You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi amfani da ko guda Waya kafin ku zo ku ga likitan, zata samu sau™i in sha Allah. Wannan na Wan gaya muku ne dabarunmu na cikin gida na gargajiya, kafin Allah ya sa ku zo ganin likitan""."

"Ya ce ""To shikenan, na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da alkhairi"""

"Ummi ta bi bayansa suka fito, suna tafe a hanya yana jaddada da mata ta ri™e abubuwan da aka gaya mata, ummi"

"kuwa gaba Waya jikinta sanyi yayi, wata irin kunyarsa ta rufe ta."

Shi kansa yayi mamaki da nurse Win ta ce masa ummi ta ce wando Waya ne da ita.

"""Ummi"""

"Ta amsa da""Na'am"""

"""Ki kwantar da hankalinki, magnunnan nan zan saya miki zuwa gobe in Allah ya kaimu, har kayan da zaki yi amfani"

"da su, duk zan yi miki har makaranta zan mayar da ke da yardar Allah, ke dai ki nutsu ki manta da komai, ban yi miki al™awarin gidana babu ™alubale ba, amma na san bai kai na ™auye ba. Ki dage ki yi amfani da shawararin da ta baki kin ji ummana"""

"Ta ce ""To na gode sosai"""

"Ya shafa kanta ya ce ""Yauwwa Allah yayi miki albarka"""

"Can gagarawa kuwa, Hashim ya sha zagi da cin mutunci da wula™anci a wurin Iya, ba Iya kawai ba, har da mahaifinsa"

"suka ™are masa tas, a kan ya kasa rufa wa Wan uwansa asiri, da har ya iya sanar da kawu yahaya halin da ake ciki."

"Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, amma har cikin ransa yake jin wannan abun da yayi shine mafita ga rayuwar"

"ummi, kuma hakan da yayi bai saSawa shari'a ba."

"Sirikan iya wasu sun jiye wa ummi rabata da gidan nan, saboda azaba da masifar iya ga ummi."

"Iya kuwa ta ji ba™in ciki da takaicin Wauke ummi da yahaya yayi, dan yanzu ta san abu ne mawuyaci idan asirinsu da take ta ™o™arin rufuwa bai tonu ba."

"Shi kansa Idris tun da aka tafi da ummi, bai dawo gidan ba, dan ya san zai sha faWa a wurin Iya da iyayensa, shi kuma"

"har ga Allah, ya tsani yarinyar nan hakan da yayi shine dai-dai."

"Horn yayi, wani matashin yaro, da zai Wan girmi ummi ya zo ya buWe gate Win, ummi ta san yaron amma da daWewa"

dan wasu lokutan ya kan zo da shi gagarawa.

"Ya shiga da motar harabar gidan, ba laifi harabar mai Wan girma ce, dan a™alla za a yi parking Win motoci uku a ciki."

"Wasu ´an mata ne ™anana su biyu farare tas da su, an yi musu kitson ™ari, Waya tafi Waya girma, suka nufo motar suna faWin oyoyo Abba."

"Ya buWe motar ya fita ya rungumo su, sannan ya juya ya buWe wa ummi motar ta fito."

"Duk da duhun magariba ya fara yi, hasken fitilar da take harabar gidan, ta basu damar tsayawa suna ™arewa ummi"

kallo.

Ya buWe bayan motarsa ya cewa yaran su Waukko wa ummi kayanta.

"Ba laifi gidan mai kyau da shi, ummi sai kallon gidan take yi."

"A falo ya kalli yaran ya ce ""Intee ina maama ne?""."

"""Ta fita da muka dawo daga tahfee, bamu tarar da ita ba"""

"Ya ce ""Ok, ga sister Winku nan, sunan ta Salma, amma ummi ake ce mata, you can call her yaya ummi, ku nuna mata"

"toilet Win ku ta yi alwala""."

"Cikin ™yama intee ta bi ummi da kallo, sannan ta yi gaba, ummi ta bita a baya."

"Ummi ta yi salla ta idar, tana ta kallon Wakin, da gani na ´an matan ne, kowacce da gadonta, ga ™atuwar wardrobe,"

"ga shoe rack Win su Wauke da takalmansu na makaranta da na fita, duka-duka babbar da ake kira da intee ba ta fi shekara goma ba, Wayar kuma bakwai."

"Ummi ta fito daga Wakin, ta koma falo ta zauna a ™asa."

"Ya shiga kitchen da kansa, ya haWowa ummi tea mai kauri, ya saka intee ta dafawa ummi noodles ta Wora mata ™wai"

uku a kai.

"Duk da yanayi na rashin lafiya, ummi ta Wan ci, dan bata taSa cin indomie ba, duk da ta na burgeta."

"Yaran suka kunna tv suna kallo tare da mahaifinsu, ummi ma kallon take yi, suna ta yi wa babansu surutu, yana ta"

"™o™arin saka ummi a hirar, ta dai yi shiru ba ta cewa komai."

"Bayan magariba sosai sannan wata mata tayi sallama, ita da wata matashiyar budurwa."

"Ya amsa ya Waga kai yana kallonsu, yaran kuma duk suka tashi suka nufeta."

"Cikin iyayi ta ce ""Abba ka dawo kenan?"" Tayi maganar tana zama da tsohon cikinta."

"""Eh"" ya amsa mata a ta™aice."

"Ummi ta kalleta ta ce ""Ina wuni?"""

"Ta bi ummi da kallo, ta ce ""wannan fa?"""

"Ya ce ""Ki fara amsa mata gaisuwar mana"""

"""Lafiya ™alau"" ta amsa a Wan yatsune."

"Ya kalli su inteesar ya ce ""Abdul, intee, shalele ku bi anty rahama maza, ummi ki bisu ki samu ki huta, a haWa mata"

"ruwa tayi wanka"""

"""Wai ban gane ba, ita wannan Win wacece?"""

"Ya ce ""Kya tsaya na yi miki bayani ai, yanzu dai daga ina ki ke?""."

"""Gidan gana na je, wata ´ar aikin nake so ta samo mini, saboda su intee wahala tana yi mini yawa""."

"""Amma ba kwanan nan ki ka rabu da wata ba, kina ta surutun tayi miki laifuka ba, shi ne zaki sake rakito wata?""."

"""To Abba yaya zan yi? Ga tsohon ciki, da na haihu zan koma school, ga ayyukan gida ba zan iya ba wallahi. Ka yi"

"ha™uri kawai ni dai""."

"""Shikenan, amma kar ki kuskura ki zo kina ce mini an yi miki kaza an yi miki kaza"""

"""Na ji wacece waccan yarinyar da ka haWa mini da yara?"""

"""Dama na san ba saninta zaki yi ba, tun da ba zuwa ki ke yi ba, ³ar wurin marigayi ce bashir?"""

"""To me zata yi a nan Win?"""

"Ya gyara zamansa ya ce ""Eh, na Waukko ri™onta ne na dawo da shi hannuna, a nan za ta zauna da mu"""

"A fusace ta ce ""Amma yaya zaka yi mini haka, ya zaka Waukko yarinya ban sani ba ba shawarata kawai ka ce in ri™e?"

"Saboda me? Abba meye amfanin kawo bare ka haWa a cikin iyalinka""."

"""³ar Wan uwan nawa ce bare kuma?"""

"""Bare ce mana, ki ka haifeta? Naga ai ba cikinku Waya da ubanta ba, gaskiya ban yarda ba, ka mayar da ita in da ta fito wallahi ba zan iya ba, dama dinginku sun tsane ni, shi ne aka haWoka da ita ta zo ta saka mini ido, wallahi ba zan"

"ri™e ba""."

"Ya dubeta ya ce""Well, ummi bare ce, amma ko ba komai ´a ce a wurina, idan har ummi za ta bar gidan nan, ki tabattar rahama ma sai ta bar mini gida, dan bani da wata ala™a da ita, dan ina aurenki ba dole ne na ri™e ki na ri™e"

"™anwarki ba, tun da baki san mutunci ba, a gobe in Allah ya kaimu rahama ta bar mini gida na gaya miki""."

"""Yahaya, ni ka ke gayawa ™anwata ta bar gidan nan?"""

"""Tun da ki ka iya kallona ki ka ce, ´a ta ta bar gidan nan, to rahama ma sai ta bar gidan nan tun da ko ban ri™eta ba,"

"bani da laifi a wurin Allah, ummi kuwa dole ne ri™onta a kaina"" ya tashi fuuu ya nufi Wakin su intisar."

"Ummi na zaune a ™asa rungume da kayanta, tana kallonsu, suna zaune a kan gadonsu, sun sakata a gaba suna ta"

"dariya, saboda yanayin ™auyanci da yake tare da ita da kuma ba™ar fatarta."

"Sallamar babansu ce ta sanya su tashi a razane, suka daina dariyar."

"""Ina ruwan wankan da na ce a bata?"""

"Intee ta ce ""Anty rahama ba ta haWa ba"""

"""Wannan ban isa da ita ba, ku na isa da ku, ki haWa mata ruwa ki nuna mata yadda ake amfani da toilet Win"""

"Ta jinjina kai, ya juya ya fita dan tafiya masallaci sallar isha'i."

"Cikin ™yama take nunawa ummi banWakin, ´ar ™arama da ita, amma ta iya wula™anci."

"Ta cewa ummi kar ta kuskura ta taSa musu sosunan wankansu, ta je ta Waukkowa ummi sabulun wanki, ta bata wai tayi wankan da shi, ta kuma nuna mata iya in da zata tsaya, tayi wakan."

"Ummi ta jinjina mata kai, sai dai ta tsaya tana kallon banWakin yadda ya ™awatu."

"""Rahama kina ina, wai ni yahaya ya Waukkowa ´a a ™auye na ri™e, wai idan ba zan ri™e ba kema ki bar masa gida"""

"Rahama ta kalleta ta ce ""In bar gidan nan wai? To me ki ka ce masa""."

"""Wallahi ba zan ri™e ba, kuma ba in da zaki je, shi ya isa ma, wallahi yayi kaWan, zai gane kuskurensa""."

"Rahama ta ce ""Anty ke da ki ke neman ´ar aiki? Gashi kin samu a Sagas, ba dai gida ne ba, ta zauna mana iya ka idan bala'i ya isheta ta gaji ta bar gidan nan, ki rabu da shi, sai dai karki saurara mata wallahi, idan ma sa ido aka turo ta ki"

"ci ubanta, ki rabu da shi kawai"""

"Ta ce ""Kuma fa haka ne rahama, haka za ayi, Wakin mai aiki kawai zata koma, na samu baiwa zata ci ubanta kuwa, sai ta koma in da ta fito dan ba zan zauna da ita ba wallahi. Nifa gaba Waya ban yarda da yarinyar nan ba, lokacin da"

"muka je gaisuwar babanta, ina jin kakarta na ta ce mata kamar mayya, ke kin ganta ba™a ™irin ™wayar idonta kamar mage""."

"Raham ta ce ""Idan ma mayyar ce ta ci kanta, dan wallahi mun fi ™arfinta, to ma ina uwarta da za a kawo miki ita?"

"Gaskiya baban Abdul yana da matsala wallahi""."

"""Oho masa, sai ta bar mini gida dai wallahi, amma na san yadda zan yi da shi""."

Ayshercool

08081012143

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS

(FREE BATCH)

"(Ku garzaya YouTube channel Wina na COOL HAUSA NOVELS, KU YI SUBSCRIBING, AN FARA ŠORA LITTAFIN ˜ANWAR"

MAZA NA SAURARO)

P14

"Har kawu yahaya ya dawo daga sallar isha'i, suna tattaunawa ita da rahama, suka gama ™ulle-™ullensu, sannan farida"

ta baro Wakin rahama.

"Yahaya ya tafi Wakin yaransa, in da suke ta tsalle-tsalle a Wakin, ummi kuma na ta gyangyaWi a zaune a ™asa."

"Suna ganinsa suka tsagaita da tsallen da suke yi, ya kalli babbar ya ce ""Ke intee, ku yi squating da kausar a kan"

"gadonki, yaya ummi ta kwana a kan Waya gadon."

"Turus suka yi suna bin mahaifinsu da kallo, cikin tsawa ya ce ""Ba ku ji me na ce ba ne?""."

"Intee ta ce ""To"" ya kalli ummi da ta buWe ido ya ce ""Ummana, ga gado nan tashi ki kwanta kin ji"""

"Ummi ta ce ""To na gode"""

"Ta tashi ta hau gadon nan ta kwanta, wani irin laushi, ga ™amshin room freshner mai daWi kayan shimfiWar suke yi,"

tun kan ya bar Wakin bacci ya fara kwasarta.

"Inteesar ta kwashe wa da kausar da dariya ta ce ""Shikenan bedsheet Win ki zai kwashi ba™i, kamar an ciro a buhun"

"gawayi""."

"KwaSe fuska kausar tayi za ta yi kuka, intee ta cigaba da dariya, ganin kausar ta fara kuka ya sanyata cewa ""Bari idan"

"abba ya daWe da tafiya, sai mu tashe ta, ta saukko""."

"Haka kuwa aka yi, intee har da le™awa, ta tabattar da ya tafi, sannan ta dawo, ta hau dukan ummi a ™afa."

Ummi ta buWe idonta tana kallonsu.

"""Saukko mana daga kan gado, kausar zata kwanta"""

Kasa magana tayi ta cigaba da bin su da kallo.

"""Ki saukko zata kwanta, dan ba zata kwana a gadona ta matseni ba"" babu musu ummi ta saukko, ta koma ™asa ta"

sake tada kai da kayanta.

"Kausar ta watso kayan kan gadon nata, har bedsheet Win da komai, wai saboda ummi ta kwanta a kai."

"Wajen ™arfe Waya na dare, ummi ta ji ana haurinta da ™afa, ta tashi firgigit, dan ji tayi kamar a gidan idris za ta buWe"

"ido ta ganta, dan shi yake yi mata irin wannan wula™ancin, na haurinta da ™afa."

"""Tashi malama, in nuna miki in da zaki din ga kwana, dan ba zaki kwanar mini a cikin yara ba, ban san irinki ba"""

"Kai ka ce sokuwa, haka ta tashi, ta Waukko jakar kayanta, ta bi bayan farida."

"Šakin ´ar aiki da yake farkon falon, ta nuna mata ta ce ta shiga a nan zata kwana. Ba ta damu da a yaya Wakin yake"

"ba, ta je ta kwanta, saboda yanayin jikinta ga rashin lafiya ga gajiyar tafiya, dan haka duk a gajiye take."

"Washegari da safe, kowa ya fito falo, rahama ce ta haWa breakfast, yaran duk sun shirya cikin uniform na makarantar"

boko.

"Abba ya fito ya kallesu Waya bayan Waya babu ummi, rahama ta gaishe shi ya amsa sama-sama."

"Ya kalli farida ya ce ""Kawo mini abincina nan"""

"Haushi ne ya kama ta, yana ganin yadda take fama da ciki, amma ya sakata aiki, bayan ta kai masa kayan abincin"

Waki.

"Bayan ta tafi Waukkowa, ya kalli intee ya ce ""Kirawo mini ummana"" intee tayi saroro tana kallon shi."

"Ya ce ""Ummi nake nufi"""

"Tunawa tayi da safen nan, ta ji maama da anty rahama suna zancen a Wakin mai aiki ta kwana, har take gaya musu"

abun da suka yi mata jiya da daddare suka din ga dariya.

"A zaune ta tarar da ummi, ita ummi Wakin ba ™aramin kyau yayi mata ba."

"Duk da ba wani abu a ciki na burgewa, amma Wakin ya yi mata kyau."

"""Ki zo in ji abba"" yarinyar ta faWa cikin fitsara."

"Ummi ta tashi ta bi bayan ta, sai dai farida na ganin ummi kamar taga kashi, ta haWe rai."

"Daga in da suka fito falon, ya fuskanci a in da ummin ta kwana."

"Ummi ta dur™usa ™asa ta ce ""Abba ina kwana?"""

"""Lafiya ™alau ummana, ya jikin naki, ina fatan baki kwana da zazzaSin ba?"""

"Ta ce ""Eh da sau™i""."

"Ya ce ""Masha Allah, baki gaisa da maman naki ba, gata nan sunan ta farida, yara na kiranta maama, kema zaki iya"

"kiranta da hakan, ga ™anwarta nan anty rahama, ga Abdurrahman Abdul, ga inteesar, ga kausar, sai kuma muna jiran unborn baby da maama zata haifa mana. Abdul, intee, kausar kamar yadda na gaya muku jiya, yayarku ce, duk da kai Abdul ka girmeta, amma ku girmamata, ku zauna lafiya. Ummina duk abun da ki ke bu™ata, ki sanar da ni, ko maama gidanku ne ki yi zamanki ki kwantar da hankalinki""."

"Cikin ladabi ummi ta ce ""To Abba"" ta kalli farida ta ce ""Ina kwana"" banza tayi da ummi kamar ba ta ji abun da ta ce"

"ba, ba ta damu ba ta kalli rahama ta ce ""Anty ina kwana"""

"Ba yabo ba fallasa rahama ta amsa mata, abun da farida tayi, ba ™aramin ™ular da shi tayi ba, bai ce komai ba da kansa ya haWa wa ummi abun breakfast a abincinsa, ya bata."

"Wanda hakan ba ™aramin tunzura farida yayi ba, cikin ™ulewa take tuna masa yara zasu makara a makaranta, amma ya kada baki ya ce ""³a´anki ne ai ki tarar musu abun hawa ya kai su, ´a ta zan kai asibiti"""

"Tsit suka yi suna kallonsa, aka rasa mai magana, ya jira ummi ta gama, ya sakata a gaba suka fice."

"Sai da ta kusa kuka, abun ka da mai ciki dama ga zuciya a kusa."

"""Rahama ki na kallo daga kawo yarinyar nan, ni zai yi wa wannan wula™ancin, ya fifita bare a kan yaransa""."

"""Kema anty farida you over react, a gabansa ta gaishe ki, ki ka shareta, ai kisan mummu™e zaki yi mata""."

"""Yanzu kwana Waya tal a gidan nan ta fara haWa ni da shi? To wallahi da sake ba zai yiwu ba"""

"Ran farida yayi matu™ar Saci, ta din ga cin alwashi kala-kala na mugunta a kan ummi."

"Ya tafi da ita wurin aikinsa, ya kulleta a office Win sa, ya je ya gabatar da lectures Win da zai yi, wajen ™arfe sha biyu"

"na rana, ya tafi da ummi kasuwa."

"Ya sai heater da nurse Win nan ta ce ya saya, ya sai mata phants dozen Waya, ya saya mata soso sabulu, brush,"

"manyan jakar omo. Ya saya mata sababbin kaya wasu ready made wasu kuma sai an Winka, kasancewar yana da yara mata, kuma shi yake sayen komai na gidan sa, dan haka duk wani abu na Wawainiyar yara mata ya sani, hatta Wan kunne sai da ya saiwa ummi, under wear vest duk ya saya mata."

"Ya ce suje mota ta zauna ta huta, ya ™arasa sayayyar, wani irin farinciki ummi take ji, saboda kayan nan da aka saya mata, gani take kamar a mafarki, wai duk wannan kayan nata ne, har da su Wan kunne da ribbon, ga takalmi mai kyau, ta din ga kwarara masa addu'a a cikin zuciyarta."

"Wurin masu sayar da kayan ™amshi yaje, domin haWa magungunan da aka gaya masa a yi wa ummi."

"Sai dai wasu abubuwan duk ya manta yadda aka gaya masa, mai kayan ya tambaye shi, mai zai yi da su, yake gaya"

masa ai maganin sanyi za a haWa.

"Kasancewar mutumin sana'arsa ce, sai ya haWa masa komai da yadda ake amfani shi."

"(Previous page, na bayar da magungunan in breif, wasu sun biyo ni suna so, yanzu zan rubuta full yadda ake amfani"

da su)

_Kanumfari

"_Tafarnuwa ´ar kaWan ba mai yawa ba, saboda idan tafarnuwa ta huda jikin mace, tana sanya warin baki, na jiki har da na al'aura ma, sai dai maganin sanyi ce sosai."

_Tumeric (yellown kur-kur)

_Namijin goro

_Citta mai yatsu

_Lemon tsami

"Kowanne za a zuba shi in a moderate amount, lemon tsami babba guda Waya mai ruwa ya isa, namijin goron ma za a"

"iya daddatsa shi, yana da Waci sosai, tafarnuwa one clove, sai citta mai yatsu madaidaiciya guda Waya, sai 1 table spoon of tumeric, sai a zuba ruwa kamar 2cups, a dafa su a din ga sha, za a iya zuba zuma, saboda yana da Waci, za kuma a iya haWe su a mazubi guda, a ji™a su, su ji™u sosai a din ga tsiyaya ana sha."

"Idan wannan bai samu ba, ana iya ji™a kanumfari, a din ga sha yana maganin sanyi sosai, amma sai an juri sha."

"Sai kuma ana samun saiwar zogale, a Waurayeta da Wan gishiri, a tafasa ta da jar kanwa, a din ga sha, salam yake"

"babu Waci, amma yana maganin sanyi sosai."

"Sai kuma kama ruwa da ruwan magarya da bagaruwa ba da yawa ba kaWan a haWa su a tafasa, ana kama ruwa da"

"shi, ganyen magarya yana gyara jikin mace, mussaman bayan gama al'ada, ayi shaving a din ga kama ruwa da shi, kuma a din ga Wiga farin miski a kan phant, ba a jiki ba, yana kawar da ™arni ko wani wari mara daWi, but mark you ba kowane wari ne yake fita a gaban mace na infection ba, akwai bacterias Win da suke wurin wanda ba masu cutarwa ba ne ba, suna haifar da wannan ™arnin wasu lokutan."

Galibi na infection ko na ™azanta ya fita daban mussman idan ya haWa da ™ai™ayi ko ™uraje shi ne na infection.

"Shi ma wannan warin, ana iya amfani da apple cider vinegar, ruwa kal da hausa, ana zuba tablespoon Win sa biyu, a"

"ruwa cikin kofin shan shayi a din ga sha, yana magance warin gaba."

"Sai dai dole a kula da abincin da ake ci, domin cin abinci mai ™arni, ko wari kamar kifi, albasa ko tafarnuwa suna da tasiri a gumin mu da sauran fluids da muke fitarwa a jikinmu."

"Kawu yahaya duk ya haWowa ummi abubuwan da suka kamata, suna tafe yana sake yi mata bayanin yadda zata yi amfani da su."

"Sai azahar suka koma gida, sai dai matar gidan bata nan, da kansa ya bi ummi Wakin masu aikin, ya dudduba abun da"

babu ya ce zai sayo mata.

"Tamkar yar da ya haifa a cikinsa haka yake jin ummi,kuma haka yake burin ta samu lafiya daga wannan ciwon, dan"

"ya san illarsa da hatsarinsa, dan ya san halinsu maza bakomai suke iya jurewa su kawar wa da kai ba."

"Ya nuna mata yadda za ta din ga amfani da heater, da sabon flask Win ruwan zafi."

"Da kansa ya tafasa magungunan, ya zuba mata a jarka, na kama ruwan ya zuba mata a cikin flask Win shayi, ya"

Waukko tsintsiya ya taimaka mata wurin gyara Wakin saboda an kwana biyu ba a gyara shi ba.

"Ya je Wakinsa ya duba bedsheet Win da shi ya saya da kuWinsa, har da bargo ya kawowa ummi."

Ya bata babban gwangwanin turare a cikin nasa ya ce ta din ga fesawa.

"Kallonsa kawai ummi take yi, cikin jin daWi da annashuwa, yadda ya zage yake ta Wawainiya da ita, daga jiya zuwa"

"yau, idan ta ce ya bari tayi da kanta, sai ya ce mata ai bata da lafiya, kuma cikin barkwanci ya ce mata albarkar ummansa yake nema."

Haka nan ummi ta din ga murmushi tana yi masa godiya.

"Ya ce ""Yauwwa ummina, Allah yayi miki albarka, saura makaranta ita ma in sha Allah sati mai kamawa, zaki koma"

"makaranta ki manta da duk abu da ya faru, iyaka dai kar ki sake ki gaya wa wani kin taSa aure kin ji ko?"""

"Ta jinjina masa kai ya ce ""Good, yi wanka ki yi salla, a cikin kayan nan akwai gurasa ki ci kiyi kwanciyarki ki huta"""

"Murmushin kawai da ya gani a fuskar ummi, ya sanya shi cikin farinciki, kullum yaje ™auye sai dai ya tarar da ita cikin kuka, sai kuma Murmushin ya™e."

"Hatta yadda zata din ga amfani da banWaki, sai da ya nuna mata komai."

"Fitowa yayi daga Wakinta, a zuciyarsa yana tawasalli da farincikin da ya saka marainiya yana addu'a Allah ya biya"

masa bu™atunsa na alkhairi.

"Ba yau farida ta fara fita yawonta ba, tun yana faWa har ya gaji ya daina yi."

"Ummi kuwa tun daga kama ruwan da tayi, ta ji daWin jikinta, ta tsiyayi maganinta ta sha bayan ta ci gurasar nan, ta"

Wauki sabon phanta ta canza.

"Wani irin daWi take ji da nishaWi, ta sake bubbuWe kayan da ya saya mata tana jin daWin hakan."

"Ko da wasa ba ta yi gangancin fitowa daga Wakin nan ba, dan ta fuskanci ´an gidan ba ™aunar ganinta suke yi ba."

"Ana kiran sallar la'asar ta yi salla, ta cigaba da zamanta a Wakin."

"Kamar an watso su, taga farida da rahama a Wakin, hakan ya sanya ta tashi a razane."

"Farida ta ce ""Tashi munafuka, ai ba zama ki ka zo yi ba"" a zabure ummi ta tashi tana rarraba ido."

"""Ba dai kawo ki aka yi le™en asiri da saka mini ido ba, zaki ci ubanki sai kin bar mini gida da ™afarki"" idonta ya sauka a kan ™atuwar ghana must go sabuwa fil."

"Ta ce ""Rahama janyo mini jakar nan ki zazzageta, wato zuwa yayi ya kashe mata kuWi, wallahi ba zai yiwu ba ya daidaita da ´a´ana, kar ta san kar ai""."

"Rahama ta janyo jaka, suka zazzageta, farida har da ashar, farida ta saka farida ta tsitstsince mata kayan, phants Win"

"ma duk ta kwashe ta bar mata uku, Allah ya taimaketa, tana da sauran wanda ta zo da su, da na'ima ta saya mata."

"Cikin ikon Allah, Allah ya taimaketa basu lura da ™ullin kayan maganin da ke bayan katifar Wakin ba, heater da flask"

Win kuma suna cikin banWaki.

"Hatta omo da sabulun da ya saya mata, sai da suka kwashe ta bar mata Wai Wai."

"Sannan ta sake dubanta a wula™ance ta ce ""Ki buWe kunnenki da kyau ki saurareni, nan gidana ne, abun da na dama"

"shi ake sha, shima kwana biyu na sarara masa ne, amma tun da haka ya zaSa zan yi maganinku duka. Ki saka a ranki ke ´ar aiki ce kawai a gidan nan. Kullum da yamma idan yara suka taso daga makaranta, zaki wanke musu uniform ki goge musu shi tas, wanke-wanke da duk wani aiki a gidan nan ke zaki din ga yin sa, idan ki ga dama ki gaya masa babu abun da zai iya yi a kai, bari in gaya miki ™iri-™iri idan ki ka sake kiransa da Abba sai kin bar gidan nan, dan bai haife ki ba."

"Kuma wanki ba na yara kawai ba, kaya ko na waye sai kin wanke a gidan nan, tashi mu je ma ki fara aikin ki daga yanzu. mummunar banza kawai""."

"Rahama ta kwashe da dariya ta ce ""Ni wallahi fuskarta ma dariya take bani, wannan ba™i kamar a dangwala""."

"""Rabu da ita tashi ki wuce"" ummi kaf maganganun su babu wanda ya Sata wa ummi rai, dan ba yanzu aka fara yi"

"mata ba, ™wace mata kaya yafi komai Sata rai."

Sai dai wata zuciyar ta ce da kin san zaki samu ne?.

"Saboda tsabar mugunta akwai injin wanki a gidan, kuma akwai mai guga, amma farida ta tula wa ummi kayan"

"makarantar su Abdul, na boko da islamiyyar su, kusan kowanne nasa set uku, daga na makarantar boko har na islamiyya."

"Ummi ko a jikinta, ta dur™usa ta fara wankin kayan nan."

"Tas ummi ta wanke

Please Login or Register in order to submit comment