You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara'a ne, ko gidan ne bakya son zuwa" ƙara cunkushe fuskata nayi, don naga
alamar waɗannan masu kuɗin da ka sakar musu fuska sai raini ko su mayar da kai wani
ɗan iska, don haka sai nai shiru nayi kamar banji ta ba
"hjy ina jin haka take don tunda muka fito banji tace ƙala ba, itama hjy munnirar
da take mata magana bata kula taba" mlm garba ya faɗa



Bata kuma cewa komai ba sai sallamar mlm garba da tayi sannan ta kira wannan
dattijuwar akan ta nuna min kitchen



INa shiga kitchen ɗin fridge kawai na nufa na buɗe, tsayawa nayi ina kallon abinda
ke ciki, babu ba abinda babu ta ɓangaren nama da veges



Kallon fridge ɗin kawai nayi na gane me ya kamata in dafa

``` chicken soup served with bread``` shine starter na

Sannan nayi ```grilled catfish served with jollof spaghetti with side salad``` a
matsayin main dish


Sannan sai ```water melon cocktail``` a matsayin dessert
*zaku samu recipe ɗin a ƙasa page ɗin in shaa Allah*


Na riga na saba da three course meal, duk ina in dai lunch ne kƙ dinner, ina
gamawa nayk serving ɗin shi a kan dinning table sannan nazo nace mata na gama


Ok kawai tace min bari inyi sallah magariba sai kizo kiyi serving ɗina,


Ban tanka mata ba sai ta kira wannan dattijuwa akan ta nuna min inda zan yi
sallah, bin ta nayi naje na gabatar da sallah magariba ta nai nafilar dana saba yi
ta bayan magariba sannan nai addua ta dana saba akan Allah ya zaɓa min komai na al
khairi sannan ya haɗa ni da miji na gari in dai ina da rabon aure



Tunda gaskiya ni bana sha'awar komawa azore har abada, anan kuwa wa zai auri ƴar
baƙa kamar ni




Sai da na idar sannan naji matar nan tace min hjy na kiran ki, ƙarasa wa nayi falon
nata na shiga da sallamata, tana zaune ita da wani ɗan matashi,


Bazan iya kallon fuskar sa ba saboda ya juya wa ƙofar baya itace ta amsa min inda
shi kuma hankalin sa yana kan wayar sa yana ta daddanawa


"kin ƙarasa ko zo kiyi serving ɗin mu don har na fara jin yunwa tun ɗazu ƙamshin
abincin nan ya dame ni" ta faɗa da fara'ar ta wanda nima yakamata in mai da mata da
martani amma sai na share ta kawai nayi wajen table ɗin



"auta zo muyi dinner" naji tace wa saurayin ok, kawai yace sannan ya ajiye wayar
ya ƙaraso wajen dinning kallo ɗaya yayi min inda ya ɗauke kansa dama ni can bashi
nake kallo ba


"mummy me kwashe kwashe ina kika samo ƴar somalia" ya faɗa yana ƙoƙarin zama akan
kujera, dariya mummyn tayi

"asmaun ce ƴar somalia, zo kiyi serving ɗinmu kinji ƙyale wannan he likes to joke
alot"


"sincerely speaking mum am not joking, kamar aljana haka take ga baƙi ga fuskan
ta sam ba fara'a balle annuri"



Ga mamakina sai naji mummy na dariya har da ƙara kallo na na ɗauka ,zata kwaɓe
shi amma sai naga saɓanin hakan wannan ne yasa na ƙara ɗaure fuskar tawa na fara
serving mummy da soup ɗin wanda za a ci shi da bread



Na gama sai na matso zanyi serving ɗin

"in kika taɓa bowl ɗin nan bazan ci abinci ba" naji ya faɗa, ai kuwa da sauri na na
ɗauki bowl ɗin na zuba soup ɗin sannan na dangwarar masa a gaban sa



Tsayawa sukai suna kallo na inda ni kuma na gyaɗa tsayuwa ta irin ta cooks
waɗanda sukan abinda suke yi sannan na ɗauke kaina daga gare su



Buɗe baki yayi zai yi magana sai naji mummy ta dakatar da shi

"asmau me yasa kika zuba bayan yace idan kika taɓa bazai ci ba" kallon inda take
banyi ba balle in kula ta



"mummy wallahi bazan ci abinda wannan ƙazamar yarinyar ta taɓa ba" ya faɗa yana
miƙewa hana shi mummy tayi sannan ta ɗauko sabon bowl a kitchen ta sake zuba masa
ta miƙa masa


"mummy bazan ci abinci ba wannan abun tana nan don sai in ƙware"


Mummy ce ta kira ni sannan ta sallame ni juyawa nayi zan fita inda naji yana cewa


"haba mummy me zakiyi da wannan fuskar ta kamar ta aljanu, gata ƴar ƙarama da ita
dai dai suffar aljanun wannan in ka ganta cikin dare ai sai ka zura a guje" yana ta
kushe hankalin sa akwance kamar be san cewar ina ji ba inda ita kuma mummy abin
yake ta bata dariya



Takaici me kawai ya gama kamani ina fita na samu wani ɗan lungu na zauna sai
kuka, mutum be sanni ba amma kalmar daya fara jifa na da ita shine kalmar kama da
aljanu




Sai da suka gama ya fita daga part ɗin natan sannan ta kira ni na shiga, na tarar
da ita tana waya daga ji da hjy munnira take don naji tana cewa


"lallai na yadda ƴar baiwa ce kinga yadda sabit yake ta santi wai ya ɗauka ni na
girka" shiru tayi daga gani hjy munnira tana magana ne



Ban hana su hirar su ba sai da suka gama sannan ta juyo gare ni


"asmau sannu da ƙoƙari gaskiya naji daɗin abincin ki, kuma ina fatan har a gama
bikin nan zaki ci gaba da kawo mana daɗaɗan abincin ki"



Ban tanka ba ta ci gaba da min bayanin irin yadda take son abincin baƙin ya
kasance, breakfast, lunch, and dinner duk ni zan dinga yi amma da taimakon
ma'aikatan gidan



Sai da ta gama bayanin sannan ta sa aka raka ni boys quaters inda main kitchen na
gidan yake, na gani kuma naga komai sannan aka nuna min ɗakin da zan zauna wanda
bashi da nisa da kitchen ɗin sannan anan ne ma'aikatan gidan suke



Sallah isha kawai nayi na kwanta dama ni hira bata dame ni balle raba dare, ina
kwanciya nayi addua sai bacci 😴



*******************



Kashegari da sassafe na tashi na haɗa breakfast aka kai wurin mummy, sai gata ta
aiko wai in zanyi lunch inyi dayawa domin yau za a fara zuwa



Kasancewar bansan mutanen da zasu fara zuwa ba sai nayi waina da sinasir da
miyar taushe me tantaƙwashi, domin kuwa ɗai ɗai ne za suce basa son waina
Sai ƙarfe 01 :00pm sannan na gama inda aka zo aka kwashe, kafin kace me wannan an
dawo da coolers ɗin wai a kuma ɗaura wani abincin akwai baƙi masu zuwa da yamma



Haka na dinga girki in sauke wannan in ɗaura wancen kamar ba gobe, kusan duk
ma'aikatan yan iska ne sai dai su saka min ido ni kuwa da ince wance zo kiyi kaza
gwanda nayi da kaina



Wannan ne yasaka bana samun zama kuma cikin hukuncin Allah kowane course a kan
lkc nane gama shi,



Abinci ne kamar ba gobe nake dafawa don ma banayi wani dayawa amma sai dai ina yin
abinci kusa kala goma a lkc ɗaya banda soups, snacks drinks duk course sai na haɗa
da waɗannan



*******************



Sabit ango sai ƙamshi ake ta zuba wa burin shi ya kusa cika ya mallaki macen da
yake ganin kamar babu kamar a duk faɗin duniyar nan


Duk wani preparation da za ayi na bikin anyi shi kuma an shiga bikin lfy, inda
aka abokanan sa suka haɗa masa dinner a sheraton hotel, sannan akai arabian night
sannan a kai mothers eve ranar kai amarya a nan gidan su sabit ɗin




Duk wanda ya ga amarya badia sai ya yaba kyan ta don kuwa gaskiya ta ɗau wanka da
gyara sai dai muce Allah ya bada zaman lfy



Duk wannan abunda ake yi asmau tana kitchen tana ta faman sarrafa abinci kala
kala wanda yake barin mutane da tanɗe hannu sannan ga santi


Sai da aka gama biki sannan ta nemi tafiya, mummy sam bata so amsau ta tafi ba
saboda ta riga ta saba da abinci yarinyar amma ya zata yi



Ta haɗa mata kayan gara sannan ta saka driver ya kai mai da ita, inda ita kuma
asmaun take jim kamar an mata bushara don kuwa gaskiya ba ƙaramin gajiya take yi ba
ga rashin sabo da muatanen



Duk da dai nan ma ɗin ba wani jan mutane take yi a jikin ta ba amma ai nan ta
riga ta saba da nan ɗin,



****************



Amarya badia ta tare lfy, to akwai wani al ada da suke yi a gidan inda ɗuk wacce
ta shigo idan tayi sati biyu zatai girki duk a haɗu a babban falon gidan gabaɗayan
su aci girkin amarya



To itama amarya badia mummy ta aika mata da wannan saƙon cewar zatai girki,
hankalin badia ne ya tashi domin ita tunda take tafasar ruwan zafi ma bata sani
balle wani girki



Bata ji komai ba ta kira sabit ta faɗa masa ita fa bata iya girki, sam sabit be
ji komai ba, ai ba lalle ne ba ace mace dole sai ta iya girki

shi wannan karin maganar da ake cewa ```women belong to d kitchen``` sam be
yadda da ita ba taya zayi ace don namiji be iya girki ba ba komai kuma wai mace
idan bata iya ba sai ya zama tashin hankali




shi zai nuna wa duniya cewar matar sa bata iya girki ba kuma ba wani abu bane
kawai ra'ayine kuma da ita kaɗai zai zauna har iyakacin rayuwar sa har illa maa
shaa Allah




waya ya ɗauka ya kira mummyn sa ringing ɗaya ta ɗauka

"yau matar ka ce da girki da fatan ka bata kuɗin da zatai cefane"


"mummy dama abinda yasa na kira ki kenan gaskiya badia bata iya girki ba kuma ni
dama ban damu ba ace wai lallai sai mace ta iya girki don haka a cire ta a cikin
wannan tsarin, waɗanda suka saba girkin su ci gaba don matata bata iya ba kuma ni
ma nayi supporting ɗin ta ai ba dole ne mace sai ta iya girki ba"




Mummy mamaki ne ya kamata har ta kasa cewa komai, har sabit ɗin ya kashe wayar,
wai matar sabit bata iya girki ba kai wallahi da sake



Nufin ta abincin masu aiki ɗanta zai dinga ci ko me, mitar ta ta dinga yi har ta
gaji tayi shiru tunda babu me lallashin ta
Takan yi takaicin rashin haihuwar ƴa mace da batai ba, don wani lkcn ƴaƴa mata ma
daɗi gare su, barin ma a irin wannan lkcn da tana da mace da ba sakata ta mata
maganin su ba



Kuma gashi ikon Allah dukkan nin ƴaƴan natan ukun da suke da aure da ƴaƴa babu me
ƴa mace, duk jikokin natan maza ne, kullum burin ta Allah ya bawa ƴaƴan ta ƴaƴa
mata lallai da anga tarbiyya




*menu of d day*

```chicken soup served with bread, grilled fish served with jollof spaghetti and
side salad, melon cocktail```



```chicken soup```

```ingredients```

-chicken breast (tsokar naman na ƙirjin kaza)
-albasa
-tafarnuwa
-maggi
-curry
-flour



_method_

1) ki sami chicken breast din ki, sai ki wanke tas sannan ki yanka shi ƙanana
yankan cubes


2) ki ɗauko tukunya ki saka naman, maggi, tafarnuwa albasa, sai ki rufe don ya
dahu


3) idan kazar ta hadu sai ki tsame naman sannan ki sai ki sauke ki tace, ruwan
naman kawai ake so, sai ki ƙara mayar da tacecen ruwan namaki akan wuta don ya kara
tafasa ki zuba naman kazar ki zuba curry


4) ki dauko flour ki kwaɓa shi da ruwa kamar zakiyi wainar flour sai ki zuba a
ruwan idan ya tafasa sannan ki rage wutar sai kiyi ta juya wa kar ki ɗauke hannu
don sai yayi miki gudaji, idan yayi ɗan kauri sai ki sauke a ci da bread


```grilled fish served with spaghetti and side salad```
```Ingredients```

_grilled fish_


-kifi
-albasa
-tafarnuwa
-citta
-attaruhu
-curry
-man gyaɗa


```method```

1) ki wanke kifin ki tas sannan sai ki ajiye shi a gefe

2) ki ɗauko kaskon gashin ki sai ki ɗan goga masa mai, sannan ki saka kifinki,

3) ki barbaɗa masa maggi, ki yanka albasa slice, a jajjaga tafarnuwa da citta da
attaruhu duk a zuba akan kifin sannan ki barbaɗa curry sannan a gasa a oven kar ki
sakar mata wuta don sai ya ƙone idan ya gasu sai ayi serving


_spaghetti_

```ingredients```
-spaghetti
-kayan miya
-mai
-maggi
-curry
-albasa


1) ki zuba mai a tukunya da ƴar albasa idan ya ɗauko soyuwa sai ki zuba kayan
miyar ki ki ci gaba da soyawa


2) idan kayan miyar sun soyu sai ki zuba ruwa da maggi curry sai ki rufe

3) a wata tukunyar daban kuma ki zuba ruwa idan ya tafasa saiki zuba taliyar ki,
kar ki bari ta dahu tafasa ɗaya biyu sai ki sauke ki tace sannan ki wanke ta
(wannan yana sawa idan kin gama taliyar ki ruwan taliyar bazai yi kaurin nan ba)


4) idan ruwan kayan miyar ya tafasa ki ki zuba tafasasshiyar taliyar ki sannan ki
rage wuta ki zuba lawashin albasa, idan ya ɗan kara tafasa sai ki sauke

_side salad_

```ingredients```
-tomato
-gwanda

```method```
1) ki yanka tomatoes ɗinki sannan ki yanka gwandar ki duk cubes zaki yanka sannan
sai kiyi serving kusa da taliyar ki da kuma kifi



_melon cocktail_

```ingredients```

-kankana
-sugar syrup


_method_

1) ki yanka kankanar ki cubes ƙanana bayan kin cire ƙwallayen,

2) ki zuba sugar da ruwa a tukunya ki ɗora a wuta idan ya tafasa sai ki sauke idan
ya huce sai ki juye a kan cubed kankanar ki ki saka a fridge idan yayi sanyi sai
ayi serving a ci da spoon


*bon appetit*



*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 6🌹




Mummy rasa yadda zatayi da sabit gashi kowa ga san ran girkin matar sabit gashi
shi kuma ya kira yace baza tayi girkin ba


Ita ba wannan ne ya fi damun ta ba tunda yarinyar nan asmau mara fara'a ta tafi
abincin gidan kamar cusa shi take sam bata jin daɗin sa
Juyi ta dinga yi akan gado tana ƙarawa daga ƙarshe ta tashi ta dauki land line na
gidan ta kira kitchen knda ta shaida musu suyi musu dinner gabaɗaya gidan


Abin yabawa ma'aikatan mamaki saboda da safe ta kira tace karsuyi amma kuma yanzu
ta kira tace suyi


Sai da yamma tayi kowa ya dawo daga aiki duk an hallara wajen cin abinci za a
fara ci sai mummy

"to amaryar sabit dai bata iya girki ba kuma mijinta ya ɗaure mata gindi yace shi
ba komai ai ba sai lallai mace ta iya girki sannan za a zauna da ita ba"


" haka ne mu ba kowacce mace ce akayi ta domin kitchen ba" maganar nan tayi
bala'in ɓatawa mummy rai inda ta kai masa harara


"to daga yau sai ku dinga cin abinci a part ɗinku in cook zaku ɗauko bismillah amma
mun daina ciyar ku"


Babu wanda ya kuma cewa komai mummy ta so daddy ya mara mata baya amma sai taji
yayi shiru dama shi mutum ne me bin ra'ayin ƴaƴan sa


Sai da suka gama cin abincin ne sannan mummy ta kuma nanata musu akan su nemi me
ciyar da su don ta tsame su daga waɗanda zata dinga ciyar wa, ko a jikin su daga
badiar har sabit ɗin suka kama hanyar part ɗin su



Kashegari badia ta kira mmn ta ta faɗa mata abinda yake faruwa da kuma hukuncin
da suka ɗauka na ɗauko cook,



Mmn badia ta sha alwashin sai ta nemo musu cook ɗin da ita kanta mummyn ma a
wajen su zata dinga kwaɗayi



Cikin hunkuncin Allah aka samo musu wata agnese kafira ce, amma tsohuwar cook ce
abincin ta da daɗi kasancewar ta daɗe tana yi


Kafin su tashi da safe ta haɗa musu breakfast haka ma kafin su dawo da yamma ta
ajiye musu lunch haka ma dinner akan lkc wannan ne ya kwantar da hankalin
ma'auratan ya kasance ba abinda suke yi daga aiki sai soyayya 😍



Ana haka ana haka badia ta samu ciki, me shegen laulayin tsiya ga miyau, ga
shegen kwaɗayi, rannan da sassafe ta na tashi wa alala zata ci, don haka sai sabit
ya sauko ƙasa don gayawa agnese tayi mata alala
Me zai gani agnese ce a kitchen hannun ta a hammat sai faman susa wa take yi,
tana gamawa ta saka shi a hanci ta shinshina yana gani yadda ta ɓata rai daga
dukkan alamu bata ji daɗin warin da hammatar ta take badawa ba sannan ba wanke
hannu kawai ta koma ta ci gaba da girkin ta



Jun shi yayi kamar zai yi amai tunanin girkin ta daya dinga ci yayi, ji yayi
gabaɗaya zuciyar shi na tashi, be yi ƙasa a gwiwa ba yana zuwa ya gayawa badia
abunda ya gani



Aikuwa itama sai amai anan inda take, abu goma da ashirin ya haɗu ya haɗar wa
sabit, shi yayi aikin aman sa don ba ba komai a aman sai ruwan da tasha



Badia da kanta ta kori agnese sannan ta kira mmn ta akan a nema musu wata sabuwar
cook ɗin ko da mmn ta tambaye ta ina agnese sai ta faɗa mata abinda sabit ya faɗa
mata



Ita kanta mmn ta koka da wannan abu inda tai mata alaƙawarin sake neman wata me
aikin, too fa aiki ya dawo sabit sabo, ya je aiki a hanyar shi ta dawo wa doƙe ya
tsaya a restuarant ya sai musu abinci kafin ya dawo



Wani lkcn in ya makara sai dai ya kira badai ta siyo musu haka suka dinga jaurar
siyan abinci sune shiga wannan restuarant fita wancan don siyan abinci



Rannan sai ya kama ranar da badia zata siyo abinci ne amma sai ta manta sabit ya
dawo gida gajiye ga yunwa ko da ya tanbayi abincin sai tace masa ba kak bane da
siyowa



Ranshi ne ya ɓaci don abun nata kamar da rainin wayo,

"so nawa zan siyo jiya ba ni na siyo ba" ya faɗa ranshi a bace, ɗaga kafaɗar ta
tayi alamar bata damu


"na manta na ɗauka kai ne yau ma" ranshi ne ya ƙara ɓaci wato ita sam bata ma san
laifi tayi ba ko, nan da nan ya hau masifa inda itama ta biye masa sukai ta bala'i



Wannan shine faɗan mu me girma na farko tun aurensu amma sun yi faɗa kamar ba
gobe daga ƙarshe kowa yayi zuciya ya kama hanyar ɗakin sa baza a kwana tare ba, a
daren badia tai ɓari
Sabit be sani ba sai da safe da ya fito ya ganta a falo da akwati tana ta ja ita
zata tafi gidan su kamar ya share ta sai kuma dai ya tambaye taa

"ina zaki da akwatin nan haka"


"gidan mu zan koma tunda wanda ya ajiye ni be damu dani ba har nayi miscarriage be
sani ba"




Kalmar miscarriage ce kawai ta dawo da shi daga tunanin da yake

"what, me kika ce" ya faɗa yana kara matsawa kusa da ita cike da tashin hankali
maimai ta masa tayi tayi ɓari



Jikin shi har rawa yake ya sunkuce ta sai mota yana ta adduar Allah yasa ba
gaskiya bane cikin daya ƙwallafa rai da shi za a ce ya zube subhanallah



Gudu kawai yake falfalawa domin son zuwa asibiti sai da badiar tai masa magana ma
akan ya rage gudun sannan ya rage burin shi su je asibitin ace bai zube ba


Cikin ikon Allah suka iso asibitin da badia ke awo suka shiga wajen ganin dr.
binciken farko ya nuna ciki babu shi



Sabit kamar yayi kuka a rayuwar shi yana son yara barin ma ace yadda badia ke da
kyan nan a haɗa da nashi ai Allah ne kaɗai yasan irin kyan da ƴaƴan su zasuyi



Hankalin sa ne ya tashi sosai inda duk ya bi ya tsagwami kansa don shi a tunanin
sa faɗan da sukai jiya ne ya zubar mata da cikin




Badia sam hankalin ta be wani tashi ba kamar yadda sabit ya tashi nashi hankalin
daga ƙarshe ma sai ita ce ta koma tana lallashin sa

" haba *SD* kar ka damu in shaa Allah we will try again, kuma cikin be fi wata
biyu"

"only kin kuwa san yadda na ɗaura raina akan cikin nan wallahi nagi nake yi kamar
fault ɗina ne da bamuyi faɗa ba da ƙila cikin bai zube ba" ya faɗa da alamar
tausayi a tattare da shi



Lallashin sa ta dingayi, bayan an basu magani an sallame su sai ta saka rigimar
ita gida zai kaita har ta warke


Ba haka ya so yaso ace ta dawo gidan sa tayi jinya amma ganin bata da lfy ya shi
ƙin cewa komai kawai yai hanyar gidan su da ita



Yana ji yana gani ya kai badia gidan su ya baro ta acan don ta samu ta ɗan huta,
kuma ta samu sauƙi, ko da ya dawo gida ya faɗawa mummy abinda ya sameta



Sai mummyn ta jajanta masa sannan tai masa ƙorafin zuwan badia gida, kyakkyaɓe
mata fuska yayi kamar zai yi kuka, wannan ne ya sa ta jan bakin ta tayi shiru




********************


Sai da badia tayi wata guda a gida sannan ta dawo shima sai da sabit yai ta safa
da marwa yana roƙon ta sannan ta dawo anna wannan karan ma da sabuwar cook ɗin su



Me suna kulu, to ita matsalar klu bata iya kowane abinci ba sai tuwo da dai
dangin na gargajiya bayan kuma su sabit ƴan zamani ne ba son tuwon suke ba



Wannan dalilin ne ya sa kulu bata daɗe ba suka sallame ta, suka koma take away
daga restuarant



Duk abinda ke faruwa a part ɗin sabit mummy tana sane ta ƙyale shi ne kawak don
taga iya gudun ruwan sa



A ka ci gaba da yin take away har Allah ya kuma haɗa su da wata sabuwar cook ɗin,
ita kuma sata duk abinda ta gani sao ta ɗauka ta ɓoye da taga lkcn ba mutane sai ta
fice daga gidan



Rannan sai ta ɗauki agogon sabit ya ajiye akan dinning table yana breakfast
kawai ya shiga ɗaki ya fito ya nemi agogo ya rasa



Tun yana nema shi kaɗai har badia taji suka shiga nema tare, abu kamar wasa agogo
yayi ƙafa ya gudu


Sam basu kawo ita ta ɗauka ba don har da ita ake ta nema, sai badia ce kamar ance
ɗaga idon ki ki kalle ta sai taga gefen zanin ta yayi wani ƙulili
Tambayar ta tayi

"ke meye a jikin ki haka" nan da na sa jikin yarinyar ya ɗaurawa, badia kuwa ta
kwacume ta ta kwance mata zani sai ga agogo



Shidai sabit tunda ya ɗauki agogon sai ya fice ya barsu inda badiar ke ta dura
mata zagi, daga nan ita ma ta kore ta,



Abinfa ya fara isar sabit wai duk masu girkin da aka samo musu sai sun samu
matsala ne me yasa baza su samu cook ɗaya ba mtsss Allah dai ya kyauta



Kuma neman wata cook ɗin sukai inda aka kawo musu wata tivi, kana ganin ta kaga
rashin tsabta, har wani tashi take don tsabar tsamin da ke fita daga jikin ta



Sabit sam hankalin sa be kwanta da ita ba don shi mutum ne me shegen ƙyanƙyami
don haka ko tayi abinci baya ci sai dai yai ta raɓe raɓe yau shine cin abinci anan
gobe a can



A maimakon shi da yake da mata a ganshi ya murmushe sam sai ma wani ramewa yake
yi, ya ya bazai rame ba sam baya samun kulawa ko ta ɓangaren cin abinci balle
kyakkyawan kula daga matar sa



Sun tashi da safe sun fice gabaɗaya idan sun dawo da yamma kowanne su a gajiye
yake don haka kowa ta kai ta kai yake balle badia ita bata san wani wahala da wani
ba balle tace wannan mijinta ne ai ba yaro bane zai iya kula da kanshi haka take
cewa



Tun mummy na ɗauke kai har abin ya zo ya fara damunta ta kasa shiru kun san
tsakanin ɗa da mahaifi balle kuma mummy me shegen son ƴaƴa



Don haka rannan da ya shigo da safe gaishe ta sai ta gabatar masa da abinci be ji
komai ba ya zauna ya takr cikinsa kamar wanda ake wa horon yunwa


"yanzu sabit rayuwar da ka ɗaukar wa kanka kenan ta horƙn yunwa, baza ka zauna ka
faɗawa

Please Login or Register in order to submit comment