You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301

[10/05 09:49] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*AUREN BAUTA*

🍷🍽🥛


~(the amazing cook)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍢🥠🍥🍤🍣🍱🍲🍡



By mmn walid and walida (mrs aliyu)



Marubuciyar
*tawa kaddarar*
*dangin sa*
*uwata*
*rabo na ce* to be continued in shaa Allah



Page 1🌹




"Sai yanzu kika dawo ƴar iska tun ɗazu da aka aike ki ɗebo ruwan sai yanzu kika ga
daman dawo wa kuma kina ji na nace miki sanwar wake da shinkafa zan ɗaura da ruwan
shine kika je kikai zaman ki don kina min baƙin cikin kuɗin da zan samu ko, shegiya
da fuskar kamar ta aljan"



Duk wannan faɗan da inna harira bata taimakawa ƴar yarinyar da take ɗauke da
ruwa akan ta, duk kuwa da ganin cewar yarinyar ta gaji sosai



sai da tayi ta gama sannan ta sauke,
"kuma kije gonar malam ki wo min in kin ga dama ki daɗe kamar kinje lahira gaida
iyayen ki"


Ɗan ɗankwalin da take ɗauro karar ta ɗauka tayi waje da shi, directly gonar ta
nufa wanda bashi da nisa da gidan ta ɗebo karar sannan ta kama hanyar gida tana yi
tana nishi daga gani yunwa ce da kuma gajiya a tattare da yarinyar



Da sallamar ta ta shiga gidan ta ajiye karar sannan ta zundumi ruwa a randa ta
ɗan sha kaɗan bata san ta cikawa cikin ta ruwa



"shiga madafi ki ɗauko ragowar ɗumame ki don yadda kike zaro min idandinan nan
naki a cikin wannan baƙar fuskar taki ai wannan sai in mummunan mafarki"




Abincin ta ɗauko zata fara ci kenan inna harira ta kuma saka ta aikin hura wuta
na wake da shinkafar da take saidawa



A bakin murhun ta zauna tana hura iccen tana cin sandararran tuwon dawan da idan
aka jefe ka da shi sai kaji ciwo saboda tsabar taurinsa



Sai da ta gama girka wake da shinkafar tsab sannan ta kwashe a ƴar fantekar da
ake kwashewa sannan ta gayaws inna harira ta gama


"lantana lantana", inna harira ta kira ƴar ta da ke yi mata talla don kuwa asmau
bata da kan inna harira tace yadda fuskar ta take baƙa haka ma kwakwalwar take sam
babu haske a tattare da ita



Asma'u ce ta ɗau fantekar inda lantana ta shige gaba suka tafi tallan haka
suke yi kullum ita lantana itace me kan talla amma ban da asma'u



Sai bayan sallah la'asar sannan suka dawo inda suka tarar da inna harira da
baƙuwa a zaune a tsakar gida akan tabarma



Ƙwalawa asmau kira tayi ta ƙarasa inda take sannan ta nuna wa matar asmau

"hjy kina ganin zatayi, don ni ƴar nan babu abinda take min anan, kullum sai dai
taci tayi kashi kan talla babu shi yanzu in ta tashi aure wazai mata kayan ɗaki, ga
shegen baƙi kamar kwalta"
Matar da aka kira da hjy ta dubi asmau sannan tace

"to ba wai baza tayi ba kamar yadda na faɗa miki abuja ni fa nake kai yara aikatau,
wannan kuma kamar yarinya ce"


"ahap haka kike gani ai wannan in ta kama aiki kamar jaka haka take, reno shara
wanki wanke wanke duk ta iya"



Hjyr ta kuma kai duba asmau wacce kan ta yake a ƙasa sannan ita sam bata fahimci
inda zancen su ya dosa ba


"ni dai da waccen ce" ta faɗa tana nuna lantana ƴar inna harira, inna harira sai
tayi dariya irin ta basarwan nan


"haba bazaki so kiɗau wannan ba ai alanƙosa ake ce miki indai lantana ce ba abunda
zata iya, yanzu tallan wake da shinkafar da take kai min ma tace zata dena tunda
ɗan me gari yace yana sonta shi yasa nake neman hanyar da kuɗi zasu dinga shigo
min, ga bikin lantana ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, kuma auren ɗan me gari
kashe kuɗi gare" ta faɗa tana ajiyar zuciya


"to shike nan indai kince wannan ɗin zatayi ai shike nan, amma idan na tafi da ita
kuma aka ƙi ɗaukar ta zan dawo miki da ita"


"na yadda amma kice su fara gwadata tukunna kafin su yanke hukunci da wannan ɗan
ƙaramin jikin nata shine yake sawa mutane suna yi mata kallon yarinya ce"



Sukai sallama kan kashegari da asuba zata zo ɗaukar asmau zuwa garin abuja
aikatau



***********************



Asmau sunana na kasance ni kaɗai a wajen iyaye na babana ɗan nan garin ne azore
wanda yake a ƙaramar hukumar minjibir ta jihar kano,



Garin fulani ne sosai don gida tsilli tsilli zaku dinga gani in kun shigo sannan
sai kuma gonar mutum a jikin gidan sa, irin dai ginin fulani, in kaga gida ɗaya sai
kayi tafiyar mill kafin kaga wani



Ban san iyaye na ba kasancewar sun rasu, mahaifiyata ta rasu lkcn haihuwar
ƙanina, inda aka rasa aka rasa ɗan,
Shi kuma mahaifina sai da na ɗan tasa kaɗan sannan Allah yayi masa rasuwa, sai
kulawata ta koma hannun wan mahaifina



Inda yake min rikon sakainar kashi, don kuwa babu ruwan shi da duk wani daya
shafe ni duk abinda matar shi zatai min baya cewa komai wannan shine taƙaitaccen
tarihi na


******************




Da sassafe hjy ta zo mukai sallama sannan muka kama hanya inda naci karo da
wasu ƴammata waɗanda zamu tafi da su, amma duk sun girme ni don ni sai na zama
kamar wata ƴar tsana a ciki su



Sai da muka je gezawa sannan muka samu ƙaramar mota inda zata kaimu abuja, haka
aka cunkusa mu a motar nan kamar dabbobi inda ita kuma hjyr ta zauna a gaba ita
kaɗai



Tafiya ce kamar ta yada shege ba ƙaƙƙautawa sai da muka je kaduna sannan
direban ya tsaya muka fito muka ɗan huta, sannan muka kama hanyar abuja




Lfy ƙalau muka isa abuja inda muka sauka a kubuwa, anan gidan hjy yake, ɗaki ta
bamu guda, tace duk mu sauke kayan mu




Ni dai kamar an min duka haka nake ji don kuwa a gajiye nake, kwanciya nayi
sai bacci, inda ƴammatan da muka zo da su kowacce take ta buri tare da fatan irin
gidan da za a kaita, ni dai tunda na samu bacci ya kwashe ni sai nace saba'ul
khairi



menu of d day
*wake da shinkafa served with local salad & zobo drink*


🍲 ```wake da shinkafa```🍲


```ingredients```

```wake```
```shinkafa```
```gishiri```
```man gyaɗa```
```haɗin salad```


```method```


1) bayan kin gyara waken ki saki ki wanke ki ɗaura akan wuta, sannan ki bishi da
ruwan kanwa (optional)

2)sai waken ya dahu, sannan ki ɗauko wankakkiyar shinkafar ki ki zuba ki juya ki
saka ɗan gishiri sannan ki rufe


3) idan ya dahu sai ki sauke ki yi serving da soyayyan man gyaɗa, ko tankwa, da
yaji sai kiyi ganishing da salad aci lfy


*LOCAL SALAD*

```ingredients```

cabbage
lettuce
carrot
cucumber
green pepper
lemun tsami
man gyaɗa
maggi


```method```

1) ki wanke lettuce, cabbage, cucumber, green pepper ɗinki, ki barsu su tsane
sannan sai ki yanka su irin yankan da kike so




2)ki kankare bayan carrot sannan ki wanke shi daga nan sai ki gurza shi


3) ki ɗauko kayan haɗin da kika yayyanka ki haɗa da carrot sannan ki haɗe su waje
ɗaya, ki ɗauko lemun tsami ki ɗiga kaɗan ba dagawa ba yadda dai zai miki sannan ki
zuba mai ki zuba maggi ki juya sai ki juye a salad bowl sai ci




*zobo drink*

```ingredients```

Ganyen zobo
Citta
Kanunfari
Abarba
Cucumber
Sugar
Flavour


```method```

1) ki ɗauko zobo sai ki wanke shi ki zuba masa ruwa ya sha kansa sannan ki ɗaura a
wuta, tare da citta, ɓawon abarba, sai dakakken kanunfari ( ```sirrin daka
kanunfari shine ƙamshin shi ya fi fitowa idan an daka shi akan a watsa shi haka```)


2) idan zobo ya tafasa ya dahu sai ki sauke shi ki juye a babban mazubi yadda zai
sha iska, kafin ya huce kuma bari mu haɗa ragowar

3) ki fere yanka abarbar da cucumber ki ƙanana yadda dai zasu miki daɗi wajen
blending sai ki markaɗa su kina yi kina tacewa kina ƙara markaɗawa har dai a samu
yadda ake so

4) sai ki ɗauko wannan zobon naki ki tace ki ɗauraye ganyen ki kuma tace wa har sai
maa shaa Allah, sannan ki haɗa da ruwan cucumber & abarbar nan


5) ki zuba sugar, flavour ki zuba a jug a saka shi a fridge yayi sanyi sai shaa


*Bon appetit*


*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:49] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



page 2 🌹




Kashegari da sassafe aka tashe mu, koko da ƙosai aka bamu, muka karya sannan hjy
ta tasa mu a gaba domin neman wa kowa gidan aiki
Muka dinga zagaya gari zuwa gidajen masu hannu da shuni da kuma masu matsakaita
ƙarfi ana ajiye mu da ɗai ɗai,



Sai da ya rage mu biyu sannan muka hau mota muka nufi wuse zone 4 kamar yadda naji
hjyr tace wa driver taxi ɗin da muka shiga



A ƙofar wani restuarant muna sauka inda muka shiga ciki,




Hjy ce ta nuna mana wani ɗan loko wai mu zauna a can kafin ta dawo, kusan
minti biyu ta ɗauka sai gata inda ta kira mu muka bi ta cikin gidan



Wata mata ce muka samu tana zaune a saman wata three sitter daga gani itace me
wurin

"gasu nan kamar yadda na faɗa miki su biyu ne" matar da ke zaune a ɗakin ta gyara
ɗan glass ɗin da ke fuskar ta sannan ta kalle mu kamar ta ga wasu kashi ko abun
ƙyanƙyami



"me zanyi da waɗannan jariran" ta faɗa a wulaƙance

"na faɗa miki indai zaki kawo min ƴar aiki babba nake so amma me zan yi da waɗan
nan, gwara ma waccen amma wannan kamar ba a daɗe da yaye ta ba"


Ta ƙarashe zancen ta idon ta akaina


"wallahi hjy munnira ƙaramin jiki gareta amma da shekarun ta"




Mahawara suka fara yi inda hjyr da ta kawo mu ta fi hjy munnira baki don haka
dole hjy munnira ta yadda ta ɗauke mu bayan an sani shara nayi



Sai da suka gama cinikin abinda za a dinga biyan mu a shekara sannan hjy tai
sallama da mu, ita kuma hjy munnira ta kira wata laure wai ta tafi da mu ta nuna
mana aikin daya dace mu



Can bayan gidan muka je inda anan ake duk wani hada hada na girki, ƙaton
kitchen ne, sai kuma wajen wanke wanke sai kuma wasu ɗakuna guda biyu da ke can
gefen daga ƙarshen katangar inda anan akace mu ajiye kayan mu
Kowaccen mu aka haɗa ta da aikin daya dace da ita, ni dai kitchen aka kai ni
inda wacce muka zo da ita aka kai ta wajen wanke wanke




Ina shiga kitchen, naga girman kitchen ɗin, ban taɓa ganin irin wannan kitchen ɗin
ba sai yanzu



Girki ake yi kamar ba gobe, tsayawa kawai nayi ina kallon ikon Allah tare da
ƙarewa kitchen ɗin kallo,



"ke ya sunan ki" naji wata ta faɗa

"asmau" na faɗa a hankali, kallon banza naga ta bini da shi

"ke amina waye yace a kawo mana ƴar jaririyar nan kitchen mu da muke aikin wuta"
ta faɗa kamar taga kashi


"hjy ce tace a kawo ta nan" inji wacce aka ƙira da aminar

"to sai sa ta tsabtace jikin ta don nan bama gayyata ƙazanta" sim sim sim na fice
inda na nemi hanyar da ɗakunan kwana suke



Ƴar jaka ta na ɗauko, sam babu wasu kayan arziƙi don duk kayan da nawan
yawancin su ba wanki, wasu kuma a yayyage


Zama nayi ina kallon ikon Allah, ban jima da zama ba sai ga wata ta shigo

"me kike yi a ɗakin nan bayan kowa yana waje yana aiki, kar dai bincike kike mana a
kayan mu"


"wallahi ba haka bane, wanka akace inzo inyi in canza kaya kuma naga kayan nawan
duk babu wanki" na faɗa d ido na duk ya kawo ruwa saboda banji daɗi zargin da tai
min ba


Jakar tawa ta zazzage a ƙasa ta fara duba kayan cikin ta, bakin ta a taɓe

"kije wajen wanke wanke ki samu ƙananan sabulai ki haɗa ki zo kiyi wanki"

Miƙewa nayi na fita, nai mamakin dana ƙarasa wajen wanke wanke na samu sabulai,
kamar ba da kuɗi a ka siye su ba, tsinta na fara yi har na haɗa iya wanda nasan zai
ishe ni sannan na tafi ɗakin


Kaya na na ɗiba sannan na je bayan ɗakin inda banɗakin mu yake na wanke kayana
tas sannan na shanya



Wanka na shiga da ragowar sabulun na saɓi jikina kamar ba gobe, don a



Don kuwa a azore ban isa in samu wannan damar ba, sai dana gama wanka na sannan
na fito



Sai yamma sannan kayana suka bushe na kwashe, a ranar dai ban koma kitchen ba
sai kashe gari


Cikin hukuncin Allah na fara aiki a kitchen amma ba abinda nake yi sai aike, dauko
wannan ɗauko wancen haka dai



Kafin ka ce me wannan har na zama ƴar gidan, na son komai na kitchen, sannan na
san inda ake ajiye komai


Gidan cin abincin hjy munnira gidane da a kullum a ke dafa kusan buhu biyu na
shinkafa da ta tuwo


Babu irin variety na abincin da ba a yi, waina sinasir, alkubus fankaso, ta
ɓangaren shinkafa ma


Jollof rice fried rice, duk dai wasu sunfari na dafa abinci ana yi, ba wai duka a
ke ci anan ba, akwai waɗanda ake fita da su,


Don kuwa akwai certain hotels ɗin da suke zuwa suna yin order abinci anan gidan,
ga kuma costomers da suke zuwa suna siya su tafi da shi



Ga waɗanda suke siya su ci anan, akwai wasu mutane ma da ake musu abincin gidajrn
su anan, kullum akwai abincin da za a dafa na certain gida akai masa



Nakan yi mamaki amma dana ji cewar yawanci gidanjen ministers ne da house of
reps da senators ake kai musu waɗanan abincin saboda mutanen da suke tarawa sai na
daina mamaki duk da dai ban san ko su waye ba



don haka aiki a gidan nan in aka tashi tun safe sai mukai ƙarfe 10 :00pm bamu
gama ba


Amma kuma mu girki ne kawai akwai ƴan wanke wanke, akwai kuma ƴan service, akwai
masu kaiwa gidaje, group group ne kowa da group ɗin sa kuma kowa ya san aikin sa



******************



*b̫a̫y̫a̫n̫ s̫h̫e̫k̫a̫r̫a̫ b̫i̫y̫u̫*




Na zama ƴar gida yanzu don kuwa ba abinda bana shiga ayi da ni ta ɓangaren
girki,


A lokcn ne hjy munnira ta ƙara buɗa restuarant ɗinta inda yanzu babu abinda ba a
yi, snacks ne ɗrinks ne, duk daia abinda kake so idan ka zo restuarant ɗin mu,


Kuma kullum cikin hukuncin Allah ƙara samun costomers muke yi, yanzu ba a shakkar
bani girki ko ya yake don kuwa a gaskiya na iya



Kasancewar ni ce ƙarama a kitchen yasa kowa sai kaji yace asmau don Allah juya
min kaza, kwashe kaza, wannan ne ya sa ni ko wane ɓangare na kitchen ina shiga


Ba kamar cooks ɗin kitchen ɗin ba, yadda in a ɓangaren sarrafa shinkafa kake to
ana zaka zauna, in a ɓangaren snacks kake to anan zaka zauna, haka ma in a ɓangare
drinks kake ko miya ko salad ko wani abu na kitchen



Ma'aikatan a rarrabe suke kowa yasan aikinsa, amma banda ni, ni ina kowane
ɓangare kuma duk inda naje sai na tabbatar da cewar na koyi abunda suke


Wannan ne yasa a kitchen ɗin nai fice tunda komai aka bani zan iya kuma zan yi
shi kamar ba ƴar ƙaramar yarinya ce tayi ba



*****************


Sabit yana zaune a office ɗinsa cikin fararen yadinsa waɗanda kana kallon su
kasan ba ƙananan kuɗi aka sa wajen siyan su ba, wayace a hannunsa yana ta danna wa


Tun ɗazu yake kiran ta amma bata ɗauka ba, tsaki ya ja tare da ajiye wayar

"wallahi sam banga amfanin wayar mata ba ace mutum sai yai ta kiran ki a waya amma
wai bakya kusa da wayar" be gama mitar sa ba sai wayar tashi ta fara ringing


Tune ɗin daya saka mata kenan don haka wayar tana fara ringing ya gane ita ce,
idon shi ya kai kan screen ɗin wayar inda aka rubutu *only u*


Ɗan tsaki ya kuma sannan ya ɗauka a yangance kamar wani mace

" *SD* don Allah kayi haƙuri wallahi ina sallah ne ka kira" duban shi ya kai kan
agogon bangon ɗakin inda ya ƙarfe 03 :15pm


*only u sallah me kike yanzu kar dai kice min azahar"

" wallahi *SD* na shiga meeting ne shiyasa ban samu nayi sallah akan kari ba, ya
kake "


"amma meeting sai ya hana ki sallah wai sai yaushe zaki san mahimman cin sallah
haba only yanzu haka zamu yi aure ki dinga nuna wa yaran mu, yanzu lkcn sallah
bazaiyi ba a bar abinda ake yi a tafi ai sallah ba"

" *SD* kasan matsalar bank fa su koman su a ka'idance yake kar ka damu in shaa
Allah tarbiyya me kyau zan muyi wa ƴaƴan mu, kaji"


Ta shiga kalailaye shi da kalaman da tasan suna kwantar masa da hankali kafin
kace meye wannan har sun koma kamar ba abinda ya faru,



Sai da suka gama shan soyayyar su sannan sukai sallama akan zai zo da daddare,
daga nan sukai sallama kowannen su zuciyar su tana alfahari da kuma ƙaunar junan su




*Menu of d day*

🍲```Veg cous cous with kidney sauce``` 🍲


```ingredients```

_Cous cous_
_Butter_
_Cabbage_
_Peas_
_Carrot_
_Canned sweet corn_


```recipe```

1) ki wanke carrot ki yanka shi size ɗin da kike so, sai ki wanke peas sai ki
haɗa su ki tafasa su da ɗan gishiri, tafasa ɗaya sai ki sauke ki wanke su da ruwan
pampo wannan wankewar zai sa su suyi shar kuma su rike kalar su sai ki ajiye a gefe


2) a wanke cabbage a yanka sannan a ajiye shi aside, sweet corn ɗin shima a tsane
ruwan shi a ajiye shi gefe
3) ki ɗaura ruwan zafi, idan ya tafasa, sai ki ɗauko cous cous ɗinki a cikin bowl,
sai ki ɗan zuba masa dan ruwan zafin, ba dayawa ba ya ɗan sha, *a zuba yadda bazai
yi wa cous cous yawa ba* sai ki ɗan bari ruwan ya tsotse

4) ragowar ruwan daya ke tasafa a kan wuta sai ki saka colander ```(in babu
colander zaki iya yin na buhu amma a tabbatar da buhun be taɓa ruwan ba)```a kan
sa, sannan ki kawo jiƙaƙƙen cous cous ɗin ki, ki zuba, ki kawo kayan peas da carrot
ki zuba ki rufe ya turara


5) idan ya ɗanyi wani lkc kika buɗe kika ya dahu sai ki sauke, ki juye cous cous
ɗin a wata roba, ki zuba melted butter, da sweet corn da kuma cabbage sannan a juya
a zuba a food flask
~bon appétit~


```kidney sauce```


```ingredients```

_Kidney_
_Attaruhu_
_Albasa_
_Maggi_
_Man gyaɗa_
_Tomato paste_
_Curry_
_thyme_


```recipe```

1) a wanke kidney a cire tsakiyar nan don kuwa wataran har tsakuwa ake gani


2)sannan sai ki tafasa ta da albasa da maggi da thyme, idan ya tafasa sai ki tsame
ta a gefe


3) a grating attaruhu da albasa, ki saka man gyada kaɗan a tukunyar ki sai ki dan
bishi da albasa da tafarnuwa, idan man ya ɗau zafi sai ki zuba attaruhun ki da
albasa a barshi ya soyu


4) idan ya ɗauko soyuwa sai ki ɗauko kidney ɗin nan ki saka ki ƙara maggi, tomato
paste sannan ki sa curry sai ki rage wuta ki bar shi ya ƙarasa

```bon appétit```

*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛
~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 3




Badia ƴa ce a wajen alh hamza da matar sa hjy bilki, dukkan su
ma'aikatan banki ne, inda alh hamza yake aiki a *CBN* ita kuma hjy bilki take aiki
a zenith bank


Ƴaƴan su uku mata biyu sai namiji 1 hauwa ita ce babbar ƴar su dr. ce a asibitin
general hospital dake abuja tana da aure da ƴaƴa biyu


Sai badia wacce a yanzu take aiki a zenith bank amma ba branch ɗin su ɗaya da mmn
ta ba, sai ɗan autan su nura wanda yake karatu har yanzu a china



Rayuwar gidan su badia irin rayuwa ce ta western style babu ruwan iyaye da
matsawa ƴaƴan su duk abinda kayi dai dai don haka rayuwa ake yi ba kwaɓa balle
harara



Yo ina ma suka ga iyayen nasun balle su kwaɓe su in suna ba daidai ba, kuma
cikin hukuncin Allah sai ya shirya musu ƴaƴan babu me abin ashsha masu zuciyar
samun na kansu ne amma batu addini sai a slow



Badia sun haɗu da sabit ne lkcn da ya zo bank ɗin su bayan ya samu matsala da
master card ɗinsa sai ya kasance badia ce ta gyara masa matsalar



Badia irin dogwayen matan ne masu ƙirar coca cola, fara ce amma duk da farin ta
hakan bai hanata shafa man da zai ƙara mata haske ba, Allah yayi da son gayu, don
haka take da manema dayawa, gayun ta da kyan ta da kuma iya ɗaukar wankan ta yasa
take taƙama da kanta
Tunda ta ɗaura idon ta akan sabit taga gaskiya wannan yayi mata don haka sai tai
tayi masa salo salo daban daban ko zai taya, amma ga mamakin ta sai taga kamar ma
tana yi da dutse ne



Don haka sai ta kau da ƴar kunyar nan tamu ta mata tace masa suyi exchanging
contact incase ko wani matsalar zai kuma tasowa ba sai ya sha wahalar zuwa bank ba



Sabit be kawo komai ba don haka sai ya yadda da abinda tace, ko bayan da to koma
gida ta ɗauka zai kira ta amma sai taji shiru, kwana da kwanaki kullum jiran call
ɗin sa take amma shiru



Rannan sai ta kira shi inda ga mamakin ta wai yama manta da ita, sam bata ji
daɗin yadda yai mata ba amma kuma sai ta ɗau ƙudurin in shaa Allah daga lkcn ba zai
kuma cewa ya manta da ita ba



daga lkcn ta zama me kiran shi, tun yana basarwa har yazo yana ɗan dauka har
kuma cikin hukuncin Allah suka fara soyayya har gashi suna shirin gabatar da junan
su ga gabatan su don a tabbatar da soyayya su,



******************



Sabit ɗa ne na huɗu kuma ɗan auta a wajen hjy fatima da kuma alh bashir,
mahaifiyar shi shuwa ce mace me kyau da kwarjini ga ƙaunar ƴaƴan ta, ita bata damu
ba ko zata ɓatawa kowa indai hakan zai farantawa ƴaƴan ta wannan soyayyar da ƙaunar
da take wa ƴaƴan natan ne ma har yasa ta sa mijinta ya gina wa

Please Login or Register in order to submit comment