You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin.

"Da suka fito ya kalleta ya ce ""Wai nawa zasu din ga biyanki ne?"""

"Cikin murna ta ce ""Dubu sha biyar duk wata"""

"""Me?""yayi maganar yana yatsune fuska."

"""Dubu sha biyar"" ta maimaita masa."

"""Share-share zaki din ga yi ne? Ki zo ki wuni a dubu sha biyar, duk girman shagon nan dan son kai""."

"Ummi ta waiwaya ta ga babu wanda yake jin su ta ce ""Kayi a hankali, dubu sha biyar ina laifi, da waye ya bani?""."

"""Degree holder da aikin dubu sha biyar a wata, me 15k zata yi miki a wata, mussman ku mata masu tsarabe-tsarabe,"

"ni fa a wata data da katin waya na dubu ashirin nake sawa zuwa sama"" Ummi ta buWe baki tana kallon sa, saboda abun ya Waure mata kai, har ya kaita gida mita yake yi, yana nanata dubu sha biyar ta yi kaWan, tayi masa shiru tai kula shi. Dan in dai shariya ce ummi ta ware a wannan fannin."

"""Ni ki ka share ko, wato idan na gaji na yi shiru?"" gyara zamanta tayi tana cigaba da kallon window."

"A hankali ya ce ""Miskili ka fi mahaukaci ban haushi""."

***

"Misalin arfe goma sha biyu da rabi na dare, raihan da mahaifinsu, chief accountant da sauran accountants mutum biyu, lawyoyin Alhaji Tahir su biyu, sai kuma manajojinsa, zaune a wani katafaren office, ko ina fitilu kamar rana, kowa gabansa da ruwa da lemo, gefe ga flask na shayi, gaba Wayansu raihan ne kawai yaro a cikinsu."

aya bayan Waya kowa ya din ga gabatar da bayaninsa n shekara a kan Sangaren da yake jagoranta.

"Suka kammala tsaf, sannan raihan ya tashi, ya yi connecting system Win sa da projector, ya fara bayanin abubuwan"

"da ya tattara daga bayanan su, ribar da suka samu a shekarar, ya tabbattar wa da mahaifinsu duk sun bibiyi shige da ficen kuWi na shekarar, kuma sun yi dai-dai da bayanan da abun da kowane accountant yayi presenting."

"Ya ware harajin da zasu biya, na ciki da wajen Nigeria, ya ware kuWin zakka, kuWin abun da ake rabawa ma'aikata na riba bayan albashinsu, abubuwan da suke buata, kuWin duk wani abu da ya shafi sadaka da makamantansu, da kuma kuWin umara na mutum goma, kamar dai yadda Alhajin ya umarce shi."

"Tafa masa Alhaji Tahir ya hau yi, ya ce ""araminsu babbansu, am so much proud of you, ban zaci zaka iya oari"

"haka ba, saboda na san aikin ba arami bane""."

"Chief accountant ya ce ""Ni kaina ya bani mamaki, yayi oari sosai da sosai, na bi duk abubuwan da yayi, kamar dai yadda ka saba ne, yayi iya yin sa, kuma da alama zai kamanta adalci kamar dai kai, sai dai rigimamme ne"""

"Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce ""Ai na san halin kayana"" suka yi dariya baki Waya."

"Suka arasa tattaunawa, da bibiyar abubuwan da Raihan ya gabatar, daga bisani Alhaji Tahir ya ce kowane Sangare"

"su rubuto abun da suke buata, na gyara ko makamancin haka, raihan zai duba, shi zai je hutun taaitaccen lokaci."

"Duk suka gamsu da abubuwan da aka tattauna, tare da yi wa Alhaji Tahir addu'a saboda mutum ne mai farantawa"

"ma'aikatansa, dan ya ce abokan nemansa ne, bayan iyalansa ba shi da sama da su."

"Dirver ya Wauke su zuwa gida, a hanya raihan ya ce ""Alhaji"""

"""Na'am babban mutum"""

"""Tsakani da Allah aikin nan da wahala, kuma ko murmurewa ban yi ba, ka ce a kawo mini duba wani abu, ni fa ban"

"san komai ba, dan Allah a kaiwa su yaya sagir, gaba Waya an kwanakin nan saboda aikin nan, ko bacci bana yi sosai"" ranwashin da Alhajin yayi masa ne ya sa shi yin shiru yana kallon sa."

"""Kana da nasibi a kan harkar kasuwanci raihan, amma wasa da shiririta sun yi maka yawa, da aikin kashe-kashen"

"kuWi, office zan baka a head branch, a din ga baka salary"""

"Cikin sangarta ya ce ""A'a dan Allah, shagona fa da nake ta processing, ka fa bani jari rance, ka manta, kayana sun"

"kusa zuwa fa""."

"""Na sani raihan, akwai abun da nake targeting ne"""

"Raihan ya ce ""To, Allah ya taimaka, amma ba sai na sake duba wani abun ba ko? Kuma ba sai na yi maka aikin ba"

"ko?""."

"""Sai fa ka yi, gara ma ka shirya"""

"Raihan ya kifa kansa ya ce ""Wayyo mami, dama ban dawo kano ba"""

"Alhaji Tahir yayi dariya ya ce ""Ko ina ka tafi, i know how to deals with you, Munnir ya sangarta ka, kashe kuWi kawai"

"ka iya, baka iya nema ba"" yayi maganar yana murWe masa kunne."

"Raihan ya Wago da sauri ya ce ""Ka tambayeshi ka ji, na sayar da agoguna, na sayar da takalma, kuma na tara kuWi"""

"Alhaji Tahir dariya kawai yake yi wa raihan, so yake dole sai ya zame, kuma ya san dalilin sa na yin haka, dan raihan"

"akwai biyayya in dai abu zai faranta masa rai zai yi, da mamansa ne ma suke faWa wasu lokutan ba su fiye shiri ba, idan ta zo da abu na son zuciya, ya ce ba zai yi ba."

"Duk da ummi ta Wan girmewa Raihan, sannu a hankali ya nuna mata shi namiji ne, domin kuwa yafi ummi wayo nesa"

"ba kusa ba, dan bata ankara ba, suka yi wani irin mugun sabo da ita da shi, duk Wari-Warinta da shi, ta sake jiki da shi, dan barkwancinsa kawai nishaWi yake saka ta."

"Kullum a wurinta yake karyawa, da safe sai ta tafi masa da abinci, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya sanya mata"

ido ya lura da shige da ficenta.

"Shi kansa raihan a tarayyarsa da ummi, ya san tana da baki dan tana magana tana tsoron yi ne, saboda yanayi na"

yadda al'umma suke karSar ta.

"Idan suna hira, wasu lokutan manager sai ya kalleta ya ce ""Wai ummi dama kina da baki haka?"" Sai ta yi shiru ta"

daina maganar cikin jin kunya.

"Gaba Waya ta daina jin nauyin raihan, haka kurum sai ya zame daga office, ya taho wurin aikinta, manager har"

"tambayarsa yake ""Wai kai Raihan baka sana'a ne? Kullum kana lie a wurin ummi?""."

"Kasancewar manager matashi ne, da kaWan zai girmewa ummi, anin mai shagon ne, dan haka Raihan ya ce ""Eh ni"

"bani da sana'a, zaman banza nake a yanzu, shiyasa kullum muke tare da ita""."

"""Ta ce Abdul yayanta ne, kai kuma aninta, anya ba ka girmeta ba kuwa? Ka yi ta mata wayo, ta zo da Wan abincinta,"

"ta ajiye maka ka zo ka cinye, ka hanata sakat da surutu, ka zo in baka aiki kaima""."

"Raihan ya ce ""Allah ya kiyaye in yi aiki ku biyani dubu sha biyar, dan wayo, dan kun ganta saliha, ai ta kusa daina"

"aikin nan""."

"Manager ya ce ""Ai tawakalli ta fika, shiyasa take aikin, kai ka raina sana'a, kullum kana lie da ita, ka cinye mata abinci, kuma kana jiran a biyata ka karSe mata kuWi""."

"Raihan ya ce ""Wai manager abincin nan daga gidanka ake kawo wa ne? Ina ruwanka ne ka dameni fa"""

"Idan suna abun su shi da manager, sai dai tayi ta dariya, kamar sako da sako manager komai sai yayi magana,"

shikuma raihan baar magana da neman tsokana.

"Ummi na jin daWin aikinta a wurin nan, ko albashin farko ba a bata ba, amma manager yana daga cikin mutanen da"

"suke mutuntata, bai taSa nuna mata yama ba, kuma tana iya oarin ta wurin kula da coustomers Win su, idan ta je da wuri ba ruwanta, har share-share yi take yi tayi mopping gaba Waya ba ta da damuwa."

Zamanta a wurin yana rage mata damuwoyi da yawa.

"Yanzu ma tana ta bawa raihan labarin rigimar noor, ba ta da wata hira sai ta noor."

"Cikin nishaWi take hirar, Raihan yana kallonta, ya ce ""Ya aka yi haorinki Waya ya Salle ne? Ko dai da kina yarinya kin"

"yi rashin ji ne?"""

"Ta yi murmushi tana dariyar yae, da tuna yadda aka yi haorin ya Salle ranar salla ta ce ""A addara bana jin"

"magana ne, na taho da gudu ranar salla, na faWa cikin kwanuka na buge baki da tukunya, haorin ya Salle"" tayi maganar tana tuna yadda idiris yayi ball da ita ranar."

"Raihan yayi dariya ya ce ""Ai da alama, kuma fa da ya Salle Win yafi kyau, amma dai mijinki sai ya rage sadaki, saboda"

"Sallewar haorin nan, duk da ta wani fannin sai ya ara, tun da kina cikin matan da malaman fihu suka ce a arawa sadaki""."

"Basar da zancen tayi, saboda jin zai Waukko wani babban karatu mai nauyin gaske, ita ina ta ga ko saurayi balle ayi"

"zancen ari ko ragin sadaki, ita da tun da take, ba wanda ya taSa cewa yana sonta?."

"Raihan yayi mugun sabo da abincin ummi, kusan kullum a wurinta yake karyawa, ba tare da ya san abincinta take"

sadaukarwa ta bashi ba.

"Suna tafe a hanya ta ce ""Raihan, manager ya ce a satin nan fa za a biya salary"""

"""Dubu sha biyar Win ki ke wa wannan washe bakin?"""

"""Eh mana, idan Allah ya saka mata albarka zaka sha mamaki""."

"Ya ce ""Oho dai, amma dubu sha biyar ya fi kuWin mayukan da zaki shafa a sata"" ta ware ido ta ce ""Ni Win? To wallahi vaselin nake shafawa ko man kaWanya"""

"Yayi murmushi ya ce ""Amma zaki kai aninki shopping ko? Muje ki yi mini sayayya"""

"""Me ka ke so in saya maka?"""

"Raihan ya ce ""Sai mun je sai in zaSi abun da nake so"""

"Ta ce ""To shikenan, in sha Allah idan aka biya sai mu je, nima na je shopping ban taSa zuwa ba fa, to ina zamu je?"""

"""Ki yi tunanin in da ki ke so mu je"" ta jinjina masa kai tana ta murmushi, wai duk saboda dubu sha biyar take"

wannan farincikin.

"""Yauwwa, ya ake ciki da aikin Alhaji kuwa?"""

"Ya ce ""Hmm kin san ya kuma haWa ni da wani, alhakin fitar da zakka, da mutanen da zai biyawa umara da aikin hajji"""

"Ummi ta Wan yi shiru ta ce ""Masha Allah, sai ka tsaya ka ji tsoron Allah, kar ka bari son rai ya shiga lamarin, wataila ya yi hakan ne dan ya gwadaka, ka bawa wanda suke buata kayi adalci"""

"""Haka ne ya sayyada, shiyasa ban so ya sakani ba, kin san ina da yayye, kamar ba zasu ji daWi ba tun da su ne manya,"

"tunda ki ka ce ina ma zaki sake ganin baba ya saki aiki, zaki yi farinciki, sai na sha jinin jikina, komai lokaci ne, wataran da kuWi nima zan nemi na ganshi ya sakani aiki, ba zan ganshi ba"""

"Ummi ta ce ""Wannan haka yake, Allah ya ara masa lafiya da nisan kwana, ya yalwata arzikinsa"""

"""Amin ya Allah sayyada"""

***

"Kamar kullum sai da ya mayar da ita gida, sannan ya koma office ya cigaba da ayyukan sa, bayan la'asar ya koma gida."

"Mami na ganinsa ta hau murmushi, wanda har hakan ya bashi mamaki, ya ce ""Mami na ga kina ta fara'a"""

"Ta ce ""Ashe kai Alhaji ya saka duba mutanen da za a bawa zakka, da wanda za a kai umara bana, har da aikin hajji"

"mutum uku?"""

"Ya kalli mami ya ce ""In ji wa?""."

"""In ji ubanka, da baka gaya mini ba, ai ni mijina ne ya gaya mini"""

"Ya Wan yi mia ya ce ""To shikenan tun da ya gaya miki"""

"Mami ta ce ""Ohh, Allah dai ya cika mini burina, to su wa ka zaSa? Dan ina da vacancies""."

"Ya dubi mami ya ce ""Vacancies kuma, na me?"""

"""Ahh wanda za a bawa zakka mana da wanda za a kai umara har ma da aikin hajji""."

"Raihan ya Wan yi shiru sannan ya ce ""Amma ni mami, duk a gidanku su Anty Saude, ba wanda ba a kai aikin hajji ba"

"wasu umara, awayenki kuma duk suna da rufin asiri, to wa kuma za a baki? Ai gara a kai waje wasu ma su amfana"""

"Ta ce ""Kai dalla yi mini shiru, nima na san waWanda suke da buata, ka bani vacancies, da kuma kuWin da zan bayar"

"nima, duk shekara Alhaji yana bani, maganar ma na yi masa ya ce kai ya bawa wannan damar""."

"Raihan ya Wan Sata fuska ya ce ""Haba mami, dan Allah me zaki yi da kuWi? Zan baku vacancies huWu, ke biyu Hajiya biyu shikenan, kuWin zakka kuma gaskiya ba zan iya baki ba, an ware percentage Win share ku fa, a ribar da aka fitar"

"ta shekara za a baku"""

"Mami ta shiga tafa hannu, ta ce ""Raihan, wai tsaya ni da hajiyar nan muka yi naudarka, da komai sai ka daidaitani"

"da ita, kuWin mijina ka ce ba zaka bani ba Raihan, shikenan ba zan kyauta ko sadaka ba nima?"""

"Ya mie yana zumSura baki ya ce ""Dan Allah mami kiyi hauri, nifa ba haka muka yi da Alhaji ba, what if gwadani yake yi, wallahi kin fi Hajiya yawan ci masa kuWi ma, haba mami dan Allah"" sai ta kasa magana ta bi shi da kallo,"

"gashi dai ita ta haife shi, amma idan ya botsare, wasu lokutan kasa magana take yi, dan bata san dalilin da ya sa yake yi mata kwarjini ba wasu lokutan, idan ta yi ba dai-dai ba Saro-Saro yake gaya mata."

"Manager ya kira ummi a waya, ya ce ta turo account number zai tura mata kuWinta na albashi."

"Bata da account number, dan haka ta kira raihan jikinta yana rawa dan farinciki ta ce ""Raihan, manager ya ce na tura"

"account number, zai turo mini salaryna, amma bani da account, ka bani naka na bashi"""

"Yayi dariya ya ce ""Gaskiya banki za su rufe mini account Wina idan aka saka dubu sha biyar, ni kuWi idan bai kai dubu"

"Wari ba, basa shiga account Wina""."

"Ta ce ""To ko kawai in bari sai da safe idan Allah ya kaimu, idan na je sai ya bani a hannu kawai ko?""."

"""Ina da lambarsa zan tura masa, amma dan Allah kar ki kasa bacci saboda dubu goma sha biyar, kuma kar ki manta"

"kin yi mini alawarin zaki kai ni shopping""."

Ayshercool

08081012143

What's app only please

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P25

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu"

Abduljalal

Wata kissar sai mata Wuta a masaa Cutarwa

anwar maza Gaba da gabanta Aidata

RuWin uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata.

8081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha

Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

25

"Cikin murna ummi ta ce ""Ban manta ba, in sha Allah zamu je, nima ina son mu je""."

"""To kin zaSi in da zaki kai ni Win?""."

"""A'a ai ni ban san wuraren ba, ko ina ne ma kawai sai mu je"""

"Yayi dariya ya ce ""To shikenan, amma dai dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi bacci a nutse kar ki kasa bacci"

"saboda 15k, you are not Wangote yet, kar ki kasa bacci saboda 15k dan Allah"""

"Ummi cikin halinta na yanga da ita ba ta gani ta ce ""Kar ka dameni fa, ce maka aka yi ba zan iya bacci ba, kuma ko"

"naira goma ce tunda ita ce gumina ai ita ce arzikina dole na yi murna"""

"""Ahaaf, ai na san ba iya bacci zaki yi ba saboda dubu sha biyar, to dai ki nutsu da ar 15k Winki kin kasa rufe baki""."

"""Ai kuma sai ka yi, ba kula ka zan cigaba da yi ba"""

"Sosai yake yi mata dariya, noor ce ta shigo Wakin ta ure ummi da take dariya da ido."

"Cikin diriricewa ta ce ""Raihan sai da safe""."

"""Akwai matsala ne?"""

"Ta ce ""A'a zan yi wani abu ne"" ta katse wayar tana kallon noor."

"Noor ta arasa ta zauna ta ce ""Yaya ummi da wa ki ke waya ne?"""

"Ummi ta ce ""Amm Wan ajinmu ne"""

"Noor ta waro ido ta ce ""Ke fa ki ka ce an ajinku ba sa kulaki, kuma ba kin daina zuwa makarantar """

"""Kai maman arya nake yi kenan?"""

"Noor ta ce ""A'a, to amma me ku ke cewa na ga kina dariya, ban taSa ganin kina waya kina dariya haka ba, ko kema"

"saurayin ki ka yi?"" Da sauri ummi ta girgiza mata kai alamar a'a."

"""To me ku ka ce a wayar"""

"Ummi ta ce ""Noor kin fa isheni, magana muke za a bani salary ne, shi ne nake dariya, ai kiwa yana son kuWi, ko ke ba"

"kya so?"""

"Noor ta ce ""Ina so mana, zamu ci daWi ashe"""

"""Sosai ma"" ummi ta yi maganar tana murmushi."

"""Kin san me yaya ummi?"""

"Ummi ta ce ""Sai kin faWa maman"""

"""Inteesar ce ta zo fa yanzu"" ummi ta Wan waro ido, ta kalli agogon wayarta arfe goma da rabi na dare."

"Ta basar ta ce ""Inteesar kawai ko? Ba na hanaki ba, ba zaki ce mata anty inteesar ba?"""

"""Kema ai ummi take ce miki, kamar fa kuka take yi, sun shige Waki ita da maama, na je in ji meyafaru wai in fita har"

"da ce mini munafuka""."

"Ummi ta kwantar da noor ta ce ""Shhh maza yi bacci, kar in sake jin bakinki, hakan gulma kenan kuma haramun ne"

"babu kyau"""

"Noor zata sake magana, ummi ta rie mata baki, tayi murmushi ta lumshe idonta kamar zata yi baccin."

"Ummi ta kashe musu fitila, ita ma ta kwanta, amma noor ta tashi ta lallaSa kunnen ummi ta ce ""Wai mijinta ne zai"

"auro mata kishiya, uncle sagir"" ta sauka daga kan katifar ummi ta fita da gudu."

"Sai da gaban ummi ya faWi, ta san akwai tashin hankali kenan, tun da aka ce za a yi wa ar gwal kishiya, tayi saurin"

kawar da tunanin daga ranta dan ba huruminta bane ba.

"Maganar raihan ta tuna, wai kar ta kasa bacci, saboda dubu goma sha biyar."

"Dariya abun ya bata, ta gyara kwanciyarta ta shiga karanto addu'oin kwanciya bacci."

"Aikuwa da safe da ta tashi, ta ga inteesar a gida, idanuwanta sun kumbura alamar ta sha kuka, kuma ba ta samu"

isasshen bacci ba.

"Ummi ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama."

"Daga haka ummi ba ta sake shiga sabgarsu ba, dan ta ga alamar iris suke jira tayi wani abu, su huce a kanta, dan"

"haka ta kama kanta, ko sallama ba ta yi musu ba ta fice."

an halak yana in da suka saba haWuwa yana jiranta.

"""Ina kwana"" ta gaishe shi, sai dai maimakon ya amsa ya ce ""Inye ka ga attajirar garin nan, ke fa yau jin kanki ki ke yi"

"daidai da kowa, saboda kina da 15K"""

"Ummi ta ce ""Ka cigaba, tuwo ne yau a cikin flask Win nan, wannan kuma kunun tsamiya, ka cigaba da tsokanata ba zan baka ba"""

"Ya kwashe da dariya ya ce ""Aikuwa sai na ci abincin nan, kuma ba zan daina tsokanar ki ba"""

"""Sai ka ci in gani ai"""

"Raihan ya kunna motar ya ce ""Girmata fa ki ka yi, ba fin arfina ki ka yi ba, wace abincin nan ba wahala zai bani"

"ba""."

"Ummi ta ce ""Idan ya zube shikenan ba""."

"""Kar dai ki manta kuWinki account Wina za a tura su, attajirar duk duniya""."

Ummi tayi dariya tana kallon window.

"Suna zuwa wurin aikin ummi, raihan ya ce a wurin zai ci abincin, idan ya tafi da shi ba zai oshi ba."

"Suna shiga wurin bayan sun gaisa manager ya ce ""Ummi, an saka miki kuWin nan fa"""

"Raihan ya ce ""Eh, sun shigo sai ka ce wasu kuWin kirki, gaskiya manager a ara kuWin nan, haba 15k yafi ta sai man"

"shafawa da cingam""."

"Ummi ta kalli raihan ta girgiza masa kai ta ce ""Manager na gode sosai da sosai, Allah ya aro mana coustomers, dan"

"Allah kar ka damu da abun da raihan yake faWa, Allah ya sanya musu albarka ka san yaro ne, sai a hankali"" tayi maganar tana kawar da kanta gefe tana dariya."

"Manager ya kwashe da dariya ya ce ""Ai shiyasa bana biye masa, bainciki yake yi miki, shi yana zaman banza,"

"wallahi ko kati kar ki saka masa""."

"Kallon ummi raihan yayi ya ce ""Me ki ka ce mini yanzu?"""

"Juyawa ta yi tana dariya, ta nufi wurin da take zama, tayi aiki."

"Aikuwa ya bi bayanta, yana sake cewa ""Maimaita me ki ka ce mini yanzu?"""

"Ta ce ""Na yi magana ne?"""

"Ya Wan tsuke fuska ya ce ""Ki maimaita""."

"Ummi ta kalli raihan ta ce ""Yaro, ko ba yaron bane?"" ta sake maganar tana yi masa dariya."

"Kyau ya ga tayi masa dariyar da take yi, haoran nan sun haska fuskarta sosai, ga laSSanta pink shar, dimples hagu"

da dama a kumatunta.

"Yadda ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta zata, ko haushin yaron da ta ce ya ji, dan haka ta sake cewa ""Lokacin da ka"

"ke tsokanata, daWi ka ke ji ai, nima yanzu is my turn""."

"Yayi wani irin murmushi ya ce ""Wai shekara nawa ki ka bani ne? Na san dai maryam ta girmeki""."

"""Ba za a lissafa ba, koma dai yane kawai na girmi mutum, kuma idan kana son ka yi albarka ka din ga yi mini biyayya"

"ka daina tsokanata"""

"Ya ja kujera ya zauna, har cikin ransa yake jin daWi idan ya ga ummi ta sake da shi tana dariya, saSanin da da kullum"

"kamar a tsorace take da mutane, da farkon haWuwarsu ne, ko haWa ido ba za ta iya yi da shi ba, amma yanzu da confidence take gaya masa abu."

"A ransa ya ce 'Irin wannan confidence Win nake son ki samu, a cikin mutane"""

"Manager ya ce ""Kai raihan, ka wani je ka gurfana a gabanta, zaka kalallame ta ka cinye mata kuWi, to ahir Winka"""

"Raihan ya ce ""Manager, idan na waiwayo kanka ba zaka ji daWi ba, yau ka sa an kirani da yaro, duk girman nan nawa,"

"the whole me aka ce mini yaro, ke kuma ai shikenan ban abincina in ci, shima dan ba zan iya fushi da abincinki ba, da yasin ba zan ci ba"" yayi maganar cikin sigar shagwaSa."

"Ummi ta yi asa da murya tana kallonsa ta ce ""Haba kar aji kanmu ayi mana dariya, ci abincinka ko manager kar ka yi"

"wa bisimillah"""

"""Dama shi ya isa?"""

"Ummi ta tashi tana ta Wawainiya da coustomers, raihan yana cin abinci, suna yi suna faWa da manager."

"A hanya ummi take yi masa faWa kuma ta haWe rai kamar wata babarsa ""Raihan, ka ce Alhaji ya baka aiki, amma sai"

"ka zo wurina ka yi zamanka ka i yi masa aikin, ko office Win fa baka zuwa, meyasa?""."

"""Haka aka ce miki bana zuwa?"""

"""To yau ka je ne? Zama fa kawai ka yi a wurin aikina, yakamata ka kammala yi masa aikin nan on time, sai shiririta ka"

"ke yi"""

"Raihan ya ce ""Nifa ba shiririta nake yi ba"""

"""To aikin ka ke yi? Banda surutun wallo, me ku ka yi kai da manager? Gobe in Allah ya kaimu ka je office ka yi aiki,"

"idan ba haka ba, ni da kai

Please Login or Register in order to submit comment