You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, ni mijinki nace miki ga abinda zan ci shine
zaki wani ce kin rufe karɓar girkin to ni zaki yi wa biyayya ko wa"


"ni ban san da wani batun aure ba aiki nake yi ake biyana, kamar yadda ka ɗauki
auren ka yada shi a kwandon shara haka ni ma na ɗauke shi na saka shi a masai kaga
yanzu ba wannan batun ake ba don haka ka ajiye wani batun mijin aiki ne na yau na
rufe karbar order in kana son parpesu gobe da safe ka kira kitchen ka faɗa" ina
gama faɗa masa na raɓa ta gefen shi na wuce



Lallai le ma yarinyar nan ni zata ce wa haka, ni da nake a matsayin mijin ta nace
ga abinda zan ci shine bazata girka ba sai wasu Ƙarti zata girkawa abinci wallahi
da sake ya za ayi wai matata ni baza ta min abinda nake so, wallahi hakurina ya zo
ƙarshe dole ne a matsayin ta na matata ta kasance tana ƙarƙashina sannan tana bauta
min ne ni kaɗai
Yana masifa ya kama hanyar part ɗin mummy dole ne duk abinda za a yi ayi a yau
amma ban yadda ba ace matata ban da iko da ita


Har ya shiga ɓangaren mummy yana masifa, tana zaune ta ga shigowar shi ko sallama
babu duk a tunanin ta ma ko faɗa sukai da badia ta ɓata masa ransa


"lfy auta na ganka haka wa ya taɓa min kai," ran shi a ɓace ya zauna kusa da ita
sannan yace


"gaskiya mummy na gaji da wannan abun da ake min wai ace matata ta zama baiwa a
gidan nan, kowa zai iya juya ta yadda yake so amma banda ni mijinta gaskiya bazata
saɓu ba na gaji lkc yayi da matata zat dawo ƙarƙashin iko na" sam mummy bata
fahimci sai tace masa


"auta wake juya maka badiar taka" mummy ta tambaya, ɓata rai yayi sam baya son
ambatan sunan asmau don gani yake yi kamar ajinsa zai zuba amma ganin mummy sam
bata ɗauko maganar tashin ba ya sa shi ambatan ta


"ba badia nake nufi" ya faɗa ƙasa ƙasa, dariya ne ya so ƙwace wa mummy amma sai
ta dake lallai tarkon data ɗana ya kama ɗan natan ke nan


Amma sai ta nuna sam bata gane me yake nufi ba

"auta a gidan nan kana da wata mata ne bayan badia, only ɗin taka" ɓata rai taga
yayi sannan ya ƙara sunkuyar da kansa tare da yin ƙasa ƙasa da muryar sa kamar
wanda yake jin kunyar furta kalmar sannan yace


"ɗayar matar tawa mana, mummy kar ki ce kin manta ta mana" shiru mummyn ta sake yi
kamar me tunani dariya ce take son suɓuce mata amma kuma tafi son sai ya faɗi sunan
ta da kanshi


"in banda abin auta ai da ka faɗa min in ka kuma ganin wata kana son ƙarawa, ai
dama na san nan gaba dole ka nemi ƙari tunda baka samu mace ba har yanzu"


"mummy wai asmaun ce kika manta" ya faɗa a fusace dariya ce ta suɓuce wa mummy

"dama ina son jin sunan ta daga bakin ka yanzu me ya haɗa ku da asmaun kazo kuma
kana complain"


"mummy yarinyar nan ko kaɗan bata san matsayin miji ba" nan ya labarta mata abinda
ya haɗa su da asmaun sannan ya ɗaura da cewar


"gaskiya hakuri kawai nake yi ni matata bata da lkcn da zata kula ni kullum sai
dai ta dinga girkawa wasu abinci amma ni sam bata da lkc na gaskiya baza ta saɓu ba
nagaji" yai ta mita


Mummyn sakin baki tayi tana kallon ikon Allah sannan a ranta tana godewa Allah
daya dawo da hankalin sabit kan asmau, don kuwa ko ba komai asmau sai tafi badia
iya kula da sabit sosai



Bata da wani buri daya wuce ace ta samu me kular mata da ɗan autan ta sabit, badia
ba me son aiki bace don haka gaba kaɗan sabit zai rasa macen da zata kula da shi


Amma asmau daga ganin ta zata juri wahala kuma zata iya ɗawainiya da wahalar sabit
kuma ta asmau sabit zai samu zuria sosai tunda tasan shi da son ƴaƴa


Amma badia ba lallai bane ta haifawa sabit ƴaƴa dayawa, juyowa tayi ta kalle shi
sannan tace

"auta yanzu me kake so"

"ni dai kawai so nake yi dum lkcn da na kira ta tai min wani aiki bana son ta kuma
cewa wai zatai aiki wani ko kuma tana wani ya sata aiki nafi son ina bata umarni
kawai ta ɗauka"


Gyaɗa kai mummy tayi sannan ta jinjina maganar sa

"in shaa Allah zan mata faɗa akan ta dinga bin umarnin ka a matsayin ka na mijin
ta" daga nan ta shiga lallaɓa shi tare da kwantar masa da hankalin sa akan babu
wanda ya isa ya raba shi da *ASMA'UN SABIT* ɗin sa


Kanshi me ya fasu kamar an masa kyauta sai da ta kwantar masa da hankalin sa
sannan yai mata sallama ya kama hanyar sa mummy bin bayan sa tayi da kallo, lallai
sabit daga gani ka fara dawowa hanya madaidaiciya ka fara gane cewa ```ba kowacce
ƙwarya me kyau ce take da daɗin shan fura ba```



********************



Ko da muka dawo kasuwa sai mummy ta kira ni akan tana son ganina sam ban kawo
komai ba don haka na shirya na tafi pary ɗin nata


Ina shiga na zauna sannan ta fara min faɗa akan halin ko in kula da nake nunawa
mijina ```wai sabit```😏


Faɗa ta dinga min wai in dinga kula da buƙatin sa, menene da menene ni jin
maganar tata ma nake yi kamar soki burutsu tunda dai ba ɗauka zanyi ba ai ni da
sabit sai dai daga nesa amma nai masa nisa sai dai wata ba ni ma'un ba


Ta gama saki burutsun ta tsap ban tanka mata ba, sai da ta gama sannan ta sallame
ni yadda na tashi na kakkaɗe rigata haka zancen nata ya zube daga kunnuwa na sukai
ƙasa banji ba balle ince zan aiki da su
Komawa nayi hidimar gabana na tattara lamarin sa na watsa a kwandon shara,
tsakanina da shi ya kira kitchen ya faɗi abinda yake so in faɗa masa


Wani sabon salo daya ɗauko shine kullum in an gaya masa menu na gidan sai ya canza
kuma abu me wahala yake ɗauko wa sam bana jin komai haka zan dafa masa


Sai kuma ya canza salo wai innai girki in dinga kai masa nan ma nace bansan zance
ba sai da mummy tai min magana sannan na fara kaiwa part ɗin nasaa


Amma bana tashi kawai sai inna ga matar sa na nan ta yadda ba yadda za ai yai min
magana ko ya kawo min wani renin sense


Amma duk da haka ban tsira ba, idan na kai masa yai ta sani aiki kenan yi kaza
gyara kaza, zuba min abinci kwashe kaza


Haka dai amma ban taɓa tunanin sakar masa fuska ba don dana shiga ɓangaren nasa
idan na cukune fuskar nan tawa har na fito be isa ya ga sakin fuskar tawa ba balle
yace ze kawo min wani wargi


Har yanzu be isa in kula shi be kai matsayin da zan tanka masa ba, duk da dai idan
na shiga ɓangaren nasun yai ta surutu kenan ko kuma yai ta tambayar


Da me dame nayi abincin wai saboda badia ta koya, in na daddage na tsuke wannan
fuskar tawa sai dai yayi tambayar sa ya gama amma ƙala bazan ce masa ba



Sai dai in ya gaji ko badia tai masa magana sannan zai dena amma gobe bazai
daddara sai ya sake, sam wannan abun da yake yi be sani tanka masa balle inji ina
sha'awar mu'amala da shi ni asmau sai namiji wanda ya san darajar mace ba muna maza
ba
[4/26, 11:44 PM] Oum Haidar: *******************

Na ci gaba da kula da tattalin kaina ina yi wa ƙanin anty fannah tanadi,


Watan azimi ne ya kama don haka anty fannah in ta zo kitchen tun safe bata barin
shi sai mun gama abincin iftar, in itace da girki muna gama wa sai ta tafi in kuwa
ba ita baca sai mu sha ruwan mu tare


A lkcn na gano ashe macece me ibada sosai karatun qur'anin nan da azkar baya
wuce ta safe da yamma, ganin haka ya sa nima na fara mata maganar akan ta koya min
in ƙara sani sosai akan addini na tunda de Allah be sa na je islamiyya ba sosai ba



Karatu sosai muka fara da anty fannah ba ɓangaren da bama taɓowa, wasu karatun
inji kunya wasu kuma ba komai, kamar karatun ɓangardn tsarki 🙈


Ba a karatun ilimin addini ba har da na ilimin aure, wallahi wani lkcn idan tana
wani maganar sai inji kamar in nutse a ƙasa saboda tsabar kunya amma ita ko a jikin
ta kamar ba itace take faɗa ba, lallai sai a lkcn nasan cewar ni babbar jahila ce
wacce ba abinda ta iya sai girki



Lallai girki ba shine kaɗai abinda zai jawo hankalin miji zuwa ga matar sa ba har
yaji bazai iya rayuwa sai da ita akwai dabaru dayawa ko in kissa



Kamar su kissar iya magana ```wata bata da wani salo na iya yi miji magana yadda
take yi wa ƙawarta haka take yi wa aikinta shi ma miji haka, ba wani ɗan laƙwasa
harshe ko yango ko kararraiya```


Sai kissar iya zance
```wasu matan sam basu iya tauna magana kafin su faɗe ta ba haka suke suyi ta zuba
kamar ƴaƴan kanya marasa daɗi``` inji mmn farency 😜


Sai kissar iya kwalliya,kissar tafiya, yanga, rangwaɗa, shagwaɓa da kuma last but
not d list wacce muke ganin kamar tafi kowacce itace iya kwanciyar aure, ```ƴammata
ku gafarce, amma maganar gaskiya ce, duk macen da ta iya waɗannan kissosin sai dai
wani ba mijinta ba```


da kuma sauran su duk waɗannan abubuwan idan muka riƙe su gam sannan muka haɗa
da roƙon Allah day in day out in shaa Allah sai dai muji anayi rigimar aure a
maƙota ba dai gidajen mu _Allah ka bamu dacewa da ƙarshe me kyau_



Ilimi sosai take koya min kuma nake naɗewa ina ɗauka ina haddace wa burina
kawai Allah ya kaimu lkcn da zan kashe wannan auren nawa na bautaswa inyi auren
soyayya 😍




*menu of d day*


*tuwon semovita miyar egusi and kunun tsamiya*


*tuwon semo*

```ingredients```

-semo
-flour
-butter

*ki zuba ruwa a tukunya sai ki rufe, idan ya tafasa sai ki zuba wani ruwan daban a
bowl sai a dinga zuba semo ɗin ana juyawa har yayi kauri


2) daga nan sai a ɗauki talge a talga tafasash shen ruwan, idan an talga sai a
saya murfin sannan a rage masa wuta talgen ya dahu a hankali


3) idan talgen ya dahu sai ki haɗa flour da semo, kamar flour ya fi semon yawa sai
a tuƙa bayan yayi ta sai a saka butter a ƙara tuƙawa sannan a rufe a rage wuta ya
turara idan ya turaru sai a kwashe a leda


*miyar egusi*

```ingredients```

-kayan miya
-man ja
-egusi
-egg
-alayyahu
-maggi
-nama
-crayfish
-kifi


Method

1) ki saka naman ki a tukunya ki zuba maggi, albasa da tafarnuwa sannan ki rufe,
idan tafasa sai ki zuba kayan miyar ki ki barshi ya dahu


2) a wata tukunyar daban kuma sai ki zuba man jan da zakiyi miyar da shi idan yayi
zafi, sai ki wanke kifinki ki zuba a mai ki soya sannan idan ya soyu sa a tsane

3) daga gefe kuma sai ki kwaɓa egusi ɗin ki da ruwa sai ki zuba a man jan sannan
sai ki rage masa wuta yai ta dahuwa a hankali, idan ruwan ya ɗan tsotse sai ki fasa
kwan ki ki kaɗa shi sannan sai ki zuba shi akan egusin ki bar shi ya ɗan dahu
sannan ki juya idan kina son egusin ki ya dundunƙule kar ki juya shi sosai


4) sai ki juye egusin a miyar sannan ki zuba crayfish, ki ƙara maggi da albasa
sannan ki rufe, in ruwan yai kaɗan sai ki ƙara ruwan


5) idan miyar ta yi dai dai sai ki zuba alayyahun ki wanda kika yanka kika wanke
sai ki zuba kifin ki ki rage wutar sannan ki rufe


Minti ɗaya sai ki sauke


*kunun tsamiya*


*ingredients*

- ƙulun kunu
-tsamiya
-lemun tsami
-sugar
```method```

1) ki zuba ruwa sannan ki saka tsamiyar ki, idan ruwan ya tafasa sai ki tace sannan
ki ƙara mayar da ruwan don ya ƙara tafasa


2) ki zuba ƙullin kunun sannan idan yayi kauri sai ki ɗan ƙara masa ruwa daga nan
sai ki zuba a cikin ruwan zafi ki rage, idan yayi kauri sai a sauke


3) sai ki kuma ɗiban ƙullin ki sakar masa ruwa sannan ki ɗauraye kunun sannan ki
ɗan matsa lemun tsami sannan ki juye a flask



*BON APPETIT*




*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:51] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 15🌹




Yin karatu a wajen malama ta anty fannah ya sani ƙara wayewa da yanayin
zamantakewa ta ɗan adam, kasancewar garden ɗin gidan a bayan part ɗin su ga sanyi
ga iska ya sa kusan kullum a can muke karatu



Idan nagama aiki sai in je part ɗin su sai mu koma garden ɗin mu zauna muyi ta
karatun mu ko tai ta min fatawowi da dai sauran su


Har akai sallah lfy muna karatun mu kuma na ɗau alwashin ko bayan sallah zan ci
gaba da biɗar ilimina don ilimi shine hasken rayuwa, in babu shi mutum zai kasance
kamar a duhu yake Allah dai yasa mu wanye ƙalau kuma ya bamu ilimi me amfani da mu
da ƴaƴan mu amin summa amin



Rannan muna garden ɗin sai ga isma'il ya zo

"ina ta neman ki a ciki ashe kina nan" ya ƙaraso yana faɗawa anty fannah, gaishe
shi nayi sannan nayi niyyar tashi don in bar su su shana



Hana ni yayi tace shima aiki ne ya kawo shi in zauna muyi karatun mu, komawa nayi
na zauna muka ci gaba, kasancewar doguwar riga ce ƙirar dubai a jikina me belt
wacce ta saka belt ɗin na ɗaure jikina da shi sai ɗan kwalinta da nayi rolling
kaina da shi


Ya sa sam ban sake ba ni da na saba yawo a cikin hijab kamar bukka 🤣, karatun mu
muka ci gaba amma sam a nutse nake



Sallamar gogan na badia na ji a bayana inda duk muna amsa ni kuma na haɗe raina
don bana son wannan shishshige min daya ke yi



Ƙarasowa yayi ya zauna dai dai kusa da ni har jikin mu yana ɗan gogar juna wanda
hakan ne ya sa ni kuma na ɗan kuma matsawa ko ya sake amma bada ni ba, basarwa yayi
kamar be san me yi ba sannan yace


"ku ashe anan kuka yini kuna shan iska me daɗi shine sam ba a san a gayyaci mutum
ba ko" ya ƙarashe zancen sa da sigar tambaya yana kallo na



Iskar data kwaso shi ma ban shaƙa ba balle in tanka masa littafi na na ɗauko na
rufe fuska ta da shi kamar ina karatu


Anty fannah ce ta tanka masa

"yo ai ba a damu da ba, balle a san a ina muke yini" na san martani ta mai da masa
murmushi yayi sannan yace


"ai matsalar taku ce ba kwa fara'a ga shegiyar shariya ko an muku magana kun san da
ku ake amma sai ku share mutum kuyi kamar baku jiba"


"wannan shine cikar mace me aji" inji anty fannah


Su ka ci gaba da maidawa juna martani wannan ya faɗa wannan ya mayar dana ga abin
nasu ba na ƙare bane sai kawai na miƙe na sannan nace
"anty fannah naga alamar kin samu abokin hira bari ni in wuce maci gaba da karatun
nan gaba" ina gama faɗar haka nai gaba abina




Nayi nisa naji yana ƙwala min kira ban tanka masa ba haka zalika ban tsaya ba,
sai kuwa gashi ya sha gaba na

"baki ji ina kiran ki bane wai asmau me yasa kike da taurin kai ne"


"ai ban ɗauka da ni kake ba, na ɗauka badia kake son kira ka manta kace asmau"
murmushi yayi wanda yai masa kyau kamar kar ya dena


"ashe kice abin naki kishi ne, to in banda abinki ai badia alba sa ar ki bace,
yarinya kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa fara me kyan ɗaukar hankali"



Haushi ne da takaici suka cika ni tsayawa kulashin da nayi gashi nan ya ɗige da
yaɓa min magana



Raɓa wa nayi ta gefen sa na wuce

"sai kace gurin ta ni kuma ka ƙyale ni Allah zai kawi min wanda zai soni ba don
abinda nake da shi ba"



Wannan kalmar tai mutuƙar ɓata masa wanda har ya sa shi shan gaba na tare da
damkar hannun da ƙarfi wanda hakan ya sani wani radaɗi a hannun daga dukkan alamu
matse mun hannun yayi


"saboda baki da hankali da auren nawa a kanki kike maganar samun wani, to wallahi
karki ga ina ɗaga miki ƙafa ina nan a sabit ɗin da kika sanni in kika sake na kuma
jin wannan kalmar daga bakin ki sai ki yaba wa aya zaƙin ta"



Wulli yayi da ni inda na faɗi ƙasa har da gurje gwiwar ƙafa ta, kuka na saki
dama me hali yana fasa halin sa ne na faɗa, kuma wallahi abinda kake nema a wajen
nawa baza ka samu ba sai dai wata



Kuma neman rabuwa da kai ban ma fara ba sai lkcn da na tara iya kuɗin da nake so
zaka san cewar shayi ruwan na faɗa a raina tare da miƙewa ina karkaɗe kayan jikina
mugu kawai


********************


Tun daga lkcn na shiga wasn ɓuya da shi don duk abinda na san zai haɗa ni da
sabit bana ma tunkarar sa shima a nashi ɓangaren naga alamun haka


Don yawan kiran da ya ke min da yanzu ya daina sam kamar ma be fara ba,



rannan da rana na gama lunch na kaiwa mummy na tarar da ita tana ta mita, zama
nayi sannan nace

"mummy lfy kuwa"


"ina fa lfy ni da wannan har iskar kishiyar taki wai tayi tafiya amma sai da ta
sauka sannan mijinta ya sani, shi ma da yake be san ciwon kansa ba ko a jikin sa"
dariya ce ta so kubce min amma sai na dake


Kaɗan ya gani be gama ganin komai ba ba dai zalinci ya riƙe ba ai ba abinda ya
soma gani ma,

"mummy garin ƙaƙa akai haka" na tambaye ta da alamar damuwa a fuska ta


"ai da yake kin san ta riga ta shanye shi tas baya ganin laifin ta, kome tayi sai
yace ai duk abinda take yi tana sane, be san mace ba a sakar mata, kai wannan yaron
wai sai yaushe ze farka ne ya fahinci abinda nake nuna masa" ta faɗa tana dafe
kanta alamar abun yana damun ta


" ke ma hadda ke sam baki san amfanin mace ga mijinta ba, kin saki mijinki wata sai
juya miki shi take sam kin kasa jawo hankalin sa zuwa gare ki, gashi dai kinje kin
sha gyara amma sam bashi da amfani tunda duk da gyaran naki kin kasa jawo hankalin
mijinki gare ki, kullum sai dai a ganki a ɓangaren wannan yaro (isma'il) kina
bibiyar fannah amma ke mijinki ko a jikin ki



Haka kika ga fannah ta nayi wa nata mijin, wallahi har da laifin" faɗa ta shiga
min tare da ƙarawa wai duk laifi na ne na kasa shishshigewa sabit balle har in samu
fada a wajen sa ya jani jikin sa har ya banbance tsakanina da badia


Kallon baiwar Allah nan kawai na tsaya yi lallai so sone amma son kai ya fi, wato
ma lefi nane, ni bata san ko a ƙafa a ɗaura min wannan koɗaɗɗan ɗan natan ba sai na
yanke na gudu balle har a kai ga faranta masa ko shishshige masa Allah ya kyauta
min Allah ya tsare ni



Sai da ta gama faɗan ta sannan ta sallemi tare da ja min kunne akan in fara jawo
hankalin sabit zuwa gare ni,


Binta kawai nayi da to amma kuma nace hmmm wayaga wallahi badai ni asmaun ba sai
dai wata ai ni da sabit hayhata hayhata
Na koma ɗakina ina tunanin abinda mummy take son nayi wa sabit wato da yake abin
son kai ne, ni da nake mace nice za a ce inja hankalin sa me makon amatsayin sa na
namiji ace ya fara ɗaukar action ni kuma a matsayina na mace a bani damar duba wa
ko zan iya manage da shi amma sam abin ba haka yake ba nice ma zan cusa kaina
lallai mummyn nan har yanzu baki san wace asmau ba



Da yamma ina cikin yin dinner na kusa kammalawa ma sai naji call na intercom ɗin
kitchen ɗin yana ringing kasancewar ba kowa ya sani zuwa ɗauka,


"hello" naji ance ko bacci nake yi nasan muryar ɗan renin hankalin nan amma sai na
nuna ban sani ba


"hello waye" na amsa

"mijinki ne" na ji ya bada da amsa, murmushin mugunta nayi sannan na mai da masa
martani bayan na maƙe muryata na shake ta sannan na gyara ta


"kana nan ƙalau ya gidan da komai da komai wallahi ina kewar ka sosai" ina jin ɗan
murmushin daya saki sannan yace min

"da gaske"

"zan maka ƙarya ne kasan ni kasan zuciyata kasan banda wani sai ka, lkc kawai muke
jira ya kasance mu kasance waje ɗaya har abada"


Daɗine ya lulluɓe shi kamar me, ni kuwa da yake nasan abinda nake shukawa ya sani
ƙara sakin baki sai faɗa masa kalaman soyayya nake yi shi kuma yana biye min sai
can dana ga ya shiga sosai sai nace masa


"ya maidugurin kuwa, Allah dai ya san ƴam matan can basa kalle min kai dan sunga
bana kusa da kai" shiru yayi na ɗan wani lkc yai jim


"ABDUL baka jina ne" na kuma maimaitawa


"uban waye abdul" na ji ya faɗa, sai da na ɗauke phone ɗin daga kunne na na
ƙyalƙyala dariya ta sannan na mai da ta na kuma cewa

"ba abdul ɗina bane na maiduguri ba, don Allah waye ya kira ni sannan yace min
matar sa" wani ƙasurgumin zagi da luluƙo ya antayo min ni da abdul ɗin ya sani cire
phone ɗin daga kunne na na kuma ƙyaƙyacewa da dariya



"Abinda kike yi Kenan dama da auren ki to yau Allah ya tona miki asiri kuma
wallahi zaki san baki da wayo" sai da ya gama bala'in sa sannan ya kashe wayar



Dariya na ci gaba da yi gobe ma ka kuma kirana, ni abin ma dariga ya bani wai
mijin ki ne, ko ta ina ya zama mijin nawan mijin suna dai girki na na cigaba da yi
ina yi ina maimaita conversation ɗin mu ina dariya ni kaɗai lallai yau na kunna
sabit



********************


Takaicine ya ishi sabit har ya rasa yadda zai yi, tun yana kwance ya tashi ya
zauna ya kuma kwanciya amma duk da haka ya rasa mafita, ya ze yi da wannan ƴar
iskar yarinyar


Wai da auren shi akanta amma take kula wani ƙato, har da cewa lkc kawai take jira
su kasance tare, kenan da take nufin kashe auren da gaske take



Gaskiya da sake ya za ayi ma in bar ta ta tafi, lallai ma dole ne in samu
mafita, mummy ce kawai ta faɗo masa a rai, lallai mummy ce kawai zata iya kawo
ƙarshen wannan lamarin



Miƙewa yayi ya nufi ɓangaren mummy sam be nuna mata komai ba kawai sai yace mata


"mummy kinga badia bata nan part ɗin nawa ba mace don haka me zai hana ki saka
waccen yarinyar ta koma tunda akwai spare ɗaki a ƙasa sai ta zauna anan"


Daɗi ne sosai ya kama mummy har tana jin daɗi ita a tunanin ta asmau ce ta ɗau
shawarar ta ta fara aikin da ta saka ta


"to shike nan auta ai dama tun farko kai kaso hakan kana da mata har biyu amma ki
ɗige a guda gudar ma mara quality" ɓata ransa yayi shi sam har yanzu be ga aibin
badia ba da mummy kullum take cikin kushe ta



Ko ma dai menene yanzu ba lkcn maganar badia a bane yanzu ta ƴar iskar yarinyar
can ake yi



Mummy shawara ta ci gaba da bashi akan yadda zai kula da asmau da kuma yadda
asmaun zatai masa rana da kuma yadda zata kula shi fiye da badiar


Jinta kawai yake yi amma yanzu ba lkcn wannan bane yanzu burin sa kawai yaga asmau
a part

Please Login or Register in order to submit comment