You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

missing dinku

Kara shigewa Jikinta sukayi suka ce Muma haka mommy

dariya duka sukayi.

Sai da sukayi kiran sallar La'sar sannan suka Mike suka tafi masallaci Wanda abba na Lura dasu haidar Ko kallon mahaifiyarsu basuyi ba.

Sai da suka idar da sallah Cikin bacin rai abba yayi musu Tatas yace kuma Idan sun koma Kowa Ya gaisheta.

a falo suka samesu suna fira Rumaisa Nashan fruits Zama sukayi gaba d'aya

Ganin bazasu gaishetan bane yasa abba galla musu harara dakyar haidar ya bude baki yace

ina wuni

Ajiyar zuciya tayi tace Lafiya lau.

Abba Ya daka mishi tsawa yace Haka aka gaisuwa

Cuno baki yayi yace Kunzo lafiya

Lafiya lau

ta bashi amsa Ya jikin?

Ya tambayeta

Jiki Alhamdulillah

Abba Ya Kalli farouk dayaki yarda suka had'a idanu yace Oya Saura kai

Kauda kanshi gefe yayi Cikin dakiya yace Abba Kayi hakuri

Dakatar dashi yayi yace

ba wannan na tambayeka ba Mik'ewa yayi Idanunshi Sunyi ja yace

wallahi a yadda zuciyata take Idan na gaisheta zan iya mutuwa.

watakila nan gaba dai amma kada ku tursasani yanzu sanin cewa Cikin dazata Haifa shima zata iya yarda shi tunda batason yara

Mari abba Ya wanka mishi yace farouk mahaifiyarka ce fa

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

30

Parlour yayi tsit Cikin kuka rumaisa tace

Daka sani baka mareshi ba Kowa tunanin dayake mini kenan amma ni nasan nayi nadama kuma Allah ne shaidata sai dai ku sani ni mahaifiyarku ce koba komai yaci na sami girmamawa daga gareku kodan nakudarku danayi.

Cikin tsananin fushi farouk yace

Nikam na tsaneki dakinsan Kalar yadda na tsani ganinki da bakizo nan wajen ba Abba Cikin fusata yace

Farouk Ashe bakajin magana haka Kai wane Kalar yaro ne mahaifiyarku ce fa. Kallon abba yayi idanu jajir yace

Duk da take mahaifiyata ta manta hakan ne a lokacin data daukeni ta kaini can Wani gari Ta bawa mutumin da bata San shi ba be santaba.

Muna yan uwan juna ta raba mu ta Hana mana kusantar mahaifiya ta Hana mana.......

Maganarce ta makale kirjinsa Ya rike da hannun Hagu yayinda hannun Daman ke nuna rumaisa Iya bakinshi ke motsi amma Maganar taki fita a haka har yakai k'asa.

Duka rudewa sukayi.

Abba ne ya d'aukeshi yayinda daddyn baby yayi Waje domin dauko mota. Kamar gawa haka aka sakashi amota Cikin tashin hankali suke gaba d'aya. Asibitin shika suka wuce

A$E suka kaishi.

K'ok'arin janyo numfashin sa akeyi amma Abu yana neman yafi karfinsu

Cikin tashin hankali su mama suke duk dauriya irinta abba sai da ya zubar da hawaye. Rumaisa kuwa gwanin ban tausayi.

Haidar da Salim Abin ba'a magana

Dan zama Salim yayi Kamar mahaukaci. Cikin fushi haidar yace

Wallahi Dan uwana ya mutu bazan yafe miki ba. Harara abba Ya galla mishi.

Hawaye Ya goge yace

Shikenan mu abba Kullum a tashin hankali.

Daddyn baby ya riko shi ya Cigaba da kwantar masa da hankali. Cikin damuwa abba yace

Yanzu ya Kake gani a sanar dasu Mai martaba Ko a kyalesu. Girgiza Kai kawai daddyn baby yayi yace

Kada ka Fara ka bari muga yanayin jikin.

Wajen awa biyu sannan aka samu numfashinsa ya daidaita Likitan yace

Ina mahaifinsa

Atare abba suka amsa Dan murmushi yayi yace

Wannan yaron daga gani Dan Gata ne ku biyoni office Bayan sunje likitan yace

A gaskiya yaron yana daf da kamuwa da mummunan heart attack. Atare suka maimaita

Me heart attack likita. Abba Ya ce

Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun. Dafashi likitan yayi yace

Ka kwantar da hankalinka bance yanadashi ba cewa nayi Ya Kusa kamuwa dashi yanzu abinda Ya kamata shine ku gujewa abinda zai dinga bata masa rai domin samin saukin Abin.

Abba yace

Insha Allah yanzu zamu iya ganinshi Likitan ya numfasa yace

babu matsala amma gaskiya bazai farka da wuri Ba. Daga Kai kawai sukayi suka fita Cikin jimami.

Mama ganin jikinsu a sanyaye yasa suma suka kara shiga damuwa Rumaisa ta goge Hawaye tace

Kada ku ce mini ya mutu.

Hannunta daddyn baby ya riko yace

Ki natsu kinsan ba aso Mai ciki na shiga damuwa da yawa ko Shiyasa naso na taho ni daya kika Nace saida kika biyoni.

A hankali Hawayen suka Cigaba da zuba daga idanunta Karamin tsaki Haidar yaja Wanda abba Ya galla masa Harara. Mama tace

Me likita yace

Abba Ya gaya musu yadda likitan ya gaya. Salim yace

Yanzu yace zamu iya ganinshi? D'aga Kai daddyn baby yayi

A hankali suka tura kofar suka shiga Kwance yake jikinshi duk na'orori. A hankali ta karasa kusada shi rayuwarta ta dace ta Fara dawo mata. Hawaye ta goge tace

Allah Ya baka Lafiya Ya Kuma fahimtar daku irin son danake muku. Abba yace kuje gida ku huta zuwa anjima kwa dawo

Rau rau da idanu rumaisa tayi Cikin lallashi daddyn baby yace Pls kije ki huta.

Daddyn baby da abba aka bari Dan har su Salim abba Ya had'a ya kora.

Suna zuwa gida rumaisa wanka kawai tayi ta kwanta amma Sam barci yaki zuwa. Mama kuwa zama tayi sannan ta kira zainab ta gaya mata.

Cikin jimami tace

Ayya Allah Ya sauwake.

Suna gama Waya Zainab ta kira Salma Bayan ta D'aga tace

Ina fatan babu sa hannunki a ciwon da farouk yakeyi Murmushin gefen baki Salma tayi tace

Bayada lafiyane? Numfasawa tayi tace

Yanzu halima ta gaya mini sannan ina fatan babu sa hannunki Salma tace

babu dan ni yanzu ina saka hannuna sai dai kiji ance ya mutu bawai yana asibiti ba Cikin jin haushi hajiya Zainab tace

Haba aunty ki dinga jin tsoron Allah mana Ya isa haka

Hajiya Salma ta gaya Cikin karaji

Ni zakiyiwa Wa'azi Zainab to ahir dinki Dan banason shishshigi kinsani. Zainab tace

Allah Ya baki hakuri. Tsaki Salma taja tace Aikin banza kawai.

Ta kashe Wayar

Salim sukayi sallama suka shigo dakin

Mama na zaune Tana ninke kaya rumaisa kuma na Kwance ta Rufe idanu a zahiri sai ka dauka barci take amma idanunta biyu.

Salim ya Matsa kusada mama ya Dora kanshi a kafarta. Shafa kanshi tayi tace

Farouk Ko?

D'aga Kai yayi Cikin shagwaba yace So yake ya kashe kanshi ya barni Mama ta Rufe bakin shi tace

Kadaina cewa Haka addu'a zakayi Allah Ya bashi Lafiya. Haidar ya Dora kanshi a kafadarta yace

Mama Wai ki Bamu labarin ya akayi har mahaifiyar data haifemu ta yarda mu alhalin bamusan komai a duniya ba.

Shiru mama tayi Cikin nutsuwa tace

Zan baku labarin sai dai akwai abubuwa masu ban mamaki a ciki. Sannan Ka mini alkawarin zaka Dena kullatar mahaifiyarku.

Shiru yayi na lokaci kadan sannan ya D'aga Kai yace Eh amma Idan Naji cewa batada laifi.

Murmushi mama tayi tace

To bude kunne Kaji.......

Nima one love nace ku bude kunne kuji

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Bashir sufyein(sardauna) na ga gaisuwa kuma na amsa sosai Allah Ya bar zumunci Ameen.

Acigaba da matafiya uku

Na gode da kulawarku Mustapha marakisiya Aeesha Adam Shamsiyya m magaji Members of

Hafsat Hausa novel h² Hausa novels by ask

Na sadaukar da wannan page din gareku

Zulaihat sani da starboy umar Kunfi Kowa damuwa Dani ina Godiya sosai ku ke k'arfafa mini gwiwa.

32

Kamar Mai martaba bazai amince ba sai kuma ya amince. Alhamdulillah bata dadeba ta Fara dawowa hayyacinta.

Sai dai bata magana sosai da sosai kunada wata biyu ta Matsa mini Akan zata koma gida. Sai dai kwana daya kwana biyu bata je ba.

Hankali ya tashi sosai sai da ta kwana uku sannan sai Gashi anganta a gefen titi. Sai da aka kaita asibiti sannan aka sami kanta.

Rudewar danayi ya janyo mini nakuda.

Anan adamawa na haihu Wanda sati na zuwa aka samaka suna Salim.

Bayan ta farfado take fad'a Mana tareta akayi aka kwace motar da yaran aka mata duka har ta suma.

Munyi bakinciki sosai Wanda a lokacin kuma munyi mamaki domin modibbo yafi Kowa shiga tashin hankali.

Kuma fadi yake shi rumaisa yakeso be san ya akayi ya auri Salma ba. Mai martaba ya daka mishi tsawa yace

Kada ka maidamu marasa hankali mana ka zabi salma da kanka kace Wai yanzu baka sonta to wallahi Kaji na rantse baka isaba kaje ka tattara kayanka kubar kasar nan ku tafi India

Ke kuma

Ya nuna rumaisa yace

Nan da sati biyu zan daura aurenku tareda kabir (daddyn baby)

Rumaisa tayi kuka sosai domin sanin cewa ta rabu da modibbo kenan har abada.

Bayan anyi auren suna zaune Lafiya sai dai fa shekararsu goma sha hudu babu haihuwa hakan yasa ta shiga damuwa har ya Zama sanadiyar samun ciwon zuciya.

Bayan Tasha wahala sosai Dan har kasar Waje aka fitar da ita sannan ta sami Lafiya sai dai takanje check up duk bayan wata shida.

To alokacin Mai martaba yace Da abbanku Ya bata fahad da farida Mama ta dubi haidar tace

Kaji labarin ku sannan ina fatan zaka yafewa mahaifiyarku. Jan numfashi yayi a hankali ya Mike ya isa wajenta

Idanunta a Rufe suke sai dai da alamu idanunta biyu domin hawaye dake gangarowa zuwa kan Hancinta.

Hannunshi yasa ya share Hawayen Cikin matukar tausayinta yace Momma

Wata Ajiyar zuwa taja domin ta dad'e Tana jiran jin wannan sunan daga bakin yaran Nata. Hannu tasa ta rike nashi hannun

A hankali ta bude idanunta ta sauke Akan shi Mik'ewa tayi a hankali har ta zauna

Cikin sheshshekar kuka tace Haidar ku yafe mini

Da sauri Ya Rufe bakinta yace

Ya wuce dama Ban taba rike ki a rainaba domin nasan yin hakan babban laifi ne a wajen ubangiji.

Ke kika haifemu koda kashe mu kikayi kinyi daidai Janyoshi tayi ta rungume tana kuka.

Ji take son yaran nata na karuwa

Babu Wanda ya rarrashe sai da suka gaji sannan sukayi shiru. Mama tace

Ku tashi kuje kuyi wanka domin anjima zaku Kai abinci asibiti. Amsawa sukayi sannan suka fita Cikin sauri

Sai da sukayi wanka sannan suka kwanta Karfe biyu suka farka

Cikin sauri sukayi alwala suka tafi masallaci

Sai da sukayi sallah sannan suka je suka amshi abincin suka tafi Ahanya Salim yace

Meka fahimta da labarin da mama ta Bamu. Ajiyar zuciya haidar yayi yace

Aikin asiri

Jinjina Kai Salim yayi yace

Tabbas nima na fahimci hakan to amma Kana ganin farouk zai fahimta Girgiza Kai haidar yayi yace

Bana tunanin haka sai dai a hankali ya fahimta.

Suna isa suka tarar dasu abba sun idar da sallah kenan zasu shiga asibitin Atare suka shiga

Yadda suka barshi haka suka dawo suka sameshi.

Jikinsu yayi sanyi sosai domin sun zaci Ya farka zuwa lokacin. Sai bayan isha sannan abba yace su tafi gida shi zai kwana

Kememe Salim yaki tafiya aka juya aka murza yaki karshe dai hakuri akayi aka barshi Ya kwanan.

Wajen uku da Rabi na dare ya Fara motsawa

Salim Wanda ke zaune Yana kallonshi yayi saurin mik'ewa Abba Ya tayar Cikin murna Yana fadin

Abba tashi farouk zai farka.

Abba da sauri Ya Mike ya fita domin kiran likita shi kuma Salim ya Matsa Kusa dashi Yana kiran sunanshi.

Kamar Wanda ya farka daga barci k'ok'arin mik'ewa yakeyi Wanda yayi daidai da karasowar likitan tareda abba.

Cikin sauri abba Ya rikeshi Likitan yace

Yanzu ya Kake jin jikin naka. A hankali yace

Da sauki sosai Likitan yace Da abba

Kubashi abincin da babu nama ko hanta ko alayyahu da kifi da wake Sannan banda tea.

D'aga Kai Salim yayi.

Bayan likitan ya fita farouk ya Kalli Salim yace Yadai kayi kuka Ko

Hararshi yayi yace Bansaniba

Dan dariya yayi yace

Dagani nayi alwala nayi sallah Dan shagwabe fuska yayi yace

Allah ka kuma irin wannan sai mun bata. Murmushi yayi yace

Kaga bari nayi alwala nayi sallah sai mu zauna gaba daya

Kamashi yayi suka shiga bayi

Abba yayi murmushi yana mamakin shakuwar Salim da farouk d'in Duba da yinin yau kwata kwata Salim d'in be ci komai ba

Sai da yayi wanka sannan ya dauro alwala yayi sallolin da ake binshi Yana idarwa

Salim ya zubo masa sinasir Da miyar zogale. Zubawa abincin idanu yayi Salim yace kaci mana Kallon Salim d'in yayi Ya Wani bata rai

Turo baki yayi yace

Kasan bazan Ci ba Idan kaima bazaka ci ba . Dan murmushi Salim yayi Ya saka hannu Suna Ci suna fira

Abba duk da baya jin abinda suke cewa amma yana farinciki da Haduwar Kansu. Wayar Salim tayi kara

Sai da ya Kalli agogo Karfe hudu da kwata Cikin sauri Ya D'aga

daga Dayan bangaren haidar yace Yaya Nawan ya farka Ko?

Kamar yana ganinshi ya balla harara yace Bansaniba bayan barcinka kaje kanayi.

Dan marairaice fuska yayi yace

Wallahi ko kan dardumar ban sauka ba sallah naketa yi. Dan murmushi Salim yayi yace

Gashi zaune muna fira Cikin tsananin murna yace Bashi Wayar please

Farouk na amsa haidar yace

Ashe da gaske ne gani nan tahowa

Be bari farouk yace komai ba ya kashe Wayar. Minti goma yayi sallama ya shigo dakin

Abba yace

Wai haidar da gaske zuwa kayi Kiran sallar yasa abba yace

To sai ku tashi Muje muyi sallah ai.

Sun tafi suka bar farouk Akan darduma ya tayar da sallah

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

35

Inda aka tanada domin zaman irin hakan Idan ya kama suka tafi. Farouk wanka Ya shiga shi kuma Salim ya kwanta.

Koda ya fito Salim d'in Danna wayarshi yakeyi Dan murmushi yayi yace

Salim kasan me Sai ka gaya

Wallahi inajin Kunyar nayi mata magana yanzu. Wace kenan?

Salim ya tambaya

Kasan Wanda nake nufi mana kuma Allah haidar zai zo ya sameni Dariya Salim yayi yace

Me zakayi masa ne ? Harararshi yayi yace Bansaniba.

Cikin nishadi suka Cigaba da firarsu har akayi kiran sallar magrib sannan sukayi alwala suka tafi masallaci.

Acan suka zauna har akayi sallar isha sannan suka dawo. Har sun shigo harabar gidan Wayar farouk tayi kara Ganin Faisal yasa ya D'aga Cikin tsokana yace

babu ruwana dakai. Faisal yayi dariya yace

Nima ai babu ruwana da Mai gaba da mahaifiyarshi. Murmushi yayi yace

Kayi d'aya kada ka maimaita In serious tune Faisal yace

Farouk ka tsaya Kaji abinda zan gaya maka Ada haidar naso gayawa sai kuma naga Kai yafi kamata ka sani

Nan ya kwashe labarin da hajiya Zainab ta bashi Kaf ya gaya mishi yace Idan kuma baka yarda ba Gashi Kaji Daga bakin ammar

Ammar na amsar Wayar shima Ya zayyane masa duk abinda Ya sani. Hawaye kawai yakeyi

Yace

Ku bari Idan muka zo anjima zamu tattauna Abin. Shiru yayi na Wani lokaci

Tabbas an cutar dasu to amma ai babu laifin mahaifiyarsu ko mahaifinsu to amma me ya kawo hakan

Sai yanzu yayi Wani tunani ai da haidar shima baya kula ta to Ya akayi yake kulata yanzu sosai?

Dole akwai abinda Ya sani me kenan? Kuma Meye Salim bazai rasa sani ba

A sanyaye ya shiga gidan Akan dinning suke hakan yasa can ya nufa kawai

Ko abincin juyashi kawai yakeyi Tabbas babu yadda za'ayi uwa na Cikin hankalinta Ta yardar da yaranta meyasa beyi tunanin Wani Abu ba?

(Oho farouk daga baya kenan )

Daddyn baby ya Dan bugi table kadan yace Farouk lafiyanka kuwa inata magana shiru? Girgiza Kai yayi yace

Babu komai.

Abincin dai kasa Ci yayi.

Wajen Karfe biyu farouk ya Kalli Salim barcinshi yake sha babu ruwanshi amma shi Ya kasa Ya ilahi ya zaiyi ya tunkari mahaifiyarshi domin ya bata hakuri

A hankali Aka turo kofar Maida Idanunshi yayi Ya Rufe Ba'a kunne light ba sai dai dim light da yake a kunne Matsowa tayi a hankali ta zo dai dai Kusa dashi

Hannunta ta d'ora Akan fuskarshi Cikin kulawa ta shafa a hankali Bude idanu yayi Wanda hakan yasa gabanta ya fadi

Juna suka zubawa idanu

Ahankali hawaye Ya sauko daga Idanunshi Ya tabbatar soyayyar uwa daban take Mik'ewa yayi Ya zauna

Rumaisa kuwa ta kasa mik'ewa haka ta kasa zama Gabanta ya tsugunna Cikin matsanancin kunya yace

Dan Allah kiyi hakuri ki yafe mini abubuwan dana yi miki bazan kuma ba yafiyarki nasan zatasa Allah Ya yafe mini nasan fushi da uwa Abu ne Wanda Allah Ya Hana amma na take sanin nake aikatawa bansan wane hukunci Allah Ya tanadar mini ba.

Kiyi hakuri ki yafe mini Hannunshi ta rike tace

Ni yakamata na nemi yafiyarka farouk domin abinda na aikata Da sauri Ya Rufe bakinta yace

Ke kika haifemu koda kashe mu kikayi kinyi daidai Rungume juna sukayi suna kuka

A hankali ya Janye jikinshi

Ya Fara goge mata Hawaye yace

Allah yana sona da rahama daya fahimtar Dani Da wuri. Murmushi tayi tace

Meya hanaka barci ?

Ina tunanin yadda zan tunkareki Daki yafe mini ne kefa Mai Ya hanaki barci? Ya tambayeta

Nayi barcin zuwa nayi domin na duba ya kuke kasan wannan ne na farko da Wani da sunan jinina yazo Kwana Anan.

To muna Lafiya ai. Shafa kanshi tayi tace Yanzu ka kwanta

Kona kwanta barcin bazai zo ba

To kayi alwala kayi nafilfili Daga Kai yayi yace

To momma

Wani farin ciki taji har saida ta murmusa

Tana fita yayi murmushi ya shiga toilet yayi alwala Ya fito A zaune ya sami Salim

Kallonshi yayi Alamar Lafiya Dariya Salim yayi yace

Finally dai yanzu angama farouk ya kira mahaifiyarsa da momma Hararshi yayi yace

Nifa gulma ne Bana so

Dariya Salim yayi ya Mike ya shiga bayi alwala yayi Sannan yazo shima Ya tada tashi nafilar

Wannan sabonsu ne tun a makaranta.

Sai da akayi kiran sallah sannan suka tafi masallaci. Bayan sun dawo suka kwanta

Basu suka farka ba sai Karfe sha d'aya. Da sauri farouk ya tada Salim

Hade rai yayi yace

Lafiya daga kwanciyata zaka tasheni. Nuna masa agogo yayi

Zaro idanu yayi kafin ya mik'e Cikin sauri Ya shirya Cikin kananan kaya jar t shirt da bakin jeans.

A zaune suka tarar da momma Tana operating system. D'agowa tayi tace

Tab sai yanzu gaskiya Kun makara d'azu na aika baby ta dubo Lafiya tace Wai barci kukeyi. Zama farouk yayi Yace

Wallahi jiya barcin da bamuyi bane Gashi yanzu nasan suna can suna jiranmu. To yanzu kuje ku karya Bari na kira su a Waya Naji suna adamawan ne.

Gaisheta sukayi sannan suka hau dinning.

Fried plantains da oat sai kunun Gyada da kosai. Farouk dai kunun yasha.

Salim kuma oat yasha.

Momma ta kira haidar ringing d'aya ya D'aga Bayan sun gaisa tace

Son kuna adamawan ne?

A'a mun dau hanya yanzu muna daf da jos. Ya bata amsa

Tab to gasu farouk suna nan yanzu suke karyawa. Dariya haidar yayi yace

Tab sai dai su biyo mu a baya. To Allah ya tsare hanya Haidar ya amsa da Ameen Kallonsu tayi tace

To ku kunji su haidar sun wuce sai dai Idan kun tashi ku tafi kawai.

Wayar Salim tayi kara

Cikin girmamawa Ya gaidashi. Mai martaba yace

Naji ance kuna taraba zaku biyo ta nan ne? Salim ya amsa da

A'a kawai yanzu zamu wuce Ta nan ne. OK to bawa farouk Wayar.

Cikin sakin rai suka gaisa sannan yace

Wajen mahaifiya dad'i ko yau an manta da Mai martaba. Murmushi farouk yayi yace

Ai Bamu dad'e da barin wajenka ba. Hakane to Allah ya kiyaye hanya Ameen Ya amsa

Driver daddyn baby ya hadasu dashi ya kaisu har Zaria Amma fa sai sha d'aya na dare suka isa.

Wanka kawai Farouk yayi sannan ya kwanta Mama tayi sallama ta shigo

Tray hannunta ta ajiye tace

Ya haka farouk Ko abinci baka ci ba Idanunshi a Lumshe yace

Mama barci nakeji ne wallahi. Tashi Kaci abinci.

To mama ajiye zanci.

Sai da ta rage musu AC sannan tace To sai da safe.

Salim yana fitowa daga wanka Ya saka kayan barci sannan ya dauko abincin ya zuba. Kallon farouk yayi dayake ta sharar barcinshi hankali Kwance.

Sai da yaci Ya koshi sannan ya kwanta.

Ai kuwa da asuba dakyar haidar ya tashe su.

Ko zaman addu'a farouk beyiba Ya wuce gida kwanciya kawai yayi sai barci Karfe bakwai yunwa tace bata San wannan barcin ba.

Haka yasa ya tashi Wanka yayi sannan ya fita

A kitchen ya tarar da Yusra da mama Husna kuma na goge dining

Sai da suka gaisa da mama Sannan husna da Yusra suka gaisheshi. Bude bude ya Fara

Mama tace Lafiya kuwa. Lumshe ido yayi yace Mama yunwa nakeji.

Girgiza Kai tayi tace

Allah Ya shiryeka wato jiyan dai bakaci abincin ka kwanta Ko Kallon Yusra tayi tace

Had'a masa tea ga doya nan sai ki zuba masa Bread na kan table.

A k'asa ya zauna Ya Fara ci Babu ruwanshi da zafi. (Nace yunwa kenan ) Sai da ya koshi sannan ya Kai kayan kitchen d'in

Kallon mama yayi yace Mama zan tafi Kano yanzu. Mama tace

Kano kuma jiya fa muka rabu. Yace

Mama baffa fa har muka rabu fushi yakeyi Dani Murmushi mama tayi tace

Baya fushi dakai farouk abinda kayi ne ya bawa Kowa haushi. Fuska ya marairaice yace

Ai na bata hakuri kuma ta yafe mini. Mama tace

Yauwa Ko Kaifa ka hakura da zuwa Kano ka bari nanda three weeks kaje kaga yanzu ana tsakiyar semester

Shiru yayi kafin yace

Mama Nidai ki Bari naje kawai. Ajiyar zuciya tayi tace

To Allah ya kiyaye hanya kayi sallama da yan uwanka ko? Yace

Mama kyalesu kinsan halin Salim yanaji zan tafi zai ce sai yaje Kuma ni yau nakeso na dawo zai wahala sosai.

Ikon Allah itadai Tana girmama wannan soyayya dake tsakanin farouk da Salim wato Bama laifi bane basu so ace daya yayi a'a harda wahala.

Dariya tayi tace

Ikon Allah kai dayake karfene ai bazaka gaji ba ko? Shafa Kai kawai yayi yace

Mama sai na dawo Kallonshi tayi tace

To haka zakaje musu babu komai tsaya ina zuwa

Tirmin atamfa guda hudu ta debo sai kayan kwalliya da turare. Tace

Kayan kwalliya ka bawa humaira turare ka bawa baffa Atamfa kuma ummanka.

Godiya yayi

Da driver suka tafi

A hanya ya kira Mamie suka gaisa sannan ya kira daddy hamma shima gaisawa sukayi momma hajiya Zainab da mai martaba sai daddyn baby da daddyn yola duka ya gaishesu

Karfe goma suna Kano. Dai dai baffa zasu fita

Da mamaki Ya ke kallon farouk.

Kherdylurhv

farouk ko haidar

Written by deeja one love=ØŠÝ

Dedicated to madina m umar 38

Yana budewa msm suka fara shigowa Ahankali ya fara budewa

Sakon haidar dayake cewa Nice makaranta tayi Kyau

Murmushi yayi sannan ya shiga group dinsu na family abinda salim ya rubuta ya bashi mamaki Sarina ta zama birni an gina mkaranta

Sai video coverage daya tura

Fira sukeyi sosai akan makarantar Ammar yace

Gaskiya ta hadu kamar a India Emoji na dariya faisal ya turo

Surayya kam harda recording din dariya

Husna ce ma me Dan tarewa kowa tsokanarsu yakeyi Kashe data yayi ya zubawa salim ido

Ware idanu salim yayi alamar lafiya Murmushi kawai yayi ya juyar dakai

Washe gari suka shiga gari asibiti da bore holes din duka sai da salim ya dauka ya tura family group

Farouk kuwa ya Kira mai martaba a waya yayi godiya tabbas makarantar ta hadu Momma ya Kira itama yayi Mata godiya

Tayi murmushi tace

Duk abinda kakeso inasonshi farouk

Hakan data gaya bakaramin birgeshi yayi ba. Suna zaune Ana gobe Zasu tafi

Duk sun gama shirya kayansu

Ammar ya Kira farouk yace gashinan yanzu suka sauka Ya rasa mai yasa sai da yaji gabanshi ya fadi

Ammar yayi dariya yace

Pls kuzo da wuri Amsawa yayi da to.

Washegari su mama sai da suka biyo suka daukesu. Tun a hanya haidar ya damesu da waya akan sun Taho. Karshe dai kashe wayar farouk yayi

Kiran ta salim yayi Salim yace

Dalla kada ka damemu mu sai ana gobe zamu taho Haidar yace

Kai salim wallahi zan mareka Basai ka Mara nagani ba Hakadai suka karaci shirmensu

Koda suka isa gida ya cika da jama'a Sai busa ke tashi

Tsaki farouk yayi Wanda yaja hankalin mama Harararshi tayi

Salim yaja hannunshi suka tafi.

A bangaren fulani suka hadu da haidar da ammar Haidar yayi dariya yace

Kaga angwaye

Hade rai salim yayi yace

Waye angon may be dai farouk. Fulani tace

Kai bakaso kazama Ango ne? Shafa kanshi yayi yana dariya Fulani ta dubi farouk tace

To me gida yadai kai baka magana Murmushi kawai yayi.

Ammar yajashi ya zauna

Hajiya salma ta dubi yafindo karima tace Na shirya mu tafi kawai

Yafindo Karina tace To muje.

Motar hanya suka hau domin idan suka dau ta gida da Matsala A bakin wani karamin kauye suka sauka.

Hajiya salma ta dubi dajin tace Mama badai nan zamu shiga ba Eh mana nan zamu shiga Girgiza kai tayi tace bazan iya ba Yafindo karima tace

Ba aikin kikeso

Wata uwar tafiya sukayi kan su iso bakin wani dutse mai fadi Hawa kai sukayi

Yar bukkar yar karama da ita Hayaki ke fita daga ciki Hajiya salma cikin tsoro tace Mama mu koma Dan allah

Wani iskace ta taso ta rufe wajen

Cikin kaduwa hajiya salma ta kankame yafindo karima

Wani irin mutum ne Dan karami gajere sai katon kai da katon hanci Shi kanshi abin tsorone

Umarni ya basu da su zauna Zama sukayi

Cikin murya mara dadi yace Ajiye kudin dake jakanki.

Kallon yafindo karima tayi

Nuni tayi mata data aikata hakan Juyewa tayi

Kallonta yayi yace da wani abun kuma Girgiza kai tayi

To tashi Ku tafi

Har ta mike ta dawo ta zauna sai kuma tace Malam maganar yaran fa

Kallonta yayi yace

Basai da nace kada ki bari su hadu da mahaifiyarsu ba kika bari kuje Ku jira mai zai biyo baya kawai

Hajiya salma tace

To yanzu babu yadda za'ayi Bokan yace

Kije ki cigaba da sa wannan dan mutunmutumin a wuta har zuwa wani lokaci Amma ki sani koda wasa wani ya taba to zaki sami Matsala.

Girgiza kai tayi alamar Ta gane

Koda suka fito yamma tayi da kyar suka sami mota Hajiya

Please Login or Register in order to submit comment