You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

na haɗa breakfast ɗina sannan na zauna ina cin abinci na kasa ci nayi

Maganar badia ce ta faɗo min a raina, wai in zama wacce zan reni cikin su, lallai
ma sun rena ni

Amma kuma wani ɓangare na zuciyata na son yi, ko ba komai zan dai ɗauki cikin da
ba a son in ɗauka

Miƙewa nayi kawai na yi na kama hanyar ɗakin sabit hankalina Akwance, suna zaune
shida badia sun yi jugum jugum abin duniya ya ishe su

"na yadda zan ɗau cikin ku amma ina da sharaɗi" kallo suka juyo wa sukai gare ni

"meye sharaɗin naki" suka haɗa baki

Kallo na bisu da shi sannan nace

"sai an biya ni ladan ɗaukar cikin"

"faɗi ko nawa kike so ni zan biya" inji sabit, tsayawa nayi na ƙare masa kallo
sannan nace

"250k kuma cash nake soo"

Badia ce ta miƙe ta fita daga ɗakin bata daɗe ba sai gata da kuɗi

"gashi nan 300k ne na ƙara miki 50k" karɓa nayi ina murmushi sannan nace

"kun biya sai a saka lkcn dashen" murna sosai ya kama su badia har da rungume sabit

Fita nayi daga ɗakin naje na adana kuɗina akwai ranar da zakuyi amfani, nace a
raina

Fara shirye shiryen dashen cikin muke yi abin mamaki shine na nemi turare na ko
sama ko ƙasa

Babu neman da banyi ba amma babu har sabit na faɗawa sai yace min zai sai min
sabo

Gaskiya nai missing wannan turaren zan so ace be ɓata ba haka nai ta neman har na
haƙura
Ranar laraba muka shirya muka je asibitin akai mana test da komai da komai, komai
ya kasance normal kawai lkcn dashe aka saka sati biyu

*****************

Ranar da kawo za ai dashen da kuɗi na na fita 200k a tattare da ni, sai da muka
gama komai na shiga ɗakin dashen sannan nace wa dr. ɗin wacce ta kasance macece
kuma bayarabiya

"nawa aka biya ki kuɗin dashen nan" kallo na tayi kamar batai magana ba, kuɗin da
ke jikina na fito mata dashi kallon su kawai tayi sai ta washe baki tare da cewa

"30k"

Ɗari biyu na ɗauko gabaɗaya sannan na bata na ce mata

"kiyi aikin ki da kyau" kallo na tayi sannan tai murmushi tare da soke kuɗin sannan
aka fara dashen fatana dai Allah ya bada sa a

Lafiya aka gama sai da nayi awa ɗaya bayan dashen sannan tace min in miƙe, kuma
aka kafa min sharaɗin kar in kwanta da kowane namiji sai an tabbatar da cikin

Badia ce me cewa ai dr. kar ki damu bata da miji, tunda muka koma gida sabit yake
nan nan da ni,

Komai na tashi zanyi sai a hana ni, har Allah ya kai mu 2 weeks inda muka koma
asibitin aka tabbatar da cikina

Murna kamar me a wajen sabit da badia, kallon su kawai nake yi dafe cikin nawa
nayi sannan nace Allah ya kawo min kai duniya lfy
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛

~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~

🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠

ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻

P⃗a⃗g⃗e⃗ 22🌹

Cikin ikon Allah na ci gaba da renon cikin mu 🤣🤣, Kulawa sosai nake samu daga
wajen sabit inda badia ke ƙorafi wai ya fiya shiga harka ta, sam banni da wata
matsala kuma duk abinda nake so nake yi

Tun cikin yana ƙarami sabit ya fara cika mana gida da siyayya tun ba a san me
zan haifa ba amma ɗaki guda haka ya ware yake kashe kuɗin domin isowar ɗan so

Allah sarki lkcn da nai ɓari ko mace ko namiji, duk banga wannan ba amma yanzu
ko aiki nake yi yai ta faɗa kenan wai sam bana son hutu ko ya isheni da sam ban
damu da cikin da ke jikin na ba

Wani lkcn abin nashi ma wallahi har haushi yake bani, daga baya ne ma ya nemo
mana me aiki wai don in dinga hutawa

Amma sam bana son wani hutu domin ni na riga na saba da shige da fice na tun ma
kafin in samu ciki balle kuma yanzu

Jina nake yi kamar cikin ba a jikina yake ba sam bawani matsala ko laulayi haka
nake ɗaukar sa salin alin karatun fatara

Sai da cikin ya zauna sannan sabit ya kira mummy yace mata badia nada ciki,
mummy tai murna sosai sannan tai fatan Allah ya inganta

Bayan kwana biyu sai ga mummy nai murnar ganin ta sosai har da saƙo na daga anty
fannah Allah sarki anty fannah nayi kewar ki sosai
Mummy tai ta faɗa wai badia mahaifar ta bata da ƙwari kuma gashi ta kuma samun
ciki amma ta ƙi zama ta kula da kanta

ba wanda ya tanka sai dai lallashi da suke ta bata wai zasu kula da cikin, ni dai
ina gefe ina kallon ikon Allah wannan rayuwa wato akwai abin mamaki sosai

Kwanan mummy biyar sannan ta kama hanyar gida, kamar nayi kuka ranar da ta tafi,
don kuwa yanzu zan koma rayuwa ni kaɗai

A hankali cikin ya ci gaba da girma har lkcn da zai zo duniya yayi

Rannan da yamma sai ga mmn badia tazo gidan ita da wata mata, ɗakin badia suka
sauka sam ban sam me ya kawo su ba amma kuma bini bini a bini da ido

ranar wata talata da safe na tashi da nakuda, tun ina yi ni kaɗai har dai dana ga
abin bana ƙare bane na fita, ina fita naci karo da wannan matar zata shigo ɗakina

"kar dai naƙuda kike yi ƴannan" gyaɗa mata kai nayi don bazan iya magana ba sabida
ciwon da ke damuna

Sabit ta kira shima ya fito jiki si ɓari yake yi yaji ina labour, asibiti muka je,
inda aka shigar da ni labour room Awa uku cur na ɗauka sannan Allah ya sauke ni
lfy, ajiyar zuciya na saki dana ji Allah ya raba ni da wannan cikin lfy

Ɗagowa nayi na kalli yaron......... Fari tas da shi kana ganin shi kaga sabit

Miƙo min shi nurse ɗin tayi na karɓi kayana na tsaya ina kallon sa, godiya nai wa
Allah daya sani ina da rabon ganin jini na

Sai da nurse ɗin gama gyara ni sannan ta karɓi babyn don gyara shi, shima, ko da
aka gama shirya shi zata fita da shi na kira ta na karɓi abuna

Ƙare masa kallo nayi kamar sabit yayi kaki ya yar addua nayi masa sosai, na so
ace yaron kamata ya ɗauko

Ko kuma ace baƙi ne amma ba komai duk abinda Allah yaso haka zan karɓa, kuma ina
fatan ya zama me jin ƙan iyaye

Ɗa na yana hannuna na fito daga labour room, da sauri suka ƙaraso tare da karɓar
sa mmn badia ce ta fara karɓar sa

"namiji ne ko mace" ta tambaye ni kalmar tai bala'in ƙona min rai ba Allah ya raya
ba komai amma wai ita burin ta namiji ne ko mace

sabit ne ya karɓi shi shima daga gani maganar tai masa ciwo, karɓar sa kawai yayi
ya wuce ɗakin da aka bamu na hutu

Addua ya dinga masa, ina amsa wa da amin, duk wannan abun da muke ita uwar ɗan
bata sani ba don sammako tayi ta tafi kwatano wai ta tafi siyo kayan da zata saka
da suna

Sai da ya gama masa addua sannan mmn badia ta kuma karɓar sa ta buɗe masa diaper
inda ta gano namiji ne

Nan da nan murna kamar me, har wani ƙara ruƙunƙume shi take yi, mijinta ta kira
ta shaida masa badia ta haihu,

Shima yai mata murna sannan yace a bawa badiar, nan ta hau ƙarya wai badiar bacci
take yi

Mummy sabit ya kira yace mata badia ta haihu ita ma mummyn tai murna sannan tace
a bawa badiar tai mata barka shima duk ɗaya yace tana bacci

Haka suka dinga kiraye kirayen waya suna shaidawa badia ta haihu, ni dai kallo ne
nawa

Zuwa can baby ya fara mutsu mutsun yunwa, dabino sabit ya tauna ya lasa masa a
bakin sa sannan aka bishi da zam zam

Wajen azahar aka sallame daga asibitin muka kama hanyar gida, wai don renin
hankali babu wanda yake ta kaina ni dana haihun sai ta baby,

Ɗakina na shige na samu na watsa ruwan zafi a jikin sannan na fito kitchen na
ɗaura indomie na ci na ƙoshi sannan na wuce ɗaki na na kwanta

Wajen ƙarfe 06:00 na yamma sai ga mummy, ina kitchen ina dafa shayi
Sai ga mummy, da sauri naje na tare ta

"mummy ashe kina tafe" tsayawa tayi tana kallona

"ya naga kamar ma kece me jegon duk kin wani ɗashe"
Ta faɗa tana kai hannun ta kan fuska ta, murmushi na saki sannan naja hannun ta
zuwa ɗakin badia

"zo muje kiga jikan naki"

Bina tayi, da sallama na shiga, suna zaune a bakin gado shi kuma babyn yana cikin
gadon sa na jarirai yana ta baccin sa

A razane suke da suka ga mummy, sai suka fara kame kame

"hjy fatima yaushe kika ƙaraso, muje falo mu zauna yaron yana bacci" inji mmn
badia

"ni da nazo ganin baby sai ace min yana bacci, ina ita mejegon"

Tsuru tsuru sukai, nidai tunda naga na haɗa su sai nai ficewa ta na barsu

Ɗakin nawa naji an turo ƙofar, ashe mummy ce ta shigo, sai da ta ƙaraso da sannan
na bata wurin zama

"har yanzu sabit ɗin basu dawo bane ko dai wani abun ne ya samu badiar"

Ni dai ban tanka mata ba saboda sam ban san ma ina ta dosa ba,

"ni wallahi duk a gajiye nake, nace musu su shirya gobee mu koma abuja ai suna
acen dama dalilin zuwa na kenan"

Ni dam ban tanka mata ba don kuwa a gaskiya na fara kewar ɗana, don haka sai nai
mata shiru,

Mara ta naji ta fara murɗa min, mitsss sai yanzu na tuna sam ban ma sha magani
ba, miƙewa nayi don in ɗauko magani sai naji mummy tana cewa

"asmau lfy naga kina tafiya kamar kece kika haihun, gashi kuma duk kin ɓata zanin
jikin ki"

Juyawa nayi don inga inda na ɓata ban ɗago ba sai ganin mata nayi kusa da ni

"asmau ke kika haihu ko badia"

Tsare ta nayi da idona wanda a yanzu suka ciko da hawaye, ɗago min fuskar tawa
tayi
"asmau ke kika haihu, ba badia ba" gyaɗa kaina nayi hawaye yana zuba a ido na

"haba biri yayi kama da mutum" inji mummy takaici ne ya kamata sai ta kama hanyar
fita

Ban san me tace musu ba sai gata da babyn,

"ungo shi bashi nono ya sha ki gama in gyara ki, wallahi idan sabit ya dawo yau sai
yaga ɓacin raina wanna wane irin zalinci ne"

Karɓar babyn nawa nayi na rungume shi sannan na zauna na fara bashi nono kamar
dama yunwa yake ji haka ya karɓa ya fara tsotsa

Muryar badia muka ji a bakin ƙofa tana masifa

"ban gane ɗan ta bane yaushe ya zama ɗanta don kawai ta rene shi a cikin ta sai ace
ɗan ta wallahi bazai sha nonon ta ba, na riga na gama booking nurse ɗin da zata
dinga kular min da yaro" ta faɗa tana shigowa a fusace da zummar karɓar mummy

Mummy ce tace

"wallahi kika sake kika katse masa wallahi tallahi sai na saɓa miki"

"mummy ya za ayi jini na ya sha nonon ta"

"ya akai ya zama jininki"

Nan badia ta kwashe komai ta faɗa wa mummy, bata gama ba mummy ta fashe da kuka,
adai dai lkcn sabit ya shigo

Ingiza badia yayi ya kora daga ɗakin, mummy kuwa kuka ta dingayi,ba irin lallashin
da sabit be mata ba amma taƙi shiru

Shima sai ya fashe mata da kuka

"anya sabit kana tuna ranar da Allah zai kama ka kuwa akan haqqin yarinyar nan,
tunda Allah ya haɗa ku kake zalintar ta, anya kana da tausayi kuwa"

"mummy don Allah kiyi haƙuri wallahi sai da ta amince muka biya ta sannan akai
mata dashen"
"wannan yarinyar me ta sani, da har zaku ce wani kun biya ta yanzu ɗan na wane na
wacce tai dakon cikin ne ko na ƴar lelen taka ne"

"mummy ƙwan badia ne"

"mummy ba nawa bane" na bata amsa

"amma ni alfarma ɗaya nake so a barni in kula da shi in dinga bashi nono in yaso
idan na yaye shi sai badia ta karɓi abinta"

Kallona mummy tayi sannan tace

"asmau ke yarinya ce har yanzu baki san ciwon kanki ba nan gaba zaki zo kiyi dana
sani"

"mummy duk yadda Allah ya tsara bawa rayuwarsa haka zai yi ta" na bata amsa
Nai ta mata daɗin baki akan maganar don bana son a jata da tsaho, ta yi mugun
jinjina min sannan daga ƙarshe ta saka aka kira badiar sannan ta kuma kafa sharaɗin
ni zan kula da babyn

Sam badia bata damu ba, shima sabit ɗin sai ya nuna ya fi son hakan,

Mummy itace ta dinga kula dani, ko da lkcn suna yayi a can wani hotel sukai sunan
su, daga ni har mummy ba wanda ya je

Amma ita da sabit da babyn sun sha hotuna kamar ba gobe, wallahi duk wannan abin
da ake yi ko kaɗan a jikina be taɓa damuna ba sdon nasan akwai ranar ƙin dillance

yaro ya ci sunan bbm badia amma anace masa annur mummy tai faɗa sosai wai ai sunan
daddy ya kamata a saka amma sam ba ai mara kara ba

Kaji mummy wani ɗigimi

********************

*BAYAN SHEKARA ƊAYA*

kamannin annur da sabit ya gama fitowa, sosai ga wayau kuma Sam baya yadda da
badia, shegiyar ƙyuya gare shi kamar
Daga ni sai ni, ko sabit in dai ba fita yaga zai yi da shi ba sam baya yadda ya
ɗauke shi

Sam badia bata damu ba, ita dai kawai burin ta taga an masa wanka an masa
kwalliya tai ta ɗaukar shi a hoto ta na ɗora shi a dp, facebook da instag.

Shima haka sabit ɗin yake sai dai in ban masa wanka ya ɗau gyara ba, nan zaku ga
da sabit ɗin da badiar duk suna rige rigen ɗaukar a pic

Sam wai nuna so ko jan yaron a jiki badia bata san wannan ba, ko tashi yayi da safe
ya tafi ɗakin ta sai dak kawai kaji tana ƙwala min kiran in zo in dauke shi in masa
wanka

Sam bata yadda ta ɗauke shi sai an masa wanka, wai ko yayi pupu ko fitsari sai
dai kaji tana kirana inzo in cire masa

Wani rashin *M* ɗin ma sai in yayi pupu a ƙasa kamar ta dake shi haka take, akwai
randa mukai faɗa da ita akan shi,

Ya shiga ɗakin ta ba diaper a jikin sa, sai yai mata pupu a kan gado, kawai
zagin shi naji tana yi

Da gudu na tafi ɗakin ta ɗaga hannu zata dake shi, da sauri naje na tare masa,

"haba anty yaro ne"
Harara ta bini da shi sannan tace

"ni ƙazanta ta yara ce bana so, zo ki kwashe kashin nan kije kiyi masa wanka"

Tabbas ba ta san ciwon sa bane don wallahi da ta san ciwon sa da uwa tana cikin
cin abincin ta ɗan ta zai yi pupu ta saki abinci ta wanke masa sannan ta zo ta
ƙarasa

Ita dai bangaren kayan sawa, kayan wasa, anan fa to kusan Rabin albashinta yaron
take kashe mawa,

Sai dai jawo shi ajiki ne dai batayi

Ana haka wani zazzabi ya kama shi aiko sai ya kasance ni kaɗai yake yarda in
dauke shi, hatta da sabit baya yarda da shi
Anan ne wani sabon rashin mutunci ya tasowa badia inda tace ita Sam atafau ayaye
yaro abata ɗanta, saboda gaskiya ita bata yadda ba tana uwar yaro amma sam be shaƙu
da ita ba

A zuciyata nace me kike masa da zai sa shakuwa da ke, don kayan wasan da kike sai
masa sani yayi shi yaro

Tuburewa nayi nace sam be isa yaye ba sai ya ƙara watanni, abi kamar wasa har
sabit ya saka baki shima sai ya goyi bayan badia wai shima baya jin daɗin yadda
annur ɗin yake masa

Ban musa ba ganin bana son sa'insa akan shi ya sa na miƙa mata shi nasan ko kukan
sa na dare ya sata dole ta dawo min da shi

Ai kuwa tana karɓar sa daya tsanyare da wani kukan ko a jikinta ni kuwa wannan
kukan jin sa nayi kamar ana yankan sa har cikin zuciyata naji

Ɗakina na shike ina jin sa yana cewa ```maaa``` da yake haka yake cemin don bakin
sa ba wani buɗewa yayi ba

Aiko ko awa daya batayi da daukan shi ba naji ana ƙwallamin kira a ruɗe na fito
inda naga yaro shame shame ahannun sabit kamar marar rai

Ruwa ne a hannun badia tana shirin sheƙa masa na karɓa a hankali na yayyafa masa
yana farfaɗowa ya fara ```maaa``` ```maaa```

"na'am baby na" na amsa masa ɗagowa yayi ya kalle ni, duk da dai jikin sa ba ƙwari
amma a hakan ya ɗago ya taho wajena da saurin sa ya rungume ni

Sosai na matse ɗana a jikina sai ajiyar zuciya yake saki, wanda hakan ya sa
zuciyata ta karye naji hawaye ya cika min ido na

Bani ba hatta sabit sai da jikinshi yayi sanyi ni ko hawaye suke sulalo min ganin
yadda yaron cikin ɗan lokaci kadan ya fita hayyacin shi amma da ganina yawani lafe
ajikina harda ƙara rungumeni

Bacci ne ya kwashe shi a kafaɗa ta ina ɗan jijjigashi ko da yai baccin sai na
sauke musu shi

"zo ki ɗauke shi" inji sabit

"ya ci gaba da zama a wajen ki har sai ya saba da badiar sai ya koma, ke kuma dia
ya kamata ki dinga samun time kina spending da shi mana don ya saba da ke kooo" ya
faɗa da sigar lallashi

"ok shike nan zan duba"

Wuce wa nai da shi ɗakina muka kwanta, kallon shi nayi sannan nace

"annur ɗana ina alfahari da kai, kuma wallahi da kai sai na nuna wa duniya cewa ni
asmau ƴar halak ce"

********************

Tun daga lkcn badia take shigowa ɗakina wai don annur ya fara sabawa da ita, amma
ko ta shigo tana manne da wayar ta tana chatting shi kuma daya ganta to ahike nan
ya liƙe min kenan har sai ta fita

Sam wannan method ɗin be yi ba haka naji tana faɗawa sabit, sai suka tsiri fita
da shi yawo, kunsan yaro da son yawo, wannan ne ma sa ya ke ɗan yadda ta ɗauke shi
in dai har ya ganta da mayafi ko hijab amma da ta zauna shikenan sai ya fara
```maaam``` yana kuka

*******************
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛

~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~

🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠

ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻

P⃗a⃗g⃗e⃗ 23

Bayan kwana biyu sai ga mummy nai murnar ganin ta sosai har da saƙo na daga anty
fannah Allah sarki anty fannah nayi kewar ki sosai

Mummy tai ta faɗa wai badia mahaifar ta bata da ƙwari kuma gashi ta kuma samun
ciki amma ta ƙi zama ta kula da kanta

ba wanda ya tanka sai dai lallashi da suke ta bata wai zasu kula da cikin, ni dai
ina gefe ina kallon ikon Allah wannan rayuwa wato akwai abin mamaki sosai

Kwanan mummy biyar sannan ta kama hanyar gida, kamar nayi kuka ranar da ta tafi,
don kuwa yanzu zan koma rayuwa ni kaɗai

A hankali cikin ya ci gaba da girma har lkcn da zai zo duniya yayi

Rannan da yamma sai ga mmn badia tazo gidan ita da wata mata, ɗakin badia suka
sauka sam ban sam me ya kawo su ba amma kuma bini bini a bini da ido

ranar wata talata da safe na tashi da nakuda, tun ina yi ni kaɗai har dai dana ga
abin bana ƙare bane na fita, ina fita naci karo da wannan matar zata shigo ɗakina

"kar dai naƙuda kike yi ƴannan" gyaɗa mata kai nayi don bazan iya magana ba sabida
ciwon da ke damuna

Sabit ta kira shima ya fito jiki si ɓari yake yi yaji ina labour, asibiti muka je,
inda aka shigar da ni labour room Awa uku cur na ɗauka sannan Allah ya sauke ni
lfy, ajiyar zuciya na saki dana ji Allah ya raba ni da wannan cikin lfy

Ɗagowa nayi na kalli yaron......... Fari tas da shi kana ganin shi kaga sabit

Miƙo min shi nurse ɗin tayi na karɓi kayana na tsaya ina kallon sa, godiya nai wa
Allah daya sani ina da rabon ganin jini na
Sai da nurse ɗin gama gyara ni sannan ta karɓi babyn don gyara shi, shima, ko da
aka gama shirya shi zata fita da shi na kira ta na karɓi abuna

Ƙare masa kallo nayi kamar sabit yayi kaki ya yar addua nayi masa sosai, na so
ace yaron kamata ya ɗauko

Ko kuma ace baƙi ne amma ba komai duk abinda Allah yaso haka zan karɓa, kuma ina
fatan ya zama me jin ƙan iyaye

Ɗa na yana hannuna na fito daga labour room, da sauri suka ƙaraso tare da karɓar
sa mmn badia ce ta fara karɓar sa

"namiji ne ko mace" ta tambaye ni kalmar tai bala'in ƙona min rai ba Allah ya raya
ba komai amma wai ita burin ta namiji ne ko mace

sabit ne ya karɓi shi shima daga gani maganar tai masa ciwo, karɓar sa kawai yayi
ya wuce ɗakin da aka bamu na hutu

Addua ya dinga masa, ina amsa wa da amin, duk wannan abun da muke ita uwar ɗan
bata sani ba don sammako tayi ta tafi kwatano wai ta tafi siyo kayan da zata saka
da suna

Sai da ya gama masa addua sannan mmn badia ta kuma karɓar sa ta buɗe masa diaper
inda ta gano namiji ne

Nan da nan murna kamar me, har wani ƙara ruƙunƙume shi take yi, mijinta ta kira
ta shaida masa badia ta haihu,

Shima yai mata murna sannan yace a bawa badiar, nan ta hau ƙarya wai badiar bacci
take yi

Mummy sabit ya kira yace mata badia ta haihu ita ma mummyn tai murna sannan tace
a bawa badiar tai mata barka shima duk ɗaya yace tana bacci

Haka suka dinga kiraye kirayen waya suna shaidawa badia ta haihu, ni dai kallo ne
nawa

Zuwa can baby ya fara mutsu mutsun yunwa, dabino sabit ya tauna ya lasa masa a
bakin sa sannan aka bishi da zam zam

Wajen azahar aka sallame daga asibitin muka kama hanyar gida, wai don renin
hankali babu wanda yake ta kaina ni dana haihun sai ta baby,

Ɗakina na shige na samu na watsa ruwan zafi a jikin sannan na fito kitchen na
ɗaura indomie na ci na ƙoshi sannan na wuce ɗaki na na kwanta

Wajen ƙarfe 06:00 na yamma sai ga mummy, ina kitchen ina dafa shayi
Sai ga mummy, da sauri naje na tare ta

"mummy ashe kina tafe" tsayawa tayi tana kallona

"ya naga kamar ma kece me jegon duk kin wani ɗashe"

Ta faɗa tana kai hannun ta kan fuska ta, murmushi na saki sannan naja hannun ta
zuwa ɗakin badia

"zo muje kiga jikan naki"

Bina tayi, da sallama na shiga, suna zaune a bakin gado shi kuma babyn yana cikin
gadon sa na jarirai yana ta baccin sa

A razane suke da suka ga mummy, sai suka fara kame kame

"hjy fatima yaushe kika ƙaraso, muje falo mu zauna yaron yana bacci" inji mmn
badia

"ni da nazo ganin baby sai ace min yana bacci, ina ita

Please Login or Register in order to submit comment