You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuka anty fannah ta fito daga office
"asmau dama sabit allurar zubar da cikin nan ya sa akai miki" ta faɗa tana kuka


Dakewa nayi don bana son taga weakness ɗina


"anty kaɗɗara tace kuma shima babyn Allah dama yayi ba me taka ƙasa bane, don haka
babu komai Allah yana kallo kuma zai saka min" kuka ne yaci ƙarfi lallai yau na
tabbatar da tsanar da sabit yake min ba kaɗan bace



Sai da muka gama kukan mu sannan muka kama hanyar gida bayan mun sai magani


********************


Sam sabit ya manta ma da wata sai asmau balle har ya tuna da cewar zata ɓari at
any moment, hidimar sa kawai yake yi


A yunwace ya ƙarasa gidan yai mamakin da ya shiga ya kan dinning table ɗin ba
komai, badia ya kira sannan ya tambayeta me ya faru yau abai girki bane ko mee


"wallahi ban sani ba ni tunda ta fita da yamma ban kuma ganin ta ba" gabansa ne ya
faɗi kai dai ace ta san abinda yai mata kuma ta gudu kai ina zata gudu ai har yanzu
batta da wannan wayon ƙila tana ɓangaren fannah


Miƙewa yayi ya kama hanyar burin shi yaga asmau acan in bai ganta ba yanzu tayaya
za ayi ya fara rayuwa ba ita, ƴar iskar yarinyar duk da dai ba kalar sa bace amma
kuma Allah ya bata wani baiwa da duk wanda ya fara sanin ta bazai iya rabuwa da ita



Gudu gudu sauri sauri a haka ya ƙarasa part ɗin fannah, itama a kulle yake bata
nan, hankalin sane ya tashi, isma'il ya kira bayan ya ɗauka ne yake tambayar sa
fannah


Inda isma'il yake cewa ta cemin suna asibiti ita da matar ka, wani ajiyar zuciya
yayi wanda shi kansa bai san zai iya ba Allah ya taimake shi
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 20 🌹




Basu suka dawo ba sai kusan 08 :00pm sannan muka dawo, directly part ɗin anty
fannah muka wuce sallah kawai nayi sannan na kwanta sai bacci ya kwashe ni



Sabit yana ɓangaren sa amma ya kasa zaune ya kasa tsaye tunanin sa kar asmau ta
faɗawa fannah yai mata allura gaban shi sai faɗuwa yake yi


Sai kusan 09 :00 sannan ya miƙe, badia da ke kusa da shi ta tambaye shi

"sabit ina zaka a daren nan"

"zanje in duba yarinyar nan ne dare yayi a maimakon ta zo ta kwanta" inji sabit


"to meye na damuwa da ita in ta gaji ai dole ne ta samu wurin kwanciya ko, amma ka
wani tada hankalin ka sai kace wata matar ka"


Wani kallon banza ya bita da shi sannan ya fice, ɓangaren fannah ya dosa, yana
shiga ya tarar da fannahr tana kallo


Sallama sukai shida badia suka shiga, kallo ɗaya fannah tai musu ta kau da kanta
gabaɗaya ta dawo daga rakiyar sabit ɗin balle wannan ƴar iskar matar tasa



"fannah don Allah ina asmau take naga har yanzu bata dawo ta kwanta ba" bata kalli
inda suke ba ɗakin da asmaun take kawai ta nuna masa da hannu


"amma ta riga tayi bacci don haka zaku iya tafiya da safe in ta tashi ta koma"
tsayawa yayi yana kallon fannah kai gaskiya da sake bazai taɓa iya barin asmau ta
kwana a wani wajen ba sai da ɗakin ta


"bari inje in taso ta" ya faɗa yana yin hanyar ɗakin, miƙewa ta bi ta sha gaban
sa
"baka isa ka tashe ta ba ai matar ka ce indai har ka matsu ta koma ɗakin natan sai
dai ka ɗauke ta in kuwa ba haka ba sai da safen"


Nannaɗe hannun rigar sa yayi yana shirin shiga ɗakin, sai badia ta tare shi

" *SD* kar kace min kana son shiga ka ɗauki yarinyar nan da kanka, ka barta mana da
safen ta dawo da kanta"


Kallon ta be yi ba ya shige, masifa ta fara yi tana cewa wallahi indai har ka
sake ka ɗauke ta wallahi zaka sani don ni kuwa ban yadda in yi sharing miji da wata
ƴar aiki ba



Kinkimar asmau yayi yai mata ɗaukar jarirai sannan ya kama hanyar fita da badia
a bayan sa tana ta balbala masa bala'i inda shi kuma ko ta kanta be bi ba



Anty fannah ta murmusa dama abinda take som sani kenan da sabit shin anya yana
son asmau kuwa ko a a amma ita a ganinta yana son asmaun amma kuma me yasa yake
mata haka



Kuma duk wani shawarar da yakamata ya bawa asmaun amma duk da haka sabit ɗin ya
kasa sallamawa wannan abun da ɗaure kai yake


Sabit har cikin ɗakin ta ya kai ta badia na biye da shi,

"to tunda ka kawo ta sai ka ajiye ta muje ko" ta faɗa masa kamar wani ɗan yaro,
abin nan yai masa ciwo yadda take nuna halin ko in kula da asmaun duk kuwa da yadda
asmaun take kular mata da gida



Wani banxan kallo ya bita da shi wanda ya sata jan bakin ta tai shiru, yana son
rungume asmau kafin ya fita amma kuma badia ta ƙi barin ɗakin


Haka ya haƙura ya fice bayan ya gyara mata kwanciyar ta sannan ya tafi ɗakin sa
badia ce ta shigo tana wani rangwaɗa tsab ya fahinci me take so amma sai ya basar
daga baya ma data ishe shi sai ya kore ta ya rufe ɗakin sa




Tinanin asmau ne kawai ya faɗo masa arai yana jin yarinyar sosai a ransa amma
gaskiya bazai taɓa barin ta ta haifa masa ƴaƴa ba



Sai da ya tabbatar da badia tayi bacci sannan ya kama hanyar ɗakin asmaun tana ta
baccin ta kamar yadda ya kwantar da ita
Kusa da ita ya kwanta sannan ya janyo ta jikin sa ya dinga shafa mata bayanta har
bacci shima ya kwashe shi



********************


Na riga shi farkawa ganin yadda yake kwance yana ta sharar baccin sa ya sani zame
jikina a hankali na shiga banɗaki tare da ɗauro alwala



Ina fitowa na tarar ashe har ya fice, sallah nayi sannan na kuma kwanciya don kuwa
ji nake yi kamar bacci be ishe ni ba



Bacci ne ya kwashe ni, cikin baccin nawa naji muryar badia tana min magana


"sai yaushe zaki tashi ki haɗa mana breakfast gashi lkcn office zai ƙule" miƙe wa
nayi sannan ta kalle


"matsayin mu ɗaya a wajen sabit kamar yadda kike tunƙahon mijinki yake haka yake
tinƙaho da ni a matsayin matar sa don haka kowacce tata ta fish she ta daga yau na
daina bauta wa ko wa kowane ɗan iskan yayi aikin sa an gama wannan wasan"


Sakin baki tayi tana kallo na lallai ma yarinyar nam,
Sabit ta ƙwala wa kira wai yazo ya yi magana


Shigowa yayi shima kamar gaske bayan ya haɗe girar sama data ƙasa


"me yake faruwa ne a ana anga ana ta ƙwala min kira"


" *SD* yarinyar nan taƙi tashi tai mana breakfast nai mata magana tana gayamin
maganar banza"

Juyowa yayi ya kalle ni wacce ni kuma idon yake ƙyam akan sa inga irin matakin
da zai ɗauka


"ke sai yaushe zaki ki haɗa mana breakfast ne"


"bani da lfy ko kana don ingaya maka abinda yake damuna ne" shiru yayi sannan sai
ya juya ga badia sannan yace mata



" Muje mu ƙyale ta tunda tace bata jin daɗi inta warke ta koma duty" ya faɗa yana
tura ta don su fita
" a a ku dawo in faɗa muku abinda ke damuna mana ya kuka fita ai kamata yayi kiji
ki san me ya same ni" na bita da wannan ina ganin ta juyo shi kuma ya hankaɗa ta
tare da riƙe mata hannu yana janta


Ai na dawo daga rakiyar sabit zai sqn ya zubar min da ciki wallahi sai ya
gwammaci kiɗa da karatu, wallahi sai ya san asmau ya taɓa bari dai in fita mu haɗu
da anty fannah nasan zata bani shawara


Guduwar ma dana ce zan yi na fasa wallahi sai na zauna a gidan nan na haifawa
sabit baƙaƙen ƴaƴa sannan hankali zai kwanta in ban haifa masa baƙaƙe ba ban rama
wulaƙancin da yai min ba



Wallahi sai ya gane bashi da wayo da asmau yake to nima yanzu lkcn da juya kaina
yayi na daina ɗaukar order daga wajen wani nima daga yanzu na zama ogar kaina



********************


Sai da na tabbatar sun fita sannan na tafi ɓangaren anty fannah, tana zaune ta
zuba uban tagumi kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa, na shiga da fara'a ta


Tana kallona tace

"lallai yaro be san ciwon kansa ba wai har kin wats tsake kin koma duty"


"wane duty ba abinda nai musu ai yanzu ciwon ido zan zame musu a gidan nan kuma
wallahi sabit abinda baya so shine baƙaƙen ƴaƴa ko wallahi anty fannah sai na haifa
masa sai na cika wa sabit gida da baƙaƙen ƴaƴan daya baya so" tsayawa tayi tana
kallo na


"asmau da niyyata in saka daddy ya ƙwatar miki ƴancin ki, yasa sabit ya sallame ki
ke ma kije ki ne mi wanda yake sonki kk aura"


"haba anty fannah ai da kin cuce ni, sabit shi nake son ya kasan uban baƙaƙen
ƴaƴana, ko yana so ko baya so wallahi sai na nuna masa shi ƙaramin ƙwaro ne a
wajena, abinda ba abinda ban sani ba nashi, wallahi anty fannah cikin sakan ƙalilan
zan iga juya sabit, kawai dai yana da taurin kai da tsatstsauran ra'ayi, amma
wallahi na ɗau ɗamarar sai na nuna masa banbanci aya da tsakuwa, sai na nuna masa
cewar wasu matan ma suna suka tara, wani ƙyalƙyal banza na mace ba lallai ta zama
me quality ba"


Tsayawa kawai tayi tana kallona na bata mamaki sosai, yama za a yi in tafi in
ƙyale sabit a haka ai ya ci galaba ta wannan yaƙi ne ya soma wallahi sai naga
ƙarshen yaƙin nan sai na haifa wa sabit ƴaƴa baƙaƙe mu ga yadda zeyi kuma wallahi
ni da sabit ya raina sai na zame masa ciwon ido
"anty fannah kayan gyara nake so" har yanzu bata daina mamaki na ba don haka sai
ta jawo ni ta zaunar dani tare da cewa


"asmau ko dai ɓarin nam ne ya juyar miki da ƙwaƙwalwa, naga duk kin rikice kin
zama wata ba asmaun da na sani ba"


"wallahi anty fannah nice hankali kawai nayi, kuma nasan ciwon kaina wanda yayi
sanadiyyar rasa baby na innace na barshi haka ai banyi ba wallahi sai na ƙun sa
masa abinda har abada bazai taɓa mantawa ba amma sai da taimakon ki sai na haifa
masa baƙaƙen ƴaƴa iya son raina, goma ma zan haifa masa ko sha biyar"



Tabbas asmau ta zauce inji fannah, zaman dirshen nayi a gaban ta ina ta lissafo
mata irin plan ɗin dana ɗauka zan aiwatar akan sabit da matar sa wallahi sai sun
san shayi ruwa ne


Tun tana basarwa har tazo ta fara bani tips na mallakar miji a hannun na ada in
tana faɗa min yana shiga ne ta kunnen hagu yana fita ta kunnen dama


Amma yanzu tsab nake haddace wa ai yanzu za a fara wasan ada ba komai akayi ba,
amma yanzu wasan zai fara


Sai yamma na kama hanyar part ɗin mu abinci na naje na dafa lafiyayye na zuba a
cooler na ajiye, na shiga ɗaki na ɗau wanka na sai da na turare jikina da turare na
daƙƙo wata fitted gown da mukai da anty fannah na saka



Falo na fito ashe ita uwar gidan ta dawo ma abanji dawowar ta ba, cooler dana
ajiye akan dinning table ta buɗe ɗan wake ta ci karo da shi da mai da yaji sai
kunun tsamiya


Wani shegen kallo ta bini da shi

"bana cin wannan ki sake ɗaura min wani"

"ai ba naki bane nawa ne, ai na dena yi wa kowa girki duk wanda ya ji yunwa ya
shiga kitchen muga in zai iya"


Hannu ta ɗaga zata kwaɗa min mari a dai dai lkcn sabit ya shigo


"ke badia me ya haɗa ku zaki mare ta"


" *SD* wannan yarinyar wai me take taƙama da shi ne, gaskiya na fara gajiya da zama
da ita ya kamata a sallame ta"


Juyowa yayi zai min faɗan da yasa wani ƙayataccen murmushi na sakar masa tare da
kaɗa masa ido cikin kissa
Tuni ya maida wuƙar tasan sannan yai gyaran murya


"me tayi miki ne da zaki dake ta, bana son hayaniya"


"ni dai kawai na gaji da ganinta" in da inda ya fara ya rasa kalma ɗaya ma da zai
ce sai wani kame kame yake



Dining na nufa n zauna na fara cin abinci na ina jinta tama jarabar wai ban kai
wannan matsayin ba tana ƙara yi wa sabit maganar ya kore ni ko ita ta barmana gidan


Lallaɓa ta yayi ya hau sama inda ni kuma na zauna ina ta cin abincina, nai
mamakin da ya gama kintsawa ya sauko ya ci ɗanwaken


Ita kuma badia tana nan kan bakan ta bazata ci ɗan wake ba sai dai in dafa mata
wani abun, iskar da ta ɗauko ta ma ban kalla ba balle ita sabit ɗin ma nai mamaki
dana ga sam be ce komai ba
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 21🌹
Tun daga lkcn na zame musu ciwon ido sai haƙuri sai abinda na ga dama nake yi a
falon sam sabit sai yayi wani sanyi ashe abun nashi ma iskanci ne



Tuni na ajiye girkin sai abinda naga dama nake dafawa wank lkcn badia taci wani
lkcn kuma tace ita bata so kuma wallahi ruwa bana bata balle in ɗaura mata wani abu



Tuni na ƙwatar wa ƴanci sam yanzu sabit baya min abun da yake min ada kamar ma
shakka ta yake yi ko ince tsoron badia tasan akwai abinda yake shiga tsakanin mu
yake oho mishi



Lallaɓawa kuwa sai dai in be shigo ɗakina ba yai ta lallaɓa ni yana min wani
daɗin bakin wai in kwantar da hankalina zai sanar da badia cewar ya mai da ni matar
sa official



Hmmm kawai nake bin sa da shi besan ni da nawa ƙudurin a raina ba, abu kaɗan idan
tayi sai in fara "ke kin san meke faruwa a gidan nan in ƙafa ta ɗauke kuwa, kina
can kin saki baki kina bacci kamar mushe" 🤣🤣🤣🤣🤣



A lkcn zaku ga rawar ƙafar sabit nan da nan sai ya janye ta yai ɗaki da ita sam
bazai bari mu ƙarasa faɗan ba, da gayya nake tsokanar faɗa, ko shi ma gogan yana
zaune yana kallo sai inzo in canja channel ɗin kuma in ajiye remote ɗin inyi gaba
sam bazai taɓa ce min ko mai



Duk wata hanyar dana san zan bi in takalo sabit faɗa muyi don in tona masa asirin
shiga ɗakina da yake yi nayi amma sam ba nasara



Daga ƙarshe na tattarar na watsar na ci gaba target ɗina na neman ciki ido rufe
abu kamar me ba ciki ba alamar sa, har wurin anty fannah naje ta bani maganin da
take sha amma shiru, lallai ma kodai sabit yana yin wani abu ne a nashi ɓangaren
sam ban sani ba amma ciki de ina nan ko ba daɗe ko ba jima sai nayi shi




********************



Wani project ne aka tura sabit lagos zai je yayi na shekara uku, sam ban so ba
saboda ba lallai bane ya tafi da mu ba tunda ina lagos ina abuja ai ba wani nisa
bane kuma ba lallai ne mummy ta barshi ya tafi da mu ba amma gaskiya ni ina son bin
sa don haka ko daya dawo ɗakina da daddare ranar na kai shi makka da madina a ƙafa
da haɗine na karɓo na musammam a wajen anty fannah na sha
Muna kwance yana min wasa da gashi na sai nace masa


"sabit kai da wa zaku koma lagos ɗin"


"kina son zuwa ne, kinga yarinyar nan ƴaɗ ƙaramar ki da ke amma baki son rabuwa da
mijinki ko, shike nan zan wa mummy magana sai mu koma tare kin ga sai muci karen mu
babu babbaka tunda badia baza ta ba"


"cewa zaka yi ka daina bin dare de kana lalube" mintsini ya mannara min au lalube
ma nake yi



Wasa mukai da sabit sosai kafin mu kwanta bacci,



Ko da lkcn tafiyar yayi badia taji da ni za a wai don in dinga yi masa girki sai
hankalinta ya tashi, itama sai taje



Sam sabit be so badia tace zata ba amma babu yadda ya iya har wani nuna jin daɗin
sa yayi wai zamuje tare hmmm ni dai kallo shine nawa



Shirye shiryen komawar mu lagos ya kankama inda sabit ne ya karɓo wa badia
transfer na wajen aiki, sannan muka kama hanyae birnin yanki



Mun sauka lagos lfy gidan flat ne me 4bedroom a apapa kowccen mu ta ɗau ɗaya inda
sabit ya ɗau master bedroom ɗin



Zaman mu lfy sam bana shiga sabgar su haka suna basa shiga tawa girki ne inna yi
in badia na da ra'ayi taci in bata da ra'ayi kuma sai ta siyo nata ba wanda yake
shigar sabgae wani tsakani na da ita



Rannan da daddare sai sabit yace badia ta shirya su fita, ina kallom su aka ci
kwalliya har tana cewa


" *SD* dinner zaka kaini restuarant" sam be tanka mata ba suka fice, ni kaɗai ma ci
dinner ta ranar kuma sam abin ma be dame ni ba saboda ni akwai zaman da nake yi
kuma wallahi ko baɗe ko ba jima sai na cimma buri na



Kusan awan su guda a waje sai gasu sun dawo, fuskar sabit kamar wacce aka aiko wa
da mala'ikan mutuwa tai jajawur kamar bashi ba
Inda ita kuma badia ita ma tata fuskar sharkaf da hawaye



"wallahi bazata saɓu ba lallai ma badiar nan wallahi bazan yadda ba"


"don Allah sabit kayi haƙuri wallahi bada son raina banr naga jikina ne yake
attracting ɗinka zuwa gare ni kuma idan haihu nayi loosing shape ba lallai ne ka so
ni ba shiya sa na cire mahaifar" 😱😱😱


Wai kunne na ne yajiye min ko kuma mafarki nake yi


"wannan ma maganar banza ce kice min wai kin cire mahaifar ki akan wani banzan
excuse naki, ni da naƙe expecting ƴaƴa na daga gare ki amma shime kika cire
mahaifar ki"



Faɗa ya shiga yi sosai ni dai dana ga abin nasu ba na ƙare bane sai na ahige
ɗakina amma gaskiya badia tayi kuskuren cire mahaifa



Wallahi akan wani ƙato bazan cire mahaifata ba, har kusan 11 :30 na dard suna
bala'i akan cire mahaifar


Ni dai bacci na nayi na ƙyale su, ko da na tashi da safe ma atmosphere ɗin gidan
ba daɗi tunda dai masu gidan suna faɗa



Haka dai akai ta zama ba daɗi don ɗan zuwa ɗakina ma sam ya daina ni ma ta shafe
ni, duk ya bi ya tsangwami kansa



Allah ya ƙara shine kawai abinda yake fita daga bakina, da ka barmin cikina da
tuni na haife shi amma gashi yanzu inda ya kai kansa Allah ya ƙara ai yanzu bashi
da wani mafita sai dai ta haihuwa da ni



********************


Sabit yana zaune duk abin duniya ya ishe shi, yanzu ya zaiyi shi fara neman matar
ma da zai aura ta haifa masa fararen ƴaƴa shine aiki


Yawancin matan yanzu ba farara bane farin kanti ne, kuma baya son kawo fara kamar
badia ya ƙara ƙarawa kansa aiki, inda ace zai samu fara kamar asmau wallahi da ba
abinda zai dame shi amma yanzu ga shi nan ya zama shi ba ga tsunstu ba baga tarko
ba



Har yanzu bashi da ra'ayin haihuwa da asmau kai sam ma bazai taɓa yadda ya haihu
da itaba, shiyasa ya bata turaren da take amfani da shi


Daga china ya taho da shi muddin mutun zai juri saka shi to har abada bazai taɓa
bari asmau ta haihu da shi ba, turare ne kamar kowanne amma ƙamshin same illa ne,
ƙamshin sa yana lalata ƙwan haihuwa



Buɗewar ƙofa yaji yasan ba me shigo masa ɗaki sai badia don haka sai ya haɗe rai
sannan yace


"me ya kawo ki" ko kallon inda take be yi ba


" *SD* na zo ne muyi magana, wallahi ban cire mahaifa ta ba har sai da san zamu
samu solution"

Jin kalmar solution ɗinne ya sashi juyowa tare da tsare ta da idon sa


Ganin ya kalle ta ya sa ta ƙaraso qa har da riƙe masa hannun sa

" *SD* me zai hana mu samo surrogate mother, wacce zata haife mana ƴaƴan mu da ƙwai
na da sperm ɗin ka kaga shike nan, ni ban yi loosing shape ɗina ba, kuma ga ƴaƴan
mu"



Zame hannun sa yayi daga nata


"kina nufin mu nemi wata arniya ta renar mana ɗa a cikin ta sannan ta haifa mana
shi sam baza ayi haka da ni ba"


"ba arniya ba, ga asmau ai an ɗaura muku aure ba sai muyi amfani da ita ba, ba
hankali gareta ba sam ba ganewa zatai ba"


Shiru yayi yana tunani tabbas wannan shine hanyar sa kawai ta samun fararen yaran
da yake so wato kenan ƙaddarar sa ce sai asmau ta haifa masa ƴaƴan sa kenan ko


"to kije kiyi mata maganaa inta yadda shi kenan in kuma bata yadda ba wallahi sai
na ƙara auren wacce zata haifa min ƴaƴa"


"zama ta yadda" ta faɗa da murnar ta tana miƙewa



Ina kwance a ɗaki ima ta shiɗin kwanciya sai badia ta shigo nai mamakin ganin ta
amma kuma sai na dake tunda take bata taɓa shigo min ɗaki ba nasan akwai abinda ya
kawo ta



stool na bata ta zauna, sannan sai tace min

"asmaj kamar yadda kika sani na cire mahaifa ta saboda wallahi ni bana son haihuwa,
amma kuma sabit yana so don haka sai muka yanke hukunci sabit zamu dasa miki cikin
a jikin ki in ya so sai ki haife mana shi"


"ban gane ba " nace mata


"za a saka miki ƙwai na da sperm ɗin sabit a cikin ki sai ki haife mana"


"kina gani sabit zai yadda da hakan" na tambaye ta

"ƙwarai kuwa da sabit muka tattauna shi yace ma in miki maganar" takaicine yazo min
har maƙogwaro na wani abu ya tokare min wato sabit jini nane baya so ko wai sai
yaushe zan samu ƴanci ne sai yaushe zan samu cikar buri na



Kallon ta nayi cike da tsana sannan nace mata

"kije ki gaya masa ciki na bazai ɗauki renon sa ba don haka yaje ya samu wacce zai
biya kuyi abunku amma wallahi ni asmau bazan yadda ayi wannan abun da ni ba"



Kuka na fashe da shi na takaici lallai sabit ashe abin nashi har ya kai haka
wallahi bazan renar masa ɗa ba


Kukan da taga ina yi ne ya sata miƙewa sannan ta fice, kwanciya nayi akan gado na
fashe da kuka


Wannan wulaƙancin da me yayi kama, wai me nayi wa sabit ne haka daya tsani sooooo
much shin baƙi laifi ne ko kuma haɗa mun da Allah yayi sam be ɗau wannan a matsayin
ƙaddara ba



Wallahi baza ta saɓu ba yacce matar sa ta cire mahaifar ta ya kasance baza ta
ƙara haihuwa ba dole ne ya haƙura nima gashi tunda nai ɓarin nan ban kuma samun
ciki ba ko menene dalilin oho


Takaicin sabit ranar hanani bacci yayi kwana nai ina kuka dana gaji da kukan sai
na miƙe na ɗauro alwala ina kuka ina faɗawa Allah matsololina duk da yasan a halin
da nake ciki amma kuma ina sake gaya masa ya kawo min ɗauki



Anan kan sallayar bacci ya kwashe ni da asuba na farka sakayau haka naji ni, da
wuri

Please Login or Register in order to submit comment