You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko sallama basuyi mana ba nima sai ya
tafi sannan hankali na ya kwanta
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*HIKIMA WRITERS ASSO.*
P⃗a⃗g⃗e⃗ 25 🌹




Da masifar su suka shigo

"wallahi sai an fito mana da ɗan mu" yayar badia ce hauwa a gaba tana masifa tana
ƙarawa


A zaune suka ga mummy da sabit sun zuba uban tagumi suna sharɓe kuka

"badia wallahi baki sa ar miji ba, ace namiji da kuka ke kuma kiyi me" wannan
maganar ta ƙonawa mummy rai sai ta tanka


Aikuwa nan da nan aka hau zage zage, mmn badia ce me cewa


"wallahi sai mun kai yarinyar nan kotu sai alƙali yai mata munmunan hukunci,
wallahi sai tayi zaman gidan yari, ku ma baku tsira ba wallahi sai an ƙwatar wa
badia ƴancin ta a gidan nan kun mai da ita baiwar ku"


Faɗa sosai shi dai sabit yana zaune ya kasa taɓuka komai yana jin yadda ƴan uwan
badiar suke ci masa mutumci duk da dai yana ganin laifin su amma asmau ta fi kowa
ƙona masa rai


Cikin hukuncin Allah sai ga muktar wan sabit shi ya shigo yai musu jan wuya
sannan suka haƙura suka tafi akan su jira kiranye daga court

"kuma wallahi idan court ta karɓar mana ɗan wallahi ya bar gidan nan ke nan har
abada tunda dai baku iya kula da shi ba har kukai sake wata yar aiki ta sace shi
wallahi annur ya bar hannun ku har abada"
Injimn badia ta faɗa tana yin waje



Sabit kara fashe wa yayi da kuka

"don Allah mummy ina zanga asmau wallahi yanzu bazan mata komai ba don Allah ta
dawo min da ɗana wallahi na yafe mata wallahi na daina yi mata duk abinda nake
mata, wallahi ina son annur sosai wallahi bazan iya rabuwa da shi ba"


"kai sabit wane irin mutum ne kai kamar ba namiji ba ka zauna sai kuka kake tayi,
ita kuma mummyn tace me" inji muktar

"don Allah muktar kar ka bari a ƙwace min annur wallahi ina son ɗana" ya faɗa yana
me riƙe ƙafar muktar ɗin
"wai mummy me yasa yarinyar nan ta ɗauke annur ɗin ne, ko faɗa suka yi, in banda
abinta ai ko faɗa kuka yi ba kya ɗauki ɗan da ba naki ba" muktar ya tambaya


Sam mummy sai ta kasa cewa komai don bata ma san ta ina zata fara ba, sabit ma
shiru yayi


******************


Fannah tana ɗakin ta suna waya da asmaun tana faɗa mata yadda gidan ya rikice, sam
ko a jikin ta asmau bata ji komai ba, ita burin ta ma Allah ya sauke ta lfy wallahi
ƙarawa gaba zatayi da ƴaƴan ta taje ta nemi dangin uwarta


Saboda tasan ko baɗe ko ba jima anty fannah zata iya tona mata asirin inda take



Sai da ta kuma jawa fannah kunne akan kar ta sake ta faɗi inda take sannan sukai
sallama


Tun ana ɓoyewa daddy har yazo magana taje wajen sa, ranar mummy ta sha faɗa sosai
kamar ba gobe daddyn yai mata yai wa sabit wanda a yanzu yake kwance saboda zazzaɓi
da ya rufe shi


Takanas daddy ya saka mutane suka kama hanyar garin su asmai don ganin ko ta je
amma ba same ta ba


Tas ya tara mutan gidan akan su faɗi ko akwai wanda yasan inda asmau take, amma
duk ba wanda yasan inda take


"har ke fannah don naji ance kullum kuna tare" jikinta ne ya fara rawa don ita
fannah Allah yayi ta surutu amma sam bata da zafi sanyi gareta da kuma sanyin hali



Amma da ta tuno irin cin kashin da sabit ɗin ya ɗinga yi wa asmaun sai ta dake
tace

"nima ban sani ba"

"to duk lkcn da ta kira ki ki ce mata ta neme ni koma menene wallahi sai na ƙwatar
wa yarinyar nan ƴancin ta tunda dai na lura kamar zaman haƙuri take yi da ku, in ba
haka ba tayaya za ayi ace ta ɗauki ɗan da ba nata ba ta gudu an rasa ta ko sama ko
ƙasa"



Ya juyo ga mummy

"anya fatima ke uwa ce kuwa tayaya za ayi ace wai a gidan ɗan ki ana samun matsala
amma sam baki sani ba, wane irin abu ne wannan, kince ke ƴaƴan ki baza suyi nesa da
ke ba amma kuma sam ba kya kwaɓar su
To wallahi ku sani duk wanda na same shi da laifi a guduwar yarinyar nan sai nayi
mugun saɓa masa, kuma ku shirya jibi monday zamu fara shiga court don iyayen badia
sun kai ƙara an aiko mana da sammaci sai ku shirya"


Sabit da ke zaune kamar mutum mutumi sai ya ƙara narke wa ɗan zazzaɓin da ke
jikin sa nan da nan ya kuma hauhawa, shi sam be ma san ya zai yi ba



Miƙewa yayi don ya tashi dole duk yadda za ayi ayau sai ya nemo inda asmau take
don kuwa wallahi bazai yiwu ace ya yi rashin ɗan sa ba


Don kuwa ya san indai suka shiga court ɗin nan da badia sannan suka ci case ɗin
dole ne ace ya bata ɗan in kuwa ya bata shi ya zaiyi da rayuwarsa




Miƙewar nan da zai yi sai jiri ya kwashe shi ya faɗi ƙasa a sume, a guje akayi
kansa inda mummy kuma ta fashe da kuka



Ruwa aka kawo aka yayyafa masa nan da nan ya farfaɗo jikin sa kamar garwashi
saboda zafi


Yana farfaɗowa kuka ya saki ya riƙe hannun mahaifin sa

"daddy don Allah kar ka bari su raba ni da ɗana, ƙila shi kaɗai ne ɗan da zan so a
duniyar nan don Allah daddy a nemo min asmau ta bani ɗana a maidawa badia ɗan ta
saboda ta barshi a gidan nan"


Ko wa a wurin sai da hankalin sa ya tashi, isma'il ne ran shi ya ɓaci ya fara
magana


"wallahi yarinyar nan idan na sake na ganta Allah ko su badia basu kai ta kotu ba
ni sai na sa an hora ta wane irin abune wannan"


Lefi suka dinga ɗaurawa asmaun bayan sam basu san gaskiya suna ta ƙoƙarin cusa wa
daddy magana saboda ya ji haushin yarinyar, da fannah ta ga haka sai kawai tace


"nasan inda asmau take"


Gabaɗaya kowa ya waigo gareta har da daddyn

"tana ina, suka haɗa baki"


Nan da nan fannah ta kwashe inda asmau take ta faɗa musu amma sam bata faɗi
dalilin zuwan asmau gidan ba


Sabit shine a gaba ya fice domin tafiya, daddy ne ya tsai da shi

"kai baka da lfy yi zaman ka nida isma'il da ita fannah zamu je mu dawo da ita"
inji daddy



"ka kira badia a waya su zo nan za a kashe maganar kafin aje court a kashe maganar
a gida"


Amsawa sabit yayi ya ɗauko wayar sa yana neman number badia wacce tunda abin ya
faru ta koma gidan su


Bayan ya samu badia ya faɗa mata ne ya zauna amma ba don ransa ba ya so ace yaje
wallahi da sai asmau ta gane bata da wayo



Ina kwance sai jin muryar anty fannah nayi a kaina

"ki fito da daddy muke"


Rasa abinda zanyi nayi na ɗauka na ja mata kunne ashe sam bata ji

"asmau ki tashi mana na ce miki da daddy muke"


Miƙewa nayi jiki na a sanyaye, na fito na same shi yana zaune a falon gidan da
isma'il da kuma wan anty fannah


Ina fitowa na gaishe su, daddy da fara'ar sa yace min

"me yaji munzo mai da ke ɗakinki maza ɗauko kayanki mu tafi"


Bazan iya masa musu ba na shiga ɗakin, anty fannah ce ta ɗauko min annur inda ni
kuma na kwaso kayana muka fito


A mota ba wanda yace min komai sai ma ɗana dana karɓa daga hannun anty fannah na
rungume shi duk da ƙaton cikin da ke jikina




Da sallama muka shiga babban falon gidan wanda yake cike da mutanen gidan harda
mutan gidan su badia


Tana ganina ta yo kaina da zagi wai in bata ɗan ta
Daddy ne ya dakatar da ita inda yace duk a zauna a tattauna me yasa na ɗauke
annur ɗin


Sai dana zauna sannan daddy ya buƙaci ai masa bayanin abin da ke faruwa, sabit ne
ya wangale baki yai masa bayanin, yadda aka samu annur


Ba daddy ba hatta ƴan uwan sabit sai da suka jinjina maganar nan, daddy kuwa faɗa
ya dinga yi yana ƙarawa sai da yai wa sabit wanki babban bargo sannan daga baya
yace

"sabit wai duk bokon ne ya saka haka ko menene, dashe ka sa akayi wa matar ka
saboda ɗayar matar taka ta cire mahaifar ta"



Rufe ido daddy yayi ya zage tas shi da badia bayan ya gama sannan kuma ya ɗaura
da nasiha akan abinda muka aikata gabaɗayan mu haramun ne


Ko da kuwa dukan su matan ka ne bw hallata a ɗauki ƙwan ɗaya a saka wa ɗayar ba
haram ne wannan


Duk wani abu daya danganci dashw na ciki indai akwai mutun na uku daya shigo
cikin abun ko da kuwa ko wane kusanci ne tsakanin su to ya haramta


Faɗa sosai daddy yayi musu duk sai suka rasa bakin magana


"ai asmau tana gaskiya ɗa ɗan ta ne babu wata badia, tai wahalar ɗaukar ciki ta
sha naƙuda yanzu kuzo kuce wani ɗan badia tayaya akayi ɗan ya zama nata, to ku sani
wallahi daga yanzu na gama case ɗin nan asmau ki ɗauki ɗan ki zan ga wanda zai kuma
kawo maganar annur anan, kai in banda ma kai sha sha sha namijin kawai ka ɗauki
ƙwan matar ka ka dasawa wata idan ɗan ya girma kace masa wacce ce uwar sa, wacce ta
ɗau cikin sa ko wacce yake da jinin ta"


Dukkan su jikin su ne yayi sanyi in banda badia wacce tace

"wallahi sai kotu ta ƙwatar min ɗana" ta faɗa tana kuka


"ai dole ne ɗa jinin ki ne duk inda aka je akai gwajin jini jinin ki za agani don
haka ban ga dalilin da zai sa ace don mace bata da mahaifa ba ace kuma sam bazata
mallaki ɗan kanta ba" inji maman su




Gyara zama daddy ya yi ya fahimtar da mmn badia sharia akan duk wacce ta ɗau cikin
ɗan adam ta kawo shi duniya itace mahaifiyar sa amma sam matar nan bata yadda
fuuuuu haka ta ja badia suka fice
Sabit wanda jikin sa yai sanyi ya ƙaraso kusa da ni zai ɗau annur daka masa
harara nayi na miƙe tare da daukar ɗana na fice



Babu wanda ya bashi gaskiya kowa sai rashin gaskiya yai ta bashi,


Ɗakin na da ke part ɗin mummy nan na koma na kwanta, sabit ne dai ya kuna
shigowa,


" Na fahimci har yanzu taurin kan ki na nan, kina gani idan munje court gobe zasu
baki annur ni ne dai uban annur kuma nace baza ki renar min ɗa ba"


"kai ma ai bamu fara da kai ba, idan an gama case ɗin annur a court ɗin dole ne
ka bani takarda ta don kuwa na gama aure da kai"


"zan ga wanda ya isa ya sani sakin ki" ya faɗa a fusace

"wannan kuma in munje court ɗin na gabatar wa da alƙali buƙatata idan ya saka ka
sake ni kace kai baka yadda ba"


Haushi ne ya kama shi sosai ya fice daga ɗakin ko ganin annur ɗin ma be yi, nima
na bi ƙofar da mukulli sannan na kwanta sai da safe Allah ya kaimu court ɗin inga
in za abata ɗan bayan bata san komai nashi ba




*******************


Kashegari da wuri na tashi na shirya ɗana don zuwa court duk da dai yanzu sam
hankalina ba a kwance yake ba ga ciki amma hakan be hanani gyara fuskata ba


Mummy ce ta shigo wai daddy na kirana

Hijab ɗina na ɗauka na same shi a falo yana zaune, har ƙasa na durƙusa na gaishe
shi ya amsa min sannan ya kuma kwantar min da hankali na


"nayi wa lawyer na magana shine zai kare ki koda kuwa jinin badia ne wannan yaron.
Amtsayinki na wacce kika ɗau ɗawainiyar yaron nan sharia ta baki naki ne ko ina
suka je ke kika haife shi ɗanki ne"


Hankali na ya kuma kwanciya, anty fannah ce ta shigo itama taci laffayar ta,


"daddy nima dani za aje, don kuwa nima shaida ce, kuma ina kamun ƙafa idan an gama
case ɗinnan ni zan karɓe shi ko asmau" gyaɗa mata kai kawai nayi amma wallahi bazan
iya bawa kowa ɗana ba
"to ai shike nan wannan ɗan ƙaramin case ne nasan ayau za a gama shi ma idan kun
shirya sai ku fito"


Mummy har gabana ta zo nasiha tai min sosai wallahi har jikina yai sanyi, akan
kar in sake in bari a ja shariar da tsaho don mafi akasari idan ana faɗa akan ƴaƴa
to wallahi su take shafa


Gabana ne ya faɗi na ƙara matse abina a jikina in shaa Allah yau za a gama case
ɗin tunda dai ƙiri ƙiri ga yadda abin yake



********************


Badia ce da mmn ta sai lawyern da suka ɗauko a zaune duk abin duniya ya ishe su,

"gaskiya hjy kamar yadda na faɗa miki duk inda aka je indak ƙasar nan ne baza a
taɓa badia ɗan nan ba tun da dai a ƙundin tsarin mulki na ƙasar nan wacce ta kawo
ɗa duniya itace uwa"


Kuka badia ta saki

" wallahi ƙwai na ne fa, ya za ayi in ɗau ƙwai na in bawa wata ƴar iska ita in
banda rashin godiyar Allah ma gawani ɗan iskan ciki nan a jikin amma kuma bata
godewa Allah ba sai ƙwaya ɗayan nan shine zata ce sai ta raba ni da shi, mummy don
Allah ya zamu yi wallahi zan iya rasa rai na idan aka ƙwace min annur"


"yi shiru yi shiru inji mummy yanzu kai barister ya kake ganin za ayi"



Shiru yayi can sai ya e

"to akwai mafita amma sai in me gidan ya yadda da hakan" nan da nan ya tsara musu
yadda za ayi


Ba musu suka yadda nan da nan badia ta kira waya lagos ta faɗa wa dr. ɗin nan da
tayi dashe akan ta bar asibitin na ɗan wani lkc kuma ta kashe wayar ta



Shi ma sabit ta kiɗa shi ta faɗa masa shawarar da barister ya yanke, nan da nan ba
tare da wani shawara ba yace ya yadda duk yadda suke so hakan za ayi


********************



*COURT*
Sai da aka gabatar da case 4 sannan aka kira su, inda magatarda ya gabatar da
case ɗin su, aka kirawo badia da asmau kowacce ta gabatar da kanta


Alƙali ya nemi badia tai bayanin abinda ya faru

"asmau kishiyata ce, kusan a tare Allah ya azirta mu da samun ciki, amma ta riga ni
haihuwa inda ita ɗanta be zo da rai ba, ni kuma nawa yazo da shi, kuma shine wannan
na hannun natan


To kasancewar ban da ruwan nono sai mijin mu yace asmau ta dinga bawa ɗana nono,
shine yanzu ta ɗauke min shi ta gudu da shi wai nata ne"



Sakin baki kawai su anty fannah sukai suna kallon ikon Allah, sai da alƙalin ya
gama rubuce rubucen sa sannan ya tambayi asmau ita kuma ta faɗi me ya faru


Nan da nan na zayyano duk yadda akayi na samu cikin annur, kowa a court ɗin sai
ya ɗau salati aka fara ƴan ƙananan surutai


Sai da alƙalin ya doka ƴar gudumar sa sannan akai shiru,


"ina me gidan nakun"alƙali ya tambaya


Nan da nan aka taso ƙeyar sabit ya fito, alƙalin ya tambayi cikin mu wake faɗar
gaskiya, mutumin nan be ji kunyar Allah ba sai buɗar bakin sa yace


" badia ce take faɗar gaskiya"


Hmmm sabit in bakai haka ba ai baka cika ɗan halak ba

"to malama asmau kinji abinda mijinku yace ko ke kina da taki shaidar"

Gyaɗa kaina nayi sannan ya bani damar faɗar menene nan nace masa dr. ɗin da tayi
min dashen kasancewar bata nan ya sa aka ɗaga ƙarar har sai dr. ɗin tazo da kanta



Daga nan sati biyu akan mu zo da dr. ɗin, aka sallame mu bayan alƙalin ya ja min
kunne akan kar ya sake naji na bar gidan balle in tafi da ɗan




*******************


Tun a mota daddy yake faɗa akan abinda sabit yayi, yana komawa gida ya faɗawa
mummy ita ma sam bata ji daɗin hakan ba
Daddy ya tambaye ni number dr. ɗin don a kira ta a faɗa mata abinda alƙalin yace


Tooo nan fa ake yi don gabaɗaya ban san komai na dr. ba ni ko sunan asibitin ban
sani ba, don inda akai min dashen daban inda kuma muke zuwa nan ma daban ne


Babu yadda zasu yi dole ne aka nemo sabit don ya faɗi a ina za a samu, abin
takaici wai sai sabit yace shi ma be sani ba wai badia ce ta san ta


Haka daddy ya zaunar da sabit yai mai masa nasiha, tunda ya ga faɗan ma sam baya
shiga, amma ƙiri ƙiri sabit yace shi be san zance ba



Daddy ya rasa yadda zai yi da sha'anin mu, don yasan ko ana ha maza ha mata badia
baza ta taɓa faɗar address ɗin dr. ɗin ba balle ayi contacting ɗin ta


Zaunar dani yayi yai ta min nasiha, sannan yace min in Allah yayi annur zan rayu
a matsayin ɗana too in kuwa Allah yayi kotu zata bawa badia to a matsayi na na uwar
sa ba abinda zai so daga gareni face in kasance ina masa addu amma shi sam baya son
ai ta ja'inja akan yaron don kar abin yai affecting ɗin sa


Tabbas maganar daddy haka ne amma kuma in shaa Allah addua zan dage da ita kan
Allah ya bayyana mana da dr ɗin nan
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 24 🌹
Renon ciki na nake yi hankali na a kwance ga ɗana a kusa dani, sam su sabit basu
tafi da shi ba nima na so hakan



Duk wani siyayya mummy tayi haihuwar kawai muke jira, amma saɓanin saɓanin cikin
annur wannan cikin girma gare shi sosai da sosai


Har anty fannah tana cewa ko dai ƴan biyu ne, ko da muka je scanning twins ɗin ne
kuwa


Muna dawo wa anty fannah ta faɗawa mummy, bashiri mummy ta kwashi anty suka tafi
kasuwa aka sake sabuwar siyayya



Cikina yana da wata 8mths sabit suka dawo shida badia, sam duk wannan abunda ake
yi badia bata san da cikin ba



Tun da suka zo bamu haɗu da sabit ba, dana ji alamar zai shigo sai in gudu ɗaki
duk wannan abun Allah bai taɓa haɗa mu da shi ba



Kwanan su uku da dawo wa ya badia ta zo da kanta lkcn ina ɗaki ina bacci ta ɗauke
annur, ita kanta badiar bata san da cikin ba


Ko da na tashi, sai ban ganshi ba, sai na tambayi mummy yana ina sai mummy tace
min ai badia ce ta ɗauke shi


Ba badiar ba hatta mummyn ta bani haushi yadda har ta bar badia ɗaukar sa bayan
tasan ƙyuya gare shi



"mummy bari inje in ɗauko shi kin san halin annur idan ya tashi be ganni ba"


"to shike nan ni sai da na hanata sai tace wai sabit ne yace ta ɗauke shi"


Ficewa nayi daga part ɗin na doshi part ɗin sabit da tsohon ciki na, a hankali
nake tafiya don kuwa cikin yai girma dayawa fiye dana annur


Tun kafin in ƙarasa ciki nake jin kukan yaron nan yana kira na, sai na ƙara ɗaga
ƙafa, da sallamat na shiga tana zaune akan kujera tana kallo shi kuma yana zaune a
ƙasa a kusa da ƙafar ta yana kuka



Sallamata ce ta sata juyowa, ai kuwa ta ci karo da ƙaton cikina, wani ashar ta
daddage ta ɗura sannan ta ƙaraso inda na ke kamar wacce zata dake ni


"uban waye ya miki cikin nan"

Kallon ta na tsaya ina yi yadda take huci kamar zaki, sai nishi take yi kamar
wacce take shirin yin dambe


"tambayar ki nayi uban waye yayi miki cikin nan" ban kula ta ba saboda tsayawa ma
kula ta ɓata lkc ne ai ta san zaman aure nake yi


Wuce ta nayi na ƙarasa kusa da annur zan ɗauko shi, ji nayi ta jawo ni sai saukar
mari naji a fuskar ta, kammm bata ajiye ba nima na kai mata bama ɗaya nayi mata
biyu


Sannan nace mata

"kina san ki san wanda yai ciki tooo mijina ne, kafin wannan ma na taɓa ɓari,
kafin in haifi annur banza kawai wacce bata san inda yake mata ciwo ba"


Ban ankara ba kawai sai jin matar nan ta hau ni da kokawa tana ihu tana kuruwar

"ƙarya kike yi me sabit zai yi da ke" faɗa sosai mukai da ita


Kasancewar cikin da ke jikina yai min nauyi ya sata samun galaba akai na hai ta
kaini ƙasa ta shaƙe ni tare da cewa


"wallahi duk macen da tace zata haihu da sabit sai na kashe ki na kashe abinda ke
cikin naki inga abinda za ai min tunda ba wani gata gare ki"



Duka ni kuma na dinga mata inda tana ta ƙoƙarin haye min ruwan ciki Allah ya jeho
anty fannah, da saurin ta ta zo ta hankaɗe badiar daga kaina



Tafiya tayi taje ta daki bango wanda har sai da kanta yai ciwo amma sam bata
daddara ba kafin anty fannah ta ɗago ni tuni ta yo kaina



Wannan karon da ƙarfi anty fannah ta hankaɗa ta sai kuwa ta faɗa kan annur inajin
yaro na ya ƙwalla wata irin ƙara, hankali na ne ya tashi na miƙe da ƙyar na yi
wajen sa amma anty fannah ta hanani ta janye ni muka bar part ɗin


Hankalina sam ba a jikina yake ba naso in san me ya samu yaro na amma anty fannah
ta hanani



Part ɗin mummy muka nufa anty fannah tana bata lbrin yadda ta ganmu ni kuma ina
ce mata annur fa yaji ciwo


"ai dole sabit ya san wannan rashin hankalim da matar sa tayi" inji mummy


"Baki ciwo ba ko" girgiza kaina nayi,

"amma mummy annur kamar ya ji ciwo faaa"

"ina ruwanki da wani annur duk kin bi kin ɗaga hankalin ki akan yaro bayan uwar sa
ba sanki take ba"


Kuka na saka musu ni kaɗai na san abinda yake damuna akan irin abinda sabit yake
min gaskiya na kai matuƙar ƙarshe a haƙuri



Ganin ina kuka yasa mummy tace min in daina sanna in shiga ɗaki na in kwanta in
huta tunda ba abinda ya same ni ita kuma badiar bari sabit ɗin ya dawo za ta ja
masa kunne ya faɗawa matar sa ta fita hanya ta



Anty fannah ce ta taimaka min duk da bana jin komai har ɗakin nawa, ban daina de
kuka ba, abin ya min ciwo, anty fannah ce ta zauna kusa da ni tana bani haƙuri


"wallahi anty fannah haƙuri na ya ƙare na zo ƙarshe wallahi sai na nuna wa duniya
wacece mahaifiyar annur"


"ban gane ba"


Nan da nan na hau mata bayanin yadda aka samu annur, sai da naga tas sannan ta hau
ni da faɗa wai nayi wauta ai duk inda muka je bani da gaskiya, tunda ga yadda aka
haife shi har kuɗi na karɓa


Kuka na dinga mata ni dai a gaskiya ɗana nake so a hannuna, kukan da nake mata ne
ya sa jikin ta yin sanyi, kuka wiwi haka na dinga mata



"yanzu asmau ya kike son in miki"


"ni wallahi in ba barin gidan nan nayi ba wallahi zan iya mutuwa don na gaji da
matsalar gidan nan" kuka na dinga mata





Please Login or Register in order to submit comment