You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min waya


Ina jin shi yana ta lallaɓe ta akan wai ko idan suna son abinci kafin in dawo sai
in haɗa musu,


Yana zaune a falo kafin lkcn tafiyar sa yayi, ita kuma gimbiyar tana kan cinyar
sa sai wani shagwaɓa take zuba masa wai zatai kewar sa, shi kuma sai wani biye mata
yake yi sai kace gaske


Ada idan badia tai masa wannan shagwaɓar tata jin sa yake yi kamar ba yashi a
duniyar nan, amma yanzi sai ganinta yake yi wani banbarakwai ba kyan gani akan
cinyar sa, kyan cinyar sa asmau amma ita matsalar ta shegen taurin kai ne da ita



Ni kunya ce ma ta sake su ta kama ni, lallai ma namiji sai a gaishe shi jiya yana
ɗakina anan ya kwana amma da safe yana wajen ɗayar har da wani zaiyi missing ɗin ta


Wallahi na dawo daga rakiyar sabit tabbas me fuska biyu ne, ɗakina na shige sam
ban ma san lkcn daya tafi ba



Yana tafiya naje part ɗin anty fannah na nuna mata ita ta nunnuna min yadda ake
operating ɗin ta ranar wuni nayi acan sai da daddare dana ci na ƙoshi sannan na
tafi inda na tarar da bala'in badia wai na barta da yunwa kallo bata ishe ni ɗakina
kawai ma wuce inda tabi ni da zagi




Da daddare da wuri na kwanta ban daɗe da kwanciya ba sai naji wayar na ringing,
ɗaukar ta nayi number sabit kawai nagani


Sai da ta kusa tsinkewa sannan na ɗaga


"hello" nace masa

"baki iya sallama ba sai hello" sallamar nayi masa sannan ya amsa


"me kike yi"

"ba komai na dai kwanta ne bacci zanyi" na bashi amsa


"ke baki san mijinki yayi tafiya ba ki kira shi ki tambayi ya ya sauka ba ko"


"yi haƙuri ya ka sauka, yau wuni nayi ina koyon wayar nan shiyasa shap na manta da
kai"


"meeeyeee kika manta dani saboda wata ƴar iskar waya lallai ma ke ɗin nan wai
fannah bata koya miki yadda ake kula da miji bane"
Masifar sa daya saba ya hauyi shiru nai masa ya gaji dayi ya kashe wayar sa

Nima ajiye tawa nayi sannan na kuma kwanciya, can sai ya kuma kira, ohhhhh yanzu
kuma menene ina ɗauka naji yace


"ke baki san mijinki ya yi fushi ya ajiye wayar sa ba ki kira shi ki bashi haƙuri
ba" shiru nayi don sam ban san me zance ba


"asmau" naji ya ambaci sunana da harufa masu sanyi har cikin zuciyata sai da naji
su


"na'am ai ban san fushin kayi ba kayi haƙuri"


"sai dana roƙa, to punishment ɗinki shine ki bani labari kawai" shiru nayi to ni
labarin me ma zan bawa sabit ni sam bamu saba hira ba balle in ce ga lbrn da zan
bashi


"baki jini bane"

"naji ai na rasa ko name zan baka ne"


"bani lbrin akai na" toofaaa ba gwanda yace in bashi lbr a kan garin da ban taɓa
zuwa ba nayo sharhin daya zo min akaina amma labari akan kan sa me na sani



Shirun daya ji yayi yawa ne ya sa shicewar

"to gaya min abu goma da bakya son nake yi" ban wani ɓata lkc ba na fara lissafo su



"na ɗaya kana da wulaƙanci, na biyu ga mugunta,........ Haka na dinga lissafo masa
halayen sa da bana soo har ya dakatar ni sannan yace


"naji yanzu ki gaya min me kike so a dangane da ni" to faaa anzo wajen


Hmmmmmmmmmmmmmmm kawai na dinga yi ashe ya ƙulu, masifar tasa dai ya hauyi, nidai
nawa jine sai da yayi ya gama sannan ya kashe wayar nima sai na kashe wayar
gabaɗaya na kwanta, tunda lkcn be kuma kirana ba har ya dawo gida



********************



Rannan da sassafe ya shirya inda Allah ya taimake sa na san da fitar sa da wuri don
haka sai na haɗa masa breakfast da wuri
Ina kitchen ina wanke wanke badia ta kira ni wai sabit ya manta da agogon sa in
kai masa agogon part ɗin mummy don kuwa a lkcn be ci ace ya tafi ba



Karɓa nayi sannan na kama hanyar part ɗin a daidai ƙofar shiga naji kamar ana
magana ana ambatan sunana sai na tsaya don inji meye ake ta ambaton sunana


"kai kuwa sabit ai na ɗauka son yarinyar nan kake yi, to me zai hana ka bari ta
haihu ɗin" inji mummy


"gaskiya mummy bana son haihuwa da asmau haka kurum ta haifa min baƙaƙen ƴaƴa inyi
da su, ni dai kawai ina zaki san dabarar da zaki dinga yi mata har ta dinga shan
ƙwayar kullum to gaskiya zan so hakan"



Duk da dai mummy taga rashin dacewar hakan amma kuma bata iya yiwa ƴaƴan ta
musu, sam bata so ba amma kuma sabit be san a a ba


"to shi kenan amma baka tunanin ya kamata ka bari ko ɗaya ne ta gwada kafin a
hanata"


"mummy akwai probability na asmau zata haifi baƙin ɗa kuma abinda bana soo kenan
inda ace dukkan chances ɗin na fararen ƴaƴa me da zan fi kowa murna amma baƙin ƴaƴa
inyi yaya da su"


Duk yadda mummy ta so hana abin amma sam sabit ya ƙi yadda ba yadda ta iya haka
ta karɓa tare da yiasa alƙawari kullum asmau zata dinga shaaa



Sulale wa nayi na zauna a ƙasa gabaɗaya duk wani service nawa ya ɗauke, shin wai
baƙi lefi ne da mijina baya son kalar nan


Na ɗauka Allah ne ya hallicce mu kuma yake son ganin mu a haka, kallon skin ɗina
yayi wanda yake a chocolate colour, wanda a kowane lkc yake glowing


Kusan sai dai in ban fita amma sai an ta yaba kyau na amma wannan kyaun nawa sam
baya burgr mijina, shi kawai baƙin nawa yake gani



Sam be damu da abinda yake cikin zuciyata ba, jin takun sa ya sani miƙewa a tare
muka buɗe ƙofar falon



Sam ban nuna masa wani abu ba inda na miƙa masa agogon nasan sannan na shige don
gaida mummy
Tana zaune da sachet ɗin maganin a hannun ta tana kallo, tana ganina sai ta ɗan
firgita amma kuma sai ta ɗake


Zama nayi sam sai na nuna mata ma ni ban san me ake ciki ba, gaisawa mukayi
sannan na miƙe zan fita


"asmauk naji ta kira ni, komawa nayi na zauna sannan nace

"na'am mummy kina son wani abun ne"


"sam ko ɗaya maganine dai na samo miki, naga ƴar uwar ki har yanzu bata haihu ba
shiyasa nace bari na samo miki magani ke sai ki dinga sha ko a dace"


Murmushi ne sosai a fuskar ta da badan naji komai ba da abinda zai sa ince ƙarya
ne, tashi nayi na shiga kitchen na ɗebo ruwa na kawo



Guda ɗaya ta bani na haɗiya da in haihu da sabit ɗan ya hanani barin sa gwanda
ban haihu da shi in yaso in lkcn tafiya ta yayi babu abinda zai hanani tafiya



Hawaye ne taf ido na wanda a hankali suka dinga gangarowa duk wannan abunda nake
wa sabit be sa shi ya fara so na ba to sai yaushe, shin wai baƙi laifi ne


Ya Allah ka dube ni ka saka min cutar wa nan da nake fuskanta ba tare da wani
hakkin na ba, ganin ina kuka ya sa mummy tambayar menene


"ba komai mummy kawai da ina farin ciki ne yadda kike nuna min soo" sanyi jikin ta
yayi ta jawo ni ta rungume ni sannan tace


"wani lkcn ni kaina nakan yi judging abinda nake yi amma i cant help it, wataran
idan kika haihu zaki fahimci halin da nake shiga in terms of deciding wat mah kids
want"


Sam ban fahimci abinda take nufi ba amma na san cewar ita uwa wacce bata saba
kwaɓar ƴaƴanta ba balle ta nuna musu sun yi ba dai dai ba, wannan shine weekness
ɗin ta



Her weekness is her boys kuma ban taɓa jin haushin ta ba saboda kowa a duniyar
nan yana weekness ɗina sa


Amma wannan karon gaskiya ta kaini bango sam na daina ganin mutumci ta at least
in ɗan ta ya tashi yin abu wanda tasan be dace ba ai sai ta kwaɓe su ko amma sam ba
haka take ba



Tashi nayi na kama hanyar part ɗin mu ina shiga ɗakina kawai nayi, na kwanta
kuka ne ya ƙwace min lallai maraici be yi ba


Inda ace iyayena suna nan a raye da ko hakan zata same ni zai kasance ya zo min da
sauki, amma yanzu bani da wanda zan tunkara


Don ko idan na faɗa wa anty fannah hana ni shan maganin zata yi tace sai na yadda
na yi cikin ni kuma kamar yadda baya son haihuwa da ni, nima haka na tsani haɗa
jini na da shi, wani wahalallen bacci ne yayi gaba da ni



Sai la'asar na tashi gabaɗaya bana jin daɗim jikina da kyar ma nayi dinner, ko
da na gama ma sam banci ba shayi na haɗa na sha sannan na kwanta sai bacci


Ina cikin bacci naji mutum yana tashina tare da balbale ni faɗan nayi bacci ban
jira shi ba


Kaina ciwo kawai ya ɗauka sakamakom tashin nan da yayi min, toilet na shiga nayi
wanka kamar yadda na saba in yazo nayi bacci nayi brush sannan na fito



Yana matsowa kusa da ni da ƙamshin turaren nan nasa ya doki hanci na sai naji
amai yana taso min, danne zuciyata mayi amma a gaskiya na ina cutuwa


Yana shirin ɗaga ni wani yunƙuri da nayi sai amai ya fito gabaɗaya na wanke masa
fuska da shi, sai da na amaye duk abinda ke cikina sannan na iya maida numfashi


A gaskiya turaren nan ya cutar da ni dani dayawa, ido na a rufe banyi aune sai
jin saukar mari nayi, na kuma jin wani a ɗayan gefe


Dafe fuskar tawa nayi na buɗe idon nawa, nan naci karo da fuskar sa wanke tas da
amai na, duk da zafin marin nan da nake ji amma hakan be hanani murmusa wa Allah ya
kara ya faɗa a raina



Ɗaga ni yayi ya shige toilet inda ya watsa ruwa yana fitowa ran shi a ɓace yace

"ki kwashe bedshit ɗin nan ki wanke min su tas idan na dawo da asuba na tarar da su
ba a wanke ba a bushe ba zaki gane kuren ki"


Ficewa yayi daga ɗakin ni kuma na miƙe tare da kwashe kayan shinfiɗar na nufi
toilet don wanke su, to me ya saka ni aman nan, ni ko kaɗan banci wani abun a zo a
gani ba balle ince ko shi ya ɓata min ciki
Ina wankin ina tunani na, ko da na gama sai na fita waje na shanya su sannan na
samu na tsarkake jikina ni ko ya gama ma oho masa, ban damu ba zani na na shinfiɗa
sannan na kwanta

Asuba ta gari 😴😴😴😴😴😴
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 19🌹




Da asubar fari ya zo lallai mutumin ya iya doka sammako tashi na yayi sannan ya
karta min warning kar ya sake ya dawo daga masallaci ban gyara ɗakin ba


Wanka na fara yi sannan na ɗauko shayata na gyara ɗakin, sannan nayi sallah
asuba, na idar ina lazimi ne ya shigo ɗakin nawa lkcn garin ya fara wayewa


Ƙamshin turaren sa ya fara dukan hanci ma wanda hakan ya sa zuciyata ƙara tashi,
da gudu na ruga toilet na fara amai, har banɗakin ya biyo ni


"wane irin iskanci ne yake saki wannan aman"

"wallahi ban sani ba ni bama abinda na ci" na faɗa a marairaice



Matsowa yayi kusa da ni ya damƙi gashi kaina sannan ya ɗago min fuskata wani
azaba naji ya ziyarci kaina fuskar nan tasa a tamke sam ba fara'a
"yaushe rabon ki da menstruation" ya tambaye


Shiru nayi don wallahi ni na manta ba calculating nake yi ba, indai yazo min
shikenan in bai zo ba matsalarsa, ƙara jamin gashin nawan yayi wanda hakan ya sani
sakin wani ƙara


"wallahi ban sani ba bana lissafi"


Sakin kan nawa yayi sannan yace

"ki yi brush ki fito ina jiran ki" brush nayi sannan na fito daga toilet yana
kwance akan gadon, alamar inzo in kwanta kusa da shi yayi min sannan yace min


"kika sake kika ƙara min amai wallahi sai na zane ki"


"wallahi warin turaren ka ne bana jin daɗin sa shi yake sani aman"


"Wannan matsalar kice don baki isa in dena saka turare ba saboda ke"


Ƙarasawa nai kusa da shi na kwanta ina mai ɗauke numfashi na, Allah dai cikin
ikon sa dai banyi aman ba amma kuma na wahala



Bayan ya fita ne naje toilet na kwarara shi kamar ba gobe kai wannan amai sai
kace me, kodai ciki gare ni 😱 ni mau naga ta kaina. Ciki a wannan marrar gaskiya
dole ne in faɗawa anty fannah don ta san abinyi



********************


Sabit yana fita daga ɗakin asmau ɓangaren mummy ya nufa, fuskar nan tasa kamar an
aiko masa da labari mafi muni


Tana zaune tana lazimi ya shiga ɗakin, sai da ta idar sannan ta juyo ganin
yanayin fuskar sa tasan ba lfy


"auta lfy me ya faru"

"mummy ina jin fa yarinyar nan ciki gareta kuma wallahi bana so"

"wake nan kake nufi kardai asmau"


"to in banda abin mummy cikin wa zan ƙi inba nata ba gaskiya i cant stand being a
father to her black kids" ya faɗa bayan ya firzar da wata iska daga bakin sa
"sabit baka ganin ya kamata kayi murna da farin ciki ganin cewar an daɗe ana neman
haihuwar amma sam badia bata haihun ba ɓarin ma da take yi kwana biyu shiru"


"mummy badia zata haihu tunda ta taɓa amma ni gaskiya banason baƙaƙen yara, itama
a matsayinta na matata ina manage ne da ita sannan kuma ace nazo na haɗu da ƴaƴa
baƙaƙe gaskiya bazan iya ba bana sooo"



Tsayawa mummy tayi sam tama rasa abinda yake mata daɗi, wai sai yaushe sabit
zai hankali ne ya fahimci halin matansa sam ita bata ga alamar badia tana son
haihuwa ba, asmaun kuma da zata iya haifa masa ko nawa ne batare da ta gaji ba shi
wai baya son kalar ta, hmmmm wannan abun yanzu gaskiya ya fara isar ta


"To yanzu me kake son ayi"


"mummy ai ba akan ta aka fara cikin da ba a so ba kawai sai a zubar da shi sannan
sai in ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan ta"


"kana nufin zaka zubar wa da asmau cikin da ke jikin ta, haba sabit me yarinyar
nan tai maka haka dat u soo much hate her"


"mummy sam baki fahince ni ba bana son baƙin ƴaƴa, farare nake so kamar ni, ki
duba cikin gidan nam kowanne ɗan sa fari ne haka kurum akai na sai a fara haifar
baƙaƙe kawai ƴaƴa na su zama bare a cikin dangi gaskiya banyi wa ƴaƴana wannan
planning ɗin ba ina son su saje a cikin dangi"


"to gaskiya ba da ni ba, duk yadda kaga zaka iya kayi tayi amma ni na riga na
dawo daga rakiyar ka kullum am trying my possible best inga na nuna maka amfanin da
darajar yarinyar nan amma kullum sai ƙara botsarewa kake yi to wallahi kaje kayi
duk abinda zakayi amma banda ni aciki"


Tana gama faɗar hakan ta miƙe tayi ficewar ta tare da barin sa a falon, sam be
tsammaci hakan daga wajen mummyn nasa ba ita me goya masa baya akan komai da yayi
amma wai yau itace ta zaɓi wata akan sa,


Lallai dole ko menene sai ya zubar da wannan cikin na asmau don bazai yadda ya
haifi baƙaƙen ƴaƴa ba, wayar shi ya ɗauko sannan ya kira wani abokin sa likita ne,
sun jima basu haɗu ba


Abokin nasan ya kasance me shegen neman matan tsiya wannan ɗabiar tasan ce ya sa
suka ɓata da sabit ɗin har suka raba hanya, yasan tabbas indai yana neman mata to
bazai hana sanin yadda ake zubar da ciki ba


Ringing ɗaya abokin ya ɗauka tare da cewa
"manya ashe za a neme mu"basar wa sabit ɗin sannan ya fara gaishe shi


Bayan doguwar gaisuwa da tambayar juna iyali sai sabit yace masa

"aboki na har yanzu ana halin ne ko an daina"


"wallahi sabit tunda matata ta haifi ƴa mace na sallama, sai dai ɗan abinda ba' a
rasa ba amma bana ɗaukar yara sai waɗanda suka jiƙu a abin kaga ban farka ba balle
a farke min tawa" ya ƙarashe zancen nasa cikin shaƙiyanci


"ashe dai ba a dena ba" inji sabit


"yo me za a fasa mutuwa ko hisabi muna dai fatan denawa kafin mu tsufa, don kar a
tsufa kuma ana bin ƴaƴan ciki"


"Allah ya shirya ka wato kai abin ma wasa ka maida shi ko to Allah ya baka sa a kar
ka shiryu ɗin" inji sabi


"kai fa ɗan iska ne ya ina neman shiryuwa amma kana min wani fatan, wai ma meye na
nemana nasan dai ba halin da nake ciki kake son jiba"


Shiru sabit ɗin yayi don shi sam be ma san ta inda zai fara ba, can dai da ta
matse shi sai yace


"wallahi abortion nake son ayi wa wata ban sani ba ko kana yi"

"ɗan iska kace kaima kayi joining grp ɗin namu ya akai haka ta faru bakwa using
protection ne"


"wane grp ɗin naku Allah ya kikaye ni, kai in kasan inda za ai min kawai ka faɗa
min bana son long story" ya faɗa a fusace don yanzu haƙurin sa ya fara ƙarewa


"sorry bro abin bai kai nan ba kawai ka shigo asibitin mu ana yi ni ma da kaina zan
mata kar
ka samu damuwa"


"kai ka isa wallahi baza ka taɓa min matata ba, in kuna da macen da zatai aikin ka
haɗa ni da ita in kuwa babu in nemi wani"


"haba bros kawai ka taho, amma me yasa kake son zubar wa da matar ka ciki"


"ai ba exams nake ɗauka ba balle ka tambaye ni kowane question sannan in amsa
wannan personal matter ɗina ne, ko kana so in dinga bayyana sirrin gidana gare ka"
inji sabit
"sorry bros kawai kuzo in shaa Allah kafin nan na tanadar da komai ready har dr.
ɗin"


"ok see u, zan shigo da daddare"


Sallama sukai sannan sabit ya koma part ɗin sa, yai wanka ya fice ko abinci ma be
tsaya ci don yarinyar haushin ta yake ji sosai wai tayi ciki to garin ƙaƙa hakan ta
faru lallai yayi sanya dayawa


Jiya jiyan nan yakai wa mummy pills akan ta dinga bata amma wai a yau wai a tashi
da ciki, kai wallahi da sake bazan iya ganin baƙaƙe a matsayin ƴaƴana ba


********************


Sai gab da la'asar sannan ya dawo, ina kitchen ya same ni ina wanke wanke


"idan anyi sallah la'asar zamu je a sibiti a duba ki wannan aman naki ban gane shi
ba"


To kawai nace na cigaba da aiki na, sai da na gama sannan, nai wanka na ɗauro
alwala na gabatar da sallah la'asr


Sannan na je falo na shi yana zaune

"na gama" na faɗa

"muje waje ki jirani gani nan zuwa"

Wajen na fita be wani daɗe ba sai gashi, motar muka shiga muka kama hanyar asibitin
hankali na a kwance nasan dai me za a ce ciki gare ni shine dai be san ina da shi
ba



Muna ƙarasawa asibitin ya kira wani abokin sa a waya sai kuwa gashi kamar daman
mu yake yi, gefe sabit ɗin ya ja shi suka fara ƙus ƙus ban san me suke cewaba daga
ƙarshe dai naji abokin yana cewa


"haba bros ai nai mata bayani baka da matsala"


Sai da suka gama gulmar su sannan suka ƙaraso, shi yayi mana jagora har wani ɗaki
in da muka tarar da wata likita tana zaune akan wata kujera


File aka buɗe mana sannan ta fara mana ƴan tambayoyi ina bada amsa iya sani na,

Sai da ta gama rubuce rubucen ta sannan tace min in kwanta a kan ɗan gadon da ke
ɗakin, kwanciya nayi sannan ta ɗaga min rigar da ke jiki na
Wani abu ta matsa min akan cikin nawa wanda yake a shafe kamar ba komai a cikin
sa sannan ta kunna ƴaɗ computer da ke kusa da gadon ta ɗauko wani abu tana goga shi
a kan cikin nawa tana kallon cikin computer


Sai da ta gama sannan ta bani tissue wai in goge, in sauko, hakan kuwa nai, ƴan
rubuce rubucen ta ta kuma yi a file ɗin nata sannan tace


"positive ya nuna cikine amma kama son ayi proceding da allurar"


"abinda ya kawo mu kenan"

"ok bari in rubuta mata sai kuje ku siya sai nurse tai mata ai bazai bada wani
matsala ba 6weeks kawai yake"


"ok mun gode" sam ban fahimci me take nufi ba na ɗauka tana nufin cikin bazai
bani matsala ba don haka sai muka karɓi



Allura ce guda ɗaya muka siya sannan muka je nurses room akai min, allurar
shegiyar zafi gare ta ga sagar da ƙafa, ko da muka fito sai muka kuma haɗuwa da
wannan abokin nasa inda ya ce mana ba wani matsala in muna son zama mu zauna in
kuma zamu tafi in matsala ta faru sai mu dawo


Sabit shine ya matsa mu tafi kawai don akwai abinda zai yi a office ɗin sa,
sallamar mu aka yi muka kama hanyar gida


A ƙofar gida ya ajiye ni, ina shiga ɓangaren anty fannah na nufa tana ganina sai
tace min

"naje wajen ku aka ba a san inda kike ba wannan ƴar iskar kishiyar" murmushi nayi
yadda anty fannah ta tsani badia ni ban tsane ta ba


"ni albishir ma na zo miki da shi amma kuma kin fara kawo zancen badia" barin
abinda take yi tayi sannan ta ƙaraso wajena


"ciki gare ki don ashine kaɗai albishir ɗin da za ki min inji daɗi" murmushi nayi
sannan na shafa ciki nace

"wata ɗaya" ina faɗa mata ina murna, rungume ni tayi tana murna nima ina yi, sai da
muka gama murnar mu sannan tace min


"asibiti kuka je aka tabbatar" gyaɗa mata kai nayi sannan nace mata


"har allura ma akai min me shegen zafi"

"allura kuma ta mecece" ta tambaya fuskar ta da alamar mamaki
"oho ni ban sani ba, don da muka shiga office ɗin su suke ta abun su banda ni"



"ƙila ko na ƙarawa babyn ƙarfi ne" inji ta muka ci gaba da hirar mu, har anty
fannah tana bani shawarar kar in sake in bari badia ta san da cikin sai dai kawai
ta ganshi



Hira tai hira muna ta yi can sai naji mara ta ta fara mintsini na, na share, abu
wasa wasa tun ina basarwa har na kasa na faɗawa anty fannah ga abinda nake ji faa


"ikon Allah tace ba yanzu kuka je asibiti ba akace muku lfy har da baku magani ba"


Gyaɗa kaina nayi bayan na cije leɓan ƙasa saboda azaba, wani murɗawa da cikin
nawa yayi sai kawai naji wani na fita daga jikina kamar fitsari


"anty fannah fitsari nake yi" nace mata

"fitsarin lfy tashi mu gani"


Ina miƙewa ta leƙa inda na zauna wani irin ƙara ta saki sannan ta kama hannun


"asmau zo muje a sibiti kar cikin nan ya zube" jikina ne ya fara rawa ina miƙewa
jinin ya cigaba da zuba yana bin ƙafa ta



Har mun kama hanyar fita sai taga ina zubar da jini don haka dole ta raka ni
toilet ɗin ta na gyara jikina sannan muka kama hanyar jikina sai rawa yake yi
kardai ɓari nayi



Asibitin da suke zuwa ta kaini inda nan da nan aka shigar da ni labour room, ciki
ya riga ya gama lalace wa, dƙn haka suka taimaka ya ƙarasa fita sannan suka dinga
min tambayoyi akan yadda abin ya faru



Tsab nai musu bayani abinda ya faru anan nurse ɗin ta gane allurar abortion akai
min, kuma cikin ya fita sam ba wani matsa, magani kawai aka bani sannan ta ce mu
fita tunda dai komai is normal



Anty fannah ce ta bita office inda tai mata bayanin abinda ya faru da ni da
kuma asarar cikin ya zube gabaɗaya bashi



Da

Please Login or Register in order to submit comment