You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mejegon"


Tsuru tsuru sukai, nidai tunda naga na haɗa su sai nai ficewa ta na barsu


Ɗakin nawa naji an turo ƙofar, ashe mummy ce ta shigo, sai da ta ƙaraso da sannan
na bata wurin zama


"har yanzu sabit ɗin basu dawo bane ko dai wani abun ne ya samu badiar"


Ni dai ban tanka mata ba saboda sam ban san ma ina ta dosa ba,


"ni wallahi duk a gajiye nake, nace musu su shirya gobee mu koma abuja ai suna
acen dama dalilin zuwa na kenan"


Ni dam ban tanka mata ba don kuwa a gaskiya na fara kewar ɗana, don haka sai nai
mata shiru,


Mara ta naji ta fara murɗa min, mitsss sai yanzu na tuna sam ban ma sha magani
ba, miƙewa nayi don in ɗauko magani sai naji mummy tana cewa


"asmau lfy naga kina tafiya kamar kece kika haihun, gashi kuma duk kin ɓata zanin
jikin ki"


Juyawa nayi don inga inda na ɓata ban ɗago ba sai ganin mata nayi kusa da ni


"asmau ke kika haihu ko badia"

Tsare ta nayi da idona wanda a yanzu suka ciko da hawaye, ɗago min fuskar tawa
tayi


"asmau ke kika haihu, ba badia ba" gyaɗa kaina nayi hawaye yana zuba a ido na


"haba biri yayi kama da mutum" inji mummy takaici ne ya kamata sai ta kama hanyar
fita



Ban san me tace musu ba sai gata da babyn,

"ungo shi bashi nono ya sha ki gama in gyara ki, wallahi idan sabit ya dawo yau sai
yaga ɓacin raina wanna wane irin zalinci ne"



Karɓar babyn nawa nayi na rungume shi sannan na zauna na fara bashi nono kamar
dama yunwa yake ji haka ya karɓa ya fara tsotsa



Muryar badia muka ji a bakin ƙofa tana masifa


"ban gane ɗan ta bane yaushe ya zama ɗanta don kawai ta rene shi a cikin ta sai ace
ɗan ta wallahi bazai sha nonon ta ba, na riga na gama booking nurse ɗin da zata
dinga kular min da yaro" ta faɗa tana shigowa a fusace da zummar karɓar mummy



Mummy ce tace

"wallahi kika sake kika katse masa wallahi tallahi sai na saɓa miki"


"mummy ya za ayi jini na ya sha nonon ta"


"ya akai ya zama jininki"


Nan badia ta kwashe komai ta faɗa wa mummy, bata gama ba mummy ta fashe da kuka,
adai dai lkcn sabit ya shigo
Ingiza badia yayi ya kora daga ɗakin, mummy kuwa kuka ta dingayi,ba irin lallashin
da sabit be mata ba amma taƙi shiru


Shima sai ya fashe mata da kuka

"anya sabit kana tuna ranar da Allah zai kama ka kuwa akan haqqin yarinyar nan,
tunda Allah ya haɗa ku kake zalintar ta, anya kana da tausayi kuwa"


"mummy don Allah kiyi haƙuri wallahi sai da ta amince muka biya ta sannan akai
mata dashen"


"wannan yarinyar me ta sani, da har zaku ce wani kun biya ta yanzu ɗan na wane na
wacce tai dakon cikin ne ko na ƴar lelen taka ne"


"mummy ƙwan badia ne"

"mummy ba nawa bane" na bata amsa

"amma ni alfarma ɗaya nake so a barni in kula da shi in dinga bashi nono in yaso
idan na yaye shi sai badia ta karɓi abinta"


Kallona mummy tayi sannan tace

"asmau ke yarinya ce har yanzu baki san ciwon kanki ba nan gaba zaki zo kiyi dana
sani"


"mummy duk yadda Allah ya tsara bawa rayuwarsa haka zai yi ta" na bata amsa
Nai ta mata daɗin baki akan maganar don bana son a jata da tsaho, ta yi mugun
jinjina min sannan daga ƙarshe ta saka aka kira badiar sannan ta kuma kafa sharaɗin
ni zan kula da babyn



Sam badia bata damu ba, shima sabit ɗin sai ya nuna ya fi son hakan,


Mummy itace ta dinga kula dani, ko da lkcn suna yayi a can wani hotel sukai sunan
su, daga ni har mummy ba wanda ya je



Amma ita da sabit da babyn sun sha hotuna kamar ba gobe, wallahi duk wannan abin
da ake yi ko kaɗan a jikina be taɓa damuna ba sdon nasan akwai ranar ƙin dillance


yaro ya ci sunan bbm badia amma anace masa annur mummy tai faɗa sosai wai ai sunan
daddy ya kamata a saka amma sam ba ai mara kara ba


Kaji mummy wani ɗigimi
********************

*BAYAN SHEKARA ƊAYA*




kamannin annur da sabit ya gama fitowa, sosai ga wayau kuma Sam baya yadda da
badia, shegiyar ƙyuya gare shi kamar


Daga ni sai ni, ko sabit in dai ba fita yaga zai yi da shi ba sam baya yadda ya
ɗauke shi


Sam badia bata damu ba, ita dai kawai burin ta taga an masa wanka an masa
kwalliya tai ta ɗaukar shi a hoto ta na ɗora shi a dp, facebook da instag.


Shima haka sabit ɗin yake sai dai in ban masa wanka ya ɗau gyara ba, nan zaku ga
da sabit ɗin da badiar duk suna rige rigen ɗaukar a pic


Sam wai nuna so ko jan yaron a jiki badia bata san wannan ba, ko tashi yayi da safe
ya tafi ɗakin ta sai dak kawai kaji tana ƙwala min kiran in zo in dauke shi in masa
wanka



Sam bata yadda ta ɗauke shi sai an masa wanka, wai ko yayi pupu ko fitsari sai
dai kaji tana kirana inzo in cire masa



Wani rashin *M* ɗin ma sai in yayi pupu a ƙasa kamar ta dake shi haka take, akwai
randa mukai faɗa da ita akan shi,



Ya shiga ɗakin ta ba diaper a jikin sa, sai yai mata pupu a kan gado, kawai
zagin shi naji tana yi


Da gudu na tafi ɗakin ta ɗaga hannu zata dake shi, da sauri naje na tare masa,


"haba anty yaro ne"
Harara ta bini da shi sannan tace

"ni ƙazanta ta yara ce bana so, zo ki kwashe kashin nan kije kiyi masa wanka"


Tabbas ba ta san ciwon sa bane don wallahi da ta san ciwon sa da uwa tana cikin
cin abincin ta ɗan ta zai yi pupu ta saki abinci ta wanke masa sannan ta zo ta
ƙarasa
Ita dai bangaren kayan sawa, kayan wasa, anan fa to kusan Rabin albashinta yaron
take kashe mawa,



Sai dai jawo shi ajiki ne dai batayi


Ana haka wani zazzabi ya kama shi aiko sai ya kasance ni kaɗai yake yarda in
dauke shi, hatta da sabit baya yarda da shi




Anan ne wani sabon rashin mutunci ya tasowa badia inda tace ita Sam atafau ayaye
yaro abata ɗanta, saboda gaskiya ita bata yadda ba tana uwar yaro amma sam be shaƙu
da ita ba



A zuciyata nace me kike masa da zai sa shakuwa da ke, don kayan wasan da kike sai
masa sani yayi shi yaro


Tuburewa nayi nace sam be isa yaye ba sai ya ƙara watanni, abi kamar wasa har
sabit ya saka baki shima sai ya goyi bayan badia wai shima baya jin daɗin yadda
annur ɗin yake masa



Ban musa ba ganin bana son sa'insa akan shi ya sa na miƙa mata shi nasan ko kukan
sa na dare ya sata dole ta dawo min da shi



Ai kuwa tana karɓar sa daya tsanyare da wani kukan ko a jikinta ni kuwa wannan
kukan jin sa nayi kamar ana yankan sa har cikin zuciyata naji



Ɗakina na shike ina jin sa yana cewa ```maaa``` da yake haka yake cemin don bakin
sa ba wani buɗewa yayi ba



Aiko ko awa daya batayi da daukan shi ba naji ana ƙwallamin kira a ruɗe na fito
inda naga yaro shame shame ahannun sabit kamar marar rai


Ruwa ne a hannun badia tana shirin sheƙa masa na karɓa a hankali na yayyafa masa
yana farfaɗowa ya fara ```maaa``` ```maaa```



"na'am baby na" na amsa masa ɗagowa yayi ya kalle ni, duk da dai jikin sa ba ƙwari
amma a hakan ya ɗago ya taho wajena da saurin sa ya rungume ni



Sosai na matse ɗana a jikina sai ajiyar zuciya yake saki, wanda hakan ya sa
zuciyata ta karye naji hawaye ya cika min ido na



Bani ba hatta sabit sai da jikinshi yayi sanyi ni ko hawaye suke sulalo min ganin
yadda yaron cikin ɗan lokaci kadan ya fita hayyacin shi amma da ganina yawani lafe
ajikina harda ƙara rungumeni


Bacci ne ya kwashe shi a kafaɗa ta ina ɗan jijjigashi ko da yai baccin sai na
sauke musu shi


"zo ki ɗauke shi" inji sabit


"ya ci gaba da zama a wajen ki har sai ya saba da badiar sai ya koma, ke kuma dia
ya kamata ki dinga samun time kina spending da shi mana don ya saba da ke kooo" ya
faɗa da sigar lallashi


"ok shike nan zan duba"


Wuce wa nai da shi ɗakina muka kwanta, kallon shi nayi sannan nace

"annur ɗana ina alfahari da kai, kuma wallahi da kai sai na nuna wa duniya cewa ni
asmau ƴar halak ce"



********************


Tun daga lkcn badia take shigowa ɗakina wai don annur ya fara sabawa da ita, amma
ko ta shigo tana manne da wayar ta tana chatting shi kuma daya ganta to ahike nan
ya liƙe min kenan har sai ta fita



Sam wannan method ɗin be yi ba haka naji tana faɗawa sabit, sai suka tsiri fita
da shi yawo, kunsan yaro da son yawo, wannan ne ma sa ya ke ɗan yadda ta ɗauke shi
in dai har ya ganta da mayafi ko hijab amma da ta zauna shikenan sai ya fara
```maaam``` yana kuka



*******************
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛
~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 23🌹




Da azimi ne muka shirya muka kama hanyar abuja don muyi sallah acan a lkcn annur
yana da wata 18 yayi wayo sosai


Kuma kullum kamar sa da sabit ƙara tatsowa take yi, ita kanta badiar tana koka wa
duk da dai wani lkcn takance ya ɗauko farin ta


Nakan yi dariya kawai in basar, tun da muka dawo naji canjin ruwa sai na gara
laulayi, ada ban ɗauka da gasken ciki gare ni ba sai da muka dawo abuja


Jakar ubacan zamu ga yadda za ayi da sabit da wannan cikin wallahi bazan taɓa
yadda ya kuma zubar min ba


Tsab muka koma muka ɗinke da anty fannah har tana min maganar wai na liƙe wa
annur bayan uwar sa ƙiri ƙiri take nuna wa bata son mu'amalar mu da ɗanta


Nakan yi murmushi nace ai ba dan ita nake yi saboda yaron make yi, satin mu ɗaya
da dawo ta ƙwace annur daga hannuna wai ya isa yaye


A lkcn gaskiya nima na so yaye shi saboda ga ciki abun yana min yawa, gidan su
takai shi, batare da sanin sabit ba


Ko da ya dawo daga yawon sa ya tarar an kai masa ɗa gidan su ranar sai da sukai
ɗan ƙaramin yaƙi da shi
Ina jin su

"wallahi baza ka hanani kai ɗana gidan mu ba, don ba kai kadai kake da iko da shi
ma nima uwar sa ina da shi"


" ta ina kike uwar sa abinda sam baki san komai nashi ba, ki bar wacce take
ɗawainiya da shi tai magana mana" inji sabit


Ai kuwa badia sai kuka wai sabit yai mata gorin ba daga jikin ta annur ya fito
ba, kuka ta dinga yi wiwi wai Allah ya haɗa ta da mijin da bai san ƙaddara ba


Ƙofata na ja na ƙara rufe wa can ta matse muku ina jin shi yana lallashin ta a
zuciya nace an dai faɗi ba nauyi



Ranar da daddare ya shigo ɗakina da ƴaɗ fara'ar sa, ina zaune ina ta shan
mangwaro na ko ƙarasa nuna ma be yi har wani ɗan tsami tsami yake yi amma ni a
hakan nake son sa


"na lallaɓa wannan rigimammiyar ta kwanta sauran ke"


Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ni


"shan mangwaro cikin dare" ya tambaya, murmushi nayi sannan nace

"ai annur ya kusa ƙani ko ƙanwa" wato ko gabaɗaya tuni wani fara'a da annushuwar da
ke tattare da shi kau


"ban gane ba me kike nufi" ya faɗa, ban ɗauka zai ɗau abinda zafi ba sai nace
masa


"ciki gare ni kusan 2mnths"

" *WAT* * ya faɗa da manyan harufa,

"ina turaren da na baki kina sakawa kuwa"


"wane turare"

"turaren mana dana baki"


Sai yanzu na tuno ya kuma bani turare bayan na haihu, da farko turare ya ɓata
lkcn da nake da cikin annur amma ina haihuwa sai ga turare ya dawo


Ko kaɗan ban kawo komai ba, zaman mummy a gidan ta nai min biƙi ya sani bata da
ta tashi tafiya, sabida gaskiya turaren ba dai ƙamshi ba


Da ƙyar ma ta karɓa sai dana matsa mata,


"me turaren yayi"

"tambayar ki nake yi kina amfani da shi ko bakyayi" to kuma zancen sa ya fara bani
tsoro


Muye kuma na zancen turare daga samun ciki,

"na bawa mummy" a zabure ya miƙe


"wace mummyn" kallon shi kawai nayi yanzu kuma wallahi na fara tsorata, a fusace ya
fice


Ko ma dai menene a cikin turaren wannan shina abinda ake cewa ramin mungunta



Mummy tana bacci sabit ya dinga buga musu ƙofa, da ƙyar ta tashi ta buɗe masa


"lfy auta" ta tambaye shi

"mummy ina turaren da asmau ta baki a lagos"

"amma auta maganar turare shine baza a yi shi ba sai yanzu cikin dare"

"mummy don Allah kice bakiyi anfani da shi ba" tsayawa tayi tana kallon sa


"wani abun ka saka a turaren ka bata ni kuma bata sani ba ta bani" rasa bakin
magana yayi kawai sai ya shige cikin ɗakin ta


Turaren yananan kan mirrow ɗin ta ɗauke wa kawai yayi yai ficewar sa, bin sa tayi
da kallo sabit zan ga ranar da zaka dawo hanya madaidaiciya


Ɗakina ya dawo a lkcn na gama shan mangwaro na har nayi shirin kwanciya don sam
ban ɗauka zai dawo ba


"ke kuma na dawo gare ki, wannan cikin ban san da shi ba kuma bana son shi yanzu,
nawa annur ɗin yake don haɗama har kin kuma samun wani cikin to ban yadda ba, nine
me gidan kuma idan lkcn da ya kamata ki kuma haihuwa yayi zan faɗa miki, a kuma
ɗaukar ƙwan badia a kuma dasa miki"



Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tunkaro ni, lallai ma sabit ɗin nan wato ya mayar da
ni baby making machine ɗin sa ko
To wallahi baza ta saɓu ba, ya ɗauka zan masa lakwa lakwa kamar yadda nake masa
ada sai ya ga ma buɗe masa wuta nima



Ai ma koya a wajen badia naga alamar sabit zuma ne sai anci da wuta ake zaman lfy
da shi,


Faɗa daya ga inayi masa nr ya sashi saukowa

"asmau ba wai bana son ki haihu bane, amma kinga kamar yadda annur yake haka nakr
son ƴaƴana su kasance bana son ƴaƴana kiga wasu farare wasi baƙaƙe"


"wannan kuma kai ta shafa wallahi bazan kuma zubar da ciki na ba ka zubar min dana
farko wallahi baka isa ka kuma zubar min ba"



Hayayyaƙo min ya kuma yi, daga ganin sa shi ba mutum ne daya iya lallashin mace
ba, ko nice dai baya son lallashi oho, yana hawa nima na hau, ko da ya ga yayi
lallami yayi faɗan amma duk da haka na ƙi yadda



Sai ya ɗauko wannan shegen turaren

"gashi nam kya ci gaba da shafawa" ya ajiye ya fice

"kuma wallahi kije kiyi nazari na faɗa miki annur be isa ai masa ƙani ba, inma ya
isa da ƙwan badia nake son cikin nan"



Inda ya ajiye turare nan na barshi ban ɗauka ba ƙiri ƙiri sabit yake nuna min
baya son haihuwa da ni kuma wallahi bazan bari ya samu abinda yake so ba



Kashegari da sassafe na kama hanyar part ɗin mummy don in kai mata ƙarar sa don
wallahi abun nashi ya fara isata


Tana zaune tana lazimi na shiga, sai dana jira ta idar muka gaisa sannan na faɗa
mata,

"je ki kwaso kayanki daga ɓangaren naku ki dawo nan inga in zai zuwa nan ya ce zai
taɓa miki cikin"


Ba haka na so ba naso ace ta kira shi tai mishi nasiha ko faɗa amma dai ko ba
komai an samu ci gaba a sha'anin natan



Daga nan ɓangaren anty fannah na wuce itama na fɗa yadda mukai da shi da kuma
shawarar da mummy ta yanke
"hakan shine dai dai, sabit yace baya son cikin don haka Allah ne kaɗai yaan abinda
zai yi don ganin ya salwantar da cikin, ki koma can kema hankalin ki zai fi
kwanciya, ko kin fi son zama kusa da mijinki ne"


"hmmmm wayaga miji indeed"

Mun daɗe muna hiɗa da ita daga ƙarshe ma itace ta ma ta raka ni na haɗe kayana
muka kama hanyar part ɗin mummy duk wannan abun da ake sabit ɗin be ma san anayi ba


Ɗaki guda mummy ta bani, amma sam ban ji daɗin yanayin fuskar ta dana gani ba,
ran ta a ɓace sai na ɗauka ko don dawowa ta ne part ɗin nata har na fara tunanin
gwanda in sabit ya tattara ya tafi in koma wurin mu



Sai kusan 12 :00 na rana sannan sabit ya shigo da sallamar sa ina ɗakin da aka
bani ina kwance ina jin shi yana ƙwala wa mummy kira


"kinga yarinyar nan ta tattara kayanta ta gudu ko naje wurin fannah bata nan, yanzu
ina zan ganta"


"ni nace ta dawo wajena don wallahi baka isa da shegen ra'ayin nan naka ba ka kuma
ɓarar min da jika ba, kai ba a haihuwa aka haife ka, saboda tsabar ka raina wa
asmaun wayo ma zaka ce wani ta zubar wallahi tallahi wani abu ya sake ya samu cikin
nan sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba ni, na fara gajiya da halin ka da kuma
shegen iyayin ka"


"mummy ƙara ta ta kawo ni fa ba cewa nayi baza ta ƙara haihuwa ba ce mata nayi ra
bari a kuma yi mata wani dashen kamar na farko, in yaso wannan sai t riƙe, kinga an
mata a dalci kenan"



" ba za a kuma dasa mata ƙwan ko wacce ƴar iskar ba, wallahi don ma ka samu asmaun
tana da sauƙin kai ne wallahi da ƴata ce da sai ka gane kuren ka duk da haka
wallahi sai na ƙwatar mata ƴancin ta daga gare ka, me kake gudu ba kar matar ka ka
gano ka ba sallamamme wai matar sa yake tsoro wallahi kaji kunya ka faɗi ƙasa ba
nauyi tiƙ haka ka faɗi"


Shiru yayi sam be ɗauka mummyn zata masa haka ba don haka sai ya kwantar da
hankalin sa


"haba mummy na ɗan autan ki ne faa, wallahi da an zubar tana watstsakewa za ai mata
sabon dashen wannan karon sai ta riƙe" lallai ma sabit ɗin nan ya wuce duk inda
mummy take tunani


"jinin asmau me yayi da baza a haihun da ita ba"
"mummy asmau in ta tashi baƙi zata haifa"


"to shikenan zan yadda a zubar mata da cikin in ka yadda da sharaɗi na ƙwaya ɗaya"


Gyara zama yayi ya san halim mummyn sa ai da ya karyar mata da kai zata amince da
shi da bishi da yadda so


"idan an zubar da cikin zan je a saka sperm ɗin bature ko balarabe kaga sai ta
haifa maka farare tas yadda kake sooo"


Zimbir ya miƙe

"mummy ban gane ba, ya za ayi a sakawa matata sperm ɗin wani kuma ace ɗana ne,
wallahi ban yadda ai ba abinda ya haɗa ni da shi" masifa yai tayi ina ɗaki ina cin
dariya ni kaɗai


"to menene ba de kai kace baza ka yadda ka haihu da ita directly ba ai dashe dashe
ne, in har zata yadda a dasa mata ƙwan wata ta ƙyanƙyashe ai kaima baza ka damu ai
mata dashen da sperm ɗin wani ba kooo"



Takaice ne ya ishi sabit yai ta faɗa wai asmaun ce ta jawo shi wallahi ba yanzu
yaso ayi wa annur ƙani ba, shi meye da meye


"yo in anyi wa annur ɗin ƙani kai ne zakai renon ko menene"


"wallahi mummy in yarinyar nan bata yadda anyi abinda nake sƙ ba wallahi zan
tsame hannuna daga lamarinta, kuma wallahi ta sake ta haifa min baƙaƙen ƴaƴa bani
ba su"


"kar ka samu damuwa kana fita lamarin ta sai in saka daddyn ku ya saka ka ka
sallame ta ai ba dole bane ita ma taje ta samu wanda zai yi alfahari da baƙaƙen
ƴaƴan natan ba kai me man ta kyauta ba"


"mummy kuma me ya kawƙ zancen saki anan"


"kai ka isa ka zauna da yarinya kana muzguna nata ina kallon ka ai an wuce wajen
sabit ya ga alamar in ba farkar da kai nayi abin naka sai ya fi haka"


Ya gama bambamin sa yai waje, yana fita mummy ta shigo

"kinji yadda mukai da mijin nakin ko, ai kema asmau da naki don kawai yana ganin
kina masa sanya ne shi yasa"


Shiru nayi lallai wannan cikin ya ja mi ƙima a wajen mummy, shawarwa ri ta dinga
bani akan yadda zan ƙwatar wa kaina ƴanci in bar zaman da nake yi a wajen sabit
Naji daɗin su sosai saɓanin anty fannah ita tana da sanyi bata taɓa cewa yi mai
kaza ba ko tace idan yayi kaza in rama amma mummy ƙiri ƙiri ta dinga zayyano min
yadda za ƙwatar wa kaina ƴanci kuma kar in sake ko da was in yadda in kuma bashi
wani haɗin har sai ya gane kuren sa



Tunda yayi fishi ya fice be kuma shigowa, nima naji daɗin hakan dom kuwa sam
bana son abinda zai haɗa ni da shi




Da yamma sai ga shi da annur, wai yaje gidan su badia ya tarar da yaron yana
kuka, mummy ya kawo wa shi wai ta riƙe


"kai dai wallahi kaji kunya zanga randa zaka tattara kan iyalen ka ku zauna waje
ɗaya lfy ba tare da matsala ba"


"mummy ni ba komai nake ba kawai ki kular min da shi, ina wannan me hijirar take
ne" ya faɗa

"oho maka kafin a tambayi me hijira sai an fara tambayar me shirin zubar da cikin
matars mara kunya" ta bashi ansa kasancewar ya san dashi take yasa shi be amsa ba
sai ya taho directly ɗakin da nake



Lallashi na ya dinga yi akan in yadda a zubar da cikin wallahi ana zubar wa zai
sa badia ta bada ƙwan natan in yaso idan na haihu sai in riƙe



Kallon shi kawai ina ƙarawa


"asmau bana son kizo ki haifa baƙi in dinga nuna masa bambamci tsakanin abinda kika
haifa da annur shi yasa don a aguje wa hakan ya sani son ɗaukar mataki da gayya"



Shiru nai masa ya gama soki burutsun sa yai waje daya ga banni da niyyar tanka
masa


Da daddare sai gashi da fura da nono na kanti me shegen sanyi, har ɗakin da nake
ya shigo ya kawo min kamar gaske


Ina kwance yace min in tashi inci insha, kallon inda yake banyi ba

"asmau ki tashi ki sha furar nan don ke na siyo ta"

"bana sha" na bashi amsa, tabbas furar ta shiga raina amma sam bana son bashi
fuskar da zai kawo min rainin hankali
Faɗa ya hau ni da shi wai yaje ya siyo kuma na baɗa masa ƙasa a ido, yadda naga
hankalin sa ya tashi ya nace lallai sai na sha ya na sakawa furar alamar tambaya


"sabit ko dai maganin zubar ciki ka saka a cikin furar da ka dage sai na sha"


Masifa ya fara ya na rashin mutumcin sa, miƙewa nayi nima na fara balbala masa
masifa,


"wallahi duk abinka sai na haife abinda ke ciki na"

"to wallahi ki haife zaki ga rashin mutunci tsirarrarsa"


Faɗa mukai da shi sosai da sosai faɗan da bamu taɓa yi ba don tun da yake min abu
ban taɓa tankawa ba sai yanzu



Wai da yake bashi da kunya bayan mun gama faɗan kuma sai yazo wai yana cewa ni fa
ayau anan zan kwana, fita nayi naje na faɗawa mummy inda ta zo da kanta ta kore shi


Babu irin magiyar da baiyi wa mummy ba akan ta bar shi amma ta ƙeƙashe ƙasa ta
hankaɗa ƙeyar sa yayi waje muka kulle


Kashegari ya tasa ƙeyar matar sa suka koma

Please Login or Register in order to submit comment