You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yake yi masa yoyo, ba zaku fahimci halin"

"da na shiga ba a kan raba ni da a ta"""

"""Eh dama ya za ayi mu gane mara kunya, ar farin ki ke wa haka"" mariya ta sunkuyar da kai tana murmushi."

"Kiran sallar farko, Raihan ya tashi, da yar ya yai shaiWan ya saukko daga kan gadon, ya je yayi alwala ya gabatar da nafiloli, sai da aka kira sallar asuba, ya tashi ummi shi kuma ya fita masallaci."

"Kafin ya dawo ta yi salla, ta koma kan gado, saboda gajiya da kuma bacci da take ji."

Jin motsinsa a kan gadon ne ya sanya ta farka ta buWe idonta da yar.

"""Kin yi sallar ne?"" Ta jinjina masa kai tare da cewa ""Good morning"" cikin kasalalliyar muryar bacci."

"""Morning honey, duk gajiyar ce ne, ake yi mini shagwaSa"" murmushi ta yi tana oarin juyawa, amma ya rie ta ya"

"sumbaci goshinta, ya gyara kwanciyarsa shima a gajiyen yake, dan haka bacci duk yayi awon gaba da su."

"A hankali ya yi juyi, ya nemi ummi ya rasa, kamar aljana, ya daWe a kwance yana mia, sannan ya saukko ya fito, can"

"Waya falon ya ganota, tana ta zazzagawa tana kallon ko ina, ta saka dogon hijjabi abun ta."

"Fito yayi, hakan ya Wan razanata ta waiwaya."

"""Me ki ke nema ne?"""

"Ta ce ""Bakomai, kawai na gaji da kwanciyar ne na tashi"""

"Ya araso falon ya ce ""Sai ki ka tashi ki kar bar ni? Ni fa yunwa ce ta taso ni ma, bari na kira hajiya a kawo mana abun"

"karyawa kan mutane su fara zuwa"""

"Ta ce ""Da in girka mana, kar a wahalar da su"" ya girgiza kai ya ce ""No, kina buatar hutu, kuma gidan bakomai na"

"masarufi, ban sayo ba tukuna bari na kira ta, akwai sponge da sabulu da toothpaste a drower mudubin Wakin da muka kwana, ki shirya kan mu fara bai""."

"Ta ce ""To"""

"A alla ta kai awa guda, sannan ta dawo falon, yana kwance a kan doguwar kujera, yana danna wayarsa, ya Waga kai ya kalleta cikin dogon hijjabinta, ya girgiza kai tare da yin murmushi ya ce ""Wane irin wanka ne haka fiye da awa"

"goma?"""

"Ta ce ""awa goma tun jiya kenan fa"""

"""Ai kin daWe ne, araso mu gaisa mana amaryata"""

"Cikin matsananciyar kunya, ta arasa gaban sa, ya tashi ya zauna, tare da zaunar da ita a kusa da shi, ya ce ""Kin tashi"

"lafiya?"""

"""Lafiya alau"""

"""To ya jikin naki? Are you ok now?"""

"Ta sunkuyar da kai, tana murza yatsun hannunta, da ya zame mata Wabi'a idan ba ta da amsar bayarwa ga tambaya."

"Cikin son ureta ya sake cewa ""To ya daren jiyan?"""

"Mutsu-mutsu ta hau yi, za ta tashi ta tafi, dan raihan Win ya wuce tunanin ta, kamar an canzo wani."

"Rieta yayi ya ce ""Ba in da zaki fa, yanzu dai bari in rama dukan da ki ka yi mini jiya, poor me kin kusa karya mini"

"ashi, you even bite my tongue daga kiss"""

"""Zan je Waki in yi abu"" tayi maganar cikin rauni."

"Yana dariya ya ce ""Koma menene yi a nan, amma sai na rama"" wayarsa ce ta fara ringing, ya Waga yayi sallama, daga"

"bisani ya ce ""Ok"""

"Ya katse wayar ya ce ""Bari na karSo mana abincin, hajiya ta aiko"" ta jinjina masa kai ya tashi ya fita."

Tayi ajiyar zuciya tana bin bayansa da kallo.

"Shiru ta yi ta tuna irin cin zarafin da idiris yayi mata, ta kwana a waje tsirara cikin ruwan sama, saboda kawai ya"

"same ta da larura, ta girgiza kai abun kamar ba zai wuce ba."

"Raihan ya yi sallama da aton kwando, ta tashi ta karSe shi, suka iso falon suka zauna."

"Sai dai ita ta kasa sakewa ta ci abinci, sai cakala take yi, ya ci ya oshi, ya hau kan kujera ya kwanta sai bacci."

Ummi ta lallaSa ta bar masa falon.

"Sai azahar sai ga su yaya maryam da mama, dan a washegari za su koma maiduguri, ummi ta ji daWin zuwansu,"

kamar ba jiya suka rabu ba.

"Suka kawo mata soyayyayiyar miya ta sha kaji, har da kayan gara, sun kai ruwa rana da dr. A kan kayan garar nan, ya"

"ce ba addini ba ce ba, idan ma sai an yi su bari a kwana biyu shi zai yi mata da kansa, suka ce sun riga sun zo da ita, sai dai ya yi hauri."

"A nan wasu daga dangin su raihan ma suka zo, suka tarar da su, wanda ba su samu damar zuwa ganin gida ba, ciki"

har da wasu daga annen mamin raihan.

"Kallonta suke suna zunWen ummi, ganin yadda take tafiya a takure, kamar mara kuzari."

"""Ji munafuka, kowa fa ya san bazawara ce, amma ji salon kinibibi da iskanci, wai a dole sai ta nuna wa mutane"

"budurwa ce"" suka yi ta surutun su, ummi ba ta ma san suna yi ba."

"Da za su tafi, mariya ta kama hannun ummi, tayi asa da muryarta ta ce ""Mamana, kin shiga sabuwar rayuwa, duk da baki da wayo sosai lokacin da na yi rayuwar nawa auren, amma aure ba soyayya ba ce kawai, kowane aure da"

"kalar jarrabawarsa, ni na samu soyayyar miji, alubale na danginsa ne."

"Ki rie Allah ki ji tsoron Allah, babu abun da ya gagari Allah, kar ki bari ki yi nesa da Allah, babu abun da zai yi galaba a kanki, sai abun da Allah ya addara. Ki rie mijinki domin Allah, banda yaji ko kan ara, matar da ta isa a Wakinta take yi wa miji yaji, ayi hauri, ayi hauri da juna"" sosai mariya ta yi wa ummi nasiha, sai dai a arshe ne kuma ta koma shirme."

"Da za su tafi ummi ta je ta kira shi, sai dai bai ji daWin garar da suka kawo ba, yaya maryam ta ce masa ai su normal ne al'adar su ce."

"Bayan tafiyar su ummi ta dudduba kayan da suka kawo mata, ta je kitchen ta jera wanda za ta jera, kayan miya,"

"busasshshen kifi, man shanu da sauran su."

"Kasancewar raihan ba ya Sangaren da take, kuma duk bain sun tafi, ya sanya ta Wan sake, tana ta Wan gyara in da"

aka Sata.

"Tana ta gyara abun da bai yi mata ba, tana yi wa kawu addu'ar samun buWi da alkhairi mara yankewa a duniya da"

"lahira, kamar an ce ta Waga kai, ta hango raihan a tsaye yana kallonta."

"Ta mie tsaye ta ce ""In zo ne, kana buatar wani abu?"" Ya Waga mata gira."

"Ta nufi in da yake tana takawa a hankali, cikin tafiyarta da yake cewa yanga ce tayi mata yawa."

"Ta arasa ta ce ""Gani"""

"Ya rio hannunta ya ce ""Dama kin tambaye ni ina buatar wani abun ne, mu je daga ciki to, sai na gaya miki me nake"

"buata"" danarewa ta yi a wurin tai yin gaba."

"""Ya haka kuma? Ke fa ki ka tambaye ni"""

"""A'a to na janye tambayar"" ta yi maganar tana son wace hannunta."

"Raihan ya yi dariya ya rie hijjabin jikinta ya ce ""Ummi nan fa ba muhallin hijjabi bane yanzu, aure muka yi, dan"

"Allah ki cire shi na din ga ganin kwalliyar ke ko zafi ba kya ji"""

"Ummi ta ce ""To, zan din ga cirewa"""

"""Ai yanzu nake son ki cire"" yayi maganar yana cire hijjabin daga jikinta."

"Doguwar rigar material ta saka, sai amshi take yi, ya cire mata ribbon Win kanta, gashin ya sauka a jikinta, ya gyagygyara mata zaman gashin ya ce ""Masha Allah, what a beautiful creature"" yayi maganar yana murmushi."

Tura baki tayi tana oarin karSar hijjabinta daga hannunsa.

"Ya rio ugunta yana are mata kallo daga sama har asa, tabbas ba dan ummi ta kasance ma'abociyar suturta"

"jikinta ba, da babu shakka mutanen banza su din ga bin ta, saboda duk in da ake fasalta mace mai diri, Allah ya yi wa ummi dirin jiki mai kyau da Waukar hankali."

"Suka koma falon suka zauna, sai dai ya hana ummi sakat da tsokana kala-kala, kuma ya rieta a jikinsa."

"""Komai na ki perfect baby, da headmastern nan ya yi gardama, da na yi masa abun da ban taSa yi ba"""

"Ummi ta Waga kanta ta kalleshi ta ce ""Wai dan Allah me ka ce masa ya fasa?"""

"Raihan ya yi murmushi ya ce ""Dubu Warin da ya ce zai baki kuWin aure, na bashi uku, na ce aje a mayar da wadda aka"

"saka a kula da iyali na gida, ya bar mini ke, jikinsa na rawa ya bar mini ke, dama na gaya miki na fi kowa sonki"" yayi maganar yana haWa fuskar sa da ta ta yana murmushi."

"""Cin hanci ka bashi dan ya bar maka ni, cin hanci ba kyau"""

"""A nan ya halarta"" yayi maganar yana dariya."

"Raihan na oarin Waukar su zuwa wata duniyar, wayarsa ta fara vibrating, sunan mami ne a kan screen Win wayar, ya"

Waga tare da yin sallama.

"""Raihan har ka fi arfin ka zo in da nake ka gaishe ni ko?"""

"Ya san a rina, ya kwantar da ummi a jikinsa sannan ya ce ""A'a ba haka bane mami, zan zo ne"""

"""Zaka zo sai yaushe? Har an yi ulle-ullen da zaka kasa zuwa ka gaisheni?"""

"""Mami, wallahi a gajiye nake ne sosai da sosai, na kira ki ma da safe baki Waga ba, but an ce mini gida haryanzu da mutane, na ce bari na yale ki, sai da daddare, amma in sha Allah a satin nan dole na na zo gaishe ki, na gaji ne"

sosai....

"""Dalla rufe mini baki, nusari shashasha. Yaushe aka yi daren da gari zai waye? Lallai lallai ka zo gida ina son ganinka,"

"yarinyar nan safiyya ma na kwance babu lafiya duk saboda kai, kar ka bari ka fusata ni"""

"Raihan bai yi mamaki ba, ya san a rina, amma shi bai ga haWin rashin lafiyar safiyya da shi ba, asibiti zai kai ta ko me zai yi mata? Kodayake ba abun mamaki bane ba idan mami na jin rigima."

"""Shikenan mami, zan zo in sha Allah"" sai dai tun da aka ambaci Safiyya, yana jin yadda bugun zuciyar ummi ya aru a"

irjinsa.

"Ya saka hannu ya Wagota, amma tai kallonsa."

"""Sweetheart, an fara kiran sallar magariba, bari na yi alwala na tafi masallaci"" ba ta kula shi ba, ta tashi ta nufi Waki,"

"ya bi bayanta da kallo, zubin manyan mata sosai."

"A hankali ya ce 'Haba mami, is too early for that'."

"Bai je kiran mami a ranar ba, dan ya san idan ya je da mutane a gidan, kuma sai ta yi wani abun da zata ci mutuncin"

"ummi, a gaban mutane dan haka ya i zuwa."

"Kwanan ummi uku a gidan raihan, ta fara girkin abinci, sai dai rigimar raihan har mamaki take bata, baya zuwa ko ina"

"sai salla, yana maale da ita kamar cingam, ga wani irin mugun kunyarsa da take ji, ta kasa sakewa da shi, kusan kullum cikin orafin saka hijjabin nan yake, ta kasa daina yawo da hijjabi."

"Kwana na ukun da daddare, Raihan ya je gida, sai da ya je wurin Hajiya yayi mata bangajiya, Alhaji dama baya nan,"

washegarin Waurin aure ya tafi umara.

Sai dai cikin fargaba ya isa sashin mamin.

"Ya tarar da ita ta hakimce, gefe ga Nihal a zaune, sai Safiyya da ke kwance a kan doguwar kujera."

"Yana shiga suka gaishe shi, ya amsa musu, sannan ya je gaban mami ya risuna yana gaisheta."

"""Sai yau Allah ya nufe ka da zuwa? Har ka sallami kanka na yi maka waya ka zo raihan amma ka i"""

"""Ba i na yi ba mami, wallahi bana iya zuwa ko ina, zirga-zirgar bikin nan na gaji ne wallahi"""

"""Uwar zirga-zirgar bikin, ka fito fili ka faWi uban abun da ya hanaka fitar, na yi dana sanin cewa zan yi maka aure ina ganin mafita ce, ashe ruwan dafa kaina ne, ka kwaso bazawara da ta tafi arfin ka, wallaahi ka shiga hankalinka, ka"

"san abun da yake yi maka ciwo"""

"Ta din ga yi masa faWa na babu gaira babu dalili, arshe ta rufe da cewar, watanni uku ta bashi, yazo ya nemi auren Safiyya."

"Ya ji ta da kunne kawai, ta gama ya ce zai tafi, ta ce ba zai tafi a lokacin ba."

"Ummi kuwa na gida na ta duba agogo, dan be gaya mata zai je wani wuri ba."

"Har arfe goma saura shiru bai dawo ba, ta kasa jurewa ta kira wayarsa."

"Bai ji nauyin mami da ke zaune tana kaWa afa cikin isa ba, ya Waga wayar ya ce ""Hello dear""."

"""Ina ka tafi tsoro nake ji"""

"Yayi murmushi ya ce ""Gani nan, babu dodo a gidan fa"""

"""Dan Allah ka yi sauri, tsoro nake ji sosai ko falo na kasa fita""."

"Mantawa yayi da mami a wurin, yayi dariya ya ce ""To yi ta addu'a kan na dawo? Kin ci abinci ne?"""

"""A'a"""

"Ya ce ""But you are not hungry ko?"""

"Ummi ta ce ""Eh"""

"""Ok ki jirani, in sha Allah yanzu zan taho"""

"Muryar mami ta jiyo tana cewa ""Zaka ajiye wayar nan ko sai na ci ubanka mara kunya"" a rikice gaban ummi ya faWi,"

ta kashe wayar ba ta san gidan ya je ba da ba zata kira shi ba.

"Mami ta tashi ta shiga Waki, raihan ya Wau mukullin motarsa ya fice da sauri."

"Abun da raihan yayi, ba aramin mamaki ya bawa mami ba, dan mugunta ta shirya yi, ta zaunar da shi har sha biyun dare, daga nan ta ce dare yayi ba zai fita ba sai da safe, bisa ga miyagun shawarwarin da Anty rakiya ta bata, sai dai"

abun da raihan Win yayi ya bata mamaki.

Ta din ga kiran wayarsa amma a kashe.

"A bedroom ya tarar da ummi, kai da ganin ummi ka san a tsorace take, ya ajiye kayan hannunsa ya ce ""Sorry dear, yi"

"hauri"""

"""Ban haura ba"" ta yi maganar cikin shagwaSa."

"""Yi hauri, ayi mini afuwa"" ba ta nuna masa ta san in da ya je ba."

"Ya cika cikinsa da abinci, yana ta yabonta tare da santin abincin."

"Ya koma ya hana ummi sukuni, ya gama tara mata gajiya, suna kwance babu tsammani ta ji ya ce ""Salma, me ki ka yi"

"wa mijinki na farko ku ka rabu?"""

"Gyara kwanciyar ta tayi, ta ce ""Meyasa ka tambayeni?"""

"Ya kalli fuskarta ya ce ""Am just curious about it"""

"Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Labarin babu daWi, auren huce takaici aka yi masa da ni, saura kwana uku aurensa, ba ya so na, ranar da ango ya tare a tsakar gida na kwana cikin ruwan sama, ba ya so na, tuntuni ni mummuna ce kuma ya"

"rasa wadda yake so yayi niyyar aure. Auren watanni biyu ne dai bai kai uku ba ma, watanni mafi tashin hankali, marasa daWin tunawa, na tozarta sosai a aurena na fari ko tunawa bana son yi"" tayi maganar tana zubar da hawaye."

"Ya rungumota jikinsa yana share mata hawayen, ya ce ""Is ok, you are much more than special, ke ta daban ce, kuma"

"ya yi wa kansa, ni kuma ya taimakeni irin sosai Win nan fa"" yayi maganar yana oarin zolayarta."

"Da safe da ya kunna wayarsa, da kiran mami ya fara cin karo, ya Waga ta are masa zagi tsaf, amma ko a jikinsa, shi"

"kasancewar sa da ummi, mantar da shi komai yake yi. Duk da kunyarta har ta yi yawa."

"Abu kamar wasa, raihan ya shafe sati biyu cirr a gida, ummi ba ta da aiki sai Worawa da saukewa, abokan aikinsa su"

"ka zo ummi ta yi musu girki, har da an china."

"Raihan ba ya jin duk wanda zai zo gidansa, saboda matarsa ta iya girki."

Haka zalika ga rigimarsa da ba ta arewa.

"Gidan farida kuwa, tun da Allah ya sa ummi ta bar gidan, komai ya taSarSare, kausar mugun sok jiki, ba ta iya aikata"

"komai, noor ce ma mai oartawa, ita ma idan ta gaji, sai ta watsar da aikin ta ce ta gaji, idan aka tursasata kuma, tayi abun da ba a so."

"Uban wankin da ummi ke yi musu, babu wanda zai yi yanzu, mopping gyaran Waki, da kuma girki duk abubuwan sai a"

"hankali, girkin ma ba daWi yake yi ba."

"Farida ta ce sai an samo ar aiki, dr. Ya ce babu mai kawo masa ar aiki, idan aka kawo ta kuwa sai dai ta din ga"

"biyanta, babu yadda za ayi ga kausar a gida, ba aure ba karatu, ace an Waukko ar aiki."

"Dr. Ya kira ummi ya tambaye ta me take so ayi mata da kuWin sadakinta, ta yi tunanin wata sana'ar, ya bata jari sauran ya cika ya saya mata kadara."

"Ummi ta tuntuSi raihan, amma ya ce a wannan lokacin, ba ta buatar sana'a a saya mata kadara kawai."

"Duk yadda mami ta so yin abun da za ta ure raihan, ta shiga hakkin ummi, raihan sai ya zille, ta yi masa faWa ta zage"

"shi, ko a jikinsa."

"Babban abun da ya ba ta takaici, bai wuce tana tsaka da duba saonni, ta ga raihan yayi status da special whats app"

"Win sa, da ba kowa ne ya san shi da shi ba, galibi family ne kawai ke da lambar."

"Hoton Ummi ya saka, tana zaune a kan dining, ta naWe kanta da mayafin doguwar rigar jikinta ""My perfect woman, khairun nisa'i, Allah ya ara miki lafiya"""

"Ya sake rubuta ""Goodnight ar aljannata"""

"A fili ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, bazawarar wannan mummunar"""

"Hankalin Safiyya ne ya koma kan mami, dan kuwa mami ta sanya safiyyan dawowa gidan da zama."

"""Mami menene?"""

"Ta mia mata wayar, bayan ta nemo status Win raihan."

"Gaban Safiyya ya faWi, duk yadda ake koWa munin ummi bai kai nan ba."

"Mami ta din ga zage-zage, tana cewa an asirce mata Wa."

"Sai da ta jera kwana biyu tana kiransa ya je tana nemansa, amma ya ce mata ai aiki yayi yawa a office, baya samun"

"isasshen lokaci, alhalin rabonsa da office Win tun saura sati biyu bikinsa."

"Asabar ce suna baccin safe, kiran Alhaji ya tashe su, raihan ya Wauka cikin jin nauyinsa."

"""Ango ka sha amshi"""

"""Alhaji ka dawo kenan?"""

"""Eh na dawo, baka nema na ko?"""

"Raihan ya ce ""Haba dai wane ni"""

"""To yaya ar tawa?"""

"""Gata nan tana jin ka, ta ce a gaisheka kan mu zo"""

"""To dan Allah ace mata ina roon arziki, a taimaka a bar mini kai ka koma office, ana ta kirana a waya ana nemanka"""

"Raihan ya ce ""To za a gaya mata, amma na zata saura sati biyu sannan na koma"""

"Alhaji ya ce ""A'a babban mutum, a duba mini lamarin nan"""

"Raihan ya ce ""Zan shigo in anjima in sha Allah, sannu da zuwa"""

"Alhaji ya sauke wayar yana murmushi ya ce ""Lallai babban mutum, ka ci gidanku da sati biyun"""

"Mami da ke kusa da shi ta ce ""Kana nufin ba ya zuwa aiki dama?"""

"""Da sabon auren zai fita aiki? Lallai wato ni ya mayar shashasha, idan na ce ya zo sai ya ce mini wai aiki ya yi yawa""."

"Alhaji ya kalleta ya ce ""Ya zo yayi miki me? Ango ne fa"""

"A fusace ta ce 'Angon banza, bazawarar?"""

"""Ba mace ba ce? Ke ina ruwanki ne, Bilkisu ki kiyayi shiga shirgin yaran nan kin i ko? Zaki yi ta fama da takaici kuwa"""

"Haushi ne ya ishi mami, tare da yi wa kanta alwashin, dole ta san abun yi a kan raihan da ummi, tun da tun ba aje ko"

"ina ba, kansa yana rawa."

"Ummi sai magiya take yi wa raihan, ya tafi da ita ta gaida Alhaji, ya ce mata sai an kwana biyu."

"Ta ja gefe ta kashingiWa a kan kujerar da suke ta ce ""To ka tashi ka je ka yi masa sannu da zuwa"""

"""Sai anjima"" yayi maganar yana Wora afafuwan ta a kan cinyarsa yana matsa mata."

"Ta buWe datar ta, taga messages da yawa sun shigo, ta din ga mamaki dan ita wanda take chatting da su ba su da"

yawa.

"Group ta ganta a ciki, na an makarantar islamiyyar su ne, kuma ta ga ana ta tagging Win ta, banda messages da ta"

gani ta private.

"Voice messages ta fara buWewa, ta din ga jin saonnin zagi da ashar, wai saboda ta auri anin maryam, ana ta cewa ta yi asara."

"Kashewa take oarin yi, ta ajiye wayar, ya karSe wayar, ya cigaba da saurarar abun da suka ce, tare da duba messages Win duk da suka yi."

"Tun tana jure jin, har ta karaya ta fara kuka, saboda cin zarafin yayi muni."

"Wayarsa ya Waukko, ya danna ya kara a kunnensa."

"""Zan turo maka wasu lambobi, ayi tracking Win su duk in da suke dan Allah, zan biya ko nawa, zan turo maka wani abu"""

"Ya ajiye wayar ya kalleta ya ce ""You don't need to cry anymore, zan yi dealing da duk wanda ya ce zai saka ki kuka ko"

"waye shi"" daga haka ya tashi ya fita."

"Gaba Waya jikin Ummi yayi sanyi matua, zagin da suka yi mata yayi mata zafi, tun da suka bar islamiyyar suka yi"

"aure babu wadda ta sake neman ta, sai yanzu da suka sakata a group na makarantar suka ci mata mutunci, da dawo da abubuwan da suka faru a baya, wai tana yawo duk da dauWa ga muni, dan son zuciya ta auri anin awarsu."

"Hankali kwance raihan ya je gida, ya shige wurin Alhaji, Alhaji ya din ga ce masa yayi iba ya ara kyau."

"Nan suka tare a sashen Alhaji, har da Hajiya da Salim."

Mami ce ta kira shi hankali a tashe ta na tambayar sa yana ina. Ya bata amsar yana sashin Alhaji.

"Ko mintuna uku ba ayi ba sai gata, ba ta damu da su hajiya da suke zaune ba, ta nufi raihan tana neman ta kai masa"

duka.

"Alhaji ya mie ya ce ""Bilki meye haka?"""

"""Aure hauka ne? A kan me zai sanya an sanda su kama matan mutane? Maryam ta kira ni tana kuka, an kama su an"

"kira shi a waya yai Wagawa, uban me suka yi maka?"""

"""Matata suka zaga babu dalili, tsakani nake so ayi musu, kar su zagar mini mata, ba tayi abun kunya ba dan ta"

"aureni"""

"""Ni ka ke gaya wa haka raihan?"""

"""Mami ba da ke nake ba, ba kuma da wata manufa na faWa miki ba, ni na saka ummi ta aureni, idan na zuba ido ana cin zarafin ta, ban yi mata adalci ba""."

"Hajiya ta yi murmushi ta ce ""Allah mai udura, Wan so ya faWa hannun matar so, ko dai ki bi a hankali ko ki rasa shi"

"gaba Waya"""

Ayshercool

08081012143

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji

Habil

Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

39

"MASU BUATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL INA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel

Please Login or Register in order to submit comment