You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko zaka koreta""."

"Manager ya zare ido ya ce ""Yayarta ka za a kora? Idan ban koreta ba ni ai yayana ya kore ni, ka san yadda yake"

"yabawa oarin ta, da yabawa amanarta"""

"Raihan ya ce ""Dan Allah ka bar wannan maganar, kawai ni dai taimakon da zaka yi mini kenan, ka ce lallai ta dawo"

aiki.

"""Ba zan yi ba, ba kun fi kusa ba"""

"Raihan ya sassauta murya ya ce ""Haba manager, dan Allah ka taimaka Please"""

"""Da ka ce ba ka ji? Zan yi mata magana, amma ba dan halinka ba, kuma ba zan ce zan wani koreta ba, zan dai yi"

"oarin ta dawo Win"""

"Raihan yayi dariya ya ce ""Allah ya bar mini manager"""

"Manager kawai yayi murmushi, ya cigaba da aikin da yakamata ace ummi ce ta yi."

"Sai dai manager bai kai ga yin hakan ba, washegari sai ga ummin ta zo aiki, sai dai ta rame sosai, kallo Waya zaka yi mata ka san akwai tashin hankali a fuskar ta."

"Manager ya kira raihan a waya, ya gaya masa ummi ta zo."

"Bai ja dogon lokaci ba, ya daidaici lokacin tashin ta ya kusa, sannan ya tafi."

"Ta fito daga wurin aikin, yana nesa kaWan da ita yana kallonta, tana tafe a hankali kamar mara lafiya."

"Zuwa yayi ya sha gabanta da motar, ta tsaya tana kallon motar, ya sauke glass Win motar suka haWa ido, sai da ta Wan"

"razana, ya buWe mata motar ba tare da ya ce mata uffan ba."

"Jikin ummi ya yi sanyi sosai da ganin raihan, dan ba ta taSa tsammani ba, kamar mai jin tsoro haka ta Wosana ta"

shiga motar.

"""Ta tabatta dai ba kya so na ko ummi? Kina iya rabuwa da ni, baki damu da halin da zan shiga ba, kin ce mu rabu, ko"

"nema na baki sake yi ba, rashin muhimmancina har ya kai haka kenan ko Salma?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a."

"""Shikenan, ni gashi na sake biyo ki ai, ranar lahadi Alhaji zai zo wurin dr."""

"A razane ta kalleshi, tana ifta ido."

"""Eh, mun haWu da dr. Shekaranjiya, na zo wurinki kin i Waga wayata, mun yi magana ya ce Alhaji ya zo su yi magana"""

"""Wai da gaske aurata zaka yi?"" Tayi maganar cikin matuar rauni."

"""Gashi ina gaya miki, kin zata da wasa nake yi? Na san wataila ba ni ne irin mijin da ki ke so ba, na san zaki ga na yi"

"miki yarinta da yawa, amma har cikin raina nake jin zan iya aurenki na rie ki da kulawa da girmamawa""."

"""Raihan zaka aureni ina bazawara"""

"""Kar ki sake kawo mini maganar kin taSa aure, zuciyata zata fashe, ummi kina wasa da son da nake yi miki kina ganin"

"kamar wasa ko? Hubban shadidan na kira shi, ban taSa jin damuwa da takura a kan son wani abu ba kamar ke, kawai in ganki a kusa da ni, shi zai kawo mini cikakkiyar nutsuwa"""

Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta.

"""Meya rabaku da tsohon mijinki?"""

"Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Kakarmu ce ta haWa auren, ba ya so na, an kai kuWin aurensa aka fasa, shi ne ya aure ni"""

"Ya ce ""Ya yi wa kansa, ni ina so. Ki saka aurenmu a addu'a salma, in sha Allah zai yi albarka, wata nawa ki ke so a saka"

"na ji kin ce a matse ki ke ko?"""

"""Ai wannan maganar dr. Ba tawa ba"""

"Ya ce ""Haka ne, nima na matsun ne, in ga kin zama tawa"" ummi dai ta yi shiru tana tunanin ko dai ba da gaske raihan"

yake ba.

"""Na ga gidan tv nan sun kira screening, manager ya ce mini kin je, ya ku ka yi da su?"""

"Ta Wan rausayar da kai ta ce ""Kyawawa suke so, ba wanda sai an ta saka musu filter ba"""

"""Kamar yaya kenan?"""

"""Haka mai wurin ya ce"""

"Kawai ta ga yayi parking Win motar, ya kalli ummi ya ce ""Ke kuma ki ka ce masa me?"""

Tayi shiru tana kallon sa.

"""Magana nake yi miki?"""

"""Ni ban ce komai ba"""

"Raihan ya ce ""Sai ki ka tsaya kina kuka ko? Gwanar kuka"""

"Ta ce ""A'a ai ban yi kukan ba"""

"Ya dano kunnenta ya ce ""Wallahi ummi, duk wanda ya kuma kushe mini ke, ki ka tsaya kina kallonsa, baki Wau wani"

"mataki ba, sai na huce a kan ki, kamar na fi ki jin takaici idan aka kushe mini ke. Ke kina da baki, amma ba zaki iya magana ba? Tun da ba aikin zai Wauke ki ba, sai ki wanke shi tas ki bar wurin, atleast ai kya ce masa Allah ya sa kyawawan su durusar da tashar, ko ki ce masa ya koma islamiyya a karanta masa Allah ne mahalicci"""

"Sosai ya rie mata kunne, ta kai hannu ta rie hannunsa da ya rie mata kunnen cikin muryarta mai cike da iyayi da"

"shagwaSa ta ce ""Babba ne fa"""

"Ya sakar mata kunnen ya ce ""Babban banza ba, tun da ba shi da hankali"""

"Sai kuma ya kwantar da murya ya ce ""My wife"""

"Ta ce 'Na shiga uku"""

"""A'a ko Waya baki shiga ba, ko ba ni ki ke so ba, dan Allah ki yi hauri mu karSi addara a yadda ta zo mana, bamu san dalilin da Allah ya sa ya haWa mu ba, kar taurin kanki yayi delaying zuwan wasu bayin Allah duniya"" tayi burus"

kamar ba da ita yake magana ba.

"""A haka kamar saliha, nan kuwa taurin kai a cikin ki kamar me""."

"Ranar lahadi gaba Waya dr. Ya manta da batun zai yi bai, dan ya faWi maganar ne dan ya kori raihan, ummi ma ta"

"kasa zaune ta kasa tsaye, dan raihan ya tabattar mata da ranar lahadin Alhajinsu zai zo."

"arfe sha Waya na safe, Abdul ya je ya sanarwa dr. Yayi bai."

"Ya fita ya ga manyan mutane a manyan motoci, suka gaisa, Alhaji Tahir ya ce ""Ka manta zaka yi bai ne? Kodayake"

"an boko sai kun bawa mutum lokaci yake zuwa, Tahir ne baban sirikinka Muhammad da ka ce kana son ganina""."

"Dr. Ya ce ""Subhanallah, Allah sarki bisimillah ku shigo"" suka bi bayan dr. Zuwa cikin gida."

"Har cikin falo, ya fita da sauri ya samu Abdul ya bashi kuWi, ya ce ya sayo musu ruwa da lemuka."

"Sun daWe suna hira da Alhaji Tahir, da wasu mutane su biyu Waya aninsa Waya abokinsa."

"Dr. Ya sha mamakin jin waye raihan, tare da yi wa ummi fatan, Allah ya sa arshen wahalarta ne ya zo."

"Nan Alhaji Tahir yake gaya wa dr. Tuni ya saka an gama yi masa bincike a kan ummi, kuma ya ji daWin sakamakon binciken, dan haka ko yanzu aka ce su bayar da kuWin aure dr. Ya yanka za su biya, idan kuma shima zai yi bincike a"

kan su tukuna shikenan.

"Dr. Ya ce ""Eh to, ina son a bani damar binciken tukuna, sannan kamar nan da sati biyu zan yi magana, saboda in kira"

"wasu daga an uwana a karSi kuWin auren"""

"Alhaji Tahir ya ce ""Babu laifi, Allah ya kaimu"""

"Ba tare da wata alkunya ba, suka ci abin da dr. Ya gabatar musu, suka yi masa godiya suka tafi."

"Farida ta din ga bin sa tana tambayarsa suwaye wannan bain, amma yai gaya mata ko suwaye."

"Ummi ta sha mamaki, ba ta zaci da gaske ba, sai da ta ga su Alhaji Tahir sun zo."

"Alhaji Tahir ya koma gida, ya kira mami sashinsa, Hajiya na tare da shi, sai dai bai gaya mata ba ita ma, sai da Mami"

"ta zo, ta tarar da su ta wani haWe rai tana harare-harare."

"Alhaji Tahir ya ce ""To ke fa abun arzki ya same mu, ban sani ba ko mun yi laifi"""

"Mami ta ce ""Meyafaru?"""

"""Babban mutum ya zo mini da magana, ya je zance an ritsa shi an ce in je in gabatar da kaina idan da gaske yake,"

"dan yau ma daga can nake da ni da su Alhaji Hamza, nan da sati biyu zamu koma mu kai kuWin aure"""

"""Ikon Allah, kuma shi ne ba a saka ni a maganar ba sai yanzu?"""

"Hajiya ta ce ""Masha Allah lallai babban mutum an girma, Ubangiji Allah ya sa abokiyar arziki ce, Alhaji a ina take zan"

"yi shishshigi"""

"Alhaji Tahir ya ce ""Au kema babbar aminiyar ta sa bai gaya miki ba? Wai wata yarinya amm.. ammi ne sunan nata ne"

"ko ummi ne, wai awar maryam ce dai""."

"Hajiya ta ce ""Laaa ko dai Ummi, Ummi dai da suka yi islamiyya tare?"""

"Ya ce ""Yes of course haka ya ce mini"""

"Cikin tsananin mamaki da takaici mami ta ce ""What! Wannan kwazgwamar yarinyar baa irin?"""

Ayshercool

08081012143

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu"

Abduljalal

Wata kissar sai mata Wuta a masaa Cutarwa

anwar maza Gaba da gabanta Aidata

RuWin uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata.

8081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

"MASU BUATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL INA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE

AYSHERCOOL 08081012143

"MASU BUATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL INA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

32

"Alhaji ya ce ""Meye kuma na wata kwazgwamemiya baa? Ba mutum ba ce ba?"""

"""Ban gane ba mutum ba ce, ta girme shi fa awar maryam ce?"""

"Ya ce ""To shi ne me? Idan har shi zuciyarsa ta nutsu da ita ba shikenan ba, ni na yaba da tarbiyyar gidansu"""

"""Wallahi da sake, tun wuri ma dole a janye wannan maganar. Na zaSa masa yarinya ya i sai ya jajibo wannan mummunar yarinyar? Gidan da take zaune ai ba gidansu bane ba, zaman boranci ta yi a gidan kamar ar aiki"""

"""To kin ga kya samu lada ma, idan ya aureta ya kula da ita"""

"Kamar zata kama da wuta dan bala'i ta ce ""Wallaahi ba zan lamunta ba, shi ne dan munafunci ni bai gaya mini ba,"

"kawai sai yau ka zo mini da wannan zancen, a'a wallahi"""

"Alhaji ya ce ""Ni dai in kin ga na fasa zancen auren nan, sai dai in shi ne ya dawo ya ce mini ya janye ya fasa, amma ba"

"zan zama mutumin banza ba, shima sai dai in yi masa jagora ya je ya samu ubanta ya ce masa ya fasa"""

"Hajiya ta ce ""Banda abun ki, ai ummi yarinyar kirki ce, nutsatsiyar yarinya ce, shi kyau ba shi ne abun dubawa ba,"

"nagarta ake da cancanta ake dubawa"""

"""Kin ga malama ki rufa mini baki, ban saka da ke ba, idan nutsatsiya ce, ki haWata da makakkun yaranki mana, sai Wa"

"na dama na san wannan duk kitumurmurarki ce, ke ki ka shirya wannan abun aka yi ban sani ba"""

"Hajiya ta ce ""Allah ya baki hauri, nima ban san zancen ba sai yanzu, kuma su makakkun aa ba laifi na yi wa Allah"

"ya bani ba, jarrabawa ce, kuma da da nutsatstse a cikin su na yi sha'awar sanya Waya ya aureta"""

"Har mami za ta yi magana, Alhaji ya yi mata wani mugun kallo, hakan ya sanya ta yin shiru tana huci."

"Hajiya kuwa tuni hawaye ya cika mata ido, tana jin zafin gori da cin mutunci da mami ke yi mata a kan yaranta, gani"

take yi kamar dabarar ta ce ta sanya Allah ya bata shiryayyun yara.

"Alhaji ya kalli mami ya ce ""Tun da kin saka mini mata kuka, sai ki bani wuri zan kula da ita"""

"Maganar ta sa ba aramin fusata mami tayi ba, ta tashi ta ce ""HaWiyeta arewar soyayya"" tayi waje fuu rai a Sace."

"Ya dubi hajiya da hawayen fuskarta suka fara zubowa, ya rungumota jikinsa a hankali ya ce ""You are brave woman,"

"kar ki karaya, ki yi hauri ke ce fa mai Kwantar mini da hankali da rarrashina, ki yi hauri in sha Allah zaki ga tanadin da Allah ya yi miki sakamakon hauri"""

"an ara sautin kukan nata tayi, hawayenta ya Sata masa riga, amma bai damu ba ya cigaba da rarrashin ta."

"Kira uku raihan ya yi wa ummi sannan ta Waga, tayi masa sallama."

"""Meyasa baki Waga ba, missed calls uku fa na yi miki"""

"""Ina aiki ne a kitchen, wayar tana Waki"""

"Raihan ya gyara kwanciyarsa ya ce ""To ya ki ke sweetheart"" wata irin kunya ce take kama ummi, idan ya ce"

"sweetheart Win nan, wai raihan ke ce mata sweetheart abun da kunya."

"""Ba zaki amsa ba?"""

"""Ina lafiya"" ta amsa a taaice."

"""To yaya, su Alhaji sun zo ko? Na ga ya dawo Wazu ina jiran ya kira ni ne"""

"A sanyaye ta ce ""Eh sun zo"""

"""Yauwwa masha Allah, daga nan zuwa kowane lokaci zaki zama matata baby"""

"Ummi ta ce ""Dan Allah ka din ga ce mini ummi kawai ko salma"""

"Raihan yayi murmushi ya ce ""Ba kya son babyn saboda me? Ba daga bakin yaro kamata ki ke son ji ba ko? Kar ki"

"yanke mini hukunci a yanzu, ina da kyakywan tanadi a kanki da rayuwarki ummi, zaki ji daWin zama da ni sosai da sosai ki yi ta yi mana addu'a kin ji my Salma""."

"Ta amsa masa da ""To"" amma tunanin yadda za ta yi rayuwar aure da raihan take yi, ita yanzu gaba Waya ma kunya yake bata."

"FaWowar mami afujajan Wakin ya sanya shi tashi zaune, ya ce ""Zan kira ki"" sai dai kan ya katse wayar ta ce ""Sannu"

"shashasha, ni zaka je ka aurowa wannan mummunar yarinyar?"" Kan ya katse wayar ummi ta ji me mami ta ce."

"""Mami meyafaru ne?"""

"""Uwarka da ubanka ne suka faru, in ce maka ga safiyya ka aura amma ka yi burus, ka je ka kwaso wannan yarinyar"

"uwar mata ka yi yaya da ita? Ta girmeka ba sa'arka ba kawai saboda baka da hankali ko dan ba ka da mafaWi?""."

"Raihan ya ce ""Mami, dan Allah ki kwantar da hankalinki, duk fa ba abun Waga hankali bane ba. Ke ki ka gabatar mini da ita da kyawawan halayenta, na ji ina jin tausayinta. Ki ka kawo mini maganar aure na ga ita ta dace da ra'ayina,"

"idan kowa ya ce ba zai aureta ba mummuna ce shikena sai ta rayu a haka, ba tausayawa babu kulawa?"""

"Rufe mini baki kan na daki bakin naka ya fashe, kai ne Wan sarkin taimako, wani ya taimaketa mana a waje, ta"

"girmeka ba sa'arka ba ce ba, ita ba ar uban kowa ba, kawai ka jajibo mana ita, to wallahi idan ma wannan matar ce ta zigaka dai-dai nake da ku. Kuma umarni nake ba ba shawara ba, ka je ka samu mahaifinku, ka janye wannan maganar da zancen auren nan da komai, dama ai ni na kawo maganar auren to safiyya na zaSa maka, ita kuma ummin na san yadda zan yi da ita"""

"Cikin sauri ya ce ""Dan Allah mami kar ki yi wa ummi komai, ni zaki yi wa ni na ce ina son ta, dan Allah kar ki sakata a"

"damuwa, dan Allah mami ki yi hauri"""

"Galala ta saki baki tana kallon sa, ""Au kar in sakata a damuwa? Har abun naka ya kai haka kenan? Dole na san abun"

"yi"""

Ta juya ta fita.

"Ummi kuwa a hankali ta sauke wayar hannunta, fes abun da ta ji mami ya faWa yake dawo mata, tabbas! Ta san a"

"rina ta san zata fuskanci wannan alubalen, tayi ta oarin ankarar da raihan, amma bai gano ba, ta san yanayin mami ar arya ce, mace ce mai iyayi da son nuna isa, ta san dama abu ne mai wuya mamin ta amince."

"Dr. Ya yi sallama a ofar Wakin ummi, ta amsa masa ya shiga, ya kalleta cikin farinciki da kulawa ya ce ""Ummana, ke"

"ashe Wan manya ki ka samo mini siriki, ai ni gatse na yi wa saurayin naki, ganin yayi yarinta da yawa, na ce ya turo mini babansa ni na ma manta, kin ga sai ga su sun zo"" Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tamkar ta ce wa dr. Dan Allah ya warware maganar."

"""Alhamdilillah, ina jin labarin Alhaji Tahir ashe babban mutum ne, mutumin kirki ne, kamar ba mai kuWi ba, yayi mini"

"bayanin komai, na Weba musu sati biyu, zan ne na yi bincike a kansu da yaron, in dai lafiya alau nan da sati biyu za su kawo kuWin auren, Ubangiji Allah ya kusa kawo miki arshen zaman gidan nan, Allah ya baku zaman lafiya, ya kawar da fitina."

"Dama wani jinkirin alkhairi ne, ki kwantar da hankalinki ummi, kar ki ga yaro ne arami, ki saka a ranki Allah ne ya duba ki, ya kawo miki miji."

"Ita nagarta ba a shekaru take ba ko tarin dukiya, babban fatan Allah ya tabbattar da alkhairi, dama ke mai biyayya ce, dan haka ki ara dan sa'anki ne kar ki ce ba zaki bi shi ba, Allah ya sanya muku dukkan alkhairi"""

"Ummi a ranta ta ce ""Ji kawu da wata magana, har da nasiha kamar an Waura auren, akwai ura fa' sama-sama take"

"jin sa, ya gama nasiharsa ya fice."

"Farida kuwa har Abdul ta tambaya, ko ya san suwaye bain dr., Amma ya ce mata shi ma bai sani ba."

Bayanin da Alhaji ya yi wa raihan ne ya rage masa damuwar abubuwan da mami ta yi masa.

"Ya Wora da cewa ""Mahaifiyarka ta fara tutsu, a kan ba ta san lamarin, idan har da gaske kana son yarinyar kana son"

"tainakonta, ka tsaya a kan hakan, ka cigaba da addu'a, ni dai yarinyar ta yi mini, ban ga aibunta ba, wani muni wani waye hotonta da ka nuna mini ban gani ba, ban sani ba ko dan kana sonta ba ka ga munin bane ya sanya nima ban gani ba."

"Ka je ka cigaba da shirye shiryen ka, a duba fili Waya ka gina abun ka yadda ka ke so, ba wata matsala in sha Allah"""

"Cikin girmamawa raihan ya ce ""Na gode sosai Alhaji, Allah ya ara maka lafiya da nisan kwana"""

"""Amin babban mutum"""

"Hajiya ta yi sallama hannunta Wauke da tray, da kayan shayi a kai."

"Tana ganin raihan ta ce ""In fara guWa tun yanzu ne, ko in Wan jira?"""

Murmushi raihan ya yi yana sosa eya.

"Hajiya ta zauna tare da faWin ""To kai raihan daga ganin ummi, har ce maka fa na yi wa ina yi wa yayanka kamu, kawai sai ka lallaSa"""

"Ya ce ""Wallaahi hajiya tausayi take bani a lokacin, na din ga damunta har muka fara sabawa. Hajiya ummi na da"

"matuar kirki da tarbiyya"""

"Hajiya ta ce ""Sosai kam, ina fatan Allah ya sanya alkhairi, na yi maka murna raihan, in dai mace ta gari ake nema, aka"

samu ummi to a gode Allah.

"Sannan shekarun da ke tsakanin ku ba abun damuwa bane, shekaru lambobi ne kawai, ka rie ta ka kula da ita, ni dai ina son ta saboda Allah, tun tana zuwa gidan nan lokacin maryam tana nan, akwai Wa'a da ladabi"""

"Raihan ya ce ""Kuma wallahi ta iya girki sosai hajiya, ba ki ga yadda take bani abinci ba, ban taSa cin abinci mai daWin"

"nata ba"""

"Alhaji ya dungure masa kai ya ce ""Sannu ciki muka kawo duniya "" suka yi dariya gaba Waya, gaba Waya sai ya manta da damuwar da yake ciki."

"Ummi na zaune na tilawar litattafanta na addini, wayarta ta fara ringing, bauwar lamba ce, tayi zaton ko raihan ne,"

dan akwai canza lambobi.

"Sai dai tana kai wayar kunneta, tayi niyyar sallama, ta gimtse sallamar jin uwar ashariyar da aka lailayo mata."

"""Sannu asararriya ar wahala, bain kunurci, saboda asara da taSewa kana da rashin kyakykyawar makoma, ummi ki rasa wa zaki ce zaki aura sai anina ummi, na yi dana sanin saninki, saboda kin zama guzuma muni yayi miki katutu"

"shi ne ki ka yi wa anina asiri, saboda zalamar abun duniya, to wallahi ummi ki kuka da kanki, ko ki janye wannan maganar ta auren raihan, ko kuma in asanta ki a idon duniya, in muzantaki kin san zan iya"""

"Jikin ummi yayi sanyi matua, ta kasa magana, har maryam ta yi tijararta a waya ta gama, ta kashe wayar, kamar"

shashasha ummi ta bi wayar da kallo.

"*Sweetheart, ki yi bacci cikin aminci da salama, zan so kiranki in ji muryar ki, amma na san wataila kin yi bacci, ki"

"kula mini da kanki, ina son ki* message Win raihan ya shigo wayarta."

"Ta mie ta tafi gaban mudubin Wakinta, tana arewa kanta kallo."

'to shi raihan ya aka yi baya ganin munina ne? A wajen ina munin nawa yake da yake Suya a idonsa baya gani?'.

"Abu kamar wasa, mami ta sako raihan a gaba, ta daina amsa gaisuwar sa, ta daina shiga sabgarsa ta ce lallai sai ya je"

ya cewa Alhaji ya fasa auren nan.

"Duk taurin kan Wa, fushin uwa masifa ne, hakan ya sake jefa shi cikin damuwa da wasi-wasi, idan ta ce ya rabu da ummi, sai ya ji kamar ta ce ya raba jikinsa da rai."

Gefe Hajiya da Alhaji suna ta arafafa masa gwiwa a kan auren ummi.

"Ga lokacin kai kuWi na cigaba da kusantowa, ga pressure office, ga ummi gaba Waya ta canza ta koma masa kamar"

"wata bauwa, tai sakin jiki da shi, kamar ma ara nesanta kanta da shi take yi."

"Yanayin aiki ya ara takura raihan, dan haka ko wurin aikin bai fiye samun damar binta ba, ga yawan barin asar da"

yake yi.

"Gefe guda maryam ta saka ummi a gaba da cin mutunci da zagi na cin zarafi kala-kala, ban da saonni da kuma"

"barazana da take yi mata, ummi ta rasa in da za ta saka kanta, daga kuka sai addu'a, dan ta

Please Login or Register in order to submit comment