You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsire a hanya, da babbar robar youghurt, ya sai mata litattafai, da sabuwar"

"jakar makaranta. Babban abun da ya burgeta da shi, shi ne yadda take ta ce masa ta gode, a yanayin tattaunawar da yayi da ita, ya san ba™ar azaba kawai take sha, bai ga dalilin da ya sanya iya ri™e ummi ba, kuma shi ma idan ya ce zai tafi da ita can gidansa, faWa za suyi da Fauziyya matarsa, dan ya san ba zata karSi ummi ba."

"Gashi shi bai san a ina mahaifiyarta take a Maiduguri ba, dan lokacin da balarabe yayi aure, yana kudu karatu."

"A mota ya sanya ummi ta ci, har ta ™oshi, wani irin daWi take ji, yau ta ci kayan daWi, wataran tana kallo ake kawo wa"

"Iya, bata sammata."

"A ™ofar gidan yayi parking, ya buWewa ummi ta fito, ya ri™o ledar maganinta, ya ri™e hannunta suka shiga cikin"

gidan.

"""Ba™ar randa, ba™in zunubi, an dawo jinsinmu na maza"" Alhassan ya faWa yana ™ya™yata dariya""."

"Yahaya ya tsaya cak, ya kalle shi ya ce ""Alhassan, wa ka ke cewa ba™in zunubi? Ummi ba ™anwarka ba ce ba? Dan me zaku din ga aibata ta?"""

Alhassan ya yi shiru ya sunkuyar da kai.

"""Kai da ubanka na halitta, da zai halittoka da wannan kunnuwan kan kamar zomo na zikiri, ga ™aton kai kamar"

"marmara?"""

"Ya girgiza kai alamar a'a, nan yayi ta yi masa faWa, ya shiga cikin gida nan ma ya Wora, tare da yi wa iya ™orafi a kan"

"lallai ta sanya ido, a daina ci wa ummi zarafi, idan ba haka ba, zata dashi ba ta karsashi a cikin al'umma, saboda gudun kar a aibanta halittarta."

"Jin sa kawai Iya take yi, amma ba dan ta ji zata iya hana wani aibata ummi ba, dan ita ma aibata tan take yi."

"Yahaya ya kawo kuWi ja bawa iya nata, kamar yadda ya saba yi mata alkhairi, ya sanya a ka kira masa magaji, ya bashi"

"dubu goma ya ce ""Ga dubu goma, dan Allah duk abun da Yarinyar nan take bu™ata, ko na rashin lafiya, ko na makaranta ka cira ka saya mata, idan da damuwa zan rubuta lambar wayata, a kira ni a sanar da ni duk abun da take bu™ata, zan biya."

"Zumunci bai ce haka ba, mahaifinta ya rasu, an rabata da mahaifiyarta, kuma a™i tsayawa a kula da ita, dan Allah a kula da marainiya""."

"Hashim ya ce ""Ina sha Allah kawu, za ayi duk abun da ya dace"" ya dubi ummi ya ce ""Sannu ummi"""

"Ta ce ""Yauwwa"""

"Yahaya ya mi™e ya ce ""To iya, sai wani lokacin kuma, ayi ta ha™uri, Allah ya rufa mana asiri"""

Iya ta kwaSe baki ta amsa da Amin.

"Da sauri ummi ta ri™e rigarsa ta ce ""Baba yaushe zaka dawo?"""

"""Da wuri in sha Allah ummi""."

"""To ka ce ina gaishe da mama"""

"Ya kalli iya, iya ta kawar da kanta gefe, ya ce ""Iya yakamata a sanya lokaci a kaita ta ga mahaifiyarta, bai kamata idan"

"ma wani abu ne a tsakanin ku da mahaifiyarta ya shafe ta ba"""

"Iya ba dan Wan abun duniyar da ya bata ba, da babu abun da zai hana, ta Wura masa ashar. Sai dai ta yi masa shiru, ya"

™araci maganarsa ya tafi.

"Hashim ya tafi raka shi, suna tafe yana sake jaddada masa, dan Allah a kula da ummi, babu wanda yafi ™arfin Allah"

ya jarrabe shi da irin abun da ya jarrabe ta.

"Suka Wan yi hira a kan karatun Hashim, yake gaya masa ai yayi jamb, ya ce duk yadda ake ciki, idan yana bu™atar"

wani taimako yayi masa magana.

"Suka yi sallama ya dawo sashin Iya, sai dai fa iya nata jibgar ummi da kara, Idris na tsaye yana kallonsu."

"Da sauri ya ™arasa ya ™wace ummi, ya ce ""Iya daga asibiti fa aka dawo da yarinyar nan"""

"""A'a daga mutuware aka dawo da ita, duk yadda nake ™o™ari a kan yarinyar nan, bata da wani buri da ya wuce ta"

"tozarta ni, ta nunawa duniya azabtar da ita nake yi"""

"""To yanzu iya me tayi miki?"""

"""Ban sani ba, tun da makaho ne kai, baka gani, munafukar yarinya, wallahi duk ranar da wani ya kuma zuwa gidan"

"nan, ki ka yi masa zancen uwarki, sai mai shirin tafiya kabari ya fiki kwanciyar hankali, sai na casa ki, shegiya mai idon munafukai"""

Ummi ta cukuikuye rigar hashim tana kuka.

"Iya ta kalli Hashim ta ce ""Kai ma Waya munafukin, bani kuWin da ya baka, ai ba ita kaWai ce ´a a gidan ba, kuma idan"

"bayarwar ne, ai ni yakamata ya bawa"""

"Cikin takaici ya ce ""Amma iya..."

"""Rufe mini baki, ka bani na ce kan na Sata maka rai"" ya ciro kuWin ya ajiye mata, ya fice."

"Ummi da sauri ita ma ta fita, jikinta na ciwo, ga zazzaSi na sake son rufe ta."

"Ta koma ™ofar gida, ta samu in da rana take da saura, Wumin yana ratsata."

"Auwwalu ya taho da tawagar abokansa, har ya wuce ta ya dawo ya ce ""Yara ba™ar randa ta koma ba™in namiji, aski"

"aka yi mata fa"""

"Šaya daga cikin yaran ya ce ""Haba dai"""

"Ya ce ""Bari ku ga"" ya tunkari ummi, yana zuwa ya fara ™o™arin ja mata hijjabi, ta rirri™e hijjabin ta fara kuka."

"˜arasawa yaran suka yi, suka taya shi, kasancewar maza ne, gashi ba ta da ™wari ga rashin lafiya, suka kayar da ita,"

suka yage hijjabin.

"Ta saka hannu bibbiyu ta rufe kanta, tana kiran mama."

"Saboda mugunta irin ta yara, daga haka suka din ga kai mata duka a ka, wai sun ci ladan aski."

"Suka tuburbuWata a cikin ™asa, duk ta kurje jikinta, kan da aka yi wa dressing, duk suka cika shi da ™asa."

"Mariya daga alhinin mutuwar miji da rabuwa da Ummi, mariya ta zarce da damuwa, ba ta hira ba ta walwala, sai dai"

"kullum cikin wuni a Waki, duk lokacin da ta kwanta, ba ta da wani aiki sai mafarkin ummi, da kuma marigayin mijinta. Asibiti da maryam ke kaita awo, suka ce da zarar ta fara na™uda, a kai ta asibiti ta haihu a can, saboda hawan da jininta yayi."

"Sai dai kusan kwanaki uku kenan, tana jin ciwo, kuma sai ta yi ta mafarkin gata ta haifi ummi tan jaririya, amma tayi shiru da bakinta, ta™i faWa."

"Mama ta shiga Wakin, da niyyar tashin mariya ta yi salla, ta tarar da ita tana jijjiga, sai datse harshenta take yi, tana"

mimmi™ewa ga kuma haWe da jini na fita daga bakinta.

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

arewabooks ayshercool7724

Watpad ayshercool7724

Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

P7

"A guje mama ta koma tsakar gida, tana ™walawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi."

"Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo ma™wabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti."

"Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ™afar ummi, ya ™arasa"

"da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi."

"Wani irin ba™in ciki ya turnu™e masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke"

"iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar Wan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba."

"Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa mari, yana ball da shi, yayi masa"

"dukan tsiya, sannan ya Waukko ummi ya shiga da ita gida."

"Gaban iya ne ya faWi ganin yadda ya shigo da ummi, ta mi™e tana faWin lafiya?."

"""Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje"""

"""Saboda iskanci, me tayi masa?"""

"""Oho masa"""

"""Kema uban waye ya ce ki fita?"" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye."

"Ya ce ""Dan Allah iya ki yi ha™uri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaSi"""

"Ya karkaWe mata ™asar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita Wakin gwaggo ya kwantar da"

ita.

"Iya kuwa mita take tana ""Na rasa wannan ba™in jini na yarinyar nan, ´a sai ka ce mujiya, ´an uwanki yara ma"

"gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba Waya kalarki ba irin ta mutane ba"" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji."

"Duk yadda likitoci suka yi ™o™arin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun"

"nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa."

"Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya"

sake hawa.

"Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta"

magana.

"Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wula™ancin da iya ta yi wa yayyenta, ta san muddin ta je, ba abun da zai sauya, kuma hakan tamkar watsawa mahaifinsu da yayyenta ™asa a ido ne."

"Ummi ba wanda yake kula da bata magani, sai idan magaji ya shigo sashin Iya, ya sanya ta a gaba ta sha, duk da iya"

"ta ™wace kuWin da kawunsu ya bawa ummi, da kuWinsa ya saya mata yadin uniform, ya canza mata nata da suka yayyage suka yi mata kaWan."

"Ummi ta ji daWi sosai da sosai, ga sabuwar jakarta dan haka cike da ™warin gwiwa take zuwa makaranta."

"Kafin kwana bakwai, tuni kan ummi ya cika da gashi, kamar ba ayi mata aski ba, kalar wanda ya fita kalar sa ne dai yake sake fitowa a kanta, ba ba™i ne wuluk ba."

"Duk wannan murnar da take yi na komawa makaranta, da tarin ™o™arin da ummi take da shi, ya zama a banza,"

"saboda ko tambaya aka yi a aji, ba ta iya bayar da amsa, saboda gudun cin zarafi da tsokana da ´an uwanta Walibai za su yi mata, koma malaman da kansu."

"Wujiga-wujiga ta dawo daga makaranta, saboda azabar yunwa, koko ne kawai a cikin ta, shima tun sha Waya da tayi"

"fitsari, take jin kamar an sace mata kayan ciki saboda yunwa."

"Da ™yar ta ™arasa gida, tana zuwa iya ta Wora mata kai ni™a, haka ta kuma kwasar rana, ta kai wa iya ni™an ta dawo, a"

"wannan wahalen da take, wannan ya ja ya aika, wancan ya ja aika, har lokacin shiga makarantar allo yayi."

"Iya ta rage mata abincin rana, bai fi loma uku ba, a loma Waya da kaWan ta cinye, ta tashi ta tafi makarantar allo."

"Naima ce ta hangota tana share hawaye da hijjabinta, ta ™arasa in da take ta ce ""Ummi, ya aka yi ki ka makara? Kuma kukan me ki ke yi?""."

"Cikin kuka ta ce ""Malam babba ne ya dake ni, na makara"""

"""To meyasa ki ka makara?"""

"""Iya ce ta aike ni"""

"""Shegiyar mata, mai zuciyar kafirai"" Naima ta faWa a ™ule, ummi kuma ta kalli fuskar naima tana mamakin yadda"

take zagin babba kamar iya.

"Ta ja hannunta ajinsu, ta Waukko wani Wan kwano ta bata abinci, aikuwa hannu baka hannu ™warya ummi take"

danna abincin.

"Na'ima ta dubi ummi ta ce ""Ya jikin amma dai kin warke ko?"" Ummi ta Waga mata kai alamar eh."

"""Gashin ya fara fitowa?"""

"Ummi ta saka hannu Waya ta buWe mata kan, Na'ima ta rufe mata ta ce ""Masha Allah, ya fara fitowa, kin wanke"

"kayanki na makarantar boko?"""

"""A'a yaya magaji ya saya mini sabon uniform na makarantar boko"" ta faWa cike da jin daWi."

"Na'ima ta ce ""Alhamdilillah, Allah ya saka masa da alkhairi, na bayar a Winka miki atamfar bikina"""

"Ummi ta kalleta ta ce ""Biki, aure kenan?"""

"Na'ima ta ce ""Eh, aure zan yi ko in tafi da ke gidana?"""

"""Eh yaya Na'ima zan biki dan Allah"""

"Na'ima ta ciro Wan ™aramin tsumma a jakarta da ruwa a jarka, ta bawa ummi ta sha, sannan ta shiga goge mata hannu ta ce ""Zan so ace za a bani ke na tafi da ke ummi, sai dai hakan ba zai yiwu ba, ki je aji idan an tashi ki jirani"

"mu tafi tare, zamu je gidan mansura, an kawo mata takalma daga Kano, idan da wanda zai yi miki, sai na saya miki na biki"""

"Ummi ta ce""Ba zaki tafi da ni ba?"""

"""Ki yi ha™uri ummi, ba zai yiwu ba"""

"""Kema tafiya zaki yi ki bar ni? Mama ma ta tafi ta™i dawowa"""

"Na'ima ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Maza je ki ajinku, ga malam can ya tafi"" ta mi™ar da ummi tsaye, ummi ta tafi ajinsu."

"Naja da take ™awar na'ima, ta ce ""Ke dai ki na son yarinyar nan naima, gashi kin saka mata ran tafiya da ita"""

"Na'ima da hawaye ya taru a idonta ta ce ""Wallahi naja ina tausayin ummi sosai, wallahi da za a bani ita zan Wauke ta, kakarta matsiyaciyar tsohuwa ce, ai babarta uwar Wakina ce, mun yi mutunci sosai, baban ummi ya rasu, ta koma"

"garinsu, Kakarta ta ™wacw ta take azabtar da ita, ko a lahira na ganni gani g matar nan na san ban yi kyakkyawan ™arshe ba"" Duk da a ™ufule Na'ima tayi maganar, bai hana naja dariya ba, saboda maganar ta ta ™arshe ta bata dariya."

"Bayan tashi daga makaranta, tare suka tafi da ummi, hannunta cikin nata suna tafe tana yi wa ummi hira, tana"

"bugun cikinta, dan jin zaman da take yi, sai dai abun babu daWi mussman da ta gaya mata abun da su auwwalu suka yi mata, da aka yi mata aski."

"Na'ima ta ce ""Bakomai Allah ya isanki wallahi, duk wanda yayi nagari kansa,. Ki yi ta ha™uri kin ji ummi, duk tsanani duk yunwar da ki ke ji, kar ki bari wani a mazan gidan ku, manya ko yara, su kai ki wani wuri, su saka hannu a jikinki, kin ji ko?"" Maimakon ummi ta amsa sai ta Waga kai tana kallon na'ima."

"Cikin sauri na'ima ta tsaya ta ce ""Suna yi miki wasan banza ko?"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""A'a"""

"""Ki gaya mini gaskiya, suna taSa ki ko?"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""A'a"""

"""Duk wanda ya saka hannu a cikin jikinki, kar ki yadda kar ki tsaya, ki yi masa ihu ki gudu kin ji ko"" ta jinjina mata kai"

alamar eh.

"""Ko bayan na tafi, idan kina jin yunwa, ki je gidanmu wurin babarmu ta baki abinci"""

"Da haka suka ™arasa gidan mai takalmi, aka yi sa'a aka samu dai-dai ™afar ummi."

"Na'ima ta ce ""Zan ajiye a wurina, ranar bikina in yi miki kwalliya ko?"""

"Ummi ta Waga kai tana murmushi, daga nan suka ™arasa gida."

"Ummi ta shiga gida hannunta ri™e da wani kara tana wasa da shi ""Ke!"" Idris ya kwaWa mata kira a wula™ance."

Ta juyo tana kallon sa.

"""Zo ki sayo mini sukari a kanti"" yayi maganar yana watso mata kuWi."

"Ta dur™usa ta Wauka, ta je ta sayo masa, sai dai ta din ga tuna gargaWin Na'ima na hanata zuwa Wakin su idris."

"Ta nemi wuri ta zauna a ™ofar shiga wurin, ya gaji da jiranta ya fito."

"""Dan ubanki ina aiken da na yi miki?"""

Da sauri ta mi™e tana nuna masa sukarin.

"""Ba zaki shigo ki kawo mini ba saboda baki da mutunci, sai ki nemi wuri ki zauna?"""

"Tayi shiru tana kallon sa, ""Ba zaki kawo mini ba"" ya sake yi mata maganar cikin tsawa."

"Ta ™arasa in da yake cikin jin tsoro, sai dai ya ya haWa da hannunta, ya ja ta cikin Wakin."

"Kuka ta fara yi masa iya ™arfin ta, yau ya samu damar da rabonsa da ita an daWe, amma ta nuna masa tayi wayo"

"yanzu, dan haka ta din ga yi masa kuka da ™arfi, kamar yadda Na'ima ta gama gaya mata Wazu."

"Wawan marin da ya kifa mata ne, ya tafi da ji da ganinta na wani Wan lokaci, ta dafe kuncinta jikinta na wata irin"

"tsuma, tana karkarwa."

"Wata sharSeSiyar wu™a ya nuna mata ya ce ""Ki ka cigaba da yi mini kuka, sai na yanka wuyanki"" kallonsa take yi, kallo mai cike da tsoro da tsana, ya ajiye wu™ar tare da sanya hannayensa cikin rigarta, rigar da bakomai a ciki sai"

teSa dan wannan dai ba nono bane.

"Ba ta karaya ba, ta fara kokowar cire hannayensa daga jikinta, tana kuka mai cin rai, iya ™arfin ta."

"BankaWo ™ofar Wakin aka yi, hakan ya razana shi, dan bai yi zaton zuwan wani a dai-dai wannan lokacin ba."

"""Idris meye haka?"" Hashim yayi maganar yana kallon sa."

"""Kamar yaya meye haka, abun da ka gani"" a fusace ya ™arasa ya hankaWe idiris, ya janye ummi, ya kalli idiris ya ce ""Wani irin banza ne kai, ba zaka girma ba a rayuwarka, da me yarinyar nan za ta ji ne?"""

"Wani uban tsaki idiris yayi, ya ce ""Ka daina shiga sabgata ba ruwanka da ni""."

"""an shiga sabgar taka, wallahi idan baka rabu da yarinyar nan ba, sai na Wauki mummunan mataki a kan ka"""

"""To ka Wauka mana kar ka fasa"" ya sake jan tsaki ya fice."

"Cikin ™unar ran yadda ™aninsa ya raina shi, duk saboda iya na goya masa baya, ya kalli ummi ya share mata hawaye,"

"ya fito da ita daga Wakin, shaidar yastun idiris kwance a kan ba™ar fuskarta, da har idonta yayi taruwar jini."

"Ya zubawa ummi ido, da haryanzu jikinta yake tsuma, ga wata irin nannauyar ajiyar zuciya da take yi, har a lokacin a"

"tsaorace take, kuma hawayenta ya ™i tsayawa."

"""Ummi"" ya kira sunanta, sai dai bata amsa ba, ta sake fashewa da kuka."

"Wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, ya din ga share mata hawayen, ya ri™e hannunta suka nufi sashin iya, tana ta"

dakan fura tana wa™e-wa™e.

"Tana ganinsu tare ta hau bala'in tun Wazu take neman ummi, zata aiketa amma daga zuwa makaranta ta zauna."

"Magaji ya ce ""Iya"""

"""Ya aka yi"""

"""Dan Allah idan ba za a iya ri™on yarinyar nan ba, a mayar wa da uwarta ita, idiris fa na kama yana neman haike"

"mata a Wakinmu, wace irin rayuwa ce wannan, kalli yadda ya mare ta, haba dan Allah"""

"Iya ta dafe ™irji ta ce ""Shi idiris Win? Ita uban me ya kaita in da yake, me ya kaita Wakin ku, ai ita ta kai kanta, amma shima zai zo ya same ni, da ni yake zancen. Kai kuma sai ka ce ba Wan uwanka ba, ka ke Waga murya tona masa asiri"

"zaka yi?"""

"""Iya to zuba masa ido za ayi, idan abun da ba a so ya faru fa?"""

"""Ba abun da zai faru sai alkhairi, jeka zai zo ya same ni, ke kuma canza kayan ki zo ki kai dusar nan gidan lami, ta"

"bawa dabbobina"""

"Hashim ya ce ""Ni bani dusar na kai, kalli yadda take a razane"""

"""Ba wani a razane, da a razane take ai da ba ta kai kanta ba, yarinya ™an™anuwarta da ita, ta san ta je wurin namiji"""

"""Haba iya, me ummin ta sani da zaki faWi wannan mummunar maganar a kanta?"""

"Iya ta ce ""Zaka zo ka kai mini dusar ko ta Wauka ta kai mini?"""

"Ya ™arasa ya Wauki dusar ya fita, zuciyarsa kamar ta tarwatse, tausayin yarinyar na damunsa sosai da sosai."

"Kwanaki biyu tsakanin abun da ya faru, sannan idiris ya shigo sashin Iya."

"Iya ta dube shi ta ce ""Idris, kashedi zan yi maka a kan yarinyar nan, kar ka kuskura ka sake saka yarinyar nan a loko"

"kana lalubeta, wallahi idan ka sake wani abu ya afku ba zan rufa maka asiri ba, kuma ba zaka janyo mini masifa ba,"

"kai gashi ba sana'a ba balle ace ayi maka aure, in huta. Ina yi maka kashedi, wallahi wani abu ya faru ba zan saurara"

"maka ba, na gaya maka"""

"Cikin fushi ya ce ""Me kuma na yi, magaji ne ya zo ya ce na yi mata wani abu?"""

"""A'a ni banga magaji ba, bai gaya mini komai ba, fuskanta kawai na yi"""

Ficewa yayi ba tare da ya sake magana ba.

"Rashin samun biyan bu™atar sa a jikin ummi, ya sanya ya ji ya ™ara tsanar yarinyar, ko son ganinta ba ya yi, ita kanta ummi, har fargaba take yi a aike ta, saboda bayan iya ta yi masa wannan faWan, sai da ya zane ta, saboda a zaton sa"

ita ta gaya wa Iya.

"Duk wannan cin kashin da ake yi wa yarinyar, daga ´an uwan ubanta da suke ciki Waya, da wanda uba suka haWa da"

"matayen su, babu wanda ya taSa shawartar iya a kan sassautawa ummi azabtarwar da ake yi mata, tamkar ´ar tsintuwar da ta faWo daga sama."

"Azumi saura wata biyu, aka yi bikin na'ima, ta yi kuka sosai, ciki har da na rabuwa da ummi, dan har cikin zuciyarta"

take jin rabuwa da ummi.

"Mariya kuwa tun ´an uwanta na ta tata, suna rarrashin ta, suna bata ha™uri, har suka zubawa sarautar Allah ido suka ™yaleta, ta riga dai ta kamu da larurar hawan jini, a hankali kuma ciwon damuwa ya fara addabar ta, kullum"

"tana Waki, daga bacci, kuka sai shiru."

"Yaya Wan lami ya fara tunanin ko ta koma makaranta, amma yanayin da take ciki, ya tabbatar masa da ko an mayar da ita makarantar ba za ta iya mayar da hankali ba."

"Dama labarin haihuwar ta ta ko su iya ba a gayawa ba, dan gaba Waya sun fuskanci sabgar Iya babu Allah a cikinta."

"Yaya Wan lami kuwa da suka ga mariya ta™i sakin ranta, ya ™are mata cin mutunci, tare da tabbatar mata da muddin ta je wurin su Iya babu su babu ita, ´a ce idan ta girma da kanta za ta neme ta."

"Watan azumin ramadana ya kama, wanda hakan ya sake jefa ummi tsaka mai wuya. Ba iya azumi take yi ba, dan"

"haka babu mai kulawa ya bata abinci, haka za ta yi ta gararanba ta wuni a kwance, idan makaranta ta je, tana kallo yara na ciye-ciye, ita ba raSar su take yi ba ma, balle ta yi musu kwaWayi, ko kuWin makaranta ba bata ake yi ba, dan haka bata saba da kashe-kashen kuWi ba."

"Sai an sha ruwa take samu ta ci abinci, sai da hashim ya fuskanci ba ta samun abun da za ta ci da rana, shi ne yake rage mata abincin sa, da safe ya bata, da rana ya sai wani abun ya bata. A haka har aka ™are azumi."

"Da salla kowane Wa cikin kyakywar shiga mai kyau, ummi kuwa kayan bikin na'ima ta saka, da suka fara koWewa, da"

"takalmin makarantar da kawunsu ya saya mata, shi ta koma tana sakawa tayi yawo da shi a gari, saboda ko silifas ba ta da shi, wanda naima ta saya mata tuni ya lalace."

"Yara na ta shiga su na fita, ummi kuwa na ™ofar Wakin mamanta, ta zauna tana wasa da duwatsun wurin."

"Hashim yayi sallama, ummi ta amsa cikin ´ar siriyar muryarta."

"Ya ™arasa in da take zaune, ya ce ""Kin je sallar idi ne?"" Ta girgiza kai alamar a'a."

"""Me ki ke yi a nan wurin?"""

"Ta ce ""Bakomai"""

"""Kin ci tuwon salla kuwa?"""

"Ta ce ""A'a iya dai ta ce zata bani"""

"Ya mi™a mata hannu ya ce ""Taso mu je"""

"Ta saka hannunta a nasa, ya ja ta zuwa sashin mahaifiyar sa."

"Babansa ma, da ake cewa baba sagir, yana zaune yana cin abinci."

"Ummi ta dur™usa ta gaishe shi, ya amsa mata babu yabo ba fallasa."

"Ya ce ""Yaya a zubawa ummi abincin salla dan Allah"""

"Ta ce ""Ga maimuna nan, ya zuba mata"" ta kalli ummi ta ce ""Ke ummi baki da kayan salla ne, ki ka saka wannan"

"koWaWWiyar atamfar?"""

Ummi tayi shiru tana kallon ta.

"Aka kawo wa ummi abinci, ya saka ta wanke hannunta, ta zauna ta saka tuwon sallar nan a gaba tana ci, tana yi tana"

kallon yadda yara suka yi kyau sosai a sababbin kaya.

"Ta gama ci ta hau tattara musu kwanukan wanke wanke, ta share musu tsakar gida."

"Hashim ya dawo sashin, ya tarar da ummi ta haWa kwanukan wanke-wanke."

"""Me kuma zaki yi?"""

"""Wanke-wanke zan yi""."

"""Ke yara na can waje suna tsalle-tsalle, suna wasanni, amma ke kina

Please Login or Register in order to submit comment