You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'an iskan yaro kawai."

"Areef ya ce ""Granny Wai meye a auren nan ne nifa bazanyi ba, Granny ta ce ""Kar kayi wllh sai mun maka auren dole kana ganin wasa ne k'aton gardi dakai amman ace ba aure tom baka isa ba, don kaga babarka tana biye maka ko bara Wazeer yazo aishi na isa dashi zai yi abinda nake so"", da d'an saurinta ta shige part d'inta, don karma yai mata iskanci da ya saba."

"Areef kuwan dariya ya yi ya ce ""Kenan ni za ai auren dole sai kace a film lallai Granny rikicin tsufa ya fara tab'a ta""."

"A haka ya haura upstairs da sauri don yazo d'aukan abune bazai dad'e ba yana son komawa da wuri ne don zuciyarshi tana fad'a mishi, ita da Dr. Zasu iya yin wani abu."

Da sauri sauri ya shiga d'akin ya d'au abinda zai d'auka ya fito a d'akin.

"Karo yayi da little a k'ofa d'akin, kallonta yayi y ce ""My girl menene? Little marairai ce k'aramin fuskanta ta yi ta ce ""Ya Areef zan bika muje tare, Areef ya ce ""A'ah little ba yanzun ba ki bari gobe saina tafi dake."

"Little ta ce ""Nifa saina bika pls Ya Areef"", Areef ganin tana son b'ata mishi shiri ya ce ""Little nace bazani da ke ba Koh""."

"Ko kallonta be k'arayi ba ya tafi ya barta tana shagwab'e fuska, da sauri ya sauka downstairs harda had'awa da gudu gudu."

"Ammi ce ta ce ""Areef ya kake sauri haka ne ya maganar wancan yar iskan yarinyar""? Areef ya ce ""Pls Ammi kibar maganarta baki da matsala akanta, yanzun Yasir ke jirana zamu fita idan nadawo zan zo har part d'inki"", bai jira tai magana ba ya fita da sauri yana bye Ammi""."

"Ammi girgiza kai ta yi ta ce ""Oh my Son"", sannan ta koma ta zauna."

Areef kuwa inda akai parking motocin gidan ya nufa ya d'auki wani daga cikin tsadaddun motan ba wanda ya dawo dashi ba ya shiga yabar gidan da sauri.

Wani k'atan shopping mall ya nufa yana shiga ya fara diban mata kayan sawanta duk English wear ne masu kyau da tsada bana arzik'i a ciki.

"Koda ya gama ya biya kud'i sannan yasa akai mishi motanshi, ya shiga ya tada yabar waje."

"Wani k'atan restaurant me masifar tsada da d'aukan ido ya shiga deluna restaurant kenan, abinci ya siya masu tsada da dadi harda su shawarma da pizza da gashasun kaza guda biyu, shima yasa akai mishi motanshi ya biya kud'in sannan ya fito daga wurin, ya kama hanyar gidansa."

*******

"Mommah kuwa dakyer suka k'arisa gida sai kuka ta keyi wai ita sai ankawo mata Nadrahta ba inda zata je, da kyer Maman Shahid da Nafisa suka lallab'ata suka tafi gidan."

"Mommah da Nafisa sai kuka su keyi Maman Shahid ke tabasu hak'uri da kalamai masu dad'i ta ce ""Maman Nadrah kiya hak'uri insha allahu Nadrah zata dawo karya su keyi zata dawo tana wurinsu wllh kawai basa son muganta ne."

"Mommah ta ce ""Ni dai Maman Shahid don Allah mu koma kila zasu barmu muganta yanzun""."

"Maman Shahid ta ce ""Don Allah Maman Nafisa mu kyalesu nasan duk abinsu baza su kashe taba kuma Allah yana bayan mai gaskiya indai batai musu komai ba suka kamata Allah zai saka mata kodan abinda sukai mana insha allahu""."

"Mommah ta ce ""Maman Shahid ni nasan halin y'ata wllh batai musu komai ba kawai mugunta ce irin na masu kud'in nan, yanzun haka zamuyi ta zuba musu ido suna cutar min da y'ata muna kallo"", Maman Shahid ta ce ""Kiya hak'uri mubar ma allah komai kawai muyi ta mata addu'a kafin Baban Shahid ya dawo musan abinyi"", da kyer Maman Shahid ta lalla basu sukaci abinci daman sun girka harsu na tafiyan ma Nadrah dashi."

******

"Dr. Anwar kuwan yana zaune ya zuba ma Nadrah ido, yana jin wani abu na taso mishi tunda ga kan yatsin k'afanshi."

"Yayi k'ok'arin controlling kanshi amman ya kasa, lumshe ido yayi sannan yakai hannunshi cikin blanket d'in da ta rufe kanta dashi, saman cikinta ya kai hannu ya fara shafawa a hankali har zuwa saman breast d'inta."

"Nadrah duk da baccin da yai nauyi ah idonta baisa ta kasa bud'ewa ba, a lokacin kuma ta faraji k'arfin jikinta, ganin Dr. ne yasa da sauri ta ture hannunshi ta matsa gefe, Dr. Anwar ya ce ""Ba kina son na tema keki ba, Nadrah banza dashi tana watsa mishi kallon tsana da takaici."

"Dr. Ya ce ""Ki bari kawai muji dad'in mu na miki alkhawari muna gamawa zan barki ki tafi don nasan Areef bazai barki ki tafi ba, shima ba tare da ya samu wani abu a gare ki ba."

"So daya kawai zanyi ni da kaina zan d'auke ki mubar wurin nan, Nadrah kauda kai tayi a hankali ta ce ""Bana buk'atan temakon naka yanzun daman mutane ba abin yarda bane""."

"Dr. Anwar ganin zata b'ata mishi lokaci kuma yasan Areef zai iya dawowa a koda yaushe, da sauri ya haura saman gadon Nadrah ganin d'an iskan nan da gaske yake ta fara kici niyar guduwa, da sauri yakai mata damk'a yana son had'e bakinta da nashi da sauri ta gantsara mishi cizo a lips d'inshi, ihu azaba ya saki ita kuma ta na k'ok'arin guduwa ta manta akwai drip a hannun sai da taji kamar abu na d'iga dubawa ta yi taga jini ne da sauri tasa hannu ta fisge drip d'in ta d'auki hijab d'inta, ta fita a bedroom din da d'an sauri tana d'ingishi."

Dr. Anwar biyota yayi yana ki tsaya mana wllh bazan fada ma Areef ba kuma kad'an zanyi inayi zan fitar dake daga nan wurin.

Nadrah batai aune ba taji tayi karo da mutun zata saki ihu kenan taji ya had'e bakinta da nashi k'ara rud'ewa ta yi don ta d'auka shine kuka tasaki tana son kwacewa.

"Dr. Anwar ganin Areef hankalinshi ya tashi sosai, da sauri ya ciro wayanshi ya fara daukansu video, don yasan akan ne kawai zai sa ya samu sauk'i a wurin Areef."

"Nadrah kuwan sai kiciniyar kwacewa ta keyi ta kasa saboda irin rik'on da yai mata, Areef shi yayi haka ne don kar tai ihu kuma gashi ya kasa cire bakinshi a nata."

"Dr. Anwar guduwa yaso yayi bayan ya gama musu video, da sauri Areef ya zare bakinshi a nata, zai damk'o Dr. Anwar kenan yaga jini na zuba a hannunta."

"Da sauri ya rik'ota ya ce ""Wannan jinin fa""? Dr. Anwar ganin haka ya samu ya zuba da gudu yabar Parlorn."

"Nadrah jirine ya fara d'ibanta, ta fara lumshe ido, Areef ya ce ""Karki rufe ido mana Kee ya fad'a da d'an k'arfi donshi baisan ma sunanta ba..."

"[9/21, 6:06 PM] _Page 27&28_"

"Da sauri ya d'auketa cak ya kwantar da ita akan kujera, ya d'auko wani doguwar riga mai kyau a cikin kayan da yasiya mata, ya zira mata da sauri sannan ya fara girgizata, amman ina Nadrah ko motsi ba tayi da sauri ya d'auketa cak ya fito da ita hankali a tashe, ya bud'e bayan motanshi ya saka ta sannan ya koma mazaunin driver yaja motan da gudu yabar gidan daman gateman ya bud'e mishi gate d'in."

"Dr. Anwar kuwan cikin gidan ya koma, yaga duk jinin da Nadrah ta zubar wani dubara ne ya fad'o mishi yasa hannu ya jin makanshi ciwo da spoon sannan ya koma ya k'ara d'id'iga jinin a duk inda jininta yake, sannan yai ma hannunshi dressing ya had'a kayanshi yabar gida me gadi da yake yasan da shigowanshi bai hanashi fita ya bud'e mishi gate ya fita."

"Dr. Anwar kuwan yana samu ya fita, sai da yai nisa sannan yai parking motanshi a gefen titi yana nishin, da kyer yasha."

"Wayarshi ya d'auko yaga videon da yai musu aikon yai murmushi mugunta ya du ba number Dad ya tura mishi ta WhatsApp numbernshi, sannan ya ije wayar ya cigaba da tuki yana cewa Areef zakaci ubanka ai."

******

"Areef kuwa direct asibiti ya wuce da ita, yana zuwa aka wuce da ita emergency room."

Hankalinshi ya tashi sosai a zuciyanshi yana addu'an Allah yasa dai ba mutuwa ta yi ba.

*****

"Daddy yana zaune a Parlorn Granny, don tunda ya dawo daga office tasa ai kiranshi shida Ammi."

"Granny ta ce ""Wazeeru daman akan maganar aure Areefu ne nace kai ma yaron nan aure amman kak'iji koh, Dady ya ce ""Mama kiya hak'uri nima nadan bashi lokaci ne akan yazabi duk wacce ya keso a aura mishi ita""."

"Granny ta ce ""To gashi har yanzun ba wani labarin wacce yake so din, yaro kullun sai k'ara lalacewa ya keyi tom indai baza kuyi mishi aure ba yanzun, tom ni da kaina zanje kauye nasa a d'aura mishi aure da wata mata a acan tunda abin nashi harda iskancin banza a ciki."

"Daddy ya ce ""insha allahu zan mishi maganar auren sai asan a binyi basai ankai ga hakan ba"", Ammi kuwan sai kun bura baki ta keyi tana kauda kai."

"Granny ta ce ""Da dai yafi kam, don nagaji da ganinshi a haka k'aton sauri dashi ace ba aure nima inason naga jikana kafin na koma ga mahaliccinah."

Daddy zaiyi magana kenan yaji k'ara shigowa message ta WhatsApp da kamar bazai duba ba ya shiga WhatsApp din ganin Family Dr. tansu ne Dr. Anwar ya sa ya bud'e message d'in.

"Video ya gani bud'ewa ya yi, abinda yai karo dashi shine Areef d'inshi ne rungume da wata yana mata kiss kamar zai cinye bakinta, mik'ewa yayi a zabure hannunshi na rawa, Ammi ganin haka da sauri tasa hannu ta amshi wayar tana Daddyn Areef lafiya kuwa""?"

"Kallon wayar ta yi itama take idonta ya gane mata abinda Dady ya gani tashin hankalin ma wannan shegiyar yarinyar ce, ihu ta saki tana sakin wayar a kasa."

Granny duk ta shiga rud'ani ganin yadda dukansu suka fita hayyacisu k'ariso ta yi inda suke tasa hannu ta d'aukin wayar.

"Itama abinda idonta ya gane mata kenan, ta ce ""Subhanallahi amman wannan ba Areefu na ba ne ko""? Daddy ya ce ""Granny shine wllh Dr. Anwar ya tura min yanzun nan""."

"Granny ta ce ""Kun gani ko abinda nake gudu kenan gashi ya faru tun yaushe nake cewa kuyi ma yaron nan aure tun kafin ya janyo mana abin zagi gashinan ai abinda ya faru kenan Allah kad'ai yasan wa inda ya tura wa."

"Ammi cikin b'acin rai ta ce ""Granny ni fa nasan Areef bazaiyi haka ba kawai wannan shaidaniyar yarinyar can ce taja hankalinshi yasa ya biye mata"", Daddy ya ce ""Wata yarinya ce""?"

Ammi cikin kufan baki ta kwashe labarin komai ta fad'a musu harda cewa ya kaita asibiti ne.

"Granny ta ce ""Ohoof gashi nan ai wannan ba asibiti bane gida ne, Daddy ya ce ku tsaya bara na kira Dr. Anwar muji komai tunda shi ya tura mana videon nasu."

"Daddy kiran Dr. Anwar ya yi ringing 3 yayi yai picking, Daddy ya ce ""Dr. Anwar don Allah ina kasamu videon daka turamin""?."

"Dr. Anwar ya ce ""Da kaina na d'auka Sir""."

"Daddy ya ce ""Ko zaka iya fad'amin yadda ka d'auki video mai ya faru?."

"Dr. Anwar harda gyara zama yai murmushin mugunta sannan ya ce ""Ina zaune a office naga kiran Areef da sauri na d'auka ya ce ""Dr. Kana ina ne nace mishi ina hospital d'ina, sai ya ce min don Allah kazo gidana dake unguwan rimi akwai wata yarinyar da zaka zubar ma da ciki ne, tom kuma nasan kaine kawai zaka iya don Allah kabar sirrin nan tsakani na dakai ko nawa kake so zan biya ka."

Sai na nuna mishi cewa nifa bana zubar da ciki saboda babu kyau ko kad'an haramun ne.

"Sai ya ce min dole sai nazo ko yasa na rasa aiki na gaba d'aya, ina jin haka hankali ya tashi naje gidan."

Ina zuwa ya bud'e min kofa na shiga yakaini har d'akin da yarinyar take naganta kwance ko motsi bata iyayi ashe ya kara haye mata ne duk ta gala baita waishi a dole cikin sai ya zube a haka.

"Koda na dubata naga cikin ma a halin da take ciki ya kusan zubewa kawai nai mata allura da zai k'arasa zubar da cikin yanda basai tasha wahala ba take ta fara bleeding shi kuma a lokacin ya ce min zai je gida ya d'auko abu ne nai mata duk abinda ya dashe na kula da ita don Allah""."

"Nace mishi insha allahu zanyi hakan sannan shi kuma ya fita, ni kuma na d'aura mata drip."

Bayan 1 hour ta tashi ta fara rok'ona akan natai maka mata na fitar da ita daga gidan tana kuka da nak'i saura ranta ita kuma sai kuka takeyi hakan ya kar yamin zuciya tausayinta yaka mani.

"Nace koda zan rasa aikina ne sai na tai maki yarinyar, aikon na rik'ota duk da har lokacin tana zubar da jini muka fara fitowa a hankali har zuwa Parlorn, shine muka had'u dashi shi kuma ya shigo Parlorn shine da sauri ya fisgeta a hannuna tana k'ok'arin kwacewa ne zatai mishi ihu shine ya had'e bakinshi da nata ya fara sumbatan ta shine nai musu video da kyer na samu nasha a wurinshi don kar narasa aikina yasa nace bara na tura maka videon."

"Ammi ihun kuka ta saki ta ce ""Wllh k'arya ka keyi Dr. Anwar nasan d'ana bazai ta tabamin haka ba kuma yarinyar ba wani had'i tsakaninsu illa rashin fahimta daza kace"

"har ciki yai mata wannan k'azafi ne wllh, Daddy ya d'aga mata hannu alaman tai shiru, don gaba daya kanshi ya d'aure da kyer ya ce ""Dr. Nagode don Allah karka nuna wa kowa video nan ka goge a wayarka kuma baza a koreka a aikin kaba kaji insha allahu, yanzun Areef d'in yana inane""?"

"Dr. Anwar ya ce ""Ni dai nabarsu a gidan, Daddy ya ce ""Don Allah zaka iya tura min da address d'in gidan yanzun ina son zuwa ne"", Dr. Anwar ya ce yanzun nan ma kuwa sannan ya fad'a mishi address d'in, Daddy ya k'ara mishi godiya da cewa ya goge videon don Allah sannan ya kashe wayar."

"Granny kuwa hawaye ne shab'e shab'e a fuskanta cikin dauriya ta ce ""Yanzun Areef ne zai aikata wannan muguntan da kanshi""?"

"Ammi ta ce ""Granny ki yarda da jikanki bazai tab'a aikata Abu kamar haka ba wllh Dr. Anwar sharri yake mishi wannan ba gaskiya bane."

"Daddy ya ce ""Yanzun dai mutashi mu tafi gidan kar wani abu ya samu yarinyar mutane""."

"Da sauri Ammi tatashi ta ce ""muje daman akwai mayafi a jikinta Granny ma ta ce ""Da ita za aje ba musu Daddy suka fito daga part d'in Granny, ko little basuyi ma sallama ba suka nufa parking space.."

"[9/21, 6:06 PM] : _Page 29&30_"

"Drivern gidan ne ya taso da gudu, Daddy ya ce ""Ya barshi kawai da k'anshi zaiyi tuk'i, shiga sukayi dukansu sannan Dad ya shiga wurin mazaunin driver yaja motar suka bar gidan."

Suna hanya Dr. Anwar ya tura musu address d'in gidan.

Areef kuwa gaba daya ya shiga tashin hankali kar yarinyar mutane ta mutu a hannunshi.

Duk likitan da ya fito daga d'akin sai ya tambayeshi ya take.

"After 1 hour Babban likitan asibitin ya aika yazo office d'inshi, da sauri ya nufa office d'in don burinshi kawai yaji tana raye shine hankalinshi zai kwanta."

"Yana zuwa ya fara tambayanshi ""Tana raye ne"", Dr. Dariya yai mishi sannan ya ce ""Please sit down""."

"Zama yayi yana zaro ido, Dr. Ya ce ""Tana raye ba abinda yasa meta kawai taji jikine sosai, saka makon rashin abincin a tare da ita da kuma jinin da ya zuba a hannunta da yawa shine yasa ta galabaita harta suma, amman don Allah garin ya taji raunika haka""?"

"Areef ya rasa abin cewa kawai ya ce ""Yanzun zan iya ganinta""? Dr. Ya ce ""A'ah kabarta ta d'an hutu zuwa minti 30 haka zaka iya zuwa don yanzun mun mata alluran bacci ne, ka je kasamo mata abin da zataci kafin ta farka, gyad'a kai kawai ya yi sannan ya tashi ya fita a office d'in."

*******

"Dr. Anwar kuwa tunani ya farayi tom idan su Dady su kaje asibitin suka gane k'arya na keyi fa, tunani yayi can ya d'auki wayanshi yai dailing wani Number ringing biyu yayi aka d'auka acikin wayar ya ce ""Da girman kujeranka babban likita yau ni aka kira lallai yau ina da babban sa'a"", dariya Dr. Anwar ya yi ya ce ""Daman na kira na tambayeka abune"" Dr. Mustapah Ya ce ""Ina jinka Babban likita""."

"Dr. Anwar ya ce ""Areef Wazeer nan yazo da wata yarinya asibitin ka""? Dr. Musty ya ce ""Kwarai kuwan yazo da ita don maganar da nake makama Yanzun yabar office d'ina yana fita kana kirana, wani ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce ""Wata alfarma nake son kaimin"""

"Dr. Musty ya ce ""Haba babban likita ba wani alfarma daza ka rok'a na kasa makashi ka manta kai kana sama na ne, fad'i koma meye insha allahu zan makashi."

"Dr. Anwar ya ce ""Ina son results d'in yarinyar da ya kawo kasa ta zubar da ciki komai ka maidashi akwai cikin daya fita a jikinta""."

"Dariya Dr. Musty ya yi ya ce ""Ai wannan mai sauk'i ne kamar anyi angama, nasan yadda zanji da komai my highness""."

"Godiya ya yi sannan ya ce ""Yanzun za kaji alert sannan ya kashe wayar cike da jin dad'in shirinshi yana tafiya yadda yaka mata, sannan yaja motanshi zuwa gida."

********

"Su Daddy address d'in da Dr. Anwar ya basu suka nufa, suna zuwa sukai Horn me gadi ya bud'e musu suka shiga."

"Parking su kayi suka fito daga motan Daddy ne yai gaba su Ammi a baya, suna tura k'ofan parlorn ya bud'e suka danna kansu ciki da jini suka fara karo Granny ta ce anshiga uku me zan gani ni hajjo jini ne fah, Ammi kuwa gaba d'aya ta kasa magana, Daddy ne ya fara kiran Areef amman shiru har bedroom d'in suka shiga duk jini ne akan bed d'in."

Hankalinsu duka ya tashi da sauri Daddy ya ciro wayanshi ya fara kiran Areef amman su kaji k'aran wayanshi a Parlorn suna zuwa sukaga phone d'inshi yana ringing a kan kujera.

"Ammi ta ce ""Tom ina Areef ya tafi""?, Granny ta ce ""Ba tsayuwa yaka mata muyi ba muje mu nemosu dukansu Kar wani abu ya sa mu yarinyar mutane""."

"Daddy gaba d'aya jikinshi ya mutu da al'amarin cikin sanyi murya ya ce ""Muje kawai basa nan"", sannan suka fito daga Parlorn dai dai lokacin motan Areef na shigowa gidan, shi bai ma lura dasu ba sai motan da ya gani yasan na Daddy ne d'ago kanshi yayi yaga Granny da Daddy sai Ammi da ke ta faman share hawaye."

"Da sauri ya fito daga motan ya k'ariso kusa dasu ya ce ""Daddy Ammi Granny ya akai kukazo na...bakinshi bai gama rufewa ba yaji saukan mari a kuncinshi, da mamaki ya d'ago da fuskanshi ya ga Daddy ne rai a b'ace sai huci ya keyi shidai yasan tunda yake da Daddy bai tab'a sa Hannun ya mareshi ba."

"Daddy hannu yasa zai kuma marinshi da sauri Ammi ta tareshi ta ce ""Haba Daddyn Areef baka tabbatar da al'amarin ba zaka yanke hukunci"", ta fad'a tana share hawayen fuskanta tana kuma tsine ma Nadrah a cikin zuciyarta tasan tunda take da Daddyn Areef bai tab'a nuna ma Areef d'an ya tsaba sai yau ta dalilinta har marinshi sai da yayi."

"Daddy ya ce ""Ina ka kai yar mutane? Areef ya ce ""Wace kenan?, Granny ta ce ""Yarinyar da kai ma ciki mana"", Areef kallon Granny ya yi cike da mamaki ya ce ""Ciki kuma Granny?"", Ammi ta ce ""Areef Ina mayyar yarinyar nan""."

"Areef ya ce ""Tana hospital Ammi?, Daddy ya ce ""Karya ne ya akai gidan nan duk jini ne, ka fad'a mana taya akai kaima yarinyar mutane ciki har kake son zubarwa ba tare da kowa ya sani""?."

"Areef cike da rud'ani ya ce ""Daddy nifa banyi wa kowa ciki ba da har zan zubar da ciki, me ya had'ani da mace ma da har zan mata ciki""? Daddy ya ciro wayanshi yai playing videon da Dr. Anwar ya tura mishi ya nuna mishi ya ce ""Wannan fah waye?."

"Areef mamaki ne ya ka mashi da kunya gashi sai faman tsotsan bakin mace ya keyi, da sauri ya kauda kai k'asa, Dad ya ce ""Wanene wannan toh?""."

Shiru Areef yayi yana tunanin ya akai aka d'au wannan video toh?.

"Cikin tsawa Daddy ya ce ""Areeef ba magana nake maka nace wanene a cikin video nan""?."

"Areef gyad'a kai yayi ya ce ""Daddy nine amman hakan ba asan raina bane kawai tsautsayine""."

"Daddy ya ce ""Good yanzun fad'amin Ina yarinyar take""? Areef ya ce ""Tana hospital""?"

"Granny ta ce ""Areefu da gaske Kai ma yarinya ciki""?."

"Areef cike dajin haushi maganar ya ce ""Nifa ba wacce nai ma ciki atoh""."

"Daddy ya ce ""Muje ka kaimu asibitin sai mu tabbatar da maganar naka."

"Areef baiyi musu ba ya ce ""Aje aikon kowa ya shiga mota ya jasu zuwa asibitin Barau dikko."

*******

Cikin 16 minutes suka isa hospital d'in don banisa daganan.

"Har ciki ya shiga dasu har d'akin da take, ya nuna musu ita, Daddy ya ce ""Toh ya maganar cikin da kai mata kasa a zubar har yai sanadiyar kawota asibitin""?"

"Areef ya ce ""Daddy nifa ban mata ciki ba balle har nasa a zubar kuma aje office d'in Dr. Mustapah a tambayeshi ko results kawai bata da lafiya ne sai dukan da tasha a police station sai zuban jini da tayi a hannu dalili ma nasa Dr. Anwar yai treatment d'inta tane shine yai k'ok'arin ne Daddy ya katseshi da cewa ""Ba wannan na"

tambayeka ba munsan komai kawai ka kaimu wurin Dr. Mustapah mu tabbatar da maganar ka ko muje da kanmu.

"Ammi ta ce ""Haba Daddyn Areef kabar shi yai magana mana""."

"Banza da ita Daddy yayi ya ce ""Muje Koh""."

Ba musu suka nufa office d'in Dr. Mustapah dukan su Granny kuwa sai addu'a ta keyi a zuciyarta kar hakan yazama gaskiya.

"Suna zuwa Dr. Musty yai musu mara ba yace su zauna suka zauna dukansu, gaisawa su kayi sannan Dr. Musty ya ce ""Ah Areef har ka dawo kenan""?"

"Areef ya ce ""Eh Dr. Nadawo daman results d'in yarinyar dana kawo zaka bani, Dr. Musty ya ce ""Atoh ba matsa d'azun na d'auka zaka amsa ne naga baka karb'a ba"", ya fad'a yana mik'a mishi amsa yayi ya mik'a ma Daddy."

"Daddy hannu yasa ya amsa, ya bud'e ya fara karantawa..."

"[9/21, 6:06 PM] : _Page 31&32_"

"Mik'ewa yayi cike da sauri ya saki takardar, Ganin haka Ammi itama ta d'auki takardar ta karanta kuka ta fashe dashi ta ce ""Wllh wannan sharri ake mishi ni nasan d'ana bazai aikata hakan ba daman yarinyar karuwa ce acan ta d'ebo abinta amman ba d'ana yai mata ba""."

"Areef cikin rud'ani ya amshi takardar a hannun Ammi shima ya karanta wani zufa ne ke ketomishi tako ina, kallon Dr. Mustapah ya yi cike da tuhuma ya ce ""Dr. Wannan fa""?."

"Dr. Mustapah sai da yasha jinin jikinshi saboda irin kallon da Areef ke mishi, shiru ya yi yana zare ido Areef ya ce ""Tambayarka na keyi fa""."

"Dr. Musty cikin dauriya da k'arfin hali ya ce ""Results d'in kenan da ka gana"", Areef ya ce ""Karya ne d'azun ba haka ka fad'amin ba""."

"Ka canza result ne cike da takaici ya damk'o wuyar Dr. Mustapah ya ce ""Waya saka ka rubuta haka wannan ba gaskiya bane, wani zazzafan mari Dad ya kuma d'auke Areef dashi take ya saki wuyar Dr. Mustapah gaba d'aya yau kanshi ya kulle da irin wannan bak'ar sharrin da ake kullu mai ga Daddy yau sau biyu kenan yana shan mari a wurinshi."

"Ammi ta ce ""Wai dame zaiji ne Wazeer da marin da kake mishi koda sharrin da aka kullamai""? Daddy ya ce ""Amina wannan ba sharri bane, likitoci baza su tab'a mishi sharri ba""."

"Granny ta ce ""Wazeer mutafi muduba yarinyar kar wani abu yasa meta, Dr. Mustapah ya ce ""Kaka ba komai insha allahu ta samu sauk'i ai sai dai tana buk'atar hutu ne batasan yawan surutu ko ta kura""."

"Granny ta ce ""Tom bokan tura mungode sosai""."

Sannan taja hannun Areef suka fito daga d'akin gaba d'aya Areef ya rasa meke mishi dad'i.

Ammi zatai ma Dr. Musty magana kenan Dad kamar ya sani ya janyota suka fito.

"Direct d'akin suka wuce banda Areef da Ammi don Ammi ta ce ""Baza ta shiga ba Areef kuwan wucewa yayi zai fita a hospital d'in Ammi ta ce ""Areef ina zaka""."

"Banza ya yi da ita ya wuce zata bishi Dady ya ce ""Karki fara kibarshi ya tafi duk inda ya keso""."

Ammi kamar tasa hannu akai tai ihu ko zataji sauk'i.

Granny

Please Login or Register in order to submit comment