You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itace Amaryar, sosai take samun kulawa wurin Areef dasu Ammie kowa na gidan yana bak'in k'okarinsa wurin kulawa da Nadrah, ko tsinke ba abarinta ta dauka ga wani kauna da Ammie take nuna mata kamar yarta na cikinta komai masha Allahu kam."

"Yasir ya saki jiki sosai kuma yana k'okarin wajen mantawa da Nadrah sai dai tun ranar basu sake had'uwa ba shima bai k'ara zuwa gidan bama, kawai yana ta shiryen shiryen bakin shi ne, daman Abbanshi ya bashi dank'areren gida anan Abuja ba nisa da gidansu Nadrah, inda zasu zauna mussanma yasa a gina mishi gidan domin Yasir dinshi don shikadai ne namiji a wurinsa sauran hud'un duk mata ne mata uku"

yayyansane daya kuma k'anwarsa ce sosai suka fara had'a kayan lefen na gani na fad'a.

"Areef kuma Daddy ya dank'a mishi dukkan companynshi, shizai cigaba da kulawa da komai na companyn, Areef ba yadda beyi da Nadrah su koma saboda gidansu ba, ita kam fafur taki ta ce ya bari ta haihu sai su koma ba yadda ya iya haka ya hakura yaci gaba da biye mata, kullun cikin more junansu suke sai dai yana binta a hankali wajen harka saboda k'aramin cikinta karya samu matsala."

"Jamcy gaba d'aya ta gama haukacewa da neman Areef a waya bata samunshi yau ta shirya ta ce ""Wllh komeye zai faru sai dai ya faru amman wllh sai tazo gidansu."

************

Areef yana rungume da Nadrah a jikinshi yana bata Kisses tako ina a jikinta tana kare lafewa a jikinshi kamar karsu rabu daman ta rakoshi ne bakin wurin motarshi da yake zata wuce part d'in Umma ne wurin Nafisa shiyasa.

"Horn sukaji Areef ya tsaya da kissing d'in Nadrah da ya keyi yaga waye, amman har lokacin tana jikinshi bai saketa ba, gate man ne ya bud'e gate d'in, idon Areef ya sauka akan motan Jamcy da sauri Areef ya ce ""Baba Isa me gadi karka bari ta shigo gidan nan"", da sauri ya maida gate din ya fara rufewa kafin ya ida rufewa Jamcy tai sauri fitowa daga motanshi ta shigo gidan da gudunta."

"Areef ya bita da kallon mamaki Nadrah da take jikinshi ta zame jikinta anashi tana kallon Jamcy don baza ta tab'a mantawa da fuskanta ba, Areef ya ce ""Jamcy me ya kawo ki gidan nan kuma?"" Jamcy da idonta ya cika da kwala ganinshi rungumeta da Nadrah kamar ta shek'e don bakin ciki, ta ce ""Honey me yasa ka kujeni bana samunka a waya na kira Yasir ya ce min bashi da numbernka yanzun Kuma nasan ba gaskiya bane, kasan irin sonda nake maka kuwan ko bacci bana iyawa, bana iya cin abinshi honey don Allah ka tausayawa rayuwata ka aureni wllh zan zauna da kai koma taya ya yane idan ba kai mutuwa zanyi"" ta k'arisa maganar tana kuka tana matsowa kusa da inda suke, Nadrah wani irin bak'in Kishine kawai yake taso mata wanda ita kanta batasan tana da irin kishin ba don kishin da takeji yanzun yafi wanda taji a lokacin da suka fita da mijinta, had'e fuskayi tana bin Jamcy da wata muguwar kallon baki da hankali wllh."

Areef yama kasa cewa komai ya zuba ma Nadrah ido ganin yadda take huci hankalinshi ya tashi baya son yaga abinda zai b'ata mata rai ko kad'an.

"Jamcy ta kuma cewa ""Honey don Allah ka aure ni wllh mutuwa zanyi idan baka aure ni ba"" ta fad'a tana rik'o hannunshi, da sauri Nadrah ta d'auketa da wasu zafafan"

"maruka har biyu sai da Jamcy ta zube a k'asa Nadrah ta hau kanta ta fara kai mata duka tako ina a jikinta don wani irin mugun karfi ne yazo mata tana cewa ""Ki mutu mana shegiya karuwar banza karuwar hofi ke karuwanci naki mazan aure kike bi, mijina yafi karfinki ni kadai ce matarsa, ba abinda zaiyi dake ni na isheshi rayuwa wllh, shegiya mayya kawai yar iska Allah ya isa tsakanina dake, Areef ta rud'e k'okarin d'aga Nadrah ya keyi akan Jamcy dake ta faman ihu tana Honey kate maka min matarka zata kasheni, aikon Nadrah ta k'ara hassala yadda take kiran mijinta da honey agaban ta dinga nausan bakinta take ya fashe ya fara jini hakan baisa ta kyale bakin ba taci gaba da dukan bakin."

"Areef yayi yayi ya d'aga Nadrah a jikin Jamcy amman ya kasa saboda wani irin karfi Nadrah takeji dashi, su Granny ne suka fito da gudu jin ihun a compound Ammie ma fitowa tayi da sauri, suna kallon abun mamaki yadda Nadrah ta dage sai duka take kai mata tako ina."

"Areef ganin Nadrah zata iya hallaka Jamcy ita kuma ga k'aramin ciki a jikinta karya samu matsala ya daga mata tsawa ""Nace ki rabu da ita ko Zawja"" Nadrah tsawan har cikin zuciyarta taji ba k'aramin tsorata ta yayiba , da sauri ta sakin Jamcy ta tashi a kanta tana huci wasu zafafan hawaye suna zubo mata, ta ce ""Ai nasani saboda karna kashe maka karuwarka dole kaimin tsawa saboda ita, kuma wllh muddin zaka aureta d'in wllh saika sakeni bazan zauna da kishiya ba"", tana gama fad'in haka ta tafi part d'in Umma da gudu tana kuka maicin rai tare dajin haushi Areef din, Nafisa tabi bayanta itama da gudun, Areef dafe kanshi yayi saboda wani irin sara mishi da yayi, yasan bak'in kishi ke damun Nadrah, furzar da iska yayi mai zafi Granny ta ce ""Yau kuma iskanci har gida akazo yin mana Jamcy da taci bugu sai kuka takeyi ta kasa cewa komai, saboda bakinta ba k'aramin azaba yake mata ba bazama ta iya motsashi ba, Ammie ta ce ""Areef wacece wannan da gaske karuwar kace kamar yarda matarka ta fad'a."

"Areef shiru yayi ya kasa cewa komai ga kunya ya isheshi, ganin shirun da yai mata ne Ammie ta ce ""Kenan da gaskene, uban me ya kawota gidan nan ma?"" Granny ta ce ""Yanzun ba wannan ba kar tazo ta mutun mana a gida mu rasa yadda zatayi ga Wazeeru baya nan, Areef ka d'auketa ka kaita asibiti gaskiya"", Areef cikin murya k'asa k'asa ya ce ""Granny bazan iya ba zansa bodyguard su d'auketa sukaita asibitin, ya kira wani a cikin bodyguard d'in gida ya ce kukaita asibiti"", yana fad'in haka ya nufa part d'in Umma."

"Da sauri Granny tasha gabanshi ta ce ""Ba inda zaka kabarta ta huta"" Areef ya ce ""Don Allah Granny ki barni naje na lallasheta kuma na fahimtar da ita"" Granny ta ce ""Banda fahimtar da tayi yanzun wllh baza ka ganta ba, Umma ta ce ""D'ana Areef kaje yanzun fushi ta keyi kayi magana da ita anjima lokacin ta sauka kaji"", Areef ya ce ""Tom kamar ya fashe da kuka burinshi kawai yaga Nadrah kusa dashi shafa suman kanshi yayi ya kalli Ammie da ta ke baza mishi harara, ta ce ""Wllh kaji kunya Areef"", tana gama fad'in haka tabar wajen ta koma parlorn."

"Su Granny tuni sun bar wajen, hannunshi yasa ya shafa fuskanshi hawaye yaji sun zubo mishi bai tabajin dana sanin hulda da matan da yayi a baya ba sai yau, yadda Nadrah tai fushi bai masan taya zai fara lallashinta ba don Nadrah akwai taurin zuciya, a hankali ya ce ""Allah ka yefemin abinda na aikata, sannan ya koma cikin parlorn don bazai iya zuwa office ba."

"Nadrah sosai take kuka, da kyer su Granny suka lallabata tai shiru saboda halin da take ciki."

*************

"Abu kamar wasa kwana biyu Areef baisa Nadrah a idonshi ba gashi yaune daurin auren Nafisa da Yasir, gaba d'aya Areef ya shiga tashin hankali har bak'in yayi ga rama ba abinda yake sawa a cikinshi sai coffe, ko da yaje ya samu Ammie yai ta mata kuka yana rok'anta akan taje tab'a ma Nadrah hakuri amman Ammie ta ce baza taje ba girmanta ya zube yaje da kanshi ita kam ba ruwanta a cikin al'amarinsu."

"Granny ma tayi fafur ta ce ""Baza ta shiga al'amarin ba"" Umma ce kawai ke tausasa mishi zuciya taita bashi hakuri, ko yaje part d'in kulle dakin dakeyi tak'i fitowa har sai ya gaji da zamanshi ya tashi ya fita."

"Nadrah ita kanta tana cikin damuwa sosai na rashinshi kusa da ita, domin tasaba dashi sabo mai matukar gaske, dakyer take iya bacci itama abincin kam don ma cikin jikinta akwai sa cin abinci da baza ta dinga cin abincin ba, tana matukar buk'atar shi kawai dauri ta keyi dajin haushin a cikin ranta, su Granny ma ba wanda yai mata magana akan Areef din sun kyaleta ne kawai suga iya gudun ruwanta."

"Areef wanka yayi ya shirya cikin farar shadda mai d'aukan idanu, hular baki ne sai sandal d'inshi baki ne shima, duk da yayi baki ya rame bai hana kyawunshi fitowa ba, sai baza k'amshi ya keyi kamar shine angon."

"Koda ya sakko k'asa Ammie ya samu zaune a parlorn tana kallo, zama yayi kusa da ita ya kwantar da kanshi a kafad'arta ba tare da ya ce mata komai ba."

Ammie tasauyin Areef ya kamata barinma da taga yadda ya rame amman ko meye shi yaja ma kanshi ai.

"Areef ya ce ""Ammie don Allah ki tausayi min ki bata hakuri ta saura reni wllh Ammie bana iya bacci"" Ammie ta ce ""Areef kaje ka bata hakuri da kanka zaifi idan ta hakura shikenan"", Areef ya ce ""Ammie ko naje part d'in Umma bana ganinta kulle kanta ta keyi a cikin d'akin don karta had'u dani"" ya fad'a murmushi na rawa Ammie ta shafa kanshi ta ce ""Karka damu my Son sai kace ba namiji ba mace duk ta rikita maka lissafinka."

Yanzun kaje nasan zata saura reka insha Allahu ka dage zuciyarka kaji my Son Ina maka fatan alkhairi.

"Areef ya ce ""Tom Ammie nagode"" sannan ya tashi yana gyara kayan jikinshi ya fita a d'akin."

"D'akin Umma ya wuce duk da akwai wasu mata a part d'in ba ruwanshi ya shiga ciki da sallama kowa ya amsa, Nadrah dake zaune suna hira da ita, taci kwalliya itama cikin wata farar lace ba k'aramin kyau tai ba, yadda kasan itace Amaryar tasha gold sai shinny ya keyi a jikinta da d'aukan ido, gaidasu yayi bai jira sun amsa ba sannan ya shiga bedroom d'in Umma ko kunya babu, wata ta ce ""To kitashi kije mana kila mijin naki yana son magana da kene"" Nadrah kamar baza tatashi ba ta mik'e tsaye batason mutanen su gane basa shirine shiyasa."

"Shiga tayi tana had'e fuska kamar wacce bata tab'a dariya ba, da sauri Areef yasa hannun ya rufe k'ofar ya janyota jikinshi ya matseta gam a kirjinshi jikinshi har rawa yakeyi."

"A tare suka sauke ajiyar zuciya sai dai na Nadrah baifito fili ba, Areef ya ce ""Zawja me yasa kikeson hukun tani haka bazan iya ba wllh inkina cigaba da fushi dani mutuwa zanyi Zawja don Allah ki barni haka ko bacci bana iyawa buddin banji duminki ba"", ya fad'a yana kara matseta a jikinshi Nadrah ta ce ""Ni ka sakeni bana so kaga akwai mutane karki suyi tunanin wani Abu"" Areef ya ce ""Sai mene idan sunyi naga ke matata ce?"" Nadrah ta d'ago da kanta ta ballara mishi harara sai sannan taga ramar da yayi da bak'in da yayi."

"K'asa tai da kai da sauri Areef yasa hannu ya d'ago kanta ya ce""Baby kinyi kyau sosai kamar na lashe ki amman na lura baga d'aya bakya tausayina ko?"" Nadrah banza dashi tayi saboda wani yanayi da takeji yadda yake k'ara matseta a jikinshi, Areef da sauri yakai bakinshi saitin nata ya fara bata wani hot kisses mai kashe jiki."

"Nadrah kasa jurewa tayi ta fara maida mishi da martani, don ba k'aramin missing d'inshi tayi ba itama."

"Hannunshi yake kokarin kaiwa saman nononta, nocking k'ofar akayi da sauri"

"Nadrah ta kwace jikinta anashi ta gyara kanta tana sauke nishi a hankali ta bud'e k'ofar, Granny ce don taga shigowar Areef koda ta shigo d'akin akace ai ya d'auki matarshi suna cikin bedroom shiyasa ta buga d'akin."

"Nadrah k'asa tai da kai saboda kunya Granny, Granny ta ce ""Kai Areefu me yake damun kane Kai bakajin kunya ne ace tana hiranta kazo ka jata cikin d'akin saboda kafi kowa son kasan cewa da matarshi, maza ka fita a dakinnan, kana nan har anfara k'okarin daurin auren, amman Abokin ango yana gida da matarshi ko kunya bakaji ba?""."

_Page 109&110_

Had'e fuska Areef yayi yana kallon yadda Nadrah ta duk'ar da kai wai ita ala dole tanajin kunyar Granny.

"Ya ce ""To waike ina ruwanki naga dai matata ce Ina da ikon yin duk abinda naga dama da ita ko a gabanki ne""."

"Granny ta rik'e baki tana na shiga uku ni Hajjo naga lukutin masifa ni kake gayawa haka Areef?""."

"Nadrah ganin haka da sauri ta kauda kai cike da kunya ita tarasa dalili me yasa bashi da kunya ne, Granny ta ce ""Ke kuma kina wani sinne kai maza kizo kibi mijinki ku tafi don wllh bazan iya ba karda na k'ara ganinki a part d'ina ko na Umma tunda rashin kunya za ku dingayi"", Areef dad'i ne ya kamashi Jin abinda Granny ta ce, Nadrah kuwa had'e fuska tayi."

Fita yayi ba tare da ya ce da Granny komai ba don lokacin yana wucewa da sauri ya fita a d'akin ko kallon matan parlorn beyi ba ya fita abinshi suko sai binsa da kallo sukeyi.

"Nadrah itama ta fito a d'akin tana sinne kai ta fita a d'akin da sauri dariya sukai mata kawai, suna mamaki rashin hak'urin Areef ne akan matarshi."

Nadrah direct part d'in Umma ta wuce nan tasamu Nafisa da Maman Shahid suna zaune Maman Shahid na mata hud'u bar zaman aure zama tayi itama iya da ita.

Karfe 1:30pm aka daura Auren Yasir Usman da Nafisa Abubakar masha Allahu Yasir ya dan saki fuska kamar yadda ko wani ango yakeyi ranar aurensa Alhamdulillah.

"Mommah ce zaune a cell sai kuka take tun ranar da aka kawosu ba wanda yazo ya kuma dubasu, ta rame tayi baki kamar ba Asmee ba ko kyan gani bata dashi, domin ba a basu abinci sai angadama tayi kukan bak'in ciki jitake kamar ta had'iye zuciya ta mutu ko zata huta da bak'in cikin rayuwar gaba d'aya, tayi da nasani yafi sau kwando dubu, gashi gobe za akaisu court a yanke musu hukuncin abinda suka aikata."

"Areef bayan an d'aura aure ya janyo yasir gefe sannan ya fad'a mishi abinda ya faru don basu samu sunyi magana akai ba daman, ya fad'a mishi gobe ne za ai zaman court a yanke ma sirikarshi hukunci dole ya rungumi matarshi hannu biyu kuma ya lallasheta tunda kumin lalacewar uwa uwace dai dole za taji ba dad'i ko yanzun yana ganin dauriyarta da tauwakkalinta, Yasir abin ya bashi mamaki sosai ba kad'an ba sai yaji tausayin Nafisan ya mamaye zuciyarshi, sannan suka nufa gida a hanya suna kara tattaunawa kan Al'amarin."

"Nafisa tanajin andaura mata aure Mommah kawai ta fad'o mata a rai don batasan tayi aure ba, inda ace itadin uwa ta gari ne a gareta da tuni tafi kowa farin ciki a wannan ranar to batai sa'ar uwa ba, wasu hawaye ne suka zubo mata Nadrah ta dafatan ta ce ""Nafisa lafiya?"" Nafisa murmushi tayi mai had'e da kuka ta fad'a jikin Nadrah ta fashe da kuka ta ce ""Anty Nadrah Mommah na"" Nadrah tausayin Nafisa ne yaka mata tasa hannu ta rungumota itama sosai a jikinta, ba tare da ta ce mata komai ba tana shafa bayanta a hankali cike da rarrashinta, Maman Shahid batace komai ba tausayin Nafisa ne sosai a cikin zuciyarta ace bakai sa'ar uwa ba ai akwai matsala gaskiya."

Sai da Nafisa tasha kukanta ta k'oshi sannan Nadrah da Maman Shahid suka lallasheta da kalamai masu dad'i suka nuna mata kowa da nashi kalar nashi kaddarar a rayuwarsa.

Aranar dai Nafisa bata tare a gidan Yasir don Granny ta ce Idan an gama shari'a gaba d'aya sai ta tare tunda gobene za ai shari'an jibi sai ta tare Yasir bai damu ba ko a jikinshi ya ce ba komai kam.

"Nadrah da daddare ba yadda ta iya su Granny suka koreta d'akinta, badon taso ba ta tafi tana had'e fuska, Areef yasan za ai haka shiyasa shima ko ne manta beyi ba shima yau yasan zaiji duminta."

"Ya na zaune a parlorn yasa sleep dress d'inshi sai baza k'amshi ya keyi yana shan coffee a hankali, don ya ce sai yai mata abinda da kanta zata ne meshi."

"A hankali ta bud'e k'ofar parlorn ta shiga, karaf suka had'a ido da Areef da sauri ta kauda kai ta kuma had'e fuskanta, zata wuce ta gabanshi da sauri ya sa hannu ya rik'ota ya zaunar da ita akan cinyarshi tana son kwacewa ta kasa, a hankali yasa hannunshi ya cusa a rigarta ya d'aura a cikinta ya fara shafawa zuwa kirjinta cike da salon jan hankali a hankali ya cusa wuyanshi a nata yana sauke mata wani zazzafan nishi, lumshe ido tayi don wllh ita kanta a matse take da mijinta amman idan ta tuna da Jamcy sai ranta ya k'ara b'aci k'okarin zafe jikinta tayi saboda yadda jikinta ya fara mutuwa kara rik'e k'ugunta yayi yana cigaba da abinda ya keyin mata."

"Hannunshi yasa ya d'auketa cak ya wuce da ita bedroom ya kwantar da ita akan bed tana k'okarin tashi da sauri ya hau kanta yai mata runfa da kirjinshin har lokacin baice mata komai ba ita ta ce ""Ni ka kyaleni ba abinda zaka samu tunda kai baka damu dani ba jikina kawai kake so ba ni kake so ba, banza da ita yayi yai sauri had'e bakinshi da nata ya shiga kissing d'in lips dinta a hankali hannunshi yana saman nononta yana murzasu a hankali."

Nadrah batasan lokacin da itama ta cafke bakinshi ba ta fara tsotsa jikinta har rawa ya keyi.

Hannunshi yasa ya barke rigar jikinta daman bata da nauyi ne don tayi shirin bacci ne daman Granny ta korata.

"Bakinshi ya Kai saman nononta yana tsotsa a hankali nishi dad'i ta saki tana kara k'ankameshi a jikinta, sosai yake sha mata nononta har zuwa wuyanta yana lashewa."

"Areef sai da ya gama gigita Nadrah da salon romancing dinshi, yasan cewa baza ta tab'a jurewa ba, sannan ya zame jikinshi a nata ya shiga toilet ya barta, yasan cewa shima a matukar buk'ace yake da ita amman bazaiyi komai da ita ba itama taji abinda ya ji lolacin da ta gudu ta barshi."

"Nadrah ganin Areef ya sauka akanta beyi komai ba da ita ba, ta matse kafarta saboda wani irin azaban feeling ki taso mata, runtse ido tayi a zuciyarta ta ce to me yake nufi ya tada min sha'awa kuma ya barni, mirginawa tayi tai ruf da cikin ta kuma runtse idonta ta dafe mararta data kunbura tana had'e jikinta waje d'aya."

"Areef wanka yayi ya fito ya canza wani kayan baccin saboda ya bata wancan ya busar da gashin kanshi, ya kuma feshe jikinshi da turaren masu k'amshi, ko kallan inda take beyi ba, itama kuma tunda ya fito daga toilet ta kura mishi ido tana binshi da ido jitake kamar tasa hannu ta janyoshi kanta, ganin zai jiyo tai saurin shigar da kanta cikin duvet tana matse kafarta ga mararta data rik'e mata wllh ji take idan Areef bai kusan ceta wllh kila mutuwa za tayi gashi shi kuma kota ita ba yayi."

"Kashe wutar d'akin yayi sannan ya hau kan bed ya kwanta nesa da ita tanajin ya ja blanket d'in shima rufe kanshi, Nadrah runtse ido tayi a zuciyarta tana tunanin to meyasa sai da ya tada mata sha'a sannan kuma zai barta, sai da suka kusan 30 minutes amman ko kulata beyi ba, kawai ta fashe da kuka saboda yadda mararta ta kuma juya mata, yana jinta yai banza da ita, ko motsi beyi ba balle tasan ba bacci ya fara ba, shi kanshi dauri kawai ya keyi."

"Nadrah ganin fa bazai kulata ba da sauri ta mirgina kusa dashi ta kwantar da kirjinta a bayanshi tana goga mishi nonuwanta, runtse ido Areef yayi saboda yadda yajishi har tsakiyar kanshi amman hakan baisa yayi motsi ba."

"Hannunta ta d'aura a kirjinshi tana shafawa burinta kawai taji Ayaba cikin kankana, amman Areef yak'i kulata a hankali Areef ya mik'e zaune ya kalleta ya ce ""Baby what's happened?"" K'asa tai da kai ta fashe kuka tana kamo hannunshi ta d'aura a kirjinta ba tare da tace komai ba, gashi kukanta har cikin zuciyarshi Areef yake jinshi."

"Zame hannunshi yayi a kirjinshi data d'aura ya ce ""Baby am so sorry, naga kamar kina tunanin jikinki kawai nake so shi yasa naji bazan iya kusantarki ba kiya hak'uri amman ina sonki sosai fiye da komai a duniyar nan zawja amman ke kin kasa ganewa, haka ki ka tafi ki ka barni kinyi tunanin halin da zanshiga idan ban kasance da ke ba? Amman hakan baisa kin dawo ba sai da aka matsanta miki ki dawo d'in ni mutunne mai yawan buk'atar mace kin san haka kika barni a ko da yaushe feeling d'inki kamar zai kasheni akanki, ki fad'a min idan kin gaji dani ne sai na auro wata wacce zata dinga dauke duka buk'atata, amman ba akan kuskure kad'an kiyi fushi ki tafi kiyi nesa dani ba, Zauja kece ma wacce zance anya kina sona kuwa inda kina sona baza ki tafi ki barni ba"", ya fad'a yana komawa ya kwanta da sauri Nadrah ta shige jikinshi tana kuka ta ce ""Pls Zauji kaya hakuri wllh Kishine yasa nai haka nima ina sonka sosai wllh Kishi ne yasa na aikata haka kaya hakuri bazan sake barin ka ba kayi duk abinda kake so kayi dani wllh a shirye nake pls Zauji ta fad'a tana shigewa jikinshi ga wani feeling dake addabanta."

"Murmushi yayi sannan ya gimtse fuska ya zame jikinshi a nata ya ce ""Shikenan duk lokacin da kike buk'atana sai ne meni na baki izinin ki koma wurin su Umma har zuwa lokacin da zaki huce fushinki a kaina Zauja"" yana gama fad'in haka ya koma ya kwanta abinshi yanajin ba dad'i."

"Nadrah kuka ta saki tana rik'e shi ta ce ""Zauji kaya hakuri bazan sake ba ka yafemin please, wllh kishi yasa nai haka forgive me Zauji"", kuka take sosai Areef kasa jure kukanta yayi don har cikin zuciyarshi yake jin kukanta a hankali ya tashi ya ce ""Zo nan"" da sauri ta shige jikinshi tana kuma fashewa da kuka a hankali ya ce ""Kiyi shiru toh Shiiiii yana bubbuga bayanta, Nadrah ta d'ago kanta a kirjinshi ta ce ""Zaujinah ka yafemin?"" Halcenta yasa ya lashe hawayen da suke zubo mata ya ce ""Ni baki min komai ba Zaujanah kuma ya wuce""."

Da sauri Nadrah ta had'e bakinshi da nashi ta fara bashi hot kisses kasa jurewa yayi ya fara maida mata mar tani tana k'ara shigewa jikinshi.

Da asuba ma sai da suka more junansu sannan sukai bacci mai dad'i.

"Karfe 10:17am Nadrah suka shirya tsaf sunyi kyau sosai Areef cikin wata had'adiyar shadda sai shinny ta keyi white color yayi kyau sosai Nadrah cikin wata doguwar rigar abaya tayi rolling d'an kwalin akanta sunyi kyau sosai, Ammi tayi farin cikin ganin sun koma yadda suke a da gaida ita sukayi ta amsa cikin farin ciki sannan ta ce ""Muje tun d'azun su Granny suna jiranmu kusan 11:00am ne zaman court din fa"" Areef ya kamo hannun Nadrah ko kunyi Ammie bai jiba ya ce ""Muje Ammie""."

"Sannan suka fito a parlorn a compound d'in gidan suka had'u dasu Granny Nafisa da sauri ta fad'a jikin Nadrah ta rungumeta sannan suka shiga mota dukkansu, Nadrah da Nafisa sai little dake gaba suna motan Areef, Granny da Umma da Ammie kuma suna"

"motan Daddy sannan suka fita a gidan, a hanya Areef yake waya da Yasir akan cewa su had'u a court kawai."

"Suna isa babban court dake garin Abuja sukai parking motansu suka fito, dai dai lokacin motan su Mommah yana k'arisowa cikin court d'in."

"Motar parking tayi kusa dasu, akan fito da Mommah daure da handcuffs kamar ba ita ba sai Alhaji Sabitu shima ya rame yayi baki sosai kamar bashi ba gaba d'aya sun fita hayyacinsu, Nafisa da sauri ta runtse idonta don baza ta jure kallon Mommah haka ba tai k'asa da kanta Nadrah kauda kai tayi ba tare da ta kalli inda take ba don idan akwai wacce ta tsana a duniya Mommah ce, kawai tana rage tsanar da take mata ne bata nunawa saboda k'anwarta Nafisa."

"Mommah sai kallonsu takeyi tana kuka gashi tana

Please Login or Register in order to submit comment