You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bani ce na haifeki ba."

"Sannan ta kwantar da murya ta ce ""Nadrah yau ni kike fad'a ma wa 'innan zafafan kalaman ko don kawai na miki aure yara nawa suke sadaukar da farin cikinsu don kawai su faranta ma iyayensu, ni nayi haka ne don rayuwarki kawai ta gyaru amman kike jefata da wa innan kalaman yanzun daman bazaki iya sadaukar da farin cikinki saboda mahaifiyarki ba amman ita uwa tana sadaukar da farin cikinta don kawai saboda yaranta nagode Nadrah shine abinda zaki saka min dashi"" ta fashe da kuka itama."

*********

Areef horn yayi sannan ake bud'e mishi gate ya shiga yai parking motanshi ya nufa hanyar parlorn gidan.

"Nadrah da sauri rik'e kafar Mommah cikin kuka ta ce ""Mommah kiya hakuri don Allah kisa nai wani abin amman banda aure zan iya sadaukar miki da komai idan kina so Mommah amman banda zance aure don Allah Mommah kite maka ma rayuwata ki raba wannan auren idan ba haka ba mutuwa zanyi Mommah na rok'eki""."

"Mommah cikin bacin rai ta ce ""Koda mutuwa zakiyi wllh bazan tab'a raba wannan auren ba dole kiyi zaman aure ato don nagaji da ganinki haka"", ta sa hannu tashare hawayen munafinci da tayi ta mik'e zata fita a d'akin."

"Da sauri Nadrah ta rik'e kafarta d'aya ta ce ""Mommah don Allah karki min haka nifa yarinyarki ce bai kamata kimin haka don Allah karki sa rayuwata ta lalace bazan iya zama da aure ba Mommah ki raba auren ne don Allah ki tausaya ma rayuwata mana""."

"Mommah ta fisge kafarta ta ce ""Wllh Nadrah na fad'a miki bazan raba auren nan ba, kuma buddin kika k'aramin magana akan raba auren nan wllh Allah ya isa tsakani na dake Nadrah."

"Ta fita a d'akin, dai dai lokacin taji ana knocking k'ofan parlour ta nufa wurin ta bud'e ganin mutun tayi da yake batasan Areef ba ta ce ""Waye kai""? Areef sai dai yai Jim kad'an sannan ya ce ""Ni ne Areef wanda aka daura ma aure da Nadrah yarinyarki"" ya fad'a kamar bazaiyi maganar ba."

"Mommah ta ce ""Maza shigo mana sannu da zuwa ta fad'a tana yashe baki."

******

"Nadrah numfashinta ne ya tsaya cak dajin abinda Mommah ta fad'a ta kasa numfashi gaba d'aya, Nafisa dake tsaye bak'in kofa tana sauraran abinda ke faruwa itama kukan ta keyi sosai cike da tausayin Nadrah, ganin Mommah ta fito ne ta shiga d'akin da sauri."

"Ganin Nadrah tayi idonta a kyame wuri daya, da sauri Nafisa ta karisa wurin da rik'eta ta girgizata da karfi ta ce ""Anty Nadrah meke faruwa dake ne""? Nadrah ta fara shure shuren kafarta tana ""Na..fi.sa ke..tai ma..ka..min na..ka..sa num..fashi..."",Nafisa ta ce ""A'ah Anty Nadrah ki gwada zaki iya numfashi ki fitar dashi da karfi sosai zai fito don Allah ki gwada Anty"" gaba daya Nafisa ta rude kuka kawai ta keyi tana girgiza Nadrah."

"Nadrah kuwa sai kokarin jawo numfashin takeyi amman ta kasa ta rik'e Nafisa gam a jikinta, Nafisan ganin abin nason yafi karfinta ta kwala ma Mommah kira."

"Mommah don Allah kizo da sauri Anty Nadrah ta kasa numfashi don Allah kizo kite maka mata""."

"Mommah da Areef zaman su kenan ko magana bazu fara ba, taji kiran da Nafisa take mata da sauri dukkansu suka mik'e, Areef yabi bayan Mommah da sauri shima."

"Suna shiga sukaga halin da take ciki, da sauri Areef ya karisa inda Nadrah take yasa hannu ya rik'ota ya rungumeta a kirjinshi, ita kuma ta k'ankameshi ya kalli Nafisa ya ce ""Maza kije ki dauko ruwa mai sanyi da sauri""."

"Da sauri Nafisa ta fita a d'akin don d'auko ruwa, Mommah kuwa tsoranta kar ace mutuwa zatayi tana tsaye a bakin kofar d'akin ta kasa ko d'aga kafarta."

"Areef kuwa gaba d'aya rud'ewa yayi ganin yadda ta keyi kara matseta yayi sosai a jikinshi, yana tofa mata addu'oin da duk yazo bakinshi."

Nafisa ce ta shigo da sauri da ruwan roba mai sanyi ta mik'a mishi.

"Amsa yayi ya bud'e kawai ya juye matashi a jikinta duka da fuskarta, wani ajiyar zuciya Nadrah ta sauke mai karfi tare da kara k'an k'ameshi."

Kunneshi yakai saitin hancinta jin numfashinta yana fita a hankali shima ya sauke ajiyar zuciya ya gyara mata kwanciya a jikinshi.

"Mommah sai a sannan ne hankali ya kwanta tajawo hannu Nafisa suka fito parlour ta ce ""Koda ya tambayeki meya faru da ita kawai kice baki sani ba kema haka kika"

"sameta karki yadda ki fad'a mishi komai idan ba haka ba saina yanka bakinki kinji ai""? Nafisa Kai kawai ta gyad'a mata."

Nadrah kuwa wani bacci ne mai dadi da nauyi ya kwasheta a kirjinshi.

"Areef ganin bacci ya dauketa ne, ya dauketa cak ya kwantar da ita akan bed dinta."

"Areef zuba mata ido yayi yana kallon kyakyawar fuskarta yar madaidaici gashin idonta zara zara kamar tasa eye lashes gashin sun kwana luf-luf sannan ya kalli k'aramin bakinta me dauke da pink lips ga d'igo d'igon ruwa a saman lip's dinta abun burgewa, lumshe ido yayi yasa hannu ya shafa yalwataccen gashin kanta, kasa jure kallon lips dinta yayi a hankali yakai bakinshi dai dai nata ya daura lips dinshi yana goga nashi akan nata wani taushi yaji da tsantsi a hankali ya tsotsi k'asan lips dinta yana lumshe ido."

"Kasa dauke bakinshi yayi akan lips dinta, don wani dadi yaji a lips dinta kamar sweet ya shiga tsotsan lip's dinta a hankali yadda bazai tashe taba."

Hannunshi ya d'aura saman tsayayyun nonuwanta ya fara shafasu a hankali.

Motsi yaji tayi da sauri ya zare bakinshi a nata yai baya da sauri.

Gyara kwanciyarta tayi tana sauke ajiyar zuciya akai akai.

"Areef dafe kanshi yayi ya ce ""Me yake damu nane kuma""?"

Gyara riganshi yayi sannan ya rufeta da blanket ya kashe mata wutar d'akin ya fito.

"Mommah tana ganinshi ta ce ""D'annan mungode sosai""."

"Areef ya ce ""Mamah me ya faru da ita ne haka""? Mommah ta ce ""Am nima ban sani ba kila ko jikin nata ne ya tashi, Areef yai shiru sannan ya ce ""Alright gobe sai akoma da ita hosoital mugani"" Mommah ta ce ""A'ah yaron arziki basai anyi haka ba ma insha Allahu zata warke mungode sosai ma hakan""."

"Tab'e baki yayi sannan ya shafa suman kanshi ya ce ""Shikenan ni zan tafi gobe na dawo na dubata sai da safe yana fadin haka ya nufa hanyar fita ba tare da ya jira me Mommah zata ce ba."

"Momma ta ce ""To mungode agai da gida sai da safe""."

Yana fita ya shiga motanshi ya tada yabar gidan.

Mommah kuwan d'akin Nadrah ta lek'a ganin tana bacci ta rufo mata kofar ta nufa nata d'akin.

Nafisa kuwa d'akin Nadrah ta shige don yau da ita zata kwana.

**********

"Areef kuwa koda ya isa gida ba kowa a parlour da yake dare ya farayi kawai ya haura sama zuwa dakinshi koda yaje yaga ancanza komai na d'akin ansa sababbi hatta TV ma sai da akacanza komai tsarin yayi kyau don yafin mishi nada kyau ma da tsaruwanshi, bedroom dinshi ya wuce da mamaki yaga komai pink and white color ne tsaki yayi ya ce ""Ai wannan kalan mata ne aka samin bedroom dina fitowa yayi ya shiga d'ayan dakin yaga komai White ne ya ce ""Kenan nan ne d'akina yanzun kuma aa bana son d'akin nan nafison nawa cikin bacin rai ya rufe d'akin ya koma wancan, yana"

mita wai basu da hankali wa inda suka sa kayan yaza ai su canza mishi d'akinshi hakan nan ya shiga bathroom don ya samu yai wanka don ko wanka tsarki baiyi ba daman ya baro gidan Jamcy don lokacin ranshi a bace yake abinda bai tab'a yi bakena zama da najasa a jikinshi sai yaji yana kyamar jikin nashi ma.

Bahon wanka ya shige ya yasakar ma kanshi shower ya lumshe idonshi.

Da mamaki fuskar Nadrah ne ke mishi yawa yana tuna abinda yai mata da yadda ta k'an k'ameshi.

"Tsaki ya saki ya ce ""To meye kuma na tunanin banziyar yarinyar can"", sannan ya fara wanka yana kokarin kauda tunaninta a cikin ranshi sai dai ya kasa hakan gaba d'aya ita kawai yake ganin a cikin idanuwanshi."

"Bayan yayi wanka ne ya dauro alaula don ko magrib baiyi ba, ya zura wata farar jallabiya yai mishi kyau sannan ya feshe jikinshi da tura ruka masu dadin kamshi."

Ya tada sallah bayan ya idar ne.

Ya je kitchen ya hada ma kanshi coffee ya fito parlornshi ya zauna akan kujera ya mik'e kafanshi akan glass table dake gaban kujeran.

"Ya fara kurfan coffee d'in a hankali yana lumshe ido, nonuwanta Nadrah ne kawai suka kara dawo mishi a rai da yadda yake shan lips dinta dadi har tsakiyar kanshi, kwarewa yayi da coffee d'in da yake sha da sauri ya ijiye akan table din gabanshi, ya tashi yaje ya bud'e fridge ya d'auko ruwa ya kafa bakinshi sai da ya kusan shanye goran Mr.V sannan ya ijye yana sauke nishin wahala."

"A hankali ya ce ""Me yasa wai indai zan kusanci yarinyar nan gaba d'aya sai narasa control d'ina ne Why""? Ya fad'a yana nufan bedroom dinshi ya kashe wutar d'akin sannan yahau gadon ya kwanta tare da runtse idanuwanshi."

Abin mamaki gaba d'aya bacci yaki d'aukanshi wani irin azaban sha'awar tane ya taso mishi daman kwana biyu ya samu sauki haka gashi yau takuma taso mishi.

"""Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"" kawai yake iya furtawa yadda mararshi ke juya mishi kamar zai cire mishi."

A daddafe ya mik'e ya d'auko wani tablet yasa a bakinshi yafara tsotsa ba tare da ya shata da ruwa ba duk d'acin maganin haka ya runtse ido yake sha ga Ayabarshi ta mike sambal sai haniniya takeyi.

_Page 71&72_

Areef kuwa haka yaita juyinshi akan bed har wani wahallen baccine ya kwasheshi.

_Asuba ta gari_

Nadrah ta bud'e idonta a hankali abinda ya faru tsakaninta da Mommah ne suka sake fado mata tai kokarin ta tuna abinda ya faru lokacin da tai kokarin neman numfashinta ta kasa tuna komai kawai tunawa da tayi wai yanzun haka tana da aure akanta kawai ta fashe da kuka.

"Sheshekan kukanta ne ya tashi Nafisa daga baccin da ta keyi tana bud'e ido taga Nadrah ce, Nafisa ta ce ""Anty Nadrah don Allah kiya hak'uri kar kisawa ranki wani damuwar."

"Nadrah cikin kuka ta ce ""Nafisa Mommah bata sona wllh batasan farin cikina Mommah taimin aure kuma tasan bana son aure har cikin zuciyata Nafisa na rasa dalilin da yasa ban tab'a kaunar aure ba koda sau d'aya ne a rayuwata zuciya k'una take min."

"Nafisa ta ce ""Anty Nadrah kiya hakuri kidauka cewa shine k'addaranki komai da ki kagani ya faru da d'an adam muk'addari ne, Mommah tana sonki Nadrah son nema yasa har tai miki aure nan amman karkisa komai a ranki kawai kiyi zaman aurenki tunda kinji abinda Mommah ta ce akai, kuma sannan ki maida hankalinki ga ubangiji ki mik'a mishi dukan lamuranki yasan dake, kuma Anty Nadrah kina wasa da Addu'oi don Allah ki maida hankali sosai akai koshi zai taimaka miki sosai zaisa ki rage tsanar auren da kikeyi""."

"Nadrah taji dadin maganar yar uwar tata ta ce ""Shikenan Nafisa na gode da kika tunatar dani"", don Nadrah har sallah ma bata cika yinshi akan lokaci ba gaskiya."

"Sannan Nafisa ta share mata hawayen fuskanta ta ce ""Muje muyi sallah rik'e hannunta tayi ta sauka akan bed don bata da karfin jiki har yanzun."

Sannan ta kaita har toilet.

"Bayan sunyi alaula ne suka fito suka tada sallah Nadrah ta dad'e akan sallaya Nafisa taje ta d'auko mata alqur'ani mai girma ta ce ""Anty ki karanta zakiji saukin abinda yake damunki""."

Nadrah rabon da tad'auki alqur'ani ma da sunan ta karanta tun suna zuwa islamiyya tun bayan tayi sauka.

Amsa tayi sai da hawaye suka zubo mata sannan ta bud'e ta fara karan tawa a hankali.

Wani sanyin ni'ima ne ya fara shigan ko wani ga bobbi na jikinta.

Alqur'ani kenan magani duk wata masifa mai sanyaya zuciyar Dan Adam a duk lokacin daya karanta ta a sa ilin da kake cikin damuwa koda baka cikin damuwa.

********

Nadrah da Nafisa basu ijiye alqur'ani ba sai da gari yai haske.

Alhamdulillah Nadrah taji sanyi sosai a zuciyarta rad'ad'in da takeji ya raguwa sosai.

"Kallon Nafisa ta yi ta ce ""Nafisa nagode miki sosai har kinsa naji sanyi a cikin zuciyata""."

"Nafisa ta ce ""Anty Nadrah ba komai duk lokacin da kike cikin damuwa kidinga tunawa akwai Allah kuma sannan ki dinga yawai karatun alqur'ani yana sanyaya zuciya sosai""."

"Nadrah ta ce ""Shiyasa Nafisa ina sonki sosai Allah ya baki miji na gari wanda zai kulamin dake sosai, murmushi Nafisa tayi cike dajin kunyan Nadrah ba tare da ta ce komai ba, kawai ta ce ""Muje sai mugaida Mommah Anty don Allah kibama Mommah hakuri tana fushi dake sosai"", Nadrah ba tace komai dai ta kama hannun Nafisa ta mik'e sannan suka nufa d'akin Mommah."

"Koda su kaje d'akin da sallama suka shiga tana zaune kan sallaya, suka duka kamar yadda suka saba suka gai da ita."

"Amsawa tayi sama sama tana kauda kai, Nafisa ta kalli Nadrah k'asa tai dakai saboda hawayen dake son zubo mata a hankali ta ce ""Mommah kiya hakuri akan abinda ya faru jiya""."

Mommah banza tayi da ita ta kauda kai Nadrah ta d'ago kai ta kalli Mommah taga kamar ba da ita take magana ba.

"Nadrah ta matsa kusa da ita ta ce ""Mommy kiya hakuri don Allah""."

"Nanma shiru Mommah ta yi bata ce mata komai ba Nadrah ta rik'e hannun Mommah ta ce ""Momm saurin dakatar da ita Mommah ta kwace hannunta."

Nadrah kuka ta fashe dashi ta kwantar da kanta akan jinyar Mommah tana Mommah karkiyi fushi dani haka bazan jure ba don Allah kiya femin Mommah bazan sake ba.

"Mommah ta ce ""Nadrah ni yanzun kinfi k'arfina ai ban isa da keba kije kiyi duk abinda kikeso kuma kikaga yafi dacewa dake."

"Nadrah ta ce ""A'ah Mommah kiya femin bazan sake gadda da ke ba."

"Mommah ta ce ""Ni Nadrah duk abinda zanyi don rayuwarki nakeyinshi amman abinda kikeso ki saka min dashi kenan ta fad'a tana kwakulo hawaye."

"Nadrah ta ce ""Mommah karki ce haka don Allah kuskure ne bazan sake ba Mommah kiya femin kuka take sosai kamar ranta zai fita tana ba ma Mommah hakuri Nafisa ma kukan takeyi, ta ce ""Mommah don Allah ki yafe mata tunda ta baki hak'uri ta gane kuskurenta""."

"Nadrah ta ce ""Mommah please na yarda zan zauna zaman auren amman karki cigaba da fushi dani abin zai min yawa don Allah Mommah kiya femin""."

"Mommah ta ce ""Shikenan na hakura na yafe miki kuma kisan irin maganar da zaki dinga fadamin a matsayina na mahaifiyarki Nadrah ta ce ""Bazan sake ba ma Mommah sannan ta rungumeta."

"Nafisah murmushi tayi sannan ta share hawayen fuskanta ta ce ""Yawwa Anty tunda Mommah ta hakura muje muyi breakfast yunwa na keji."

"Rik'eta ta yi suka fito don Mommah ta ce ""Tana zuwa daga baya."

Suna zuwa parlour su kaje dining table already anjera komai na breakfast zama sukayi Nafisa tai serving dinta ta ije mata a gabanta sannan itama ta zuba nata.

"Nadrah kuwa kasa sa komai tayi a bakinta sai ruwan tea koda Mommah tai mata maganar ko farfesun kazan ne ta diba taci amman tace batajin yunwa ne""."

Tab'e bakinta Mommah tayi sannan tahau yin breakfast dinta ita kam.

*********

"Areef kuwa koda ya tashi da asuba yai sallah bai koma bacci ba d'akin Ammi ya wuce yana zuwa ya sameta akan sallaya tana lazimi gaida ita yayi sannan ya kwantar da kanshi akan cinyarta murmushi tayi ta ce ""My son wai Kai kullin baka sanin ka girmane""."

"Areef ya ce ""Ammi nifa yaro ne a wurinki har yanzun murmushi tayi ta fara shafa gashin kanshi kamar yadda ta saba mishi idan ya kwanta a cinyanta, bacci ne ya kwasheshi mai dadi don daren jiya bai samu wani bacci ba sosai."

"Jamcy kuwa tasha kukanta ta k'oshi tayi ma Areef kiran duniya amman yak'i d'aukan wayanta, D'akin Fadeelah ta nufa har lokacin tana sume tsaki tayi sannan ta samo ruwan sanyi ta watsa mata a firgici ta farka."

"Jamcy shak'o wuyanta tayi ta dinga watsa mata mari masu zafi ta ce ""Shegiya muna fuka daman cin amanata kikeyi ni naga take takenki ashe da walakin goro a miya wllh sa'arki daya ya ce ""Kar nai miki komai da wllh yau dinnan saikin bar gidanna kuma ko yanzun ma ba kyaleki nayi ba, ta tureta ta fita a d'akin tana sambatu"

***********

"Areef da rana wanka ya kumayi ya shirya cikin k'ananun kaya yayi kyau sosai, komai fess sai baza k'amshi ya keyi abinshi."

K'asa ya sauko a parlorn yasamu Ammi da iftee suna kallo iftee sai surutu take mata.

"Ammi ta ce ""Lovely Son ina zaka kuma haka""?."

"Areef ya shafa suman kanshi ya ce ""Am Ammi zani wurin Yasir ne kuma daga nan inason na biya company tunda Daddy baya nan ni kuma hutuna ya kusan k'arewa."

"Ammi ta ce ""Shikenan Son sai ka dawo, sannan kuma ka d'auki bodyguard's don na lura kwana biyun nan idan zaka fita Kai ka dai kake fita ni ban ga amfaninsu ba agidan nan""."

"Areef ya ce ""Ammi kinsan fita kai daya yafi dadine babu takura shiyasa ni kadai zanfita pls Ammi zan kula da kaina na miki alkhawari fa""."

"Ammi ta ce ""Son bakajin magana koh shikenan sai kadawo Allah yadawo dakai lafiya please ka kula sosai fa""."

"Ya amsa da Ameen Ammee yana Jan Kumatun iftee ya ce ""Shine bazaki min magana ba iftee ta ce ""Ya Areef bakai bane gaba daya kwana biyu ka dena kulani baka damu dani ba""."

"Murmushi yayi ya ce ""Sorry my little idan nadawo zan kiraki kizo d'akina yau tare zamu kwana ma dariya tayi ta ce ""Yeeeeh sai kadawo ya Areef""."

Murmushi yayi sannan ya fita a parlour.

Parking lot yanufa ya zabi motan da yai mishi ya shiga sannan ya tada motar yabar gidan.

******

Areef kuwa direct gidansu Nadrah ya nufa saboda haka kawai yau yake son yaje ya ga Nadrah yaga yanayin jikin nata.

Koda ya karisa gidan horn yayi mai gadi ya bude mishi gate ya shiga yai parking motanshi a parking lot sannan ya fito ya nufa k'ofan parlorn.

A lokacin Mommah ne kawai a parlorn don Nafisa ta raka Nadrah takinta don tai wanka.

"Masu aikine suka bud'e mishi ya shiga Mommah tana ganinshi tai mishi sannu da zuwa gai da ita yayi sannan yake tambayanta yamai jiki""?"

"Momma ta ce ""Alhamdulillah taji sauki""."

"Sannan aka kawo mishi kayan motsa baki ruwa kawai yasha sannan yake tambayanta ina take Mommah ta ce ""Ai tana d'akinta kaje""."

"Tashi ya yi ya nufa d'akin yana shiga Nafisa kawai ya gani akan bed tana danna waya, tana ganinshi ta gai dashi ta tashi zata fita a d'akin Areef ya ce ""Tana ina ne""?"

"Nafisa ta ce ""Tana toilet ne wanka takeyi sannan ta fita a d'akin da sauri."

Zama yayi yana jiran fitowarta.

"Bud'e kofar toilet d'in tayi a hankali daga ita sai wani karamin towel iya jinyarta kawai ta tsaya ta ce ""Nafisa zoki rikeni na fito na gama."

D'ago kanshi yayi ya nufa bakin toilet d'in don bata ganshi ba saboda bata bud'e k'ofan toilet d'in gaba daya ba.

Mika mata hannunshi yayi ita kuma ta bud'e k'ofan bathroom d'in ta d'ago kanta ganinshi tayi tsaye da sauri tai baya zata fad'i saboda tsoratan da tayi da ganinshi.

"Da sauri yasa hannu ya janyota jikinshi ihu ta saki tana ""Dalla malam sakeni tasa hannu ta tureshi da karfi mantawa tayi ba kwari a jikinta haikon tsantsi ya d'ebeta ta fad'i tim a k'asa......"

"[9/21, 6:07 PM] _Page 73&74_"

"Nadrah kuka ta saki saboda azaba tana ""Ashhhh bayana hannuna zai cire Uhmm Uhmm Areef dariya ya kwashe dashi ya ce ""Wato ke me taurin kai""."

Banza tayi dashi ta kauda kai gashi tana son tashi amman ta kasa saboda bayanta da hannunta sun rik'e mata kuma daman ba wani kwari ne da ita ba.

"Areef shiga toilet d'in yayi ya sa hannu ya dauketa cak kamar yar Baby ya fito da ita, Nadrah kuwa kukanta kawai ta keyi."

Zaunar da ita yayi akan bed towel d'in ta ya kunce daga kirjinta take fara raren nonuwanta suka baiyana a tsaye suke cak sai shyning sukeyi bulbul dasu.

Areef kasa dauke idonshi yayi akan su ji yake kamar yakai hannunshi ya tab'a su don tunda yake wllh bai tab'a ganin nonuwa masu kyau kamar nata ba.

Nadrah kuwa ganin ya zuba ma kirjinta ido yasa ta kalla ashe towel d'in ne ya zame bata sani ba azaba kawai ya isheta.

"Ganin baza ta iya d'aurawa ba yasa tasa d'ayan hannunta ta d'aga towel d'in sama ta rufe nonuwanta, sai a sannan Areef ya kalleta ya ce ""Ke meye haka kuma""."

Banza kallo ta watsa mishi gashi har lokacin hawaye ne yake zubowa a idonta.

"Areef ya ce ""Sauke towel d'in"" da mamaki take kallonshi ta ce ""Kamarya ma sauke towel d'in""? Areef ya ce ""Yaza ai ina kallon abu kizo ki rufe min"" Nadrah ta ce ""TV ne daman""?"

Hannu ya sa ya fisge towel d'in gaba d'aya Nadrah ihu zatai da sauri yasa bakinshi ya rufe bakinta dashi ya hau tsotsan lips dinta.

"Fisge kanta tayi da karfi ta ce ""Dalla malam barni kazo kana wani tsotsan min leb'e da kazamin bakinka a wurin"" tasa d'ayan hannunta ta goge bakinta tana sakin tsaki mtswww sannan ta jawo blanket d'in dake kan bed d'in ta rufe jikinta, ta ce "" Don Allah kafita a d'akin nan."

"Areef murmushi yayi ganin yadda take kyamar shi sannan ya ce ""Hmm ke har kin ma isa ki bani umarni nine nan wanda zai baki umurni ba keba kuma dole ki bi saboda"

"ke yanzun Matata ce akarkashi na kike, kuma da kiki cewa kazamin bakina na tabba kaf mazan da kike bi ba wanda yakaini dadin baki""."

"Nadrah tasa hannu ta goge hawayen fuskanta ta ce ""Allah ya kyauta na zama matarka kuma ka sani wllh bazan tab'a zaman aure da Kai ba don bana kaunanka balle kaunar ganin mummunar fuskarnan taka na tsaneka da kuma auren da kake ikirari akaina""."

"Areef ya ce ""Kamar yadda kika tsane ni nima haka natsaneki ko fiye da yadda kika tsane nima kodan nayi maganin rashin kunyar nan taki dole nayi zaman aur... Nadrah saurin dakatar da shi tayi don batasan ko maganar auren ta ce "" Malam ka isheni da surutu a kunnena ka fitamin a d'akin don baka da ikon da zaka hanani abinda nayi ninya."

Areef da mamaki ya kalli Nadrah don abinda take mishi ba macce da tatab'a yin mishi har yana magana ta dakatar dashi.

"Areef ya ce ""Shikenan zan fita amman karki d'auka cewa na kyaleki ne don wllh gobe zan nuna miki ikon da nake dashi akanki""."

"Yana gama fadin haka ya fita a dakin zuciyarshi tana zafi da abinda Nadrah tai mishi, yaci sa'a ba kowa a parlour ya fita daga cikin gidan."

"Nadrah ta ce ""Aikin banza kawai ni an hadani da jarababben mutun maye kawai taya zanyi zaman aure da wannan mutumin"", tasa hannu ta kuma share wasu hawayen da suka zubo mata"", sannan ta kwala ma Nafisa kira akan tazo ta temaka mata don Hannunta da bayanta azaba yake mata baza ta iya shirya kan taba."

"Areef kuwa da kyer ya isa gida saboda yadda zuciyarshi ke mishi zafi, koda ya shiga gidan yai parking motanshi ko murfin bai gama rufewa ba bodyguard ne suka rufe mishi motan suna mishi sannu da zuwa ko kallon su baiyi ba ya nufa part d'in Granny."

"Granny tana zaune a parlonta tana kallon wa'azi malam Aminu daurawa, kawai taga Areef ya fad'o mata daki ko sallama Babu don tsoro ya bata ma, Harara ta watsa mishi ta ce ""To Dan banza yaro fita min a d'aki""."

Shafa suman kanshi yayi yana furzar da iska ya fita don yasan baza ta kulashi saboda baiyi sallama ba.

"Ciki ciki yai sallaman baijira ta amsa ba ya kuma shigowa, Granny ta ce ""Wllh Areefu kacika taurin kai baza ka bari na baka izini ba zaka kuma fadomin d'aki."

"Areef ya ce ""Don Allah kiyi shiru ke tsohuwan nan kin cika kwazala da yawa"" ya nema kujera kusa da ita ya zauna."

"Granny ta ce ""Naji ai kadai dinne dole sai ana maka haka, ba wannan ba ni fadamin me ya kawo ka d'akina ma don nasan haka kawai taka bazai kawo ka ba."

"Areef ya kuma shafa yalwataccen gashin kanshi ya ce ""Granny daman zan fad'a miki gobe nake son a d'auko min yarinyar nan""."

"Granny ta ce ""Wata yarinyar kenan""? Areef ya ce ""Wacce kuka lik'amin mana"" ya fad'a yana turo baki kaman k'aramin yaro."

"Granny ta ce ""Kaini ban gane ba kaimin bayani Dalla dalla ko katashi

Please Login or Register in order to submit comment