You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri akwai matsala fa""."

Da sauri ta mik'e tabi bayanshi suna shiga a dai dai lokacin jaririya na fad'owa cike da kuka.

"Aisarah kuwa salati takeyi wanda take neman numfashi Asmee da sauri ta k'arisa kusa da ita ta rik'ota ta ce ""Aisarah menene"", da sauri ta kalli Sabitu ta ce ""Ka dauketa muje asibiti mana da sauri yasa hannu ya dauketa ita kuma ta dauki jaririyar dake ta faman tsula kuka."

Da gudu suka isa parking space suka shiga mota zuwa a sibiti...

"[9/21, 6:07 PM] : _Page 43&44_"

Koda suka isa aka wuce da ita Emergency room wata nurse kuma ta amshi jaririyar ta tafi da ita wani room.

"Asmee gaba daya jikinta yayi sanyi a al'amarin amman idan ta tuna irin kaunar da take ma Abubakar sai ta tabe baki ta ce ""Allah yasa ta mutu ma."

"Alh. Sabitu kuwa murna har cikin zuciyarshi ya cika burinshi na kusantar Aisarah, Asmee ta katse mishi tunani da cewa ""Idan suka gane an mata fyad'e fa""? dariya Sabitu yayi ya ce ""Bazasu taba ganewa ba sai dai idan kece zaki fad'a musu"" wata ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce ""Yaka mata mukira Umma musanar mata muna asibiti""."

"Alh. Sabitu ya ce ""Hakane kuma ya fad'a ya na ciro wayarshi a aljihu gaban riganshi, yai dailing number Umma, ringing biyu ya yi wayar aka dauka ya ce ""Umma kizo hospital Anty ta haihu fa pls kizo da sauri"" Umma bata jira tai magana ba ta kashe wayar ta juya kan motar zuwa hospital din don daman ta baro gidan kawartata gida zata wuce."

"Likitoci sai da sukai wurin 1 hours akan Aisarah amman ba wani ba yani, har Umma ta iso fadi take ina Aisarah da jaririyar Asmee da tunda taga Umma tazo ta fara kukan karya ta ce ""Umma Aisarah suna Emergency room jaririyar da ta haifa kuma tana wurin wata nurse ta amsheta."

"A lokacin likitoci suka fito a dakin kowa fuska ba walwala da sauri Asmee taje ta rik'o wani likitan ta ce ""Dr. Ina Yar uwata zan iya shiga ciki na ganta?""."

"Wani Dr. Ya ce ""Kiya hakuri mun kasa ceto yar uwarki saka makon zuciyarta ya buga kuma tasha wahala a wurin haihuwa shiyasa ina mai baku hakurin rashinta, wata irin zufane ya fara keto ma Asmee Umma kuwa take ta zube a kasa a wurin."

Da sauri itama aka dauketa zuwa Emergency room.

"Asmee kuwa kuka ta fashe dashi cike dana sanin abinda ta aikata mata tana k'awata ki yafemin abinda na aikata miki nasan harda bakin cikin haka yasa zuciyarki ya buga"", Alh. Sabitu ganin kuka yai yawa kuma kar wani yaji abinda take fad'i da sauri ya duk'a gabanta ya ce ""Asmee kiyi shiru mana kar wani ya gane abinda yake faruwa keda burunki ma ya kusan cika yanzun nefa kike da damar da zaki auri Abubakar kinga kenan kin cika burinki na aurenshi."

"Ya rage sauran nawa ni kuma zanji da komai daga baya kiyi kuka kawai amman ki dena surutu kinji"", gyada kai tayi cike da gamsuwar shawarar da ya bata."

Kuka kawai taci gaba dayi inda take sak'a yadda zatai rayuwarta da masoyinta.

"Umma kuwa bata farfado ba sai da tasha drip leda biyu da allura, sannan ta farfad'o cike da muwa wai Aisara ta rasu kamar a film abinda yakara d'aga mata hankali wai zuciyarta ya buga kenan daman tana da ciwon zuciya ne ko yaya, Asmee ne ta shigo dauke da jaririyar a hannunta ta mik'a ma Umma har lokacin tana share kwallan makirci."

"Umma ta amshi jaririyar a hannunta ta zuba ma kyakyawar fuskarta ido tana kama da mahaifiyata komai sak farin fata ma na mahaifiyarta hancin irin nata idon ma irin nata karamin bakin ma haka gashin girane kawai ta kwaso Abbanta don nashi shima a cike yake da gashi baki wulik sosai masha Allahu tabarakallah kyakyawa ce sosai, tunani ta farayi yaza a gaya ma Abubakar wannan tashin hankali wani hawayene ya zuba mata masu zafi cike da tausayin jaririyar da kuma mahaifinta."

"Umma ta share hawayen ta kalli Asmee da har lokacin kuka takeyi itama ta ce ""Asmee kiya hakuri Allah dayafi mu sonta ya dauke abunsa yanzun addu'an kawai take bukata""."

"Asmee ta girgiza kai sannan ta ce ""Umma me yasa mutuwa zatai mana haka meyasa baza ta daukemu mubiyu ba Aisara ta wuce k'awa a wurina itadin jini ta ce tun muna yara muka taso tare komai tare mukeyinshi abin burgewa gashi yanzun ta tafi tabarni"

nikadai ya zanyi da rayuwata Umma bana tunanin nima zan iya cigaba da rayuwa ni kadai ba tare da ita ba ta kuma fashewa da wani kukan mai tsuma rai.

"Umma ta ce ""Subhanallahi Asmee meyasa zaki fad'i haka sai kace ba musulma ba Allah daya fimu sonta ya dauki abinshi don haka kawai addu'anmu take bukata kuma kidena kuka muddin kina sonta kimata addu'an Allah yaji kanta da rahma."

"Asmee ta share hawayen fuskanta ta ce ""Shikenan Umma bazan kara mata kuka ba Allah yajikanki yar uwata Allah ya yafe miki kura kuranki yasa can ta fiye miki nan duniyar."

"Umma ta amsa da Amin ya hayyu ya qayyum, Sannan ta ce ""Anba jaririyar madara ne Asmee ta ce ""Aah don tunda sukai mata wanka yarinyar keta bacci bata farka ba tukunnan, Umma ta ce ""Allah sarki yarinyar kinsha wahala a ciki dole kisha bacci Allah yajikan mahaifiyarki Aisaratu."

Asmee ta amsa da Amin.

"Umma ta ce ""Yaka mata a tanadi madaran daza a bata kije ki tambayi likitocin wani irin madara ya dace a dinga bata zasu rubuta miki sai asiya kafin ta tashi don da yunwa zata tashi."

"Asmee ta ce ""Umma zan bata nonona tasha"", da mamaki Umma ta ce ""Haba Asmee kefa budurwa ce wacce bata tabayin aure ba taya zaki kashe nononki tun kafin kiyi aure Aah bazan yarda da haka ba gaskiya kawai kije kiyi abinda nasa ka ki""."

"Asmee wasu hawayen ne suka zubo ta ce ""Umma don Allah karki hanani bana son jaririyarnan tai maraicin Mahaifiya kusa da ita ko kadan, don Allah kibarni na shayar da ita nifa kamar mahaifiyar tace kuma banason tasan bata da mahaifiya zan riketa kamar nice wacce ta haifeta don Allah kar wanda ya hanani haka domin itadin jini nace kamar yadda muke da mahaifiyarta bazan bari tasan cewa bani na haifeta ba don Allah Umma kar kice A'a ta kuma fashewa da wani kukan muna funcin don haka yana daya daga cikin plan d'inta da suka tsara da Sabitu."

"Umma tausayi Asmee ne yaka mata yadda ta sadaukar da farin cikinta saboda jaririyar, nisawa ta yi cike dajin dadin kalaman Asmee sannan ta ce ""Shikenan insha Allahu ba wanda zai fada mata bake bace Mahaifiyarta ni da kaina na baki ita koda mahaifinta bai amin ceba balle nasan ba abinda Abubakar zaice akan hukuncin da na yanke sannan ta ce ""Kije kima likitan bayani don sun baki magungunar da zai tsatso miki da ruwan nonon saiki fara shayar da ita Allah yai miki albarka, Asmee ta amsa da amin sannan ta mik'e ta fita a daki tana share hawayen fuskanta cike da murna."

"Wayanta ta dauka ta kira Sabitu ta ce ""Kun tafi da gawar ta ne""? Sabitu ya ce ""Eh Umma kuma mun sanar ma Abubakar akan yazo yanzun nan amman bamu fada mishi halin da ake ciki ba ya ce gashinan zuwa dai""."

"Umma nisawa ta yi cike da tausayin d'an nata ta ce ""Shikenan muma gamunan zuwa gidan insha Allahu"", Sabitu ya ce ""Allah ya kawo ku lafiya sannan ya kashe wayar."

Alh. Abubakar kuwa tun lokacin da akai mishi waya akace yazo kaduna yasan ba lafiya ba amman ya daure zuciyarshi ya kamo hanyar kaduna gashi gabanshi sai faduwa ya keyi ya rasa gane dalilin haka kawai yaita addu'a gashi sai kiran number Aisarah yakeyi bata dauka.

Asmee yadda Umma ta ce tayi haka tayi Dr. Yabata magunguna tasha sannan ya fada mata kayan fruit d'in da zata dinga sha sannan ta fito tai mishi godiya taje tasamu Umma sukaje suka biya kudi a wurin biya suka fito daga Hospital din zuwa gida.

Suna isa gida a lokacin mutane sun fara taruwa Asmee duk rashin imaninta koda taga gawan Aisarah kwance bata motsi sai da hankalinta ya kara tashi.

"Suna tsaye jaririyar na hannu Asmee Umma ta ce ""Asmee kije ki zauna ki huta Asmee ta girgiza cike da damuwa."

"A dai dai lokacin motar Alh. Abubakar ya shigo gidan, da sauri yai parking ya fito koda yaga mutane a waje hankalinshi ya tashi gashi ya shigo gida ma ya gani mata sai kuka sukeyi zuciyarshi ce tatsinke lokacin da ya hango mutun rufe kwance a kasa a kan carpet."

"Da sauri ya karisa wurin ganin Umma sai hankalinshi ya kwanta ganin yaga Sabitu da kowa da kowa hankali ya kara kwanciya tashin hankali lokacin daya duba mutane dakyau baiga matarshi cike da fad'uwar gaba ya ce ""Umma ina matata?""."

"Wani kuka ne ya sufce ma Umma wanda batai tunanin zai zo ba, Abubakar ya kara rud'ewa ya ce ""Asmee ina matata take itama Asmee kukan ne ya kara zuwa mata saboda tausayinshi da sauri ya karisa kusa da ita don ko gani ba yayi balle yaga jaririyar dake hannunta ya rik'ota da karfi ya fara girgizata yana ina matata take nasan zaki fadamin ko kukane ya kara zuwa mata ta kasa cewa komai sai girgiza kanta ta keyi, cikin tsawa ya ce ""Ya ina tambayan kowa yai min shiru ne nace ina matata take ne?""."

"Jaririyar ce ta fara tsala kuka alaman ta tashi sai a lokacin ya kalli yaririyar dake hannunta fuskan Aisarah ya gani wani dariya ne ya sufce mishi yasa hannu ya fisgo yarinyar a hannu Asmee ya rungumeta ya ce ""Daman kina jina shine kikai banza dani ina kika shiga hankalina ya tashi inata nemanki Umma ganin irin matsan da yai ma jaririyar gashi sai kuka takeyi da sauri tasa hannu ta kwaceta da karfi ta ce ""To wanna ba matarka bace matar ka ta riga da tarasu""....."

"[9/21, 6:07 PM] _Page 45&46_"

"Kallon Umma yatsaya ya nayi kamar wawa can kuma ya fashe da dariya ya ce ""Umma ki bani mamata bana son irin wasan nan Umma baki tabamin irinshi kuma sai yau, ni nasan itace matata ki bani ita karki rabani da ita bazan iya rayuwa babu ita ba please Umma."

"Umma ta mik'a ma Asmee jaririyar ta ce ""Gata kinga tana kuka kije ki bata nonon shiga ciki kafin mu shigo muma."

"Kallon Abubakar yabisu dashi shikuma fuskan Aisarah yake gani a fuskar yarinyar, Umma ta kamo hannunshi ta jashi dai dai inda gawan yake sannan ta zaunar dashi tasa hannu ta kara bude Aisarah dake kwance ko motsi batayi."

"Rudewa yayi yana kokarin mik'ewa da sauri Umma ta rik'eshi ta ce ""Ka yarda matarka Allah yai mata rasuwa wacce kake gani yarinyar kuce da kuka haifa da ita wacce wurin haihuwarta Allah ya amsa Mahaifiyarta, gani tayi ya fashe da kuka yasa hannu ya d'ago gawan Aisarah yana suru katai me yasa zaki tafi kibarni me yasa zaki tafi a lokacin da nake tsananin bukatarki kusa dani Umma ta ce ""Abubakar kaya hakuri nasanka da hakuri da dangana kar kayi sak'o Allah shiyasa dalilin da ya dauke abinshi kaya hakuri kai mata addu'oin don Allah ta fada tana shafa bayanshi dake ta faman kuka kamar karamin yaro ba wanda bai tausaya mishi ba a wurin Umma ganin masu daukan gawa suna ta jira tace kabarta haka a suturta ta akaita gidanta na gaskiya kuka yake sosai yana zubo mata addu'oin na rahama a gareta."

Yana kallo aka fita da ita daga gidan Umma dakyer ta lallabashi yayi shiru suka shiga ciki aka dauko masa jaririyar ya hamsheta gaba daya fuskar matarshi yake gani a tare da yarinyar rungumeta yayi a jikinta cike da kaunarta sannan yai mata hud'u ba da sunan Mahaifiyarshi Aishatu yaso yasa suna Aisarah Amman ya dade yana burin sa sunan Ummanshi za ana kiranta da Nadrah.

***********

"After 5 weeks da rasuwar Aisarah Umma ta gama yanke shawara akan ya auri Asmee don ta lura da kulawan da take bama Nadrah gashi tayi kyau so sai kyawunta sai kara fitowa yakeyi don ta fi Mahaifiyar tata kyau ma kowa sai fadi yake tabarakallah masha Allahu, Asmee kuwa harga Allah tana dan son Nadrah koba komai itace tai sanadiyar mutuwar Mahaifiyarta."

Koda Umma ta samu Asmee da zance tana son hada aurenta da Abubakar batai musu ba inda murnanta yakara baiyanuwa.

Sannan ta samu Abubakar da da maganar inda sam yaki amin cewa akan shikam bazai taba auren Asmee ba don gani yake kamar yaci amanar Aisarah Umma ba yadda batai ba amman yaki amin cewa data matsama yace zai kwace yarinyarshi a hannu Asmee

ya tafi da ita wani kasan suyi rayuwarsu acan ganin haka Umma ta bashi hakuri akan ta janye maganar.

Tasamu Asmee ta bata hakuri wanda tunda ga ranar ta shiga tashin hankali ko kulawa sosai ta rage ba Nadrah don tace akan me zata dinga wahalar da kanta tunda ubanta baya son hada jini da ita.

"Ta samu Alh. Sabitu da maganar ya ce ""Karta damu gobe ta shirya zasuje gurin wani boka wanda shima wani abokinshi ne ya hadashi dashi."

Cike da murna ta koma gida taci gaba da kulawa da Nadrah don Umma ta fara fahimta kamar yanzun Asmee bata ba wani Nadrah kulawa sosai.

Washe gari tace ma Umma Sabitu zai kaita Shopping zatai siyayya Umma tace ba damuwa haka suka tafi da Nadrah duk da taso ta barta a gida amman kar Umma tai wani tunanin yasa ta taho da ita haka suka kama hanya zuwa wani kauye dake hanyan Zaria.

"Suna isa da mamaki bokan ya ce yasan abinda ya kawo su Asmee da Sabitu kallon mamaki sukayi Sannan sukaji bokan ya kwashe da dariya ya ce ""Kai kana son dukiyar d'an uwanka ita kuma tana son Dan uwanka shikam baya sonta""."

"Sabitu ya ce ""Kwarai boka hakane dariya bokan yayi ya ce ""Angama sannan ya kalli Asmee ya ce ""Ita kuma yarinyar hannunki me za aimata shiru tayi don bata da ninyar cutar da Nadrah gaskiya ta ce ""Babu komai boka nidai kawai na mallaki mahaifinta koma ta yayane dariya bokan ya karayi Hahhhhh sanna ya hade fuska ya ce ""Kiyi tunani dai domin na hango tabbas idan har kina son ki auri mahaifin yarinyar nan to dole fa sai kin yarda da abinda zan fadi""."

"Tace ba komai boka koma meye zanyi dariya ya yi sannan ya ce ""Abu na farko dole zaku bar garin nan kuyi nesa da garin nan keda Abubakar da yarinyar nan, sannan na biyu kuma dole yarinyar hannunki baza tai aure ba har abadan muddin kina son ki auri mahaifinta dole baza tai aure ba kuma musa mata tsanar aure a cikin zuciyarta idan kuma ba haka ba tabbas burinki bazai tab'a cika ba idan baki Amin ceba zaki iya tafiya don ba wata hanyar da zamusa Abubakar ya aureki dole sai munbi ta yarinyarshi don ya yanke wa rayuwarshi har abadan bazaiyi aure ba tom idan muna son karya alkhawarin da yayi to fa tabbas yarinyarshi ce zata kasance baza tai aure ba har abadan."

"Wani zufane ya keto mata ya za ai wannan al'amarin kuma ta sadaukar da Mahaifiyar yarinyar kuma yanzun ma dole ta sadaukar da farin cikin yarinyar to rashin imaninta bai kai nan ba, wani zuciyan nata ya ce ""Kenan ke kin fison ki zauna baki da aure har abadan saboda yarinyarnan kema kina son kiyi rayuwar farin ciki kuma kema ki haifi naki yarinyar, meye a ciki don batai aure ba kawai ki amince."

"Nisawa tayi ta ce ""Na amince boka"", sannan ya ce akwai sharadi guda d'aya karki yarda tasa kafarta a Kaduna idan kuka bar garin nan domin ta shigowa Kaduna tom fa tabbas daga ranar zaman aurenki zai kare da Abubakar kuma itama sihirin jikinta zai"

"karye dariya ta yi ta ce Abu mai sauki ita dai muddin zata mallaki abin kaunanta ai bata da matsalar komai a ranar da aka daura mana aure da babanta zamu bar garin""."

"Bokan ya ce ""Tom shikenan yaushe kike son ayi auren da sauri ta ce ainikam koma yaune ina so"", bokan ya ce ""Kina koma gida kuwa zakiji labarin an daura miki aure da Abubakar daga yau yazama naki har abadan sai yadda kika so kiyi dashi yanzun yana tafin hannunki ne""."

Wani dadine ya rufeta Abu kamar wasa wai itace za ta mallaki Abubakar kuma a yau dinna sai ta kasa gas gatawa harta k'osa taje gidan.

"Wani bak'in zare ya daura a hannu Asmee ya ce karki yarda ya kunce koda wasa ita kuma yarinyar amshi wannan maganin ki tabba kinsha shi da ruwa idan kika sha ita kuma zata shane a nononki daga nan ne kuma komai zai tafi miki yadda kike so, ta ce ""Yawwa boka Nagode sosai""."

"Sannan ya ce Alh. Sabitu kai kuma daga yau suna barin garin nan komai zai dawo hannunka sai yadda kayi da dukiyar dariya Sabitu yayi don burinshi ya cika ya ce ""Nawane kudin aikin ka duka""? boka ya ce ""Aa bana amsan kudin aiki sai komai ya Kamala ka kawo min daga baya idan kuma baka kawo ba... Ya kwashe da dariya Sabitu ya ce ""Wannan ba matsala bane idan kudi ne kaida kai mana hanya kudi to mezai hana baza mu baka kudi ba."

Ya ce Asmee taso muje har suka bar wajen Nadrah sai baccinta takeyi hankali kwance suka kama hanya koma Kaduna a hanya ta zuba garin magani a raguwar ruwanta na Mr.v ta shanyeshi duka.

********

A hanya Asmee sai tunani takeyi anya hakan zai faru wai kafin taje gida zataga andaura mata aure da Abubakar.

"Abubakar kuwan yana zaune bakin gado yaji zuciyarshi ta tsinke take yaji yana son aure Asmee a yau dinna idan ba haka akwai matsala da ya dauki abin wasa ne yaga da gaske ne da sauri ya nufa dakin Umma ya fada mata yana son auren Asmee Umma sai da tai jimkadan sannan ta ce ""Aah kaida kace min baza ka aureta ba yanzun kuma kazomin da maganar kana son aurenta to bazan yarda ba don bazan iya zuwa nace mata kuma yanzun ka amince zaka aure taba bayan kasa na fada mata baza ka aure ta ba ai sai ta mai dani karamar yarinya har rokanka nayi akan ta amince da aurenka haka ta amince ba jayayya haka ka watsamin kasa a ido, yanzun kuma na koma Aah bazan iya ba kaje da kanka idan ta amince kazo ayi maganar auren Abubakar ya ce ""Umna pls nifa yanzun nake son a daura mana auren da ita"", Umma kallonshi ta yi cike da son gano wani abu to ya akai ya canza ra ayi lokaci guda haka har yake faman sauri a al'amarin?..."

"[9/21, 6:07 PM] _Page 47&48_"

"Umma zatai magana da sauri ya rik'o hannunta ya ce ""Please kisa a daura auren yanzun zan mata magana kuma nasan zata amince kinji""."

"Gyad'a Kai kawai Umma ta yi sannan ta ce ""Tom kaje ka fada ma kawunka tunda yanzun za a shiga sallar Azhar sai a daura kawai"", cike da murna ya fita Umma kuwa don kar tai tunanin wani abu a zuciyarta ta d'auki waya tai dailing number yan uwa ta fada musu za ai dauri auren Abubakar da Asmee wasu sunji dadin hakan ganin yadda take kulawa ada yarinyarshi wasu kuma akasin haka."

"A hanya Asmee ta ce ""Muwuce shopping don na fad'a ma Umma zamu Shopping ne Sabitu ya ce ""Tom kyayi Shopping da yawa tunda yau zaku bar garin kam sai da gaban Asmee ya fadi a zuciyarta ta ce ""Tom wai ma idan sun tafi kenan baza suji dadin rayuwa ba ina zasuje toh."

Sabitu ya k'atse mata tunani dacewa zan dinga tura muku kudi kisiya duk abinda kike so kinji my love ya shafo kuma tunta murmushi ta saki sannan suka cigaba da tafiya har suka shigo garin Kaduna.

A b'agaren Abubakar kuwa tuni ya shirya cikin farar shadda yayi kyau sosai sannan ya nufa massalacin dake unguwan don anan za a daura auren.

Umma tasa a daura abincin duk da ba wani taro za ayi ba amman tasan yan uwanshi zasu zo shiyasa haka akashiga hidima gashi ta k'osa Asmee ta dawo din takira su sunce suna hanya dawowa.

Karfe daya da rabi aka daura aurenshi da Asmee akan sadaki naira dubu dari biyar tunda ai budurwace ita kamar yadda ya biya na Aisarah.

"Su Asmee suna zuwa gida aka fara mata guda wata yar uwarshi ta amshi Nadrah a hannunta sai a lokacin take tashi kuka ta fara saki mai karfi da sauri Halima ta ce ""Au daga amsanki baza ki bari a shirya uwar taki ba tazamo amaryar babanki atoh"", Asmee wani dadi ne ya mamaye zuciyarta tana kara gas gata maganar bokan Halima ta ce ""Amshi jaririyarki baza tai shiru ba ki bata nono sai a shiryaki kila mu samu tayi bacci."

"Hannu tasa ta Amsheta aikam tayi shiru Halima ta ce ""Kaji yarinya wato ke a dole mai Uwa ita tana amsanki kikai shiru nikam kika tsilliramin kuka""."

"Dariya saura sukayi sannan suka shiga ciki yan 'uwa suna ta ta yata murna nan ne kunya yaka mata da sauri ta nufa dakinta cike da murna ta ijiye Nadrah aikam ta saki kuka Haushi ne yaka mata ta ce ""Kiji shegiya yarinya yau ma kadai baza kibarni naji"

dadi ba yau kam ko nonon bazan baki ba Sai ubanki yasha sannan zan baki kisha aikam kamar taji me tace ta kara volume kukanta.

"Ganin kar wani yaji da sauri ta dauketa ta zauna sannan ta ciro nonon aikam sai da ta mintsileta a cinya sannan ta tura mata nonon a baki kukan ta kuma saki ganin kar aji da sauri tafara lallashinta ta kara tura mata nonon a bakinta dakyer tai shiru ta amsa a zuciyarta ta ce ""Shegiya kawai ai kinci sa a ina da saura imani akan ki da tuni kema nasa akashe ki amman bazanyi haka tunda gashi kin min amfani ta dalilin ki zan auri mahaifinki""."

"Umma ce ta shigo da wasu kaya a karamin a kwati, da sauri Asmee ta gai da ita Umma ta ce ""Allah yai miki albarka Asmee ta amsa da Amin Umma""."

"Umma ta ce ""Wannan yar taki baza ta barki ba tana shan nono tana bacci kawai ki kwantar da ita ke ki samu ki shirya ga wasu kaya kisa daman na ije ma marigayi yane tasa da fitan sunan Allah bai nufa ba ashe rabonki kine gashi kisa kafin Abubakar yai miki naki akwatin""."

"Duk'ar da kai tayi ta ce ""Nagode Umma kuma Allah yajikan Aisarah Umma ta amsa da Amin sannan ta ce ""Idan kin gama shiryawa saiki zo parlour na"", Asmee ta ce ""To Umma""."

Kwantar da Nadrah ta yi sannan ta shiga wanka.

"Bayan ta fito ne daga wanka, ta shirya abinta fess cikin wata duguwan lace tasha stone work sai shining ya keyi ta kalli kanta a mudubi tabbas tasan ta yi kyau kam ba kad'an ba ta dauki ma yafi tasa ta kalmi ta nufa part Ummah nan tasamu kanwar Umma Saratu zama tayi ta kara gai dasu suka amsa ba yabo ba falla sanna sukai mata nasiha da rik'on Nadrah Amana a gareta taji nasihan harda kukan karya sannan suka bata Umarnin ta tafi."

"Fita tayi tana share hawaye inda taci karo da Abubakar yana sakin mata murmushi kauda kai tayi cike da kunya a zuciyarta ta ce ""Wai yanzun nazama matar shi gaban tane ya fad'i tunawa da tayi dole fa subar garin ji tayi a rungumeta wanda ya katse mata tunaninta."

"A jiyan zuciya ta sauke ta ce ""Abban Nadrah kar wani fa yazo ya ganmu"", kiss d'in wuyanta ya yi sannan ya ce ""To meye a ciki kefa matata ce"", ta ce ""Uhmm ni dai zan tafi""."

"Ya ce ""Ina zaki""? Ta ce ""Daki zan tafi""."

"Ya ce ""Dai dai kenan muje tare toh tura baki tayi ta ce ""Uhmm nidai Aah ganin zatai mishi musu yaja hannunta suka tafi d'akin yasa key ya rufe daukanta ya yi cak ya ijeta akan bed yai mata runfa da kirjinshi, Asmee harga Allah wani irin nishadi take ji wanda bata tab'a ji ba."

"A hankali ya ce ""Kina sona""? Shiru ta yi sannan ta gyad'a kai alaman eh tana sonshi da sauri ya hade bakinsu ya hau tsotsan lips dinta batai wata wata itama tahau kissing dinshi kukan Nadrah ne yadawo dasu da sauri ya cire bakinshi

Please Login or Register in order to submit comment