You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma ban ce ki saka baki a kan maganar ba, tun da ni mai kuWin ban yi magana a kai ba"""

Kawai Hajiya ta kwashe da dariya.

"Farida tana ta murna, dr. Bai ce mata komai ba tsawon kwanaki, ya sanya ta saki jiki ta cigaba da sabgoginta, noor"

kanta ta san zancen auren dr. Amma ta yi shiru ba ta gaya wa farida ba.

"Da daddare ta shirya tana jiran dawowarsa, tun safe tana kiran wayarsa shiru bai Waga ba, tun da ya fita da safe bai dawo ba."

"Shigowa yayi cikin manyan kaya, da gani ka san a gajiye yake, ta bishi Waki tana tambayar sa ko lafiya."

"Ya zube mata goro da alawa, ya ce ""lafiya alau ga wannan an Waura mini aure yau a Maiduguri"""

Ayshercool

08081012143

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha

Dilke da kalta

Kayan Garan jiki

Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI. CUTARWA!"

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

46

PAID ADVERT

"*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? an bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir Win da na zo miki"

"da shi. Shin ko kin san sirrin shein fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sano, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson arfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuSe su a kan lambar wayar su dan arin bayani 07045971194 ko 08140450950*"

46

"Wata irin zabura farida ta yi, ta fizgo babbar rigar dr. Ta ce ""Ni! Ni yahaya wai da gaske ka ke ko wasa?"""

"""Na taSa yi miki irin wannan wasan ne? Na yi aure kamar yadda na gaya miki"""

"Girgiza kai ta yi ta ce ""Ni zaka ci wa mutunci, wallahi idan bacci ka ke gara ka farka, dan baka isa ba, da can da"

"uruciyata ba ka yi mini kishiya ba sai yanzu? Wallahi ba zai yiwu ba ba a gidana ba"""

"Ya fizge hannunta ya ce ""Ni nake aurenki ba ke ki ke aurena ba, farida rashin mutuncinki da wulaancin da ki ke yi"

"mini, ya sanya na yi miki koma menene. Aikin gama ya riga ya gama, zan gyara tsohon gidana na sakata a ciki, nan da sati Waya zuwa sama idan visarta ta zama ready zan tafi da ita uganda. Zan saka miki dubu Wari biyu da hamsin a account Winki, kya sayi wani abun"""

"""Dubu Wari biyu da hamsin Winka ta banza da ta wofi, wallahi ba zai yiwu ba"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Ya riga ya yiwu ma, ba wata ba ce na aura a waje, mariya ce mahaifiyar ummi, abun da yakamata"

"na yi ne tun a baya, ban samu dama ba, sai a yanzu"""

"Farida ta ce ""Ka rasa wadda zaka auro a matsayin kishiyata sai mahaukaciya, wallahi yahaya kai butulu ne azzalumi"

"wallahi ba zan zauna da mahaukaciya ta kashe ni a banza ba, kai ba zai taSa yiwuwa ba ma wallahi ni zaka tozarta?"""

"Ya tsaya ya are mata kallo ya ce ""Farida, duk abubuwan da suke faruwa a baya, kallonki kawai nake yi, tsantsar zaluncin da ki ka yi wa yarinyar nan a zamanta da ke, ina kallonki, saboda ba ki da mutunci kin mayar da ni Wan iska"

"da son nuna wa duniya ban isa da gidana ba, auren ummi ya samu matsala ta zo gidan ki koreta ga dare, saboda baki da hankali kin san yadda nake jin yarinyar nan a raina kuwa? Ita kaWai take babu wa ba ani, ki yi mini alfarma ki rieta da mutunci ki ka gaza, bayan ni na rie taki ar uwar babu cuta babu cutarwa? Wannan dalilin ne ya sanya na ga lallai yakamata ummi ta ara shigowa cikin iyalina in sama mata farinciki ta hanyar auren mahaifiyarta, na san kome zai sameta a rayuwa ba zata taSa korarta ba"""

"Tayi wata irin shewa mai cike da takaici ta ce ""To ayi mu gani? Wannan dai ba abun da zata tsinana maka, ba uban"

"da zaka tsinta a tare da ita, ka ce auren na ramuwar gayya ne? To ka yi mu gani, wallahi sai ka yi bankwana da farinciki da kwanciyar hankali har abada""."

"Ya nufi gadonsa yana faWin ""Allah ba zai gwada mini rashin kwanciyar hankali ba, in sha Allah auren nan alkhairi ne a"

"gareni"""

***

"Cikin mamaki da takaici mami take kallon hajiya, da take yi mata dariya cike da son tura mata takaici."

"Ta ce ""Wato Alhaji a duniya mace ta samu nagartaccen miji irin raihan, to ta Waga hannu ta godewa Allah ta haye, yaron kirki Allah dai ya ja zamanin babban mutum"""

"""Hauwwa babu ruwanki da ni, da sabgar iyalina ban saka da ke ba, ashe shiyasa ki ka turo makakken Wanki ya ci mini mutunci yana gaya mini maganar banza, wallahi ki shiga hankalinki babu ruwanki da ni"""

"Hajiya ta ce ""Ko ba makakke ba, ai gara makakken waya, idan wayar ta sake shi zai iya dawowa daidai, wanda yake"

"cikin mayen soyayya kuwa ko za a shekara dubu ba zai farfaWo ba, dan haka akwai banbanci ko dai ki nutsu ki yi playing role Winki na uwa, ko kuma idan yarinyar nan ta waiwayeki, ki ka cigaba da saka mata iyayyar ki, sai ganin Wan naki ma ya gagare ki, Wan Waya tilo da ki ke alfahari da shi shiryayyye ta rabaki da shi""."

"Alhaji ya ce ""Hajiya wai kwanan nan meyake damunki ne? Ban sanki da irin wannan abubuwan ba, idan tana yi a"

"baya ba kya mayar mata da martani, amma yanzu duk kin canza"""

"Ta ce ""Duka yau duka gobe shi yake sanya bain ba'auzine tawaye, kuma komai girman gona akwai kunyar arshe, sai a wannan karon Allah ya kawo ni lokacin ramawa da mayar da martani, ko kun manta Wigimin da ku ka din ga yi"

"da ka aureta, sai da na ji kamar mu rabu na huta, Hajiya Aisha tayi ta bani hauri, matar nan ta din ga yi mini gorin zafin kishi zan kashe aurena ita tafi arfin goga kishi da ni, ka din ga yi mini halinku na maza? To Alhamdilillah koma"

"menene abun kunyan da na yi, bai kai naki ba da ki ke kishi da matar Wanki, duk da zafin abun da ki ke ji, bai kai"

wanda na ji ba da ki ka auri mijina.

"Anyway, Alhajin Allah zan shiga in yi wa sirikata Wan abun da zan tafi mata da shi na dubiya, ka san mace mai ciki bakomai take iya ci ba, idan ana inta ni ina yinta tun ba yau ba, dan gara munin fuska da munin hali, duk da Alhamdilillah ba ta da muni"""

"Alhaji kuwa sakin baki yayi yana kallon Hajiya, ta gama cashe musu ta fice."

"""Ciki kuma? Ba cewa yayi ba shi da lafiya ba? A ina ta samu ciki kuma?"""

"A ule Alhaji ya ce ""Kin ga dan Allah jeki ki bani wuri, kar saka mini ciwon kai"" kamar ta fashe da kuka yau ita Alhaji"

"yake kora, tamkar mahaukaciya ta fice daga sashin nasa tana tuntuSe, tana tafe tana tambayar kanta ciki a jikin ummi, arya yake yi kenan lafiyarsa alau?."

"Raihan yana ta shirin fita aiki, ummi ta lallaSa ta dafa masa tea, ta dawo ta kwanta a falo, aka wanwasa ofar"

falon.

"Raihan ya tashi ya buWe sai ga noor, ya kalleta ya ce ""A'a kin gama gudun namu kin dawo?"""

"Noor ta ce ""Ai na ga zamana a nan ya fi alkhairi, gidanmu kamawa da wuta yake neman yi"""

Ta shigo falon tana yi wa ummi sannu.

"Ummi ta ce ""Noor wace irin wuta kuma? Meyake faruwa a gidan?"""

"""Wai Abba ne yayi aure, ya kawo mata alewa da dabino take ta masifa da bala'i da tashin hankali, daga na ce in ci"

"dabinon kin ji zagin da tayi mini? Ni kuwa na Webo na haWo kayana na dawo, dama sai da ku ka ce kar na tafi na ce sai na tafi. Gidanmu yana nan yadda ki ka san rasha da ukrain"""

"Ummi ta harari noor, saboda yadda take ta zuba, a gaban raihan."

"Amma cikin mamaki Ummi ta ce ""Amma aure kuma?"""

"Noor ta ce ""Eh mana, ashe jiya maiduguri ya je mamanku ya aura, dama na daWe ina ce masa dama ya aro mana"

"anty"""

"Ummi ta ce ""To baba suda na ji ya isa haka"""

"Noor ta sake cewa ""Kin san Allah anty ummi, na daWe ina tausayin Abba, dan ba kya gidan ba kya ganin yanzu"

"abubuwan da suke faruwa, tayi ta Waga masa murya, amma kin ga takwarata ai saliha ce a hankali ma take magana"""

"Raihan ya ce ""Lallai dr. Ya shamamce mu, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, tun da gaki kin zo, bari na tafi aiki"""

"Bayan tafiyar sa aiki, ummi ta din ga yi wa noor mitar yadda ta saki baki a gaban raihan."

"Noor ita ba ta ga abun laifi ba, dan a ganinta yanzu ai sun zama Waya da raihan."

"Sannan ta kira can gida maiduguri, suka tabattar mata da hakan."

"Cikin mamki ummi ta ce ""Amma anty maryam, mama ta gama warware ne?"""

"Anty maryam ta ce ""Jikinta fa da saui sosai da sosai, ai kuna waya ki ji, ya ce wai can wurin da yake karatu zai tafi da"

"ita, amma ni matarsa nake ji ye mata tsoro"""

"Ummi ta duba taga noor ta tafi kitchen, sannan ta ce ""Babu abun da zai faru sai ikon Allah anty Maryam, kuma in"

"sha Allah mama ta shigo gidan nan kenan, dr. Mutum ne managarci, kuma zan tsaya iya yi na hakan ya tabatta, babu wanda zai cutar mini da uwa, kuma da ba a aure ita ma da ba a aureta ba"""

"""To ki dai ta yi musu Addu'a"""

"""In sha Allah"""

"Noor ta dawo falo da plate, da aramar wayar ummi a hannunta ta ce ""Yaya ummi, ga mutuniyarki indomie mai yaji"

"da kifi, Yaya salim ne za su zo"""

"Ummi ta kalleta ta ce ""Wane Salim Win?"""

"""Yayan MD mana"""

"Cikin mamaki ta ce ""Ya aka yi ki ka sani"""

"Sai kuma ta Wan diririce ta ce ""Yaya raihan ne ya gaya mini"""

"Ummi ta ce ""Allah ya kawo su lafiya, me zamu girka musu?"""

"Noor ta ce ""Zan yi musu abinci, amma ki koma Waki ki kwanta, kar ki ce warin girkin zai saka ki amai"""

"Ummi ta tashi tana murmushi ta ce ""Yauwwa ta wajena, shiyasa nake son ki ummana, bari na je na yi wanka na"

"kintsa kan su zo, kar su zo su same ni a haka, kalli kaina ko taza babu na fi kwana uku ban taje ba, MD jiya har ya jona hand dryer zai taje mini na ce bana so da zafi, ya yale ni"""

"Noor ta ce ""Ohh, yaya ummi soyayya da daWi ko? Ke ban da wannan abun da ya faru na ga yana sonki ba kwa faWa, amma anty intee da wayona fa lokacin da mijinta Salim yake zuwa suke shan soyayya amma yanzu kullum cikin faWa"

"kamar abokiyar gabarsa"""

"Ummi ta ce ""Waye ya ce miki bama faWa? Babu wata soyayya da za ayi zaman aure ace babu saSani, sai dai danganta da yadda aka gina soyayyar, idan har ta gaskiya ce kuma an fahimci juna, ko saSani yazo za a warware cikin saui. Ni"

"kaina MD ba dan yana sona ba, kuma mutum ne mai fahimta ba da laifukan da na yi masa a kwanakin nan wani zancen ake yi ba wannan ba, shiyasa ko mun samu saSani nake duba alkhairnsa bana taSa yi masa hukunci da laifin da ya yi mini""."

"Noor ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ni wallahi soyayyar da ba a faWa nake so, idan muka yi faWa kuka zan yi"""

"Ummi tayi dariya ta ce ""Sai ki tafi littafi ko film, ko kuma tatsuniya, a nan zaki samu wadda ba a faWan. Bari na shiga"

"daga ciki"""

"Noor ta yi shiru tana ta zancen zuci, ita har ga Allah ta fi son ayi ta soyayya babu faWa."

"Ummi daga yin wanka ta ji sanyin Ac, ta kwanta ta hau bacci a Wakinta. Noor ta zage tana ta gyara gidan, ta iya aiki"

sosai da sosai saboda zama da ummi.

"Ta gama aikin ta shiga ta yi wanka ta saka wata ar doguwar riga da Wan kwali, ta dawo falo tana shan lemo mai"

sanyi. Ba ta daWe da zama ba a ka buga ofar falon.

"Ta tashi ba tare da tambayar waye ba, ta buWe ofar, kallonsa ta tsaya tana yi tana murmushi, hannunsa Wauke da"

"manyan kulolin abinci, ta ce ""Sai yanzu ko? To koma mun yafe"" alama yayi mata da ido, ya tura ofar hajiya ta gani a bayansa."

"Da sauri noor ta nutsu, ta durusa tana gaishe ta, saboda ta shaidata, ta karSi kayan hannunta suka arasa cikin"

falon.

"Hajiya ta ce wa noor ""Kamar na so na gane ki"""

"Salim ya ce ""anwar ummi ce"" ya kalli ummi ya ce ""Ga hajiya, in faWa mata me ki ka ce a kan ta?"""

"Noor ta kalleshi da sauri tana zare ido, ta girgiza masa kai."

"Hajiya ta kalleshi ta kalleta, ta ce ""Laifi na yi mata?"""

"Yayi murmushi ya ce ""Hotonki ta gani a wayata, ta ce na sanki, na ce eh ar uwammu ce ke, wai ranar bikin su raihan"

"tana ta kallonki, wai kwalliyar ki tayi kyau, gashi kin iya turanci, kina magana kina turanci, har gwada maganarta ki ka yi ko ba ayi ba?"""

"Noor tamkar ta nutse a wurin nan, ta sunkuyar da kai tana hararsa ta asan ido."

"Hajiya ta yi dariya ta ce ""To ai da saui tun da ba laifi na yi mata ba, ina ummin ne?"" Duk da noor ta san ummi bacci"

"take yi, ta tashi da sauri ta ce ""bari na kirawo ta"" har noor ta bar falon kallonta yake yi yana dariya."

"Hajiya ta ce ""Wai ya aka yi har ku ka saba haka ne?"""

"Ya gyara zamansa ya ce ""Ina ganinta a nan gidan, sai kuma lokacin da aka samu matsalar nan na su raihan, da na je"

gidansu ita ta gaya mini. Ta wurinta na din ga samun information Win da na samu ummi a can garinsu. She's very funny ne kawai tana bani dariya.

"Hajiya ma ta yi murmushi, noor ta dawo falon amma ta laSe ta bayan labule ta ce ""Na duba bacci take yi"""

"Ta gudu ta koma kitchen, ta haWa musu ruwa da fruit, amma ta kasa fitowa tana jin kunya, sai a yanzu ta fuskanci"

"hajiya mahaifiyar Salim ce dan suna kama sosai, saSanin da ya ce mata ar uwarsu ce."

Da yar ta dawo falon tana sunkuyar da kai.

"Hajiya ta ce ""Ya sunanki ne?"""

"""Mariya, amma ana ce mini noor, maman ummi aka yi wa takwara aka saka mini sunanta"""

"Hajiya ta ce ""Masha Allah noor, kar ki damu da abun da ya faWa rabu da shi, bari mu tafi ga abinci muka zo wa da"

"ummi, na zo na ara duba jikinta"""

"Noor ta ce ""Dan Allah kar ku tafi, bari na tashe ta"""

"Hajiya ta ce ""A'a ba sai kin taso ta ba"""

"Muryar ummi suka ji tana cewa ""Hajiya sannunku da zuwa, wallahi bacci ne ya kwashe ni"""

"Hajiya suna can suna hira da ummi, Salim ya fita, noor ta bi bayansa."

"Yana tsaye yana waya ya ji muryarta ta ce ""Allah ya kama ka"""

"Ya waiwayo ya ce ""Da na yi me?"""

"""Ashe mamanku ce"""

"Ya ce ""A'a anwar Alhaji ce"""

"Noor ta ce ""To wallahi mamanku ce, shi ne ka gaya mata abun da na ce, duk na ji kunya""."

"Salim ya yi dariya ya ce ""Last born"""

"Ta ce ""Ba wata last born, wallahi ka bani kunya sosai"""

"Yayi dariya yana kallonta, ar arama da ita sai baki."

"""Ka san me? Babanmu yayi aure fa, ya auri babar su yaya ummi, mamanmu sai fitina take yi a gida, ni kuwa na yi"

"tahowata nan"""

"Ya ce ""Kin kyauta, ba kyau kallon manya idan sun samu saSani"""

"Kawai ta saka hannu a aljihun rigarsa, sai ga kwalin sigari."

"Ta ce ""Ba ka daina ba ko? Ka ce mini fa ka daina"""

"Ya haWe rai ya ce ""Meyasa ba ki da kunya ne? Dan kin ga ina yi miki dariya har ki ka saka hannu a aljihuna?"""

"Noor ta ce ""To ai ba kuWi na Waukko ba, kuma ka ce mini ka daina"""

"Hannu ya kai ya karSa, ya mayar da kayarsa cikin aljihunsa, ya juya ya tafi."

3 MONTHS BACK

"Salim ya je gidan raihan, amma maigadi ya sanar masa raihan ya ce duk wanda ya zo ace masa baya nan."

"Ya tambayi maigadin dalili, ya ce bai sani ba, amma tun da hajiya bilki ta je, ummi ta tafi tana kuka da kayanta a"

"hannu, amma bai san meyafaru ba."

"Tun daga nan jikinsa ya bashi akwai wani abu, da safe neehal za ta fita suka haWu, ya tambayeta meyafaru a gidan"

"raihan da mami ta je, ta ce masa ba komai, sai da ya zageta sannan ta gaya masa abun da ya faru."

"Da azahar ya wuce gidan su ummi dan jin meyafaru, ya haWu da noor a hanya za ta je makarantar islmaiyya . ""Ke!"" Yayi maganar yana sauke glass."

"Ta tsaya ta ce ""Sunana mariya wato noor"" tsyaawa yayi yana kallon ta ya ce ""Kin gane ni?"""

"""Eh, na ganeka Wan uwan su yaya raihan"""

"""Yauwwa, ummi na gida ne?"""

"Ta ce ""A'a tana gidanta"""

"Ya buWe motar ya ce ""Ba ta can ki gaya mini gaskiya """

"Ta ce ""Eh ta zo gida, mamanmu ta ce wai ba zata zauna ba, ba a san fa in da take ba, yaya raihan ya zo ana ta"

"nemanta, sakinta fa yayi""."

"Salim ya ce ""Ina ta tafi yanzu?"""

"""Gaskiya ba zan gaya maka ba, islamiyya fa zan tafi, kar na makara""."

"Salim ya ce ""Shigo mu tafi na kai ki islamiyyar """

"""A'a ni ba zan hau motar wanda ban sani ba"""

"Ya ce ""A'a ai ni kin sanni, yayan raihan ne ni"""

"Ta ce ""Bari na gaya maka dai, duk da ta ce kar na sake na gaya wa kowa, gagarwa ta tafi, can garinmu a jigawa,"

"amma kar ka gayawa yaya raihan, ta ce kar na faWa, jiya kan ta tafi ta gaya mini""."

"Salim ya ce ""Na gode sosai da ki ka gaya mini, daga gagarwan ina za a yi aje gidan"""

"Ta wassafa masa komai, kwatancen gidan tun daga tasha, da yake ba Soyayye bane ba, ya yi wa noor godiya ya tafi."

"A yammacin ya tafi gagarawa, bai jira sai washegari ba, yayi sa'a ya tarar da ummi, kuma ta sanar masa duk abun da"

"ya faru, da shawarar da ta yanke, ta kuma roe shi a kan dan Allah kar ya gayawa kowa in da take."

"Bayan wata guda, ya haWu da noor ta je gidan yayar farida, a sharaWa, shi kuma ya je wurin wani abokinsa."

"Suka gaisa, yake bugun cikinta ko an ga ummi, ta ce masa ba a ganta ba, ta nuna masa yadda take cikin damuwa,"

rashin sanin in da ummi take.

"Ta saki baki tayi ta bashi labarin zaman da ummi ta yi a gidansu, da yadda ake yi wa ummi gorin ta auri yaro aninta."

"Ta ce ""Yauwwa ka ce kai yayan yaya raihan ne, amma ba mamanku Waya ba ko?"""

"Ya ce ""Eh"""

"""To wallahi in gaya maka mamansa ce ta saka ya saketa, ba ta sonta wai mummuna ce ta auri yaro, dan Allah ai"

"auren yaro ba haramun bane ko? Kuma ai yaya raihan babba ne yana da gemu fa"""

"Ya ce ""Eh gaskiya ba laifi ba ne, in dai mutum yayi gemu ba yaro bane"""

"Message ya shigo wayarsa, ta kalli lock screen Win sa, da hoton hajiya ne a kai, ta ce ""Laa ka san wannan matar?"""

"Ya amsa da ""Eh, ar uwanmu ce"""

"""Innalillahi, ta burgeni lokacin bikinsu yaya ummi, ta iya wanka, gashi ta iya turanci"""

"Yayi dariya ya ce ""Gaskiya ne"""

"Noor ta ce ""Wallahi duk arfin hali nake yi, rashin yaya ummi har kuka nake yi, rayuwarsu tayi ta bani sha'awa da"

"MD ba sa faWa, amma kawai ya saketa na zata auren saurayi ya fi daWi, amma na fasa"""

"""Tsoho zaki aura kenan? Ai shi ma yana sonta ba laifinsa ba ne"""

"Ta ce ""A'a ba tsoho nake so ba, me dai gemu kamar naka, wai dan Allah da ka je gagarawa ba ka ga yaya ummi ba?"""

"Abun da ta faWa na farko ya bashi dariya, ya ce ""Da na ganta ai da na gaya miki, amma me zaki bani na nemo miki"

"ita?"""

"Noor ta ce ""To ai bani da kuWi"""

"Ya ce ""Ba kuWi zaki bani ba, zan gaya miki amma sai na nemo miki ita"""

"Tun daga ranar suka saba da Salim, lokaci-lokaci ya kan bi unguwarsu, dan ya ganta, saboda yana son surutunta."

"A haka ta gane yana shan sigari, tayi ta masa mita, ya ce idan ya nemo mata ummi, zai daina sha."

Haka nan yake jin daWin mu'amalarsa da ar yarinyar da da yayi auren wurin zai haifeta.

CIGABAN LABARI.

"Hajiya sun daWe tare da ummi, kuma ummi ta samu ta ci abincin da hajiya ta kawo mata sosai ta oshi, kuma Allah"

ya taimaketa ba ta yi amansa ba.

"Bayan tafiyar Hajiya, Dr. Ya kira ummi a waya, bayan sun gaisa ya ce ""Noor tana gidanki ko?"""

"Ta ce ""Eh kawu"""

"""Na san ta riga ta gaya miki komai ma, bayan mun zo gidanki mun yi wannan maganar, na yanke shawarar yin abun"

"cikin gaggawa, saboda kar wani abun ya kutso ya hana."

"Na kira baban maiduguri, muka yi magana da shi, da na tabattar da ya amince, kawai da muka je jiya, na tafi da"

"sadaki aka Waura, dan hatta an gagarawa ba su sani ba, sai da aka Waura na san za a iya samun matsala ko daga gare su ko wani Sangaren."

"Nan da sati Waya idan komai na ta ya zama ready, zan Waukkota ta yi miki kwana Waya ko biyu sai mu wuce""."

"Ummi bakinta ya kasa rufuwa, ta ce ""Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya cigaba da faranta maka kamar yadda ka ke"

"yi mana kawu, Allah ya saka da alkhairi na gode sosai da sosai"""

"Dr. Ya ce ""Ba komai ummi, yi wa kai ne""."

"Can Maiduguri kuwa, mariya na zaune ta yi shiru tayi zurfi a tunani, mama ta ce ""Mariya, wai menene? Ko abincinki"

"fa baki taSa ba"""

"Ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Wallahi mama tunani nake kawai"""

"""Tunanin me?"""

"""Auren nan mana, ni fa banda baba ya matsa ba zan yi wani aure ba, ido ya mutu kwalli ba zai farfaWo da shi ba, kuma idan ina tuna wahalar da na sha a hannun iya, ko a mafarki bana fatan sake yin aure"""

"""Ashsha, mariya ba a fitar da rai da rahamar Ubangiji, kuma ke ba tsohuwa ba, haryanzu da sauranki, babu wanda"

"zai ce kin haifi ummi, gashi albarkaci auren har jirgi zaki hau"" ta arasa maganar cikin zolaya."

"Mariya dai ta rausayar da kai ta ce ""Wallahi mama ba na aunar abun da zai sake haWa ni da iya, auren nan ya sake"

"mayar da ni jikin su"""

"Mama ta girgiza mata kai ta ce ""Akwai banbanci, tsakanin Bashir da Yahaya, Kuma ai ba wuri Waya zaku zauna ba"""

mama tayi ta lallaSata tana kwantar mata da hankali.

"Can gidan dr.

Please Login or Register in order to submit comment