You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anata sai yaji kunya Nadrah ya ka mashi Ya ce ""Daman tana dakin ne""? Gyad'a kai tayi cike da kunya hannu tasa ta d'auketa ya ce ""Nono zaki bata yunwa takeji"", Asmee ta ce ""Aah don yanzun ta gama shan nonon shine ta kwanta Murmushi ya yi ya ce ""Sai a ba baban yasha koh""."

"Asmee ta ce ""Aah na baby ne"", Ya ce ""Baban babyn kenan baza a bashi komai ba kenan murmushi ta yi takara rungume Nadrah a kirjinta."

"Dadi yaji ganin yadda take kula mishi da Yarinya, Asmee ta ce ""Amm daman nace ko zamu iya barin garin nan cike da zumudi ya ce ""Me zai hana indai kina son haka"", ganin fa komai yana rafiyan mata yadda yaka mata ta ce ""Yanzun fa nake son mu tafi sai muci amarcin mu acan"", shafa fuskanta ya yi ya ce ""Indai haka kike so kidauka cewa kamar an gama yanzun ki kafara hada kayan naki dana baby bara naje na fada ma Umma"", gyad'a kai ta yi sannan yai mata kiss a kumatu ya fita a d'akin dadi ne ya kamata ta ce ""Muna tafiya kuma shikenan"", sannan ta kwantar da Nadrah ganin ta koma baccin ta tafara hada kayanta cikin akwatinta."

"Koda Abubakar ya fada ma Umma yau zasu bar garin Umma ta ce ""Ina zaka kuma a yau daga daura aure kuma""? Alh. Abubakar ya ce ""Umma kano zamu tafi saboda akwai wasu aiki da zanyi acan dinne Umma batai musu ba ta ce ""Toh Allah yabada da'a kuma Allah yatsare ku Abubakar ya amsa da Amin Umma nagode sannan ya fita a d'akin shima ya nufa part dinshi don shirya kayanshi na bukata Umma gaba daya sai takejin wani yanayi daban ganin take kamar gani na karshe takeyi ma Abubakar amman zuciyarta ya kasa sa tayi waswasi akai tai musu fatan alkhairi."

"Karfe 3:00pm sun gama shirya komai nasu tsaf Sabitu ya bata mak'udan kudi masu yawa sannan ya ce ""Zasu dinga waya duk abinda take so ta fad'a mishi""."

"Sannan kukai ma Umma sallama Nadrah ta dade a hannu Umma sannan ta mik'a ma Asmee ta ce ""Don Allah y'ata itadin amana ce a gareki kirik'eta amana ki kula da ita sosai duk da nasan kina sosai kuma Allah yai miki albarka murmushi Asmee ta yi ta ce ""Haba Umma Nadrah y'ace a gareni zan kula da ita sosai na miki alkhawari""."

Murmushi Umma ta yi sannan ta shafa fuskan Nadrah tai musu sallama suka tafi.

"Sai da suka dau hanya ta ce ""Love ba kano zamu ba Abuja zamuje kuma bana son kowa yasan inda zamu dagani sai kai Abubakar baiyi mata musu ba haka suka dauki hanya Abuja."

**********

Karfe 7:35pm suka isa garin Abuja daman Abubakar yana da gidan acan nan suka sauka.

"Haka suka fara rayuwarsu cike da sha'awa Asmee sai juyashi takeyi yadda take so, shi kuma yana kokarin son yasamu aiki amman fa abin yaki koda ya hadu da abokon huldanshi nacan basu bashi aikin ba, Asmee kuwa ko a jikinta tasa ya canza layi ko waya da Umma basayi."

Haka suke rayuwarsu Asmee ke bashi kudi ayi cefanen abinci Nadra kuwa ta fara wayau abinta ba laifi Asmee tana kulawa da ita don gaskiya Asmee tana son Nadrah batajin zata iya cutar da ita a yanzun kuma.

Alh. Sabitu kuwa komai ya dawo hannunshi kamar yadda yake da buri shi yake tura ma Asmee kudi idan tana buk'ata.

*********

Bayan shekara goma a haka suke rayuwarsu komai ya kare musu sai dai Sabitu bai dena tura musu wani abu ba inda Asmee take da yarinya yar shekaran 9 wato Nafisa taci sunan mahaifiyar Asmee ne ita kuma Nadra tana da 11 year a duniya yarinya ce kyakyawa sosai mai wayau da aji ga iyayi wacce abin sha'awa ce don Allah yai mata baiwar ilimi da basira ko a makaranta ita take daukan na d'aya don yanzun tana Secondary school ne komai nata burge kowa ya keyi a haka Abubakar yake d'an fafutukanshi da d'an neman abinyi saboda yaranshi Asmee kuwa talaucin ya fara sata a gaba amman tunawa da irin sonda take ma Abubakar yasa saita danne abinda takeji.

Umma kuwa tsufa ya fara sata a gaba gaba daya tacire rai dasu don iya nema an musu amman ba adace ba haka ta ha kura ta fara tunanin ko sun mutu ne.

*******

"Asmee wata rana takira Sabitu akan ya tura mata Kudi har 5 million ya nuna bazai tura wannan kudin ba sunyi yawa tahau yin mishi bala'i da cewa zata tona mishi asiri ai dukiyar na mijinta ta ne, shima ya ce ""zai tona mata asiri ai yadda ta sa yai ma Aisarah fyad'e harta mutu da kuma zuwa wurin bokan da sukayi har ta auri Abubakar tarabashi da kowa nashi, ji tayi Abu ya fadi kasa timm juyawa ta yi da sauri ta ga Abubakar kwance hankali a tashe ta ce ""Sabitu Abubakar yaji komai fa Sabitu ya ce ""Garin ya to Asmee ta ce ""Wllh yanzun haka ya suma ma Sabitu ya ce""Bara naje wurin boka yanzun cike da rud'u Asmee ta fara kuka a kanshi da sauri ta nema ruwa ya watsa mishi a fuska ya bude idonshi a hankali amman ya kasa cewa komai da sauri ta samu ya tashi ta kwantar dashi a gado ta fara mishi fiffita, gashi yana son magana ya kasa cewa komai.."

"[9/21, 6:07 PM] : _Page 49&50_"

"Asmee kallo kawai ta bishi dashi tana addu'a kar Allah yasa ya ji duka abinda suka fada, can taji ya ce ""Asmee fadamin komai kar ki boyemin komai don Allah""."

"Asmee shiru ta yi don harga Allah batasan me zata ce ba, kallonshi ta yi ta ce ""Babu komai fa Abban Nadrah kawai. a hankali ya ce ""Naji komai fa karki yarda ki musa"

min idan ba haka ba wllh zan sake ki a yau dinnan.

"Gaban Asmee ne ya fadi a zuciyarta ta ce ""Shikenan asirina ya tonu."

"Sabitu kuwa ya ce ""Shikenan shirunmu ya baci yaushe har zani gurin wani boka tunawa yayi ai akwai numbernshi da sauri kuwan yai dailing."

"Ringing uku yayi aka dauka Sabitu ya ce ""Boka akwai matsala fa Mijin Asmee yaji komai fa meye ma fita akai, boka dariya ya yi ya ce ""Wannan karamin al'amarine yanzun me kake so ayi so kake akasheshi ko kuma a rufe bakinshi wanda zai kwanta rashin lafiya da ko magana bazai iya ba Sabitu ya ce ""Eh Boka kardai akashe shi kawai a rufe bakinshi d'in kamar hakan zaifi boka ya ce ""Angama yanzun nan ma kuwa"" sannan Sabitu yai ajiyar zuciya ya kashe wayar."

Asmee kuwa ta kwashe komai ta fad'a mishi harda zuwa wurin bokan da sukayi da Sabitu bata boye mishi komai ba harda irin sonda take mishi.

"Ya bude baki zaiyi magana kenan ya kasa magana da sauri Asmee ta ce ""Kai min magana mana amman don Allah karka sakeni ina sonka wllh duk Saboda sonda nake maka ne na aikata hakan kaji."

Alh. Abubakar kuwa kokarin magana yake sonyi amman ya kasa ga jikinshi dake mishi azaban ciwo ko wani sassan jikinshi.

"Asmee ta fahimci haka hankalinta ya tashi da sauri ta fita a dakin ta kira number Sabitu ta ce ""Me kai ma mijina""? Sabitu ya ce ""To ai hakan ne kawai ma fita a tunanin idan yasan abinda kika aikata zai cigaba da zama da kenan ina wllh rabuwa dake zaiyi kuma sai an kamaki kinyi rayuwar prison ko anfada miki idan ba ai hakan zaki cigaba da ganuwane don umma kawai saita kashe ki da hannunta daman tana kukan kin rabata da yaronta da jikarta, gwanda kiyi hakuri kawai idan zaki cigaba da zama dashi a haka kiyi idan baza ki iya ba kawai kizo muci gaba da Jin dadin rayuwarmu anan batare da kowa ya sani ba."

Cikin bacin rai takashe wayar ta fashe da kuka tana tsine ma Sabitu a wannan halin ne Nafisa da Nadrah suka dawo daga makaranta koda suka ga Mommah tana kuka sai suma suka hau kuka ganin haka ta share hawayenta ta fara lallashinsu.

Abubakar kuwa gaba daya wani irin ciwo yakeji a gabobin jikinshi gashi ba daman magana ko su Nadrah da sunzo wurinshi suyita ta mishi labarai masu dadi sai dai kawai yaita zuba musu ido yana lumshewa.

"Haka rayuwarsu taci gaba, gaba daya ba dadi ga Sabitu ya dena tura mata da kudi ga kayan abincinsu ya k'are sai a hankali, su Nadrah ma sundena zuwa makaranta don ko kudin makaranta basa biya shine aka koresu gashi dukkansu suna da burin karatun don Nadrah tana aji hud'u ne a secondary wato s.s 1 Nafisa kuma j.s.s 2 amman"

"yanzun karatun ya tsaya, islamiyya kuma tana class 4 ne Nafisa kuma 3 amman da yake islamiyya kyauta suna cigaba da zuwa shi."

Asmee haka take fita taje ma kwata tai musu wanke wanke tasamo musu abinda zasuji wani lokacin saitaji kamar su koma Kaduna amman tana tunanin idan ta koma asirinta zai tonu don sunyi sharadi da boka.

"A haka ne tasa gidan da suke a kasuwa akazo a kasiya sannan suka siya karamin gida mai ciki da parlour sai wani karamin daki inda nan ne su Nadrah suke kwana, sauran kudin ta kama sana'ar sai da kayan miya dasu magi kuma Alhamdulillah ana siya su Nadrah suka fara government school tunda basu da kudin cigaba da wancan kowa aka bashi ajin da yatsaya da yake suna da kokarin sosai"

**************

"Bayan shekara 5 su Nadrah sun kammala secondary school dinsu dukkansu ga jikin Abubakar sai kara tsanani ya keyi Asmee idan takira Sabitu baya dauka, daga baya ma wayar ta dena shiga gabaki d'aya."

"Nadrah a lokacin tazama cikakkiyar mace 16 years kamar yar 20 years wacce komai ya fito mata Allah ya zuba mata kyau da kiran jiki masha allah farace kyakyawa sosai mai tsayi komai a cike suke bulbul, Nafisa ma haka tana da kyanta dai dai gwargwado sai dai kowa yasan cewa Nadrah karshe a fagen kyau samari har layi sukeyi a kofar gidan masu kudi da marasashi amman kota kansu bata bi don Momah ta ce ""Idan taka mata tana kula samari saita yankata shiyasa ko tasu bata bi itama, idan ko kace mata aure ne yakawo ka wurinta wllh sai kasha mari da zagin da ko hanya gidan baza ka kara zuwa ba, don bata kaunar maganar aure koda wasa ne bata so."

Nadrah tunda tatashi Allah ya daura mata wutar sha'awa tun batasan me take jiba harta fahimci tana bukatar na miji ne a tare da ita.

"Tana da kawa Maryam ranar abun yasata a gaba ta tashi da sauri ta ce ""Ma Mommah zataje wurin Maryam ta ce ""Sai ta dawo amman karta dad'e, haka takama hanya ta fita a gidan a hanya ne wani ya dinga mata horn hakan baisa ta kalli inda yake ba harta karisa gidan su Maryam din shikuma kaman maye har kofar gidan ya bita."

"A tsakar gida ta samu Umman su Maryam d'in, gai da ita tayi cike da ladabi sannan ta fad'a mata Maryam tana daki ai."

"Shiga ta yi dakin Maryam tana ganinta ta ce ""Yau kece kikazo wurina lallai kam""? Nadrah ta zauna ta ce ""K'awata wllh ina cikin damuwane na rasa yadda zanyi kuma nasan kece kawai wacce zata bani shawara akai Maryam ta ce ""Subhanallahi me yake damunki bestie""?"

"Nadrah ta ce ""Maryam wllh Sha'awan na miji nakeji har bana son na hadu dana miji a hanya, kullun cikin yin azumi nake amman hakan baisa nakarajin wata sha'awar wllh ko bacci banayi kwana biyun nan, Maryam shiru ta yi cike da tausayin Nadrah, don ta dade da gane Nadrah itadin Harija ce kawai ta yi shiru ne don data cemata tana zumi yau zata fahimce halin da take ciki."

"Nadrah ta kuma cewa ""Bestie ko kinsan maganin da ake sha mutun ya denaji""? Maryam ta ce ""Kona fada miki maganin illah zai miki balle ke mace kawai maganin shine kiyi aure."

"Nadrah take ranta ya baci ta mik'e tsaye zata fita a d'akin da sauri Maryam ta rik'ota ta ce ""Kiya hakuri ni a gani nan shine kawai ma fitan abinda yake damunki bestie."

"Nadrah kuka ta fashe dashi ta ce ""Maryam kinsan bana son maganar aure a wllh har cikin zuciyata nake jinshi""."

"Maryam cike da tausayjn Nadrah ta rungumeta, tasan tabbas bata son maganar aure amman a yanzun dole tai mata maganar aure tunda harta fara sha'awar na miji."

"Maryam ta ce ""Nadrah don Allah me yasa bakison maganar aure Nadrah dagowa ta yi daga cikin Maryam ta ce ""Maryam ban taba son maganar aure ba balle auren shi kanshi ganin nake har abanda bazan tab'a son aure ba don Allah Maryam karki kara min maganar aure idan har kina son muci gaba da mu'amala idan kuma baki so kawai murabu muddin zaki cigaba da yinmin maganar aure""."

"Maryam ta ce ""Subhanallahi Nadrah me yakawo maganar mu rabu indai maganar aure ne baki so wllh bazan kara miki maganar aure ba""."

"Nadrah ta share hawayen fuskan ta ce ""Ni zan tafi Mommah ta ce ""Karna dad'e Maryam ta ce ""Kiya hakuri kawata nasan na bata miki rai kawai kici gaba da addu'a kina azumin insha Allahu zakiji sauki komai Nadrah ta ce ""Nagode sannan tai ma Umma Sallamah ta fita a gidan."

"Ga mamakinta wannan motar ce da tadinga mata horn a hanya itace har yanzun a kofar gidan a fake, don ita tama manta."

"Ta fiya ta farayi da sauri don anfara kiran sallar magrib horn ya dinga mata, ko kallon idan yake bata bi ba harta shiga gida."

Parking yayi ya sauke glass dinta motar wani handsome boii ne me jini a jika fari ne shi yana da kananan idanuwa mai dauke da karamin baki sai d'an dogan hancishi dai dai misalin.

"Wani yaro ya gani yafi to daga gidan ya kira woshi, ya ce ""Don Allah wata yarinya budurwa yanzun ta shiga gidan nan ina ne gidansu yaron ya ce ""Ai nan ne gidan su murmushi ya yi ya ce ""Don Allah ya sunanta""? Yaron ya ce ""Nadrah sunanta Kudi ya dauko har 5k ya mik'a ma yaron da kamar bazai amsa ba ya hamsa godiya ya yi sosai sannan ya tafi shikuma ya juya motanshi yabar kofar gidan...."

Nadrah koda tashiga gidan tasamu jikin Abbanta yakara zafi kuka taci sosai Ita da Nafisa gashi basu da kudin da zasu kaishi asibiti duk wannan shekarun haka ya dauka ko motsi baya iya komai sai dai yayi a kwance komai yinmishi akeyi Asmee ita kanta abin ya fara ishenta har dan dana sani ta farayi.

"Bayan sun idar da sallar Isha',i ne sune zaune suna cin tuwo wani yaro ne ya shigo da sallama suka amsa sannan Momma ta ce ""Me za abaka yaron ya ce ""Wani mai mota ne wai yake kiran Nadrah a waje Mommah ta ce ""Wani mai mota kuma""? yaron ya ce Eh ""To kaje kace baza tazo ba din""."

"Yaron ya fita ya sanar dashi wai baza tazo ba ya kuma aikawa Mommah ta ce ""Kaji Dan shegiya bara na fita da kaina irin masu nacin nan ne inaji""."

Ita dai Nadrah tana zaune tana cin tuwanta don ita kadai tasan yadda takeji a halin yanzun ba wani abinda akeyi take ganewa ba.

"Tana kallo Momma ta dauko mayafinta ta fita tana fita taga kutuwar mota mai tsada sai da taji wani iri aranta, karisawa ta yi sannan tai knocking glass d'in motan a kabude murmushi ya sakar mata ya ce ""Ina wuni Mommy amsawa ta yi sannan ta ce ""Kaine kake kiran yarinyata Nadrah ko""? Ya ce Eh nine Mommy sunana Fahad Mommah ta ce ""To kuma gashi bamu shirya yin mata aure ba yanzun""."

"Ya ce ""Badamuwa Mommy kawai ina son mudinga gaisawa ne da ita, sannan ya d'auko kudin dami guda yan one thousand ya mik'a ma Mommah jiki na bari tasa hannun ta amsa godiya ta yi don ta dade bata ga kudin haka ba ta ce ""To bara na tura maka ita"", ya ce tom shikenan ngd Mommy idan akwai abinda kuke buk'ata ma ki fada mata sai tafadamin."

"Mommah ta ce ""To Dannan mungode fa sosai."

"Tafiya tayi a zuciyarta ta ce ""Alhamdulillah kudi har gida lokaci yayi dazan fara samu kudi da ita tunda nasan baza ta ba gigin cewa zatai aure ba tunda a nono tasha, talaucin ya isheni haka gaskiya, ta shige gidan ba kowa a tsakar gidan."

"Dakinsu ta wuce ta ce ""Nadrah maza ki shirya kije yana kiranki na baki izini kije duk wanda yazo ne manki kije kuma duk abinda aka baki ki amso ki kawo min."

"Nadrah da mamaki ta ce ""Mommah yanzun dare ya farayi a bari zuwa gobe saina fita. Mommah ta ce ""Yau dani zaki jayayya kuma"", Nadrah ta ce ""Kiya hakuri Mommah daman bani da lafiya ne""?"

"Mommah ta ce ""Ya hakuri kije gaisawa kawai zakuyi kinji yar albarka"", Nadrah a halin yanzun bata son ta kusanci na miji don gani take bazata iya jurewa ba muddin akwai na miji a kusa da ita, Mommah haka ta lallabata ta tashi tasa hijab ta fita a d'akin."

"Mommah ta ce ""Alhamdulillah"", sannan ta shiga da kinta ta rufe kofa ta boye kudin Abubakar yana kallonta."

"Nadrah ta na fita ta tsaya a jikin motar tai shiru ta kasa bugawa, Fahad yaga k'arisowanta ganinta gaba daya yakara daga mishi hankali don yasan tunda yake bai taba ganin mace mai kyawunta ba duk da ya fita kasashe da ban daban baiga wacce tai mishi kyau kamar taba ya ce ""Wannan kyawun nata da ban yake sai da ya kare mata kallo sannan ya bude mota ita kuma a lokacin harta juya zata koma gida da sauri ya ce ""Hajiya ya hakuri don Allah shigo mana ya bude mata dayan mazunin mai zaman"

"banza, dago manya idanuwanta ta yi ta kalleshi sai da taji wani zirrr a yatsin hannunta don tasan yana dakyau ba laifi, girgiza kai ta yi ta ce ""Ina wuni kin amsawa yayi yanajin san yaiyyar muryanta."

"Sannan ya ce ""Don Allah ki shigo mota mana kinga bai dace ba ace kina tsaye a waje kuma ga mota kinga kuma kofar gidan naku ba dakali balle ni nafito na zauna don Allah ki shigo mana."

Nadrah ta ce bazan shigo ba ni wucewa zanyi ta juya ta kama hanyar zauren gidan su da sauri ya fito daga motan yabi bayanta tana gab da shigewa cikin gidan taji mutun yasa hannu ya janyota baya batai haune ba taji ta fada kan kirjinshin.

"Zuciyarta ne ya fara bugawa da sauri tai kokarin kwace jikinta anashi zata tafi don takasa cewa komai, kuma matseta yayi a jikinshi a hankali yakai bakinshi dai dai kunnenta ya ce ""Baby Kar kiji tsoro nine Fahad"".."

"Runtse ido tayi wanda batasan lokacin da itama ta rungumeshi ba, ganin haka Fahad ya fara lalubanta ji tayi ya fara shafa mata nonuwanta da sauri ta runtse ido don tunda take hannun wani na miji bai tab'a taba koda karamin yatsanta ba yau gashi wani hannunshi akan dukiyar fulaninta."

"Ji tayi bakinshi anata ya fara tsotsan lips dinta cike da salo gaba d'aya jikinta ya mutu takasa ko motsi balle ta hanashi abinda yake mata a hankali Fahad ya zare bakinshi anata ya ce ""Baby komai naki akwai dadin tab'awa ga bakinki dadi sosai pls kizo muje mota kar wani ya ganmu anan yafada yana kokarin kara tura bakinshi cikin nata Nadrah wani bangaren na zuciyarta ya na fada mata wannan babban zunubi ne abinda kuke aikata bai kamata ba, kar finta ta tattaro ta tureshi a jikinta ta zube a kasa wurin dafe ba maranta da yakara daure mata tana sakin nishi Fahad ya ce ""Baby kizo muje mota kinji, Nadrah a hankali taja jikinta ta shiga cikin gidan ta barshi tsaye a wurin."

Fahad shafa lips dinshi yayi sannan ya tsotse yasan cewa yana son kiss sosai amman bai tabajin baki mai dadin tsotsa ba kamar nata sai kace zumah murmushi yayi sannan ya je idan motanshi yake ya shiga ya bar kofar gidan.

Nadrah da kyer ta karisa dakinsu ta zube akan katifarta ta fashe da kuka.....

_Page 51&52_

"Kuka tasha wanda ko bacci ya gagara d'aukanta, tashi ta yi ta dauro alaula sannan ta tada sallah tai ta neman yafiyan Allah har bacci ya kwasheta akan sallaya don ta samu marartata ta rage mata zugi."

Fahad kuwa koda yaje gida gaba daya ya kasa bacci wani irin sha'awa Nadrah ke taso mishi tabbas ya fahimta bazai sha wahala ba wurin shawo kanta ba.

Duk yadda zaiyi sai yayi domin yasa meta wannan alkhawarinshi ne.

*******

Da asuba Nadrah ta tashi tai sallah sannan ta tashi Nafisa itama ta yi sallah sannan suka fara karatun alk'ur'ani kamar kullun don haka sukeyi har garin Allah ya waye.

"Mommah ce ta shigo d'akin gaida ita sukayi sannan ta ce ""Nadrah ya kukayi da yaron jiya Dan albarka ta fada tana yashe baki""? Kauda kai ta yi batare da tace komai ba""."

"Asmee tab'e baki tayi ta ce ""Tom ga koko can da kosai kuje kusha"", da mamaki Nafisa tace Mommah da gaske harda kosai Asmee ta ce ""Ehmn harda kosai yau na siya muku harda sigari ma a cikin kokon"" da sauri Nafisa ta fita a dakin don sun dade basu sha koko da sugar ba balle harda wani kosai""."

"Mommah ta ce ""Nadrah ki taso kada kokan ya wuce, gyad'a kai kawai ta yi Asmee ta fita a d'akin gaba daya ta lura da Nadrah komai nata yayi sanyi ita kam ko ajikinta tunda gashi ta dalilinta tasamu kudi da yawa."

********

"Gaba daya yinin ranan Nadrah haka tayishi ba walwala tana daki kwance rufe da zanin gado, Nafisa ce ta shigo d'akin ta zauna kusa da ita ta ce ""Anty Nadrah wai baki da lafiya ne""? Nadrah ta ce ""Eh Nafisa cikina ke min ciwo tun jiya""."

"Nafisa ta ce ""Tom ki fad'a ma Mommah mana saita kaiki pharmacy"", Nadrah ta ce ""Aah Nafisa zan warke kinji Mommah bata da kudin da zata kaini chemist."

"Nafisa ta ce ""To Allah ya baki lafiya""."

Nadrah ta amsa da Amin kawai.

Yau Alhamdulillah Nadrah batajin wani ciwon marar sosai ba da sauki amman tana jinshi kad'an kad'an.

Ta samu ta manta da wani Fahad bata son ko tunawa dashi.

Bayan sallar Isha' i kamar jiya suna zaune suna cin shinkafa don a cikin kudin da Fahad ya ba Mommah ne ta siyo shin kafa ta dafa musu.

Wasu yarane suka shigo da buhun shinkafa da kwalin taliya da jarkunan man gyad'a da manja harda kwallin maggi dana indomie ga kwalin biscuits da sweet dana macaroni gana couscous ga sugar ma buhu d'aya kayan abinci dai masu ban mamaki.

Mommah kuwa tama rasa abinyi a zuciyarta tace yaushe rabon dataga wa inna kayan lallai ma wanda yai mistake din kawo kayan abinci gidan bai kyauta mata ba don tasa rai da dan taliya yaushe rabo.

"Nadrah ne ta bude baki ganin Mommah bata hanasu shigo da kayan ba, ta ce ma daya daga cikin yaran ""Kuya hakuri ku kwashe kayan nan banan gidan bane akace ku kawo dayan yaron ya ce ""Nan nefa Anty Nadrah yamace kije yana jiranki a waje a mota shi yasa mu kawo duk wa inna kayan gidan nan, gabantane ya fad'i jin an anbaci mota sai ta tuna da abinda ya faru jiya cikin bacin rai ta ce ""Kaje kace bazan fito ba kuma ku kwashe kayan abincin nan ku maida mishi da abinshi""."

"Mommah ta kalleta ta ce ""To yar bakin ciki baki isa ba kuma wllh saikin fita, Nadrah zatai magana Mommah ta ce ""Tashi ki fita kisa meshi wannan kayan arzikin ki mana asara kinyi kadan kuwa wllh."

"Nadrah ta ce ""Mommah nifa bazani ko ina ba"" tana fadin haka ta shige takinsu Mommah cikin Jin haushi Nadrah da tsanarta wanda yau ne ta farajinshi akanta ta bita dakin tasa meta harta kwanta."

"Mommy ta ce ""Nadrah wllh saikin fita ko kuma nai miki dukan tsiya a dakin nan"", Nadrah ta ce ""Mommah wllh d'an iskane tab'a jikina fa yakeyi taya zanje wurin wanda yake son b'ata min rayuwa Mommah""?"

"Mommah ta ce ""To sai me don ya tab'aki Nadrah yanzun daya tab'aki nunawa yayi a jikinki ko kuwa bazaki duba halin da muke ciki ba ki duba fa abincin da za muci dakyar muke samunshi kuma yanzun kina son mana bukulu a mazan yanzun dayawansu dole sai sun taba mace zasu d'auki abu su baki."

"Cike da mamaki Nadrah take kallon Mommah ta ce ""Mommah anya ke kika haifeni

Please Login or Register in order to submit comment