You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara danƙon
soyayyar ku amma wallahi ka sani ka sake naga ƙafar a gidana wallahi kaji na rantse
maka sai na kira daddy ya raba mu```


Ina gama rubuta saƙon na kashe wayata, haba sabit daaa kenan zakai min ba tare da
na ɗau mataki akan ka ba amma ba yanzu ba da kan mage ya waye


*******************


Sabit yana zaune a gidan sa yana ta haɗa kayan sa zai taho kano sallama da asmaun
sa sam wannan tafiyar da badan ta zame masa dole ba da ba inda za shi


Tunda ya kira daddy ya faɗa masa maganar tafiyar yace masa da asmau za shi daddy
ya soke tafiyar da ita yace ana sanyi ga yara basu yi ƙwari ba gwanda kawai ya tafi
da badia in yaso ita asmaun sai ya kaita hajj yake jin wani iri a jikin sa


Sam ya kasa yi wa asmaun bayani a waya yafi son idan yaje can sai yayi mata bayani
face to face ya san zata saurare shi kuma zata fahimta




Ƴar ƙara yaji daga wayar sa alamar message ya shigo, sam be damu yasan ko waye ya
turo ba ya fison idan ya gama komai sai ya duba


Sai daya gama komai sannan ya ɗauko wayar da don ya duba sakon da aka turo masa


Yai mamakin daya ci karo da saƙon asmau, hankalin shi ya tashi sosai ya rasa
abinda ke masa daɗi ya akayi asmau ta san da batun tafiyar sa da badia


Yasan muumy sam bazata taɓa faɗa mata balle kuma daddy, inbanda su biyun nan babu
wanda ya sani sai badia


Badia tabbas badia ce ta faɗa mata rasa abinda zai yi don takaici


Ɗaukar wayar ta yayi ya fara trying a kashe ya jita, shit ya faɗa sannan yai jifa
da wayar sa wai sai yaushe zasu samu zaman lfy da asmau ne


Ya daɗe ya na tanadin lkcn da zasu haɗu da asmau amma yanzu duk wannan budget ɗin
nasa ya ruguje, mtsss, gashi ƙarshen satin nan zasu tafi


wallahi shi ya sa da daddy yace asmau baza ta je ba yace bazai tafi da kowa ba,
daddyn ne ya matsa masa sai ya tafi da badia, yanzu gashi nan ga abinda aka jawo
masa ya rasa abinda ke masa daɗi wannan wace irin rayuwa ce ace kullum ka rasa
farin cikin da iyalan ka da komai


Sam baya ganin laifin asmau shi ne ya fara ɗora ta akan wannan hanyar ita kuma da
ta tashi sai ta doke shi,


Lkcn da yake iskanci sam be taɓa hanata haƙƙin ta na aure amma ita da ta tashi
ramawa nata ya fi ci masa tuwo a ƙwarya ta hana shi kanta ta hanashi ganin ƴaƴan sa


Kai wannan da me yayi kama


Zai ci gaba da trying ɗin wayar ta har ya samu ta shiga, don ya kamata ace lkc ya
yayi da zasu daina involving mutane cikin maganar sha'anin auren su



Ya kamata idan ka girma ka san ka girma ƴaƴa uku tsakanin su, gaskiya lkcn da
zasu zauna su magance matsalar sune yanzu ba lkcn da zai dinga ya maɗiɗi da duk
wani ɗan saɓanin da suka samu bane



Wayar shi ya ɗauka yai mata reply kamar

```baby na don Allah idan kin kunna wayar ki ki kirani wallahi zan miki bayanin
komai, na so ace na zo kano nai miki bayani ni da ke amma ganin text ɗin ki ya
dakatar da ni don Allah call me```



Kwanciya yayi kawai akan gado yana me fatan Allah yasa idan taga message ɗin shi ta
kira shi



Tun sabit ya jiran call ɗin asmau har ya sare, har badia ta zo, inda ranar da ta
sauka ma sai da akai abunda aka saba don tana sauka ta fara masa maganar dashe
wanda shi kuma ya taka burki wanda
hakan ya kai su ga faɗa


Har ranar da zasu tashi ba asmau ba labarin ta abin ya dame shi sosai bazai iya
tafiya ba ba tare da yaji muryar ta ba



Ɗaukar wayar sa yayi ya kira anty fannah tas ya kwashe mata abinda ya faru ya
faɗa mata sannan ya roƙe ta akan don Allah ta sa asmaun ta kunna wayar ta ko
sallama ne suyi tunda ta hana shi zuwa gidan
Anty fannah ta tausaya masa sosai sam bata san haka abin yane ba kuma sam bata
san cewar asmaun ta aikata hakan ba


Haƙuri ta bashi tare da yi masa alƙawarin zatai wa asmaun magana



Suna gamawa ta miƙe da ɗan cikin ta wanda a yanzu ya fara nuna wa tayi hanyar part
ɗin asmaun,


Tana zaune tana bawa annur abinci sukuma twins ɗin suna baccin su da sallamar ta
tashiga


"anty fannah yanzu nace bari in gama bawa annur abinci yaje wajen ki don in samu in
bacci wallahi ya hanani da rigimar sa"


"ba dole yayi rigima yaro yaushe rabon da yayi magana da bbn sa" shiru nayi don
bana ma son ayi min maganar sabit ko kaɗan


"yanzu asmau duk faɗan da nai miki rannan ashe baki jiba, sai da kika kira sabit
kika ƙara tayar masa da hankalin, yanzu asmau dama an taɓa rayuwa a haka,


Kin ganni wallahi a gidan mu sam bamu san wai namiji yai maka laifi ba kace zaka
rama, duk abinda namiji yai maka indai har ya dawo ya tuba wallahi sai ka yafe masa
ku zauna lfy


Yau namiji yai miki kin yafe gobe ya miki kin kuma yafe wa wallahi jibi kunyar
ɓata miki zai yi,


Amma idan kina yi namiji haka asmau kina ƙara ɓata masa rai kina ƙara nisan ta
kanki ne da shi, lkcn da zaki zo ki so shiryawa sai kiga shi kuma ya riga yai miki
nisa


Don me yasa duk abinda sabit yake miki ban taɓa cewa ki rama ba, saboda nasan
kowane *AURE BAUTA* ne


Kuma duk matar da tace wallahi ba za tai haƙuri da jarabawar da Allah ya jarabce
ta da shi a rayuwar auren ta ba to wallahi tallahi tai kuka da kanta


Kin taɓa jin inda akace wannan abin ibada ne kuna ya kasance ka same shi kasatan
ba wani wahala ko wani abu


Wallahi ki nutsu, ke me kishiya, ma d more kike nisanta kanki da mijinki d more
shima yake ƙara nisanta kanki da shi duk kuwa da son da ya ke miki za a wayi gari
wataran yaji da ke da babu duk ɗaya
Duk matar da tai sacrificing farin cikin ta ga mijin ta wallahi ko ba daɗe ko ba
jima sai ya dawo wajen ta, ko kin taɓa jin inda akace haƙurin wacce be mata rana ba
sai dai a ce rashin haƙurin haƙurin wacce ya cutar ta


Kiyi haƙuri ki ja mijin ki a jikin ki, in shaa Allah wataran sai labari wataran
ke zaki girbi abinda kika shuka walau khairan au sharran"


Tun da ta fara nake kuka nasan tsab anty fannah macece me haƙuri sosai da mai da
komai ba komai ba shiyasa tunda muke da ita ban taɓa jin tace wani abu akan isma'il
ba


Amma ni yanzu wai ace duk abinda sabita ya min in share in mai da komai ba komai
ba to wai sai yaushe ne duk waɗannan abubuwan zasu zo ƙarshe


Ko da yake ance aure ibada ce kuma aure bautar Allah, muna fatan a wannan bautar
Allah yasa mu kasance muna yin ta iyakacin iyawar mu


"in shaa Allah anty zan kira shi komai ya wuce"

"indai har da gaske kinji abinda na faɗa miki ɗauki wayar ki kira shi, kuma ki
bashi haƙurin tayar masa da hankalin da kikayi"


Wayar na ɗauka na kunna sannan nayi dialing number sa, ringing ɗaya ta ya katse
wayar daga dukkan alamu shi ya kashe kallon ta nayi alamar ta gani ko


Murmushi tayi sannan tace

"ki bari zai kira ki nasan yana wani abun ne"

"nasan ba wani abun da yake yi yana tare da badia ne suna ta shirye shiryen tafiya
mtsss"


Kallona tayi sannan ta saki murmushi

"asmau manya duk kishin ne haka, ana so ana kaiwa kasuwa daaa kina kishin nasan
kika bar mata shi, wa ya gaya miki ana bar wa kishiya miji, barin ma ita da suke
tare kullum,


Wallahi asmau ki shiga hankalin ki da wannan wautar taki ta nuna halin ko in kula
da sabit, yaro kina ganin shi sabon jini son kowa ƙin wanda ya rasa amma kina miss
using damar ki


Yarinya idan yaje ya haɗu da ƴammatan lagos masu shegen naci, maƙale mata kya
faɗawa ƴan garun ku"

Ta ƙarashe zancen ta da dariya

Kyakyaɓe mata fuska nayi kamar wacce zatai kuka a dai dai lkcn call ɗin sa ya
shigo, kallo na tayi sannan tace

"tashi ki shiga ɗaki ku sha hirar ku zan ci gaba da kula da yaran sauran kar ki
bashi haƙuri sauran kar ki kwantar masa da hankali wallahi ya kuma kawo min ƙarar
ki sai dai ki nemi wata ba ni ba"


Miƙewa nayi jiki na asanyaye nayi hanyar ɗaki tare da ɗaukar wayar sannan na kara
ta a kunne na tare da cewa


"hello daddyn annur ya lagos"
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠




🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚




ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN* 🤲🏻🤲🏻




*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 30🌹
Sai kashegari da sassafe sannan muka kama hanyar a jirgi,


Muna sauka directly asibitin muka wuce inda na tarar da tashin hankali wanda ban
taɓa gani ba


Sabit ne a nannaɗa kamar me, baka ganin komai nashi sai idon sa wanda yake a rufe
sai kuma bakinsa sannan hancin sa wanda yake ɗauke da oxygen


Mummy ce a zaune akan sallaya tana addua, jikin ta ne na faɗa ina kuka, rungume ni
tayi ita ma muka cigaba


Sallamar daddy muka ji, wanda hakan ya sa muka sake sakin wani sabon kukan

"nasiha ya zauna yai ta mama akan mu gode wa Allah tunda ba wani abun bane, karaya
ya samu a cinyar sa ta dama sai kuma ƙafar sa ta hagu


Sannan hannun sa na dama ya samu karaya, na hagun kuma ya samu gocewar ƙashi da
kuma tsage war sa" kuka na kuma saki sosai


Lallai bawa ba a bakin komai yake ba


"daddy kansa fa da a ka nannaɗe" na tambaya don ni sam ban yadda da naɗin kan na
ba


"Ba komai ɗan bigewa yayi a kan"


Na ɗauka zasu gaya min abinda ya same shi sai naji sun yi shiru ni ma haka,
ƙarasawa nayi kusa da shi na kira sunan shi


Amma sam be amsa ba kamar ma bacci yake yi ko a sume yake oho,

"mummy bacci yake yi ne"

Ajiyar zuciya tayi ba tare da tace komai itama kamar bata sani ba,

Likitoti dai sunce zai farka, zuwa yamma,

"Allah ya kaimu shine kawai abinda nake cewa"


Zuwa goma ƴan gidan an cika asibitin ana ta kuma jaje


Daga ganin su ba wanda ya san me ya same shi, don cewa sukai kawai kiran su akayi
aka ce yayi accident, to me ya haɗa su da badia
Tabbas ko ba a faɗa ba nasan badia tana bayan wannan hatsarin nashi amma kuma
Allah ne masani


Har zuwa yamma ba abinda ake bashi sai kunu, inda ake feeding ɗin shi ta hanci sam
be ma san inda kansa yaba


Sai ledar ruwa da yake ta shaa,

Bayan magariba aka kuma cika ɗakin lkcn duk sun dawo daga wajen aiki, kusan anan
suka ci dinner ana yi ana jajan tawa juna, isma'il ne yace


"shin mummy wai badia bata san sabit yai accident bane ni sam ban ganta ba"


Taɓe baki tayi taƙi cewa komai, ragowar ne suka dinga tankawa ni dai ban ce komai
ba saboda kar ince wani abun ace kishi ne amma ni kaina naji haushi


Sai goman dare sannan aka tashi tafiya mummy ce ta kalle ni

"asmau kije gida ki huta kinga tunda kuka dawo twins suke gida sam basu gan ki ba,
gwanda ki tafi, don ma nace a kai su can gidan mu ba naku ba, kije ki zauna acen
har muga yadda hali zaiyi"


Kuka na saka mata

"wallahi mummy ba inda zani, jinyar mijina zanyi, mummy don Allah ki barni in zauna
anan"


Na ɗauka zasu goya min baya sai naga kowannesu yana cewa in tafi in huta na dinga
zuwa da safen tunda ba komai ake masa mummy ma ta isa



Kuka sosai na dinga yi, inda a lkcn daddy ya shigo yaga halin da muke ciki sosai
ya musu magana akan su barni, gwanda in zauna ana hankali na zai fi kwanciya akan
ina gida


Naji daɗin yadda daddy yayi supporting ɗina lallai shi kaɗai ne yasan halin da
zan shiga idan na koma gida a wannan halin



Sallama sukai suka tafi, inda ni da mummy muka zauna, yadda aka tsara shine zan
dinga zuwa gida sau uku ina bawa yara nono kullum ko a dinga kawo sun suna sha


Na yadda da wannan tsarin amma sam bazan yadda inyi nisa da mijina ba


Haka muka kwana lfy vba wani abu sam sabit ko motsi ba ya yi, sai dai in ya daɗe da
kwanciya likitocin su zo su juya shi su gyara masa kwanciya wanda sam ko motsi baya
yi idan an taɓa shi kamar wani matacce


Zuciyata tana karye wa idan naga wannan halin da mijina ya ke ciki wai wannan
sheine sabit ɗin dana sani kai ɗan adam ya shiga uku



*******************



Tin muna sa ran farfaɗowar sa har abin ya fara bamu tsoro, likitocim ne suka bada
shawarar za a kuma ɗauko wani likitan ƙwaƙwalwa ya duba ko akwai matsala a
ƙwaƙwalwar ta sa wacce ta hana shi farfaɗowa


Likitan dr. jamal daga lagos ya zo, dole da accomodation ɗin shi da komai nashi
su daddy ne suka ɗauka


Sai da ya zo sannan aka kuma yi wa sabit general check up inda aka gano ,akwai
matsala a kansa hmmm wata sabuwa inji ƴan caca



Dole tasa akai emergency operation na kansa inda akai masa fixing matsalar

Awan su shida a cikin theater inda daga baya aka gangaro shi aka fito da shi kamar
matacce,


Babu wanda bai yi kuka ba lkcn da muka ganshi kamar ba rai a tattare da shi,


Awa 48 aka bamu akace in bai tashi ba dole a kuma wani, addua ce kawai tamu yanzu
da kuma fatan ya miƙe, kusan bana daɗewa sai na kalli agogo ina yi ina lissafin
awowin kamar basa gudu



Anty fannah ma ranar da akai masa theater ta dawo lkcn kwanasu goma sha ɗaya,
itama tana ganin sa kuka kawai ta saki sabida gaba ɗaya sabit ya canza kamaninsa na
da sun canza ya wani kunbura kamar ana hura shi



Har dare ta kai sannan ta tafi akan itama zata koma ɗakin mummy ta ci gaba da
jegon ta saboda ta dinga saka ido akan yaran namu


Sosai mukai mata godiya ni da mummy don kuwa ragowar ba wanda ya kawo wannan abun
a ransa


********************


Yau kusan kwanan mu goma a asibitin amma sam ba badia balle wani wani nata tun abin
baya damuna har ya fara damuna nai wa mummy maganar


Kuka kawai ta fashe min da shi

"asmau kin san kuwa badia itace silar wannan abun da ya samu sabit, wallahi har
duniya ga naɗe bazan taɓa yafe wa ƴar iskar yarinyar nan ba wallahi ta cutar min da
ɗa ba kaɗan ba"


Jikina ne yayi sanyi yadda naga mummy na kuka lallai na koka da lamarin badia amma
sam ban ɗauka za a ce mijin ta na wannan halin ba amma ta kasa zuwa ko wani nata ya
zo ya duba shi



Hira mukai da ita sosai inda ta dinga bani irin rayuwar da sukai da badia a
turkey yadda suka dinga faɗa, akan ita lallai sai sun sake yin dashen don taga ƙwan
ta a duniya



Ooooh ni asmau na ɗauka badia ta bar wannan maganar ashe ba a barta ba, ashe har
yanzu badia batai hankali ba


Yanzu gashi nan abinda ta jawo wa mijin ta kuma sam ko a jikin ta abin be dame ta
ba, shin dama akwai mutane masu irin wannan halin a duniya



Wallahi ko da kuwa za a ce sabit yankan naman jikina yake yi saboda tsabar ƙiyayya
na ganshi cikin wannan halin wallahi sai ba zqn bar shi ba sai na kula da shi in
yaso idan ya farfaɗo sai mu ɗora daga inda muka tsaya




Hira muka dinga yi da ita har kusan 12 :30am na dare inda nishin sabit ya tayar da
mu daga wajen hirar tamu


Nishi kawai yake yi na alamar zafi ko azaba, dr. na kira inda ya zo ya duba shi
sai yayi murmushi yace aiki yayi kyau



Wata allura ya kuma yi masa a cikin ruwan da aka saka masa sannan ya fice,
wallahi a ranar haka ya kwana yana wannan gunji wanda kuma ni da mummy muka kwana
muna masa addua tare da kuka shaɓe shaɓe


Sai gab da asuba sannan yai shiru alamar bacci, sai a lkcn nima na ɗan rintsa
inda mummy ta ɗauro alwala ta tayaɗ da sallah


Tun daga lkcn kullum da daddare sai sabit ya mana wannan gunjin indak aka ce sha
biyu tayi na dare ya fara kenan sai a suba
Kuma duk wannan abin da yake yk sam be farka ba balle ya zauna


Rannan da yamma wajen ƙarfe huɗu na yamma, lkcn watan mu guda da sati biyu muna
zaune sai ga badia da bbn ta


Nai mamakin ganin ta, sosai muka gaisa da mahaifin natan inda ya bada haƙurin wai
wallahi baya gari ne sai daya dawo sannan ya samu lbr


Sam badia bata ji kunya ba ta ƙaraso kusa da gadon da sabit yake kai, kallo. Shi
tayi sannan ta taɓe baki

"Allah ya sauwaƙe" bbn ta ne ya hauta da zagi da faɗa, wallahi wani haushi da ya
ziyarci zuciyata kama in maƙe ta


"hjy fatima gatan su haɗu ita da ƴar uwar tata suyi jinyar mijin su ke kuma ki
koma gida ki huta, ai ba haƙkin bane jin yar saba"


Ƙiri ƙiri mummy tace bata yadda ba in badiara zatai jinyar ta zauna mu haɗu mu
uku amma ita sam baza ta bar ɗan ta ba


Ganin hakan ne yasa itama badiar tace

"daddy kawai ka barsu su dinga kwana ni na dinga wuni, don Wallahi ni ban ma san ta
yadda zan fara kwanan asibiti ba"


Harara ya bita da shi sannan sukai sallama akan zata dinga zuwa da safe tana wuni
mu kuma mu dinga kwana sai mu dinga shiftinga kamar gaske



Sam badia bata nuna tausaya ga sabit ba sai ma dai kamar wani da take yi kamar
da gayya




Badia aka fara zuwa jinya amma sam ba abinda take yi wuni take tana chatting ko
kuma idan ta zo sai ta ajiye jakar ta ta fice


Ba zamu kuma gani ta ba sai dare, dats in ta zo ma kenan, wannan abun ya fara
bawa mummy haushi rannan da ta zo mummyn tai mata tas ta ce kuma idan ta kuma
takowa sai ta saka an mata duka, tun daga lkcn ta daina zuwa


*******************
Sai da sabit yai wata biyu sannan aka cire masa naɗin gaskiya yanzu ya samu sauƙi
sosai, yanzu fara koyan tafiya kawai ya rage mana



amma kuma wani abun mamaki ga sabit shine sam baya magana


Baya wani abu ko na farin ciki ko baƙin ciki, baya umm baya umm umm, haka yake
kamar wani mutum mutumi


Kuma wani abu da yake yi shine, kawai yana zaune sai ya saki pupu ko fitsari, ran
da muka fara ganin wannan abun ni da mummy mun yi wani abu wai shi kuka


Ko da daddy ya zo aka faɗa masa shima abin ya bashi mamaki, dama tun kafin lkcn ya
na complain ɗin rashin maganar sabit ɗin


Dole ta sa aka sake yi masa check up, mu dai ba a faɗa mana ko menene ba daddy de
yace mana dole sai an fita da sabit waje an duba masa kan sa,


Sam ban kawo komai ba, muka ci gaba da jinyar sa inda yanzu ƴan uwan sa maza suke
koya masa tafiya


Rannan sai ga badia da mmn ta sun zo, tunda sabit ya kwanta a asibiti in banda
bbn badia da yake zuwa a kai akai ba wanda muke gani nata


A tsats tsaye muka gaisa don mummy ko kallon inda suke ma bata yi ba



"sannu sabit ashe kuma haukace wa akayi, Allah ma ya taimake ka kana da wata matar
ta kula da kai amma wallahi ƴata ba kalar wahala bace don haka wallahi baza ta
wahalta maka ba"


Mummy ce ta miƙe ranta a ɓace ta matso har kusa da mmn badiar kamar zata dake ta

"duk rashin mutuncin da kuke yi ban taɓa tanka muku ba amma ki rasa abinda zaki ce
wa wanda ya rufa wa ƴar ki asiri sai haukace wa, ai in ya haukace ya shafi ƴar ki
tun za ace mijin ta ya haukace"


Wani banzan kallo ta bi mummy da shi sannan tace

"au ance fa ku ba a faɗa muku maganar haukan sa ba, ai ya samu matsala ne a
ƙwaƙwalwar sa" ta faɗa da fara'ar ta


"wannan abun da yake yi ai duk samun taɓin haukan ne, baki gani, in ba mahaukaci
ba wanene be san komai ba sai dai komai ayi masa, haba ki duba mana"


"maama ni fa wallahi bazan iya zama da mahaukaci ba haka kurum a dinga ce min matar
mahaukaci" inji badia


"barsu a wallahi dole ne ma a sakar min ƴa da ƙuruciyar ta baza ta ƙare a jinyar
mahaukaci ba, wallahi ko a samu me sakar ta a cikin ku, ko in kai court a ƙwatar
mata ƴancin ta yana lafiyayye ne ya ke mijin aure amma yanzu ya zama sai dai yai
depending akan wani to wallahi ba dai badia ta ba" inji mmn badia


Gaba ki ɗaya service ɗin kaina ne ya ɗauke na rasa abinda ke damu na haba biri
yayi kama da mutum ashe matsala ya samu a ƙwaƙwalwar sa


Tausayi ya kuma bani kallon inda yake nayi yana kwance idon shi a buɗe yana kallon
sama, baya umm baya umm umm,


Wasu hawaye naji suna zubar min na tausaya masa Allah sarki sabit Allah ya tashi
kafaɗar ka


"wallahi ba ɗa bare jika bazan zauna a matar mahaukaci ba, Allah na gode maka ma
annur ɗin ba ɗana bane Allah na gode maka banni da ɗa da shi balle ace min ko don
ɗana in zauna"


Kallon inda nake tayi

"kema wallahi ki kama gaban ki tun da jajayen sahun ki kar ki zauna ki yi jinyar sa
a banza ya haukace bashi da wani amfani yanzu" mari kawai taji na sauka mata shi a
fuskar ta wanda ni kaina ban san lkcn da na yi hakan ba


Ɗaga hannun ta tayi zata mare ni wanda kafin ta sauke shi a kan fuskata, na kuma
ƙara mata wani sannan na rufe ta da duka


Mmn ta ce ta hau duka na wanda sam bana ji buri na sai nayi wa badia illar da ita
sai an kwantar da ita don ta san cewa tsautsayi yana kan kowa


Sai da mummy taga abin namu da gaske ne sannan ta kira nurses suka raba mu


Zage zage suka dinga tare da kiran sabit mahaukaci miskini mara amfani wannan
kalmar itace take ƙara ƙona min rai na


Sai da suka fita sannan na fashe da kuka naje na faɗa kan sabit ɗin wanda duk
abinda ake yi yana nan kwance sam be ma san anayi ba


Kuka nayi wanda itama mummy iɓa jin nata, haka muka zauna muna ta abinmu babu me
lallashin wani, har mukai muka haƙura kowacce ta lallashi kanta sam wannan abun ba
abin kuka bane


"asmau kema kar ki zauna anan ki ɓata lkcn tunda kinga yadda Allah yayi da shi"
"mummy wallahi ko sabit ya fi haka bazan iya rabuwa da shi ba, balle sam ban yadda
da maganar badia ba, kusan yawancin maganar ta ƙarya ce ƙalilan yake gaskiya"


Mummy ba babu yadda batai da ni ba amma sam naƙi yadda dana ga ta matsa min sai na
fashe mata da kuka

"mummy ya za ayi in iya fuskantar ƴaƴana ince na bar mahaifin su ne kawai saboda
kawai wata jarabawa ta same shi, wallahi mummy yanzu ne ma nake son zama da sabit
fiye da daa, wallahi bazan taɓa barin shi ba wai don wani ya same shi ba"


Kuka sosai mummy

Please Login or Register in order to submit comment