You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BIL IMAN* 🤲🏻🤲🏻




*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 29🌹




"hiii baby na wallahi na wahala kwana biyu ban jiki ba don Allah my asmy duk
abinda zan miki nan gaba kar ki ƙara kashe min waya, a hukun tani ko ta wane hali
ne amma don Allah banda hana ni jin muryar ki kinji"

A ɗan shagwaɓe na amsa ƙasa ƙasa
"fannah ta matsa miki ki kira ni koo, shike nan kar ki takura kanki duk lkcn da
kika sauko zan jira"


Ya faɗa tausayi ya bani sai nace masa

"ni ba haka bame anty fannah ce tace idan ka haɗu ka matan lagos masu maƙewa namiji
zan sani ne"


Murmushi yayi sosai wanda hakan ya ƙara sani ƙuluwa

"haka tace"

"hmmmm" na amsa a takaice

"shike nan rabu da ita in ma zan samo ƴan matan lagos zan samo wacce zata dinga
baki arona"


Kuka na saka masa

"wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita wallahi bazan kuma zama da wata ba, bayan ga
badia kuma ka kuma kawƙ wata wallahi sai na haɗa ka da daddy"


Daɗi ne ya rufe sabit, wanda sam be san ina zai saka kansa ba

"haba baby na daga gani har yanzu baki yadda ba dana ce miki daga ke an zo d end,
in shaa Allah ba wata macen da zata kuma ɗaukar hankalina sai ke my asmy, i really
love u sooo much"



Hira mukai tayi yana faɗa min kalamai masu ɗumi wasu in mayar masa wasu kuma sai
dai inji amma ba bakin mayar wa


Kun kusan awa guda muna waya sannan mukai sallama inda yake gayamin is tooo late
daya zo kano


Nuna masa nai ba komai zan ta bin shi da adduar Allah ya kaishi lfy ya kuma dawo
da shi lfy sannan mukai sallama




********************


Tun daga lkcn duk wani motsin sa sai ya gaya min sosai muke communicating da shi
duk wani motsin sa ko tusa yayi wacce ta canza wari sai ya gayamin ƙarewa kenan


Munyi wata irin shaƙuwa wacce bazan iya fasalta ta ba, ban dai san alaƙar da ke
tsakanin shi da badia ba amma ina ji a jikina ko ita bata isa tace sun fi kusa ba
Yara na sun ƙara girma sunyi ɓula ɓula da su kamar kaji kiwon gidan gona


Sam basu damu da shan nono ba ko cikin dare sai dai su sha feeder su don wani lkc
ma sai na danne su nayi musu dole sannan suke sha


Itama anty fannah cikin ta na nan ya ƙara girma sosai ya fito haihuwa ko yau ko
gobe duk wani siyayya da za ayi na haihuwa munyi shi mun gama jiran ta kawai muke
yi



A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, har sun gama course ɗin nasu suna ta shirye
shiryen dawowa a lkcn ni kuma duk wani gyara nayi shi


Duk wani abunda nasan anace masa mai da tsohuwa yarinya ya daɗe da tsima a jikina
buri na kawai mijina ya dawo in nuna masa banbancin da ke tsakanina da badia


Ranar wata alhamis ana sauran kwana biyar sabit ya dawo anty fannah ta tashi da
naƙuda inda Allah ya sauke lfy ta samu baby girl ɗin ta itama

Murna a wajen ta kamar ba gode, haka muka haɗu aka cika gidan ana ta murna,
kashegari da sassafe ta kama hanyar maid. na so in bita amma sai sabit yace in bari
sai ya dawo


Ko da na faɗawa mummy sai tace inyi haƙuri Allah ya dawo da shi ɗin, ban damu ba
saboda nasan yana dawowa zai saka ni a gaba mu je maid




Ana gobe zasu dawo da yamma ina zaune na kunna data muna chatting da anty fannah
sai naga sabit ya aiko min da messages


Buɗewa nayi me zan gani

Pics ɗinsu ne kala kala shi da badia wasu ba laifi don an yaɗa su amma wasu sam be
dace ba


Kala kala sun kusan 20pieces haka aka turomin su wallahi wasu sam ba kyan gani
ma, takaicene ya rufe ni


Nasani sarai ba sabit bane ya turo badia ce amma don me ze bata wayar sa har ta
shiga ta duba mana sirrin mu


Duk abinda zasu yi bazan hana su ba amma don me zata turo min wallahi sai ta gane
bata da wayo,
Haɗa kayana na fara yi maiduguri ma zan tafi,


Isma'il na kira nace yai mana booking flight ni da baaba da kuma yara zamu suna,
sai dana gama komai sannan na tattara kayana naje gidan mummy na sauke mata annur
sannan na kama hanyar maid.



Sai da na sauka sannan na kunna wayata, ina kunna wa naci karo da text ɗin sabit
yana min faɗan wai bana jin magana bayan yace min ƙar in tafi sai ya zo


Forwarding pics ɗin ta aka turo min nai masa, bayan nayi copy and paste yadda zai
gane daga phone ɗin sa aka turo min



Ƙanin anty fannah ne ya zo ɗaukar mu, ko dana sauka sam ban nuna mata ba itama
sam bata kawo komai ba


Masauki guda akai mana inda aka sauke mu ɗakin da anty fannah take, kusan kwana
mukai muna hira kasancewar bata san ba da san ran sabit na taho ba ya sa sam bata
kawo min wani zancen yi min faɗa ba


Kuma ina ta sa ran sabit zai kira ni yai min wani bayanin yadda akai pics ɗin suna
zo wayata sai naji shiru


Tun ina sa ran call ɗin sa har na haƙura, a haka na kwanta cike da takaicin rashin
kirana da sabit be yi ba


********************


Da wurwuri muka tashi saboda ana ta shirye shiryen gobe suna duk wani gyara mun
sha shi barin ma ni da biyu nake gyaran nawa


Kitson bare bari akain min wanda yake zuwa gaban nan sanna a tifke shi ya koma
gefe bayan wanka da turare da nake ta sha


Duk wani gyara na tarar suna mun sha shi kawai jiran zuwan sunan muke yi, in ka
ganni zaka ɗauka banni da wani damuwa amma can ƙasan zuciyata tana tunanin yanzu
sabit yana nigeria faa


Amma sam be neme ni ba wallahi ni ma bazan neme shi ba, har la'asar muna ta hidimar
mu duk da dai ni ba abinda nake yi ina kusa da anty fannah dai dai da yaran wallahi
sai su wuni ban gansu ba suna can cikin gidan wajen mmn anty fannah itace take
kular min da su
Ina zaune kawai naji sallama kamar muryar sabit, ina ɗagowa mukai ido huɗu da shi


Kunya ce ta kama ni na kaaa tashi daga inda nake,

"jibi ƴar ƙauyen nan dama haka karɓar baƙo" inji anty fannah


"ƙyale ta anty ni me laifi ne a wajen ta shiyasa na tako da ƙafata in bata haƙuri"


"au baki daina faɗa da mijiba, dama shine dalilin daya sa kika taho lallai ma asmau
ashe bakyaji magana dama" inji anty fannah


"don Allah ki ƙyale ta wallahi am at fault kuma na karɓi laifi na kuma nazo bada
haƙuri ne"


Ƙarasowa yayi kusa da ni ya tsugunna inda ni kuma kai na yake ƙasa

"baby na ayi min afuwa"


Faɗawa jikinsa nayi wallahi babu ƙarya nayi missing ɗin shi sosai

Wata kyakkyawar runguma naji ya min wanda ya sauke ajiyar zuciya tare da fara
shinshina min wuya na wanda ya tsumu da ƙamshi


"anty wannan ƙanwar taki ta sha gyara sai kace wata amarya" ya faɗa muryar sa a
shaƙe


"sabit ko dai in muku gadin ƙofa ne don naga daga dukkan lamu anan zaka bada
tsarabar taka"


"wallahi da kuwa kin kyauta" ya faɗa

Wallahi duk a tunani na wasa suke sai naga ta ɗauko mukullin ɗakin ta miƙo masa

" ka saka key ni kuma zan zauna daga can ɗakin ina kallo ɗakin don kar a katae muku
hadda"


"anty wasa fa yake yi" na faɗa


"waye yake wasan" naji sun haɗa baki sabit hadda zare ido


Shiru nayi, ban tabbatar da maganar su ba sai dana ga anty fannah ta fice shi kuma
ya mai da ƙofa har da key sannan na tabbatar da rashin kunyar sabit


Tsere muka fara yi da shi a ɗakin

"wallahi ni kunya nake ji"
Yana bina yana dariya

"in banda abinki ko min yi wani abu ko bamuyi ba ai duk ɗaya ne ba gwanda munyin ba
in yaso baza mu musa ba"


"wallahi ban yadda ba wayo zakai min" na faɗa ina zame wa a lkcn da ya kai hannu
zai cafko ni


Taku ɗaya yayi ya cafekeni ya ɗaga ni sama inda ni kuma ina ta wuntsile wuntsile
ne na ina ce bana so bana so

Sauke ni yayi dai dai fuskar sa yace min

"baby na bakya so na"

Yadda naga ya nutsu ya sani ni ma shiga taitayi na

"ina sanka mana" na faɗa ina shigar da kaina jikin sa

"to me zai hana a barni in nuna miki yadda nai missing ɗinki"


Ban tanka masa ba hakan ya bashi dama fara kwance min tsarabar da ya taho min da
ita 😜😜😜😜



*******************



Lallai gaskiya sabit yai wani abu wai shi missing ɗina, don haka ya dinga min
kuka, yana roƙona kar in sake in kuma cewa zan rabu da shi


Wallahi sosai ya bani tausayi, inda nima daga ƙarshe na tausaya wa kaina don kuwa
tas sai dana biya bashi ba sassauci



Sai da mukai wanka sannan ya buɗe ƙofar inda yace min in kira anty fannah yunwa
yake ji, tooo fa anan ake yin ta wallahi bazan iya fita


Babu yadda be yi da ni ba amma naƙi wallahi kunya nake ji, sai daya gaji da
tsokanata sannan ya ɗauki wayar sa ya kira ta wanda bata daɗe ba sai gata ta shigo


"haka da wuri na ɗauka sai kun yi awa uku haka"


"wannan ƙanwar taki itace ta hana mu sake wa da yaya ma ta yadda" nintsini na
mannara masa, zabura yayi kamar da gaske

"kinga har da mintsini na a gaban ki"
Harara ta doka min wacce ya sani ƙaɗa shigewa jikin sabit shi kuma jin daɗin
hakan ne ya sashi ƙara rungume ni


"sai wani shishshige mishi kike yi sam baki iya saukar baƙi ba ko ruwa balle
abinci amma kin iya shishshige masa"


"kai anty wallahi ba haka bane"

"ke kika sani bari inje in kawo maka abinci in kuma kafin in dawo kun kuma komawa
sai a tabbatar an rufe ƙofar don kar inga abinda ya fi ƙarfin idon"


Ta fita tana dariya, ƙara jawo yayi jikin sa ya fara wasa da kitson da ke kaina
yana faɗa min yadda yai kewa ta sauraren shi kawai nake yi ina ƙara tausaya masa
lallai tabbas yayi kewar tawan


Har ta kawo abincin ta zauna yana ci muna ɗan taɓa hira har ya gama sai da ya
gama sannan ya miƙe suka shiga ciki domin gaisawa da mutan gidan lallai ma aka ce
namiji ba kunya



Ba shi ya tashi barin gidan ba sai kusan ƙarfe goma, inda anty fannah tace min in
bishi sam ban so hakan ba amma sai dabta matsa min na bishi inda na bar yaran a nan
gidan su wajen baaba


Hotel muka je muka kama, wanka kawai mukai sannan muka kwanta wanda duk wata
maganar sabit bata wuce ta kewa ta da yayi ba,


Kashegari da sassafe ya kama hanyar abuja, inda ni kuma ya mai dani gida, da faɗa
muka rabu da shi saboda badia ce ta kiɗa shi tana masa magana har ya tashi ya kama
hanya ba shiri


Baza ka taɓa canza wa ba sabit na faɗa a raina



Kasancewar ina jin haushin sa yasa sam ban samu damar kiran sa ba balle inji ya
ya sauka


Sai wajen ƙarfe goman dare duk hankali na yana kan sabit ko ya ya sauka wallahi
tunda ya tafi, hankalina yake akan sa na so ace in sa ya ya sauka amma sam banna
son kiɗan shi saboda nasan suna tare da badia kuma sam bana son kiran shi idan suna
tare kamar yadda bana son ta kira shi idan muna tare da shi



Wayar anty fannah ce tayi ringing yadda naga ta kalli wayar tai murmushi yasa na
san isma'il ne ɗauka tayi da sallamar ta suka gai sa
Sai naji tace gata nan, nan da na gabana ya faɗi me ya faru,

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai naji tace me ya same shi


Tuni na gama tsurewa Allah Allah nake yi ta gama waya ta faɗa min menene, Allah ya
sa ba wani abun ne ya samu sabit ɗin ba


Sai da taga ma sannan ta kalle ni tace min asmau sabit ne yai accident a abuja
yanzu yana asibiti be ma san wanda yake kansa ba


Wani irin kuka ne ya ƙwace min sabit ɗin nawa ya Allah kar ka kashe min sabit
ɗina ya Allah ka dube ni marainiyar ka kar ka raba ni da mijina ya Allah ka dube ni
ba don halina ba ina faɗa ina kuka ina haɗa kayana


"anty wallahi tafiya zanyi wallahi wajen sabit zanje inga halin da yake ciki"
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN* 🤲🏻🤲🏻




*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 28🌹
Satin twins 2, sabit ya tattara yanasa yanasa ya koma lagos duk wannan zaman da
yayi ko kaɗan baya samun daman ta, wai ko sakin fuska ko kaɗan


Idan yana parlour to ina ɗaki, sam ba abinda yake haɗa mu, amma ta ɓangaren yara
kuwa kusan shi yake renon su


Don ko cikin dare sai kawai in ganshi a cikin ɗakin nawan ya zo ganin su sam na ƙi
sakar masa fuska, sai dai kawai ya ta abinsa shi kaɗai ni dai ido ne nawa



Ko ran da zai tafi ya shigo ɗakin nawa inbawa hoor nono

"me jego mu office yayi kira faa, in shaa Allah yau zan koma bakin aiki na"


Kamar yadda fuskar nan tawa take haka na bar ta sannan na bishi da
" Allah ya kiyaye hanya"


"babu wani kalmar i will miss u ko love u" ƙara shan kunu nayi wanda hakam ya
sashi cewa

"ayi haƙuri naga alamar har yanzu ba a sakkowa ba ni me lefi ne don haka bazan yi
fishi ba zan jir har sai lkcn da Allah ya sa kka sakko dan kanki kika fahimcin irin
son nake miki........


Ɗago ido na nayi na kalle shi dana ji ya furta kalmar sooo ɗin nan


"kina mamaki ne wallahi asmau i really doo love u, u r d only one i doo love"


Wai love kaji kuma zance, kamar da gaske, hmm sabit kenan u love abinda kake love
de amma badai ni asmaun ba kuma wallahi abinda kake love ɗin is d last thing da zan
baka


Surutan sa ya ƙaraci yi daga ƙarshe daya ga ba reply ya miƙe ya fice jikin sa ba
ƙwari, a daidai bakin ƙofa ne na ce masa

"Allah ya kiyaye hanya"


Dawowa yayi fuskar shi ɗauke da murmushi, ɗan kiss ya sakar min a lips wanda ban
bar shi ya daɗe ba na ɗauke fuska ta tare da ƙara shan kunu


"sorry na kasa haƙuri ne" ya faɗa, hannun shi ya kai kan fuskar hoor wacce ta
daddage sai tsotsar mama take tayi


"my lil princess a sha a ƙoshi a rage wa daddy" ya faɗa da murmushi a fuskar sa,
ban tanka mishi ba sai daya gama wasa da ita sannan ya juya ya fice
Ina jiyo shi shida annur a falo suna hira shi da annur a falo yana ta masa
gwarancin sa shi kuma yana ta biye masa


Sai da ya shafe kusan rabin awa sannan yai sallama da su mummy wacce tunda akai
haihuwa bata tafi ba


*******************


Har kusan yamma ina ta sa ran inji mummy tace sabit ya sauka ko wani abun amma
na ji shiru wannan ne ya sakani fitowa parlour ɗin suna zaune ita da baaba suna
hira


Baaba tana yiwa twins wankan yamma

"me jego an fito ne" inji baaba


"wallahi zaman ɗakin ba daɗi"

Na nemi waje na zauna kusa da mummyn

"mummy ya matafiya sun sauka ƙalau"

Tsayawa tayi tana tunani can sai tace

"ke yanzu tunda suka sauka baki kira kin tambaye su sun sauka ƙalau ba, haba asmau
ya ina ganin hankalin ki ace mutane sun taho daga kano amma har su koma baki kira
ba"

"mummy bafa su ba ai na kira waɗancen"

Na bata amsa, wallahi sam bana son ina damun kaina da lamarin sabit amma bazan
ignoring ɗin shi ba


Ko da dai ace bazan masa directly ba nayi masa indirectly

"waɗannan matafiya ne kuma suka kuma tafiya bayan ƴan uwanki"


Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina ƙasa

Baaba ce ta ɗago ni sai naji tayi dariya tace

"lallai mmn annur wato kunya ake ji, hjy ai me gidan ta take tambaya"

Murmushi mummy tayi sannan tace

"ƙyale ta baaba tsab na fahimci abinda take nufi, yo ni ina ruwana da wani mijinki
ba ke ya kamata ki kira shi kiji ya ya sauka ba"


Muryar anty fannah naji a bayana tana cewa

"lallai kam mummy ke dai ai kina gama naki tunda yanzu yayi aure ai haƙƙin kula shi
ya koma kan matar sa"


"kai anty fannah don Allah yanzu har da ke ake wannan abin, don Allah kira shi
muji ko ya sauka lfy"

"wallahi bazan kira ba inkin matsu ki kira shi" inji anty fannah

Kallon mummy nayi wacce kafin ma ince wani abun tace

"kar ma ki ɓata bakin ki, kije ki nemi mijinki inkuwa ba haka ba wallahi babu me
kira miki shi"


Tsayawa nayi ina kallon bayin Allah nan yanzu so suke yi in zubar da ajin nawa in
kira shi

"malama dalla can tashi kije ki kira shi ana so ana kasuwa Allah ya haɗa shi da
matan lagos masu shegen naci"inji anty fannah


Da gudu na na miƙe nayi cikin ɗaki yanzu ace sabit zak ƙara aure ai ƙaramin hauka
zanyi

Kasa kiran shi nayi don haka sai nayi masa text

```ka sauka lafiya```


Be fi minti biyu da text ɗin ya shiga ba sai ga call ɗin sa ina ɗauka yace

"baby na kina nan ƙalau"

"ba babyn ka bace asmau ce" na faɗa cike da takaici

"oh ai na ɗauka baby ta ce to ya kike mmn twins"

Wani ƙululun baƙin ciki ya zo ya tokare min a maƙogwarona da ƙyar na haɗiyi miyan
da ke baki na sannan nace masa


"ka kira babyn taka kuyi hirar kawai sai anjima"


Da sauri sa ya dakatar da ni

"haba my husna ai kece babyn tawa daga ke ba wata, wallahi tun da na sauka nake son
kiran ki amma bana sƙn takura miki ban ɗauka zaki damu ba don baki jini ba"


"ba damuwa nayi ba dama mummy ce tace bata sani ba ko ka sauka, shine nace bari in
kira ka inji"


Murmushi yayi don tuni ya ranfo jirgin natan yana sauka yayi wa mummy waya akan ya
sauka ƙalau amma shine wai take masa wannan gidogar


"kai amma wannan mummyn ta kyauta wannan ya nuna an damu da nine ko, kai amma naji
da daɗin da wannan mummyn ta nuna damuwar ta gare ni"


Shiru nai masa inda shi kuma yai ta tambayar yara ina bashi amsa a taƙaice, mun
ɗan jima muna waya daga bisani kuma mukai sallama


Shike nan tun daga lkcn sabit ya tsiri kirana safe rana dare kamar baya jin kuɗin
wayar sa wani lkcn idan ƴan jujun suna kaina yana kira sai in haɗa shi da annur yai
tayi masa gwarancin sa wani lkcn kuma in ɗauka


Sam baya gajiya da gaya min ni kaɗai ce a zuciyar sa nakan rasa gane gaskiya ne
ko ƙaryar sa ce, itama badiar haka yake mata ko a a

In dai aka ce kana auren me mata sai Allah


Rannan ya kira ni a waya da yamma

"baby na kiyi min addua akwai wani course da zanje turkey inyi na wata biyar in
shaa Allah nan da wata ɗaya ne tafiyar, kuma ke zaki min rakiya sai mu tafi tare
da su annur ko"

Daɗi ne ya lulluɓe ni don wannan ne ya nuna ana yi da ni, ranar mun sha hira kamar
baza mu gama ba har sai da wayata tai zafi sannan muka kashe


Kamar da gaske na fara sakin masa jikina, saboda tafiyar da yace za ai dani ko ba
komai zan nuna wa duniya da ni miji yake yayi



Na so ace a lkcn ya kuma min maganar tafiyar amma sai naji shiru har gashi watan
ya kusan cika sai na ɗauka ko ga fasa tafiiyar ne don haka nima sam sai ban ƙara yi
masa zancen ba don kar yace abin ya dame ni ne, tunda dai haɗ yanzu bama ƴar hakan
da shi


Kullum ya kira a waya shine yake hirar ni kuma ina sauraro ko bada amsa amma sam
bana taɓa kawo mana topic


*******************



Mummy sai da mukai sati huɗu sannan ta tafi gida wai ai yanzu zamu iya kula da
su, amma sai ta ƙara kawomin ƴar aiki amma wannan karan ƙarama ce


Rannan da yamma muna zaune a falo muna hira da anty fannah sai ga badia, wallahi
dana ganta sai da gabana ya faɗi


Rabo na da ita tun a court da aka raba mu, da sallamar ta ta shigo kamar gaske,
me aiki na aika ta kawo mata abin sakawa a bakin ta
"a a barshi ba zama zanyi ba, dama nazo ne in miki sallama don kuwa gobe zan tafi
lagos daga nan zan yi wa sabit rakiya zuwa istanbul don akwai course ɗin da zaiyi
na wata biyar acan"


Ji nayi kamar an ɗauki guduma an doka min a kaina, sam sai na kasa gane inda
zancen ta ya dosa na kasa gane maganar ma da zan mata ko baƙa zan mata ko me daɗi
zan mata


Lallai sabit ɗin nan na gaishe shi wato bazai taɓa dena abinda yake min ba ko


"kin san daa nace ya tafi da ke da farko har ya yadda amma daga baya sai yace shi
baya son gayyar ƴaƴa haka kurum kije da ƴaƴa ki hana shi sakewa shi yasa nace to
shike nan bari kawai in bi shin"



Kalaman ta ƙara ƙona min rai suke suna kuma tabbatar min da sabit ba zai taɓa
canza wa ba,


Zata buɗe baki ta ƙara wani maganar anty fannah ta katse ta

"wannan tsakanin ki ne ke da mijin naki sai kuje can ku ƙarata amma mu ba abinda ya
dame mu ko kinga wani abu daya shafi sabit a nan in ba ƴaƴan sa ba, don Allah ki
tashi ki tafi in ba fitina kike nema ba"


"toooo daga zuwa abin arziƙi sai ya zama na tsiya, to shi ke nan bari in tafi amma
a sani duk abinda mace zata yi wallahi baza ta kamo ƙafa ta don kuwa ance farar
mace alkyabbar mata, duk wani jiji da kai da mace zata yi ta tuna cewar sai naga
dama zan bar ta ta sake da miji




Anty fannah ce ta miƙe suka fara cacar baki da badiar inda daga ƙarshe sai baaba
ce ta raba su domin ni ina zaune kamar gunki ba motsi


Wallahi sabit ya gama bani mamaki wallahi na gama dawowa daga rakiyar sabit har
abada, da ƙyar na iya riƙe kukana har badiar ta fice sannan na saki abina


Janye ni anty fannah tayi zuwa cikin ɗaki inda sai da ta lallashe ni sannan ta
tambayeni menene na kukan


Tsap na kwashe yadda mukai da sabit na faɗa mata itama sam bata ji daɗi ba kuma
ta jinjina da lamarin amma sai ta ce min ki kira shi kiji ya mw ya faru


"wallahi anty bazan kira shi ba bazan kuma yadda da maganr sabit ba, ya cutar da
ni na yafe masa ya kuma wallahi wannan karon bani bashi ai ba zuciyar dutse gare ni
balle yace bazan ji abinda yake min ba"
Haƙuri dai anty fannah ta dinga bani kamar kullum ni kuma na riga na gama kulle
shafin sabit a rayuwa ta sai dai wani ba shi ba


Nunawa anty fannah nayi naji faɗan natan don haka sai ta tafi, tana fita na ɗauki
wayata na tura masa da text kamar haka


```naji ashe da badia zaku tafi turkey tooo Allah ya kaiku lfy ya

Please Login or Register in order to submit comment