You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yin murna sannan na
sanar da mummy abinda mummy tace shine

"ki dawo da wuri saboda ɗora abinci" naji daɗin yadda bata hanani fita ba ko tace
sai na tambayi ɗan renin hankalin can


Kuɗina na wajen ta na karɓa kasancewar kuɗin aiki na a wajen ta yake na fito sai
ɓangaren anty fannah inda na tarar da ita ta gama shiryawa muka kama hanya



Shoprite muka nufa don yin siyayyar mu, wurin man shafa wa muka je sannan sai
wurin turaruka, sutura, nai mamakin irin kuɗin da anty fannah take kashe wa kamar
bata san ciwon su ba
Rasa me zan siya na yi, sai dana ga alamar muna neman hanyar fita sannan nace
wa anty fannah


"ni fa ban siya komai ba kuma ga kuɗina na zo da su" kallo na tayi sannan tai
murmushi


"ai duk wannan siyayyar taki ce, jiya isma'il ya bani kuɗi kuma ba abinda zanyi da
su don haka sai nace bari kawai in kashe miki su"


Riƙe baki nayi ina kallon ikon Allah ni na rasa bakin gode mata ma, can dai sai
na ɗan buɗe baki sannan nace mata "na gode"


Yi tayi kamar bata ji ba, muka je counter ta biya sannan aka loda mana kayan mu
a boot ɗin motar muka kama hanya


Na ɗauka gida zamu wuce sai kawai ganin mu nayi a saloon, muka shiga, ba kowa don
haka muna zuwa aka hau yi mana gyaran kai, inda hair dreeser ɗin ta buɗe kaina
wanda ya kusan sati uku da wata shegiyar kalba da nayi wa kaina



Sai da ta tsefe min sannan tai min steaming ɗin sa tunda bana retouching kan nan
nawa ya sha gyara dama gani da gashi, don ma bana kula da shi,


tuni ya sauko har baya na, su ma kansu mutanen shagon sai yaba gashin nawa suke
anty fannah ce ta kalle ni sannan tace


"kin ga waɗan nan ma sun yaba balle sabit" haɗe gira ta nayi

"ni wallahi anty fannah indai don sabit kike min wannan gyaran gwanda ma ki daina
don ni ba san shi nake yi kuma babu abinda zai haɗa ni da shi"


"ko kaɗan ba don shi nake yi, asmau buri na ki zama mace yadda ko sabit ya sauwaƙe
miki zaki zama me class yadda samun namijin da zai soki bazai yi wuya ba, kinga
maza ba abinda suke so kamar mace me gyara, gyara shine mace


Amma dube ki dubi fuskar ki tukunyar kitchen ɗin ma tafi fuskar ki samun kulawa,
haba asmau in ba kya son sabit mu bar zancen shi a gefe akwai wani ƙanina wallahi
irinku yake so, ke dai kawai abinda nake so da ke shi, duk abinda na siyo miki kiyi
amfani da su har ki goge wannan baƙin naki me dusashewa ya koma baƙi me kyau a lkcn
zan sa sabit ya sake ki sannan in haɗa ki da ƙanin nawa wallahi zaki sha gata"



Ta ƙare zancen ta da murmushi daɗi ne ya cika ni ganin zan samu wanda zai soni,
amma ni da sabit haihata haihata, har aka gama mana gyaran kai da kuma pedicure da
manicure tana bani duk wasu tips na gyara mace inda ni kuma nake recording a
ƙwaƙwalwata
Sai gab da magariba sannan muka koma gida, don haka kawai sai na ɗora wa gidan
jollof na spag ɗuk da de na san sabit baya son



A zuciyata nace in bazai ci ba matar sa ta dafa masa wani ai tana koyon girki (a
ƙaryar ta) anty fannah ce ta tana ni muka gama sannan ta sani yin wanka na shafa
sabon man data siyo min tare da turare na kwanta



Dama haka ƴan gayu suke ko ba miji a kusa da kai sai ka baɗe jikin ka da turare
ka nemi lfyr katifa ka kwanta hmmm nima in shaa Allah sai na zama ƴar gayu sai na
kwatar wa kaina ƴanci daga wajen sabit sannan sai na auri mijin da zai ji dani
murmushi nayi dana tuno da ƙanin anty fannah



********************



Cikin hukuncin Allah nima na fara canza wa, wannan baƙin nawa wanda yake tsokane
idon mutane ya fara kyau inda na koma chocolate colour sannan ƙamshi ya fara ratsa
ni amma duk da haka sai anty fannah tace be mata ba don haka sai muka fara shirin
zuwa maiduguri wai zata ganin gida inda ni kuma zan mata rakiya


Da ƙyar aka shawo kan mummy ta yadda muje muyi kwana uku, inda anty fannah tace

"taga tafiyar dawowa ba sai lkcn da muke so ba"


Ban sani ba ashe ta samu sabit sai tayi masa zancen tafiyar tamu buɗar bakin sa
sai yace


"in ta tafi wa zai dinga mana girki
Wai yarinyar sam bata san aikin ta bane, bata san biyan ta ake ba zata wani tsiri
tafiya to ban yadda ba in kuwa ta sake ta biki wallahi sai na zare a albashinta" ya
faɗa a fusace


"sabit matar ka ce faa kana nufin ba ka hanata bane saboda matar ka ce a a ka
hanata ne saboda abincin da take maka anya kasan haqqin aure kuwa"


Wani banzan kallo ya bita da shi sannan tace

"itace ta ke gaya miki ni mijinta ne, bata gaya miki sharaɗin auren namu bane, wai
yarinyar nan me take nufi ne, ni me zanyi da ita Allah ya sauwake min zama da baƙar
mace ai ni sai fara kamar yadda nake farin nan"



Babu yadda anty fannah batai ba akan ya gaya mata yadda asmaun take a wajen sa
amma duk kalmar da zata fito daga bakin sa game da asmaun ta ashsha ce da kuma yi
wa kansa Allah ya tsare shi da baƙar mace


"shike nan tunda ka rainata saboda baƙa ce ka bata takarda ta inya so sai ta samu
wani ta aura wanda zai so ta"



Nuna mata yayi ko a jikin sa sannan ya ƙara gaba, tsayawa tayi tana ƙare masa kallo
lalle ma sabit ɗin nan ashe haka yake,


Shi ya ɗauka kyan mace a fuska ne kawai be san duk kyan mace in dai bata haɗa
abubuwan da ake so na zama cikakkiyar mace hoto ce kawai kuma na wani ɗan lkc ne da
an ɗan zauna an zama jiki shike nan sai kyan ya gushe kuma sai a koma zaman gaskiya
zaman da ba kwaskwarima ba ƙyalƙyal banza


Amma shi sam kamar be fahimta ba shike nan mu zuba ido ni da kai sabit zamu ga wa
zai zo nan gaba yana ƴar murya, lallai ma sabit ɗin nan ta kuma maimaitawa tana yin
gaba abinta



Shiri muka soma yi na tafiya, ni dai murnata ɗaya zan huta sannan zanje in haɗu
da wanda zai soni kamar yadda nake so, sannan in samu kulawa



Cikin ikon Allah muka kama hanyar maid. ni da anty fannah tafiyar da ta canza
min rayuwa, wacce ta fidda ni ƙuncin nan sannan ta saka ni cikin wani hali da babu
abinda zance sai godiyar Allah



Muna sauka muka wuce gidan su anty fannah, babban gida ne nayi mamakin irin girman
gidan su, sassane daban daban, family house ne wanda yake cike da iyalai daban
daban


Mahaifin anty fannah shine babba a gidan kuma shine me abin hannun gida duk da
dai kowa yana da nashi amma nashi ya fi na kowa


Ɓangaren su ƙato inda mahaifiyar anty fannah ce kawai mata a wajen bbn su, tunda
muka sauka nake zare ido inga ko zanga ƙanin natan da take cewa zata haɗa ni,
wayaga azarɓaɓi



Sauka ta musammam akai min, kasancewar yaren su na kanuri suke yi yasa sam ban
ma gane me suke nufi ba amma kuma kamar da ni suke don naga alamar sukan ɗan saci
kallo na sannan su ci gaba



Kunya ce ta kamani, ko anty fannah tana wa mmn bayanin nice wacce za ta haɗa da
ƙanin ta Allah ya sa na faɗa a raina cike da kunya
Sai da suka gama tsab sannan anty fannah ta ja ni zuwa ɗakinta muka ci abinci inda
take gaya min cewar zamu koma gidan ƙanwar mmn ta da zama acan za ai mata gyara
jiki ne in ina so sai in faɗa sai ai min



Ganin cewar jikina a haka is ok ya sani cewar bana so nafi son gani na a haka,
sam bata tanka ba ko ta musa min sai da muka gama komai sannan muka shirya inda
muka kama hanyar gidan kanwar mmn tata



Mun isa gidan ana kiran sallah la'asar gida ne de irin namu na mutan kano, tsarkar
gida ne babba sosai sai ɗakuna da suka zagaye gidan sai banɗaki sannan wani
tafkeken kitchen



Kusan rabin tsakar gidan cike yake da shirgi, da tukwane waɗanda duk aka ajiye su,
sai uban itatuwa a buhu buhu sai kace ƴar me magani



Gidan banda ƙamshin turare babu abinda yake yi kamar ma'aikatr sarrafa turaruka,
mata ne sun kai kusan 20 kowacce da abinda take yi, daga masu haɗa turare sai masu
sassaƙa icce ko dai wani abu.


Suna ganin shigowar mu su hau yaren su, wanda sam bana ganewa amma daga dukkan
alamu murnar ganin anty fannah suke, kayan mu suka karɓa, sannan suka shigar mana
da shi wani ɗakin inda muma muka shiga bayan mun gama gaisawa



Wata mata ce zaune a kan tafkeken carpet ɗin daya malale ɗakin tana ta magana a
waya wanda sam ban san me take cewa ba, amma fuskar ta taf da fara'ar ganin mu
sannan sai ta dinga ma na nuni da hannu na alamar mu zauna


Wuri muka samu muka zauna sai da ta gama tsab sannan ta juyo gare mu, inda anty
fannah ta ɗan kƙara durƙusawa tare da gaishe ta da yaren su ni ma durƙusawar nayi
amma sai nayi gum



Anty fannah ce take mata bayanin gaishe ta nake, da hannu ta saka ta yafito ni
inda ni kuma na tashi na ƙarasa kusa da ita


Yaran su ta dinga yi tare da ƙare min kallo ido na kai kan anty fannah sai take
cewa

"tace kina da kyau" kunya ce ta kamani na sunkuyar da kaina


Wani ɗan mai ta ɗakko kusa da ita a wata ƙatuwar roba ta kwaɓa min a fuskar ta ba
abinda man yake sai ƙamshi


A hankali ta fara shafa min shi sai daya game fuskar tawa gabaɗayan ta sannan ta
soma murza min kamar nayi kuka don zafi amma sai na dake


Sai da ta gaji don kanta sannan ta dena ta juya tayi wa anty fannah yaren su wanda
anty fannah tabi matar da murmushi nuna jin daɗin ta



Wai magunguna ta ɗauko sannan ta kira wata mata inda ta dinga ɗiba tana yi wa matar
bayanin yadda za ai amfani da su ni dai ko kalma ɗaya bana fahinta,


Sai da ta gama sannan anty fannah tace min

"tashi ki bita ita zata miki gyaran jikin" tsayawa nayi na saki baki sai da ta ƙara
maimaita min sannan na tashi na bayan mayar


Wani ɗaki naga mun shiga wanda ada ban ganshi ba domin yana ƙarshen gidan, muna
shiga ɗakin kamar kitchen haka yake saboda tsabar tarkacen sannan tukwane sai wasu
robobi manya manya ga kuma wani abu da akayi shi kamar da icce me ko me gashi nan
dai kala kala


Wani ƙaton baho ta ɗauko ta zuba wani ruwa ta gama haɗe haɗen ta sannan tai min
nuni da in yi wanka da ruwa, bokiti na ɗauka na zundumin ruwan sannan na kama
hanyar toilet don in watsa, ko da na shiga banɗakin sai ga matar ta biyo ni


Tsayawa nayi ina kallon matar nan kar dai tace min itace zata min wanka, tsare ta
nayi da ido don in san me take shirin yi



Wani riga ta ɗauko min ƴar ƙarama kamar shimi amma half vest, da wandon sa tace
min in saka, ganin na ƙi karɓa ya sa ta fara min faɗa


Karɓa nayi sannan na juya mata baya, kayan sababbi ne na saka sai da na gama
sannan ta juyo,


Wani botiki ta ɗauko, ta lakuci wani sabulu sannan ta fara gurza min, zafi ne
kawai yake ziyartata


Ko ina na jikina wanda yake waje haka ta dinga bin jikin nawa tana dirza tana
ƙara sheƙa min ruwan tare da ƙara saɓar sabulun tana ƙara wanke ni


Sai da ruwan ya ƙare ta kuma fita ta kuma ƙarowa, ko da ta dawo, sai ta ɗibo ruwa
tace min in ɗauraye jikina
Ruwan na zuba na ɗauraye jiki na sannan ta kuma zaunar da ni akan wata kujera inda
ƙasan kujerar




Turiri yake fita yana ratsa ni ta ƙasan sannan jikina kuma tana ta saɓar min shi
kai ranar na gurzu sai kace za a canza min fata



Sai da aka gama tsab sannan na cire rigar jikina da wandon na ɗauro zani na
fito, inda tazo ta sakani a cikin wani abu shi ba kwando gashi nan dai


Turare ne yake ta tashi a cikin sa gabaɗay jikina na ciki in banda kaina da ke
waje, gaskiya ranar na sha gashi


Shi kanshi kai na ba a barshi a baya ba, haka ya sha gyara sai wani ni'imantaccen
ƙamshi yake fiddawa



Kwanan na 7 sati ɗaya kenan ana min wannan gyaran wanda nasan dana gama zan haɗu
da ƙanin anty fannah nasan yana ganina zai ruɗe yace saini


Ga kuma na sha wanda shi wannan da anty fannah muke sha, lkcn da aka gama aka
bani izinin kallon mudubi na ɗauka ba ni bace 🤣


Ɗau haka na yi da baƙin nawa amma ba kamar na da ba, ƙwal haka na koma kai sai
kayi zaton daga inji na fito ga wani ƙamshi daya ke tashi a jiki na kamar wacce
tayi wanka da ruwan turare sannan ga santsi da laushin duk na haɗa


Ni kaina daɗin taɓa fatar jikina nake yi balle kuma wani ya taɓa, ita kanta anty
fannah sai yaba min take da irin wannan haɗuwar dana ɗauka



"kin ganki kuwa asmau ai wallahi yanzu idan sabit ya ganki sai ya ruɗe ya dena
kula wannan ja ja amalen tasa"


Zunɓurar baki nayi sannan nace

"ni fa ba don shi nayi wannan gyaran ba fatana Allah ya haɗa ni da mijin da zai so
ni kamar ba gobe ba wannan ɗan renin hankalin ba"


Dariya tayi sannan tace

"hmmmm shima sabit ɗin bari ya afka tarkon nan zaki ga love 😍 har sai kince ya
ishe ki" ni sam maganar wani sabit ma bana so balle inyi tunanin zai so ni
Me ya haɗa ni da shi ai na riga na gama da babin sa, haka muka ci gaba da hira na
so ace ta kuma sako zancen ƙanin natan sai naji bata sako ba Allah dai ya sa ba ta
manta bane



Satin mu biyu a maid. muka kama hanyar abj, cike da samun nasara daban daban barin
ma ni ƙara kilewa da nayi da kuma gogewa,



Lfy lau muka sauka agida inda na wuce part ɗin mummy directly don inyi reporting
na dawo, nai mamakin yadda ta saki baki tana kallo na kamar bata taɓa ganina ba


"mummy lfy ko sai kace yau kika fara ganina"

"asmau wannan canji haka sai kace inji kika shiga a maidugurin, kinga yadda kika
koma kuwa lallai maa shaa Allah wannan gyara yayi sai dai kawai ace wa sabit ya
kawo kuɗi"


Ɓata rai na nayi sannan nace


"mummy sabit ɗin daya ce in matar sa ta iya girki sakina zai yi nima ai a hakan
take, ina gama haɗa kuɗin da nake so ko matar sa ta iya girki ko bata iya ba dolen
sa ya ƙyale ni in tafi"


"shi yace miki idan matar sa ta iya girkin zai sake kin" shiru nayi don be faɗa
min haka ba amma alamu ne suka nuna min


"asmau har yanzu sabit be san irin baiwar da Allah yai miki ba amma daya gano hakan
wallahi bazai iya rabuwa da ke ba, ni ma kaina bazan so hakan ba kuma bazan bari
ba"

Tsayawa nayi ina kallon ikon Allah naga alamar matar nan ma son kanta ma yayi yawa
don haka nasan duk yadda zan fadalta rashin son zama na da sabit baza ta gane ba


Bana son shi kamar yadda shima yake ikirarin rashin sona da baya yi, miƙewa nayi
sannan nace

"mummy ni na gudu kitchen gwanda inje in ɗaura abincin gidan don kowa yasan na
dawo" murmushi kawai tayi sannan ta gyaɗa kanta inda ni kuma na fice




*menu of d day*


*curry rice served egg sauce and banana cocktail*

*curry rice*

```ingredients```
-shinkafa
-curry
-gishiri

*method*

1) ki zuba ruwa a tukunya idan ya tafasa sai ki auno shinkafar ki ki wanke ki zuba
ki barta tayi tafasa ɗaya sannan ki sauke ki tace ruwan ki wanke ta

2) ki ƙara zuba ruwa amma ba dayawa ba yadda zata ƙarasa dafa miki shinkafar, idan
ruwan ya tafasa sai ki zuba curry da gishiri ki barshi kamar minti ɗaya haka sai ki
zuba shinkafar ki ki rage mata wuta a barta ta ƙarasa idan ta dahu sai a sauke



*egg sauce*

```ingrdients```

-egg
-attaruhu
-albasa
-maggi
-sardine


*method*

1) ki jajjaga attaruhu da albasa sannan ki a jiye su

2) ki samu sauce pan ki zuba mai da albasa kaɗan idan man yai zafi sai ki zuba
jajjagenki sai ki bari ya tafasa


3) kasancewar ba ruwa don haka bazai ɗau lkcn ba, ki zuba maggi, da sardine (bayan
ki dagargaza shi) sai ki juya

3) ki fasa ƙwai a bowl daban sai ki kaɗa, idan miyar ta ɗan ƙara soyuwa sai ki zuba
kwan sai a barshi kar a juya amma a rage masa wuta


4) idan ƙwan ya dahu sai a ɗan juya kaɗan don kar ƙwan ya dagargaje sai a saike



*banana cocktail*

```ingredients```

-banana
-sugar syrup
-milk
-flavour


*method*

1) ki tasafa ruwa kaɗan da sugar idan sugar ta narke sai ki sauke ki juye don ya
huce


2) ki zuba madara a cocktail bowl sai ki zuba syrup da flavour ɗin ki sai ki saka a
fridge don yayi sanyi, idan an tashi za ci sai a yanyanka ayaba ƙanana a zuba sai
aci a take


*BON APPETIT*



*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:51] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 14🌹




Gyara jikina ya kankama ko dana koma gida ban dena ba sai ma abinda ya ƙaru yanzu
na zama ƴar gayu don anty fannah har tsokana ta take yi wai na kile na haɗu saura
haɗuwar mu da sabit


Na kan ɓata rai a ni yanzu na fi ƙarfin sabit sai wanda zai so ni mu gwada
soyayya tare wacce zata kasance a tsaftace ba mix ba irin ta sabita ba



Duk wannan abun da nake bamu taɓa haduwa da shi ba tunda ba ɓangaren sa nake
zuwa ba tunda badia tayi ɓari Allah ya yaye min wannan bautar


Sai dai ita badiar wacce ganina da ita na farko bayan na waye sai da ta tsorata da
ganina inda ta dake sannan ta fara kushe ni har da cemin


"inde ma don sabit kike yi to ki sa ranki a inuwa don bazaki taɓa birgeshi ba sabit
sai ni kaɗai" sam ban raga mata ba nima clna ce mata
"ai ni mijin da zan aura sabo zai kasance dal a leda ba saura ba" maganar ya ƙona
mata rai kuma ƙiri ƙiri ta nuna hakan



Tana shirin mai da martani ne sai anty fannah don haka sai ta haɗe rai tare da
barin wurin tunda basa shiri dama ko da anty fannah ta tambaye ni me ya haɗa mu sai
nace mata ba komai


Don bana son ta ga ko na zaƙu in haɗu da ƙanin ta na fi son ta fara yi min
maganar sa da kanta bana son nuna gazawa ta bayan na zama me class 😎


Rannan da safe na tashi mai na ya ƙare don haka sai naje part ɗin anty fannah na
faɗa mata in zata fita zan bata kudi ta siyo min, sai ma tace min inzo bayan azahar
sai muje siyayyar tare don itama zatayi


Da murnata na koma na je na ɗauka girki kafin wannan na gama na bayar aka kai
kowanne part nashi sannan na ɗauki na mummy don in kai mata


Da sallama na shiga falon na ajiye mata, tunda na ɗau gyara na zama kamar wata
sabuwar aba a wajen mummy kullum na shiga sai tayi ta bina da kallo kamar bata taɓa
gani na ba




Yau ma haka na kai mata har nayi hanyar waje zan fita sai ta kira ni, dawowa nayi
na tsaya sai kuma ta rasa abinda zata faɗa min can dai sai tace


"kije kice wa badia ina son ganin ta" rai nane ya ɓaci ba abinda na tsana daya wuce
wai inje part ɗin sabit


Jikina a saɓule haka na fice na kama hanyar, na zo dai dai hanyar da zan shiga
part ɗin sabit ne naga anty fannah


"muje ko don na gama shirya wa" ta faɗa min


"gani nan zuwa mummy ce ta aike ni wurin anty badia" na faɗa murmushi naga ta saki
sannam tace min


"maza kije ki dawo kuma ki dinga tafiya da nutsuwa kamar yadda na koya miki" ban
kula taba hmmm kaji ta tafiyar da tace min sai a gaban mijina zanyi shi shine take
son inyi shi zan shiga part ɗin wannan mara *M* ɗin
Ƙara sauri nayi ko dana ga na kusa zuwa ƙofar falon sai na saka gudu don inje in
dawo da wuri,


Kiciɓis muka ci da wani dai dai corridor ɗin da zai sada ni da ƙofar falon, ruƙo
ni yayi wanda da badan ruƙon ba da tuni nayi ƙasa


Ko da nayi gaining balance ɗina maimakon ya sake ki sai ya ƙara riƙe ni tare da
shaƙar ƙamshin da nake yi



Can sai ya sassauta min riƙon inda ya kwantar da ni akan hannun sa muka haɗa ido
*WAT* sabit ne



"kina gudu ina zaki je, dubi jikin ki lenge lenge kamar bakya cin abinci da
badan na riƙe ki ba da tuni kinyi ƙasa kuma irin masu jikinku basa wahalar karye
wa"



Ya faɗa fuskar sa taf da fara'a har wani kashe min ido yake na salon yaudara,
hankaɗe shi nayi wanda yai taga taga zai faɗi sai kuma ya tsaya ƙyam duk da haka
ina jikin nasan


"kar ki kayar da muna preety" ya faɗa


Haushi ya kuma kama ni, na kuma haɗe raina sai ya sake ni

"ki dinga tafiya a hankali don kar kiyi wa kanki illa" ya faɗa wanda ni ko ta
kanshi ban bi ba na shige ciki


*******************


Sabit tsayawa yayi yana tunanin wacece wannan gaskiya tayi matsalar ta ɗaya baƙa
ce kai da fara ce wannan da anyi haɗuwa


Kasa daurewa yayi sai daya bi bayan ta don yaga ko meye dangantakar su da badiar


Ima shiga falon ma dinga ƙwala mata kira, sai mula sannan sai gata ta sauko


"bashi na ci miki da kike min wannan kiran"


"mummy ce tace kije" na bata ansa


"me zata min" ta tambaya
"wannan kuma imkinje kyaji" na amsa mata tare da juya domin in fice cin karo muka
ƙarayi da shi amma wannan karon sam jikin mu be haɗe ba


"asmau" naji badia ta ƙwala min kira, juyo wa nayi ba tare da na tanka mata ba


"me zaki dafa da daddare"

"tuwon semo miyar egusi" na bata ansa


"bana son tuwo jollof nake so kuma ki kawo da wuri, *SD* me kake son yin dinner da
shi" ta tambaye shi


Be amsa ta ba saboda gabaɗayan hankalin sa baya tattare da shi sai da ta ƙara mai
maitawa har da ƙwala masa kira sannan ya amsa inda kunya ta saka shi shigewa
kitchen wanda ni kuma na fice na bar musu falon ina jiyo badia tana tambayar sa wai
tunanin me yake a zuciyata nace can ta matse muku



Ina fitowa na ɗanyi nisa daga part ɗin nasu najiyo ana kirana ban tanka ba don
nasan sabit ne ƙarasowa yayi ya sha gabana


"kina ji ina ta kiranki" shan kunu nayi nai masa banza

"naji kince tuwo zaki da daddare ni bazanci tuwo ba kiyi min parpesun naman kai da
meat pie" kallon sama da ƙasa nai masa sannan nace


"ai na riga na gama rufe girkin da zanyi yau, in zaka ci abincin da matar ka zata
ci wato jollof too in kuwa baza ka ci ba sai ka sata ta girka maka ai ta koyi girki
a wajena"


"ban gane kin rufe karɓar girki

Please Login or Register in order to submit comment