You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowanne daga cikin
ƴaƴan natan ɓangaren shi a cikin tafkeken gidan da suke,



Sannan ƙwararriya ce wajen haɗa sanwa, idan ta shiga kitchen ta haɗa dinner sai
mutum ya manta sunan sa saboda tsabar daɗi da kuma tsari, wannan ne ya sa ta sha
alwashin duk ɗan ta daya yi aure matar bata iya girki ba sai ya ƙara kuma a hakan
ake har yanzu



Alh bashir mutumin adamawa ne fulani ne fari kyakkyawa da shi, wannan kyan na
bayin Allahn nan yasa idan kaga ƴaƴan su sai ka saki baki barin ma ace sabit wanda
kamar su da hjy fatee har ya ɓaci, don haka duk cikin ƴaƴan su ya fi su fari da
kyau



Ƴaƴan su huɗu isma'il shine babba, likita ne matan sa biyu, ta farkon auren
soyayya ne, amma matar bata iya girki ba don haka sai ta saka shi ƙara aure inda
ita ma ta biyu ya kasance da babu ce hausawa suka ce gwanda ba daɗi
Wannan yasa har yanzu isma'il a ɓangaren iyayen shi yake cin abinci, na biyun su
shine sulaiman shi ma matan sa biyu duk babu gwanda wajen girki sai na uku mansur
wanda shima matan nasa biyun amma su da ɗan sauki sauƙi



Sai auta sabit wanda ake ta shirye shiyen auren sa tooo shin badia ta girki
kuwa bari dai mu bisu mu ji ita kuma ya nata yake



********************




Sai ƙarfe 06 :30pm na yanna sanna ya shigo gida duk saurin sa na dawo wa gida da
wuri don ya samu ya shirya ya tafi wajen badia amma hakan bai samu ba


Wanka kawai ya shiga yana cikin wankan ne ma yaji wayar shi na ringing ko be gani
ba yasan badia ce don ringing ɗin daya saka mata ne



Hankalin sa akwance ya ƙarasa wankan sa ya fito, yana fitowa wayar tana kuma
shigo wa, towel ɗin da ke hannun sa ya ajiye sannan ya ɗau wayar

" *SD* sai yaushe zaka zo tun 05:00pm nake jiran ka amma shiru kamar bazaka zo ba"


"only yi haƙuri wallahi aiki ya tsare ni a office, more over ina son mu haɗu da alh
ku don ina son jin yadda za a tsara wannan lamarin don na ƙagu in ganki a gidana"


Ɗan dariya tayi irin na nuna jin daɗi sannan tace masa

"kamar kasan kuwa ya dawo shima, bari in gaya masa kana son ganin sa don kar ya
fice"

"dats my only shiyasa nake son ki, kuma nake ce miki only don daga ke ba ƙari" ya
faɗa hankalin shi a kwance don shi mutum ne da baya son tarkacen mata


Tayi bala'in jin daɗin wannan maganar tasan wanda har ta kasa ɓoye murnar ta ta
fara zuba masa shagwaɓa


inda shi kuma wannan abun nata na bala'in birge shi yana bala'in son yaga mace
ta iya shagwaɓa, haba me zakayi da macen da babu wani sanyi a tattare da ita, shi
ya fi son mace faran faran wacce kullum zaka ganta very lively sannan wacce ta iya
shagwaɓa


Ta kasance fara doguwa kyakkyawa duk wannan abun daya ke nema a mace ya same shi
a badia shi yasa yake tunanin daga ita babu ƙari, haba gashi fari kyakkyawa ai sai
fara me kyau inji sabit
Sauri yai ya ƙarasa shiryawa inda ya shiga masallacin gidan su yayi sallah
magariba daga nan ya wuce gidan sahibar tasan


A ƙofar gidan su ya faka motar sa sannan ya kira ta, tana zaune a gaban
dressing mirrow ta gama tsara kwalliyar ta irin yadda sabit yake so taji call ɗinsa


Ɗauka tayi a yangance sannan cikin shagwaɓa tayi masa magana

" *SD* sai yanzu ka zo duk na bushe kwalliyar da nai maka duk ta goge" ta faɗa
kamar gaske, wannan maganar tata har cikin ranshi ya ji ta yadda ta kashe muryar ta
sannan cike da shagwaɓa

"awa nawa kike ki sake min wata zan iya jira a waje"

"wasa nake maka bari insa a shigo da kai"

"ok " ya amsa tare da maida wayar aljihun sa sannan ya tsaya gana jiran ai masa iso
zuwa cikin gidan, bai daɗe ba sai ga me aikin su ta fito inda ya bita har
farfajiyar gidan inda suka saba taɗi ya samu wuri akan ɗaya daga cikin fararen
kujerun da suke wajen ya zauna



Ko da ta gama kwalliyar tata da fesa duk wasu turakan da ta san masu ƙamshi ne
sai ta ɗauko hijab ta saka, tana ta mita a ranta


Ita ta rasa irin sabit, duk irin kwalliyar da tayi sai dai yace tabi kwalliyar da
hijab, sannan kuma ya hana su taɗi a ckkin sitting room sai dai a waje yacce duk
wanda zai shigo ko zai fita sai ya gansu, wallahi daba dan san da take masa ba da
tuni sun rabu don wani lkcn abin nashi kamar ɗan ƙauye haka yake yi ba wayewa ta
faɗa tana fita wajen sa




*menu of d day*



```Alala```




Ingredients


_Wake
Kwai
Hanta
Dankali
Alayyahu
Oil
Maggi
curry
Attarugu,
albasa
Leda


```method```



1) surfa waken ki saiki wanke shi sosai kisa attarugu , albasa da ki kaishi inji a
Markado miki


2) ki wanke hantar ki ki dafa ta da albasa,maggi thyme idan ta dahu saiki sauke ki
aje gefe


3)ki fere dankalin turawanki ki yanka shi cubes ƙanana, sai ki yanka dafaffan ƙwan
ki shima ƙanana, alayyahu a fara wanke shi sannan shima a yanka shi sannan a ajiye

4) sannan sai ki ɗauko markaden ki saiki dauko mai ki zuba aciki kisa maggi da
curry ki kara ruwa in ƙullun yayi kauri amma ruwan da kika tafasa hantarki kikara
yanka albasa ki buga kullon ki ɗauko hantar ki da ƙwan ki, da dan kalin da alayyahu
kixuba ki ƙara bugawa, sai ki ɗan ɗana, idan komai yayi sai ki saka cray fish
(niƙaƙƙe amma optional ne)



5) sannan kije ki ɗora tukunyar akan wuta kisa ruwa bayan ki ɗora saiki zo kina
ɗiban ƙullun kina sawa aleda kina ƙullawa kina sawa cikin ruwan zafin nan har ki
gama ki rufe har ta dahu saiki sauke .


*Minced meat sauce*


Niƙaƙƙen nama
Attarugu
Oil
Green papper
Maggi
Albasa
Tafarnuwa



```method```
1) ki ɗauko frying pan sai ki zuba ɗan man ki ki saka masa albasa kaɗan idan ya ɗan
yi zafi sai ki zuba niƙaƙƙen naman ki sannan ki ƙara zuba albasa, tafarnuwa maggi
sai ki ta juyawa har sai ya koma brown, ba a ɗauke masa hannu don sai ya ƙone



2) idan naman ya koma brown sai a ɗan zuba ruwa a rufe ya dahu, ruwan kadan ba
dayawa
3) idan naman ya tsotse ruwan sai a zuba niƙaƙƙen attaruhu, da albasa curry sannan
sai a rage masa wuta har ya soyu, shima a dinga juyawa don kar ya kone

Sai aci da alalan




*Pineapple drink*

madara
sugar
abarba
flavour

1)ki fere abarbar ki ki markaɗa a blender sai ki tace saboda ba duka bane suke
markaɗuwa ba


Sannan sai ki ƙara mayar da wadanda basu markaɗu ba ki ƙara markaɗawa suma ki
tace ki ci gaba da markaɗawa har dai ki samu yadda kike so

2) ki juye a cikin roba mai kyau sai ki ɗauko wannan madarah ki juye a cikin
wannan ruwan abarbar ki zuba sugar (amma nafi gane in dan tasafa sugar da ɗan ruwa
idan ya narke sai ki sauke ki barshi ya huce) kisa flavour

3) a juye a jug a saka a fridge don ya yi sanyi sai sha 🍸


*bon appétit*


*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 4🌹



Da sallamar ta ta ƙaraso inda yake cike da tafiya cikin yanga da karairaya sai kace
zata karye, iskar farfajiyar sai ɗauka hijabin da ke jinkinta yake inda ƙamshin
turaren ta yai masa sallama


A rayuwar sabit in akwai abinda yake so da badia be wuce ƙamshin ta da gayun ta
ba ga uwa uba fara ce tas kamar jinin larabawa, ƙarasowa tayi cike da yanga da kuma
shagwaɓa ya zauna kujerar da ke kallon tasa sannan tai narai narai da ido kamar me
shirin yin kuka sannan tace

" gaskiya *SD* ka shanya ni, tun biyar nake ta jiran ka sai yanzu, kuma kasan dokar
ka ta gama hira ƙarfe 08:00pm gashi yanzu takwas ɗin ta kusa" ta ƙarashe zancen ta
tana kyakkyaɓe fuska kamar me shirin kuka



Wannan abun da badia take yi shine abinda yake ƙara hargitsa wa sabit tunani har
yake ganin kamar bazai iya rayuwa ba tare da ita ba


Haƙuri ya shiga bata inda ya kuma kawo mata uzurin office ne ya hana shi zuwa
da wuri, sai ya kawo mata zancen da yasan zatai farin ciki da shi na batun auren su



Nan ta nuna murnar ta kamar ba gobe bata da wani ragowar buri a rayuwar ta daya
wuce ace ta mallaki sabit a matsayin miji, miji na nuna wa sa'a, mijin daya ke
kallon ta ya daki ƙirjin sa cewar daga ita ba ƙari, mijin da a kullum zai dinga
saka ta cikin farin ciki



Tattaunawar su suka ci gaba akan yadda za a gidanar da bikin da kuma shirye
shiryen da zasuyi na bikin, har mahaifinta ya dawo sannan sukai sallama inda ya je
domin su tattauna da shi akan magabatan sa da yake son turowa




Cikin hukuncin Allah sukai tsaida magana inda mahaifin badia yace wa sabit ya turo
da iyayen sa sai a ƙarasa maganar tunda maganar ta manya ce


Sabit cike da farin ya koma gida inda ya sanar da mahaifiyar sa,

Mummy ta taɓe baki ta gyara zama, sarai ya san dalilin wannan abu mummy tana da
wani aqida ne wai sai lallai mace ta iya girki, shi kuwa sabit ba shi da wannan
tunani shidai kawai ya auri badia

"auta kana ganin wannan me rawar kan da kake son ɗauko wa ta iya girki kuwa, ko in
nemo maka wata in yaso dai ka haɗa biyu kamar ƴan uwanka"


"mummy na ɗauka mun gama wannan maganar da ke,ni dai gaskiya bazan ƙara aure ba
akan girki, kin yadda da wannan inda ni kuma na yadda bazan nemi aiki a ƙasar waje
ba zan zauna kusa da ke"


Ya faɗa yana kallon ta don ya son ba abinda mahaifiyar sa ta ƙi jinin ji daya
wuce yace zai fita ƙasar waje neman aiki takance duk abinda baka samu a ƙasar ka ba
to bazaka same shi a waje ba
"to kuma me ya kawo wannan maganar, don kawai na tambaya ka a kan iya girkin ta"


"mummy ma'aikaciyar banki ce don haka ko aure mukai ba zama za mu dinga yi a gidan
ba, ita tana wajen aiki nima haka don haka karki damu"



Taɓe baki tayi Sam ita ba haka take so ba, ta so ace sabit ya ɗauko macen da ta
iya girki sosai tunda shi mutum ne me son girki different varieties amma wai ya
ɗauko wani tsari wai aiki, duk cikin matan ƴan uwansa babu wacce take aiki sai
matar shi kawai, lallai dole ne ta dakatar da wannan aikin taya ma za ayi ta iya
kular mata da ɗanta bayan tana aiki



Sabit yadda yaga mommy ta zurfafa cikin tunani yasan tasa saƙa wani abunne don
haka sai yace mata

"mummy i hope u r not thinking about any strategy don mun riga mun gama yarjejeniya
da ke akan baza ki shiga maganar aure na ba"


"to me kaji nace, ni batun aikin nata ne kawai bana so"


"mum ki bar komai kawai mun riga mun gama tattaunawa da ita da aikin ta na ganta
don haka bazan hanata ba, kuma aikin ta bazai hanata kula da ni ba" ya faɗa yana
ficewa don yasan idan ya tsaya sai mummy ta kawo wani abun da bazai iya magance shi
ba



*******************



Cikin hukuncin Allah aka kai kuɗin auren sabit inda da yake abin na manya ne aka
saka wata biyu, ba abinda zamuce sai dai muce Allah ya kaimu



********************


Asmau an ƙara wayewa ta ɓangaren girki, kullum ƙara gogewa take yi ta ɓangaren
sarrafa abinci kala kala, wannan ƙwarewar tata yasa ya ƙara jawo wa restuarant ɗin
su customers sannan restuarant ɗin ya kuma yin suna lungu da saƙo an san shi kuma
ana zuwa ko cin abinci ko yin order



Wannan iya girkin na asmau ne ya saka hjy munnira tura ta zuwa ga wani catering
school don ta ƙara ƙwarewa, don duk wani abinci na zamani a restuarant ɗin sai a
hankali sun fi siyar dana gargajiya
Domin a ƙara haɓaka restuarant ɗin ya kasance duk irin sunfarin abincin da kake
so akwai sai hjy munnira ta tura ta catering school inda taje ta fara koyan abincin
na garuruwa iri iri kama daga na turai, larabawa, chinese da dai sauran su



Shekarar asmau ɗaya tana karatu inda ta ƙware ta fi da ƙwarewa har ta kai duk
restuarant ɗin itace chef de cuisine wato itace shugaban ƴan kitchen ɗin gabaɗaya
duk da ƙanƙantar shekarunta



Girki take fesawa na kece raini, babu wanda zai ci abincin ta baiyi santi ba,
wannan ya sa restuarant ɗin ya kuma haɓa ka har hjy munnira ta ƙara buɗe branches
inda duk anan ake yin girkin sai ana gama duk sai akwasa akai can branches ɗin



Duk wannan ɗaukakar da Allah ya bawa asmau me sa ta ta fara kula da jikin ta ba,
tana nan baƙar wuluk kamar da fuskar ta ake girkin, ga rashin fara'a wannan ɗabi'a
ce sam a lamarin ta ba fara'a



Ga miskilanci sai ta wuni bata cewa kowa uffan ba, don haka da wuya kaji anyi
faɗa da ita ko cecekuce, ita dai kawai tayi aikin ta ta koyi sabon girki sannan
tayi kuma a yaba



Rashin fara'ar da sakin fuskar ta yasa duk mazan da ke cikin kitchen ɗin suke
ganin girman ta duk da dai a kitchen ɗin har yanzu ita ce ƙarama, don har yanzu
batai 16yrs ba, ga ƙaramin jiki sai ka ɗauka ma she is only 13yrs amma sai shegen
basirar sarafa abinci kamar da wannan hikimar aka haife ta




******************


Ko da lkcn auren sabit da badia ya matso sai mummy ta zo restuarant ɗin hjy
munnira akan tana son cooks waɗanda zasu dinga yi mata girki da bikin ko dan baƙin
da zasu zo na kwana



Ganin yadda mummy tace wa hjy munniran zata biya su labour ɗin su ne yasa hjy
munnira amincewa har da saka asmau a ciki tunda girkin kwana uku kawai zasu yi anyi
bikin an watse, don haka sai ta yanke hukunci tura asmau ita kaɗai tunda mummy tace
akwai ma'aikatan da zasu taya su aiki, ita kuma hjy munnira bazata iya barin iyayen
kuɗin nan da mummy take da niyyar biya ba




Asmau bata san hawa bata san sauka ba kawai sai taji hjy munnira tai mata
maganar tafiya gidan wata wai zata dinga abincin biki da taimakon wasu



Fuskar nan tata da kullum take cunkushe ba fara'a ta ƙara tsuke ta sannan tace

"hjy ban gane ba, ai ni aiki na anan yake"


"can ma aiki zaki yi na kwana uku ki dawo, biyan ki nake yi don haka ina da ikon
tura ki duk inda na ga dama, sauran inkin je ki ci gaba da wannan turɓune fuskar
taki" ta ƙarashe zancen ta tana ficewa tare da barin asmau ita kaɗai a ɗakin



Ran asmau yai mugun ɓaci wai taje wani gida aikatau duk da dai aikatau aka kawo
ta amma yanzu ai ta wuce wannan matsayin amma shine matar nan take son kai wani
gida wai ta zame musu cook ta biki, ƙara cunkushe wannan fuskar tata tayi sannan ta
fito ta fara haɗa kayan ta




A cikin restuarant ɗin taci karo da driver na gidan da zata yana jiran ta, inda
bayan ta fito hjyr take ce masa

"gata nan ita kaɗai ce zata" bin asmaun yai da kallon raini inda ita kuma ta daka
harara tare da ƙare haɗe ranta


"hjy madam fa mutane uku tace ya zaki haɗani da wannan ƴar yarinyar" dariya hjy
munnira tayi sannan tace


"kace wa madam wannan itace best chef ɗin gidan nan shigasa na bata aron ta" ƙara
kallon baƙar yarinyar yayi sama da ƙasa yadda ta wani haɗe ranta kamar an aiko mata
da mala'ikan mutuwa ga ƙanƙanta amma wai ace ta fi kowa iya girki lallai ashe ma
girkin ba wuya, ya faɗa a ransa


"muje to da rabon madam ta dawo da mu"

"in bata yadda ba kace ta gwada giɗkin yarinyar kafin a dawo da ita" gyaɗa mata kai
kawai yayi suka fice inda asmaun ta fice ba tare da tayiwa hjy munniran sallam ba
don har yanzu haushin ta take ji




Sunyi tafiyar kusan minti ashirin sannan suka ƙaraso wani tafkeken gida, tunda
muka fito drivern nan yake min surutu iskar da ta kwaso shi ma ban shaƙa ba balle
zancen sa ko da ya ga alamar banni da niyyar tanka masa sai ya ja bakin sa ya tsuke
har uka isa gidan layi guda ya cinye, a ƙofar wani makeken get driver ya tsaya inda
suka fito tare



Tsayawa tayi tana ƙarewa gidan kallo dabadan hjy munnira ce ta ce mata ta biyo
shi ba da ba abinda zai sata biyo shiva wannan gidan kamar na yankan kai
Sai da suka ƙwanƙwasaƙofar sannan wani turƙeƙen arne ya leƙo

"who's knocking" ya tambaya da wata muryar sa wacce zata iya sawa mutum ya zura a
guje, ganin driver ɗin ne yasa shi wangale baki wai yana murmushi



Shi kanshi murmushin ƙara masa muni yake balle kuma, buɗe mana get ɗin yayi muka
shiga, inda muka tasamma tafiya kamar zamu wata unguwa ba acikin gida muke ba



Sai da mukai tafiya me nisa sannan muka isa wata ƙofa inda drivern ya danna door
bell sai ga wat ƴar dattijuwa nan ta zo ta buɗe

"mlm garba tun ɗazu hjy take ta jiran ka har ta gaji ta hau sama sai ku ɗan jira
kaɗan sai ta sakko naga ma kamar ba a samu masu girkin ba ko, ai dama na faɗa wa
hjy ko miliyan zata basu baza su bata wacce zatai mata daddaɗan girkin da take
siyar wa ba ita dai tafi son kawai ai ta siya a wajen ta" duk wannan bayani tunda
ta ɗauko shi bata numfasa ba sai da ta kai aya



Wanda aka kira da mlm garban wato drivern bai ce komai ba sai kawai ya nemi waje
ya zauna, ni bece min ga guri ba don haka sai na ci gaba da tsayiwa ta



Ina da wani abu in ba bani abu kayi ba ko kuma ba nunain kayi ba bazan taɓa
motsawa ba balle insan Allah ya yi ruwan abun anan



Sai daya ga na daɗe da tsayuwar sannan yace min

"baza ki zauna ba, ke gaki ƴar ƙaramar ki da ke amma zuciyar ki kamar ta kafirai
tunda muke tafe nake ta miki hira amma kamar gunki yanzu kuma ki nemi waje kin
tsaya an gayamiki hjy yanzu zata sauko ne"



Iskar da ta kwaso shi ban kalla ba balle shi, ya buɗe baki kenan zai ƙara magana
aka buɗe ƙofar falon wannan dattijuwar ce dak ta kuma fitowa


"hjyr ta sakko" tace da mu, tashi yayi yai gaba ni kuma ina biye da shi a baya muka
shiga fatana Allah yasa hjyr tace baza ta karɓe ni ba




*menu of d day*


*chinese fried rice served with russian salad & mixed fruit juice*
*chinese fried rice*

```ingredients```

-rice (a tafasa sannan aka wanke)
-eggs
-carrot( a kankare shi a wanke sannan a yanka shi cubes)
-peas
-green beans(a wanke a yanka shi kamar girman carrot)
-man gyaɗa
-tafarnuwa
-albasa
-curry
-nama tafasashshe shima a yanka shi ƙanana


1) ki haɗa carrot, peas, greenbeans ki dafa su da gishiri, idan sun dahu ki sauke
ki wanke su da ruwa, (wannan yana sawa suyi retaining colour ɗin su)


2) ki ɗauko frying pan, ki zuba mai da ɗan albasa sai tafarnuwa, idan man ya ɗan
fara soyuwa sai ki zuba naman, da kayan veges ɗin da kika dafa kiyi ta juyawa


3) idan sun ɗauko soyuwa sai ki matsar da gefe, sannan ki ɗauko kwai wanda kika
fasa kika kaɗa shi sai ki zuba a gefen da ba komai ki bar shi ya ɗana fara soyuwa


4) da kinga kwan nan ya dauko soyuwa sai ki saka cokali ki fara dagargaza shi, kina
yi kina juyawa haɗ ya soyu sannan ya zama dagargajajjen ƙwai, sai ki haɗe da
ragowar veges ɗin da kika matsar gefe ki ci gaba da suya



5) idan sun soyu ko ince sun ɗanyi laushi, sai ki ɗauko shinkafar ki wacce kika
tafasa ta kika wanke ta tsane sai ki zuba, ki zuba maggi curry da duk wani
seasoning ko garnish da kike so sai ki cigaba da juyawa har sai ta soyu ita ma sai
ki sauke a juye




*russian salad*

```ingredients```
-Dankalin
-peas
-cucumber
-carrot
-green pepper
-egg
- bama mayonnaise


```method```

1) Ki free dankalin turawan yanka shi ƙanana sannan a tafasa shi a sauke a barshi
ya huce)

2) a kanakare carrot sannan ayi yanka shi kamar yankan da akai wa dankalin a haɗa
shi da peas a dafa su (irin dahuwar da nake faɗa)


3) a yanka cucumber irin yankan carrot, dafaffan ƙwai shima green pepper ɗin


4)ki haɗa komai a roba, dankalin, carrot, peas, egg, cucumber, green pepper sannan
a dan barbaɗa maggi saboda ɗanɗano sai a saka mayonnaise a juya sai a juye a mazubi



*mixed fruit juice*

```ingredients```
-Kowane kayan marmari da suke tashe

-sugar
-flavour


```method```


1) ki haɗa kayan marmarin nan tas ki markada kina makaɗawa kina tacewa kin sakewa
har a samu yadda ake so


2) a zuba suga da flavour sannan a saka a jug a saka fridge don yayi sanyi sai sha


*bon appetit*



*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e 5 🌹
Muka shiga falon ba abinda yake tashi a haɗaɗɗen falon sai ƙamshin turaren ƴan
maiduguri da kuma sanyin ac



Falon ya sha gyara sosai na kayan ƙawata falon, duk da dai ban taɓa shiga
haɗaɗɗen falo irin wannan ba amma hakan be sani na fara ƙauyanci ba


Kallo ɗaya nayi wa falon na ɗauke kaina inda kaina ya sauka kan wata farar mace
kamar balarabiya tana zaune a kan couch ɗin da ke falon



Fara ce tas da ita ta sha jan lalle wanda yake ƙara mata kyau da kwarjini, kana
ganin ta kasan ta manyan ta amma gayun ta da ɗaukar wankan ta sai ya ɓoye mata
tsufan nata



kusa da ita mlm garba ya zube yana ɗiban gaisa inda nima na ɗan tsugunna

"mlm garba ina masu girkin naga da wannan yarinyar" ta tambaya

"ai hjy babu yadda banyi ba akan ta bani masu aiki amma sai tace min sai dai mu
tafi da wannan yarinyar wai babu wanda ya fi ta iya girki"


Ina jin shin shi yana ta bayanin yadda sukai da hjy munnira ni dai ban tanka ba
kaina a ƙasa, ɗago wa tayi ta kalle ni sannan tace

"don ta raina min hankali wannan ƴar mitsitsiyar yarinyar me zata yi, duk irin
kuɗin dabna bata na saka a jakar ta amma baza su sa ta bani su aro na kwana uku ba,
shike nan ka mayar da ita kace nace wai ta baka kuɗin ka dawo mun da su na samu
wasu cooks ɗin"


Tana gama faɗar haka na miƙe don dama ni haka nake so

"a a tsaya mana, hjy ita hjy munnirar tace ki fara cin girkin ta kafin ki yanke
hukunci"



Musu suka shiga yi da hjyr da mlm garba kasancewar yana shegen surutu yasa shi
yin galaba akan ta don haka sai tace min in shiga kitchen ɗin ta mata abinci dare


Miƙewa nayi sannan da dakakkiyar fuskata nace mata

"ina kitchen ɗin yake"kallo ta bini da shi

"bakya

Please Login or Register in order to submit comment