You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar makarantar kafin muzo bikin su saifullahi.

Kashe Wayar tayi ta Mike tana safa da marwa Tabbas bata shirya barin daular datake ciki ita da ya'yan ta ba.

Madam Zainab ta Kalli Faisal tace

Ka Nemo mini marasa ji na makarantar nan.

Bayan ya kawosu ta kallesu tace

Aikin zan baku Wani nakeso Kuyiwa dukan tsiya amatsayin fad'a kukayi Zaro idanu sukayi dayan yace

Tab amma madam ina fatan baki manta Meye hukuncin Wanda aka Kama Sunyi fad'a a makarantar nan ko

D'aga Kai tayi tace

Kada ku damu zan San yadda zanyi ku dawo Kun yarda

Ta tambayesu Eh

Suka bata amsa Nuna musu hotonshi Tace da Faisal

Wayarshi Ya Danno hoton Kallonshi sukayi suka ce Ai munsan wannan guy d'in To shi

Angama sai balance dinmu

Kudi Faisal ya ciro Ya Mika musu yace

Ga dubu talatin nan Idan kun Gama aikin naku zan cika muku. Cikin farin ciki suka amsa suka tafi

Farouk kuwa suna isa suka kirashi suka gaya mishi Bayan sun Gama Wayar ya wuce cafe

daga can library ya wuce

Sai after eleven sannan ya tafi daki ya kwanta

Washegari kasancewar Sunada tutorial eight yasa da wuri Ya shirya Kallon Hafiz yayi yace

Zo Muje school cateen na siya Wani Abin naci Kiran farouk ne ya shigo wayanshi

Da sauri Ya D'aga yace Yaya kun taho

Eh yanzu dai zamu taho yaya Adnan zai kawo mu Cikin farin ciki yace to ni yanzu ma tutorial zan tafi Adawo Lafiya

Allah yasa kuma haka

Hannunshi rike da cake Dayan kuma yoghurt.

Bangajeshi yayi Wanda yasa Abin hannunshi gaba d'aya ya zube Shi kanshi sai da ya Kusa faduwa

Hafiz da sauri Ya tarboshi D'agowa yayi Ya kalleshi yace

Haba kana gani ka bige ni ai ko hakuri ka bani Hannu yasa ya bugeshi a kafada yace

Ko zaka Rama ne?

Cikin fushi haidar ya Kai mishi naushi

Suna daga gefe sukayi saurin tasowa suka rufeshi da duka Dakyar sauran mutanen suka rabasu

Wasu suna basu Rashin gaskiya wasu kuma suna bawa haidar d'in Jan hannun Hafiz yayi suka tafi

Ranshi a bace har suka Gama tutorial din

Suna dawowa ya kwanta Akan gado barci ya d'aukeshi Cikin barci Hafiz yazo yana tashinshi

Bude idanu yayi yace Ya akayi ne?

Hafiz Cikin kaduwa yace

Yanzu nagani a notice board Wai ana nemanku a admin block office din co-ordinator Mik'ewa yayi yace

OK Bari nayi sallah naje

A can ya tararda wai'nda sukayi fadan Tana hakimce Akan kujerarta ya sameta Murmushin mugunta tayi tace

Amsa

Hannu yasa ya amshi takardar Takardar expelling from school ce Ta Dora da cewa

Makaranta ta sallameka saboda fadan da kukayi. Murmushin gefen baki yayi yace

Well done Ya juya ya fita.

A daki ya sami Hafiz jiki a sanyaye ya tareshi yace Ya akayi ? Murmushi yayi ya Mika masa takardar

Kallon shi yayi yace

Innalillahi yanzu ya zakayi.

Zan jira yaya Adnan Idan ya kawo su Nawan zanji me zaice. Kiran farouk ne ya shigo wayanshi yana dagawa yace Gamu a main get kazo ku gaisa da yaya Adnan

OK Ya amsa

Kallon Hafiz yayi yace

Kada ka damu gasu nan sun iso Suna tsaye ya samesu

Yaya Adnan ya kalleshi yace

Babyn momma kaga yanda ka rame kuwa dariya yayi yace

Hmm Wlh karatu yaya

Kace gwara da bakazo ba da yanzu Mamie ta tada hankalinta Yanzun ma data ga Salim da farouk fad'a tayi Wai basa cin abinci ne

Ina da ace ta ganka

Murmushi haidar yayi yace

Yaya ba wannan ba anyi expelling Dina daga school Atare suka ce me?

Basu labarin meyafaru yayi Jinjina Kai yaya Adnan yayi yace Bari na kira daddy Naji me zai ce Kiranshi yayi Ya gaya mishi Cewa yayi suje office din HOD

Tunkan su karasa har ya kirashi Yana zuwa ya bashi appeal ya cike Kallonshi yayi yace

Ku dinga kulawa pls Jinjina Kai kawai yayi Office din ta ya koma Kallonshi tayi tace Au baka tafi ba Murmushi yayi yace

Kada ki damu amma dai ki sani Wani yafi Wani nasha gaya miki Idan baki kyaleni ba zanyi sanadiyar barin ki wannan kujerar and ga wannan ki ajiye zai miki amfani Idan kinzo sallamar Wani

Mik'ewa tayi tace

Get out from my office now Murmushi yayi yace

K

Dama yanzu zan fita ko baki gaya ba sannan ki sani yan daban da kika haya Sunyi kokari Dariya yayi sannan ya juya ya fita.

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Am so sorry for not hearing from me two days Wlh kaina ne ya dau zafi sosai yauma kaina ciwo yakeyi kuyi hakuri da wannan

16

Table d'in gabanta ta buga da karfi Cikin Tsakanin fusata tace

Da sake wallahi zaka San ni ka mayarwa martani. Sauri suketa yi Dan 7 sukeda lectures

Farouk ya harari Salim yace

Duk bakai ka janyo mana ba Dariya Abin ya bashi

Sai da ya dara sannan yace

Kai Dan uwa kaine fa ka janyo mana Sallama haidar yayi Ya shigo Kwanciya yayi kafin yace

Da wannan Maganar dama shiryawa kukayi kuka tafi kawai. Sai 4 suka dawo

Bokiti kawai farouk ya d'auka Ya tafi tap Salim yace

Nidai Wlh satin nan guduwa gida zanyi Dariya haidar yayi yace

Tab ai gaka ga Nawan nan kana ganin zai Barka ka tafi. Ya mutsa fuska yayi yace

Wlh nagaji over yau

Dariya haidar ya tuntsire dashi.

Ganin Abin nashi da wulakanci yasa shi cewa Wlh zan mintsineka

kasa tsayar da dariyar yayi Hararshi Salim yayi yace Hmm zaka sanine.

Eh naji babu komai

Sai da sukayi sallah sannan farouk ya Dora musu abinci Suna ci suna shirmensu har suka Gama

Salim yace

Yauwa Dan uwa yau mu Dan shiga gari mana. Daga Kai yayi Alamar to

Sun shiga sabon gari kasuwa filin polo Wajajen silver daga nan Sukaje

Pz.

Dariya haidar yayi yace

Dan allah Nawan mu karasa Republic mana.

Kayan kwalam suka kwasa daganan suka koma makaranta

Cikin satin suka Fara jarabawa a lokacin haidar ya Fara Rashin Lafiya Hankalinsu ya rabu kashi biyu ga karatun jarabawa ga rashin Lafiyarshi. Ganin hakan yasa shi daurewa domin gudun tada musu hankali

A daddafe ya tsaya aka Gama exam din

Kasancewar shi Ya Fara gamawa yasashi cewa zai tafi Kallon shi Salim yayi yace

Haba mutumina ka bari mu karasa tamu nan da upper week sai mu tafi tare Girgiza Kai kawai yayi Ya Cigaba da had'a kayanshi

Shidai farouk binshi da kallo kawai yakeyi. Haidar me wasa da dariya tunda har ya damu ya tafi

to beda Lafiya sosai ne

Kallonshi ya mayar kan Salim yace

Ka kyaleshi Ya tafi mana may be akwai abinda yakeson yi ne Kamar zaiyi kuka Salim ya Kalli haidar yace

Kodai bakada Lafiya ne? Daga Kai yayi Alamar a'a

Cikin nutsuwa farouk ya kuma cewa Tashi Muje mu rakaka.

Jikin Salim a sanyaye suka tafi Har dad'i motor park suka kaishi Salim yace

Wlh sai inaji Gabana na faduwa Murmushi haidar yayi

Ka yawaita addua.

daga can makaranta suka koma

Washegari da safe dukansu sauri suke domin su tafi jarabawa Farouk yaceda Salim

Kaga fa har yanzu Nawan be kiraba Salim yayi Ajiyar zuciya yace

Ka bari Idan muka dawo sai mu Kira Mamie

Sai biyu suka fito alwala sukayi suka farayin sallah sannan farouk ya kirata Tana ta ringing ba'a D'aga ba

Jinjinawa farouk yayi Tabbas akwai abinda ke faruwa Ya ilahi Allah yasa me kyau ne

Salim ya katse masa tunaninsa da cewa Itama taje kuwa

Eh amma ba'a D'aga ba

Cikin tashin hankali Salim yace Allah yasa dai Lafiya

Ameen.

Kusan kwana uku Ranar suna zaune

Farouk yana operating system yayinda Salim ke Karatu Karar wayan farouk ne ta dakatar dasu

Kallonshi ya Kai kan Wayar da sauri Ya d'auka Sallamar ya amsa kafin ya gaisheta

Ta Dora da cewa

Yi hakuri Wlh Wayar na gida banma bi ta kanta ba sai yau Ajiyar zuciya yayi yace

Wlh mamie har gabana Ya fadi Yake tayi tace

Ai kuwa to ku kwantar da hankalinku. Farouk yace

Mamie ina Nawan na kira wayarshi akashe

Sun fita tareda Adnan.

To Idan ya dawo kice ya kunna wayarshi.

Insha Allah Ta gaya Tana sauke Wayar Daga kunnenta Shafa gashin kanshi tayi Tana share kwallar data zubo mata. A bangaren su farouk kuwa Yana kashe Wayar

Salim yace Me ya faru

Murmushi yayi yace

Lafiya lau Wai yanzu ma sun fita tareda yaya Adnan.

Ganin yau paper d'aya sukayi kuma itace last paper yasa Salim damun farouk Akan su fita. Kallon shi yayi yace

Ka damemu mu fita ina Kake so Muje ne. Republic mana

Kwaikwayar muryarshi yayi

Wai Republic kace kawai zomuje kwadayi Dariya Abin ya bashi.

Jan hannunshi yayi suka tafi Ahanya Salim ya kalleshi yace Wlh na kosa abba Ya bani mota Murmushi farouk yayi yace

Kuma kana tunanin waye zai hau mota kana tuk'awa Shafa gefen bakin shi yayi yace

Kai da haidar mana Dariya yayi yace

"Allah Ya tsare Bamu shirya mutuwa ba,nifa nayi mamaki da Har yanzu haidar be kiraba Anya lafiyanshi kuwa."

Tunda mun Gama exam ba sai Muje ba. Salim ya bashi amsa

Maganar shice ta tsaya saboda had'a idanu da sukayi Cikin mamaki Ya zuba musu idanu

Nunashi da yatsa Faisal yayi Alamar yazo Jan dogon tsaki yayi

Da mamaki Salim yace Yadai Kake tsaki

Duba kaga wancan mata mazan tareda Wani Dan daudu Dariya Salim yakeyi

Cak dariyar ta tsaya ganin su gabanshi Zaro idanu yayi yace

Ammar

Yafi minti biyar kan yace Kai wama Kake da suna? Sunkuyadda Kai yayi yace

Salim

Faisal yayi murmushi yace

Ana tareda Wanda yafi Dan uwane Da mamaki ammar yace

Me?

D'aga Kai Faisal yayi yace Exactly haka wannan yaron yace Shafa kanshi ammar yayi yace

Tab da sake wallahi ai Idan yafi ka ni be fini ba ko? Shidai Salim kasa cewa komai yayi

A zafafe Faisal ya Kalli farouk yace

Kai karamin Dan Iska ai Naji labarin kaje ka yiwa mummy Rashin kunya to ka sani ina nan zan zo kanka.

Farouk kuwa ko kallonsu be yiba Hakan ya k'ara hasala shi Wuyan rigarshi ya riko yace

Kai ina magana kana jina

Hannu farouk yasa ya kwace rigarshi yace

Ni bana fad'a da mata maza Idan akwai namiji a gidanku ka turo shi. Cikin zafin zuciya Faisal ya wanke farouk da Mari.

Shima dai farouk d'in mari ya wankeshi dashi

Kan yace komai ya kara wanke shi da Wani Marin. Tab ai duk Wanda ke wajen sai da ya juyo

Mutane Nata mamakin yau an Mari Faisal kasancewar Kowa yasan halinshi na Rashin mutunci sannan duk Wanda ke yawan zuwa republic yasan shi.

Ammar Ya ce

Kai wannan waye haka Kai kasan waye Ka mare shi kuwa? Kallon Faisal yayi yace Lallai brother ka tsaya yayi downgraded dinka.

Huci kawai Faisal yakeyi yayinda farouk yadda kasan bashi yayi ba Ammar Ya dubi Salim da jikinshi yayi sanyi yace

Ah lallai kana kallo ana wulakanta Dan uwanka ko da kyau

Idanun Salim har ya kawo ruwa kallon farouk yayi jiki a sanyaye yace Dan uwa Dan Allah mu tafi Ni Kake janyowa matsala.

Har sun Fara tafiya ammar Ya riko rigar farouk ta baya Kallon Salim yayi yana huci yace

Na d'auka Rama mishi zai yi.

Sai a lokacin Faisal ya sami damar Jan numfashi idanu jajir ya farawa farouk kallon zakasan koni waye.

Ammar ya dubeshi yace

Kai baka iya bada hakuri bane Farouk yace

Ai ni yayi wa laifi sannan Bana iya bawa Wanda ya mareni hakuri. Cikin zafin zuciya yace

Wai Kai Dan isakan inane?

Murmushin gefen baki yayi yace

Ka bari Ranar daka shiga sahun maza sai ka tambayeni Mari ammar ya Kai mishi

D'aga hannu yayi zai Rama Salim yayi saurin rikewa Idanunshi na zubar da hawaye yace

Baka nema mini zaman Lafiya farouk kazo Mu tafi please Da mamaki ammar yace

Ramawa da zakayi.

Har zai yi magana Salim ya Rufe mishi baki a sanyaye yace Please.

Juyawa Salim ya yi yace Da ammar Kayi hakuri.

Suna barin wajen mutane suka fashe da dariya Wanda hakan ya tunzura Faisal Motarsu suka shiga

Cikin bacin rai yaja motor Kallonshi ammar yayi yace

Take it easy mana ba haka zamu barshi ba. Shidai Faisal be ce komai ba har suka isa gida.

farouk Ko haidar

Written by deeja one love=ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Ina Godiya agareku wa'inda suka kira sukayi mini sannu da wa'inda sukayi flash kuma duka ina Godiya Kai harda wa'inda basu kiraba.

Love u to the moon and back 17

Suna isa gida suka tarar da Hajiya zainab a zaune Tana Waya Kashe Wayar tayi sannan ta kallesu tace

Har kun dawo

Ammar Ya Jinjina Kai yace Eh wanine Ya Mari Faisal

A rude take tambayar waye haka? Idanu jajir Faisal yace

Waye kuwa banda wannan Dan iskan farouk d'in. Cikin sanyin jiki tace

Kyaleshi kawai wannan yafi karfin na hukuntashi. Murmushi ammar yayi yace

Amma ai befi karfin my dad ya hukuntashi ba ko? Murmushin mugunta tayi tace

Hakane kam gaskiya ka birgeni haka akeson Dan uwa me kishin Dan uwansa.

Yanzu me zakayi?

Ta tambayeshi Cikin fara'a Bari ki gani

Wayarshi ya ciro Ya dannawa babanshi kira

Yana dagawa ko gaishe shi beyiba Cikin shagwaba na ya'yan masu kud'i yace Dad yau Wani ya mareni a Zaria

Cikin mamaki dad d'in yace What?

Ya mareka meya had'aku ?

Wai Dan munje Wani oasis da Faisal shine Yazo Ya takani ina magana ya mareni shima Faisal yana cewa kasan Ko Dan gidan wa ka mara?

Ya kira sunanka

Cikin Rashin kunya ya mareshi shima Wai inmun isa mu d'auki mataki. A zuciye daddyn yace

Wallahi ko Dan gidan waye sai na hukuntashi ba'a taba mini yara na kyale. Bari zan kira general din dake nan Jaji ka sanshi ai.

Bazan ganeshi ba sai dai ko Faisal. An gama

*** *** ***

Dalibaine sama da Dari biyar tsaye suna hada hadar tafiya kasancewar duk kusan an Gama jarabawa a pharmacy dept.

Cikin su na hango farouk da Salim Salim yace

Kaga yau Idan muka kwana a gidanmu zuwa jibi sai Muje kaduna mu dubo ya haidar yake Daga nan sai ka wuce Kano in wuce Zaria tunda kaga nanda four weeks za'ayi bikin su yaya Mubarak.

Me Keke napep suka tare

Tsayuwar motor sojoji yasa suka tsaya da shiga Salim yace

Su kuma wa'innan Ko Lafiya.

Daya daga Cikin sojojin ne ya bude wayarshi kallon pic din yayi Ya Kalli farouk Da hannu ya mishi Alamar daya zo.

Salim yace

Bro me ya had'a ka dasu. Daga kafada yayi Alamar Be saniba.

Kallon sauran yayi yace Ku sashi a mota.

Obeying suka yi

Be musu gardama ba ya shiga.

Salim Cikin tashin hankali ya taho da sauri amma kan ya karaso har sun ja sun tafi Awajen ya tsaya kawai

Students dake wajen Kowa da abinda yake fad'a

Wani course mate dinsu ne ya Dafa kafadarshi yace

Ba Tsayawa zakayi gida ya kamata kaje ka gaya domin kasan ba imani garesu ba zasu iya kasheshi.

Zufa Ya share kafin ya hau napep su tafi. Daidai bakin get aka saukeshi

Ko me gadi yasan yau babu Lafiya tunda duk fita da shiga Idan yanayi sai yayi masa magana amma yau Ko kulashi beyiba

A main parlour Ya tarar da su husna. Sannu da zuwa sukayi masa

Husna tace

Yaya lafiyanka kuwa? Yusra ta Dora da cewa

Ina yaya farouk kace tare zaku zo Ajiyar zuciya yayi yace

Ina mama

Tana dakin abba Can ya juya ya tafi

A can kuwa Ya tarar da ita Zama kawai yayi

Abba da mama har suna hada baki wajen tambayar Lafiya? Sojoji sunzo sun tafi da farouk fa

Da sauri suka Mike suna salati

Mama Cikin Tsakanin tashin hankali tace Me yayi musu?

Babu komai mama

Nan ya basu iya labarin abinda yasa sani

Dan yama manta da sun sami sabani dasu ammar Mama tace

Innalillahi yanzu ya za'ayi? Abba yace

Bari zan nemi Wani abokina dake barrack Naji Ko yana can Har dare dai babu labari

Gashi su yaya Muhammad basa nan Dan ya tafi adamawa (saboda zuwan su ammar da k'anwarshi amra)

Kuma biki ya kawosu.

Salim Cikin tashin hankali yake ya kasa koda cin abinci Da safe abba yace

Ba'a gaya wa iyayenshi ba a tada musu da hankali ba Mu bari muga abinda Allah zai yi Nisawa mama tayi tace

Allah Ya kyauta

Salim dai Cikin rana daya ya zabge ya rame kodayaushe rike yake da waya yana trying number dinsu haidar da farouk amma babu Wacce Allah Ya bashi sa'a ta shiga.

To tashin hankali ba a sa mishi rana Allah Ya kyauta.

Mama kuwa she keeps asking kodai akwai Wani Abin da suke a makaranta Wanda basu Sani

ba

Akodayaushe amsa d'aya yake bata itace su Allah ne shaidarsu. Yau ma tun safe abba Ya fita domin bibiyar ina yake

Da yamma Salim na zaune Kamar kodayaushe Waya ce a hannunshi Idan yayi trying number din wannan sai Ya koma na wannan.

Mama ce ta fito daga daki Wanda yayi daidai da shigowar abba Kusan had'a baki sukayi wajen tambayar

Andace anganshin?

Zama yayi yace har yanzu maman Mubarak. Kallon shi tayi tace

Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun Ya Allah ka dubemu Ka dubi iyayen yaron nan ka kiyayeshi aduk inda yake.

Mama ta Kalli Salim tace

Wai kuma babu abinda kuke aikatawa Wanda bamusan dashi ba? Allah ne shaidarmu.

Nisawa tayi tace

To Idan fa akwai Ya kamata ku gaya mana Dan musan me zamuyi. Kallon ta Salim yayi yace

Haba mama Idan baki bada shaida Akan Abin da zamu aikata waye zai bada. Ya karasa Maganar muryarshi na rawa.

Abba yace

Ya isa haka Allah Ya kyauta in Allah Ya yarda za'a ganshi. Share Hawayen daya zubo masa yayi yace

Abba Wlh bama aikata komai mama ce kawai ke sa zargi aranta na rasa Ya zanyi haidar tunda ya bar Zaria wayarshi bata shiga shikuma farouk anzo an Kamashi ita kuma Kullum Tana zargin mu

Tsakanin da Da uwa sai Allah

Sai Ya bata tausayi tasan iya shakuwa sun shaku Gashi duka ba'a da makama Janyoshi Jikinta tayi tace

Kada ka damu kaje kayi wanka kaci abinci kazo na kira maka mamien taku. Mikewa yayi jiki a sanyaye ya fita

Da idanu suka bishi

Abba Ya Fara Cewa kamata yayi ki dinga rarrashin sa bawai kina k'ara masa damuwa ba Cikin sanyin jiki tace

Yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halinsu ba amma Yana bani tausayi wallahi duk barkwanci

irin na Salim amma ya koma Wani shiru

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

18

Suna zaune suna breakfast da safe Wayar mama tayi ringing Koda ta D'aga bayan sun gaisa

Audu yace

Dama mun kira ne muji Lafiya kuwa tun jiya muke jiran ganin farouk ya dawo amma shiru mun kira wayarshi akashe mun kira ta haidar itama haka itama Ta Salim a kashe

Shine na kira Mamie tace Wai basu zo ba to shine muka kira mun san sunanan Mama tayi Ajiyar zuciya tace

Abdallah (Dan haka take ce mishi) Kai da waye a wajen ?

Ni kadai ne Ya bata amsa

Bashi labarin meyafaru tayi

Audu banda innalillahi wa'inna ilaihirrajiun babu abinda yake cewa

Abba ne ya amsa Wayar ya kwantar masa da hankali sannan yace kada Ya gayawa Kowa Amsawa yayi da to

Yana kashe Wayar Wani kiran ya shigo Ganin Mamie Daga kaduna yasa ta D'aga Bayan sun gaisa tace

Yanzu Dan uwan farouk ya kira yana tambayar Lafiya? Hmm Mamie Kedai Bari nan ta kwashe labarin ta bata Salati tayi sannan tace

Ai be kamata ku zauna bakuyi informing kowaba ya kamata har iyayenshi ki gayawa saboda kada a sami matsala fa

Jinjina Kai tayi tace Insha Allah zan gaya musu yanzu ya za'ayi Nisawa Mamie tayi tace

Gaskiya Kinga nima haidar wallahi tunda ya dawo bayada Lafiya Dan Ranar ko barci bamuyi ba jiyane ma Allah Ya Fara kawo mishi sauki

Abinda yasa ma ban gaya.musu ba kenan saboda kada hankalinsu ya tashi Ayya Allah Ya bashi Lafiya Ko zuwa gobe zamu shigo mu duba shi.

Mama ta fad'a

Amsar Wayar Salim yayi yace Mamie ina haidar

Cikin lallashi tace

Yayi barci amma zuwa anjima Idan ya farka I promise zan hadaku

Sannan pls kada ka sawa kanka damuwa Kaji gobe Idan Allah Ya kaimu zaku taho nan Kaji kuma haidar ba Lafiya gareshi Ko kanaso kazo ya ganka a damuwa shima Ya shiga Cikin Ta? Girgiza Kai yayi kafin yace

"A, a"

Yauwa to Naji mama tace ka rame to kayita cin abinci kafin gobe ka maidar kibarka. Still dai D'aga Kai yayi yace

To

Yauwa to me zan dafa maka

Danbun Dawa?

Dariya yayi Ya Rufe bakinshi da sauri Yauwa my boy sai kun zo

Cuno baki yayi yace

Bakince zaki hadani da haidar ba

Eh zan had'aku Idan ka kwantar da hankalinka kada kuma ka gaya mishi komai To Ya bata amsa

Yauwa my boy take care of yourself bye Kashe Wayar yayi sannan ya mik'awa mama Murmushi yayi daya tuna Wai

"""Dambun Dawa """

Mikewa yayi yayinda mama da abba suka bishi da kallo rabon da sukaga farincikinsa haka har sun manta ma

Lallai haduwarshi dasu farouk akwai alkhairi.

Mama ta kira Audu ta gaya mishi Akan ya gayawa su mamanshi Koda ya gaya musu hankalinsu tashi yayi

Karshe sai da baffa yasa ya kira abba Ya kwantar musu da hankali Akan gobe zasu je kaduna suji yadda za'ayi

Baffa yace

Nima idan Allah yaso zamu taho gobe

Yaso ya hanashi sai kuma ya ga gwara ya barshi Suna gama Wayar ya Kalli matanshi yace

D'aya sai ta shirya gobe mu tafi Duka suka amsa da to

Kallon juna sukayi Wanda yasa Inna Mari saurin sunkuyadda Kai Murmushi baffa yayi yace

Yau soyayyar d'anki tasa kin kasa kawaici Ko Girgiza Kai tayi tace

A'a taje kawai ai duk dayane

Amma duk da haka addu'a take Allah yasa Inna hadiza tace taje kawai Cikin ikon Allah kuwa tace

Babu komai yaya kije kawai Sai ku tafi da Audu

Eh hakane Allah Ya kaimu goben Ameen suka amsa gaba d'aya.

Washegari suka shirya suka d'auki hanyar zazzau Suna isa fly over Audu ya kira Salim ya gaya mishi Mukullin mota Ya d'auka Ya tafi domin daukosu Suna kan hanya kawai yayi murmushi

Audu dayake yana gaba Ya kalleshi yace Ya akayi ne

Tunawa nayi da ana gobe za'a d'auki farouk muke fira Nace mishi

Na kosa abba Ya bani mota

Dariya yayi tareda hawaye yace Kasan me yace

A'a Audu ya bashi amsa Cewa yayi

Kuma waye zai hau mota kajashi Nace mishi shida haidar Hawayen Ya share yace

Cewa yayi Wai basu shirya mutuwa ba

Sai Gashi baya nan yau an bani na dauko ku inama yana nan ya gani Dafa shi Audu yayi yace

Kada ka damu zai dawo sai ka bashi labari Murmushi yayi yace

Aikuwa zanso Naji amsar da zai bani Had'e rai yayi yace

Kai a shiriritar ka ka tuka mini iyaye. Yanayi yana kwaikwayan muryarshi

Dariya duka sukayi su baffa kuwa tsananin tausayin shi ne ya kamasu Suna isa gida suka tarar da mama da abba sun shirya

Cin abinci sukayi sannan suka D'auki hanya Salim ke driving Audu na gefenshi

A tsakiya kuma abba da baffane Sai husna

Can karshe kuma mama da Inna Mari ne da Yusra Tafiya suke Kowa da tunaninshi

Yusra dai da husna murna sukeyi yau zasu had'u da sumayya da suke yawan Waya da ita Sai a lokacin suka tuna

Kallon juna sukayi Ta madubi sukayi murmushi Husna tace

Baffa Wai meyasa baka taho mana da Indo bane Murmushi mama tayi tace

Humaira zaku ce ko Aisha Dariya baffa yayi yace

Har kuka tayi zata biyo mu Nace a'a Abba yace

Kayya daka sani ka taho da ita Baffa yace

Rigima zata zo tayi ta mana Bakin get din sukayi horn Me gadi yazo Ya bude

Suna shiga Cikin gidan Salim ya fada jikin Mamie yace Ni Wlh na gaji

Dan bubbuga bayanshi tayi tace

Me yafaru ka gaji

Cuno baki yayi yace

Ba abba bane ya sani driving Dariya tayi tace

Au kace tare kuke amshi Mukullin parlourn baki ka kaisu can Kallon su mama tayi tace

Sannunku ku zauna na barku a tsaye Mama tace

Babu komai

Dan murmushi tayi tace

Wlh ya'yan Nawane akwai rigima Mama ta Kama baki tace

Ba 'a magana Inna Mari tace

Aikuwa dai Allah Ya kyauta

Gaisawa sukayi sannan sukayi mata ya Mai jiki Jiki Da sauki

Salim ya dawo jikin Mamie kawai ya nufa Mama tace

Ikon Allah kai baka girma ne Mamie tace

Ai fad'a suke Akan zaman jikina. Dariya duka sukayi

Mamie tace masa

Jeka ka Kira haidar d'in mana yana d'aki Yadai shiga wanka amma nasan yanzu ya fito Dariya yayi kafin ya Mike ya tafi

Husna tace

Mamie ina sumayya ne

Tana makaranta dakyar na korata yau Dan cewa tayi bazata jeba Tunda na ce zakuzo shikenan sai jiya zuwa yau firarku akeyi Tare da Salim da haidar suka fito

Bayan sun gaisa suka masa Ya jiki

Mamie ce ta Kama hannun husna da yusra tace kuzo ku rakani Mu kwaso abinci Lafiyayyen tuwon shinkafa da Miyar agushi ne sai jallop d'in couscous Wanda ya wadatu ta vegetables

Sai kayan cin cin da su cake

Gefe kuma farfesun kifi ne dana kayan ciki

Su haidar suka kaiwa su baffa yayinda su kuma su mama suka ci nasu Anan Sai da akayi sallar azahar sannan daddy Ya dawo

Bayan sun yi sallah sannan suka had'u domin asan yadda za'ayi

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Dan Allah ku tayani da addu'a kwana biyu nan da ciwon Kai nake wuni me tsanani Wlh sannan Allah Ya biya mini bukatuna na alkhairi

Ameen.

Ya Allah ka bawa khadija haihuwa Tana tsananin bukatar addu'ar

Please Login or Register in order to submit comment