kin Waukar wa iya kuWi"""

"Ta girgiza masa kai, ya ce ""Na san ba zaki Wauka ba ummi, yi ha™uri taso ki fito"""

"Ta girgiza masa kai ta ce ""Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni"

"wurin mama, wallahi zan mutu"" tayi maganar tana sheshshe™ar kuka."

"Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana i™irarin ta mutu, ""Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun"

"ya cije ki"" Da ™yar ya fito da ita daga Wakin."

Iya kuwa duk ta gama barbaWawa mutanen gidan ummi ta sace mata kuWi.

"Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka."

"Tana banWaki, Hashim ya samu Iya ya ce ""Iya dan Allah meyasa ba kya ™aunar ummi ne?"""

"""Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ™aunar uwarta ne, kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi"""

"""Ba wannan ba, Iya kin duba Wakin nan da kyau baki ga kuWin ba? Ummi bata taSa yi miki sata ba fa?"""

"""In ji uban wa? FaWa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon Seranya"""

"Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana Wingisa ™afarta."

"Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a"

hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka.

"Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi."

"Iya ta watso mata ™ullin kayanta, ta ce sai dai ta koma Wakin itace ta cigaba da zama."

"Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba."

"Da kansa ya share wa ummi Wakin, ya samo buhu ya shimfiWa mata, ya kawo tabarma ya shimfiWa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata ha™uri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka."

"Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ™asan katifarta ya Waukko Wari biyu, Alhassan ya fito"

"da wata leda a hannunsa ya ce ""Iya ba wannan kuWin ki ke nema ba?"""

"A razane ta karSa tana ™ifta masa ido, gaba Waya ta manta ina ta ajiye su."

"Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuWinta, duk wasu"

"kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi ha™uri, saboda ™arfin hali, har da Murmushin ta, tare da ™o™arin nuna bakomai."

"Da daddare ya sayo gyaWa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ™ara rarrashin ta, ya daWe yana sake kallon"

"Wakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a Wakin, kuma ba za a rasa ™wari masu cizo a ciki ba."

"Ya kalli ummi ya ce ""In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaWe ko"

"ina, ki tabattar babu wani abu a Wakin kan ki kwanta""."

"""To yaya na

Please Login or Register in order to submit comment