You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan ma"

"dan in bar miki rigir ne ki ke kuka, ba zan baki ba, fito mu tafi"""

"Ba tare da ta saki fuska ba, ta ce ""Ni ka fita na cire rigar"""

"Ya basar ya ce ""Ki batta a jikinki, ki zo mu tafi""."

"""Dan Allah ka fita na cire"" tayi maganar a raunane tana Soye jikinta."

"A hankali ya taka ya nufi hanyar fita, ya sake waiwayo wa, tana tsaye jiran ya fita ta canza kayan."

Ya fita ya koma reception.

"Ba ™aramar kunya ce ta kama ta ba, ganin da yayi mata a haka, gashi dai doguwar riga ce, amma ta kasa manta irin kallon da yayi mata, da ya sanya ta shiga wani yanayi da ba ta san menene ba, gaba Waya sai ya canza mata, kamar"

ba raihan Win da ta sani ba.

"Ta mayar da hijjabinta, ta fito da rigar a hannunta, matar ta kallesu ta ce ""Rigar ta yi?"""

"Ya ce ""Eh, bamu wasu kalolin a haWa da wannan, su zama biyar sai takalmi uku da zai shiga da kowacce"" komai da"

"ummi aka gwada, kuma ba ta kawo komai a ranta ba."

"Šan nazarinta ya din ga yi, ko fushi take yi da shi, amma ya lura kawai ta tsorata ne, ta kasa sakin jiki ma tayi masa"

"magana, dan abu ne mawuyaci ka ga ummi ta yi fushi, dan zai iya cewa bai taSa ganin tayi ba, idan ma abu bai yi mata daWi ba, sai dai ta yi shiru."

"Suna tafe a hanya ya cigaba da yi mata hira, kamar bai ga komai ba, yana koWa kyan da kayan suka yi."

"Sai dai gaba Waya shima jikinsa yayi sanyi, basarwa kawai yake yi."

"Wani restaurant suka je, yayi reserving VIP, aka kawo musu abinci kala-kala, amma ummi ta ce ba za ta ci ba, ya"

gama kawai su tafi ita hankalinta yayi gida.

"""Amma mussman saboda baki je walimar nan ba na shirya mana wannan"""

"""Sai ka ce wani film, ni ka yi sauri mu tafi, kar na je gida na kasa kare kaina""."

"""Da na san zaki watsa mini ™asa a ido, da ban kashe kuWina ba, i did all this because of you"""

"Ta Wan kalleshi ta ce ""Ni ban taSa cin abinci a waje ba, dan Allah ka yi ha™uri"""

"Raihan ya ce ""Zan fita na baki wuri ki ci, amma idan ki ka yi mini haka ba zan ji daWi ba""."

"˜arshe dan kar ya ji haushi, da ™yar ta cakala ta ci, suka tafi gida."

"A hanya yake ta ce mata tayi ™o™arin rarraba CV Win ta, ko Allah zai sanya ta samu wani aikin da ya fi wanda take yi."

Ta ce masa zata jarraba yin hakan.

"Raihan ya dage sai ya mayar da ummi ´ar gayu, ta hanyar kaita wurare da zasu Webe mata kewa, ba tare da ™etare"

iyakar addini ba.

"A Wan fitar nan da ummi suke yi, take ganin mata kala-kala, masu dressing kala-kala, ba ta sani ba ko rashin shiga"

"cikin mutane ne ya sanya ita duk ba ta iya wannan abubuwan ba, hatta Waurin Wan kwalin da ta kan gani a kan mata yana burgeta, amma ita ba yi take yi ba, daga aikin gida sai makaranta ba ta da wani hope balle tayi tunanin wata kwalliya."

"Da Raihan yaje gida ya duba ledar da ummi ta bashi, sabon agogo ne kar, da links sai littafin azkar babba, da carbi"

counter.

"Ta yi rubutu kamar haka ""Allah ya taya ri™o mai girma MD, wannan ce gudunmuwata, ban san me kake bu™ata ba,"

"amma ina fatan ba zaka raina kyautar yayarka ba, Ummi"""

"Ya yi murmushi a hankali ya ce 'Kin rama kenan, a ta™aice kin dawo mini da kuWina'"

"Ya kirata a waya, sai dai wayar a kashe."

"Ya kashingiWa yana tuno ummin, mussaman Wazu da ta saka doguwar rigar abaya, tayi wani irin kwwarjini da kyau,"

"daga cikin abun da ya Wau hankalinsa dogon gashin ta har tsakiyar bayanta, ya fara tunanin anya ummi ba ta haWa dangi da wani ahali na yankin ™asashen ™etare ba? Idonta da gashinta, sun nuna hakan."

"""You are beautiful fa ummi"" ya faWa a fili ba tare da ya shirya yin hakan ba."

"Dubu talatin Win nan da ya bata, dubu biyu ce tayi saura, dan sai da ta saya wa kawunta turare, ta saya wa Abdul, sai"

"´ar Wakinta wato noor, har da su farida, amma kausar ta yatsuna fuska ta ce Allah ya kiyaye ta shafa wannan abun kamar ´ar bori, suka bar ta da abun ta."

"Duk da abun da suka yi mata, ummi ta ji daWin murna da addu'a da dr. Yayi mata, hakazalika Abdul ma yayi mata"

"addu'a sosai, mutuniyarta kuwa kasa zama wuri Waya tayi, dan ´ar tsana ta saya mata."

"Ummi ta yi mamakin yadda aka yi kuWin ma suka isheta, ba ta taSa tunanin haka yi wa mutum kyauta yake da daWi"

"ba, ayi ta yi maka addu'a."

"Kwanaki biyu da fitar su ita da raihan, tana Wakinta tana tilawa Abdul yayi sallama, ta kaste karatun tare da amsa masa."

"Ya mi™a mata ledar hannunsa, ta karSa tana kallonsa bakinta fal tambaya."

"Kan tayi masa tambayar ya ce ""Wani guy ne muka haWu a waje ya ce na baki, wani Wan dogo mai haske"" gaban ummi ya faWi, ta san ba wani bane face raihan."

"Abdul bai sake yi mata wani bayanin ba, ya fita daga Wakin."

"Jikinta na rawa ta hau duba kayan, dogwayen riguna nan ne da suka sayo, har takalman da komai."

"Da sauri ta tashi ta le™a ™ofar Wakin, ta tabattar babu kowa, me raihan yake nufi ne? Wannan kayan idan aka"

tanbayeta ta ce a ina ta samu?

"Layinsa ta fara kira, ya Waga a nutsensa tare da amsa sallamar da tayi masa."

"""Raihan, shine ka bawa Yaya Abdul wannan kayan ya kawo mini, idan aka tuhume ni a ina na samu me zance? Kar ka"

"janyo mini matsala fa"""

"""Kar ki ji komai ki ce ni na saya miki, saboda na fuskanci kina so, budurwa ce ke ba tsohuwa ba, dan haka mace sai"

"da kwalliya, ni ina da yayye da ™anne mata, duk in da mace take tana bu™atar kulawa, a kan bu™atunta na yau da kullum, kar ki ji komai yayata, ki yi kwalliyarki dai-dai da addinin musulunci, Allah ya kawo mana abokin rayuwa na gari"" maganar sa ta ™arshe, da yayi addu'ar sai ya ji wani abu mara daWi a ™asan zuciyarsa."

"Ya kashe wayarsa, ummi ta bi kayan da kallo, ina ma zata iya amfani da kayan nan, ta tashi ta kulle ™ofar Wakin, ta"

"Wauki kayan tana gwadawa Waya bayan Waya, karo na farko da ta Wauki jambakin da yasa mata wancan karon, ta ™ara tisa shi a kan jajayen laSSanta, ta saka kwalli a idonta."

"Ta ™urawa kanta ido a gaban mudubin, ta din ga juyi a tsakiyar Wakin, wai yau ita ce ta saka wannan kayan masu"

"tsada, ta kalli takalmin ™afarta mai tsini, ta din ga kaiwa tana komowa a Wakin."

"""Allah ya ™aro maka arziki mara yankewa, ya yalwata maka duniya da lahira"" hakanan ta ji ina ma ya ga kayan a"

"jikinta, har da janbaki ta saka yau, abun da yake so ya mayar da ita ´ar gayu."

***

"Gaba Waya farida ta kasa sukuni, tun da mijin inteesar ya ce zai ™ara aure, suke yawon neman asiri, amma babu abun"

"da ya sauya, ga azabar takura daga dangin miji, da gori na cewa ita juya ce."

"Da ya ce kan ya ™ara auren zai canza mata gida da furnitures, amma babarsa ta ce bata yadda ba, da wanne zai ji, kuWin da zai kashe yayi wani auren, ko kuma wanda zai kashewa juya, da ma tana haihuwa ne da sau™i."

"Gefe ga kausar dr. Ya ™ara hura mata wuta, a kan lallai ko tayi karatu, ko sai ta fitar da miji."

"Farida kuma ta yi alwashin, sai ummi ta koma ™auye ta bar mata gida, ko kuma ta fitar da miji itama, dan ba zai yiwu ya takura wa ´ar ta ita kaWai ba."

"Ga noor wani irin rashin ji take yi, ba ta shakkar farida ko kaWan, tsagera ce ta gaske, ummi ce kawai sai dr. Suke iya tan™warata, dan ko Abdul sai ta ga dama take jin maganar sa, dan ta ce faridan ba ta sonta, su inteesar kawai take"

"so, ita kanta ummi tsagerancin da noor take yi da ™anan shekarun nan, yana bata tsoro, amma babu yadda ta iya, tana yi mata addu'a, tare da yi mata fatan shiriya."

"Gashi farida ta Wora laifin hakan a kan ummi, wai ita take zigata, take hurewa ´ar ta kunne."

"Kamar a baya da duk abun da za ayi ummin ba magana take yi ba, haka yanzun ma, ba wani abun take cewa ba, duk"

abun da za ayi sai dai tayi shiru.

"Babban abun da ya Waga mata hankali, bai wuce kawu Yahaya da ya je gagarawa, ya dawo da katin bikin Yaya magaji"

"ba, kuma ya tabbatar mata da ita za su je bikin nan, kuma a yadda yayi maganar umarni ne kawai ba wai neman yardarta ba."

"Ta amsa masa da to, amma ™asan zuciyarta wani irin lugude take yi da fargaba, da fatan Allah yasa ba da sun je za a"

"baro ta a can ba, dan kuwa farida ta ™ara matsa lamba sosai da sosai, ta addabi ummi da gorin rashin aure da kuma"

™ara tabattar mata da barin gidan.

"Gefe guda kuma, abokin shawarar ta ta, ya zama very busy, wataran sai su wuni ma basu yi waya ba, ga tafiye-tafiye"

"da suka sako shi a gaba, saboda importing na kayansu, nan da nan kuwa ya fara rama, duk ranar da zai dawo gari, sai ya yi wa ummi waya tayi masa abinci, ya aika a karSo masa ba zai ci na gida ba."

"Alhaji Tahir ya sha suka da caccaka, a kan yadda ya Wauki ragamar babban kasuwanci kamar wannan, ya dan™awa raiha, a matsayinsa na ™aramin yaro, Alhaji Tahir ya toshe kunnensa, dan kuwa bai ji zai canza ra'ayi ba."

"Abunka da mata da miji, mami tayi ta lallaSa Alhaji, har ya amince da maganarta a kan raihan yayi aure, amma ya ce"

"ba ruwansa da zaSa wa raihan Win matar aure, balle auren ya™i daWi ace laifinsa ne."

"Shima Alhajin yayi iya ™o™arin sa wurin fahimtar da raihan muhimmancin ace yana da iyali yanzu, tun da ya samu"

matsayi.

"Raihan ya ce ""Wai Alhaji da wanne zan ji?, tsufa zan yi da wuri, ka manta nauyin da ka Wora mini?"""

"Alhaji ya ce ""Ni meyasa ban tsufa da wurin ba?akwai riba a cikin yin aure da wurin babban mutum, aure ba takura"

"bane ba, kwanciyar hankali ne da nutsuwar zuciya ka yi tunani a kai""."

"Raihan ya ce ""To Alhaji zan yi, zan yi shawara da hajiya"""

"Alhaji ya ce ""Ba maminka ba?""."

"""A'a Hajiya"""

"""Šan gidan Hajiya, ni ba zan bayar da shawara ba sai Hajiya kenan? Ai shikenan babban mutum""."

"Gidansu ummi kuwa yau gaba Waya jikinta babu daWi, ta gaji sosai da sosai, dan farida ba™i tayi, kan ummi sai ciwo"

"yake yi, kamar za ta yi zazzaSi da ™yar ta lallaSa ta yi aikace-aikace."

"Sai da ta jera kwana biyu ba ta zuwa aiki, ta sanarwa manager ba ta da lafiya ne, haka islamiyya ma, kwana biyu"

zazzaSi ya sakata a gaba da matsanancin ciwon kai da na ciki.

"Dama Ummi ba ta saka ran wani ya bata kulawa ba, ita da noor kawai suke jinyar, noor ta yi wanke-wanke da abun"

"da zata iya, a daddafe ummi take aikin gidan, farida ta lura da hakan, amma ko a jikinta dama da dr. Yana nan ne ya fuskanta zai kaita asibiti."

"Raihan kuma ba sa iya waya, sai ta what's app, dan kuwa baya ™asar gaba Waya, dan haka bai san halin da take ciki"

ba.

"Tun ™arfe shida ummi ta ga farida sun Wauki mota da ita da kausar sun fice, Abdul kuwa aiki ya™i samuwa, dan haka a wani kamfanin sarrafa taki, dr. Ya samar masa aiki, shima farida ta din ga kushewa, da nuna Wanta ya fi ™arfin"

"wannan, amma Abdul ya ce yana so zai yi."

"Ganin da noor tayi ummi babu lafiya sosai, ya sanya ta karya da buredi ta tafi tahfeez, ummi ta din ga burgima a"

"Wakin ta, ga amai kuma cikin ta babu komai."

"Wayarta tayi vibrating ya fi sau shida, da ™yar ta Waga ta yi sallama."

"""Baccin safe ki ke yau kenan, ko islamiyyar baki je ba? Na shigo gari jiya da daddare, abincinki nake son ci, kuma in"

"ganki""."

"Cikin ™arfin hali ta ce ""Dan Allah ka yi ha™uri, bana jin daWi amma zuwa yamma in sha Allah idan na gama zan kira"

"ka""."

"Bai san lokacin da ya tashi tsaye ba ya ce ""Ummi kamar fa haki ki ke yi, kina Asibiti ne?""."

"""A'a ina gida ne, zan warware in sha Allah"" tayi maganar da ™yar kanta na sarawa."

"""Bani 20minutes gani nan"" kan ta sake magana ya kaste kiran, ya fita da sauri."

"Ummi ba ta sake sanin in da kanta yake ba ma, sai da ta ji ana buga ™ofar Wakinta."

"A hankali ta ce ""Waye?""."

"""Mai gadi ne, kin yi ba™o ne, yana sallama"""

"Ummi ta ce ""To"" maimakon ta tashi, sai ta cigaba da bacci na rashin lafiya, a ™alla maigadin ya zo sau uku, kan ta iya"

fitowa.

"Hankalin raihan ba ™aramin tashi yayi ba, da ya ga ummi, idanuwanta duk sun yi waje."

"Tana ™arasawa ta nemi wuri zata zauna a ™asa, ya hanata hakan ya saka ta shiga motar."

"Tun da ya ja motar yake faWa a kan wasa da lafiyarta, oho ba ta ma san takamaiman zahiri ne ko mafarki ba saboda zafin zazzaSi."

"Ba a samo kan ummi ba, sai bayan ta sha ruwa roba biyu, sai dai a halin da take ciki, hankalinta yana gida, kar wani"

ya dawo a tarar ba ta yi girkin rana ba.

"Likita ya din ga yi mata tambayoyi cikin harshen Ingilishi, dan ba ya jin hausa, da ™yar take iya amsawa saboda ciwo,"

kuma hankalinta yayi gida.

"Ya ce ""Akwai ciki ne?"" Sai da ummi ta kalli likitan, amma ta kasa magana."

"Raihan ya ce ""Babu""."

"""Ka tabattar? When last ta yi period?"""

"Maimakon raihan ya ce ba ta da aure, sai ya kalleta ya ce ""Yana tambayar ki""."

"Likitan ya ce ""Kai baka sani ba ne? Are you not couples? Na ji ka ce babu ciki"""

"Raihan ya wani gyara tsayuwa ya ce ""Ai da yake bana gari, shiyasa ban ri™e ba, ummi ki gaya masa"" ta sunkuyar da"

"kai ta yi shiru, kamar ta buWe ido ta ga ta Sace, raihan ya gama da ita gaba Waya."

"Raihan ya ce ""She can't recall, but she's not pregnant"""

"Aka yi wa ummi teses, malaria da typhoid sun yi mata mummunan kamu."

"Likita ya ce a bari ta kwana Waya a asibitin, ummi ta ce ba ta san zance ba, ta sha faWa a wurin raihan kan rashin kula"

"da lafiyar ta, tare da yi mata kashedin saura ta je gidan a sakata aiki tayi. Ji yake tamkar ya samu wani kauwamammen wuri, ya ajiye ummi ya din ga kula da ita, kulawa ta musamman."

"Ta so ace zata iya abun da raihan ya ce, ta™i yin aikin gidan, dan a galabaice take, amma da cin mutuncin da za ayi"

"mata, gara aikin gidan."

"Tayi ta yi wa Allah godiya, har suka dawo bayan azahar su farida ba su dawo ba, dama noor sai la'asar zata dawo."

"Haka ta lallaSa take aikin, lokaci-lokaci sai raihan ya kira ummi, ya tambaye ta ya take ji a jikinta, gaba Waya ya kasa"

"nutsuwa hankalinsa ya ™i kwanciya, dan babban fatansa ace a kwance take ko ruwa za ta sha, a Waukko a bata."

"Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda headmastern makarantar islamiyyar su ya zo dubata ba,"

"har da kawo kayan dubiya, headmaster yana daga cikin mutanen da su kan hantari ummi, mussman idan ta je a makare, gashi ita kuWin makaranta take biya, wurin Waukar nata karatun, ita kuma koyarwar da take yi, ko sisi basa bata, dan raihan har mita yake yi, a kan hakan ya ce yakamata ko ba yawa a din ga biyanta."

"Amma ga mamakinta sai ga headmastern ya zo dubata, ba ta kawo komai a ranta ba, tayi masa godiya ya tafi."

"Saboda rigimar raihan, ummi ta lallaSa ta koma aiki, dan kuwa idan ba ta yi wasa ba, a sintirin da yake yi, sai an san"

"da ala™arsu, ala™ar da ba ta san ta yaya za ta yi bayaninta ba."

"Har wurin aikin yake bin ta, ya tabbattar ta ci abinci ta sha magani."

"Ta sanar masa da batun zuwa gagarawa, da yadda take cikin damuwar hakan, kar idan ta je a ri™eta a can."

"Raihan ya ce ""Ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru sai ikon Allah, kuma babu wanda zai rabaki da garin"

"nan, abun da nake so da ke, ki yi iya ™o™arinki ki sake samo information a kan mama idan kin je, zan san ™o™arin da zan yi a kan hakan, da wallahi suka ri™e ki a garin nan, ba abun da zai hana ni binki"""

"Šan buWe baki ta yi tana kallon sa, da gaske har cikin zuciyarsa yayi maganar."

"""Raihan wai ranar da na yi aure, yaya zaka yi ne?"""

"""Yaya zamu yi dai? A ´an uwanmu zan samo miki miji nagari, ni kin san kuwa mami ta sakani a gaba, wai tun da"

"Alhaji ya bani ragamar kasuwancin nan, wai sai na yi aure"""

"Ummi tayi dariya ta ce ""DaWina da mami hangen nesa, wallahi kuma da gaskiyarta"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Ba zaki gane bane yanzu haka kawai ganina ki ke yi, bana son yawan takura miki, amma sai kin"

"tayani da addu'a, akwai ™alubale sosai a harkar kasuwancin nan, kuma kamar yadda ki ka faWa, akwai bu™atar yadda ki ka gaya mini, ina bu™atar mace ta gari to assist me, wallahi ummi ban taSa budurwa ba, kuma bana son auren haWi, ni ba zan auri matar da bana so ba"""

"Ummi ta yi dariya ta ce ""Za a sha ™iriniya, amaryar ka za ta sha fama da ™uruciya"""

"Kallonta yayi ya ce ""Kin rainani da yawa fa, idan na fita kin ga yadda nake tsare gida kuwa a waje, a man of 24yrs, ki"

"ke cewa za a sha ™uruciya"""

"Ummi ta waro masa idanunta ta ce ""24 kuma, ka ji tsoron Allah raihan, yaushe ka kai 24yrs kuma?"""

"Ya ce ""Wallahi na cika 24yrs"""

"Da suka yi lissafi, watanni goma sha huWu ummi ta bashi."

"Ya ce ""Da na san ba wani girmata ki ka yi ba, ba zan bari ki raina ni ba, ashe ma sa'ata ce na ma fa fiki girma ummi,"

"daga yanzu ma ni ne yayanki yaya zaki din ga ce mini"""

"Ummi ta ce ""To meye a ciki Han? Ai duk in da namiji yake jagora ne, mai girma MD, sai dai ba a canzawa tuwo suna,"

"ni yayarka ce"""

"Yayi dariya yana shafa sajensa, ya na bin ta da kallo, ya kasa gane a wane bugire ma ya ajiye ummin ne a yanzu."

"""Me ka ke kallo ne?"""

"""Your eyes, masha Allah i like them, ina son idanunki"""

"Ummi ta rausayar da kai ta ce ""Idan ka faWi haka kana tuna mini da babana, idan na ce masa baba wai idona irin na"

"akuya ne da mage? Sai ya ce A'a, idonki mai kyau ne, ina son idonki ummina"""

"Raihan ya ce ""Allah sarki, Allah ya ji™an baba da rahama"""

"""Amin Yaya Han, ina godiya sosai da sosai"""

"Yayi murmushi ya ce ""Han sai ka ce sunan ´an china, amma duk yadda ki ka faWa zan amsa, ki kula da kanki sosai a"

"garin idan kin je, zamu din ga waya har ku dawo"""

"Ummi ta ce ""To, in sha Allah"""

"Ummi na son nunawa raihan hotunan da ta yi da rigunan nan a wayarta, amma ta kasa, shi kuma bai takurata da"

tambayar bai taSa ganin ta saka kayan da ya bata ba.

"Ummi ta lura kamar babu jituwa tsakanin dr. Da farida tun wancan karon da ya koma aiki, har wannan dawowar"

"tasa, sai dai kasancewar ummi ba huruminta bane ba, ya sanya ta cigaba da sabgoginta."

"Ranar tafiyarsu gagarawa na ™aratowa, adadin tashin hankalinta, da fargaba na ™aruwa, sai dai ta na ta addu'a a kan"

Allah ya kare faruwar dukkan wani abun ™i.

"Ta Wauki Waya daga cikin dogwayen rigunan wurin raihan, da abun da ba a rasa ba, ta haWa kayan da zata yi tafiyar da su."

"Dr. Ya ce har da noor zasu tafi, noor ta din ga murna, tana jin daWi."

"Suna tafe a hanya, adadin fargaba da tashin hankalinta, yana ™aruwa, tana tuna irin azabar da ta sha a gagarawa, ta"

"din ga fatan ina ma har ta je ta dawo, ba zata haWu da wasu mutanen ba, dan ko ambatar sunansu na sanyata cikin damuwa."

"Kwantsin yaran gidan ne suka firfito, suna shelar ga kawu Yahaya ya zo, yaran da galibi duk ba ta san su ba, dan da"

yawansu bayan ta baro garin aka haife su.

"Kallon gidan ummi take, zata iya cewa wannan gidan shi ne kurku mafi azaba a tarihin rayuwarta."

"Da yawa yaran basu san ummi ba, dan haka suka din ga bin ta da kallo."

"A tsakar gida sashen iya, mata nata hada-hadar shirin biki, sallamarta ce ta janyo hankalin matan."

"Wanda suka santa, suka din ga zuzuta girman da tayi, ta Waga kai ta kalli Wakinsu, Wakin mai Wauke da Wumbin tarihi, alamu ya nuna akwai mutane a Wakin, amma ba ta san suwaye a Wakin ba."

"Šakin Iya ta nufa, ta tarar da Iya zaune a tsakar Wakin ta, tana ta bayar da umarni."

"Saroro ta bi ummi da kallo, cikin ™arfin hali ummi tayi murmushi tana gaida Iya."

"""Yau Allah ya kawo ki wurin mayu kenan, wanda za su cinyeki?"" Ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kai."

Noor dai ta kame tana kallon kowa Waya bayan Waya.

"Dr. Ya shigo shima yana ta gaisawa da mutane, da ya isa Wakin iya, ko gaisawa ba su yi ba, ta fara masifar ya bar ummi ta balage ba aure, kodayeke dama ya za ayi ta auru, ai dama tun da tun farko ta™i amincewa da rufin asirin"

"aure, ya goya mata baya, haka zata ri™e a gida ba aure."

"Aikuwa kawu yahaya ya haWe rai ya ce ""Iya dan Allah ya isa haka, haba ummin guda nawa take? Ke ba ki yi farincikin ganinta tayi ilimi, a nutse a kame ba, ni na zaci wannan abubuwan duk sun wuce tun a baya?""."

"Ummi ta sha mamakin yadda Iya ba ta canza ba, tsawon wannan lokacin."

"Tun a daren yaya magaji ya zo wurin ummi, sun daWe suna hira, tare da murnar ganin sauyin da ummi ta samu, ya"

din ga gaya mata irin yadda abubuwa suke ta kwaSewa a cikin dangin nasu.

"Abubuwan duk babu daWin ji, mussaman gidan Idris, yarinyar su ta gaba da alfatiha, ™alubalen da take fuskanta ya"

sanya ta fara fanWarewa ita ma.

"Al'amarin bai yi wa ummi daWi ba, wanda jahilci ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutanen gidan."

"Washegari Waurin aure, bayan ummi da noor sun yi wanka sun shirya, ta ja noor suka fita gidansu na'ima, amma ta"

"tarar maman na'ima ta rasu, ™annenta duk sun yi aure."

"Doguwar riga ummi ta saka ta wurin raihan, sai dai tana jin ta kamar ba ita ba, saboda jin ta take a takure a cikin"

"kayan, dan ma rigar isashiya ce, sai dai fa ta zama a bar kallo a cikin gidan, duk in da tabi sai a kalleta."

"Iya ta din ga nuna wa mutane ummi, ga ´ar wurin bashir, da Idiris ya aura ta™i zama, ta bi kawu yahaya gashi"

haryanzu ta gama balagewa ta ri™a ba aure shi yanzu yana da yara biyar.

"Idiris kuwa tun da ya ga ummi kamar maye, saboda azabar kallo, sai dai ga mamakinsa ummi tayi masa kwarjinin da"

"ko magana ya kasa yi mata, gashi dai ba wani abun ta canza ba, kamaninta suna nan, sai dai ta girma ta cika, kai ba ka ce tana fuskantar ™alubale a in da take ba."

"Ko in da Idris yake bata kalla ba, balle ya sanya ran za ta gaishe shi."

"Su Alhassan ma duk sun girma, da su auwwalu, sai dai babu wani cigaba su ma, dan kuwa auwwalu ma ya zama Wan shaye-shaye sosai da sosai, dan har prison yayi, babu sana'ar kirki ya zama criminal."

"Alhassan ma babu sana'ar kirki, sai kamasho da ´an buge-buge."

"Raihan kuwa yana ta kiran ummi a waya, da jin ko komai lafiya ™alau."

"Ana dawowa daga Waurin aure, kawu yahaya ya ce zasu

Please Login or Register in order to submit comment