You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mota aka bude musu suka shiga

Mutanen gari sai surutu sukeyi.

Daddy hamma kuwa Garin yake bi da kallo Cikin tsananin tausayawa Filin jirgi suka wuce Daga nan suka D'aga zuwa adamawa

Dai dai lokacin sallar La'sar suka isa Dan haka masallaci suka shiga kawai sukayi sallah Suna fitowa suka wuce d'akin iyalai haka suke cewa wajen domin Idan sarki zai Gana da iyalanshi nan ake zama

Wajen Fa mutane ne zaune

Bayan sarki sai daddyn yola gefe kuma daddy hamma ne

Ata Dayan hannun kuma daddyn Abuja ne sai Gefensa abba ne Dama dasu hajiya Salma Da hajiya Zainab ne sai hajiya yaya Matan sarki Fulani sai yafindo Hari sai yafindo karima

Daddy ne sai baffa suna facing d'in su daddyn Abuja K'asa kuwa Salim sai farouk sai haidar

Gefe kuma amra da ammar sai sumayya da Muhammad.

Kanwar sarki ce ta shigo hajiya delu Waje ta samu itama ta zauna Abba Ya bude taro da addu'a

Mai martaba ya Kalli baffa da daddy yace

Inaso na sani shin da gaske kune iyayen yaran nan na ainihi? Shiru sukayi

Daddyn yola yace

Shin ba tambayarku sarki yake yi ba? Baffa ya

farouk Ko haidar

Written by deeja one =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Kunason typing da yawa amma ku bakuyin comment yadda ya kamata

Zan dau minti goma ko ishirin ina typing amma ku Idan kun tashi Wani ma dakyar zai iya yin comment da Tnxs Wani kuwa t kawai zai sa

And kuma still kunaso nayi typing da yawa.

To mu taru mu gayra mana inyi typing me tsayi kuma ku tattauna Akan page d'in da nayi type d'in domin tanan zan gane me nayi kuskure ko badai dai ba.

Duk Wanda a Cikin ku yaga nayi ba daidai ba ka kasa gayawa mini to gaskiya ba masoyina

bane.

Like comment and share pls

Vote comments and follow @13deeja

Comments and forward it to other groups

Much love

Hafsat Hausa novel h² Khaleesat haydar Hausa novel

Kunfi sauran group comments Hakan nasa Ko banyi niyyar typing ba Idan na tuna daku sai Naji

inaso nayi.

Kada kuyi mini wata fassara ku Bari Kuji karshen littafina kada Wacce ta zageni pls. Nasan zakuce taya uwa zata yardar da yaranta to ku Bari na kai karshe tukunna pls.

24

Baffa yace

Eh ba Wai karya zamu fad'a ba

Dan murmushi daddyn yola yayi yace

To ai kunsan hukuncin Wanda yayi karya Dan haka munaji Dan numfasawa yayi kafin yace

Shekara ashirin da biyu data wuce wata Ranar alhamis na dawo daga gona ina tafe da fatanya ta sab'e a kafada.

Wata matace sanye da kaya na alfarma hannunta rike da jariri sallama tayi mini na amsa Bayan mun gaisa tace

Dan Allah bawan Allah ka taimaka mini da ruwa na bawa yarona kishi yakeji

Kallon yaron nayi sai Naji ya bani tausayi Dan haka na ajiye fatanyata na nufi Wani bingi Ya Debo ruwa akwanon sha Na kawo mata

Neman Waje tayi ta zauna ta bashi yasha Kallona tayi tace

Mun gode sosai sai dai motarmu na gaba kadan da Garin nan ko zaka taimaka ka daukar mini yarona Muje tare

Ganin irin wahalar datasha yasa na amsheshi Tana gaba ina baya har muka fito wajen motar Mace daya da maza biyu na gani.

Bindiga Dayan Ya sa mini. Matar ta juyo tace

Yaron dake hannunka yarona ne amma bana kaunar ganinshi saboda abinda mahaifinsa yayi mini ka rikeshi ka raineshi ka kuma bashi ilimi na Boko.

kasa magana nayi

babu damuwa Ko Wani fargaba ta bude motar ta shiga

Duka suka rufa mata baya har Sunyi nisa ta Leko ta window tace Sunanshi FAROUK......

Jan numfashi baffa yayi yace Wannan shine abinda na san ya faru.

Rumaisa kuwa fashewa tayi da kuka Cikin matsanancin tashin hankali tace Me marta......

Da sauri Ya D'aga mata hannu yace Bana bukatar kice komai Daddyn yola ya dubi daddy yace

"Kaine ainihin Wanda ya haifi haidar Girgiza Kai yayi yace a, a"

Yadda mal Adamu Ya bada labari kusan hakanne sai dai nawa bayan Na taso wajen aiki ne ta tsareni Akan na taimaka na rage mata Hanya tausayin data bani yasa na yarda na dauketa Kawai sai jin bindiga nayi akaina Tabbas abinda ta gayawa Adamu haka ta gaya mini kan cewa Dan tane Wanda ta Haifa sai dai ta tsaneshi saboda abinda mahaifin shi Ya Mata

Tanaso na bashi ilimi sannan sunanshi HAIDAR . Daddyn yola ya juya ya Kalli rumaisa Ya nuna ta yace Waccen ce

Baffa yace duk da shekaru sunja amma Tabbas itace.

Daddy yace

Ni tunjiya da suka fito daga mota tareda ita na ganta na tabbatar itace sai dai da yake bansan Meye dangantakarku ba yasa nayi shiru.

Kallonta duka yan d'akin keyi

babu abinda ke tashi sai gunjin kuka

Cikin tsananin kuka rumaisa ta durkusa tace Kuyiwa Allah ku yafe mini wallahi nayi nadama Daka mata tsawa daddyn yola yayi yace

Ashe bakida hankali har da zaki d'auki ya'yan Cikin ki ki Rabar a duniya Ansan modibbo yayi miki laifi saiki hukunta wa'inda basu sukayi miki ba. Daga mishi hannu Mai martaba yayi yace

Ya isa haka

Juyawa yayi Ya Kalli rumaisa yace

Mahaifiyarki ta mutu ta barku na daukeki na rainane ki bayan kin girma na daukeki na aurar dake ga dana Wanda na fiso bayan kaddara ta gifta kika dauka a laifi yayi miki yana sane na d'auka ahaka na hukuntashi da hanashi zaman kasarnan gaba d'aya.

Kika bukaci ki koma wajen Yar uwarki a Zaria na yarda kika koma

Kika zo mini a matsayin Kunyi hatsari jikokina sun mutu murus (lol) a wutar data tashi.ko gawarsu ba'a samu ba

Domin Kauda miki da kewa na aurar dake ga kaninshi domin wanke laifin daya yi miki .kika kawo mini korafin bakya haihuwa haka nasa yayan mijinki Ya dauki yaranshi har guda biyu ya baki Ashe duk shirine?

Kukanta ne ya tsananta.

Girgiza Kai Mai martaba yayi yace

Ni bazan hukuntaki ba Akan abinda kika aikata sai dai akwai Abu daya zuwa biyu dazan gindaya muku keda mijinki.

Juyawa yayi Ya Kalli daddyn baby (haka suke kiranshi dashi kasancewar suna kiran farida da baby)

Yace inaso ka d'auki matarka ku tafi taraba kada ka sake na k'ara ganin ta tako da sunan tazo gaisheni ko dubani Idan har Baso kuke na mutu ba sannan ku maidawa da Ahmad yaranshi danasa ya baku.

Kallonsu duka yayi yace sannan kada Kowa yazo mini da sunan Wai na yafe Mata ni banyi fushi da ita ba ta nemi yafiyar yaranta gasunan Idan sun yafe Mata shikenan.nidai bana bukatar k'ara ganinta a gidana.

Juyawa yayi Ya tafi

Wajen tsit yayi sai sautin kukanta daya ke tashi

Hajiya Zainab ta Kalli hajiya Salma ta kashe mata ido daya.

Ganin shirun yayi yawane yasa daddyn yola ya Rufe zaman da addu'a

A hankali mutanen ciki ke fita har sai da ya rage Daga su baffa sai su daddy

Sai rumaisa dake kuka sai daddy hamma daya kasa motsawa idanu kawai ya zuba musu.

A hankali ya mik'e nuni Ya musu dasu taho kowannensu iyayenshi ya kalla Murmushi sukayi musu Alamar su tafi mana

A sanyaye suka Karasa kusada shi janyosu yayi Ya rungume kuka ya fashe dashi yana fadin

Kuyi hakuri Laifina ne ya shafeku har yasa kuka Kasa samun soyayyar mahaifa. Hannunsu Ya rike ya juya ya Kalli su daddy yace

Ku shigo daga ciki mana.

Tab ai sai ka shiga gidan wato labari har ya zagaye gida Akan cewa anga yaran daddy hamma Kowa ina zai sakasu yake

Shidai modibbo yana rike da hannun yaranshi da kyar Ya samu Ya kutsa Tsakanin mutane bangarenshi Ya nufa dasu

Part ne na alfarma Dan kayan dake ciki daga gani kasan na Wanda yaci Ya tada kaine A kujera ya zaunar dasu shafa Kansu yayi yace

Yanzu ku gaya mini me kuke so

Farouk ne Wanda bakinshi yayi nauyi da kyar Ya bude baki yace Inaso nayi wanka

Hannunshi ya rike ya kaishi har bathroom Kamar ya mishi wankan haka yakeji Wai yaranshi kenan ikon Allah kenan

Zuwa yayi Ya zauna Ya zubawa haidar idanu Shidai haidar babu eh babu a'a

Ganin shirun yayi yawa yasa daddy hamma yace FAROUK KO HAIDAR?

Da kyar haidar ya bude baki yace haidar Kaine ke kaduna kenan

D'aga Kai kawai yayi

Wanda yayi daidai da fitowar farouk kallonshi daddy hamma yayi yace Ina zuwa haidar kaima shiga kayi wanka

Fita yayi Ya shiga Wani hadadden bedroom Wanda yake blue and white in colour Kaya ya ciro a hadaddiyar wardrobe d'in d'akin

Dakinshi Ya koma ya tarar da farouk tsaye gaban dressing mirror Mika masa kayan hannunshi yayi

Warwarewa yayi kayane hadaddu masu tsada da kyau Bakin Wando ne sai Riga light purple

Yana sakawa hakan ya haska fatarshi Kallonshi daddy hamma yayi murmushi

Wayarshi Ya ciro domin kiran dayake shigowa wayarshi duk na yan uwa ne da suke masa Barka da ganin yaran nashi.

Sai abokananshi dayake kira yana gaya musu ganin yaran nashi Haidar ne ya fito hakan yasa farouk yace

Ga kayan da zaka saka Amsa kawai yayi Ya saka

Daddy hamma yana ajiye Wayar Wani kiran ya shigo ganin daddyn yola yasa yana dagawa yace

Afuwan yaya wanka suka shiga yanzu suka fito mun Kusa fitowa

** *** *** ***

Bangaren rumaisa kuwa ganin babu Wanda yabi ta kanta ne yasa tabi ta kofar baya Ya wuce sasan yafindo Hari ta kwanta Tana Cigaba da kukan ta ahakan har zazzabi ya saukar mata.

Su haidar suka fitowa mutane suka kara taruwa Kowa Na murna

Wasu kuwa yake sukeyi kawai Kamar su hajiya Zainab da hajiya Salma Su dai su farouk burinsu kawai suga iyayensu haidar ya Kalli Yusra yace Inasu Mamie suke

Murmushi tayi tace suna bangaren Fulani

Can suka nufa yayinda duk inda suka wuce sai an kallesu domin Kamar da suke Gashi kayan da suka saka kala d'aya.

Kuyangu kuwa sai Mika gaisuwa sukeyi.

Acan kuwa suka tarar da su Mamie din Waje suka samu suka zauna babu Wanda yayi magana cikinsu

Dan murmushi Mamie tayi tace

Ikon Allah yau Babyn momma babu shagwaba kenan Dariya akayi duka dakin

Fulani ta karbe da cewa

Yo yayi shagwaba bayan yasan ya Girma Inna tace

Me martaba yace Sai jibi zamu koma shi a yadda yakeso ma mu dawo nan da zama to amma mun fison can din dai

Murmushi farouk yayi yace

Hakan yayi Dan banason zaman mu Anan

Kusan duk Wanda ke Falon beji dadin furucinshi ba Mamie tace

Amma kasan nanne gidanku ko? Shagwabe fuska yayi yace

Allah zamana a Cikin mutane da yawa sai sa mini matsala Dariya haidar yayi yace

Mamie Anan fa busa ke farkar Da mutum daga barci Dakuwa tayi musu

Dan murmushi farouk yayi yace Ina Salim

Mama tace Yana wajen garden d'in kusada fada Mik'ewa sukayi suka tafi domin zuwa wajenshi Ammar da Faisal ne zaune suke a balcony suna fira Sai da suka zo kusa da juna sannan ammar yace

Hi brothers

Kallonshi kawai farouk yayi Ya juya ya Cigaba da tafiya Haidar ne ma yayi k'ok'arin cewa

Sannunku da hutawa

Shima daga haka be k'ara ko A ba ya bi farouk da sauri.

typing is not easy oh. Ni daku one love



farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar 25

Salim yana hangosu ya Fara dariya

Da gudu haidar ya karasa

Shi kuma ganin haidar ya taho shima yasa gudun

Zagaye garden d'in suke yayinda Salim d'in be Dena dariya ba Su daddyn yola ne suka shigo wajen

Tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah

Haidar yana ganinsu yayi saurin Tsayawa ya daure fuska Gwalo Salim yayi mishi Wanda ya k'ara bashi haushi Apple dake gaban Wani saurayi yana d'auka Ya jefa masa

Kaucewa yayi yana dariya kara k'uluwa haidar yayi Wanda yasa kadan Ya rage yayi kuka Zaro idanu daddyn Abuja yayi yace

Meye haka?

Shidai Salim be Dena dariyar ba

Dakuwa daddyn baby yayi mishi kafin ya janyo haidar jikinshi Kyaleshi kawai

Farouk kuwa kallonsu kawai yayi Ya Kauda fuska

Tashi yayi Ya matsa Kusa da Salim d'an Marin fuskarshi yayi a wasa yace Shine sai ka gudu ko?

Dariya yayi yace

To me zan tsaya nayi muku tunda mun zama d'aya ai zaku nemeni.

Rumaisa ce tafe ta riko hannun fahad farida kuma na gabanta Daga gani karfin Hali take Dan ba Lafiya gareta ba

Sallama tayi musu suka amsa Kallonsu Salim daddyn baby yayi yace Ku Bamu Waje zamuyi magana.

Dasu da sauran wa'inda ke wajen suka Fara kokarin fita Farouk ma Ya juya zai fita

Daddyn Abuja ya riko hannunsa yace Malam ai harda Kai a Maganar

Sai da suka nemi Waje suka zauna sannan daddyn Abuja yace Ga mahaifiyarku tazo baku hakuri

Rumaisa hawaye na k'ok'arin zubo mata Cikin raunin zuciya irin na Mata tace

Dan Allah kuyi hakuri ku yafe mini nasan na cutar daku amma ina neman yafiyarku. Farouk Ko kallonta beyi ba

Haidar kuwa Yana jikin daddyn baby yana wasa da links d'in hannunsa Kamar badasu Take magana ba

Daddyn Abuja yace

Wai ba magana ake muku ba A hankali farouk yace

Me kace daddy bamuji bane

Tsabar mamaki Kasa cewa komai sukayi wato Dan rainin wayo ma basusan Tana magana ba kenan.

Links d'in hannun haidar daddyn baby Ya kabar yace Wai ba magana ake muku ba

Cuno baki haidar yayi yace Wayyo hannuna.

Kuka rumaisa ta fashe dashi Daddyn Abuja yace

Mamanku na neman yafiyarku kunji

Kada ku tilasta ma jikokina Akan abinda aka zalince su Juyawa sukayi da sauri

Mai martaba ne da daddyn yola

Nuni Mai martaba ya musu da su taho Da sauri suka karasa wajenshi

Shafa Kansu yayi yace Allah yayi muku albarka

Ameen suka had'a baki suka amsa. Wai waye farouk waye haidar dariya sukayi gaba d'aya

Haidar ya nuna kanshi yace Nine haidar

Murmushi Mai martaba yayi yace Aliyu gadanga kusar yaki Hannun farouk ya girgiza yace Jarumi Mara tsoro umar

Oya kuzo Muje kuga Garin adamawa Juyawa yayi Ya Kalli daddyn baby yace

Zan Saba maka Idan har na dawo na tarar da wannan a gidan nan. Tafiya suke yana jan su da fira

Wanda duk Wanda ya gani sai Ya tsaya Yana mamaki amma ganin wa'inda suka fi shekara ashirin da biyar basa mamaki saboda sun San soyayyar dake Tsakanin sarki da babansu haidar d'in.

A parking space suka tsaya inda motoci sunfi talatin suke a jere suna jiransu. Farouk ya Kalli me martaba yace

Bari na kira Salim

Dan murmushi yayi yace

Bazaku iya tafiya babu shi ba kenan dama jarabaku nakeyi nagani abotar Tana nan. Umarni ya basu da su shiga mota

Bude musu akayi suka shiga

Mai martaba ma Ya shiga Yana tsakiyarsu haidar yace

Gashi zamu tafi baka kira Salim d'in ba? Nuna mishi gaban mota yayi

Salim ke zaune Yana game a Waya Dariya haidar yayi yace

Wallahi Allah Ya taimakeka amma Bari Mu dawo zaka sani

A hankali motar ta Fara tafiya yayinda sauran motocin suka biyo su a baya Tafiya sukayi sosai kafin haidar yace da Mai martaba

Wai ina zamuje ne Siyar daku zanyi

Rufe bakin shi yayi yace Allah Ya huci zuciyarka

Duka yan Motan sai da sukayi dariya saboda yadda ya Wani zaro idanu ya kuma Tab'e fuska. Farouk kuwa murmushi kawai yayi Ya juyar da Kai

Wajen Wani k'ato halla sukayi parking wajen ya tsaru sosai. Ciki suka shiga direct

Daga gani mutanen wajen Manya ne

Sai dai ana yiwa sarki iso suka Mike gaba d'aya Bayan ya zauna su haidar dai na Kusa dashi.

Mik'ewa yayi Godiya sannan ya gabatar dasu haidar a jikokinsa da suka bace Ya k'ara da cewa Shiyasa Nace

Bari nazo dasu ku gansu na kuma gabatar dasu

Kowa a wajen taya sarki murna yakeyi da ganin jikokin nasa Sannan masu yi musu kyauta sunayi

Kafin atashi Daga wajen sai da suka sami kyautar miliyan Dari uku da dubu tamanin da biyar da motoci Guda goma sha biyu da filaye guda takwas gidaje guda biyar

Masha Allah farin ciki wajen sarki ba'a magana domin yanason me son abinda Ya fito daga jikin modibbo

Sai wajen hudu suka bar wajen

Gaba d'aya Dan anci an sha Kowa yayi murna

Wajen Wani guri suka wuce Kamar company ginin irin storey building ne Mai Martaba ya Fara shigar dasu wajen Wani garden yace to ku jirani Anan kafin na fito six.

Zama sukayi shi kuma ya wuce Ya tafi Yana Mai farin ciki.

A bangaren rumaisa kuwa kuka me tsanani ta Cigaba domin gani take Kamar sun rabu kenan gashi sai yanzu tayi Tana tsananin son yaranta.

Daddyn Abuja yace

kadai ji me Mai martaba yace ko

Dan haka ka bata hakuri ku tafi kawai Daddyn baby yaje ya dafata yace

Kiyi hakuri ki taso Mu tafi taraba may be Idan muka bi umarninsa ya yafe miki Hawayen ta goge tace

Ka rokeshi yayi hakuri ya Bari mu koma South Africa. Cikin matukar tausayinta yace

Zan rokeshi.

Dagata yayi tsabar Jikinta babu karfi Kamar zata fadi haka takeji. Bangaren yafindo Hari ya kaita

Ita ma dai hakuri da kwantar Mata da hankali ta rinka yi. A haka ta tashi ta shiga wanka

Ta shirya

Daddyn baby yazo Ya dauki kayan Ya kai mata mota

Yafindo Hari ta rikota suka fito Dan Tsayawa tayi Tana kallon bangaren Fulani A sanyaye tace

Idan na shiga bazata yi mini komai ba Cikin tausayawa yafindo Hari tace Wallahi ban saniba

A hankali tace Muje wajenta.

Nan suka tarar da su mama da Inna Mari da Mamie sunata fira Sallama sukayi suka shiga

Fulani tace

Me zan gani haka bakida Lafiya ne Hawaye Ya gangaro mata ta tsugunna tace Ki yafe mini jafar miki da jikokin ki da nayi. Dagota Fulani tayi tace

Kada kice haka ai yaranki ne duk yanda zan shiga tashin hankali Bai Kai Wanda zaki shiga ba ganin gaki gasu amma bakida damar kije Kusa dasu sannan ki sani ba karamin sa'a kika taka ba ubangiji na sonki da rahama Shiyasa Ya dawo dasu kinada rai amma Da Ya zakiyi da hakkinsu ubangijinki ya miki kyauta kin nuna bakiso.

Kuka ta kuma fashewa dashi tace Wallahi nayi nadama Fulani

Allah Ya yafe mana baki daya Allah Ya kyauta gaba. Tana Gama fadin haka tayi gaba abinta.

Kallonsu Mamie tayi tace

Na gode sosai da kuka rike mini yarana da amana abinda na kasayi kuka aikata Allah Ya saka da alkhairi Inna Mari ta ce

Kada ki da mu da na Kowa ne ai

Juyawa tayi yayinda yafindo Hari ta riketa suka tafi

A parking lot suka had'u dashi sun Gama sallama da daddyn baby kenan Kallo d'aya yayi mata Ya dauke Kai

Cikin sanyin jiki ta shiga mota

Fahad da farida ne suka taho da gudu suka rungumeta Mommy ina zakije baki tafi damu ba

Hawayen fuskarta ta share tace Yanzu nake shirin kiranku

Amma kuje ku dauko takalminku ke kuma ki hado da hijab To da sauri suka amsa

Suka juya da gudu domin su dauko.

Kuka ta fashe dashi lokacin da driver yaja motar Gidan ta kuma Juyawa ta kalla

Tabbas daddyn baby tausayi take bashi Driver yacewa Fara kaimu modibbo hospital. Acan suka tarar da daddy da daddyn yola Magani aka bata sannan suka tafi

To Nidai Anan nake cewa Allah Ya kiyaye hanya Ameen

Haidar d

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

26

Sai shida da Rabi sannan Mai martaba suka fito daga meeting din Duka mik'ewa sukayi suka shiga mota

Haidar yace da Mai martaba

Dan Allah mu biya shopping mana D'an murmushi yayi yace Shopping ni kuma

Had'e rai yayi yace Eh mana

Ya riko hannunshi yace

Haba aliyu da girmana da kimata ace zan je shopping kuma. Juyaddakai yayi yace

Ai daga yau mun bata

Dan murmushi yayi yace Da driver Ka kaimu modibbo shoprite.

Haidar Abin mamaki yake bashi Idan yaga sarki na bin abinda haidar yakeso A fili yace ikon Allah

Suna parking ya kallesu yace kuyi sauri Make kafada haidar yayi yace

Sai dai mu shiga tare Zaro idanu sarki yayi yace Ni mu shiga tare kace fa? Cuno baki yayi yace

Eh mana

Kallon dogaransa yayi yace Ku mu shiga

Kowa a wajen mamaki yakeyi Dan basu tab'a ganin sarki yazo shopping da kanshi ba

Su Kansu ma'aikatan na wajen mamaki sukeyi Manager ya fito da sauri yace

Ranka ya dade da kiranmu kayi ai da munzo Hannun farouk ya rike yace

Kaga wa'inda suka kawo ni nan shopping suke so Shi kanshi yayi mamakin jin abinda sarki yace

Kujera aka kawo mishi Ya zauna yayinda suka shiga siyayya Kowa sai da ya d'auki abinda yakeso sannan suka fito

A gajiye suka taho

A hanya suka wuce Wani suya spot daru haidar yasawa sarki sai da ya tura aka siyo musu Bayan sun Fara tafiya ya dubi haidar yace

Amma mamienku na kokari Ya dubi farouk yace

Bakaga yadda Dan uwanka yake ba Turo baki yayi yace

To aishi daban ni daban. Dariya Salim yayi yace

Wlh Mai martaba Ko a makaranta haka nake fama dashi Dan murmushi farouk yayi yace

Kake fama dashi ko nake fama daku kaima ai ba baya bane. Dariya Mai martaba yayi

Yace

Kace kana kokari

Ya mutsa fuska Salim yayi yace Mai martaba wasa yake fa.

Mai martaba yace

Gashinan ko yanzu kayi ma.

Dariya akayi gaba d'aya yayinda farouk yayi murmushi. Suna isa direct masallaci suka wuce

Sai da sukayi sallar magrib da isha sannan suka shiga Cikin gidan. Daddyn yola yace

Mai martaba tun d'azu muke sa ran ganinka mukaji shiru har muna tunanin bin hanya. Dan murmushi yayi yace

Ina tare da tagwayen maza ne Dariya sukayi gaba d'aya Abba yace

Yanzu dai an soke mana walimar yau kenan Eh gobe ayi Idan yaso jibi sai su tafi.

Su Salim kuwa hanyar shiga bangaren su sukayi Daidai lifter suka had'u da Faisal da ammar as usual Faisal yace

Ikon Allah akarade har an tafi yawo Allah yasa ba ku bane jikokinsa na farko balle ku dinga

tinkaho.

Dan murmushi gefen baki farouk yayi Ya bude lifter ya shiga Ammar ya riko hannun haidar yace

Ka bawa Dan uwanka hakuri and congrats for been part of this family Faisal da mamaki yake duban ammar

Murmushi haidar yayi yace

Tnxs bro sannan zai fi kyau Ka bashi hakurin da kanka. Yana Gama gayan haka ya bude lifter ya shiga

Salim yabi bayanshi A zuciye Faisal yace Me hakan ke nufi

D'aga kafada yayi yace

Nifa bazan Cigaba da munana musu ba alhalin yan uwanane su. Da mamaki Faisal yace

Kenan bazaka tayani yaki dasu ba kenan

Calm down my brother yanzu fa su yan uwanka ne wane yaki kuma ana zaune Shikenan tunda ka koma tsaginsu

Yana fadin haka ya tafi ya bar ammar a tsaye

Haidar kuwa suna shiga Kamar yadda suka Zata har ya shiga wanka yana fitowa Salim ya shige shima haidar ya shiga

Husuma ta tashi Tsakaninsu kan Wanda ya Riga Farouk yana jinsu yayi banza dasu

Dan Kansu suka gaji suka Bari

Salim ya Fara wankan sannan haidar

Blue t shirt da Wanda blue black suka saka duka Su ukun Suna bud'e kofa daidai ammar ya karaso dariya yayi yace Kaga yan ukun Mai martaba

Duk da haushin shi da farouk yakeji saida Ya murmusa. Kallon farouk yayi yace

Am sorry

Kara Had'e rai yayi Ya juya ya tafi

Duka jikinsu sanyi yayi Dafashi Salim yayi yace

Kayi hakuri zamuyi masa magana

A bangaren Fulani suka sameshi shida daddy hamma suna zaune da alamu magana sukeyi Daddy hamma yace

Yauwa haidar karaso nan mana

Inaso ku yafewa mahaifiyarku kunji ko Shiru sukayi Kamar basa wajen

Haka ya gaji da magana ya kyalesu Wayar farouk ce tayi k'ara

Da sauri Ya D'aga

Muryar Indo yaji Cikin kuka take cewa

Yaya farouk kaje adamawa ka manta dani ko? Runtse idanu yayi yace

Kin taba ganin mutum Ya manta da numfashinsa? To Idan ni numfashin kace meyasa ka ki kirana Kada k damu kina zuciyata

Ya gaya Yana d'ora hannunsa daidai zuciyarshi

Haka suka dinga fira har ta yanke Alamar kudin Ya k'are Salim ya Kalli haidar yace

Nifa Ina mamakin mutumin dayake nuna shi babu ruwanshi Agefe kuma tantirin Dan iskane Wai kin taba ganin mutum Ya manta da yin numfashi

Ya gaya yana nuna yarda farouk yayi Filo ya jefa masa yana dariya

Da sauri yayi hanyar stairs

Dan Tsayawa yayi Ya saka hannunshi a daidai saitin zuciyarshi Ya Lumshe idanu yace Kada ki damu kina zuciyata

Da sauri farouk ya Mike zai bishi

Salim kuma ya juya da gudu Da Mamie yaci Karo Wanda yasa tayi saurin cewa Kai Kada ku karyani banga yan dagwai dagwai ba

Dago fuska yayi yace Nasu wa kenan Naku mana

Rufe fuskarshi yayi yana Wani kakkare jiki Kamar an bude kwaila Tana wanka. Dariya haidar ya kuma tuntsirewa dashi.

Dariya harda hawaye

Daddy hamma daya ke kallonsu tun d'azu yayi Ajiyar zuciya

Salim yaja hannun Mamie ya zaunar da ita ya kwantar da kanshi a Jikinta Mama tace

Me zan gani haka maza dagata Shafa kanshi tayi tace

Barshi kinji dama kwana biyu ba'a hadu ba. Gwalo yayi wa haidar

Haidar yace

Yaro ni jikin umma zan kwanta Dan Had'e rai farouk yayi yace Bakada Kai ne salon ka karyata Mama tace

Kai farouk wannan qeqe da qeqen fa wato kada a karya maka uwako Da sauri Ya juyar da Kai yana murmushi Dan yama manta suna wajen Hannun haidar Inna Mari ta rike tace

Ai suma yarana ne

Dariya Salim yayi yace Bari na baki labarin yadda

Please Login or Register in order to submit comment