You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin hijjabinta."

"""Kin manta sunan naki ne?"" Ta girgiza masa kai."

"Ya sake cewa ""Ko ba turanci ne?"" Nan ma ta sake girgiza masa kai."

"""Oya ya sunanki?"""

"""Salma Muhammad Bashir"""

"Yayi murmushi ya ce ""What a beautiful name, na ga duk a tsorace ki ke, but mark you, this is university idan"

"malamai suka gane kina jin tsoron magana a public, za su yi ta takura miki da tambaya, ke kina jin tsoron amma ki ka zaSi aikin jarida? Ai harkar jarida na masu baki ne. But you can do it when you overcome your fear"""

"Ta Wago a hankali ta ce ""Thank you sir"""

"""³ar wace ™asar ce ke?"""

"""Jigawa"" tayi maganar muryarta na Wan rawa."

"""˜asa fa"""

"Ta ce ""Au Nigeria"""

"""Are you sure? Ko dai ta Sarauniyar hanya ki ka shigo mana ™asa? Kin yi kama da ba™a™en larabawan Afrika"""

"Ummi a ranta ta ce 'Amma kuwa an cuci larabawa, ko kuma ni aka cuta, maybe ba'a yake yi mini'"

"³an ajin kuwa dariya suka hau yi, ya ce ""Kalar idonta da complexion Win ta, ba irin na ´an Nigeria bane, dan haka"

"zamu bincika idan baki da lasisin zama a Nigeria mu mayar da ke ™asarku"" yayi maganar cikin zolaya."

A dole ummi ta ™a™alo murmushi.

"Ya ce ""Yi zamanki, Allah ya yi albarka"" kan ta zauna ta risuna ta ce ""Na gode sosai Allah ya ji™an magabata"" ya Wan"

"™urawa ummi ido, yadda take amsa masa magana ma, kawai ya isa ka gane tana da tarbiyya sosai. Ya ce ""Amin"" sannan ya suce gaba."

"Yayi musu nasiha sosai da sosai, a kan kula da ilimi da kuma tarbiyarsu, da ba su shawarar su ri™e addinansu, kar su"

lalace saboda kawai sun ga sun shiga jami'a.

"Kowa harkarsa yake ba ruwan wani da wani, dan haka ummi ta ji daWin hakan, da babu wanda ya matseta balle ya takura mata."

"Baki har kunne ta koma gida tana murna, duk da tana zuwa gidan ta tarar da uban kwanukan wanke-wanke, da"

"wankin kaya, kuma an cinye abinci tas, kuma ana jiran ta Wora na dare."

"Hijjabi kawai ta canza ta hau aiki, noor ta din ga bin ta, tana tambayarta ""Anty, kin yi magana a gidan radiyon?"""

"Ummi ta ce ""A'a mamana, sai an kwana biyu tukuna"""

"""To ta ina zaki din ga shiga radion kiyi magana?"""

"Sai dare yayi kin yi bacci, zan buWe gurin batirin in shiga ta ciki."

"Noor ta buWe baki cikin mamaki, sannan ta ce ""To zaki shiga da ni nima?"""

"""Sai kin ™ara girma sosai tukuna, noor ta dinga tsalle tana murna."

***

"""Bilki, ki kira Bauchi ki gaya musu ba fa haka muka yi da su ba, ni fa ba bar musu Wa na na yi ba, haba sun ri™e mini"

"Wa ko le™o ni baya yi""."

"Ta kalleshi ta ce ""TaS, ba ruwana kun fi kusa, ka kira su ka gaya musu mana"""

"Yayi murmushi ya ce ""Shima zan gamu da shi ne, ko a waya baya nema na"""

"Ta Wan yi murmushi ta ce ""Wai Wazu da ina bacci, da wa ka ke magana ne, ka ke ta faWa?"""

"Ya Wan ja guntun tsaki ya ce ""Salim mana, wai zuwa yayi na bashi kuWi zai yi gyaran mota""."

"""To meyasa ba ka bashi ba?"""

"""A kan me zan bashi? Duk iya ™o™arin da zan yi na yi wa yaran nan, dan su zama na gari, amma abu ya gagara. Yanzu"

"daga shi har Wan uwansa da a nutse suke, da yanzu yaushe zan din ga wannan zirga-zirgar?"""

"Bilki ta Wan yi ajiyar zuciya ta taSe baki ta ce ""Laifin babarsu ne, da ta bari suka lalace""."

"Yayi saurin girgiza kai ya ce ""No, Hajiya na iya ™o™arin ta a kan tarbiyyar yara, dan har ta fiki tsanantawa ma wasu"

"lokutan"""

"Ta tsuke fuska ta ce ""Eh, nice mai sake da tarbiyya kenan?"""

"""A'a mai gado ba haka nake nufi ba, ai kin ga matan duk lafiya ™alau, gashi duk sun yi aurensu suna zaune lafiya, su"

"Win ne dai, kuma shima na san jarrabawa ce, ba a barin Wan Adam haka""."

"""Allah ya kyauta, amma nikam ba zan bari auta ya ri™a ba yazo na kasa contrilling Win sa ba, aure zan yi masa yana dawowa"""

"""To hakan ma yana da kyau, Allah ya zaSa abun da ya fi alkhairi mai gadon zinari"" yayi maganar yana jan hancinta."

"""Ba wata mai gadon zinari, ka koma wurin dattijuwar matarka"""

"Kwashewa yayi da dariya, ya ce ""Bilkisu, hajiyan ce dattijuwa Allah ya sa ta ji ki, ai shekarunta ba sa nunawa, saboda"

"gayunta, kuma ni bana ganin girmanta, ba ta fi fifty fihe ba, amma idan ta Waura Wankwali kamar ´ar 30yrs. Ai da yake ni na mayar da ita tsohuwar, ganinta nake kamar ´ar 16 lokacin da na aurota, hajiya ba ta tsufa"""

"Wani irin haushi ya kama bilkisu, ta yin™ura za ta tashi ta bar masa wurin, ya ri™eta yana dariya ya ce ""Danne kishin nan kar ki bari ya fito""."

"Alhaji Tahir kenan, tsohon Wan boko, kuma babban Wan kasuwa, da yake juya naira yadda yake so."

"Mutum ne mai sau™in kai da matu™ar son iyalinsa, mussaman ´a´ansa, dan mutum ne mai biyewa ra'ayin yaransa,"

"duk abun da suke so muddin bai saSawa addini ba, zai yi musu shi, yana bawa iyalansa ´ancin yin abun da suke so, ba tare da ya takaura musu ba."

***

"Rashin wayar hannu, yana daga manyan abubuwan da suka zama barazana ga ummi, a harkar karatunta, gashi ita ba kowa take raSs ba, balle idan an bayar da assignment ko class work tayi, idan assignment ne ta gwammace ta kai yamma a makaranta, ta je Library ta yi."

"Gashi farida ta tsiro da sababbun hanyoyin muzguna mata, ta hanyar ™ir™irar mata abun da za ta sanya ta makara, wataran har ma ta rasa lectures baki Waya."

"Daga baya ne take iya ro™on Abdul aron wayarsa, tayi assignment da ita."

"Abdul ne ya gaya wa dr. Yakamata a saya wa ummi waya, saboda makaranta."

"Da ya tashi dawowa ya taho mata da sabuwar waya, mai kyau da tsada, amma farida ta ™wace ta bawa kausar, kuma ya kasa magana a kai."

"Ba waya kawai ba, hatta undeas ummi na fuskantar matsala a kan su, sai dai idan ta tara ´an kuWi da ™yar, idan"

farida ta aiketa kasuwa ta sai na gwanjo.

"Daga baya Abdul ya saya mata wata ´ar ™aramar waya, gionee take amfani da ita."

"Makaranta ma da nata irin ™alubalen, domin kuwa ´an ajinsu, akwai yaran masu kuWi, akwai ´an ™arya da yaran talakawa masu jin cewa su wasu ne."

"Gani suke ummi ba tsararsu ba ce da za su yi mu'amala da ita, mussaman ganinta babu suturar kirki, kullum cikin"

"hijjabi, hijjaban nata da guda biyu ne take zuwa da su, sai takalminta Waya Wan wambai."

"Banda masu zunWen halittar ta, ko tambaya za ayi a aji, idan za a tanbayeta, sai malami ya ce dark skin girl."

"Ummi ta sanya a ranta babu wani ™alubale, da zai sanya ta kasa ha™uri ta cimma burinta."

"Yunwa da tafiyar ™afa a kan karatun nan suka zamewa ummi jiki, ko lissafasu ba ta yi a cikin wahalar rayuwa,"

"handout kuwa ba kowanne take iya saya ba, wataran idan har zata sayi handout, sai ta yi trecking, domin samun kuWin sayen handout."

"Ta wuni a makaranta ba cin abinci, ta koma gida ta ci uban aiki, a ™arshe ba godiya sai zagi da muzantawa."

"HOD kuwa ba ™aramin mutunta ummi yake yi ba, saboda idan ta ganshi sai ta kai ™asa take gaishe shi, idan ta ganshi"

"da jaka, sai ta bishi ta karSa."

"Yana jinjinawa tarbiyyar ta, da bayar da misali da ita, dan shi rabon da yaga Walibi mai biyayyarta tun a zamaninsu,"

shima zamanin na su ba kowa ba.

"Ummi ta dawo daga masallacin makaranta, tana ta sauri ta ™arasa aji, saboda malamin da zai shiga, ko da minti Waya ya rigaka shiga aji, ba zaka shiga ba."

Abun da kunnuwanta suka jiyo mata wani Wan ajinsu ya faWa ne ya tayar mata da hankali matu™a.

"""Kai isha™, ka yi sauri mu tafi kar malamin nan ya rigamu shiga, ga gorillar ajinmu can na ta sauri""."

"Kalmar gorilla! Ta daki ™irjin ummi, hakan ya haifar mata da wata irin mutuwar jiki, munin nata har ya kai a kira ta da"

gorilla?

"Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri-sauri, tamkar zata kifa ™asa ta shiga ajinsu tana wani irin kuka, wane irin abu ne"

wannan?.

"Ishaq ya kalli abokinsa ya ce ""Kai Nura kamar fa ta ji ka"""

"""Ahha haba dai?"""

"""Tana kusa fa ka faWa"""

"Nura yayi tsaki ya ce ""To sai me?""."

"Ishaq ya ce ""A'a nura, zuciya ba ta da ™ashi, cin fuska ba shi da daWi, tuntuni na gaya maka ka daina kamanta ta da"

"dabba, yarinyar so silent ba ruwanta da kowa bai kamata ba wallahi"""

"""Ka ga kar ka isheni, jokes ne"""

"""Ai gaskiya ce, ba wani jokes wallahi, ko kusa yarinyar nan ba ta yi kama da abun da ka ke misalta ta ba, hidden"

"beauty ne da ita, ba™inta da rashin gayu ke hana kyanta fitowa, amma ba ta yi kama da abun da ka ke faWa ba""."

"Suka tafi aji, yana ta yi masa faWa, suna shiga aji kuwa, kan ummi a ™asa da alama kuka take yi."

"Gaba Waya jikin Ishaq yayi sanyi ya ce ""Ka gani ko? Kuka take wallahi""."

"Shigowar malamin ya sa kowa ya nemi wuri ya zauna, ya fara gabatar da abun da ya kawo shi."

Sai dai yana lectures yana ganin yadda ummi ke sharSar hawaye.

"""Ke are you ok? Meyake damunki ne?"""

"Ta kasa magana ta tashi tsaye tsam, ta Wauki jakarta cikin kuka ta ce ""Sir dan Allah ka bani iznin tafiya gida"""

"Duk da zafin malamin da rashin son wargi, amma kukan da ummi take yi, yana nuna akwai tsantsar damuwa a"

zuciyarta.

"Kamar yadda ake son malami ya kasance cikin kulawa ya ce ""Babu damuwa, amma zaki iya tafiya? Ko ki na da ™awa"

"ta raka ki gidan?"" Ta girgiza masa kai ta ce ""Zan iya tafiya"""

"""Kin tabbata?"" Ta jinjina masa kai alamar eh."

"Ya ce ""To shikenan, ki tafi a hankali ki yi ta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta jinjina masa kai ta risuna masa ta yi"

masa godiya sannan ta fice ta tafi gida.

"Ta daWe ba ta yi kuka mai yawan na yau ba, tun noor tana rarrashinta, har ita ma ta fara kukan."

"Ta rarrashi noor, ta aiketa kitchen, ta mayar da ™ofar Wakin ta rufe, ranar ba irin bugun da farida ba ta yi ba, a kan"

"ummi ta buWe ta zo ta yi mata aiki, amma mursisi ta™i buWewa abun za ba ta taSa yi ba kenan. Ta san ™arshen abun dai, zagi ne za ta sha shi da cin mutunci a wurin farida."

"Tayi shiru tana tunani kala-kala a zuciyarta ""Ko zan ji daWi a rayuwata? Ko zan huta, ko kuma a haka zan cigaba da"

"rayuwa, sanin gaibu sai Allah."

"Idan ina da rabon hutawa da jin daWi, Allah ka kawo mini su da wuri, ba dan na gajiya da karSar jarrabawar ka ba,"

"ni'imominka gareni sun ninka jarrabawar, Allah ka shiga lamarina"" tayi maganar a bayyane cikin kuka"

"Sai da ta jera kwana biyu ba ta je makarantar nan ba, ranar da ta je, malamin da a period Win sa ta tafi gida, ya kirata"

"ofishin HOD, suka din ga tambayar ta meyake damunta, dan malamai da yawa sun fuskanci kamar tana da social fear."

"Kukan da ta kasa ri™ewa a gaban su, ya tabbattar musu da tana da damuwa sosai da sosai."

"Duk yadda suka matsa ta, ba ta gaya musu abubuwan da suke damunta ba, duk da tana da abubuwa da dama a"

"ranta, da take son tattauna shi da wani, amma ta kasa samun wanda zuciyarta za ta nutsu da shi, su tattauna sosai, ko ba ayi mata maganin damuwar ba, atleast ta furta abun da yake damunta."

"Suka nemi zasu zauna da mahaifinta, amma ta din ga yi musu magiya, a kan kar su yi hakan, dan a ganinta idan aka"

"yi hakan tamkar ™ure babanta kawu yahaya ne, domin kuwa yana iya ™o™arin sa a kanta."

"Nasiha suka din ga yi wa ummi, tare da bata ™warin gwiwa, a kan muhimmancin mayar da hankali a kan karatunta, da shanye ™alubale, wanda ba ™aramin jin daWin nasihar ta su yi ba."

"A ™arshe HOD ya cigaba da tsokanar ta, da cewar ba ta da visa ba™ar balarabiya ce ta shigo musu ™asa."

"Šaya malamin yake ce mata, tun da ´ar jarida ce ita, kuma an san su da neman suna, idan ta mutu yana son idonta"

"zai saya da tsada, ta shiga kundin tarihi."

"HOD ya ce ""Allah ya kiyaye, wannan idon na larabawa ne a Nigeria Masha Allah, in dai wannan tarihin ne mun yafe,"

"ko Salma"""

Ummi ta sunkuyar da kai tana murmushi.

"Ummi ta ji daWin mutuntawar da malaman da take wa kallon iyaye suka yi mata, da nuna damuwarta kamar ta su,"

"nasihohin su, sun shige ta sosai da sosai."

"HOD yaje ajin su ummi, ya yi musu jirwaye mai kamar wanka, ta hanyar gugar zana a kan wula™anta Wan Adam, da muhimmancin girmama Wan Adam."

Ta samu sassauci daga jin wani abu mai nauyi da yake damun zuciyar ta.

"Sai dai ta kasa manta kalmar gorilla, noor da Abdul suna falo suna kallon film Win king Kong, ummi har ta wuce ta"

"dawo, ta ce ""Yaya Abdul"""

"Ya Waga kai ya ce ""Na'am yaya ummi"""

"""Dan Allah wai ina kama da gorilla?"""

"Wani irin banzan kallo yayi mata ya ce ""Wace irin magana ce wannan?"""

"Cikin son Soye abun da ya faru ta ce ""Amm, dama kawai na tambaya ne, dan na ji ana cewa ni mummuna ce"""

"""Kuma sai ki haWa kanki da biri, haba ummi, ke tsakani da Allah idan aka ce ke mummuna ce sai ki yarda? Ki ™arewa"

"kanki kallo, a kan me zaki yadda ke mummuna ce? A halittar Allah babu mummuna, duk wanda ya ce miki mummuna ki ce ubansa ya sassa™o kamar ki"""

"Noor ta ce ""Maama kenan za a gayawa, itama tana cewa yaya ummi mummuna, kuma fa yaya ummi gashinta har"

"nan, tafi fa maama gashi"""

"""Tashi ki bar nan wurin kan na tatsileki, baba suda"" yayi maganar yana kallon noor."

"Ummi kuma ta ce ""To shikenan yaya Abdul, na gode sosai """

"""Dan Allah kar ki kuma faWar haka """

"""Ba zan sake ba in sha Allah"" sai dai a ranta tana jin har ta mutu ba zata manta da Nura ba, ya shiga cikin jerin"

mutanen da take yi wa wani irin kallo a zuciyarta.

"³an ajinsu ummi ba su tashi mamaki ba, sai da result ya fito na first semester, ummi ta ja magana, GPA Win ta 4, wanda kaf ajin babu mai wannan grade Win."

"Kasancewar Wabi'a ce ta Wan adam, mu'amala domin cikar muradi, ya sanya suka fara lallaSowa, domin shiga jikin"

"ummi, amma fafur ta™i ta cigaba da rayuwar kaWaici."

***

"Gidan Idris kuwa, kamar masu zaman bariki, saboda faWa zagi yana zagin hindu tana ramawa, tana kiran sunan"

"uwarsa da ubansa tana zagi, idan yayi gangancin dukanta kuwa, ta dinga wawurar abubuwa tana kwaWa masa kenan, dambe da zage-zage har ™ofar gida kamar dabbobi, ma™wabta suna raba su."

"Sulhu kuwa an yi musu shi babu adadi, amma abu ya ci tura."

"Sam ba ta ganinsa da mutunci, shi ma kuma haka, taje gidansu ta gaida Iyayensa kuwa ba ta wannan, saboda ta ce ba zata je gaida tsohuwar banza ba, ta ji labarin zaman da yayi da matarsa ´ar uwassa, ita ba zata lamunci cin zarafi ba."

"Ya gaji da iskancinta, ya kamata yayi mata tulus da duka, ashe tana da juna biyu, ta yanke jiki ta faWi, ™arshe dai sai"

"da iyayenta suka rufe Idris a police station, aka wula™anta shi aka kai ruwa rana kafin a sake shi, banda kuWin magani da aka saka ya biya."

"Kwana biyu da dawowar sa daga hannun ´an sanda, ya je ya samu hashim a kan ya bashi shawara, so yake a lallaSa"

"kawu yahaya da ummi, a dawo da auren su."

"Hashim ya ce ""Haba Idris, lokacin da na din ga ankarar da kai ai kasa ganewa kayi, ummi tafi ™arfin ka yanzu, wace"

"irin azaba ce ba ka yi mata ba, tun tana ™aramar yarinya. Yanzu ta sauke Alqur'ani har sau biyu, ta shiga jami'a tana karatu, ka ce ta dawo, to tayi maka me? Kai da ko kwalin sakandare baka da shi""."

"Idris ya waro ido ya ce ""Ummin ce a jami'a, kai waye ya gaya maka?""."

"Hashim ya ce ""Muna waya da ita, bautar ™asa nake son na gama, idan Allah ya sa na samu aiki, zan nemi auren ummi""."

"Idiris yayi masa wani mugun kallo ya ce ""Amma dai ka ci kai, matar da na saki zaka aura? Bazawara ce fa kai kuma"

"baka taSa aure ba. Haryanzu bana son ummi, ban taSa jin ™aunarta a raina ba, amma ina da muradi a kanta, idan har ba ta dawo mini ba, idan ina raye baka isa ka aureta ba""."

"Hashim ya yi murmushi ya ce ""Zamu gani ai"" Idris ya tashi fuuuu ya tafi."

"Idris yayi shiru yana tunani, tun da mahaifinsu ya takura masa da maganar aure, ya gaya masa ga ™udurinsa, Iya ta"

"ce bai isa ba, ba zai auri bazawar da ™aninsa ya saki ba, kuma ta riga ta cire ummi daga jikokinta tun da ta ™i yarda a rufawa Idiris asiri!."

"Babansa kuma ya ce Idan ya sake Waga maganar nan, zai yi masa abun da bai taSa tsammani ba."

"Duk son ummi da islamiyya, haka ta ha™ura, saboda yanayin makaranta, ta samu wata makarantar, a nan"

"unguwarsu, take zuwa asabar da lahadi Waukar karatu."

"Sai dai ganin ummi tana da ilimin addini dai-dai gwargwado, idan aka yi mata ™arin nata karatun, sai a haWata da aji"

tayi musu ™arin Alqur'ani da wasu litatafan.

"Duk da ayyuka sun ™ara yi mata yawa, hakan yayi mata, saboda tana zama busy sosai, tana hana zuciyarta tunane-"

tunane da sukan jefata cikin damuwa.

"Ga bikin Intee ya matso kusa, sai gori take sha a gidan nan, wai ta zama guzuma, babu mashinshini a haka za ta"

dauwwama wanke-wanke da shara.

"Kawu yahaya yayi rawar gani, ya yi wa inteesar kaya na kece raini, ya so ace ta fara makaranta kan yayi mata aure,"

"amma ta dage soyayya ta rufe mata ido, ta ce ita fa aure take so, dan haka ba yadda ya iya ya ™yale ta."

"Sagir ya dan™aro mata uban kayan lefe, kaya ba na wasa ba, ya ciko akwatuna da kaya, sai iyayi take tana rawar kai."

"Albarkacin auren inteesar, a wannan karon da kawu yahaya ya yi mata Winki, farida ba ta ™wace ba, har da sabon"

"takalmi, farida kuma ta bata tsohon mayafi, kalar kayan."

"Ranar party, farida ta ce ta zauna a gida, ta kula da ba™i masu shige da fice, kuma ta tsaya a kan girke-girken da za ayi."

"Ummi ta zage ana can ana party, tana gida suna aikin girki, dan ita ta jagoranci aikin abincin bikin."

"Ranar wuni ya kama ranar da za'ayi Waurin aure, dan haka da wuri motoci suka kawo ´an gagarawa."

"Su Idris da babarsa, su magaji kafatanin ahalin Iya."

"Lokacin ummi ba ta gidan, suna can tana ta hidima da ™awayen inteesar, ana yi wa inteesar kwalliya."

"Ummi ta yi wanka, ta yi wa noor, ta saka kayan ankonta da ita da noor."

"Sai da inteesar ta kalli ummi ganinta babu mayafi, dan zata iya ™irga rabonta da ta ga ummi babu hijjabi."

"Tayi ture ka ga tsiya, ta kanannaWe gashinta a ™eyarta, Waurin ya zauna cas a kanta, ga Winkin ma dai-dai jikinta."

"Ta shafa man leSe, ta yafa mayafinta a kanta, ta rufe jikinta sosai, ta kama hannun noor, suka fice."

"Wani irin farinciki ya kama ummi, ganin ´an gida gaba Waya sun zo, dan rabonta da su tun da ta baro gagarawa."

"Duk bin ummi suka yi da kallo, yadda ta girma ta zama budurwa."

"Cikin su ummi ta shiga tana gaishe su, Iya sai wani hura hanci take yi."

"Ta ce ""Ina yaya magaji?"""

"Sa'adatu ta ce ""Sun tafi wurin Waurin aure""."

"Ummi ta karrama su da abinci, dan matar gidan ba ta ta su take yi ba, ta kai su Wakinta, ta yi ta Wawainiya da su."

"Bayan azahar su Hashim suka dawo daga wurin Waurin aure, ummi baki ya™i rufuwa saboda duk ´an uwan mahaifinta sun zo."

"Šaya bayan Waya ta din ga gaishe su, suna mamakin yadda ta girma, ta zama cikakkiyar mace, sai dai ko kusa bata kalli in da Idris yake ba."

"Farida sai bin ummi take yi da kallo, dan ba ta taSa tsayawa ta kalli ummi sosai cikakken kallo ba sai yau, rashin gyara"

"ne ke ™ara munanta ummi, idan ka kalleta sau Waya sai ka sake kallonta, mussaman yadda take kokowa da mayafin, kasancewar ita ba ma'abociyar ta'amalli da shi ba ne ba."

"kasancewar hashim shi ne mutumin ummi, can harabar gidan suka koma, suna ta hira."

"Ya dubeta ya ce ""Ummi, kawu yayi miki magana kuwa a kan batun nemo mamanki?"""

"Cikin sauri ta ce ""A'a, ya ake ciki?"""

"""Subhanallah, ya ce dai kar na kuskura na gaya miki saboda wani dalilinsa, amma dai idan bai ganta ba yana daf""."

"""Ya salam, bai gaya mini ba, ko maganar zan yi masa?"""

"""A'a, dan ya yi mini kashedin kar na gaya miki, ki kwantar da hankalinki duk abu zai haWaku""."

"Cikin karaya ta ce ""Yaushe hankalina zai kwanta, tana raye amma rabona da ita kusan shekara goma sha, ina son"

"ganinta""."

"Idiris kuwa wani abu ne ya din ga yi masa zillo a ma™ogwaronsa, ganin ummi tare da Hashim, gashi ta gayar da"

"kowa, amma ko sashin in da yake ba ta kalla ba, balle ta gaishe shi. Kasa daurewa yayi, ya nufi in da suke zaune."

"Sai dai ummi na hango shi, ta mi™e tsaye ba tare da ta gama maganar da take yi da Hashim ba."

"Cikin zafin nama ya sha gabanta, ya kalleta ya ce ""Ina zaki je? Saboda wula™anci ki ka gaida kowa baki iya gaisheni"

"ba, kuma na taho da ki ka ga nan zan zo, shine ki ka tashi""."

"Cikin ™wayar idon Idris ta kalla, wani abu mai kama da wuta yana zafi a ™irjinta."

"Tuni idanunta suka tara hawaye ta ce ""Cikin abun da bana ™aunar sake gani a nan duniya har da lahira, har da"

"fuskarka, ka matsa ka bani hanya, ko kuma in yi maka abun da baka taSa zato ba!"""

Whats app only please

Ayshercool. 08081012143

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P21

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu"

Abduljalal

Wata kissar sai mata Wuta a masa™a Cutarwa

˜anwar maza Gaba da gabanta

A™idata

RuWin ™uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata.

8081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da ´an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da ™amshi.

"Mafaka gidan ™amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ³AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ˜ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ˜AWATA GIDAJENSU DA HAŠAŠŠUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAŠAŠŠUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAŠAŠŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ˜ARIN BAYANI,

Please Login or Register in order to submit comment