You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

salma tace Kice mama wannan gama aikine Yafindo karima tace

Kamar kinsani yar uwa amma fa da sharadi

Hajiya salma tace

Meye sharadin? Yafindo karima tace

Zaki kai kanki wajensa ma'ana zaki bashi kanki( ) Murmushi tayi tace

Babu matsala allah ya kaimu gobe

Ai ni indai bukata zata biya to ko meye zan aikata

Jira nake agama da wannan ma sai mu koma kan wancan idan yaso daga baya naji da ubansu shi fa atunanunshi son yaranshi nakeyi

Dariya suka Kara shekewa dashi suka tafa kamar wasu kawaye(allah ka sa mufi karfin zuciyarmu ameen)

Washegari suka tafi wajen malam din

Babu laifi yanada tsafta watakila ko dan yana cikin garine oho Yafindo karima a waje ta tsaya ita kuma ta shiga ciki

Wajen awa uku sannan ta fito a hargitse Da mamaki yafindo karima ta kalleta Cikin matukar galabaita tace

Mama muje gida kawai

Tun a hanya tafara barci Dan haka suna komawa ta kwanta bata farka ba sai bayan magrib. Tana cin abinci tace da yafindo karima

Gobe zan je Zaria daga nan zan shiga kano a matsayin zan duba wancan Dan iskan yaron. Dariya yafindo karima tayi tace

Hmm aike kam naga kinfi tsanarshi ne da sauri tace eh mana. Firarsu suka cigaba.

Washegari da wuri ta shirya ta tafi

Amra kuwa sai murna take yau mamanta zatazo

Yaya muhammad ya kalleta ya tabe baki sai daf da isha tazo Amra ta shirya komai sai murna take kamar me

Sun sha fira sosai sannan ya muhammad ya dauketa ya kaita wajen mama kasancewar basuda nisa da juna

Acan ta kwana

Washegari Abba yace dama suma sunaso su koma Dan haka su mama suma suka shirya Suna isa kano asibitin murtala suka wuce Domin can akayi transfer dinshi

Gaskiya duk Wanda yaga halin dayake ciki sai ya tausaya mishi Domin idan ka ganshi zakace barci yakeyi sai dai fa rama dayayi. Cikin tausayawa mama tace

Allah ya yaye maka Hajiya salma tace Ameen.

Suna zaune su salim suka shigo

Da kallo mama ta bisu su kansu duka sun rame kadama salim yaji labari Dan shi dama bai iya sa abu araiba.

Gaishe dasu sukayi sannan mama ta Kara musu nasiha akan su Kara hakuri cuta ba mutuwa

bace

Haidar yayi ajiyar zuciya yace

Nanda next week ma zamu wuce adamawa ai

Ok allah ya kaimu but dan allah Ku Kara hakuri kunji Allah zai bashi lafiya Jinjina kai sukayi

Haidar ya kaisu sarina domin sure gaisa da sure baffa Hajiya salma dai ruwa batasha agarin ba ta tattara ta tafi Ita kuma mama sai da akayi magrib sannan suka tafi.

Haidar kuwa a sarina zai kwana tunda yanzu shifting sukeyi idan haidar ya kwana yau gobe salim jibi audu

Sai dai wajen juyashi da goge masa jiki shine sai da safe idan wani yazo acikin su sai su hadu

su biyu suyi.

Bayan sati daya mai martaba ya zo aka shirya aka maida su adamawa

Koda aka maidashi adamawa abubuwa sunyi sauki tunda yanzu sukan hadu suyi jinyarshi da yawa

Faisal kam tuni ya fara aiki amma su haidar mai martaba babu fadan da be musu ba amma sunce su bazasuyi aiki ba tareda farouk ba

Bayan an kwana biyu ya sake tarasu ya Nuna musu yanzu sun girma fa ya kamata susan da hakan

Duk yadda ya bullo musu abu ya gagara karshe harya fusata yace Kamar baku yarda da kaddara ba yanzu kuma idan mutuwa yayi fa ? Kuka salim ya fara mishi yana fadin bazai mutu ba

Haidar kam tabe fuska yayi

Ganin abin Nasu da gaske sukeyi yasa ya tattara ya zuba musu idanu Sun je aiken da mai martaba yayi musu sun dawo

Haidar ya ajiye maganin akan bedside table ya shiga wanka Salim kuma ya kwanta

Kamar a mafarki yaga idanun farouk na neman budewa Cikin farinciki ya fara kwalawa haidar Kira

Ba shiri haidar ya daura towel ya fito.

farouk ko haidar

https://www.facebook.com/groups/156937

* FAROUK KO HAIDAR*

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~ *

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~D'we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our

creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*

written=ØŠÝ By Deeja One Love Written by deeja one love=ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

46-47

A hankali ya bude idanunshi

Maidawa yayi ya lumshe idanun domin haske yayi mishi yawa Da sauri salim ya tafi sanar da su mai martaba.

Cikin farin ciki suka taho

Kowa so yake yayi mishi magana amma abu ya gagara domin koya bude baki da nufin yin magana sai abu ya gagara

Hamdala mai martaba yayi yace Da alamu sauki ya fara samuwa

Kan lokaci kankani har labari ya bazu a family haidar ya bude idanu. Kowa murna yakeyi domin sauki ya fara zuwa

Momma kuwa tanaji har hawayen farin ciki sai da tayi Daddyn baby ya na ta tsokanarta

Murmushi tayi tace

Ni dai idan allah ya kaimu gobe zamuje ko? Kallonta yayi yace

Da wannan cikin naki zakije a'a gaskiya sai kin haihu Shiru tayi bata kuma cewa komai ba

Daddare tana zaune Tana tsefewa baby kai.

Mararta taji ta murda Mata cikin dabara ta zame kan baby ta mike A bedroom ta sami daddy yana aiki da laptop

Kallonta yayi Cikin kulawa yace Ya dai ko da matsala ne?

Girgiza kai tayi

Kan ta yunkura juwa ta kwasheta Da sauri daddy ya tarota

Daukarta yayi cak ya nufi parking lot da ita. Koda suka isa hospital da sauri aka amsheta 50mins ta haifo yaranta guda biyu duka Mata Bakin daddyn baby ya kasa rufuwa

Sai buga waya yakeyi

Salim na zaune yana Danna waya kiran daddyn baby ya shigo Kallon haidar yayi dayaketa shakar barcinshi

Daga wayar yayi Cikin farin ciki yace Mamanku ta haihu

Ihun murna salim yayi.

Cikin sauri salim ya bude ido yana mazurai Kallon salim yayi ya dalla mishi harara Yace

Kai dai wallahi akwai banza Muna barci kawani tasheni Kafin salim yace wani abu an bude kofar an shigo Yafindo hari

Cikin sauri salim ya rungumeta

Da haidar da farouk zuba musu idanu Da mamaki salim yace

Wai mai ya faru ne? Salim ya washe baki yace Momma ta haihu

Da gudu haidar yazo ya rungume salim Murna kam ba'a magana

Farouk kuwa da idanu yake binsu. Ga abin murna amma babu dama Murmushi yayi

Haidar yace

Lah! Ji nawan yana murmushi

Ranar dai Kwanan farin ciki familyn sukayi

Washe gari da wuri yafindo karima da yafindo hari suka tafi taraba Ana sallamota daga hospital suka wuce da ita adamawa.

Suna isowa suka sami gida ya cika da yan uwa Kowa na kokarin daukar yaran

Hannun haidar ta rike tace Ina dan uwanka

Murmushi daddyn baby yayi yace Muje ki huta sai kije anjima mana Daga kai tayi badan ranta yaso ba Bangaren fulani ya kaita

Ruwa mai sadi tayi wanka dashi

Kafin ta fito an ajiye mata tuwon dawa da miyar kubewa yaji man shanu Sai da taci ta koshi sannan ta kwanta

Daddyn baby da yafindo hari suka shigo da babies a hannunsu Ajiyesu sukayi

Yafindo hari ta juya ta fita

Kallon daddyn tace

In taso muje ka kaini wajen farouk din? Murmushi yayi yace

Ina zuwa

Bai dade ba suka dawo tareda fulani Yace

Fulani ga yaran nan zamuje ta dubo farouk Fulani tace

Kekam ki bari ki huta mana Daddyn baby yace

Fulani Barta muje kawai idan ba haka ba yau bazata barni na huta ba Murmushi fulani tayi tace

Adawo lafiya

Har bangaren mazan ya kaita Salim yana kwance yana barci Haidar kuma yana wanka

Da idanu ta bishi yayi haske sai dai ya rame Murmushi yayi Mata

Hannunshi ta rike tace Ya jikin

Lumshe idanu yayi ya bude Haidar daya fito daga bayi yace Momma har kinzo ganin jikinshi Daga kai tayi alamar eh

Ya Dora da cewa

Ai ma ya sami sauki

Kallon salim yayi ya daka.mishi duka yace Tashi kallallaba

Harararshi farouk yayi ya kauda kai Momma tayi dariya tace

Ah lallai jiki da sauki tunda an iya harara Duka sukayi Dariya

Yafindo karima ta kira hajiya salma tace Kinji rumaisa ta haihu

Hmm naji mana jiya.mijinta ya kira hamma ya gaya mishi. Ta gaya cikin takaici

Yafindo karima tace To yaushe zakuzo Nisawa tayi tace Sai ranar laraba

Allah ya kaimu dole idan kinzo mu koma wajen malam din nan Ana Jibi suna su ammar da mutanen kano sukazo

Yan zaria da yan kaduna suma sunzo

Gida ya cika masha Allah

Ammar ya kalli amra yace

Ki bari anjima idan aka tafi sallar magrib sai mu duba Jinjina kai tayi alamar to

Da yamma yafindo karima tace Bari zuwa anjima mu karasa shi

Su kuma yaran gobe idan an gama taron suna Murmushi hajiya salma tayi tace

Ai gwara ayi ta ta Kare kawai

Ana kiran sallah kowa yana haramar shiga masallaci Amra ta Kira ammar tace

Bro yafindo karima ta shiga toilet kayi sauri Yana ajiye wayar cikin sauri ya kalli faisal yace Ka tanaji ashana kazo wajen garden

Da sauri yace To

A bakin kofar ya tarar da amra Kallonta yayi yace

Muje

Suna shiga suka fara bincike bincike

Kaf duk Indiana suke tunanin gani sun duba amma basu ganshi ba Amra ta tsugunna kasan gado ta janyo wani akwati

Cikin sauri ta bude ta ciro kayan ciki Da sauri suka fice

A garden suka Tarar da faisal zube kayan sukayi Wannan karamar randar

Ammar ya daga

Yafindo karima ta fito daga bayi Kallon gadon tayi

Zaro idanu tayi ta dafe kirji Da sauri ta leka window

Ganin aika aikan da su ammar suke shirin yi yasa ta kwallara kara Dai dai lokacin dasu mai Martaba suka dawo masallaci

Jin Kara yasa suka nufi garden

Suma dake cikin fada suka fito da gudu

A rikice yafindo karima ta zubo da gudu tana fadin kada ka fasa Zaro idanu hajiya salma tayi itama tace

Ammar kada ka aikata

Su mai martaba kallonsu kawai sukeyi domin basu fahimci me ake nufi ba Ammar ya kalli faisal yace

Action

Murmushi yayi ya banka musu wuta Ammar ya bugata da kasa ta tarwatseee

* FAROUK KO HAIDAR*

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~ *

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~D'we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our

creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*

written=ØŠÝ By Deeja One Love

Bashier sufyein ina gaisuwa sosai duk da kwana biyu naji shiru Allah ya kara hazaka yasa kafi haka

Ameen 48-49

Gidan gaba daya yayi baki wani bakin hayaki ya fara fita daga cikin fasashshiyar tukunyar Ihu yafindo karima tayi lokaci guda fuskarta ta koma baka.

Farouk kuwa ji yayi kamar an kwanceshi daga daurin da aka masa Cikin sauri ya mike ya fito

Ganin harabar gidan babu kowa yasa shi nufar garden

Yana isa wajen yafindo karima tayi ihu ta shaki wuyan hajiya salma tana fadin Sun lalata mana komai kinga abinda yaranki sukayi mana

Mun shiga uku zamu mutu Na gaya miki zamu mutu.

Hajiya salma kuwa idanu yayi jajir domin ba karamar shaka tayi Mata ba Cikin sauri su hajiya zainab suka kwaceta

Ihu ta kumayi ta fara fuzge fuzge

Duk wani kulle kulle da sukeyi sai da ta fada tanayi tana soshe soshe 'Ya'yanta kuwa kuka suka farayi

Mai martaba ya bawa doagarai umarnin da su kamata su kaita cikin turu. Mai martaba ya dubi mutanen wajen yace

Kowa ya shigo ciki

Bayan kowa ya zauna daddyn yola yace

Salma munaso muji meke faruwa? ko kuma nace mai ya faru? Kuka ta fashe dashi tace

Dan Allah Ku yafe mini wallahi nayi nadama Daddyn yola ya daka Mata tsawa yace Tambayarki fa akayi mai ya faru?

Hawaye ta share tace

A lokacin da mahaifinmu ya rasu muka dawo nan gidan tun lokacin nakeson hamma

Sai dai hankalinshi kwata kwata baya kaina yana kan yar uwata Ganin hakan yasa na fara kishi da ita

Nayi bakin ciki lokacin da akayi bikina da abbansu ammar

Amma duk da haka ban saduda ba kuma ban Dena son hamma ba

Lokacin da akayi auren rumaisa da hamma naji bakin ciki sosai sai dai babu yadda zanyi

Ana haka watarana mama ta kirani a waya kan ta sami wani malami da zai mini aiki mun dade muna ja in ja da ita kafin na amince

Farkon aikin daya fara mana shine kashe abbansu ammar

Domin babu yadda za'ayi na auri hamma ba tare da aurena ya mutu ba

Bayan malamin ya tura aljani ya kasheshi sai mukaji labarin rumaisa nada ciki ansha tura Mata aljani ya sace cikin amma abu ya garara saboda yawan addu'arta

Da hakan bai samu ba sai muka sa aka kwance tayar motarta duk da haka muka bita abaya nida mama har sai da muka ga konewar motar sannan muka juya muka koma wajen malamin Aranar ya bani maganin da nasawa hamma har ya fara sona

Abin ya bamu mamaki da mukaji bata mutu ba

Alokacin mama tace mu koma a kasheta sai dai na nuna a'a

Hakadai har tayi convincing dina akan cewa idan fa ban kasheta ba to lallai har yanzu sunada abinda ya hadasu wato 'ya'ya

Wannan yasa na yarda domin banason abinda zai hada hamma da rumaisa

Wannan yasa muka koma ya bamu magani akan mu sa Mata a abinci hakan zai Kara Mata kiyayyar hamma kuma zai sa tayi duk abinda muka sata

Sai layar da muka binne Wanda hakan shine zai sa bazata taba cewa mu muka sata ta yar da yaran nata ba

Haka kuwa akayi muka bawa zainab ta sa Mata a abinci ta kuma ci Ni na Kira ta a waya tace da ita akan ta cewa halima zata taho Babu musu tace to

A hanya mama ta tareta suka je kaduna suka fara bayarda haidar sannan suka wuce kano suka bayar da farouk kuma mu muka tsara abin ya zama kamar hatsari ne.

Duk da haka bamu kyalesu ba mama ta kuma cewa mu koma wajen bokan a samusu ciwon da zai dinga wahalar dasu

Haka muka koma wajenshi ya bamu amma da sharadin cewa duk ranar da asirin mu ya tonu to daya daga cikin mu zai haukace

Haka muka yarda dan a tunanin mu asirinmu bazai taba tonuwa ba

Mun so a tura musu aljanune sai dai inda suke akwai kariya sosai wannan yasa hakan bai yiwu ba

Duk da haka sai akayi amfani da yawan zuciyar farouk aljanun suke shafarshi shi kuma haidar sai akayi amfani da yawan kallace kallacenshi aka turo wanda suke taba idanunshi

Ta kwashe sauran abinda ya faru ta gaya musu Tsit wajen yayi

Sunkuyad da kai tayi tace

Dan Allah ina neman yafiyarku Ku yafe mini Amra ta mike tace

Wallahi bazai taba yiwuwa ba kullum kina yaudarar mu akan mahaifinmu rasuwa yayi

Ashe kasheshi kikayi ashe ba sonmu kike ba Daddyn yola yace

Ya isa haka amra koma ki zauna Komawa tayi ta zauna tana Kuka

Kowa shiru yayi yana jiran hukuncin da mai martaba zai yanke Gyaran murya yayi yace

Alhamdulillahi abubuwa sun faru da yawa a wannan familyn to mu godewa allah da hakan ya faru domin idan har yana sonka ne sai ya jarabceka

Dan haka komai ya faru zamu dauka a matsayin jarabawa

Ni yanzu bazan yanke muku hukuncin komai ba sai dai zan barku da Allah shi yasan mai. Yafi dacewa daku

Sannan magana ta karshe shine nidai allah ya gani koda Dan uwana ya mutu ya barku nayi dai dai iya yanda zanyi Ku sami kyakkyawar tarbiya Allah kuma yana sheda

Don haka tunda hakan ya faru zaki koma bayan gida da zama sannan ki nemi yafiyar wa'inda Kika yiwa laifi idan sun yafe miki shikenan

Ran da kika kashe shi kuma keda mahaliccinki. Yana gama fadan hakan ya mike yayi cikin gida

Tashi tayi tana kuka ta dubi daddy hamma da rumaisa tace Dan Allah Ku yafe mini

Ajiyar zuciya daddy hamma yayi yace Allah ya yafe mana gaba daya

Ita ma momma abinda ta fada kenan Su haidar da farouk ta duba tace

Nasan na cutar daku sosai na raba mahaifiyarku da mahaifinku na rabaku da juna na raba Ku da lafiya amma duk da haka ina neman yafiyarku

Haidar yayi murmushi yace

Komai ya wuce mummy Allah ya yafe mana Farouk yayi ajiyar zuciya yace..............

* FAROUK KO HAIDAR*

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~ *

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~D'we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our

creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*

Written=ØŠÝby deeja one love

Dedicated to madina m umar

50-51

A sanyaye farouk yace

"""Allah ya yafe mana gaba daya"",kowa yaji dadin abinda ya fada."

Sai da aka kai ruwa rana sannan amra da ammar suka yafewa mahaifiyarsu.

Sai da suka koma bangarensu sannan salim yace

"""Ashe farouk ya farfado""."

Dariya haidar yayi yace

"""Baka ganshi ba sai yanzu"",Murmushi kawai yayi yace ""Kyaleshi haidar neman magana ne kawai kalar nashi""."

Matsowa salim yayi yace

"""Wai ya akayi ka Tashi ne?,Shiru farouk yayi."

"A ranar cikin farin ciki suka kwana,sai dai da safe aka wayi gari da yafindo karima ta mutu,"

Mutuwar da ta sa jikin mutane da yawa yayi sanyi.

"Bayan anyi suna hassanar aka sa mata sunan inna Mari wato mariya suna ce Mata islam,hussaina ita kuma taci sunan mamie wato khadeeja suna ce Mata iman."

Suna yayi yadda ake so sai dai muce Allah ya raya Islam da iman.

"Bayan kwana biyu da suna kowa ya fara shirin tafiya ,"

"Haidar da salim sun tafi kasuwa domin siyayya,farouk kuma yana kwance."

Momma tayi sallama ta shigo kallonshi tayi tace

"""Mai yasa bazaku zauna anan ba?"

"""Saboda can yafi dadin zama"""

Ya bata amsa atakaice.

Shiru tayi na Dan lokaci kan tace

"""Saboda me kace haka?""."

"""Saboda can babu hayaniya da yawa """

Ya Kara bata amsa .

Riko hannushi tayi tace

"""To farouk mu tafi taraba tare mana"""

Murmushi yayi yace

"""Momma duk yadda zamuyi bazai yiwu ba saboda su baffa da daddy gani zasuyi kamar ke muke so mu dawo wajenki;"

Jinjina kai tayi alamar ta gamsu Farouk ya Dora da cewa

"""Kidai bari kawai mu dinga kawo miki ziyara amma bazai yiwu ace Dan mun hadu da iyayenmu"

"ba muce zamu juya musu baya""."

Numfasawa tayi tace

You have a point.

"Fira suka cigaba da yi har su haidar suka dawo , Nan suka dinga shirmensu ,"

Farouk dai murmushi kawai yakeyi Momma ta girgiza kai tace

"""Ku wallahi bakwa girma har yanzu kuna abu kamar kananan yara"""

Ta mike ta fita.

"Washe gari da wuri suka dauki hanya,sai da suka ajiye su farouk a kano sannan suka wuce,ana"

zuwa Zaria su salim suma suka wuce gida.

"Bayan wata biyu daddy hamma ya fara Gina musu tafatsetsen hospital a cikin garin yola, daddyn yola yaso ya sama musu aiki amma sukace su basa son na gwamnati abarsu da private"

din da daddy ke gina musu.

"Yanzu indo anzama yan Mata ta Kara wayewa sosai, Dan lokaci zuwa lokaci takanje Zaria ko kaduna har taraba ma wajen momma,"

Su Islam kuwa watansu uku amma sunyi Wayo sosai da sosai.

Shekara mai zuwa indo zata zana waec da neco hakan yasa farouk ya dage da koya Mata

abubuwan da bata Sani ba.

Farouk ya gama shirin shi na zuwa Zaria Indo ta shigo dakin daga bakin kofa ta tsaya.

Hade rai tayi kallonta kawai yakeyi yana murmushi.

"Hawaye ya gangaro daga idanunta still kallonta kawai yakeyi,ganin yaki cewa komai yasa ta fara bubbuga kafa a kasa"

Kusa da ita ya matso yace

"""Humaira tsaya kiji""."

Girgiza kai tayi ta turo baki gaba tace

"""Nidai kawai yaya farouk kaje dani"""

Ajiyar zuciya yayi yace

"""To jeki shirya kayanki""."

"Tsallen murna tayi da sauri ta juya ta tafi,girgiza kai yayi yace"

"""Humaira rigima ""."

Cikin lokaci kankani ta gama shirinta cikin tsokana yace

"""Wai ni na rasa mai kike zuwa yi Zaria kodai kinyi saurayi acan ne?, Rufe fuskarta tayi tana dariya."

"Sai karfe biyu suka shiga zaria a gidan hajiya zainab suka fara yada zango,"

Cikin murna faisal yace

"""Ah lallai wannan Karon anyi abin kai "" Murmushi kawai farouk yayi ."

"Sai da suka ci abinci suka huta,sannan faisal ya kwashesu a mota suka tafi gidansu salim,"

a bakin get ya ajiye su sannan ya wuce wajen aiki.

"Suna shiga ya samu husna da yusra suna ta dambe akan hijab, Sun cika gidan da hayaniya,"

Yanayin sallama kowacce ta natsu.

Yace

"""Ina mama?"

Da sauri sukace

"""Ta tafi kasuwa amma bazata dade ba zata dawo"","

"""Ina salim"""

"Ya Kara tambayarsu, ""Yana bangarensu"""

Be ce komai ba ya mike ya tafi har ya wuce ya dawo yace

"""Ku cigaba da damun mutane tunda Ku bakusan me yake muku ciwo ba"""

"Sunkuyad da kai sukayi ""Oya bani hijab din"""

"Da sauri yusra ta mika mishi,"

Amsa yayi kawai ya wuce.

"Yana tafiya husna ta bata rai tace ""Wannan fa yazo kenan wallahi"""

"Humaira tayi dariya tace ""Ko na kirashi ne?"

"Cikeda kuluwa yusra ta harareta tace ""Kirashin mana"","

"Cikin tsokana humaira ta fara kwala mishi Kira,"

Husna ta dau filo ta bita dashi humaira ta haye sama tana dariya.

"Farouk kuwa yana zuwa ya sami salim sai sharar barci yakeyi , Ajiye jakarshi yayi ya shiga bathroom yayi wanka ,"

Sai da ya gama shiryawa sannan ya tasheshi.

Da mamaki salim yace

"""Yaushe kazo?"

Harararshi farouk yayi yace

"""Taya zaka San nazo kato da kai kazo ka kwanta kana shakar barci""."

"Dariya salim yayi yace ""Wallahi nagaji ne """

Farouk yace

"""Wai ka gaji to me kayi daka gaji?"

Salim yace

"""Kai dai bazaka gane bane kawai"""

Girgiza kai farouk yayi yace

"""Shiyasa ai kaji dadi da har yanzu ba'a fara aiki ba ko"", Dariya salim yayi kawai."

Da yamma mama ta dawo ta tarar dasu farouk Da farin ciki tace

"""Maraba da mutanen kano, ai dama tunda naji gidan shiru babu hayaniyar wa'inann marasa jin nasan kazo""'"

Murmushi kawai yayi.

Bayan sun gaisa ne tace

"""Zakuje amsa kiran mai martaba ne?,daga kai kawai yayi."

"Washe gari da wuri suka wuce kaduna,sun tarar da haidar yana hospital din su daddy."

Salim yayi dariya yace

"""Kaga namiji jarumi"",harara haidar ya galla mishi yace"" kafa fita idona kallaba kawai"",farouk ya harari haidar ya kauda kai."

"Indo kuwa sai murna take domin kuwa tareda su husna suka taho,tunda tazo ko farouk ma bata"

"nema ba,shima kuma haka be nemeta ba."

"Da safe yaya adnan ya kwashe su sukaje gidan amare,bayan sun fito ne suka wuce companyn motoci kowa ya zabi wadda yake so,da farouk da salim kala daya suka dauka baka range rover"

sai haidar daya dauki camry new model 2008 ash in colour(ruwan toka).

"Cikin farin ciki suka dawo gida,kowa ya tayasu murna,yaya adnan kuwa yasha"

"godiya,murmushi kawai yayi yace""komai nayi muku ban fadi ba kannena""."

Daddy yana dawowa suka bashi labari shima ya tayasu murna sosai.

"Washe gari suka wuce adamawa kowa da motarshi,farouk ya dauki indo,salim kuma surayya da"

"husna,haidar kuma sumayya da yusra."

Sun iso ana kiran sallar magrib wai a hakan ma sunyi sauri sosai(kun San dai yadda mutum

yake idan aka bashi sabon abu especially abinda ya shafi ride ).

"Masallaci suka fara wucewa sai da sukayi sallah sannan suka shiga gidan,shidai farouk"

"bangarensu ya wuce,da haidar da salim kuma bangaren fulani suka wuce."

"Sai da yayi wanka sannan yaje ya samesu,shirmen da suka saba shi suke tayi dai,fulani nayi"

musu dariya.

"Tsaki farouk yaja yace""wallahi kudai baku girma ,anan suka ci abinci sannan suka wuce"

"bangarensu,wajen wankan ma sai da suka Kara raba hali sanana sukayi."

"Ana idar da isha suka biya suka gaida sarki,cikin farin ciki ya tare su har yana Jan su da wasa."

"Washe gari da safe bayan sun karya,wani dogare yazo ya tsuguna yace""ranku ya dade mai martaba na nemanku a falonshi"""

"Salim ya amsa da ""kace muna zuwa"""

"Dogari yace""yace Ku taho da kannenku"""

Salim ya kuma bashi amsa da to.

"Sai da suka biya bangaren Mata na gidan suka dauki su sumayya sannan suka wuce,a zaune"

"suka sameshi bangarenshi na dama fulani bangaren hagu kuma yafindo hari,sai faisal da ammar akasa,suma kasan suka nemi waje suka zauna."

Mai martaba yayi gyaran murya yace

Alhamdulillahi abinda yasa na kiraku shine kunsan dai cewa yanzu kune akan layi.

"Haidar ya dago yace ""layin me?,mai martaba yace""aure,dariya abin ya basu."

"Da mamaki mai martaba yace""meye na dariya?ya isa haka kai ammar ga yar uwarka nan yusra,farouk ga humaira nan,haidar ga surayya nan,faisal ga husna nan,salim kaida sumayya."

* FAROUK KO HAIDAR*

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~ *

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~D'we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our

creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u

np pain~*

written=ØŠÝ By Deeja One Love

Bashier matafiya uku munji shiru fa ya kamata a duba mu.

52-53

"Shiru sukayi domin basuda ta cewa,mai martaba yace""bakuce komai ba""."

"A sanyaye ammar""mun gode Allah ya saka da alkhairi."

"Haidar zai yi magana faisal ya take masa kafa,dagowa yayi ya kalleshi shi kuma ya galla masa"

harara.

"Murmushi mai martaba yayi yace""masha Allah naji dadi Allah ya muku albarka,da sauri suka"

Amsa da ameen.

"Suna fita haidar yace""gaskiya banji dadi ba a rasa wacce za'a bani sai wacce muke sa'a,salim"

"dariya ya dinga yi,cikin jin haushi ya bishi da gudu,ganin ya taho shima yasa gudu."

"Faisal yace""ai wallahi za'ayi kallon shirme,shidai farouk bece komai ba."

"Mai martaba kuwa daddyn yola ya Kira yace ya kira members na family nanda three weeks bikin su farouk,duk wanda aka Kira sai yayi murna idan yaji cewa tare da bikin bude asibitin za"

ayi.

"Sai da suka Kara kwana sannan suka tafi taraba,kowa zolayarsu yake akan angwaye,duk da"

"babu mai

Please Login or Register in order to submit comment