You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga toilet, tai wanka ta fito ta shirya cikin wata rigar t-shirt da syket da kad'an ya wuce gwaiwarta amman ya bud'e ta k'asa yaka mata ta sama ba k'aramin kyau tai ba ta saki gashinta gaba d'aya ta zubo da wasu gaba ta gyara musu zama agefe yadda kasar yar India haka tayi ita kanta tasan tayi kyau sosai sannan ta saka hijab d'inta ta fito parlorn ba kowa a parlorn amman anjera kayan breakfast akan dining d'in, k'arisawa tayi ta ja kujera ta zauna sannan ta fara breakfast don yunwa ta keji sosai, koda ta kammala taje d'akinta ta wanke bakinta ta kuma fitowa don taje gaidasu Granny."

"Iftee ta ce ""Ammie ba Daddy ya ce ""Min Ya Areef yana da mata ba yanzun, wacce fa jiya tazo gai dake kike ta mata fad'a ita nake magana"" ta fad'a a iyakar gaskiyarta."

"Dai dai lokacin Nadrah take sakko akan upstairs sai baza k'amshi takeyi, a hankali take takunta cike da kamala, d'agowa ya kalleta don yasan itace nan duk da tana cikin hijab ne ba k'aramin kyau tai ma Areef ba."

"A hankali ta k'arisa inda suke a zuciyarta sai addu'a takeyi da fargaban abinda zai biyo baya kanta a k'asa harta k'arisa inda Ammie take zaune, wacce da tun fitowanta fara an fuskanta ya d'auke gaba d'aya kamar taga mala'ikan mutuwa."

"Nadrah duk'awa tayi ta ce ""Am..mie ina...kwa..na"" bakinta narawa Ammie banza da ita tayi kawai tana tunanin abinda zatai mata ne don harga Allah ta tsani ganin ta ne gaba d'aya."

"Nadrah ta kara cewa ""Ina kwana Ammie""."

"Ammie cikin b'acin rai kawai ta watsa mata tea dake hannunta wanda bata dad'e da had'ashi ba zafinshi yasa itama take sha a hankali, ihu Nadrah tasaki Allah yaso bata sameta a fuska ba a jikinta ne ta watsa mata, Areef da sauri ya mik'e yasa hannu ya d'agota Nadrah ta fad'a kirjinshi ta rungumeshi ta fashe da kuka jikinta na rawa tana ""Wayyo Allah hannu na cikina zafi"" Areef gaba d'aya ya rud'e kawai ya yasa hannun ya d'auketa cak ya haura da ita saman stairs, Ammie da mamaki take kallon Areef yadda ya rud'e akanta, a fili ta furta bawai yaron nan yana son yarinyar nan bane da har zeyi kalan wannan rud'ewar me yake faru?""."

"Ganin ba mai bata amsa kawai ta mik'e harzata haura saman kawai ta shige d'akinta, Iftee kuma gaba d'aya ta rud'e itama, tana mamakin yaushe Ammie tazama muguwane haka.."

_Page 89&90_

"Areef bai direta ko ina ba ya wuce da ita bathroom yana zuwa, ya kunna mata shower ruwan sanyi yana dukkansu gaba d'aya suka fara jik'ewa, Nadrah tana makale a kirjinshi har lokacin tana kuka, sai dai saukan ruwan da taji a jikinta sai da ta sauke wata ajiyar zuciya a hankali yake yawo da hannunshi a bayan yana lallashinta, hannunta zugi yake mata da cikinta don tafi tunanin nan ne inda Ammi ta sameta da ruwan zafin."

Areef ya d'ago da kanta yayi a kirjinshi sannan yasa hannu zai cire mata rigar jikinta Nadrah ta girza mishi kai harara ya ballara mata yasa hannu ya fara cire mata rigar a hankali.

"Koda yazo dai dai hannun ta ce ""Ashhh pls a hankali zaka cire"", cirewa yayi a hankali gashi ko bra bata tsaka ba take fararen nonuwanta suka baiyana runtse ido yayi ya mannata da kirjinshi da sauri yana sauke nishi a hankali, sunkai wurin mitin 10 a haka, Nadrah ta ce ""Ruwan sanyi yana sani mura"" ta fad'a a hankali, hannu yasa ya kashe shower sannan ya ce ""Zaki iya cire syket d'in, gyad'a Kai tayi shi kuma ya d'auko mata towel ya mika mata shima ya cire nashi kayan ya d'aura towel a k'ugunshi, ya kwashe kayan da suka jike ya sasu a washing machine, sannan ya d'auki k'arami towel ya d'aura mata akanta saboda gashinta dake d'igar da ruwa, shima yasa wani akanshi ya koma d'ayan hannunta da bai kune ba suka fito a bathroom d'in, Nadrah tunda ta kalleshi sau daya bata kara ba, bawai tanaji kunyan ganinshi a haka"

bane sai dai yadda jikinshi yake a murd'e da yadda kiran jikinshi yake bata tab'a ganin na miji me irinshi ba.

"Zaunar da ita yayi a bakin bed a hankali sannan ya bud'e wardrobe ya d'auki wasu kayan yasa ka sannan ya goge gashin kanshi bai tsaya busar dashi da dryer, ya ce ""Ina sauran kayanki suke?"" Nadrah kanta dake katsa tana hura iskan bakinta a hannunta dake mata zugi ta ce ""Yana d'ayan bedroom d'in ne""."

"Fita yayi bai dad'e ba ya shigo da wasu kayan a hannunshi ya mik'a mata y'ace ta saka amsa tayi half vest ne black mai net ne asaman sai wandon k'arami fari ne tas iya cinyarta yake ba ta ce komai ba ta fara sakawa a hankali yana kallon yadda take kare jikinta, murmushi ne ya sufce mishi don idan tana wani abun har mamaki ya keyi sai kace ba wacce mazan waje suka gama kalleta ba."

"Tana gama sawa ya bita da ido ba k'aramin kyau kayan sukai mata ba, vest d'in yak'ara haska fatarta saman nonota duk ana kallo ga k'aramin cikinta dake shafe kamar wacce bata tab'a sa komai a cikin ba, shima a waje yake saboda konewan da tayi ne a ciki yasa ya d'auko mata half vest d'in daman, nisawa ya yi a hankali ya rik'o hannunta suka fito parlorn tayi kyau sosai sai takara k'ank'anta kamar yar 12 years."

"Zaunar da ita yayi a kan kujera, sannan ya je fridge ya d'auko k'ananan k'ank'ara yazubasu a wani karamin towel mai taushi kamar ba towel ba, ya ce ""Bani hannun ganin bada wasa yake mata ba ta mik'a mishi hannun kallon hannun yayi yadda fatar wurin tai jawur nisawa yayi sannan ya fara daura mata kankara da yake kan towel d'in lumshe ido tayi saboda yadda sanyi ya d'auki wurin ba k'aramin dad'i taji ba, a hankali yaita daura mata kankaran a wurin, sai da yaga wurin ya rage jan da yayi ya ce"

"""Kwanta saboda nai miki na cikin"", batai musu ba ta kwanta saboda taji dad'in hannu sosai kuma ya rage mata rad'ad'in sosai."

"Sannan shikuma ya fara d'aura mata k'ankara a cikinta, sai da Nadrah ta ce ""Oushhhh"", barin ma da taji saukan ruwan a cibiyarta a hankali yake yawo da kankara dai dai inda ta kunne don shima wurin ja yayi sosai."

"Bayan ya gama ne ya d'auko wani cream ya shafa mata a hannu da cikinta din, saboda kar wurin yai tabo kuma yana saurin warkar da k'una sosai, wani wahallen bacci ne ya kwasheta a haka ganin tayi bacci ya gyara mata kwanciya akan kujeran sannan ya shiga d'akin don busar da gashin k'anshi."

"Yana gamawa ya k'ara feshe jikinsa da turare sannan ya fito parlorn kallonta yayi yadda take bacci a nutse sannan ya fita a d'akin yanaji wani Abu dake tasowa a zuciyarshi, sakkowa k'asa yayi amman ba kowa a parlorn d'akin Ammie ya wuce don yasan tana fushi da abinda yayi, da sallama ya shiga d'akin, Ammie ciki ciki ta amsa sallamar, Areef ya k'arisa kusa da ita ya zauna zai kwantar da kanshi akan cinyarta ta matsar da k'afartata, ta ce ""Areef mena gani d'azun badai harka fara son yarinyar can bace ba ko?"" tai tambayar tana had'e fuska."

"Areef ya ce ""Haba Ammie taya zan so wancan yarinyar, kawai Ammie nayi hakan ne akan abinda zai biyo baya ne, kiyi tunani idan Daddy yasan ki k'onata ko Granny kina tunanin zasuyi shiru ne Ammie, ya kamo hannunta ya ce ""Ammie nasan ba kyason yarinyar ko kad'an amman kidena nuna fushinki akanta haka karki rauna nata saboda hakan matsala ne sosai, kar wata rana a samu matsala ki sassauta tsanar da kikai mata kidingayin ne a nutse Ammie, koda tazo gaidaki Ammie kidinga amsawa"

"tunda gaisuwa ne kawai ba wani abuba"", Ammie ta zame hannunta tana kare ma Areef kallo, kana ta ce ""Naji bazan k'ara nuna fushina haka akan taba, amman kuma maganar gaisuwa bana buk'atar gaisuwarta, karta kara zuwa inda nake idan ba haka ba bazan dinga rik'e kaina akan taba saboda na tsani ganinta"" Areef zai kuma magana tai sauri tarar numfashinshi ta ce ""Areef fad'amin gaskiya kodai ka fara son wancan yarinyar ne naga gaba d'aya kayi sanyi ne akanta?, tom inma ka fara ne kai maza ka dena don bazan tab'a amsar karuwa a matsayin sirikata ba, kuma na baka nan da sati d'aya kafito da wacce kake so zanma Daddy magana a d'aura maka aure da ita"", tana gama fad'in haka tatashi ta shige toilet d'inta, Areef wata zazzafan nunfashi ya furzar sannan ya shafa suman kanshi ya tashi ya fita a d'akin, gidan gaba d'aya ya bari yarasa meke mishi dad'i a ranshi kawai ya wuce gidan Yasir don anjima zai biya airport ya d'auko Daddy."

"Koda ya isa gidan Yasir yasa meshi tare da Eysha ne, suka gaisa sannan Eysha ta tattara kayanta ta tafi daman sun gama abinda zatayi don anan takwana gida zata wuce daman."

"Areef ya ce ""Yass ka hak'ura kenan da Baby Zumah?"" Yass ya ce ""Areef idan kaga na hak'ura da ita tom Baby Zumah mutuwa tayi koni na mutu shine kawai zan iya hakura da ita"", Areef nisawa yayi sannan ya ce ""Tom Allah ya kyauta"", Yass yai dariya ya ce ""Amin dai, yana ganka haka baka da lafiya ne?"" Yass yai magana yana kallon Areef, Areef ya ce"

"""Yass akwai matsalane""."

"Yass ya ce ""Meya faru ne Abokina?"""

"Areef ya ce ""Na kasa komai akan yarinyar asalima wllh wani irin bala'in kishinta nakeji ga zuciyata dake har bawa a duk sa'ilin dana kalleta wllh Yass na rasa me yake damuna akanta ga tausayinta kuma zuciyata ta kasa cutar da ita, me yasa nakejin haka akantane?"", Yass da badin yadda yaga Abokin nashi cikin damuwa da wllh ba abinda zai hanashi dariya, ganin tun ba aje ko ina ba Abokin nashi har ya fad'a don yaga tsantsar kauna ce kawai a idon Areef."

"Yass ya ce ""Areef maganar gaskiya kayi sauri a al'amarin nan, kaida ka gama cika baki akan cewa ba abinda zakayi da ita to meye najin kishinta da duk wa'inna abun akanta? Just 2 days ka karaya da sauri haka"", Areef ya ce ""Kaga Yass ni ba wannan na tambayeka ba kawai ka fad'amin me yasa nakejin haka akanta mene ma'anar haka shine kawai abinda nake son sani""."

"Yass yasan cewa Areef da gaske yake baisan menene so ba, saboda baitabayi ba, barshi kawai da neman matan banza abinda kawai ya sani kenan, sannan ya ce ""Areef maganar gaskiya ka fara son yarinyar nan ne, Areef yazaro ido ya ce ""So me hakan yake nufi?""."

"Yass ya ce ""Duk wani alamun sone abinda ka keji akanta, kishi mai tsanani, tausayinta, da zuciyarka da take harbawa a lokacin da ka ganta, idan ba soba ba abinda yake kawo wa dannan abubuwan, saboda haka ka fara sonta ne Abokina""."

"Wani zufane ya fara keto ma Areef tako Ina a jikinshi yana juya kalaman Yass kuma zuciyarshi takasa karyata mishi abinda Yass ya fad'a, Yass ya fahimci abokin nashi yana cikin rudani ne ya fad'a tarkon da bai tab'a tunanin zai fad'a ba nan kusa, Yass ya ce ""Areef dole ka yarda da cewa ka fara sonta ne kawai ka nuna mata soyayyarka a"

"gareta itama baza taki Amincewa da kai ba, saboda ba macen da zakace kana sonta baza ta Amince maka ba, wanda ba kace kana so ba sun biyoka sunce suna sonka balle kaine zaka ce kana sonta kawai ka nuna mata soyayya koda bata sonka ka koya mata yadda zata soka dole""."

"Areef ya ce ""Yass me yasa sai yanzun zanji soyayya akan mace bayan ni banyi shirin taba a yanzun Kuma sai akanta ma zanji soyayya?"" Yass ya ce ""Areef ita soyayya ba ruwanta da sai kashirya mata saboda a lokacin da kakamu a lokacin zata fara aiki bata jira sai anshirya mata kawai ka d'auki kaddarar taka a haka tazo"", Areef a jiyar zuciya ya sauke sannan ya ce ""Amman ai Ammie baza ta b'ata sonta ba, ya kwashe labarin abinda ya faru da yadda sukayi da Ammie kafin ya fito."

"Yass ya ce ""Ammie ba sati d'aya ta baka ba, da lokacin yayi ka fad'a mata cewa matarka kake so kai ba wacce kake so bayan ita, kuma Ammie tana son abinda kake so Areef baza taki Amincewa ba inshallahu Ammie baza ta bada matsala ba""."

"Sannan suka d'an tab'a hira har Yass yake ce ma Areef ai gobe zashi kano saboda Abba ya ce ""Ya dawo maza maza kafin yazo Abuja da kanshi yasa meshi, Areef ya ce ""Kenan baza kaje kaganta ba kafin ka wuce Yasir ya ce ""Eh tom zan leko da daddare inshallahu, idan ma ban samu zuwa ba idan nadawo zan zo tunda ba dad'ewa zanyi acan ba baifi nai 2 Weeks ba don dakyer ma nakai gaskiya"", Areef ya ce ""Shikenan tom Allah yakaimu kuma Allah ya tsare hanya"" Yass ya amsa da Amin""."

"sannan ya ce ""Ya zakayi da Jamcy toh?"" Areef ya saki tsaki mtswww ya ce ""Nifa ba sonta nake ba jikinta nake so saboda tana da abinda nake so, ita a tunaninta zan iya aure tane bazan aure taba infact, naji da daya ma tukunnan na afka soyayyar da ban shirya ba""."

"Dariya Yass yayi ya ce ""Kai ko, ka bar wannan maganar tun wuri kar itama ka Afka ma soyayyarta zaka gane ne ai"", Areef ya ce ""Ni kuma na kare ana titi kenan Allah ya isa tsakani na dakai Yass""."

"Yass ya ce ""To sai meye an fad'a maka basa auruwa ne to?"" Areef ya ce ""Mubar maganar nan kaji muje ka rakani d'auko Daddy naga kamar time d'in saukar jirginsu ya kusa kuma nasan bodyguard dinshi sun isa can saura nine kawai kar jirgin ya sauka ban k'arisa ba"", Yass ya ce ""Sorry bazan iya fita ba yanzun kaje kawai zamuyi waya later inshallah"" Areef bai takura mishi ba don yasan tunda ya fadi haka da gaske ne bazai iya fita ba, yai mishi sallama sannan ya fita a gidan."

"Koda ya isa Airport din ya samu bodyguard din harsun isa suna jiran saukar jirgin su Daddy ne kawai, suna ganin Areef suka fara gaidashi cike da ladabi amsawa yayi dai dai lokacin jirginsu Daddy ya fara sauka k'asa."

"Yana sauka mutane suka fara fitowa a cikin jirgin Daddy ne na uku da sauri Areef ya je ya rungumeshi yana ""Daddy sannu da zuwa"" Daddy ya ce ""Yawwa my Son"", sannan bodyguard suka fara gaidashi cikin girmamawa ya amsa sannan suka bud'e musu k'ofan motan baya suka shiga cikin, sannan suka kwaso kayan Daddy da 3 set na akwatinan Nadrah wanda ya biya Dubai daga Australia ya taho dasu a wurin Aneesha, bayan an gama zubawa a motan suka shiga motan suka jasu sai zuwa gida."

"Nadrah ta dad'e tana bacci sannan ta farka a hankali ta bud'e idonta ba kowa a parlorn kuma hannun da cikinta din basa mata zafi, ta duba a gogan dake manne a"

"bangon d'akin taga 4:56pm da sauri tatashi ta shiga bedroom d'inta don batai Azhar ba gashi har la'asar ya wuce, da sauri ta shiga toilet ta d'auro alaula ta fito ta sako hijab d'inta har k'asa sannan ta tada sallah."

Bayan ta idar ne tai addu'oi sosai sannan ta fito don taje ta gaida Granny.

"Tana sauka k'asa Allah yaso ba Ammie a parlorn, sai masu aikine da suke ta jera abincin akan dining kala kala, suna ganinta sukai sauri duka mata suna gaida ita, kunya taji saboda duk kansu ba wanda bai girmeta ba har da wa'inda suka haifeta ma a cikinsu, bata amsa ba kawai tai murmushi tana musu sannu da aiki, sannan ta fice a parlorn ta wuce part d'in Granny."

Da sallama ta shiga parlorn.

"Granny da inna Larai ne suka amsa sallamar, Granny ta ce ""Yar halak tak'i ambato yanzun nake maganarki ai yau najiki shiru, nace Larai taje ta dubamini ke sai gaki kuma"", murmushi Nadrah tayi ta zauna a gefen granny akan carpet, ta ce ""Granny ina wuni ya aiki ya k'afar taki kuma?"" Granny ta ce ""Lafiya kalau Alhamdulillah Yar albarka naji sauki sosai ai tunda kika matsamin kafarnan tawa ta dena min ciwo Alhamdulillah ai nagode miki sosai kam"", Nadrah ta ce ""Allah yakara sauki Granny ta ce ""Amin ya Allah, kina lafiya dai ko?"" Nadrah ta ce ""Lafiya kalau nake"", Granny ta ce naga idonki sun kun bura ne Areefu baya miki mugunta dai ko idan yana miki ki fad'amin naci mutuncinshi?"" Nadrah tai murmushi ganin jiya ma tai mata wannan tambayar ta ce ""A'a Granny ba abinda yake min kawai nayi bacci ne yau sosai shiyasa"", Granny ta ce ""Shikenan ai Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a na gari"" Nadrah bata ce komai ba, ta gaida inna Larai ta amsa tana mata ya Karfin jiki kuma, Nadrah ta ce ""Ai ta war ware Alhamdulillah."

"Granny ta ce ""Nasan yanzun hakan yaje d'auko Wazeeru ne a Aipot tunda naga yau banganshi ba gaba d'aya"", Nadrah batace komai ba sai dariya da tayi jin Granny ta ce ""Aipot ai maimakon Airport, sai inna Larai ne ta ce ""Eh kamar ya tafi kam don na dad'e dana ga fitarshi a gidan gaskiya""."

"K'aran bud'e gate sukaji motaci suka fara shigowa cikin gidan, Granny ta ce ""Kilama sune suka dawo"", inna Larai ta lek'a ta window d'akinta Granny ta ce ""Eh sune kam"" ta fita a a d'akin ya rage daga Granny sai Nadrah."

"Nadrah tatashi zata tafi Granny ta ce ""Ba inda zata ta zauna abinta suyi hira, ba yadda ta iya haka ta koma ta zauna."

"Daddy da Areef ne sukai sallama a d'akin Granny, amsawa sukayi sannan suka shiga ciki d'akin."

"Granny ta fara wake sannu da zuwa sannu da zuwa Wazeeruna sannu da Wazeerunah fuskanta dauke da fara'a, zama sukayi akan carpet d'in d'akin Daddy yana nishin gajiya had'e da murmushin wakar da maman tashi take mishi, Nadrah tashi tayi da sauri ta nufa wurin fridge din Granny ta bud'e ta d'auko goran ruwa na Mr.v mai sanyi sai k'ananan cups a saman farantin asaman fridge din, ta d'auko guda biyu, Areef tun shigowansu yake binta da ido har ta k'arisa gabansu ta ije ruwan ta zuba ma Daddy a cup ta mik'a mishi tana ""Sannu da dawowa Daddy"", Daddy cike dajin dad'in yadda ta karramashi ya amsa ruwan daman kishi yake ji sosai ya ce ""Yawwa yar albarka sannunki"", ta koma ta zauna kusa da Granny, Areef ganin bata zuba mishi ba, ya ce ""Ke zoki zubamin nima"" ba kishin yake jiba gulma ce kawai, har ta mik'e Granny ta ce ""Ke zauna bazaki zuba mishi ba d'in, bashi da hannu ne sai kece zaki"

"zuba mishi ruwan"", Granny ta kalli Areef ta ce ""Karka shan ruwan idan itace zata zuba maka""."

"Nadrah ta dago da kanta ta kalleshi ganin yadda ya had'e fuska yana kallonta, ta tsinci kanta da sakar mishi murmushi wanda yakara fito mata da tsantsar kyawunta kyawawan dimple dinta suka lotsa, bashiri Areef ya kama tari ya kware sosai, Daddy da sauri ya zuba mishi ruwa a cup ya miki mishi da sauri ya fara sha, sai da ya shanye ruwan tass ya ije cup d'in yana sauke wahallen ajiyar zuciya."

"Daddy ya ce ""Kai kuma lafiyarka, girgiza kai kawai Areef yayi yana satan kallon Nadrah da tai k'asa da kanta sai kace ba ita bace taja mishi wannan k'arewar."

"Granny bata ce komai ba, Nadrah ta ce ""Daddy ina wuni fatan an sauka lafiya, Daddy ya ce ""Lafiya kalau Alhamdulillah ngd sosai Allah yai miki albarka, Nadrah ta amsa da Amin kawai."

"Daddy ya ce ""Granny ina wuni fatan nasa me ku lpy?"" Granny ta ce ""Alhamdulillah ya hanya yasu Aneesha kuma kasa mesu lafiya da duka yaran ko?"" Daddy ya ce ""Suna lafiya kalau sunce agai da kowa anan Granny tai murmushi ta ce ""Aikon ina amsawa, Daddy ya ce ""Nasa ankai akwatinan Main parlour ne idan mukaje dinner sai a bud'e kayan ki gani ko"", Granny ta ce ""Ato masha Allahu sannu da kokarin Wazeeru Allah ya saka da alkhairi ya k'ara arziki yai maka albarka"", Daddy yanajin dad'in addu'an Granny sosai ya ce ""Amin ya Allah Granny nagode sosai Allah yakara miki lafiya, ta amsa da Amin sai a sannan Areef ya ce ""Ina wuni Granny"", Granny ta tab'e baki ta ce ""Sai yanzun ka gadamar gai dani bazan amsa ba d'in toh karike abunka banso tunda y'ay'ana sun gaida me zanyi dana jikalle""."

"Areef kauda kai yayi yana karki amsa d'in tsohuwa sai rigima, Granny ta ce ""Nayi din bazan amsa ba"" Daddy ya ce ""Kinga Granny kyaleshi"" don yasan idan sun fara basa gajiya, ya fara jan Granny da hira kwana biyu ba ai ba, Nadrah kuwa bata sake d'ago da kanta ta kalleshi ba shikuma sai kallonta ya keyi Granny ya lura da yadda yake bin Nadrah da kallo tai murmushi kawai, suka cigaba hirarsu."

"Kiraye kirayen sallar magrib ne yafara tashi, Daddy ya ce ""Granny bara muje muyi sallah idan nadawo zan aiko sai muzu muci abinci dare a parlorn"", Granny ta ce ""Adawo lafiya Wazeeru nan"", Areef ya tashi yabi bayan Daddy yana bin Nadrah da kallo, Granny ta ce ""Wannan kallon fa?"" Areef ya ce ""An fad'a miki ni ke nake kallo tsohuwa dake"" yana fad'in haka ya wuce, Granny tasan ba ita yake kallo ba ta kalli Nadrah ta ce ""Ke naga sai kallon ki ya keyi badai kin fara bashi kanki bane?"" Kunya yaka Nadrah jin tsohuwa da wannan zanje, Nadrah ta ce ""A'ah Granny""."

"Granny ta ce ""Karki yarda ki bashi kanki har sai yafurta miki kalmar so sannan zaki Amince masa, zanyi maganinshi ba yace baya son auren ba zanga iya gudun ruwanshi."

"Nadrah dai bata kara cewa komai ba ta tashi ta shiga toilet d'in Granny tai alaula ta fito, Granny ma ta shiga don tai alaular itama.."

_Page 91&92_

Bayan sun idar da sallar magrib su Daddy basu dawo ba sai da sukai sallar Isha'i sannan suka shigo gidan.

"Sai a sannan Daddy ya had'u da Ammie daya shiga d'akinta, tana tsaye bakin mirror tana daura d'ankwali tayi kyau sosai ba kad'an ba, rungumota ta baya ya yi ya ce ""Madam Wazeeru kina lafiya"" lausassan murmushi Ammie ta yi ta ce ""Daddy ina wuni fatan ka sauka lafiya"" ya manna mata kiss a gefen kuma tunta ya ce ""Ina lafiya qlu balle yanzun dana ganki sai naji kamar.. da sauri Ammie tasa hannunta ta toshe mishi bakinshi ta ce ""Wai Daddy bakasan mun girma bane yanzun"" Daddy yai murmushi ya ce ""Soyayya ai bata tsufa dariya tayi sannan ta ce ""Tom muje parlorn dinner is ready""."

"Ammie koda ta fito d'azun da taga uban akwatinan zube a parlorn tasan cewa na Nadrah tai fuska kota kansu bata biba, suka fito parlorn abun burgewa sunyi kyau da junansu sosai murmushi Iftee ta yi ta fad'a jikin Daddy tana ""Daddy i miss you so much"", Daddy ya ce ""Miss you too autar Daddy sannan ya sauketa k'asa tana dariya. Daddy ya ce ""Maza kije ki taho da Granny muzo muyi dinner Daddy yunwa yake ji sosai"" Iftee ta tafi da gudu part d'in Granny."

"Areef ya ce ""Ammie barka da fitowa, Ammie ciki ciki ta amsa ta ce ""Barka dai my son, Areef ya fahimci fushi ta keyi dashi har yanzun kawai yai k'asa dakai yana danna wayarsa."

"Aftee tana zuwa part d'in Granny ta fad'a jikin Granny tana granny Daddy yace muzo muyi dinner yunwa ya keji sosai"", Granny ta ce ""Wayyo iftihar zaki k'arisa min y'an k'afaffun nawa"", dariya iftee ta yi ta ce ""A'ah bazan karya kiba ai kin fini nauyi Kon Anty?"" Ta fad'a tana kallon Nadrah dake musu dariya, ta gyad'a mata kai ta ce ""Eh iftee""."

"Iftee ta ce ""Yawwa Anty nasan zaki fadi gaskiya ai, nida Granny wayafi wani kyau?"" Nadrah tai murmushi ta ce ""Kin fita kyau, Iftee ta ce ""Yeeeeh tana ma Granny gwalo ta ce ""Granny kince kin fini kyau Anty ta ce na fiki kyau"", Granny ta ce ""Iyayen surutu muje ni muci abinci kar Daddyn naki yagaji da jiranmu"" ta fad'a tana sauke Iftee a jikinta."

"Granny ta ce ""Nadratu tashi muje muci abinci, Nadrah kamar baza ta taso ba don tsoro had'uwa take da Ammie gaba d'aya don tasan duka gidan

Please Login or Register in order to submit comment