You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma kidage da addu'oi da Ibada kar kiyi wasa dashi shima zai tai maka miki sosai"", Nadrah ta ce""Tom Maman Shahid amman fa Mamanshi bata kaunata ko kad'an"", Maman Shahid ta ce ""Ke zaki sa ta soki Nadrah koda kina gaida itane bata amsawa karki gaji kullun kidingayi koda bata kulaki ne idan kin gaida ita, karki yadda kiyi mata rashin kunya har d'aki kidinga gyara mata karki bari masu aiki su dingayi duk wani abu nata kidinga kokari kinayi wllh a haka zata soki koda tana zaginkine ki daure komai tunda bautar Allah kika zoyi"", Nadrah shiru kawai tayi Mamah Shahid tana kara bata shawarwari akan yadda zatasa uwar mijinta taso ta, da shi kanshi mijin, bayan sun gama wayan ne tai mata godiya sannan sukai sallama."

"Ta ijiye wayar ta mik'e ta d'auki dogon hijab d'inta ta saka sannan ta fito parlorn, zaune tasa meshi yana latsa waya, tai hanyar fita ya ce ""Ke Ina zaki""? kamar bazatai magana ba ta ce ""Zanje nagaida Mama ne da kuma Granny"", Areef ya ce ""Ba Mama ba Ammee zaki ce yar kauye kawai"", banza tayi dashi tai fice warta a d'akin don tsoronta karya kamata don tasan bazai kyaleta ba."

"Areef yasan ko taje wurin Ammie ba amsa gaisuwarta zatai ba, ya tab'e baki yaci gaba da latsa wayarshi, don chart su keyi da Yasir har Yasir yake tsokananshi ya angonci Areef ya bashi labari yadda sukayi da kukan data dinga mishi ta hannashi bacci shikuma sai dariya yake mai, Yass ya ce ""Na d'auka ai sai da kayi abinda kayi ninya, Areef ya ce ""Ai zanyi amman ina son na bata lokaci ne yadda zata san cewa ni ba kanwan lasa bane"" dariya Yasir yayi ya ce ""Ashe cika baki ne kawai, dariya Areef yayi ya ce ""Kawai akwai dalilin da yatsa na kyaleta kasan abinda nayi ninya bana fasawa Yass amman idan ta shiga hannu zata gane wanene ni"" a zahirin gaskiya abinda yasa Areef bai ma Nadrah komai ba kawai wani irin bala'in kishine da tunanin maza nawa tai mu'amala dasu yasa ya kasa yin mata komai shi kanshi hakan ba k'aramin mamaki ya bashi ba akan me zai tsaya yana kishi akanta ma."

"Nadrah a hankali take sauka k'asa, Ammie ta na zaune ita da iftee suna hira da yake ba school sun gama exam, Nadrah a hankali ta karisa idan Ammie ta ke ta duk'a har kasa tai k'asa da kai ta ce ""Ina kwana"" Ammie banza da ita tayi taci gaba da kallonta, iftee ta ce ""Anty ina kwana"" Nadrah kasa amsawa ta yi kawai tai mata murmushi itama iftee ta maida mata, tana duke har lokacin ta kara cewa ""Ina kwana Ammie"" Ammie cikin b'acin rai ta ce ""Da ban kwana ba zaki gani shegiya uwar naci tunda kika gaidani da farko ban amsaki ba ai kinsa bana buk'atar gaisuwar taki ne, karuwar banza karuwar hufi kawai tashi kibar gabana raguwar maza kawai don bala'i ma a rasa wanda za a had'a ta aure da d'ana sai karuwa"", Areef a lokacin yake sakkowa k'asa yaji duk abinda Ammie ta ce A zuciyarshi baiji dad'in kalaman Ammie ba amman yai fuska ya k'arisa parlorn ya zauna kusa da Ammie iftee kuma taje ta zauna a jikinshi tana kallon Nadrah don tausayi ta bata yadda Ammie ke mata fad'a."

"Nadrah kuwa kuka ne ta fashe dashi a wurin gashi ta kasa mik'ewa tabar wajen saboda kafarta yayi tsami da duken da tayi, Ammie ta ce ""Son fito kenan, Areef dake satan kallon Nadrah ya ce ""Yes Ammi ina kwana"" Ammi ta amsa cikin sakin fuska ta na shafa yalwataccen gashin kanshi daya sha gyara iftee ma gai dashi tayi tana mishi k'orafin yayi alkhawarin bai cika ba."

"Ammie ta kalli Nadrah dake duke sai kuka takeyi mai sauti, ta ce ""Munafuka tashi kibar wajen nan karki yarda ki kara zuwa dasun kinzo gai dani"" Nadrah kokarin tashi tayi amman gaba d'aya ta kasa, Areef kallonta kawai ya keyi baice komai ba."

"Ammie ta mik'e cikin zafin rai ganin yadda Nadrah taki mik'ewa, ta nufa inda take tasa hannu ta rik'ota da k'arfi ta mik'ar da ita ta turata waje, Nadrah zubewa tayi a kasa timm saida ta buge hannun kuka ta saki da k'ara saboda yadda hannunta yahau yin mata zugi, Areef gaba d'aya ya fara rasa natsuwarshi da sauri ya mik'e zai fita Ammie ta ce ""Son Ina zaka kuma"" Areef ya shafa kai ya ce ""Zanje na gaida Granny kinsa gobe Daddy zai dawo karta fad'a mishi bana zuwa gai da ita Ammie ba tare da tayi tunanin komai ba ta ce ""Eh haka ne kuma shikenan""."

"Areef da sauri ya fita, ganinta yayi durkushe a k'asa wurin tana ta kokarin tashi amman ta kasa sai kuka ta keyi da sauri yasa hannu ya d'agota ya rungumota jikinshi wani ajiyar zuciya ya sauke Nadrah kuwa ta kwantar da kanta a kirjinshi tana kuka saboda yadda hannunta kemata azaba, a hankali ya d'ago da kanta a kirjinshi ya tallabe fuskan nata ya ce ""Mene ne kike ma kuka kuma""? Nadrah kasa cewa komai tayi tai kokarin zame jikinta a nashi da sauri ya k'ara rik'eta gam a jikinshi ya ce ""Ba tambayanki na keyi ba"", cikin muryar kuka Nadrah ta ce ""Hannu nane kimin ciwo na buge ne a hannun, d'aukanta yayi cak ya nufa da ita hanyar part d'in Granny da yake ba kowa ta bangaren, yana zuwa ta zaunar da ita akan kujera da ake ijewa Granny"

"idan tafito san iska sannan ya ce ""Bani hannu kin mik'a mishi hannun tayi tana share hawayen fuskanta, hannunshi yasa ya kamo hannu nata sannan ya jashi da karfi yasan zatai ihu da sauri ya toshe bakinta da nashi ya fara tsotsan lips dinta kokarin kwacewa tayi saboda azaban da hannu yake mata kin sakin bakinta yayi sai da yaja hannun sosai sannan ya saki bakinta wani kukan Nadrah ta saki duk da taji hannun yad'an sakin mata, Areef ya ce ""Kimin shiru saboda bana son kuka"" dena sheshekar kukan tayi amman hawaye suna zubo mata, ya ce ""Me yasa da tace ki tashi kikak'i tashi to""?, a hankali Nadrah ta ce ""Lokacin k'afata ya rik'e ne shiyasa na kasa tashi""."

"Nisawa yayi ya ce ""Saiki tashi kije ki gaida Granny, sannan kuma ki dena kukan nan domin Granny zata tambayeki meya faru karki yarda kice mata Ammie ne"", yana fad'in haka ya juya yabar wajen."

Sai da tashare hawayen fuskanta duka sannan ta mik'e a hankali ta shiga parlorn Granny.

"Da sallama ta shiga d'akin ba kowa a parlorn Granny ta amsa sallama tana d'iyata ce shigo ciki mana"", Nadrah wuri ta samu ta zauna a parlorn Granny ta ce ""Kishigo uward'akin mana yau k'afata ciwo take min shiyasa bazan iya takata ba"", Nadrah ta shiga d'akin da sallama Granny ta amsa ta ce ""Zauna kusa dani, zama Nadrah tayi a hankali tai k'asa da kai sannan ta gaida ita cikin ladabi da biyayya, Granny ta amsa tana kin kwana lafiya ya bak'unta kuma""? Nadrah murmushi kawai tayi tana Alhamdulillah Granny""."

"Granny kallonta tayi tana son fahimci wani abu, ta ce ""Baki da lafiya ne ko kuwa Areefu yai miki mugunta ne don nasan halinshi ""? Nadrah ta ce ""A'ah Granny ina lafiya kalau kuma ba komai, kawo kafar taki na matsa miki ita"" don karta k'ara mata wani tambayan Granny ta ce ""Yawwa yar albarka daman ina jira Larai ne tagama aiki tazo ta matsamin kafar, tunda zaki matsamin shikenan ai ta mik'a mata kafar Nadrah ta fara matsa mata shi a hankali yadda zataji dad'in kafar sosai aikwan Granny harda lumshe ido tana kai Allah yai miki albarka ashe kin iya matsa kafa haka sosai"", Nadrah ta ce ""Lokacin babana yana jinya haka nake matsa mishi kafa kusan kullun har Allah ya amsa abinshi"" Granny ta ce ""Ayya Allah sarki Allah yajikansa da Rahman da yan uwa musulmai gaba d'aya"" Nadrah ta amsa da Amin tana kara matsa mata kafar, Granny kuma sai shi mata albarka ta keyi."

"Tana zaune tana matsa ma Granny kafarta har lokacin Granny kuwa tuni tayi bacci saboda ba k'aramin dad'i take jiba, Nadrah kuwa bata gaji ba ta ciga ba da matsa mata kafar."

"Areef ne ya shigo part d'in Granny amman yaga ba kowa a parlorn direct ya wuce bedroom d'inta, yana shiga yaga Nadrah tana matsa ma Granny k'afa zama ya yi a bakin gadon ba tare daya ce mata komai itama ko kallon inda yake batai ba."

"Sukai wurin 30 minutes a haka sannan Areef ya d'ago kanshi ya kalleta yaga har lokacin matsa mata kafan takeyi, ya ce ""Tunda tayi bacci ki barta mana, karaf a kunne Granny ta mik'e a kwance da take ta ce ""To d'an bakin ciki wato na samu tana matsa min k'afa shine zaka ce ta bari tunda nayi bacci to Allah yasa baccin nawa beyi nisa ba, Areef ya ce ""Granny naga ta dad'e tanayi ne waita huta ne daman yasa na fad'a haka""."

"Granny ta ce ""Kaji wai shi mai mata yaushe har kasan haka Areef matar da kace baka so shine yanzun zaka zo kana wani gulma kai a dole kana jin tausayinta to baza ta dena ba din idan ka isa kai kazo kaimin""."

"Areef banza da Granny yayi yana danna wayarsa, tasan ba kulata zaiyi ba ta ce ""Me ma ya kawoka d'akina ne"", Areef sai a sannan ya kalleta ya ce ""Nazo na tafi da matata ne"" Granny ta rik'e baki ta ce ""Sannu mai mata tashi ka fitan min a d'akin kafin kaimin rashin kunyar da kasa ba"", Areef ya ce ""Ba inda zani kuwa"" Granny ta ce ""Kinga yarinyata mik'omin jalbinnan na kusa dake Nadrah ta d'auki jalbin ta mik'a ma Granny, Areef yasan zata iya zula mishi kuwa da sauri ya mik'e yana wato ke muguwa harda mik'a mata koh Nadrah dai batace komai ba ta kauda kai."

"Areef kuwa ya fice a d'akin Granny tun kafin ta zuba mishi bai masan me ya kawo shi d'akin ba, siririn tsaki ya saki mtsww sannna yabar wurin gaba d'aya ya nufa wurin parking lot bodyguard ne sukazo da sauri zasu bud'e mishi mota ya d'aga musu hannu alaman baya buk'ata, ya shiga yaja motan yabar gidan."

**********

"Nadrah bata bar part d'in Granny ba sai bayan sallah Isha'i, da yake sun d'anyi hira kad'an da Granny Nadrah ta saki jiki da ita kuma ta ci abinci so sai ba laifi, sannan tai ma Granny sai da safe ta tafito daga part d'in."

"Tana shiga parlorn taci sa'a ba kowa a parlour, daman tsoranta karta had'u da Ammie, don ita yanzun tsoroma take bata, harta fara haura upstairs taji ance ""Ke daga gidan ubanwa kike ko kinje yawan karuwanci naki ne?"""

"Nadrah shiru tayi ta kasa cewa komai, Ammie ta daka mata tsawa, ""Ke dan ubanki ba dake nake magana ba koni sa'arki kine ina miki magana zakiyi banza dani?"" Nadrah muryarta yana rawa ta ce ""Kiya...ha..kuri..ina...part d'in...Granny...ne"", Ammie batare da ta ce mata komai ba tabar wajen, Nadrah ganin Ammie tabar wajen yasa tatafi da gudu ta fad'a d'akinta ba tare da ta lura ba taji ta bangaje mutun tsorata tayi ta zaro manya idanuwanta zata kwara ihu da sauri yasa hannun ya toshe mata baki, Areef ne daman ya jita shiru ya tashi don yaje ya taho da ita sai gata kuma."

"Areef ya ce ""Ke matsoracciya nine nan"", wani a jiyar zuciya ta sauke sanna ta kwace jikinta anashi."

"Batare da ta ce mishi komai ba tabar wajen ta shige dakinta, komawa yayi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, shi gaba d'aya tsakanin jiya dayau ya kasa gane me yake damunshi ne, tashi yayi ya shiga bedroom d'inta ita kuma lokacin tana cire rigar jikinta zata shiga wanka, kauda kai yayi ya ce ""Ke idan kin gama ki sameni a parlorn"" yana fad'in haka ya fita a d'akin baki ta tab'e sannan tai shigewarta toilet."

"Bata d'au lokaci ba ta fito ta gyara jikinta ta feshe jikinshi da turare sannan ta saka wata k'aramar riga ce sai k'aramin wandonshi na bacci ne ba k'aramin kyau kayan sukai mata ba, da kamar baza taje ba tasan halinshi yasa ta zunbula hijab d'inta da yake har kasa ta fito parlorn, akan kujera 3seater ta ganshi zaune yana kallon film a TV a hankali ta k'arisa inda yake ta ce ""Gani""..."

"[9/21, 6:07 PM] : _Page 87&88_"

"D'ago da kanshi yayi ya kalleta ya ce ""Ina za kije"", da mamaki ta kalleshi ido cikin ido da sauri ta kauda fuskanta anashi saboda yadda yai mata kwarjini, sannan ta ce ""Ni fa ba inda zani bakai kace min nazo ba, kuma kana tambayata ina zani""."

"Areef ya ce ""Naga kin saka hijab ne sai kace wacce zataje masallaci"", bata ce mishi komai kawai ta kauda kai, nisawa ya yi ya ce ""Ki cire wannan hijab d'in"", Nadrah ta ce ""A'ah bazan cire ba gaskiya"", kallonta yayi ya had'e fuska ya ce ""Ni sa ankine ina miki magana kina cemin A'a"", Nadrah ta tura baki ta ce ""Naga fa kayan bacci ne kawai a jikina shiyasa, haka kawai sai kama cire hijab sanyi akeyi ai"" Areef da mamaki ya d'ago ya kalleta ya ce ""Lallai ma mazan banza nawa suka ganki ba kaya nida nake halak d'inki mijinki shine zaki zo kina wani boye boyen banza mezan gani to?, common ki cire wannan hijab d'in tun kafin ranki ya b'aci a wurin nan""."

"Nadrah batason wa inna kalaman da yake mata, cikin sanyi jiki ta cire hijab d'in badon tanajin kunyar shigar bace kawai batasan yai mata rainin wayau ne shiyasa ta saka hijab d'in daman."

"Kallonta yayi From head to toe, gashinta ta tufkeshi ne daman a tsakiya kanta kamar yar tsana yayi mata kyau sosai gashi gaban goshinta ya kwanta sosai luf-luf a fuskanta abinshi, yar baby face dinta ya k'ara kyau, k'aramin bakinta sai shiney yakeyi ka d'auka tasha jambaki ne yadda yai pink sosai, rigar jikinta yabi da kallo daman mai bottle ne agaba kallon yadda shape d'in nononta yayi ya na kallon tsayayyun nonuwanta yadda sukai kyau a rigar ba k'aramin tsole mishi ido sukai ba, hips d'inta ya kalla yadda suka ciko a k'aramin wandon data sanya mai had'e da rigar duk da ba kibane da ita ba amman akwai hips mai d'aukan hankali, fararen cinyarta ya zuba ma ido yana lumshe idanuwanshi, Nadrah ganin yadda ya zuba ma jikinta ido, kawai ta kauda kai, tai kaman batasan yana yi ba, tana mamakin yadda yake kallon jikinta yadda kasan yana neman abun da ya b'ata a jikinta."

"Wani boyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalleta, cikin cool voice dinshi ya ce"

"""I need coffee""."

"Nadrah yi tai kamar bata jishi ba tana wasa da jelar gashinta daya biyo ta k'ugunta, ganin ashe abinda zai ce kenan ya tsaya yana raina ma kanshi hankali."

"Areef yasan taji shi a hankali yasa hannunshi ya janyota jikinshi ta fad'a kan lallausar cinyarshi ta zauna zare ido tayi tana kokarin tashi a jikinshi d'in, ya k'ara matse hannunta, zuba mata idanuwanshi yayi wa inda suka janza kala zuwa launin jajawur ya ce ""Me yasa kika rai nani ne ina miki magana kikai banza dani ni sa'anki ne""? D'ago kai tayi ta kalleshi zatai magana ganin yadda idanuwanshi suka sauya kala yasa ta kasa bashi amsa tai k'asa da kanta kawai, Areef a hankali ya kara matso da fuskanshi zuwa nata Nadrah da sauri ta kauda kai gefe sai jin saukar numfashinshi taji a wuyanta yana shin shinar wuyanta, da sauri ta mik'e jitayi ya maida daita kan cinyarshi yadda baza ta iya tashi ba, ya d'aura hannunshi a saman k'ugunta yana matsawa da mirzawa a hankali, runtse ido tayi lokacin da taji k'anshi a kan nononta yana cusa k'anshi yana shak'an daddad'an k'amshin dake fitowa a wurin, Nadrah kasa kwakwarin motsi tayi tanajin yadda yake fitar da zazzafan nunfashi akan kirjinta din."

"Ji tayi ya juyar da ita ya kwantar da ita akan kujera kokarin tashi tayi yai sauri danneta da kirjinshi ya kai kanshi wuyanta yana hura mata iska mai dumi da dad'i, sannan yakai bakinshi kan lips dinta ya fara yawo da halcenshi akan lips dinta runtse ido kawai Nadrah tayi a hankali ya zira halcenshi a cikin bak'inta ya fara tsotsan lips dinta cike da k'orewa, hannu yasa ya fara b'alle bottle d'in gaban rigarta, Nadrah kasa hannashi ta yi tanajin yadda ya fara yawo da hannunshi a saman kirjinta yana matsa saman nipples dinta wani irin nishi Nadrah ta saki don jikinta ya fara amsan sakkon nin da yake aika mata dashi."

"Hannunshi d'aya ya sa ya fara matsa hips d'inta wani irin gigicewa yayi yana kara tura halcenshi cikin bakinta wani irin cafka Nadrah tai ma lips dinshi ta fara maida mishi da martani sosai take bashi Hot kiss wanda ke kara rik'ita Areef, Areef basai ya kara gigicewa ba yana kara matsa mata kirjinta da hips d'inta, zare bakinshi yayi anata ya d'aurashi kan nononta yana lashewa yana tsotsan nipple d'inta yana shafa mata d'ayan a hankali, Nadrah kara tura mishi kirjinta tayi, saboda salon da yake mata yakara haukatata itama, Nadrah bakinta ta takai setin kunneshi ta zira halcenta a cikin kunneshi tana zuk'an kunnen tare da hura mishi wani sanyayar numfashinta a kunnenshi, karamin ihu Areef ya saki Ashhh yana kara tura bakinshi cikin nononta kamar zai had'iyeshi, hannunshi yakai kan cibiyarta ya fara yawo da hannunshi a wurin yana zagaye yatsanshi a wurin yana matsa mata yatsanshi a ciki, nishi Nadrah ta saki tana kara zira halcenta cikin kunneshi, hannunshi ya kai kan cinyarta ya fara shafawa a hankali yana yawo da hannunshi zuwa saman HQ dinta da sauri Nadrah ta zare halcenta ta dake cikin kunneshi ta zame jikinta da karfi tana son tashi kara damketa Areef yayi ta matseta sosai a kirjinshi yana sauke wani wahallen numfashi sai da suka kai kusan minti 20 a haka ko wannensu yana sauke numfashi sannan Areef ya d'ago da kanshi a wuyanta ya zuba ma fuskanta ido, da idanuwanta da suke lumshe kamar mai bacci, kasa jurewa yayi ya manna ma bakinta kiss kana a hankali ya ce ""Nadrah!"", tunda take bata tabajin yakira sunanta kuma batai tunanin yasan sunanta ba ma."

"Bud'e idonta ta yi ta d'aura akan nashi da sauri tai katsa da idonta, don idonshi kwarjini yake mata, hannu yasa ya shafa yalwataccen suman kanta wanda suka fara hirgitsewa sannan ya kuma cewa ""Fad'amin maza nawa suka sanki a y'a mace""?"

"Nadrah kuwa shiru tayi don harga Allah ita tambayar nauyi yake mata asalima batasan yana mata wannan tambayar, amman me yasa yake min wannan tambayar to?, tafada a zuciyarta."

"Jitayi ya kwantar da kanshi a kirjinta yana sauke numfashi ya ce ""Nasan kina tunanin me yasa nake miki wannan tambayar ko, nima kaina bansa dalili ba, haka kawai zuciyata take son sani, don Allah ki fad'amin idan ba haka ba zuciyata baza ta samu natsuwa ba"", Nadrah baki ta bud'e zatai magana kawai tari yazo mata ta kware, da sauri ya mik'e yaje ya d'auko mata ruwa a fridge wanda ba sanyi sosai, ya d'agota daga kwance da take ya fara bata a hankali ta fara shan ruwa sai da ya isheta sannan ta kauda kai tana sauke ajiyar zuciya."

"Nadrah bottle d'in rigarta fara mai dawa a hankali, Areef yasa hannunshi ya karisa mai da mata, bata hanashi ba har ya gama, sannan ya kalleta amman ita bashi take kallo ba ya ce ""Bazaki fad'a min ba?"" Nadrah a hankali ta ce ""Nima ban sani ba gaskiya"", kallonta yayi ya ce ""Me kike nufi kina nufin bakisan iya adadin mazan da"

"suka kwanta dake ba ko mene kenan suna da yawa?"" Yai maganar lokacin yaji ranshi yana baci sosai."

"Nadrah wasu hawaye ne suka zo mata ta ce ""Eh amman bawai suna da yawa bane kawai ban irgawane"", Areef mik'ewa yayi batare da ya kuma ce mata komai ba ya bar waje ya wuce bedroom d'inshi."

Nadrah kukane yazo mata ta kifa kanta a hannun kujera tanajin haushin tambayar da yai mata don batasan yana tuna mata da abinda ya wuce a wurinta.

"Areef yana cika dakinshi direct bathroom ya wuce, yana shiga ya cire kayan jikinshi duka yai wurgi dasu ya shiga bahon wanka ya kunne wa kanshi shower yana furzar da numfashi mai huci ya runtse idonshi ya na shafa banananshi data mike tana neman agaji."

"Saida ya kusa 1 hour yana cikin bahon wanka yana tunane tunane kala kala daban daban, shi gaba d'aya ya rasa meyasa yakeji wani bala in kishinta a cikin zuciyarshi wanda tunda yake bai tab'a jinshi akan mace ba sai akanta."

Wanka yayi sannan ya fito d'aure da bathrobe a jikinshi sai k'aramin towel da yake tsane gashin k'anshi dashi.

Nadrah kuka tasha har bacci ya dauketa akan kujeran wanda ita kanta batasan baccin ya d'auketa ba.

"Areef harya gama shirin baccinshi zai kwanta kawai yaji yana son yasha coffee l, ya fito parlorn da mamaki yaganta kwace Inda yabarta, ko kallon inda take bai karayi ba saboda a duk lokacin da zai kalleta sai zuciyarshi ta harba, kitchen ya shigo ya had'o coffee ya zauna akan kujera dake kallonta sannan ya fara kurban coffee d'in a hankali, idonshi ya kasa hakura yanayin yana satan kallonta yadda baccin yai mata kyau yadda take fitar da numfashi a hankali, alamun ya nuna ba jin dad'in baccin take ba barin yadda tai da fuskanta."

"A haka har yagama kurb'an coffee d'in hannunshi, ya tashi ya kashe duka wutan parlorn a hankali ya k'arisa kusa da ita yasa hannun ya dauketa cak, har zai kaita can d'akinta kawai ya wuce da ita d'akinshi yana shiga ya kwantar da ita akan bed d'in ya rufeta da blanket sannan ya tsinci kanshi da manna mata kiss a goshinta ya shafa gashin kanta, sannan ya kashe wutar d'akin gaba d'aya shima yahau gadon ya kwanta nesa da ita, bai d'au lokaci ba bacci ya d'aukeshi shima."

"Sanyi asuba ne ya farkar dashi daga baccin da yake yi a hankali ya bud'e idanuwanshi da mamaki ya d'aura akan kyakyawar fuskanta wacce ke malake dashi shima kuma hannunshi rungume da ita, zame hannunshi yayi a jikinta ya sauka akan bed d'in ya gyara mata kwanciya sannan ya shiga toilet alaula yayi ya fito, ya saka jallabiyarshi ta sallah sanna ya hau kan sallaya ya ta da sallah."

"Koda ya idar yaje ya tasheta a hankali ta bud'e idonta ta d'aurashi anashi kauda kai yayi yabar wajen tunda tatashi, a hankali ta sauki akan bed d'in, bud'e kofa tayi ta fita a d'akin."

"Tana shiga d'akin nata ta fad'a toilet ta d'auro alaula ta fito, ta saka duguwar riga da hijab sannan ta tada sallah."

"Bayanta ta idar da sallah bata koma bacci ba tai ta addu'oi da karatun al'qurni da yake tana da App a wayanta, a haka har garin Allah ya yi haske, sannan ta ijiye wayar bayan ta kasheta gaba d'aya saboda tasan za a iya kiranta shiyasa take kashe wayar gaba d'aya inba amfani dashi zatai bata kunnata."

"Areef koda ya tashi da safe wanka yayi ya shirya cikin English wear riga da wando yayi kyau sosai ya graya gashin kanshi sosai sai baza k'amshi ya keyi, parlour ya fito bai ganta a parlorn ba ya fita a d'akin gaba d'aya."

"Sauka ya yi k'asa a dining ya samu Ammie da Iftee suna breakfast kujera yaja shima ya zauna, sannan ya ce"

"""Ammie ina kwana"""

"Ammie cike da fara a ta ce ""My Son lafiya kalau, fatan katashi lfy?"""

"Areef ya ce ""Fine Ammie"", sannan ya kalli Iftee da take ta faman gai dashi yak'i amsawa, Iftee ta turo baki ta ce"

"""Ya Areef yanzun ka dena sona ko?"""

Dariya Areef yayi ya ce

"""Kin tab'a ganin wanda ya dena son yar uwarshi ne, ai sai da ma soyayya tak'aru a zuciyarshi, kawai nayi busy ne shiyasa kwana biyu, amman har gobe ina matukar kaunarki my little sister"", ya fad'a yana jan kuma tunta."

Murmushi little ta yi ta ce

"""Ya Areef nima ina matukar kaunarka"" Dariya yayi ya ce ""Yawwa my girl""."

"Little ta ce ""Ya Areef ina Anty ne?"" Ammie ta ce ""Ke uban wacece Antyn taki?"""

Iftee shiru tayi tana kallon Areef da shima ido kawai ya zuba mata ba tare da ya ce mata komai.

"Nadrah tashi ta yi

Please Login or Register in order to submit comment