You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaskiya
baza ta saɓu ba shi dai wallahi sai an bashi matar sa,


Har ɗakin mummy ya shiga ya shigo ɗakin da nake ina ta haɗa kayana annur kuma
yana zaune kusa da ni


Sam yaron ya kasa sakin jikin shi da kowa, wai wasa da zaka ga yaro yana yi ko yai
ta guje guje ko kuma yai ta yawoce yawoce sam annur be san wannan ba
Shi dai yafi san kullum yana kusa da ni,

Banji sallamar sa ba kawai sai jinayi ya rungume ni ta baya

"asmau don Allah kar ki tafi ki barni wallahi duk abinda kike so zan miki, wallahi
ko bawanki kike son in zama zan zama amma ida kika tafi ya zanyi"



Ban gama sauraren soki burutsun saba na yakice shi daga jikina don nasan innace
zan saurari uzurin sa har ƙarshe ƙila ya karyar min da zuciya


"sabit ka fita ido na aure ne nace ma gama na ɗauka daddy yai mana katangar ƙarfe
tsakanin mu, shin wai sai yaushe zaka san cewar ni da kai is over"


Dafe kansa yayi, yana saurare na ina kwaɓa masa duk wata magana data fito daga
bakina, hmmm lallai ruwa ya daki babban zakara, sabit ne a da zai zauna ina kwaɓa
masa be ɗauki mataki akai na ba


Mummy ce tazo ta janye shi jikin shi gabaɗaya ya gama mutuwa da maganganu na,
ina kallon ta tana share hawaye da gefen zanin ta nace ai duk wanda yai shuka
tabbas wataran dole ne yai girbi




*******************


Kashegari da sassafe muka kama hanyar sabon gidan mu da anty fannah sai isma'il


Flat biyu ne na ɗauki ɗaya suma suka ɗauki ɗaya, naji daɗin yadda tsarin gidan
yake ɗaki uku ne a kowanne flat, kowane ɗaki da toilet ɗin sa


sai falo sannan kitchen da store, kuma kowanne ɗaki ya sha gyara sosai komai an
saka, hatta kitchen da store ɗuk a cike suka, ɗaki ɗaya na ɗaukar mana ni da annur
ragowar na rufe


Rayuwar abin sha'awa da daɗi sam babu wani hayaniya, idan isma'il yana gidan a
flat ɗina nake kwana idan kuwa bayanan can wajen anty fannah nake tare wa wacce
itama yanzu take laulayi


Duk da dai bata gaya min ba amma kana ganin yanayin ta kasan ta harbu,


Bamu daɗe ba mummy ta zo ta kawo min me aiki wata mata iya sannan ta kawo min duk
wata siyayyar da tai min na haihuwa,


Mun sha hira da ita sosai inda take ƙara bani haƙuri akan sha'anin sabit, a bakin
ta nake jin wai badia iyayen ta sin dawo da ita
Amma sam babu zaman lfy da ita da sabit kullum sai faɗa, wani ƙululun baƙin ciki
ne ya tokare min wuya wato samun badia ne ya sa shi ko sau ɗaya be taɓa zuwa ganin
mu ba ko


Sam ban ɓoye fishi na sai dana gaya wa mummy

"ai badia tafi annur shiyasa tunda muka tare be taɓa zuwa yaga ɗan sa ba" na faɗa

"ayya asmau ba haka bane, daddyn ku ne yace idan yaji labari daga gare ki cewar
sabit ɗin yana takura muku da zuwa sai ya saka shi ya sake ki a take shiyasa ya ƙi
zuwa, amma wallahi kullum kuna ranshi kullum sai yayi hirar ku" ta faɗa a sanyaye


"mummy to idan yazo ya ga ɗan sa sai in kai shi ƙara"


Murna naga ta nuna sosai

"kai amma naji daɗi sosai asmau lallai ke ƴar halak ce kuma in shaa Allahu zan
sanar da shi ya zo ya dinga ganin ɗan sa"




Mun sha hira sosai da mummy dan bata tafi ba sai da akai isha ni nai mana girki
taci tana ta santi wai tayi kewar abimci na



Har mota muka raka ta mukai sallama da ita sannan na dawo, kasancewar an kawo min
me aiki yasa ranar nan kwana a part ɗina


Cikin dare na tashi da naƙuda, ni kaɗai nayi abuna kamar wasa sai gashi Allah ya
sauke ni lfy


Baaba wacce mummy ta kawo sai jin kukan jaririya taji, ta fito

"ƴan nan ai sai ki ce min abin yazo amma sai kika yi ke kaɗai"


Ban tanka mata ba saboda duk da dai babyn ta faɗo amma wani irin ciwo nake ji
kamar ba ayi abinba,


Janye jaririyar ta tayi wacce sai tsanya ra kuka take duba na kai ga jaririyar da
ta buɗe bakin ta kamar me


Wani shegen murmushi nayi duk da dai ciwo naji na amma hakan be hanani murna da
jin daɗi ba


Kalar da sabit yake sooo ne wato baƙi, baƙa ce yarinyar amma daga dukkan alamu
baza ta kaini ba amma kuma sam babu alamar zatayi haske
Tsakanin ta farkon da ta biyu be fi minti biyar ba itama ta faɗo kamar su ɗaya
sannan kalar su ɗaya


Wayyo ya zanga fuskar sabit idan yaji labarin na haifi baƙaƙen ƴaƴa lallai akwai
drama a gaba


Tsab baba ta kimtsa mu ni da babies ɗina waɗanda abin takaici kamar su ɗaya da
annur wada hakan yasa suke kama tas da bbn su


Sam na so ace ƴaƴa na da ni suke kama amma ba hakan Allah ya so sai ta ta shirya
mu tsab sannan ta kama hanyar part ɗin anty fannah don ta gaya mata
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 27🌹




Ina kwance sai anty fannah,


"lallai me jego kice kina hanya amma shine ba a kira ni ina can na saki baki ina ta
bacci"


Murmushi kawai nai mata, ƙarasowa kusa da babies ɗin tayi tana ƙoƙarin ɗaukar ɗaya
"lallai maa shaa Allah kalar mu kalar da sabit baya so zan ga yadda zai yi yanzu da
Allah ya haɗa shi da kalar mu"


Murmushi na kuma yi

"wallahi nima anty tunanin da dinga yi kenan"


Tattaunawa muka dinga yi da ita akan irin reaction ɗin da sabit zai ɗauka idan ya
ji labarin ƴaƴan baƙaƙe ne biyu ma ba guda ɗaya ba



Sai gab da asuba sannan bacci ya kwashe ni bayan na sha tea me kauri da anty
fannah ta haɗa min


Ban san lkcn da anty fannah ta kira mummy ba nidai kawai naji muryar ta ne a
kaina tana cewa


"maa shaa Allah fannah kin yaran nan wallahi gaba ɗayan su kama suke yi sabit"


"haka ne kuwa
mummy amma inda za ai rikici da shi idan yaga kalar su"



"hmmm fannah sabit ɗin daa kika sani na yanzu ba me tsirface tsirface ba na yanzu
yayi laushi, jiya dana koma gida ake bani labari har get ta bishi tana zagin sa
tare da ci masa mutunci,


Hmmm wannan ƴar iskar yarinyar da badan daddyn ku yace inya sake ta sai ya sashi
ya saki asmau ba wallahi da tuni ya manta ya rabu da ita


Wallahi yanzu zancen da nake gaya miki tun daya fita tun jiyan har yanzu be dawo
ba, a hanya ma ina ta trying ɗin shi in faɗa masa haihuwa amma wayar shi a kashe"


Tausayi ya bani wallahi sosai, kai gaskiya banji daɗi koman lalacewar sabit uban
ƴaƴana ne kuma bazan so wani abun ya same shi ba


Tunda indai akwai wani ya same shi sai dai ƴan uwan sa su koka amma kuma ƴaƴan har
abada a rayuwar su haka zasu kasance suna masu rashin uba


Tashi nayi na gaishe ta da fara'ar ta amsa min da


"sannun asmau abinda bamu taɓa samu ba kika kawo mana ƴaƴa mata, tunda aka faɗamin
na faɗawa daddyn ku yake murna don ma yana da meeting ne da wasu turawa amma ana
tashi zaki gan shi, suma ƴan uwan naku nasan yanzu zaki gansu"
Bata rufe bakin ta ba kuwa sai ga sallama

Dukkan mutan gidan ne suka shigo, dole ne ya sank fitowa parlour saboda yawan su



Sai hayaniya ake tayi tare da murnar samun mace a dangi, barin ma mummy ta ɗauki
babbar ta goye ta baya duk wanda zai ganta sai dai ya ganta a bayan ta sai dai
ƙaramar ce ake ta passing passing da ita


"mummy don Allah muga ta bayan ki" inji kishiyar anty fannah

"wannan da kuke ganin ta takwara ta ce shiya sa bana son a jagwalgwala min ita"
mummy ta faɗa


Ana haka mazan ma suka ƙaraso amma banda sabit ko ba komai ai zan ji daɗi idan na
ganshi ko amma sam be zo ba


Duk wanda ya zo gidan nan murnar samun ƴa mace yake a dangin nan, don kuwa har
zuwa yanzu mummy bata da jika mace sai maza sai waɗan nan baƙaƙen dana haifa


Abinda ya min daɗi da ƴan uwan sabit da matan su shine babu wanda ya luɗa da cewar
yaran.ba farare bane sam ba wanda ya kawo wannan


Kawai yaba kyan yaran suke yi, suna ƙara musu adduar Allah ya raya su cikin
addinin islama


Ana cikin hakan ne daddy ya zo, kasancewar parlour ɗin a cike yake yasa sam bamu
ji sallamar sa ba duk an saki baki ana ta hira akan jariran da Allah ya hana kowa a
dangin ya ba sabit



Sai da daddy ya daka tsawa sannan aka san ya shigo


"haba tun ɗazu na shigo a miƙo min yaran in gansu amma kun saki baki sai zuba kuke
yi kamar ƴaƴan kanya, dan Allah a miƙo min da baƙi nake a waje


Na kasa zaman meeting ɗin ma sai ce musu nake yi ba a taɓa haihuwar mace a gidana
ba sau yau kuma Allah ya bamu guda biyu"


Sai da kowa ya dara da maganar daddy, is'mail da muktar ne suka fita da babies
ɗin sai a lkcn mummy ta sauko babbar



Sunfi awa guda sannan suka dawo inda daddy yace


"lallai yaran nan daga gani da albarka suka zo, mutanen nan suna ganin su sukai
mana signing contract ɗin da mukai kusan wata biyu ana ta fama akan ta, lallai in
gama suna suna da rabo in shaa Allah, ko ba"


Mummy ce tace

"Allah daga zuwan su har ka fara nuna banbanci tsakani na da su"

"yoo ke ba tsohon hannu bace, kinci kuɗin kinci kuɗin har kin gaji sukuwa ai kinga
sababbi ne"


Raha suka dinga yi tsakanin su inda wasu suke goyan bayan mummyn wasu kuma suna
goyan bayan twins


Ni dai ina gefe murmushi kawai nake yi ina jin daɗin yadda suke nuna kulawa ga
abinda na haifa



Sai da suka gama sannan ya tasa ƙeyar mazan suka fice inda aka bar gidan daga
matan sai ƴaƴan su



Mummy ce ta sa anty fannah ta kaini asibiti ko akwai wani problem, muka je suka
duba ni tas ba komai, sai dai magani da suka bani muka dawo gida



Gidan ƙin kyau yayi sai da kowa ya bar gidan da daddare sannan gidan ya dawo
hayyacin sa


Mummy ce kawai bata tafi ba, wai ita ta dawo kenan sai bayan suna


Muna zaune a falo wajen ƙarfe 10 :30na dare muna ɗan taɓa hira kafin mu kwanta
sai nace wa mummy


"har yanzu ba a san inda sabit yake ba" juyowa tayi ta kalle ni, dagani ita ma
abin na damun ta

"wallahi asmau tun rana nake ta trying mumber sa amma sam a kashe take wallahi
kawai ƙarfin hali nake amma hankalina ba a kwance yake ba"



Hankali na ne ya tashi ya za a yi ace ba gan shi ba kuma ba wanda ya damu,


"mummy yanzu baza a duba a sani ko lafiyar shi ƙalau ba" na tambaya


"wannan daddyn ku ne kawai zai iya kuma nasan inna faɗa masa bazai yi ba saboda
har yanzu haushin sabit ɗin yake ji akan abinda ya miki"
Kuka na saka mata nidai mummy don Allah ki sa a nemo shi, shekaran jiya ya fita
ba a san inda yake ba amma ba wanda ya neme shi yanzu in wani abun ya same shi fa
me zance wa ƴaƴana, wallahi duk lalacewar sabit na fi son ganin shi kusa da mu
saboda ƴaƴana mummy dƙn Allah ki taimaka kiyi wa daddy magana"


Shiru tayi daga dukkan alamu bata son yin kuka ne yasa ta ƙin yin maganar, wayata
ta ɗauko tayi dialing number daddy sai da ta fara ringing sannan ta bani



ringing ɗaya ya ɗauka tare da sallamar sa daga gani bashi da number ta

"daddy asmau ce"

"asmau kina nan lfy ko, ko akwai abinda kuke so ne"


Kuka na saka masa sannan nace

"daddy ba aga sabit ba don Allah ka sa a nemo shi don Allah daddy"


Shiru yayi kamar be ji ba sai da na sake bashi haƙuri na ɗauka ko be haƙura ba ne
sannan yace


"asmau lallai ke ƴar halak ce kuma wallahi baza ki taɓa taɓewa ba, ki kwantar da
hankalin ki mijinki nanan ƙalau yana lagos ne, wajen aikin sa can ya koma amma in
shaa Allah zan koro miki shi"


Kunyar sa naji nai murmushi sannan nace

"ni fa daddy ba ni nake son ganin sa ba, kawai dai ya zƙ yaga babies ɗin ne"


"ato abu ne sauƙi kawai zan sa a aika masa hotunan su kinga shike nan ya huta da
zuwa kooo"


"a a daddy don Allah ya dai zo" dariya yayi irin tasu ta manya sannan yace


"shike nan in shaa Allah zan sa a gaya masa"


Mukai sallama sannan na sanar wa da mummy abinda ya faru, ta nuna jin daɗin ta
sosai itama tai ta sa min albarka kamar ba gobe



********************



Sabit yana kwance a kan kujerar gidan sa na lagos duk abin duniya ya gama isar
sa, sam ya rasa farkn ciki, yana matuƙar kewar asmau daba dan daddy ya kafa masa
doka akan zuwa wajen ta ba da tuni ya san yadda zai yi ya taho da ita lagos


Tabbas asmau tana da taurin kai amma kuma zuciyar ta tana da sanyi, shiyasa duk
abinda yake mata yasan bata riƙo



Gashi yanzu wallahk yadda yake kewar to ko kaɗan baya kewar badia, wacce sam baya
ma son ganin ta, burin shi kawai asmaun sa wacce yanzu aka kafa masa takunkumin
ganin ta


Knocking yaji ana yi, agogon bangon parlour ya kalla 11 :20na dare, waye wannan
da daren nan yake min knocking



Kamar bazai buɗe ba sai kuma ya tashi yaje bakin ƙofa yayi shahada ya buɗe


Wani yaron daddyn sa bola inda ya faɗa masa wai daddyn yace ya kunna wayar sa
matar sa ta haihu


Ai ko sallamar yaron ma baiyi ba ya tafi ciki a guje shi sai a lkcn ma ya tuna da
batun wayar sa tun da ya kashe ta lkcn da ya baro abuje



Watsappa ya shiga don yasan ta nan zai ga pics ɗin babyn, aikuwa messages ne
sukai ta shigowa kamar ruwan sama


Message ɗin ƴan uwan sa kawai ya shiga dubawa, nan ya ci karo da wasu jarirai
kyawawa an turo masa


Duk da dai yaran ba farare bane amma kuma sun masa kyau sosai ashe shima baƙi yana
da nashi kyan


Duk da dai ƴaƴan shi baƙaƙe ne amma ya ga kyan ababan sa sosai kamar ba nasa ba,
kamar su ɗaya da annur


Miƙewa yayi ya fara haɗa kayan sa dalilin ganin asmau ya kama shi yanzu inyaje
gidan ba wanda zaice masa don me


In shaa Allah sai ya samu ya shawo kan asmau kafin a ƙara yi masa get da it don ba
ƙaramin wahaltuwa yayi da rashin ta ba barin ma waɗannan ƴan kyawawan ƴaƴan nashin
da ta kawo masa duniya


Sai yanzu yai dana sanin zubar mata da ciki da yayi, inda yasan cewar idan asmau
ta haifo masa ƴaƴan sa ko da zasu kasance baƙaƙe amma za suyi kyau ai da tun farko
be dinga wannan abin da yake ba
A gaskiya ya cuci asmau a rayuwa, sam shi sai yanzu yake jin kunyar kansa ma,
yarinyar nan ba abinda tai masa kawai ya kafa mata ƙahon zuƙa



Hawayene su ka sauko daga idon sa da ya tuna irin abubuwan da dinga yi mata,
lallai yayi nadama kuma yana fatan ita ma ta yafe masa



Da asuba ya kama hanyar abuja a jirgi inda yayi sa'ar samun flight na ƙarfe
06 :00 na safe, suna sauka diretly gidan da asmaun take ya wuce


Gidan da yake ganin sa kamar na wani shugaban ƙasa saboda tsabar takunkumi da
daddy ya saka masa



*******************


Ina kwance ina bacci kawai naji mutum ya kwanta kusa da ni ko ban kalle shi ba
nasan sabit ne don nasan duk duniyar nan babu wanda ya isa ya rungume ni sai shi


Da sauri na miƙe tare da haɗe raina

"lfy" na faɗa raina a ɓace, ai na waye yanzu ya za a yi in barshi ya same ni a
banza bayan sam be san daraja ta ba


"my asmy godiya zan miki akan wannan kyauta da kika kawo min duniya Allah ne kaɗai
zai biyaki"


Baki na taɓe sannan nace

"baka ganin baƙaƙe ne"

"au haba ban lura ba ni kawai kyan ƴaƴana nake gani"


"au ƴaƴan ka ma, ƴaƴan da ka so in zubar su sune yanzu kake kira da naka"


"wai har yanzu ba a yafe min bane"


"sabit ai tuban dole kayi tuban muzuru da kaga na dawo gareka shi ke nan sai a
koma gidan jiya"


"ke kuma baza ki min fatan shiryuwa ba"


"wannan kai ta shafa ko da kai ko babu kai zan iya rayuwata"
Duk yadda ya so ya ga na sakar masa jikina sam yaga hakan be samu ba, da ƙwarin
gwiwar sa ya shigo ɗakin amma ganin yadda na dage ban yadda da tuban sa ba ya sa
jikin sa yin sanyi




Ƙarasawa yayi ya ɗauki ɗaya wacce itace ƙaramar addua ya hau yi mata ina ganin shi
yana ƴar ƙwallar sa ko me ya tuno oho


Ganin zai karya min zuciya ya sani miƙewa na fice na bar masa ɗakin parlour na
koma na zauna kusa da mummy


Sam bata tanka min ba, ya daɗe sosai sai gashi ya fito

"mummy ni zan wuce gida in ɗan huta, akwai abinda kuke buƙata ne"


Lallai ma sabit ɗin nan dama ba dan mu kazo ba don kazo kaga badia kazo kenan har
da wani zaije gida kenan nan daji ne


Harara mummy ta bishi da shi inda ni kuma na miƙe na bar wajen, sam be fahimci
manufar mu ba ya ɗauka daga mummyn har ni fushin muke da shi


Sim sim sim yasa kai ya fice shi sam ya ma rasa tudun dafawa wannan shine abinda
ake cema rana zafi inuwa ƙuna




Ko da ya koma gidan nan har gidan asmau yafi ni'ima don badia tana ganin sa ta hau
shi da zagi da cin mutunci, sam be kula ta ba


Ɗakin sa kawai ya wuce yana shiga ya rufe ƙofar da key kamar ya sani yana juyawa
zai shiga toilet yaji bugu kamar za a ɓalla ƙofar


Share ta yayi ya shiga toilet, hmmm lallai badia har yanzu batai hankali ba wai
ita har yanzu burin ta sai ya bada sperm ɗin sa sun ka nemo wacce za a sake mata
dashen ta haihu ita lallai sai taga ƙwanta a duniya ta nuna wa asmau


Ƙin yadda dan da baiyi ba ne yasa kwanaki sukai fada ta bishi har waje tana ci
masa mutuncin sa


In banda ma daddy wallahi da tuni badia ta manta da rayuwa da wani sabit don
wallahi in ya tashi katse auren da ke tsakanin su ko duka ba tare ya rage ko igiya
ɗaya ba don ya
: "wallahi sabit ka buɗe ƙofar nan ka ɗura min sperm ɗin ka a robar nan in kai
asibiti a ɗura wa wacce za tai mana ɗaukar cikin, don baka isa ba kace wai bazan ga
ƙwai na a duniya ba, wallahi ba za ta saɓu ba"


Surutai tai tayi wanda suka saka sabit ɗin yin nadama sosai gaskiya ada ya bi son
zuciyar sa sosai na cewae shi bazai auri baƙar mace ba balle ya haifi baƙin ɗa amma
yanzu in shaa Allah ko ƴaƴa zai dinga haifa kamar baƙaƙen tukunya zai so kayan sa
kuma ya basu tarbiyya


Balle baƙin asmau ba me muni bane irin wanda yake da tsadan nan ne wanda bature
yake cewa chocolate


Barin ma yanzu da haihu ɗin nan tai wani fresh da ita duk sai ya jishi ya matsu ya
jishi a jikin ta tana sarrafa shi kamar yadda take masa idan suna shiri



Wani irin yarrrr yaji a jikin sa lallai akace wani kaya sai amale, asmau tayi wa
badia nisa nesa sosai wanda duk abinda badiar zata yi ba lalle ne ta kamo ƙafar
asmaun ba



Kai lallai wallahi dole ne ma in dawo da matata wallahi duk abinda za a yi sai na
dawo da matata


Yana fitowa daga toilet ya tsiri haɗa kayansa shima gidan zai koma da zama duk
yadda za ayi da shi wallahi sai dai ayi amma sam bazai iya rayuwa babu asmau ba



********************



Ina zaune a ɗakina takaici ya ishe ni wai sai yaushe sabit zai fahimci shi wani
jigo ne a rayuwa ta da bazan iya cigaba da ita ba face da shi a kusa dani kusan
kullum banni da buri daya wuce inga na mallaki mijina a hannuna yai treating ɗina
kamar yadda ake wa kowacce mace amma ni sam har yanzu ba samu ba


Ina cikin tunani na naji muryar mummy tana magana


" lfy kai kuma meye haka sai kace me shirin hijara"


"ai mummy duk inda asmau take da yarana ni ma ina nan, zuwa nayi gida ai na kwaso
kayana ni ma ayi jegon dani"


Murmushi nayi amma kuma sai na haɗe raina don kar ya shigo ya ganni ya raina ni


Na ɗauka zai shigo ɗakin ko ince naso ya shigo ɗakin amma har na gaji da gyaran
fuskar da zan sauke shi da ita na saki fuskata ba shi babu dalilin sa




Sam be shigo ɗakin ba ina jin shi a parlour yata ta zuba cikin mata, kuna duk
wacce ta zo sai ya shigo ɗakin ya ɗauke su don kai wa yan barka


Kuma shigowa goma fita goma sak ya min magana, ƙala bana ce masa amma baya gajiya


Haka aka dinga yi da shi ina jin anty fannah tana mai tsiya


"ni na taɓa ganin jego har da namiji"

"kin san ai autar mata ce ta haihu duk abinda take dole ne ai mata, ko da dai
bazata yaba ba"



Murmushi kawai nake yi ina cikin ɗaki na


Har azore garin mu mummy ta aika da mota akan idan da masu zuwa suna



ƴan garin mu da yake ba hankali haka suka ciko motar wata akan wata ƴaƴan su da
jikokin su, har da me tsohon ciki


Ɗadin abun ma acan gidan mummy akai sunan can muka je saboda kar a ɓata min gida,
inda ƴaƴana suka ci sunan

*FATIMA & FATIMA*

sunan mummy da kuma suna mahaifiyata, ɗaya muna ce mata nur ɗayar kuma hoorain
amma hoor in short


Hoor da noor sun shaa kaya sosai da kyautuka da kuma hotuna


Tunda aka fara sunan nan har aka gama sabit yana maƙele da ni kamar jaka, duk wani
hoton da za ayi tare da shi yana riƙe da baby ɗaya


Wallah tun abin na bani dariya har ya zo ya faɗa bani haushi don kuwa tuni mutan
garin mu suka fara magana


"shi mijin mau haka yake abin nasa sam ba kunya"


Ga dukkan kayan da na saka sai shima ya saka, ko kaɗan bansan ya akayi akai mana
kaya iri ɗaya ba, ko da yake nasan aikin waye
Na anty fannah ne don kuwa itace akan komai na kayan da zan saka ranar suna,


Mun sha pics sosai da mu da ƴan biyun mu da annur


Suna yai suna haka akai suna aka tashi lfy a daren muka koma gidan mu don gidan
mummy babu masaka tsinke

Fatana dai Allah yasa mijina ya shiryu kenan har a bada
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN

Please Login or Register in order to submit comment