You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar ka gaskiya ba ta tashi ta zama mace ta iya girki don ka dinga ci amma
sai ka dinga ɗaurewa karya .....🙊 kullum kai kenan zama da yunwa wai akai a
matsayin na me mata to meye amfanin auren kenan"



Ta ɗauka zai tanka ko ya kare matar tasa sai taji yayi shiru yana gama ci sai ya
miƙe

"mummy don Allah ki neman mana cook me tsafta wacce zata dinga mana girki" yana
gama faɗar haka yai ficewar sa maganar tayi mutuƙar ƙona wa mummy rai wato har
yanzu shi ba daddara ba




*menu of d day*


```danbun shinkafa served with offal pepper soup and kunun zaƙi```


```danbun shinkafa```

_ingredients_

-shinkafa
-zogale
-gyada
-mai
-maggi
-cabbage
-carrot
-green pepper
-albasa
-attaruhu


1)ki ɗauki tukunyar ki ki zuba mata ruwa ba dayawa ba idan kina da colander ki
ɗora idan ba colander kuma sai ki saka murfin tukunya wanda zai shige cikin
tukunyar a tabbatar ruwan yana ƙasan murfin yadda idan an saka buhu ruwan bazai
taɓa shi ba, ki ɓarza shinkafar ki sai ki tankaɗe ta ko za a samu gari a yi amfani
da barjajjen kawai, ki wanke sai ki zuwa a buhu ko colander, sai ki saka a tukunyar
sai ki rufe

2) ki samu zogalen ki (idan ɗanye ne ki zuge ki wanke, idan bushash she ne sai ki
jiƙa shi da ruwan zafi ki ajiye shi)

3) ki ɗauko gyaɗar ki ki ɗan daka ta sama sama kar ta dake

4) idan shinkafar ta fara tirira sak ki sauke ki juye aroba ki zuba zogale gyaɗa ki
juya ki ɗan yayyafa mata ruwa si ki ƙara mayar wa


5) ki wanke cabbage, green pepper, carrot (bayan kin kankare shi) sai ki yanka
yadda kike so ki ajiye,

6) ki yanka albasa manya manya, jajjaga attaruhu duk ki ajiye, idan shinkafar ta
tirara sosai sai ki sauke ki juye a roba ki zuba ƙayan cabbage ɗin nan albasa
attaruhu maggi mai, gishiri ki juya a ɗanɗana idan komai yaji sai a ƙara yayyafa
mata ruwa a kuma mayar wa a buhu a mayar tukunya sai a barshi ya tirara sosai har
sai komai ya dahu sai a sauke ayi serving

*p s* a dinga yi ana duba ruwan ƙasan tukunyar idan ya ƙone sai a ƙara, ga masu
amfani da buhu kenan
_offal pepper soup_


```ingredients```

-kayan ciki
-dankali
-attaruhu
-albasa
-maggi
-curry
-thyme


```method```
1) a wanke kayan ciki tas da kyau yadda za a cire duk wani ƙazanta da ke tattare da
su sai a ɗora a tukunya a sakar masa ruwa sosai ya sha kansa, a zuba thyme albasa
tafarnuwa, maggi sai a rufe a barshi yai ta tafasa


2) ki fere dankalin turawanki ki yanka shi irin yankan da kikai wa kayan cikin sai
ki ajiye a jajjaga attaruhu, a ƙara yanka albasa sai a ajiye su


3) idan kayan cikin ya dahu sai ki zuba dankalin ki da albasa da attaruhu da curry
da maggi in baiji ba ki ƙara ruwa sai ki rufe ki rage masa wuta ya ƙarasa dahuwa a
hankali idan ya ƙarasa saiki sauke sai aci shi da ruwa ruwan sa da danbun shinkafa



*KUNUN ZAKI*


*ingredients*

_Gero_
_Citta_
_Sugar_
_Lemun tsami_
_Flavor_
_kanunfari_
_kimba_


*method*




1) Ki jiqa geronki a ruwa tare da in da hali da daddare kafin safiya ya jiƙu


2) ki wanke a ki haɗa da citta kanunfari da kimba a markado ki tace. Sai ki dibi
kadan ki dama koko dashi ki ajiye shi ya huce
3) idan ya huce ki zuba ruwa ciki, Kisa sugar da flavour da ruwan lemun tsami kisa
a fridgeyayi sanyi, idan an tashi sha sai an ɗan juya shi kafin shaa🍸


*bon appetit*


*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 7🌹




Duk a tunanin sabit mummy zata nemo musu cook amma sai yaji shiru kamar an shuka
dusa don haka sai ya yanke hukunci tunkarar ta ya tambaye ta



Ai kuwa yana kawo mata zancen cook ɗin ta rufe idon ta tai masa tas tai masa
wankin babban bargo sannan ta kore shi jikin shi a saɓule haka ya fita daga part
ɗin nata



Shi sam ya kasa gane mummy to menene don macr bata iya girki ai shi be ga wani
abu ba ace mace bata iya girki



Shi wai ace ai wacce ta iya girki shi sam abin baya birge shi, ko yaga abokan sa
suna kurin matan su sun iya girki shi tausayin matan ma yake ji gani yake yi kamar
an tauye wa matar haƙƙin ta
Don haka in shaa Allah zai ci gaba da neman cook har su dace amma badiar sa fara
tas da ita ga gayu ai kitchen be dace da ita ba



*******************



Bayan kwana biyu sai mummy ta tashi da zazzaɓi me zafi inda aka kai ta asibiti
bayan test ɗin da akai mata sai aka gano damuwa da kuma rashin bacci yake damun ta



Haka ƴaƴan suka tasa ta a gaba sukai tai mata faɗan wai me ta rasa, aka bata
magani aka sallame ta, ko da ta dawo gida sai ta kasa cin komai duk abinda aka bata
sai tace baza ta iya ci ba haka suka yi da ita har ta kwana bata ci komai ba ciwo
kuma sai ƙara gaba yake



Kashegari tana tashi sai taji sha'awar wani pepper soup da asmau ta taɓa yi lkcn
zamata da bikin sabit don haka sai ta faɗawa sabit akan ya je yasa a yi mata


Be wani ɓata lkc ba ya karɓi address ɗin restuarant ɗin hjy munnira, yana zuwa ya
ci karo da hjy munnirar ashe ma mummyn ta kira ta faɗa mata har tasa asmaun ɗaurawa



Don haka bai daɗe ba ya karbo ya taho, ko da ya kawo yadda ya ga mummy tana shan
pepper soup ɗin nan ya saka shi ma ɗan zubawa don sha



Ai kuwa daga ƙarshe tas ya shanye har mummy na cewa ya bar mata na anjima, sai a
lkcn ya faɗa mata ai ya shanye

"ai yarinyar ce ta iya girki ga ƙanƙanta amma girkin ta ko babba sai haka" shi dai
sabit don santi ko tankawa be yi ba


Tun daga lkcn ya zama daily customer na restuarant ɗin kuma yana zuwa zaice a sa
yarinyar da mummy take son girkin ta tayi masa



Tun daga lkcn ya kasance kullum shi yake zuwa yana yi musu order shi da badia



Baya iya cin abincin ko ina sai na restuarant ɗin safe rana yamma kullum yana
hanya



Rannan sai yaje da safe wurin mummy tana zaune ta gama breakfast, tayi masa tayi
sai ya ƙi ci, gyara zama yayi sannan ya fara koro mata bayani



"mummy tunda mun neman cook me zai hana kije restuarant ɗin nan kice su bamu cook
ɗaya ta dinga mana girki, wallahi kullum na fita daga gidan sai na cen cin abinci


Kuma idan aka taso haka har na fara gajiya"


Taɓe baki mummy tayi sannan tace

"yo me kake son inyi maka tunda kai ka riga ka yadda matar ka ba matar kitchen bace
ai sai kaje kai ta muku order ɗin tana zaune ba abinda take yi" ta faɗa tana mikewa
don barin wajen



Binta yayi yana mata magiya tare da faɗa mata irin wahalar da yake sha wajen yin
order ɗin kullum


Buris tayi da shi kamar bata ji ba duk da dai abinda ya faɗa mata ya taɓa mata
zuciya sosai, amma saboda tana son ya gane kuskuren sa sai ta yi kamar bata san
yana yi ba



Magiyar yaci gaba da yi mata kamar zai yi kuka kun san tsakanin ɗa da mahaifi ai
kuwa nan da nan zuciyar ta ta tsinke inda tai masa alƙawarin zuwa da yamma



Murna yayi mata sosai hadda bata kuɗi wai ko da za abuƙaci payment a take kuma
cash, tausayin sa ne ya kamata, ohhh Allah Allah be haɗa shi da mace da ta san
darajar aure ba ga shegen ra'ayin shi na ƴan boko ta faɗa tana mita




Sai bayan la'asar sannan mummy ta saka driver ya kaita wajen hjy munnira, don
ta gabatar mata da buƙatar ta na son karɓar asmau a matsayin cook




Kasancewar mumy ta nuna wa hjy munnira ƴaƴan banki ya sa maganganun nasu basuyi
wani tsaho ba hjy munnira ta yadda da zata ba mummyn asmaun inda za adinga ba hjy
munnira kuɗin aikin natan



Asmau bata san hawa ba bata sauka ba kawai sai ce mata akayi ta haɗo kayan ta,
ta ɗauka azore za ta koma har ta fara jin ba daɗi,
Ko da suka fito ta ci karo da mummy sai ta ƙara haɗe wannan fuskar tata da sam ba
fara'a, mummy tana hango ta ta saki murmushi duk da dai asmaun ranta a haɗe yake


"wai ni hjy munnira yarinyar nan bata fara'a ne", mummy ta tanmbayi hjy munnira
dariya kawai hjyr tayi bata tanka ba don itama bata taɓa ganin murmushin ta ba
balle dariya, babu bayanin da hjyr tayi wa asmaun kawai dai tace mata zaki koma
gidan hjy ki dinga musu girki



Ƙara haɗe girar ta tayi wai me yasa mutanen nen suka son mai da ni wata mara
gahilu ne daga ni ce nan sai nice nan


Gani bata tanka musu ba yasa mummy ta miƙe


"to hjy mudai mun tafi fatan mu Allah ya bamu damar riƙe wannan amanar"

"to hjy na gode ai asmau bata da matsala sam baza ki ji ta tana cecekuce da wani ba
magana ma bata dame ta balle kuma faɗa"


"ai ba sai kin faɗa ba daga ganin yanayin ta" sukai sallama sannan suka kama hanyar
gida



Ko da suka iso gida sai mummy ta sa aka bata tsohon ɗakin da ta zauna lkcn biki
sannan mummyn tai mata bayanin yadda take son abincin ya dinga kasancewa



Tun daga lkcn asmau ta fara girki a gidan breakfast lunch dinner kullum ba fashi,
da farko daga mummy sai ɓangaren sabit kawai take wa abinci amma da ragowar ƴaƴan
suka gano daɗin abincin sabuwar cook ɗin duk sai hutash she da matan su



Tun daga lkcn duk abincin gidan asmau ce take yi, kowa ya saba da cin daddaɗan
girkin ta me sanya mutum santi, kafin kacr meye wannan sabit ya murmure yayi ƴar
kiba yai fresh da shi abin shi kamar ba shi ba wannan abun yasa kullum mummy take
godewa Allah daya haɗa ta da asma'u a matsayin cook ɗin su



Ba sabit ba gabaɗayan yaran ta duk sun saba da wannan girkin da baiwar Allahn nan
take yi sam babu wanda ya taɓa sawa a ransa cewar wataran zata bar gidan kunji ɗan
adam




*BAYAN SHEKARA BIYU*
Ba abinda ya canza a rayuwar gidan su sabit sai lalacewar matan gidan, yo
lalacewa mana don yanzu kowacce ta sakankance da asmau



Duk wani abu da suke so daga sun ɗaga waya sun kira kitchen sun faɗa nan da nan
za a kawo musu


Ta ɓangaren sabit kuwa sau biyu badia na kuma samun ciki yana zube wa inda daga
ƙarshe aka gano cewar indai har suna son ciki ya zauna a marar badia sai da ta ta
samu cikin ai mata ɗaurin mahaifa




Ga sabit da shegen son ƴaƴa duk inda yaga ɗa sai ya ɗauke shi barin ma ace ɗan
fari ne, shi dai yana son mutum fari duk munin farin mutum baya gani


Haka zalika duk kyan baƙin mutum sabit baya gani sai yace ak shi wai baƙin ne
yake kare masa ganin kyan, sai yayi taji ana cewa black beauty black beauty amma
shi sam be taɓa sanin me kyau a baƙi ba



Har musu suke yi da abokan sa musammam masu baƙaƙen mata akan ɓaƙi ma yana da
nashi kyan amma sabit sam be gane wannan karatun ba shi dai in kai baƙi ne to kawai
kallon muni yake maka



Duk da dai yana da son yara amma baya son baƙin ɗa gashi mataɗ shi Allah ya haɗa
ta da matsalar haihuwa inda suke ta fafutuka, Har yanzu a wannan halin suke inda
sabit ya biya musu ummara suka kama hanyar ƙasa don su roƙi haihuwa



Ita badia sam abin be damun ta dama can ita ba child person bace ita ba mace bace
me son yara ba don haka abin ko a ƙarƙashi takalmin ƙafarta wai rashin haihuwarta
sam be dame ta ba




*menu of d day*


*cornflakes crispy cake, miyar gyaɗa with tuwon shinkafa, coconut drink*


*cornflakes crispy cake*

*ingredients*
-corn flakes
-chocolate bar
-butter
-sprinkles (ko wane iri)
-marshmelow (optional)
-vanillah extract
-salt

*method*

1) ki narka chocolate da butter ko a micro wave ko a kan wuta amma pls kar a sakar
masa wuta


2) idan sun narke sai ki juye su a roba sannan sai ki zuba vanilla da ɗan gishiri
kaɗan


3) ki rugurguza cornflakes ɗinki da hannu ƙanana sannan sai ki zuba ki juya sai
kasance kamar tuwo ne, irin zasu cure ne waje ɗaya amma duk da haka cornflakes ɗin
zai kasance da ƙarfin sa


4)sai ki ɗauko cupcake case ɗin ki ki dinga ɗiban haɗin nan kina sawa kina
ajiyewa, idan kin gama sai ki bi kowanne da marshmelow sannan ki watsa sprinkles ki
saka a fridge domin yin sanyi sai aci




*tuwon shinkafa served with migar gyaɗa*


*ingredients*

- farar shinkafa ta tuwo

-gyaɗa
-tomatoes
-attaruhu
-albasa
-tafarnuwa
-citta
-wuyan rago
-curry
-alayyahu
-thyme
-maggi & salt

*method*

1) ki haɗa naman,maggi, gishiri, albasa, tafarnuwa sai ruwa a cikin tukunya ki dora
ki barshi yaita dahuwa


2) soya gyaɗa sama sama ta yadda ɓawon gyaɗar zai fita, sai ki surfa ki cire ɓawon
sai ki daka ko kiyi blending, ki haɗa tomatoes da attaruhu kiyi blending shima

3) idan naman ya ɗauko dahuwa sai ki zuba kayan miyar ki da soyayyan man da kike so
amma kaɗan kasancewar gyaɗar itama zata fitar da nata man


3) idan sun ɗan tafasa sai ki dama dakakkiyar gyaɗar ki da ruwa ki zuba, ki ƙara
ruwa iya irin ƙaurin da kike son miyar sannan ki ƙara maggi in baiji ba ki rufe ya
ci gaba da dahuwa


4) idan ya dahu kin tabbatar da komai ya dahu, sai ki ɗauko alayyahun ki ki wanke
sannan ki yanka sai ki zuba a miyar ki gare mata wuta ki bashi minti 1 sai ki sauke


5) ki wanke shinkafar tuwon ki ki jiƙa ta

6) ki zuba ruwa a tukunya wanda zai ishi shinkafar sannan sai ki rufe, idan ruwan
ya tafasa sai ki tace jikakkiyar shinkafar ki ki zuba ki rufe don ya dahu


7) idan shinkafaɗ ta ɗauko tsotsewa sai ki rage mata wuta ya koma low saboda ta
ƙarasa tsotsewa a hankali,


8) idan bayan ta tsotse sai kika ji bata dahu ba sai ki ƙara mata ruwan zafi amma
karki taɓa ta ki barta haka akan low heat har ta shanye ruwan sai a tuƙa a kuma
rufewa akan low heat ɗin


9) idan ta turara sai ki kwashe


*P S* ki sani dahuwar shinkafa ko ta ci ce ko ta tuwo ce ta fi son wuta kaɗan kaɗan
da ta ɗauko dahu




*coconut and banana milk shake*

*ingredients*

-ruwan kwakwa
-ayaba
-ice cream ko madara
-sugar
-ƙanƙara


*method*

1) bayan ki markaɗa kwakwar ki kin tace ruwan to ruwan kwakwar shi zamuyi amfani
da shi

2) ki yanka ayaba ƙanana ki haɗa da ruwan kwakwa ice cream ko madara sai sugar sai
ƙanƙara sai kiyi blending ɗin su


3) idan suka marƙadu sai ki juye a cup ko jug sai ki ƙara yanka ayaba a kai ayi
serving


*Bon appetit*


*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: [4/17, 2:24 AM] 🥦: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 8🌹




Mummy tana zaune rannan da yamma sai ga hjy munnira sam mummy bata kawo komai ba,
suka zauna suka gaisa sai hjy munnira tace


"hjy takakkiya nayi, wallahi iyayen asmau sunce a dawo da ita lkcn aure yayi"


Mummy ji tayi kamar hjy munnira ta soke ta ita sam bata taɓa kawo wa cewar wai
asmau zatai aure ba, ta gama sakankan cewa kaji san kai


Gyara zaman ta tayi don wannan magana ce da a za yi ta sosai asmau zata tafi bayan
sun gama sakin jiki da girkin ta ai da sake



"hjy munnira ya baki taɓa min wannan maganar ba sai yau" inji mummy

"yo hjy sai na gaya miki ai kema kinsan mace ce kuma wataran dole ne tayi aure ko
ba haka ba" shiru mummy tayi don kuwa zancen hjy munnira gaskiya ne



Tattaunawa suka shiga yi inda daga ƙarshe aka yanke hukunci mummy zata neman mata
miji a cikin ma'aikatan gidan tunda ko taje can ma sai Allah ya haɗa ta mijin


A haka sukai sallama akan idan mummy ta samo mata mijin zata kira hjy munnira



Mummy ta tara ma'aikatan ta maza sannan ta musu albishirin akwai yarinyar da
take son aurar wa cikin su ko akwai me so
"kar ku damu sadaki da kayan aure duk ni zanyi"


Kusan mutane biyar suka amsa suna so amma tunda mummy ta ambaci sunan asmau sai
kowa ya janye


Mummy ba yadda batai da ma'aikatan ba amma kowa sai ya ƙi, kowa sai ya dinga kawo
uzurinsa


"wa zai auri wata asmau ga baƙi ga rashin fara'a" inji driver, babu yadda mummy
batai ba amma fafur suka ƙi haka ta sallame su suka watse



Duk wannan abun da ake yi asmau bata san wainar da ake toyawa ba, hankalin mummy
ne ya kuma tashi don duk yadda ta ɗauki abun ba haka yake ba


Shawara ce ta faɗo mata sai ta tara ƴaƴan ta ko akwai wanda zai auri asmaun in
yaso sai ta zauna amatsayin cook ɗin daga baya idan ta girma ta mallaki hankalin ta
a san yadda za a yi



Bayan duK sun taru amma banda sabit wanda yake ƙasa me tsarki shida matar sa,
mummy ta gabatar musu da maganar da kuma hukuncin da ta yanke na ɗaya daga cikin su
ya aure ta in yaso daga baya a san abin yi amma yanzu wannan shine kawai shawara



Shiru sukai kowannen su na jimamiba wanda yake son auren asmau, da babban ɗanta
tafa ra


"isma'il me kake tunani"


"gaskiya mummy bazan aure ta ba saboda kwananan zan sake aure ƴar meduguri ce
magabata kawai zan gabatar a fara shirye shirye"



Ako koma kan na biyu sulaiman shima ya kawo uzurinsa, mummy tana kallon muktar
ɗan ta na uku yace


"gaskiya bazan iya ba matana sun iya girki"


Tooooo faaaa abu ya taru ya haɗar wa mummy

"yanzu duk cikin ku babu wanda zai auri yarinyar nan na wani ɗan lkc haka kune son
yarinyar nan ta tafi, a banza a wofi" ta faɗa ranta a ɓace
Kowannen su ɗauke kansa yayi mummy ta dinga faɗa kamar ta ari baki dukkan su
suka tsuke baki can sai sulaiman yace


"mummy ai mu mun matan mu sun iya girki, ɗan autan ki ne matar sa bata iya girki
ba kuma yarinyar nan kamar saboda su take zaune me zai hana ki aura masa ita"



Dukkan su suka amsa da haka ne kam shi kaɗai ne ma mata ɗaya


mummy shiru tayi tasan halin sabit da rigimar sa zata iya lanƙwas kowanne su amma
banda shi,


"kun san halin sabit zan iya lanƙwasa ku amma banda sabit taurin kansa yafi komai"


"mummy ba sai ayi auren ba kafin ya dawo sai dai kawai ya dawo ya tarar da
amarya" muktar ya faɗa yana d ariyar mugunta don ba ƙaramin rigima za a sha da
sabit ba idan ya dawo ya tarar da ya angwance 💑




Babu yadda mummy ta iya haka ta ɗauki shawarar ƴaƴan ta dole ne ta aurawa sabit
asmau kafin ya dawo in yaso idan ya dawo ayi duk waccd ayi da shi ita dai ta riga
ta gama



Bata ɓata lkc ba taje ta faɗawa mijinta batun auren sabit ɗin da asmau amma bata
faɗa masa dalilin auren ba



Dady sai yace
" to shikenan dama gobe zani kano ɗaurin aure sai kawai mu ƙarasa can garin su
yarinyar sai a ɗaura mata tunda kince ya dawo kike son ayi"



Mummy sai taji daɗin yadda sam dadyn be yi tambayoyi akan auren ba


Aka gama shirye shiryen auren duk mutanen gidan suka dunguma sai kano auren sabit
da asmau har da asmaun wacce sai a mota sannan mummy tai mata bayanin auren



Da yake da ƙuruciya a tattatare da ita sai ta yadda, lfy suka isa kano suka sauka
a hotel ɗin tahir guest palace suka kwana



Kashegari suka kama hanyar azore, kasancewar ba a san da zuwan su ba don haka
suna isa suka sauka a gidan me garin na fulanin



Suka gabatar da abinda ya abinda ya kawo su sam me garin be gane asmau ba sai da
tayi bayani sannan ya gano ta



Nan da nan yasa aka kira kawun na tan ya zo shima aka gabatar masa da maganar
auren



Mummg tayi mamaki da taji cewar basu suka tura hjy munnira ba da maganar auren
suka ce musu su rabon da hjy munnira ma ta bada kuɗin aikin yarinyar har sun manta



Ko kaɗan dady be ji daɗin wannan abun ba yarinya tana aiki amma sam iyayen ta
basa samun ladan aikin ta, sai da ya biya su kuɗi a madadin na aikatau ɗin ta
sannan suka kuma gabatar da aurawa ɗan su asmau



Babu wani ja'inja wan mahaifin asmau ya yadda inda atake a ka ɗaura auren sabit
da asmau akan sadaki mafi ƙanƙanta



Baffa wan mahaifin asmau shi aka ba sadaki amatsayin sa na uban ta, daga nan
daddy ya shiga rabon kuɗi



Mutanen gari sai turuwa suke suna ƙara ƙaruwa kamar sallah ana cewa ai asamau ta
je binni ta haɗu da me kuɗi




Baffan ya so su kwana amma sai suka kawo masa uzurin zasu koma ne kasancewar
kashegari ake sa ran tasowar ango sabit 😂




Amma sai da suka ƙarasa gidan baffan suka ga gidan sannan suka kama hanyar
kano inda suka sauke daddy a kano sannan suka kama hanyar abuja



Mummy kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ganin ta mallaki asmau yanzu asmau ta zama
mallakin ta, kuma babu abinda zai raba ta da ita



```ni kuwa mmn walid nace anya kuwa sabit zai yadda ya zauna da baƙar mace
amatsayin matar sa mutumin da baya son baƙi```
******************




Cikin hukuncin Allah sabit da badia suka dawo gida lfy sai da mummy ta kwaɓi
dukkan ƴaƴan ta akan kar wanda ya faɗa masa maganar auren



Don haka ko daya sauka sam be sani ba hidimar sa kawai ya ci gaba tare da kwasar
girkin wacce a yanzu take a matsayin matar sa



Itama mummyn ko da suka dawo bata ce asmaun ta bar inda take ba tunda auren ai
kamar suna ne, don kawai asmaun ta zauna a nan wajen su



Sai da suka huta suka nutsu sannan mummy ta kira shi da matar sa badia da kuma
asmau dukkan su ta tara su a falo



Sabit da badia da mummy suna zaune a kan kujera inda asmau take zaune a ƙasan
carpet fuskan nan tata sam ba annuri don kuwa tasan kiran menene



Sai bayan da kowa ya nutsa sannan mummy tace

"sabit bayan ka tafi matsala ta taso ta yadda dole ne a aurar da asmau don haka sai
nai mata aure"


Kallon mummy yayi

"yo mummy ina ruwana da auren ta ai aiki aka ɗauke ta kuma ake biyan ta idan zata
iya aikin da auren to idan kuma baza ta iya ba ta ƙara gaba ai ba ita kaɗai ce ta
iya girki ba sai mu nemi wata"


"ai kai ne mijin" tsab sabit yaji abinda mummy tace amma sai yake jin kamar kunne
sa ne yake masa kuwwa



"mummy me kinace" bata maimaita ba face idƙ da ta zuba masa


"kamar naji kince nine mijin wannan abun koo" ya faɗa yana nuna asmau


"ashe kaji kuma wallahi da wasa ka sake ka furta mata kalmar saki wallahi sai nayi
mugun ɓata maka wallahi sai kaga ɓacin raina tunda auren ka da asmau babu wanda zai
taimaka sai kai


Tunda de duk ƴan uwanka kowannen su yana da mace biyu kuma acikin biyun akwai
wacce ta iya girki amma kai kana zaune da ɗaya ɗayar ma wacce

Please Login or Register in order to submit comment