You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin wurin da yake sai ta
rena masa ashe ma ƙazami ne ta faɗa a ransa



Sabit sai yamma ya dawo yadda ya ga part ɗin nasa ya canza ya sa yaji daɗi a
ransa, kitchen ɗin ya kira ya buƙaci asmau ta zo, ƙin zuwa tayi sai da ya kira
mummy ta kira ta sannan ta tashi ta shirya ta je tana shiga falon ya hauta da faɗa


"ke wai don ubanki ba biyanki nake yi ba da zan ce ki zo kiƙi zuwa har sai na kira
mummy sannan zaki zo" fuskar nan tata da kullum take a cunkushe ita ta ƙara cusheta
kamar wacce bata taɓa fara'a ba wannan abun shine yake ƙara ingiza sabit yake kuma
ƙara tsanar ta wai ace mace sam a lamarin ta ba fara'a




sai da ya gama zage ta tas sannan ya saka aiki wai ta haɗa masa dinner, cikin
kitchen ɗin ta shiga ta haɗa masa taliya me ruwa sosai ta kawo masa
yana buɗewa yana gani. abinda ta dafa ya antaya mata shi a jikin ta, wani irin
ihu ta saki inda ta fara sosa hannun ta da ƙafar ta daya ƙone




"don ubanki ance miki ina cin taliya ne kin taɓa ganina na ci taliya, tashi kije
ki kuma dafo min wani abun useless kawai"




duk dakiya irin na asmau sai da ta tsorata da lamarin sabit, ta ɗauke kayan jiki
na ɓari tayi hanyar kitchen,



tana shiga ta rushe da kuka, ita sam bata ma san me zata dafa masa ba, ga hannun
data ƙone da shi sai raɗaɗi yake mata




Jin takun shi tayi wanda hakan ya firgitar tar da ita ta ɗauki tukunya tare da
zuba ruwa tana shirin ɗorawa a kan gas,

"me zaki dafa min" ya faɗa da husky voice ɗin nan nasa


"doya da miya" ta faɗa a firgice, wani ɗan iskan kallo ya watso mata,

"kinga alamar ina cin doya ne, wai me yasa ke daƙiƙiyace, tun ɗazu nake jin yunwa
amma ki bani abinci abun ya gagara sai kace ba biyan ki nake yi, shike nan dafa min
doyar amma bana son miya ki kawo min ita haka gaya"



Abin yai mutuƙar bata mamaki amma kuma sai ta dafa masa


Tana gamawa ta juye a plate ta fita, yana zaune yana shan furar sa, ta ajiye masa

"je ki ɗauko min abin kwashe sharar can, (parker)" bata kawo komai ba ta tafi ta
ɗauko masa


Tai mamakin da taga ya juye doyar akai, sannan ya miƙe ya zare belt ɗin jikin
sa, guda ɗaya ya sakar mata tai wani tsalle ta dire sannan yace mata

"oya maza ɗauki doyar nan ki cinye ta a haka in ba haka ba wallahi yau sai dai
gawar ki" ya faɗa yana gyara belt ɗin hannun sa



Kallon doyar tayi wacce take a cikin parker idon ta na hawaye ta ɗauka ta dinga
cusawa ba miya ba ruwa haka ta dinga cusa doyar tana rawar jiki


Gashi a ƙoshe nake, gani ba masoyiyar doya ba, ga doya ba miya haka azzalimin
nan ya dinga saka ni ina ƙasimar ta ina haɗiya da kyar ga belt a hannunsa



Amai ne naji yana taho min inda na fara yunƙurin yinsa, saukar belt kawai naji a
bayana wanda ya kuma saka ni tsalle tare da haɗiye wata ƙatuwar doya wacce ban
tauna ba

"idan kika sake kika min amai sai na karya ki, daga yanzu idan na kuma buƙatar
abinci daga gare ki kika kuma kawo min abinda bana ci zaki ga abinda zan miki, da
wata fuakar ki kamar ta aljanu baƙa ƙirin" ya faɗa



Sai dana cinye doyar nan tas sannan ya saka ni dafa masa tuwon shinkafa miyar
kuɓewa ɗanya


Ba ni na gama girkin ba sai ƙarfe 02 :54am na tsakar dare duk na gaji har wani
dishi dishi naƙe gani saboda tsabar baccin da nake ji



Ina fitowa baya falon kuma ƙofar falon a kulle take da mukulli, na rasa yadda
zanyi, ɗan zama nayi a ƙasan tiles ɗin falon don injira fitowar sa har bacci ya
kwashe ni be fito



Ruwan sanyi kawai naji ana zuba min ina cikin bacci na a zaune wanda ya farkar
dani




Bayan ruwan zafin nan sai naji an take min hannu na dana ƙone wani zafi daya
ziyarce har sai dana kusa yin pitsari



Kukan azaba na saki tare da riƙe masa ƙafar daya take min hannun nawa ina roƙon
ya ɗaga min hannu na


"waya baki damar yin bacci ko an gaya miki bayi nayi bacci ne ba tare da izinin
iyayan gijin su ba" ya faɗa yana ƙara take mata hannun nata



Kuka na saki sosai tare da yiwa wannan mutumin Allah ya isa, sai da ya gaji don
kansa sannan ya ɗaga min hannun wanda naji kamar an min gafara


"kuma ki haɗa min breakfast" ya faɗa yana wucewa, kuka na saki kamar ba gobe, na
miƙe na wuce can inda nake da zama BQ kenan



Sallah na farayi sannan na fara haɗa breakfast yanzu tsoron sabit nake ji ban taɓa
tunanin akwai mutum daya iya zalinci ba kamar sabit



Sai da na haɗa breakfast aka rabo kowanne part sannan na samu nutsuwar duba ciwo
na, ya kunbura, ga raɗaɗi da azaba da yane min



Hawaye ne kawai naji suna zuba daga idona masu zafi, wai sai yaushe zan samu ƴan
cin kai ne, yaushe ne nima zan san jin daɗin a duniyar nan



Magani ma samu na saka a hannu na inda na ƙone da ƙafata, sannan na samu na
kwanta, ban daɗe da bacci ba naji call ɗin intercom ɗin kitchen


Kasancewar bani kaɗai bace yasa na share kawai, ganin sai ringing take tayi ba a
ɗauka ba ya sani miƙewa na je na ɗauko, sabit ne jin muryar shi sai daya sa
zuciyata bugawa


"ina asmau" ya tambaya da muryar nan tasa me rikita min ƴaƴan hanji

"nice" na faɗa jiki na a sanyaye

"na fahimci har yanzu baki yi hankali ba, iskancin da ke kanki har yanzu be ragu ba
kizo part ɗina ina jiran ki yanzu kika ɓata min lkc zaki san sauran"


Katse wayar yayi kafin in masa complain ɗin hannun nawa, hannun nawa na kuma dubawa
yadda yake shirin chaɓewa inban yi hankali ba



Hijabi na kawai na ɗauka nayi part ɗin nasan ina takaicin wannan rayuwa, ina
shiga yana ,zaune shida sahibar tasan suna kallo



Da sallamata na shiga sallamar da ba wanda ya amsa min kamar ba musulmai ba

"shiga kitchen kiyi mana abinci" ya faɗa ba tare da ya kalli inda nake ba


"hannuna ciwo yake, ƙonewa nayi in ban kula da shi ba sai ya fara ruwa"


"Muga hannun" ya faɗa kamar gaske, nuna masa nayi sai ya miƙe ya shiga kitchen
sai gashi da wata baƙar leda


"nannaɗe hannun ki da wannan ledar sai kiyi mana girkin bana son cin ƙazantar ki"
ya faɗa saboda tsabar mugunta



Hawaye ne ya fara zubar min na karɓi ledar zan fara ƙullawa a hannuna sai naji
badia tace


" gaskiya *SD* bazan iya cin abincin da yarinyar nan tayi ba yama nake cin abincin
ta balle kuma da wannan jagwalon a hannun ta" ta faɗa fuska a yatsune, sallamat
sukai inda nai ta wa Allah godiya don ina da tabbacin idan na cigaba da girki akai
akai ciwon zai iya kuma chaɓewa




Ina fita daga nan part ɗin mummy na nufa na gaya duk abinda ya haɗa mu da shi,
kallo na tayi sannan tace


"to in banda abin asmau ai *AURE BAUTA* ne, duk abinda kika ga ya faru a cikin
aure ki tabbatar yana daga cikin ƙaddarar ki sannan bauta kike yi kije kiyi ta
haƙuri har Allah ya kaimu lkcn da badia zata gama koyon girkin ta sai a raba ku
amma yanzu biyayya shine naki"


Wani baƙin ciki ne ya zo ya maƙale min a ƙirjina wato *AUREN BAUTA* ke nan nake
yi, na zama baiwa kenan, na yadda duk *AURE BAUTA* ne amma ba irin wannan bautar ba



Ganin bani da wata mafita yasani tafiya ɗakina na kwanta ina me roƙon Allah ya
saka min da gaggawa



******************


Bikin isma'il ne ya taso inda zai yi aure a maiduguri ta uku ce, sai shirye
shiryen tafiya suke yi harda mummy balle kuma ƴan uwan sa


Buri na da fatana ace sabit ya bar gidan don yanzu wata baiwar ba tafi ni ƴanci
indai aka ce sabit yana gidan, mugunta kala kala yake gwada min kamar wani mara
imani


Banda wahalar gyaran part ɗinsa da ya zame min tilas kullum don matar sa tana da
ciki mtssss



Ranar friday da yamma suka shirya domin zuwa maiduguri biki inda shi angon ya
rigasu tafiya tin da safe, wannan uban rigimar ina kitchen yasa aka kira ni sai
dana bushi iska sannan nazo



Abinda ke haɗa mu da sabit kenan ya fi san daya kira ni in zo ni kuma gani da
shegen taurin kai, kusan kullum da muguntar da zai gwadamin amma gobe bazan daddara
ba


Ina shiga sai da sha ruwan takalmin sa ya doddoke ni da takalmin sa ni kuma na
bishi da Allah ya isa a zuciyata



sannan ya sani gyaran kayansa sai kace wata matar sa ooops na manta ashe da aure
tsakanin mu ko, sai da na gama haɗa masa kayan sa sannan ya sani fitar masa da
akwatin


Kinkimar akwatin nayi na fita ina ja da ƙyar, a ƙofar get ɗin gidan naci karo da
daddy har ƙasa na durƙusa

"daddy ina kwana" sai daya kalle ni ya gama ƙare min kallo sannan yace

"kar dai matar sabit ce wannan" ya faɗa yana nuna ni, mummy da ke gefe ta murmusa
sannan tace

"itace asmau kenan ƴar baiwa" murmushi yayi yana gyaɗa kansa irin nasu na manya, a
wannan lkcn sabit ya ƙaraso

"sabit kasa matar ka ta haɗa kayanta sai muyi tafiyar da ita tunda a hotel zamu
sauka kaga itama taga gari" sam ban kawo da ni ake ba shima sabit ɗin sam be kawo
ni ba ya ɗauka badia don haka sai yace


"daddy ai bata jin daɗi kuma dr. yace ta daina nisa da gida" kallona daddyn yayi
sannan yace

"asmau me ya same ki" ɗagowa nayi na kuma kallon sa sannan na girgiza kai alamar ba
komai, kallon sabit yayi sannan yace

"kace bata da lfy" sai a lkcn na gane wai dani da yake shima sabit ɗin sai a lkcn
ya gane


"a a daddy ba sai naje ba anty badia bata da lfy ni nake kula da ita" na ƙarashe
zancen


"zancen banza kenan kishiyar ki zaki kula da ita ko mijinki, maza kije ki haɗo
kayanki muna jiran ki"


Kallon sabit nayi wanda ya haɗe ransa kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa
sannan na duƙar da kaina mummy ce naji tace

"muje in taya ki haɗa kayan nakin" ƙafafu wana a sage na ja su sannan na bi bayan
mummy a zuciyata bace dady ka ba sabit license ɗin cin ƙwal ubana




*menu of d day*
*yam balls, potato pancake, fish cake*


*yam balls*

*ingredients*
-yam (doya me gari tafi daɗi akan me danƙo)
-eggs (dafaffe da ɗanye)
-attaruhu
-danbun nama ko kifi
-albasa
-curry
-maggi
-garin bushash shen burodi


*method*

1) ki fere doyar ki sai ki ɗora ta a wuta ki bi ta da sugar da gishi, sugan ya
ninka gishirin yawa

2) bayan doya ta dahu sai ki sauke ta ta huce, ki ɗauko wankekken turmin ki ki zuba
albasa da attaruhu ki jajjaga sai ki kwashe a roba


3) ki zuba doyar itama ki daka ta ba kirɓawa ba ki farfasa tasai ki sauke ki haɗe
da kayan attaruhun

4) ki zuba maggi da curry danbun ki sai yanka ƙwai ƙanana a ciki ki ƙara sai ki
duddun ƙula kamar ball 😁 Kamar fuskar na

5) ki zuba mai a kasko ki dan saka albasa sannan ki barshi ya huce, ki fasa ƙwai a
roba ki zuba maggi da albasa isashshe sannan ki kaɗa


6) ki dinga ɗaukar ƙwallon doyar kina sakawa a garin burodin kina tsomawa a ruwan
ƙwai sannan ki soya har sai yayi brown sai a kwashe a barshi ya tsane



*potato pancake*

*ingredient*




-dankali
-albasa
-attaruhu
-maggi
- mai

*method*

1) ki fere dankalin turawan ki sannan ki gurza shi, itama albasar ki gurzata
2) ki jajjaga attaruhunki sannan sai ki haɗe da dankalin da albasa sai ki saka
maggi, idan yayi ruwa dayawa sai ki ɗan ɗaure da flour, (ni dai nafi amfani da
potato flour)


3) ki zuba mai a kasko idan yayi zafi sai ki zuba kullin dankalin ki ki soya idan
ɓangare ɗaya yayi brown sai ki juga ɗayan idan ya soyu sai ki sauke


*fish cake*

*ingredients*

-kifi (kowane iri ne)
-shrimps
-squid
-attaruhu
-albasa
-maggi
-mai
-flour da corn flour


*method*
1) ki gyara kifinki ki cire ƙaya in me ƙayar ne, ki gyara shrimps da squid sannan
ki saka su a food precessor ɗin ki, ki haɗa da albasa, attaruhu, corn flour da
flour sai ɗan mai kaɗan sai ki rufe ki kunna

2) idan baki da food processor, sai kiyi blending kifin da shrimps da squid, albasa
attaruhu ɗin sai ki juye a roba sannan ki haɗa kayan flouɗ ɗin da maggi da ɗan mai


3) in babu blender sai ki tafasa su sannan ki daka su kafin ki haɗe da kayan flour
ɗin

4) kaɗan zaki saka flouɗ ɗin yadda dai kwaɓin zai ɗinga danƙo a hannu bi ma'ana ya
dinga kama hannu ba da tauri ba


6) bayan kin gama haɗa komai sai ki zuba mai a kasko sannan ki dinga ɗiba kina
sakawa a cikin man kina soyawa har ya soyu sai ki kwashe


*BON APPETIT*


*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*ina masu cikin mu 🤰🏻🤰🏻da mmn .....reeda da real me ........... Ban kama suna
ba 🤣🤣🤣 duk ina muku fatan sauka lfy*



Page 11🌹



Part ɗin mummy muka je itace ta bani ƴar ƙaramar jaka, sannan na wuce ɗakina,
kayana na haɗa sannan na fito zuciya ta sai dukan uku uku take na san akwai rikici
tsakanin mu da sabit



Motar da mummy take ciki nan na shiga kusa da mummy na zauna na tsuke fuska
don kar ace in fita in koma motar da sabit yake, ilai kuwa sai sulaiman wansa yace

"asmau ki fito ki zauna kusa da mijinki don daddy ne ze zauna" kau da fuska ta nayi
kamar banji ba har daddyn y ƙarasa sai yace

"ke me kike yi anan ga mijinki can ya shiga waccen motar maza wuce kije wajen
mijinki ni ma ki barni da matata" kunya ce ta kamani na tashi na fita daga motar na
wuce motar da sabit yake zaune


Shi kaɗai ne a bayan motar, rasa ina zan shiga yayi, gaban motar zan shiga ko
bayan motar,

"bazaki shigo bane ko so kike a zauna ai ta jiranki gimbiya" sabit ya faɗa cike da
takaici, kusa da shi na shiga na zauna inda ya matsa can ƙarshen sai kace wacce zan
goga masa cuta



Muka fara tafiya, har muka je airport ba wanda ya tanka wani, muna sauka na gudu
wajen mummy ni wallahi yanzu sabit tsoro yake bani




Private jet ɗin daddy zamu shiga don haka babu wani ɓata lkc ko duba passport,
muka hau, ina shiga na fara dibi dibin gurin zama, muryar daddy naji yace

"sabit kama hannun matar ka ka zaunar da ita kusa da kai naga kamar first flight
ɗin ta ne"


Jinayi cikina yai ƙululu ban ankara ba naji ta damƙi hannu na, tare da matse min
shi yacca har ƴar ƙara na saki


Sakin ƙarar ne ya shi take min ƙafa wanda zafin takalmin nan nashi kamar na ƙarfe
ya shige ni kamar an ɗaura min dutse a kafar



Toshe baki na nayi inda wasu hawayen azaba suka fara sauka daga cikin idona, jaa
na yayi ya zaunar dani a kan kujera sannan ya fara kiciniyar saka set belt ɗin sa



Har lkcn ban dawo daga duniyar zafin takanin da yayi ba don haka sam ban ma san
ana saka wani belt ba


Sai da mummy tace "sabit asmau kuwa ta saka set belt" sannan na lura da cewar
ana sakawa


Yunƙurowa yayi jikina domin ɗauko set belt ɗin inda ya saka gwiwar hannun sa a kan
cinya ta tare da danna na gwiwar sa


Cinyar tawa kamar zata tsage don azaba haka naji wani irin kuka na saki wanda
hakan ya janyo da hankalin duk wani wanda yakd cikin jirgin


Daddy ne ya fara tambayar lfy, kafin in bude baki ba tuni sabit ya yi magana

"daddy wai tsoron flying take ji" sakin baki nayi ina kallon babban mutum da ƙarya

"karki damu asmau ga mijinki a kusa da ke ba abinda zai same ki, kai kuma ka
lallashe ta" daddy ya faɗa cike da kulawa sannan ya juya


Kukana na cigaba tare da yi masa Allah ya isa, mintsini na kuma ji ya mannara
min cizo sosa wurin na kuma yi tare da ƙara furta kalmar Allah ya isa da ƙarfi
Ƙwafa yayi sannan yace

"zaki gane kuren ki idan mun sauka zaki san baki wayo"


A haka flight ɗin ya tashi, don tsoro gaskiya na tsorata amma sai na dake don
bana son wannan ɗan rainin sence ɗin ya samu damar ta


Lfy ƙalau muka sauka a maid. daga nan motoci suka kuma zuwa ɗaukar mu wannan
karan da sauri na shiga kusa da mummy sannan na kyafe, ko da daddy ya zo sai be ce
infita ba sai kawai ya shige gaban motar har yana tsokana ta wai yaga nafi sabawa
da mummy akan sabit, murmushi kawai nayi na jin kunya



A wani hotel muka sauka inda bayan an kai mu ɗakunan da muka kama, nayi mamaki
ko ince nai takaicin da aka ce wai ɗaki ɗaya zamu ɗauka da sabit g
Ai nasan cewar na kaɗe daga ni har ganye na, Muka shiga ɗakin yana ɗan girma
sosai, muna shiga ya faɗa banɗaki, ni kuma na samu wuri na ajiye jaka ta sannan na
ɗan rakuɓe na zauna, bai daɗe ba ya fito da towel a jikin sa daga gani wanka yayi



"oya maza tashi ki shiga toilet ɗin nan ki zauna a ciki ko kina tunanin tare
zamu zauna a nan ɗaki da ke, ai rayuwar banɗaki zakiyi"


Sam ban fahimci abinda yake nufi ba sai dana ga ya hankaɗa ni cikin toilet ni da
jakar tawa sannan na fahimci ashe a toilet yake nufin zan zauna yau naga ta kaina
Kan toilet sit ɗin na koma na zauna na zuba uban tagumi ina kallon ikon Allah, rasa
yadda zanyi nayi, ƙarewa toilet ɗin kallo nayi yana da ɗan girma ba laifi,


Bath ne babba sai sink sai toilet sit, sai ɗan space haka


Zama nayi na zuba tagumi da na gaji da zaman sai na ɗauro alwala, na fito duk
dai jarabarsa ai baze ce in sallah a toilet ba ko Yana yana gaban laptop ɗin sa
yana ta danne
Ƙarasowa nayi ɗakin sannan na tsaya ina tunanin ina ne gabas, ɗago kai yayi yana
kallo na inda ni kuma nayi kamar ban ma san yana yi ba

"uban me ya fito da ke bana ce ki zauna a toilet ba" ya faɗa fuskar nan tasa a
murtuke

"naga alamar kina son zama kusa da namiji Allah dai yasa ba kin saba bin su bane
shiya duk inda nayi kina biye da ni, inda wata macen ce me kunya yadda ta ganni
daga ni sai gajeren wando ai kunya zata ji amma ke ko a jikin ki"


Kallon shi kawai nayi wani takaici ya rufe ni

"sallah zanyi ko itama sallah inyi ta a banɗaki ne" na faɗa kaina tsaye

"ni na isa ince kiyi sallah a toilet kije can kiyi amma kina idar wa ki koma toilet
don bazan iya zaman ɗaki ɗaya da ke ba, naga ke kina son mood ɗin na ganin mu tare
amma ni ko a ƙafa aka ɗaura min sai na yanke na gudu" ya faɗa yana maida kai tare
da ci gaba da abinda yake yi



Zuwa nayi inda ya shinfida sallaya na tada sallah, sai da na idar sannan na miƙe
na koma toilet, yunwa ce kawai take cina ina zaune akan toilet sit ɗin sai naji an
buɗe ƙofar


Wata leda ya wullo min ɗaukar ledar nayi na buɗe, kaza ce a ciki da yoghurt,
kasancewar toilet ɗin ba wani ƙazanta a ciki ga kuma yunwa ya sani buɗewa na fara
ci



Sai da naci na ƙoshi sannan nai brush zani na na ɗauko na shiga bath ɗin na
shimfiɗa da niyyar kwanciya sai naji ya hankaɗo kofar
Maza fice min da gani zanyi fitsari inyi alwala in kwanta, shiru nayi kamar bacci
nake yi, shima sai ya ɗauka da gasken baccin nake yi don haka sai ya saki jiki ya
fara fitsarin sa


Sai da naji ya fara yi sannan na tashi zinbir zanyi waje, a guje ya nemi ƴar
kaciyar tasa ya mayar wando be gama fitsarin ba ni kuma nai waje da gudu


Sai daya gama sannan ya fito

"meye na fitowa da gudu bayan kin saba gani, nawa ne dai sai dai kiyi fata amma
yafi ƙarfin ki"


Ni dai ban kula shi na raɓe shi na shige naje na shiga cikin bath ɗin na kwanta,
wayyo Allah kamar ina kwance akan ƙashi juyi nake amma bacci yaƙi zuwa



Can na kasa bacci sai na tashi na fito daga toilet ɗin, ɗakin ya ɗau sanyi
sannan an kashe fitilar lallaɓawa nayi naje kan gadon na kwanta sannan na rakuɓe
ƙarshen gadon don kar in tada shi



Ban daɗe da kwanciyi ba bacci ya kwashe ni,



Kiran sallah naji sai na ƙara juyi tare da ƙara duƙunƙune wa saboda sanyin da
ake yi, sannan na kuma komawa bacci na me daɗi na sakankance ina bacci kawai naji
an haɗaka ni na faɗo ƙasa tim


A guje na tashi inda shima ya biyo ni ze dake ni, toilet na faɗa na saka key na
kulle, dukan ƙofar a ya shiga yi yana cewa in buɗe



Kin buɗewa nayi, har ya gaji ya dena nasan duk wanda ɗakinsa yake kusa da namu
yaji don yadda yake bugun, a zuciyata nace mugu ai na waye na daina barin ka kayi
min mugunta



Can aka fara kiran assalatu, nan ma yazo ya fara bugun in buɗe masa zai yi alwala
a zuciyata nace sai dai karkayi sallah, sai daya gaji da bugun sannan ta tafi



Jin buɗe ƙofar ɗakin ya sani ni ma na buɗe toilet, sai da na gama fitowa sannan
mukai ido huɗu da shi ashe be fita, na juya zan koma ya damƙo ni,


Tsalle na dinga yi ina ihu ai na waye yanzu wallahi sabit bazan kuma bari ka
kuma duka na ba, tsaya wa yayi yana kallo na yadda na daddage sai tsalle nake yi
Belt naga ya ɗakko wanda hakan ne ya sani na ƙara ƙwala ihu wanda ban daɗe da
kwalawa ba sai ga knocking a ƙofar mu, shi yaje ya buɗe



Mummy ce ina jin tana tambayar lfy da yake bashi da kunya sai yace


"mummy ba komai kawai faɗa tsakanin mata da miji, daɗi ne yake sata wannan ihun
amma in shaa Allah baza ta kuma ba"


Sam be bari ta shigo ba balle in gaya mata Itama mummy da yake ta iya ɗaurewa
ƙarya .......🤭 sai ta juya ta tafi, dawowa yayi na ɗauka wajena zai yo har ina
shirin wage baki 😱 sai gana yayi hanyar toilet


Alwala yaje yayo sannan ya fito yai sallah asuba lkcn gari har ya fara wayewa a
zuciyata nace ba lada, yana idar wa ya tasa ƙeyata na koma toilet sannan yaja ƙofar
wai ni a toilet zan dauwama ne


Ina zaune bacci ya fara ɗauka ta, sai na fara gyangyaɗi a kam toilet sit ɗin,
ƙarar buɗe ƙofar naji wanda hakan ya tabbatar min da shi don haka sai na tashi


Harara ya doka min sannan yace

"maza tashi ki fice wanka zanyi" sim sim sim na fice na bar masa toilet ɗin, ina
fitowa naci karo da breakfast an kawo, daga dukkan alamu ya ci


Kallo ɗaya nayi wa abincin na ɗauke kai ba a bani ba duk da dai nasan hadda ni
aka siyo amma ba a bani ba bazan ci

Please Login or Register in order to submit comment