You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Iya."

"Su kuma suka wanda suka kawota suka gama tijararsu da rashin mutunci, suka fice suka bar gidan."

"Iya ta ce a Wauki ar a kai wa babar Idris, dan ita ba ta san ya za ta yi da jaririya Wanyen goyo haka ba, ita ko nonon"

"ma yanzu babu sun suWe sai fata, dan haka sai dai uwarsa."

"Babar Idiris kuwa ta ce ""Iya ke yakamata ki rie wannan a ba ni ba, tun da dama sunanki suka sawa yarinyar, ba yadda ban yi ba na bawa yarona tarbiyar da ta dace, amma ki ka i saboda yana da sunan mahaifinki, kin Wau son"

"duniya kin Wora masa. Ko laifi yayi na yi masa faWa, sai ki ci mini mutunci."

"Dan haka Iya ke zaki kashe wannan wutar, wallahi ki ka bani jaririya ban san yadda zan yi da ita ba""."

"Cikin fusata Iya ta ce ""Ni ki ke gayasa haka lami?"""

"""Iya ba rashin kunya ba ce gaskiya ce, da kin bari na bawa Wa na tarbiyya da haka ba ta faru ba""."

"""Rufe mini baki, har wata tarbiyya ce da ke da zaki bawa wani? Ke Win a yaya ki ke? Ki zo ki Wauke yarinyar nan ki san"

"yadda zaki yi da ita"""

"Lami ta ce ""Ban gane ba iya, ni na yi mata cikin, wallahi ba zan Wauka ba"""

"""Lami uwata ce take faWa kina faWa?"""

"Lami ta ce ""Maganar gaskiya ce fa, in Wauki a in yi yaya da ita? Ta in da aka hau ta nan za a sauka ai"""

"Iya ta ce ""Rabu da ita, na san maganinta, yanzu abun da ya fi dacewa shi ne ka je, ka ce musu mun amince a Waura"

"auren nan su karSi ar nan. Amma wallahi Idiris ya cuce mu, ya janyo mana masifa da abun kunya, ga ragona da nake son sayarwa lokacin sallar layya, sun tafi da shi, ku san yadda zaku yi ku karSo mini ragona""."

"Ilyasu ya ce ""Iya yanzu waye yake ta rago, muntuncinmu ya gama zubewa"""

"Baban su Idris ya ce ""Ina ga kawai mu je mu samu iyayen nata, ina sa'adatu ta zo ta yi wa yarinyar wanka, a saka"

"mata sutura, mu je gidan su Hindun"""

"Sa'adatu ta ce ""TaS ar gaba da fatihar? Wallahi ba zan taSa azanta ba, sai dai uwarsa ta wanketa, haka kurum in"

"taSa masifa"""

"Sakin baki Iya tayi tana cewa ""Wai me yake damun matan nan ne? addara ce fa, kowa zata iya faWa a ka"""

"Sa'adatu ta ce ""A'a irin wannan addarar Allah ya tsayar da ita a kan wanda ta sama"""

"Haka dai gida ya yamutse, kamar ayi yai."

Da yar babar Idris ta yi wa yarinyar wanka.

***

"Yau lahadi, ummi sun yi hutun makarantar islamiyya, sai dai ta kasa zama wuri Waya ta hutawa ranta, dan kuwa ta san babu wanda ya bata wannan damar."

"Dan haka wuni tayi tana kaiwa tare da komowa, wurin yin kwalema da tsabtace ko ina na gidan."

"Tana sanye da dogon hijjabinta, da ya zame mata tamkar uniform, duk zafi ko sanyi, ko a cikin gida, da hijjbi take"

"yawo, dan ko da ta fara irgar dangi, tsananta rufe jikinta tayi, balle yanzu da take aji biyar na sakandare ta ara cika sosai."

"Dan idan tana girki, wuta ta sha kamo mata hijjabin, ko ta yi Sarna a kitchen, farida ta ci mata mutunci, amma hakan bai sanya ta daina sawa ba."

"Hijjabin jikin nata ya sha jiki ya koWe, sai dai kasancewar a goge yake, muninsa ya ragu."

"Tana mopping noor na biye da ita suna hira, ta saki jiki tana biyewa noor, suna shiririta."

"amshin turaren da ya cika falon ne, ya sanya ummi Waga kai, aikuwa tayi tozali da intee ta fito, sai taku take Waya- Waya."

"Ta sha doguwar rigar abaya, amshin kansa ummi ta kasa tantance wane iri inteesar take yi."

"Tayi light make up, sai wani yatsuna fuska take yi."

"Ummi a ranta ta ce ""Tubarkallah masha Allah, kyau yana in da yake"" ba iya kyan da inteesar tayi ne ya burge ummi"

"ba, doguwar rigar jikinta ma ta tafi da ita, ta ji ina ma ita ma tana da ita ta saka, taga ya zata yi a ciki, dogayen riguna irin haka suna burgeta""."

"""Ke! Kalli gabanta kar ki kama mini kurwar a"" farida tayi maganar cikin tsawa."

"an zabura ummi tayi, ta cigaba da aikin gabanta."

"Kausar kuwa ta kwashe da dariya, yadda ummin ta Wan shagala da kallon yayarta kamar shashasha."

"Farida ta yi murmushi ta ce ""Farar mace...."

"Caraf kausar ta ce ""Alkyabbar mata"""

"""Farar mace kalar kyau, kalar babban gida da manyan motoci, kalar hutu da jin daWi farar mace mowar mata"""

"Inteesar kamar kanta ya fashe, saboda kirarin da mamanta ke yi mata."

"Ta dubi ummi ta ce ""Baar mace borar gida""."

"Farida ta amsa da ""Idan ta samu mijin ba"""

"""Idan ba ta samu ba kuma ta dauwwama ar wanke-wanke"""

"Ummi tayi burus, ta cigaba da hirarta da noor, tana jin zuciyarta na wani irin zafi."

"Intee ta yamutsa fuska ta ce ""Maama bari na je, ya kirani a waya, ya zo""."

"""To shikenan, a kula sosai, a iya karairaya da jan hankali"""

"""Kar ki damu maama, ammm ummi kin kammala girkin da na saki?"""

"""Na gama"""

"""Ok, ki shirya mini komai a tray, in the next few minutes ki kawo mana"""

"Kallon asan ido ummi tayi mata, ta yi mata girkin tarar saurayi, kuma ita za ta kai musu."

"Tayi ajiyar zuciya, tare da Wan girgiza kanta."

"Farida ta ce ""Ke ummi in tambayeki mana"""

Ummi ta Wago tana kallonta.

"""Wai dan Allah ina babarki ne?"""

"Ummi ta Wan yi jimm, dan ba ta zaci wannan tambayar ba."

"""Ban san in da take ba"""

"""Kamar yaya baki san in da take ba?"""

"Ummi ta ce ""Ai tun ranar da ta tafi, Iya ta hana a tafi da ni, ban sake ganinta ba, sau kusan uku an uwanta na zuwa"

"su tafi da ni, amma ta i bayar da ni""."

"""Kuma saboda rashin lissafi, ba ta sake neman in da ki ke ba, daga ita har an uwanta, yau shekarar ki nawa a gidan nan, ko kare daga dangin majaifiyarki ba wanda ya nemi in da ki ke, wace irin uwa ce wannan? Ko suma ba sa"

"buatar ki ne, an rasa mai rie ki, aka lia mana, anya babu lauje cikin naWi a game da ke, ta hanyar aure aka same ki kowa yake gudunki?"""

"Tuni idon ummi ya fara tara hawaye, cikin oarin kare mahaifiyarta ta ce ""Ai an ce ba ta da lafiya, tun da aka wace"

"ni, ta haihu Wan babu rai, ta samu matsalar wawalwa"""

"""Mahaukaciya ce kenan?"" Kausar ta faWa kai tsaye."

"Farida ta ce ""To ai mahaukaci ya san Wan sa, jahilci kawai da rashin sanin ciwon kai, idan ita ba ta da hankali, an"

"uwanta fa?"""

"Ummi ta yi shiru, ta kasa magana."

"Farida ta shigo falon a fusace ta ce ""Wai ke ummi me ki ke taama da shi ne? Cewa fa na yi ki kawo mana abinci,"

"amma dan wulaanci kin shanya ni, bana son rashin mutunci"""

"Ummi ta jingine mopper ba tare da ta ce komai ba, ta je ta Wauki tray, ta kai wa saurayin intee. Kallo Waya ummi ta yi masa ta sunkuyar da kai, gaba Waya bai yi kalar mutane masu Wa'a ba."

"Tunanin abun da farida ta faWa ya Warsu a ran ummi, idan an ce mamanta ta samu matsalar wawalwa, to an"

"uwanta fa, yakamata ace sun nemeta, ta san da a hannunsu take, ba za su wahalar da ita sosai ba."

"Sakawa tayi a ranta a wannan karon idan kawu ya zo gida, za ta tuna masa alawarin da yayi mata na binciko maata"

"in da mamanta take, dan ita ba ta taSa jin ko sunan garinsu wani ya faWa ba."

***

"Can gida gagarawa kuwa, an samu da yar da siWin goshi, su hindu sun karSi jaririya, babanta ya ce idan ta yi arba'in,"

"su zo su kawo kuWin aure, kuma yadda ake auren budurwa komai da komai, haka za a haWo mata, kuma shayarwa da hindu, za ta yi, sai an biyata kuWin shayarwa ko su dawo musu da jaririyar."

"Kan su dawo gida, sai da babanta ya caje su kuWi masu yawa, sannan suka dawo, suka sanar da Iya abun da babanta"

ya faWa.

"Iya ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin matsiyatam mutane ne? Sai an yi mata komai kamar"

"auren budurwa ba ta riga ta haihu ba, har wani kuWin shyarwa suke nema, a gidan ubanwa aka taSa haka, ai da an dawo da ar a din ga bata nonon akuya""."

"""A'a iya, a samu a lallaSa mu rabu da mutanen nan lafiya, kowa ya Webo da zafi ai bakinsa, gobe ba ya ara ba""."

"Da labari ya iske idiris kuwa, masifa ya fara yi, yana balooon shi fa ba ya son Hindu, ban da zalunci yarinyar da har"

"haihuwa ta yi, tayaya za a ce wai ayi mata kaya kamar budurwa, saboda son zuciya."

"Cikin tsananin fusata mahaifinsa ya ce ""Rufe mini baki, ko na turmushe ka a wurin, mara mutunci, muna zaman"

"zamanmu ka janyo mana masifa, ka sanya kowa a tashin hankali, kuma wallahi ko ka so, ko ka i sai ka auri yarinyar nan, ka arata can bayan auren"" yayi masa ta tas ya tafi ya bar shi."

"Magaji yayi murmushi ya ce ""Allah sarki ummi, baiwar Allah yanzu idan na ce hakkinta ne ya fara bibiyarku, sai ace"

"arya ne a hayayyao mini, da ka yi hauri da ummi, ka nema mata magani tsaf zata warke ku zauna lafiya, amma ka din ga muzanta ta, kana yamaWiWi da ita a kan larurar da ta same ta, har abokan ka suna ce maka angon WaWWoya saboda zunzurutun wulaanci da tozarci, ka saketa bayan ka gama azabtar da ita, saboda ka na taama da kai Wan iska ne."

"Kai ma gashi Allah ya tozarta ka, gara nata tarihi zai iya shafe shi, naka kuwa har gaban abada ba zai goge ba, kuma kaWan ka gani, ba dai bariki ba sai ma ka auro wannan Win, zaka san ka yi asarar mace""."

"Duk wannan faWan da magaji yake yi masa, bai iya cewa komai ba, saboda ya san ba shi da gaskiya, kuma yanzu yana cikin tashin hankali da tunanin menene mafita."

***

"Ummi tana ta dakon zuwan kawu, tare da fatan Ubangiji Allah ya sanya ya samo in da mama take, gara ta tattara ta koma can wurinta, dan da ta san in da take da ta daWe da barin gidan nan, ko bola take bi za ta din ga bin ta."

"Sai da aka shafe kusan sati uku, sannan dr. Ya zo gida, bayan yayi kwana biyu ya Wan nutsu ya huta, ummi ta same shi"

"shikaWai a falo, ta gaishe ta samu wuri ta zauna."

"""Ummana, ya aka yi ne?"""

"""Dama ba wani abu bane kawu, dama tambayarka zan yi ko ka gano in da maman take?"" Tayi maganar kanta a asa"

tana wasa da yatsun hannunta.

"Ya Wan yi shiru yana nazarin ta, sannan ya ce ""Akwai matsala ne?"""

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"""Na san ba zaki faWa ba dama, rabonki da yi mini wannan zancen an kwana biyu, na san a takure ki ke ummi, amma ki yi hauri, ina nan ina ta oari a kai, ba yadda ban yi da Iya ba, ta ce mini ita ba ta sani ba."

"anin babanmu da yayi masa walicci ma ya rasu, su ilyasu sun ce basu san sunan garin ba, su dai kawai an zo da mota an kai su, na san faWa kawai suke yi, Iya ce ta hana su faWa."

"Amma ina nan ina ta bincike, ina da hotunanta biyu, da aka yi mana bayan bikin da na je gida, ina ta bincikawa, na samo sunan garin, ainihin yankin da take a garin ne ban sani ba, ana ta bincikawa ummi, ina sane ban manta ba, ki cigaba da addu'a da kula da karatunki, komai zai warware in sha Allah""."

"Ummi ta risuna ta ce ""Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi""."

"Ya ce ""Amin ummana, baki ce Allah ya yi mini albarka ba"""

Rufe fuska ummi tayi tana murmushi.

"Ya Wora da cewa ""Kwanaki an ce mini Wan uwan mamanki ya zo ganinki, Iya tai gaya masa in da ki ke, ta ci mutuncin"

"sa ya tafi. Amma dai in sha Allah ina nan ina oari a kai""."

"""To kawu na gode"""

"Ta tashi ta nufi Wakinta, tana sake jinjina iyayyar da Iya take yi wa mahaifiyarta da an uwanta."

"Kasancewar maryam gaba take da ummi dama, dan haka ta riga ummi candy, tun kan ta yi candy aka kawo kuWin"

"aurenta, dan haka an yi candy babu daWewa bikin ya tinkaro."

"Maryam ba ta tsaya saurarar ummi ba, ta sayi anko ta bawa ummi duk kyauta, sai dai da yar farida ta bar ummi ta je rana Waya bikin, shi ma da ta je kasa sakewa tayi, dan wareta an makarantar ma suka din ga yi, dan haka nan da"

nan ta koma gida ta bar wurin.

"Satin Maryam biyu a gidanta, mijin ya tafi da ita can wurin aikinsa, kasancewar soja ne babba."

***

"Kwanci tashi asarar mai rai, iyayen hindu suka din ga tatsar su Iya kuWi, har sai da ta yi watanni shida cif a gida, sannan aka Waura auren Idris da hindu, saboda babanta dagewa yayi a kan sai an kai kuWin aure da duk wani abu na al'ada da ake yi."

"Tare da cigaba da yi musu barazanar cewa, zasu dawo musu da ar su."

"Abun kunya dai da ake gudu, ya riga ya gama watsuwa a cikin gagarawa, na abun kunyar da jikan Iya ya tabka."

"Gidan da ummi ta zauna, aka sake kama haya, kansancewar ba kowa a ciki, aka ara gyara gidan, aka kai hindu da jaririyarta."

"Ko kallo hindu ba ta ishi idris ba, haka ita ma ba ta kansa ta bi ba, ta cigaba da sabgoginta da ar ta, sai dai cikin dare"

"yarinyar nan ta tashi, ta din ga tsala ihu kamar za ta shiWe."

"A fusace ya tashi ya ce ""Dalla malama ki Wauki ar ki saka tayi shiru, ta cika wa mutane kunne da kukan banza""."

"""To kai mai zai hana ka saka tayi shirun, na ga kaima ar ka ce"""

"""ar gaba da fatihar? Kar ki sake haWani da ita""."

"""Ko ar gaba da meye uban waye yayi cikinta, ai ba ita tayi kanta ba, ka ga wallahi ka ce zaka takura mini, ko ka Waga"

"mini hankali sai na koma gida na gaya musu. Kai ba ma ka da kunya, ni ka ke gayawa ar gaba da fatiha ce, uban waye ya lalata ni?""."

"""Iyayenki dai suka ja miki, da ba aurenki zan yi ba, suka hana ni""."

"Hindu ta yi shewa ta ce ""To uban wa ye zai baka auren a? Kana Wan iska?"""

"""Eh ina Wan iskan amma ai gashi an lia mini ke"""

"""Oho kai ka sani dai"""

"Ta dubi ar da ke ta tsala ihu ta ce ""Ke hajara tsohuwar banza, ubanki ya ce ki yi masa shiru, ar gaba da fatiha"""

"Idiris ya ce ""Tsohuwar banza, kakata ki ke zagi kenan?"""

"""Eh to, idan ka tsargu hakan ne"" haka suka din ga faWa kamar kaji, a tsakiyar daren nan mawabta na jin su."

"Abdul ne yayi sallama a kitchen, ummi na girki, suna ta tilawar Alqur'ani ita da noor."

"Raino ummi take yi wa noor da kulawa, bacci ne kawai yake raba su, baccin ma wataran a Wakinta take yi."

"Tun kan noor ta shiga makaranta, ta iya azkar da karatun Alqur'ani, dan ba ta yi pre nursery ba, kai tsaye nursery 1 aka kaita, saboda ta har rubutu ta fara iyawa."

"Sai dai noor masifaffiya ce, ba ta taSuwa a wurin yayyenta, dan baki ne da ita sosai da sosai."

"Ba ta jin maganar farida, kamar yadda take jin maganar ummi, fitsara da rashin kunya kuwa ba a magana, ummi da Abdul kawai take Wagawa afa, ar mitsitsiya da ita ga azabar taurin kai, ummi ce kawai take iya sarrafa ta yadda take so, dan haka ba wani shiga shirgin noor suke yi ba, tayi maka rashin kunya ka jibgeta ba za ta yi kuka ba."

"Ummi tayi ta mata faWa, dan ita kanta tana mamakin rashin kunyar noor."

"""Yaya ummi"" Abdul ya kira sunanta."

"Cikin haWa baki ita da noor suka ce ""Na'am yaya Abdul"""

"Abdul ya tsuke fuska ya ce ""Da ke nake?"" Ta girgiza masa kai tana Wan murguWa baki."

"Ummi ta kalli Abdul ta ce ""Yaya Abdul yaya ake ciki? Ka dubo mini"""

"Ya mio mata envelope ya ce ""Eh to, congratulations you got nine credits including maths and English, i know you"

"can do it ai"""

"A take ummi tayi sujjadar godiya ga Allah, noor ma ta durusa tayi, ummi ta Wago tana Alhamdilillah."

"Noor ta ce ""Wai menene? Me aka yi?"""

"Abdul ya ce ""Yaya ummi ta ci jarrabawa, dan haka ita ma very soon zata shiga jami'a"""

"Tsalle noor ta din ga yi tana ihu, ba tare da ta san ma menene cikakken bayanin ba."

Kausar ta shigo kitchen Win tana tambayar lafiya.

"Noor ta ce ""Yaya ummi ta ci jarrabawa, za ta shiga jami'a""."

"Tsaki kausar ta yi ta ce ""Shi ne kuma ki ke yi mana ihu?"""

"""Eh Win, yeeee yaya ummi ta ci jarrabawa "" tayi maganar tana tsalle ta fita daga kitchen Win."

"Kausar ta yi tsaki ta fice, Abdul ya ce ""Yaya Ummi, kina zaune an haifi mai tare miki faWa"""

"Ummi ta ce ""Ni mamana saliha ce, amma mama arama ta fiye tsiwa"" suka yi dariya, ummi na sake godewa Allah a"

kan wannan gagarumar nasara da ta samu.

"Takanas saboda ummi dr. Ya dawo gari, saboda shirye-shiryen nema mata admission, Abdul yana level 2 a BUK yana"

karantar Agric.

"""Dr. Wai ya na ganka a gida a tsakiyar sati haka? Kuma na ga baka daWe da tafiya ba""."

"""Abdul yayi mini magana a kan waec Win ummi, ina son in arasa mata abubuwan da yakamata kar ayi mini ba dai-"

"dai ba""."

"""Shi ne ba zaka wakilta wani ba, sai ka dawo da kanka?"""

"""Ki na da damuwa da hakan ne?""."

"Haushi ne yakamata tayi masa banza, duk iya oarin ta a kan cire hankalinsa daga kan ummi, ta kasa nasara Wari"

bisa Wari.

"Ta sake kallonsa ta ce ""Wai ni dr. Zuwa yaushe zan cigaba da jerawa da ummi a gidan nan, intee tana gama"

"secondary, nake son a aurar da ita, yaron ya matsa, ita kuma tana nan shirin tafiya jami'a ma take yi, gaskiya ina son privacy a gidana, ba zan cigaba da jerawa da gandamemiyar budurwa ba""."

"""Intee ke ki ka takura a karSi kuWin aurenta, ba dole na yi muku ba, ni kuma a yale mini a tayi karatu. Guda nawa"

"ummin take da ki ke wani zancen gandamemiyar budurwa, yanzu fa za ta shiga jami'ar""."

"""To wai ina uwarta, a mayar da ita wurinta mana""."

"A fusace ya ce ""Wai a kan ki ummin nan take ne?""."

"Muryar noor ce ta katse shi, tun daga wajen Wakin take wala masa kira."

"Ya ce ""Na'am shalelena"""

"""Kalli littafina, uncle ya saka mini 10 over 10, assignment Win da anty ummi ta koya mini""."

"Ya ce ""Wow masha Allah, congratulations baby""."

"""Thank you "" ta faWa cikin iyayi sannan ta ce ""To nima tunda na ci jarrabawar, zan shiga University?"""

"Ya kwashe da dariya ya ce ""From primary one to university?"""

"""Eh, ba anty ummi ma ta ci jarrabawa zata shiga university ba?"""

"Yayi dariya, ya biye mata ta gama shirmen ta, ta tafi, sannan ya kalli farida ya ce ""Farida wai zuwa yaushe zaki daina"

"planing Win nan, noor tayi girma yakamata ace kin sake haihuwa, 4yrs fa""."

"Farida ta yamutsa fuska ta ce ""Nifa na gama haihuwa, yaushe Allah ya amfana guda huWun""."

"""Amma da bani da yadda zan yi na rie ne, sai ki faWi haka, Allah ya yassare mini yadda zan kula da yarana, meyasa"

"zaki ce kin daina haihuwa?""."

"Ta mie tsaye ta ce ""Ka auri ummi ta haifa maka!""."

"Wani irin damm irjinsa yayi, ya bita da kallo, saboda munin maganar da ta faWa."

"Ya girgiza kai kawai, domin ba shi da abun da zai faWa gaba Waya."

"Iya oari kawu yahaya ya yi wa ummi, a kan harkar makarantar ta, dan ma farida na ta yi mata mugunta a kan wasu"

abubuwan.

"Yayi mata komai sai dai Sangaren sutura ummi na fuskantar barazana, domin kuwa ummi ba ta da suturar kirki, duk da ma'abociyar hijjabai ce, su kansu hijjaban nata duk sun mutu su yi haske."

(Kowane alubale ummi za ta fuskanta a jami'a? Bright pens na godiya sosai )

Whats app only please.

Ayshercool 08081012143

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P20

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu"

Abduljalal

Wata kissar sai mata Wuta a masaa Cutarwa

anwar maza Gaba da gabanta Aidata

RuWin uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata.

8081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daWi da amshi."

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki

Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

20

"Ummi ganin al'amuran take yi kamar a mafarki, duk da tsanani da matsi, haWi da alubale daban-daban yau ga ta a"

"makarantar jami'a, lallai lokaci yana sauri."

"Hakazalika ta na ta shirye-shiryen haWa saukarta ta biyu, domin kuwa bayan ta yi sauka ta cigaba da zuwa"

"makaranta, an ajinsu galibi duk sun yi aure, dama duk sun girme mata."

"Wuri Waya ta samu ta zauna a ajin, jikin window ne in da take, hakan ya bata damar kallon shige da ficen Walibai,"

"tsofaffi wanda sun kusa fita ma, da masu rawar kai wanda yanzu suka shigo jami'a."

"Shigowar wani babban mutum ajin ne ya sanya Waliban ajin nutsuwa, tare da gaida mutumin."

"Ya amsa musu, tare da gabatar da kansa a matsayin HOD Win su, ya nemi da kowanne daga cikin Waliban, ya tashi ya"

gabatar da sunansa da kuma garin da yake.

"Haka nan gaban ummi ya faWi, dan kuwa ba ta son mutane, da duk wani dalili da zai sanya a takurata da kallo."

"alibai suka din ga gabatar da kansu Waya bayan Waya, kan azo kan ummi gaba Waya jikinta yayi sanyi, sai wata irin fargaba take yi."

"Da yar ta iya miewa tsaye, fuskarta sanye da facemask, malamin yayi mata alama da ta sauke facemask Win."

"Gabanta ya sake faWuwa a karo na biyu, hannunta har rawa yake yi, ta sauke facemask Win tana jiran jin anan"

"magana kamar yadda ta saba, sai dai ba ta ji hakan ba."

"Sai dai ta kasa magana, sai da ta Wan sauke numfashi, sannan ta ce ""My name is Sai dai ta kasa arasawa, saboda"

yadda gaba Waliban suka juyo suna kallonta.

"Ummi na da murya mai matuar Waukar hankali, duk wanda bai santa ba, idan har tayi magana dole zai waiwaya"

domin ganin mai muryar.

"Ko a islamiyya idan ana musaffa, Alla-Alla suke yi a zo kan ummi, saboda ta iya ira'a mai daWin sauraro."

"Ganin ta diririce saboda kallon da ake yi mata ne ya sanya malamin takowa zuwa gabanta, ta ko ara sunkuyar da kanta asa, tare da wasa da yatsun hannunta a

Please Login or Register in order to submit comment