You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

salma tace

Yafindo karima Anya kuwa wannan aikin yanayi kuwa? Wannefa?

Da wancan da wannan

Yafindo karima tace aikuwa aikinshi naci sosai Hajiya salma tace

Nifa ban taba jin sun Kira babansu wai basuda lafiya ba kodai kece bakya yi musu? Aikuwa lokaci zuwa lokaci inayi yauma zanyi musu ki Gani.

Hajiya salma tayi dariya tace To na zubar da cikin fa?

Yafindo karima tace

Aikada kiyi mamaki idan akace miki yanzu ma ya aika an zubar.

Cigaba da firarsu sukeyi har suka isa gida.

Gidan cike da mutane hakan yasa ba kowa ya fahimci basa nan ba. Bayan sallar magrib su momma suka ISO

Kowa na murna da zuwanta

Farouk ya karasa kusa da ita ya amshi jakarta

Haidar kuwa hannunta ya rike suka jera cikin shagwaba yace Momma shine tun dazu inata wayarki baki daga ba.

Murmushi tayi tace

Tana silent ne meya faru? Turo baki yayi yace

Ai wannan dambun kazan nakeso ki Taho mini dashi. Murmushi tayi tace

Na taho dashi yana cikin jaka ta Daddy hamma ya kalli Abba yace Na lura yaran nan sunfi son uwarsu Dariya sukayi gaba daya

Daddyn abuja yace Hamma kodai kishi kake? Dariya yayi yace

A'a

A falon yafindo hari suka yada zango Jakar haidar ya hau budewa

Folder paper ya dauko cikinfarin ciki yayi peck dinta a goshi Salim yace

Ka isa ka cinye kai daya Nan fa rikici ya tashi Yafindo hari tace

Kudai wallahi anyi girman banza

Farouk dai tashi yayi ya fita ya barsu awajen Momma ta mike ta bishi

Har ya kusa fita ta Kira sunanshi Farouk

Tsayawa yayi ya juyo yana murmushi yace Momma

Karasowa tayi tace Ya akayi ne

Dan shafa kanshi yayi yace Kawai gabana ke faduwa Hannunshi ta rike tace Kayita addu'a

Girgiza kai kawai yayi.

Hannunshi ta kama ta daura mishi agogo tace Yau kuma an manta ba'a saka ba

Agogon Rolex mai kyau dashi Murmushi yayi yace

Na gode momma.

Jerawa sukayi suna fira har suka fito

Abakin balcony suka sami daddyn yola da daddy hamma suna fira Gaisawa sukayi sannan suka wuce

Duk inda suka bi kallon sha'awa ake binsu dashi Fada suka fara zuwa suka gaida mai Martaba Kamar wani abu bai faru ba haka sukayi fira.

Sannan suka wuce bangaren fulani Da murna ta taresu

Ta kalli farouk tace FAROUK KO HAIDAR.

Murmushi yayi yace Farouk

Tace

Kace miskili kafi mahaukaci ban haushi

Mamie tayi sallama ta shigo anan suka Dan taba fira kafin su tashi su tafi bangaren yafindo karima.

Acan suka sami hajiya zainab sa hajiya salma Da fara'a suka tareta kamar babu komai.

Nan suka Mata sannu da zuwa suka taba fira har fura tasha Sannan suka tafi

Bangaren yafindo hari suka koma sannan tayi alwala tayi sallah Farouk yana dandanna Mata kafa har tayi barci.

Yafindo hari tayi murmushi tace

To ai kaima saikaje kayi sallah Dinko Kanshi ya shafa sannan ya mike

Sai da yayi sallah tareda mai martaba suka jero Har harabar gidan sannan farouk yayi bangarensu. Azaune ya tarar da su suna fira.

Faisal yace

Alhamdulillahi gashi ma yazo sai ka dauko muci Farouk yace

Meyafaru Ammar yace

Wannan salim din ne wai baza muci ba sai ka zo nan dai suka zauna suna ci suna fira

farouk ko hairs

Written by deeja one love=ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

39

Cikin barci mama taji kamar ana mintsininta. Farkawa tayi a gigice domin wata azaba data ji Cikin sauri ta sauko domin ta fito

Dumi taji a kafafunta wanda yayi daidai da shigowar yafindo hari Da sauri tace

Nashigesu ni harira mai zan gani rumaisa bari zakiyi Cikin sauri momma ta duba kafarta

Innalillahi take ambata kawai kafin jiri ya kwasheta. A daidai wannan lokacin

Yafindo karima ta ciro wani dan gunki wani karamin kaskon wuta ta dauko ta zuba rushi Wata karamar leda ta dauko

Sai da tayi murmushi sannan ta dauki allura guda daya ta saka a wuta Dariya tayi tace

Yau zakiga practical

Awannan lokacin farouk ya fito daga bedroom su salim na falo suna kallon kwallo Ji yayi kanshi kamar ana dafa kwanyarshi

Tsugunnawa yayi ya dafe kanshi Yafindo karima ta ciro allurar daga wuta Da karfi ta furta farouk

Sannan ta saita kirjin wannan gunkin ta soka Farouk ji yayi kamar ana soka allura akirjinsa

Da sauri ya kamo hannun salim ya dora a wajen yana fadin Salim mutuwa zanyi.

Cikin tashin hankali haidar yayi waje domin kiran abba Daidai balcony suka hadu da yafindo hari itama a rude Su abba suka kallesu suka ce

Lafiya

Yafindo hari tana haki tace

Rumaisa ta suma kamar cikin jikinta zai zube. Innalillahi wainna ilaihir rajiun

Tashi sukayi zasu bita haidar yace Abba farouk fa mutuwa zai yi

A gigice daddy hamma yace Kamarya

Riko hannunshi yayi yace Zo.muje ka gani

Daddyn yola yace

Kai kabiru jeka dauko matarka Ahmad dauko mota

Mu kuma zamuje muga farouk din.

Iya galabaita ya galabaita

Salim kuwa tasa shi yayi a gaba yana kuka

Farouk kuwa duk inda yafindo karima ta soka allurar nan ji yake kamar ajikin shi ta soka A guje daddyn baby ya dauko momma ya saka a mota suka tafi asibiti.

Daddy hamma yace

Wane kalar shirme ne haka salim mai makon ka masa addua sai kuma ka fara kuka Inna mari da mamie ne suka shigo a rude

Inna mari tasa hannu ta rungumoshi jikinta tana addua tana shafa mishi

Ruwa tasa haidar ya debo mata addua tayi ta tofa sannan tayi bismillah ta shafa masa A take barci ya daukeshi haka zafin jikinshi ya ragu.

Yafindo karima ta daure fuska tace da hajiya salma

Kin gani ko wainnan mutanen bazasu bari mu idar da aikin mu ba. Hade rai hajiya salma tayi tace ki bari zan koma kansu ne.

Wani wahalallen barcine ya dauki farouk.

Inna mari ta kalli su haidar kowa ya wani marairaice sai suka bata tausayi Tace

Idan hakan ya faru ku dena masa kuka addua zakuyi mishi kunji Daga kai sukayi.

Hajiya salma tace Yanzu yi wa dayan Murmushi tayi tace To

Wata karamar kwalba ta dauko.

Da wani yar sanda karamar kwalbar ta bude ta tsiyaya akan sandar Cikin sauri haidar yace

Daddy idona zafi yake Mamie tace

Ikon allah daga wannan sai wannan allah ka mana maganin masifa. Hannushi ta rike ta zaunar dashi

Idanun ya kada yayi jajir. Hawaye ke zuba kamar famfo.

Ragowar ruwan adduar farouk din ta deba ta shafa mishi a idanun Ya dai rago amma har lokacin yana da ragowar ja

Kan wani lokacin jijiyar kanshi ta mike Kwantaciya yayi zuciyarshi na bugawa da karfi Yafindo karima tace

Yanzu muje muga me suke ciki Cikin sauri amra ta bar bakin kofar

Sai da suka maida kayan sannan suka fito.

Suna fita amra ta shiga dakin kalle kalle ta fara yi Meye su mum sukeyi har suke kiran sunansu farouk . Bincike ta farayi amma bata ga komai ba.

Da sauri ta fita ta bar dakin

A hanya su hajiya salma suka hadu da mama da hajiya zainab zasu fita

Hajiya salma tace

Lafiya halima naga kunata sauri

Hmm kedai bari aunty salma rumaisa ce babu lafiya da alamu ma bari zatayi shine zamu bita mu duba ta.

Kallon juna sukayi sukayi murmushi

Tana juyowa suka hada ido da hajiya zainab Hajiya zainab ta banka mata harara.

Zaro idanu tayi tace Inasu farouk ne.

Mama ta nunfasa tace

"Suna section dinsu babu lafiya ma naji farouk.,......"

Kafin ta karasa hajiya zainab ta ja hannunta suka shige motar.

Sai da ta fara tuka motar sannan ta leko ta nuna hajiya salma da yafindo hari ta sa Hannu ta nuna idanun alamun tana sane dasu.

Hajiya salma ta daga kafada alamar Whatever.

Da sallama suka shiga dakin Cikin farinciki suke kallonsu

Allah ya basu lafiya sukayiwa su mamie sannan suka tattara suka fita Sai sha biyun dare sannan momma ta farka

Hajiya zainab ta gani kawai Kallonta tayi tace

Cikin ya zube ko?

Mama ta fito daga bayi tace A'a

Murmushi tayi

Daddyn baby yayi sallama ya shigo Bayan ya zauna hajiya zainab tace Dan allah ina neman alfarma Daddyn baby yace

Inaji Tace

Inaso ya kasance babu Wanda yasan cewa cikin na nan bayan mu Hudun nan pls Daddyn baby yace

Saboda me Hajiya zainab tace

Nidai pls ku mini wannan alfarmar To insha allahu.

Murmushi tayi tace Na gode sosai.

Alwala mama ta taimaka Mata tayi sannan taci abinci Sai karfe goma farouk ya farka

A hankali ya mike ya shiga bayi sai da yayi wanka sannan yayi alwala

Sallolin da ake binshi yayi

Salim yayi sallama ya shigo Murmushi yayi yace

Sannu da farkawa bari na amso maka abinci.

Fita yayi saiga haidar da ammar da faisal sun shigo Kallon haidar yayi idanu yayi Jajir irin jinin nan ya taru A sanyaye yace kaikuma meyasameka?

Murmushi hairs yayi yace Kawai ciwo sukeyi mini Jinjina kai yayi.

Sai da yaci abinci sannan ya shirya ya fito Haidar da salim suka biyoshi

Salim yace Ina zakaje ne?

Gaishedasu momma Haidar yace

Ai tana asibiti batada lafiya Da sauri ya kalleshi yace Meya sameta?

Nima bansaniba. Da mamaki yace To muje asibitin Haidar yace to

A parking lot suka hadu da hajiya salma da mamie wai zasu tafi asibitin Gaishe dasu sukayi sannan suka tafi

Tare

Suna shiga haidar yayi ajiyar zuciya

Kusa da ita yaje ya zauna ya dora kanshi akan kafarta Shafa kanshi tayi tace ya akayi babyn momma

Cuno baki yayi yace Nagaji ne yajiki

Salim ya harareshi yace Kato kawai dashi wai baby. Haidar ya hade rai yace

Gulma waya saka dakai ni ai karami ne

Kuma yaushe na girma ma Kawai ka wani sakawa mutane baki amegbo. Farouk ya harari haidar yana dagowa suka hada ido da mamie kauda kai yayi Mamie tace

Ka kauda kai mana tunda kana nuna mana banbanci. Momma tace

Wa.kenan? Mamie tace

Farouk mana a fili yake nuna yafison salim akan haidar

Momma tayi murmushi tace

Ai duk daya suke awajenshi Haidar yace

Mamie aini ban damu ba nasan yafi sonshi tun tuni. Hajiya zainab tayi dariya tace

So gamon jini kuma ai salim din yafi kula dashi ne kunga dole ita zuciya tana son mai kyautata Mata.

Hakadai suka cigaba da fira har zuwa azahar sannan su Abba sukazo. Hajiya salma ta mike tace

To allah ya Kara sauki Momma tayi murmushi tace Angode sosai ki gaida gida Hajiya salma tace

Allah ya kawo mai amfani Ameen

Da yamma aka sallameta

Koda suka dawo gida sun tarar da duk an tafi sister's evening Bangaren yafindo hari aka wuce da ita

Sai da tayi wanka sannan ta kwanta Kowa tunaninshi Cikin ya zube

Salim yace kuzo mu tafi wajen eve din Shiru farouk yayi

Haidar yace

Nawan taso muje mana Tsaki yaja yace

Kuje bazan je ba.

Salim ya riko hannunshi yace Wallahi sai ka je

Murmushi kawai yayi ya bishi.

farouk ko haidar

Written by deeja one love=ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

40-41

Yau aka daura auren muhammad da amra sai adnan da Bilkisu sai abbas da asma'u aure fa masha allah domin komai ya tafi yadda akeso

Bayan biki kowa gida ya wuce farouk yayi kano salim Zaria haidar kaduna. Sati hudu dayin biki akayi posting din corpers

Hajiya zainab ita ta shiga ta fita akabar kowa agarinshi Farouk cikin garin kano zai yi

Haidar kaduna

Salim kuma Zaria.

Kwana biyar farouk yake shiga cikin garin kano domin services dinshi. Haidar kuwa asibitin daddy aka barshi.

Komai yana tafiyan musu dai dai

Ammar zaune a garden wayarshi tayi Kara Da farunciki ya daga wayar

Amra tace Miss u bro. Same

Ya bata amsa atakaice Amra tace

Bro akwai abinda nakeso na gaya maka. To inajinki

Shiru tayi for some seconds sannan tace

Akwai abin dana gani a dakin yafindo karima su sokawa allura ajiki kuma suna kiran sunan farouk

Shiru ammar yayi yace

Yaushe ranar da momma tayi bari. Ammar yace

To meyasa baki dauko ba

Na shiga na duba banganshiba Ta bashi amsa

Ammar yace

Ke me kike tunani Shiru tayi tace

Ni gaskiya banace ba. Ammar yace

Inajin hakanne beda wani amfani ki manta kawai. To shikenan

Ammar yayi shiru azuciyarshi yace Kenan mum tana zuwa wajen boka Ya ilahi!

Tasan abinda takeyi ba mai kyau bane bayaso yar uwarshi ta sani domin hakan zai iya dasa mata kiyayyar mahaifiyar

Hajiya salma ta tabashi tace Ammar lafiya kake kuwa?

Daga Mata kai yayi yace

Eh kawai inaso na huta ni dayane akwai abinda nake tunani. Hajiya salma tace

Ok to kaje daddynku na kiranka Mikewa kawai yayi ya shiga ciki Akan sofa ya tarar da daddy hamma

Daddy yace

Dama mai martaba ya kirani yace na tambayeka kai wa kake so domin so yake nanda next year kuyi aure kai da yan uwanka

Ammar ya shafa kai yace

Daddy yusra ce dama sai dai har yau ban tareta da maganar ba Daddy hamma ya girgiza kai yace

Ok

Hajiya salma ta kira yafindo karima tace Mama yau adan tabasu mana

Yafindo karima tace

To zan Dan tabosu sai dai kinsa yadda zakiyi dasu domin malam yace aljanu bazasu iya xuwa kusa dasu ba

Hajiya salma tace

Kada ki damu yan daba zamuyi hayarsu sure sace haidar idan yaso mu yanka kudi makudai tunda marikinsa yanada kudi idan ya biya sai muce su kashe shi

Shi kuma farouk guba zamu sa mishi a abinci idan yaso sai muyi amfani da salim ya bashi kinga yadda suke son juna babu wanda zai zargi salim ne.

Dariya yafindo karima tayi tace

Gaskiya akwai ki da basira yanzu bara na tabosu.

Ajiye water sukayi ammar yayi ajiyar zuciya yana Kara mamakin mahaifiyar Tashi. Lallai mutum abin tsoro ne.

Yau farouk agajiye ya dawo ga kanshi yana Sara mishi Bokiti ya dauka ya ja ruwa ya shiga wanka

Sai da ya shirya sannan ya shiga dakin inna Mari Abinci ta ajiye mishi

Dakyar yayi loma biyu jikinshi ya dau zafi hakan yasa ya ajiye abincin Da mamaki inna Mari tace

Yau bakasha maganinka bane Daga kai yayi yace

Ya karene kuma ban siyo wani ba

Mikewa inna mari tayi ta debo ruwa tayi addua ta tofa Sai dai yau abin yayi yawa domin jini ta baki ta hanci Salati ta fara tana kiran inna hadiza

Da sauri ta shigo dakin ganin halin da farouk yake ciki yasa ta rudewa baffa ta bugawa waya Hankali a tashe ya taho

Da salim sukayi karo ahanya

Ganin yanayin da baffa ya shiga gidan yasan babu lafiya Dan haka yasa shima ya Bishi kawai Tare suka dauko farouk din suka sakashi a mota

Cikin sauri salim yake tuki

Kan su karasa wudil numfashin ya tsaya cakk. Baffa shiru yayi gabanshi na faduwa

Salim kuwa gudu kawai yake zubawa hankali a tashe. Mamie ta kalli haidar tace

Wai kai lafiyanka kalau kuwa tun dazu na kawo maka abinci amma ka zauna ka zubawa abincin

idanu

A sanyaye ya daura hannunta saitin kirjinsa yace Mamie ji yadda zuciyata take bugawa

Ita kanta shiru tayi tace

Haidar kada ka sawa kanka damuwa fa kasan dai bugawar zuciyarka is abnormal za'a iya samun matsala fa .

Shiru yayi kawai.

Da lallashi ta dinga bashi abincin har ya dan ci da yawa Kallonta yayi yace

Mamie kaina na ciwo.

Magani ta dauko ta bashi yasha

Wayarshi ya dauka yayi dialing number din salim Mamie tayi saurin amshe wayar tace

Haidar kwanta kayi barci

Kamar zai yi magana kuma sai ya fasa Kashe wayar tayi sannan ta fita

A falo wayarta yayi kara Dagawa tayi tace Anyini lafiya

Momma tace Lafiya lau

Bayan sun gama gaisawa sai kuma ta kasa tambayar haidar din Mamie ta fahimci kunyar tambayarta takeyi hakan yasa tace

Wallahi haidar din ne kansa ke ciwo to shine yasha magani ya kwanta Murmushi tayi tace

Ayya allah ya sauwake dama zance ko sunyi waya da dan uwansa na kira wayarshi bata shiga ta salim kuma ba'a daga ba .

Mamie tace

Bari na gwada Kira naji

Itama data Kira ta farouk din bata shiga ba ta Kira ta salim wayar na ringing amma ba'a daga ba Mama ta kira tace Mata

Salim ya tafi kano Mamie tace

To allah ya sa lafiya Ameen

Mama ta amsa

Bayan ta kashe ta kira momma ta gaya Mata Gabanta ya fadi

A sanyaye tace

To allah yasa lafiya

Hawaye suka fara zubo Mata fahad da gudu ya fita A palour ya tarar da daddy yace

Daddy zo kaga momma tana kuka

Da sauri ya taso har lokacin hawaye be bar zuba ba. Daddyn baby ya rungumeta yace

Lafiya kike kuka? Cikin kuka tace

Daddyn baby jikina yana bani farouk bashida lafiya Ajiyar zuciya yayi yace

Haba maman baby yazakice haka Tace

Gashi wayarshi bata shiga Dan murmushi yayi yace

Nifa na lura ko kawaicin Dan fari bakiyi karara kike nuna kinfi son farouk Girgiza kai tayi tace

Ba haka bane Daddyn baby yace

To yane bayan gashi ance dake haidar kanshi na ciwo amma baki damu ba sai farouk da Kika kira wayarshi a kashe may be ma caji ne babu .

Dan murmushi tayi tace Kuma fa hakane Dariya yayi yace

Wlh ke kamar ba bafulatana ba babu Kara babu yunwa.

Shiru tayi Dan ta lura tsokanarta yakejin yi

farouk ko hairs

Written by deeja one love=ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

42-43

Koda suka isa asibitin wudil cikin gaggawa aka amsheshi. Shidai baffa jikinshi a sanyaye yake

Salim kuwa hankalinshi ya tashi sosai ganin halin dayake ciki Alokacin mamie ta kuma kiran wayarshi

Dagawa kawai yayi amma ya kasa magana domin yasan yana bude baki kuka zai yi Mamie ta kuma kiran sunanshi

Um

Kawai yace Yace

Salim lafiya kuwa anata Kira baka dagaba

Shiru yayi zuciyarshi na bugawa da mamaki tace Ba magana nake maka ba salim

Cikin karfin hali ya bude baki domin yayi magana amma abu ya gagara

Kuka ya kufce

Shiru tayi tana sauraran shi. Can tace

Salim meya faru Hawaye ya goge yace

Mamie farouk bashida lafiya inaji mutuwa ma yayi tun dazu likitocin babu Wanda ya fito kuma da muka kawoshi jini ta hanci ta baki

Shiru tayi na wani Dan lokaci kafin tace

Salim ka kwantar da hankalinka cuta ba mutuwa bace insha allahu zamu taho gobe idan allah ya kaimu.

A sanyaye yace To mamie

Baffa da kanshi ya kira daddyn baby ya gaya mishi sannan ya Kira mai martaba shima ya gaya mishi ya Kira daddy hamma da abba.

Kankace me ciwon farouk ya zagaya fada Yafindo karima ta yi murmushi aranta tace Ai insha allahu daga nan bazaka Tashi ba. Hajiya salma ta kirata cikin farinciki tace Kinji abinda naji kuwa?

Dariya yafindo karima tayi tace

Ya zakice haka bayan nice sila daya kuma hakan Wata dariyar mugunta tayi tace

Kai mama shiyasa nakeji da ke wallahi yanzu dai komai yana tafiya yadda ya kamata Jinjina kai yafindo karima tayi tace

Komai yana tafiya dai dai saidai kudi yayi kasa Hajiya salma tace

Indai kudine kada ki damu zan turo miki Cikin farinciki tace

To nagode 'yata

Sai bayan awa biyu wani likitan ya fito Da sauri suka bishi

Tsayar dasu yayi yace

Kuyi hakuri ina zuwa amma za'a kara masa jini leda biyu Dan haka idan kunada Wanda zai bada sai Ku kirashi idan kuma babu sai dai asiya.

Salim cikin sauri yace

Nawa 0± ne zan iya bashi muje kawai adeba Likitan yace

To kaje lab za'ayi gwaje gwaje sannan sai a diba amma duk da haka ya kamata a nemo wani domin a debi left dayan

Salim yace

Likita babu lokaci muje a debi biyun kawai Baffa yace

A'a salim leda biyu yayi yawa ka bari a nemo wani kada hakan ya shafi lafiyarka

Salim yace

Baffa pls ka bari a deba ni be dameniba indai shi zai tashi shikenan Baffa yace

Haba salim ya za'ayi abata biyu daya bata gyaruba Salim cikin lallami yace

Leda biyu bazai bani matsala ba Baffa yace

Duk da haka dai

Ajiyar zuciya salim yayi yace Okay

Lab yaje inda aka gwada jinin Kallonshi yayi yace

Leda biyu zaka diba Amsawa yayi

Sai da ya Dan kwanta for some minutes sannan tashi Sai da suka tace sannan suka sa mishi

Likitan yace dasu baffa

Ku kwantar da hankalinku an shawo kan Matsalar stress Ya tarawa kanshi sannan gaskiya Idan zan gaya muku ita to ciwonshi ba na asibiti bane ya kamata ku dinga hada mishi dana musulunci

Jinjina Kai baffa yayi yace Insha Allah

Daddy hamma da ammar ne suka shigo hankali a tashe

Sai da likitan ya kwantar musu da hankali sannan ya gaya musu yadda ya gayawa su Salim. Shiru daddy hamma yayi yana tunani

Ammar a zuciyarshi yace

Mum Anya babu hannunki a Matsalar nan kuwa?

Haidar kuwa Yana farkawa yayi wanka sannan ya fito a zaune ya tarar da Mamie Tana karatun Al Qur'ni

Kusada ita ya zauna yace Mamie ina wayata

Dan Jim tayi tace Me zakayi da ita? Zan kira Nawan ne. Ya bata amsa

Mamie ta numfasa tace

Haidar daddynka dazu yake amsa Turo baki yayi yace

To Ara mini taki A takaice tace Na Barta a office

Zuba mata idanu yayi

Zai yi magana ta katse shi ta hanyar cewa Jeka kaci abinci

Shiru yayi D'agowa tayi tace

Ba magana nake maka ba

Jiki a sanyaye ya Mike ya hau dinning Washegari da safe Mamie tace Shirya muje unguwa

D'aga Kai kawai yayi domin tun jiya har yau be dawo dai dai ba Wanka yayi kawai ya shirya ya fito

Ganin harda daddy abin ya bashi mamaki Amma beyi magana ba Yaya adnan shi yake driving sai daddy da mamie da haidar suna baya Ganin sun dauki hanyar kano yasa gabanshi faduwa

Cikin sauri ya kalli mamie batace masa komai ba Suna isa suka hadu dasu daddyn baby

Tare suka shiga asibitin

Sun tarar da mai martaba shima yazo Momma ta karasa kusa dashi

Idan ba numfashi dayake ba sai kace gawa ce Fashewa da kuka tayi

Daddyn baby ya riketa yace

Amma kin mini alkawarin bazaki yi kuka ba ko? Girgiza kai tayi tace

Ji halin dayake ciki

Ajiyar zuciya mai martaba yayi yace Yanzu wane hali yake ciki

Daddy hamma yace Likitan yace

At any time zai iya farkawa Shiru dakin yayi

Salim ne ya turo kofa ya shigo Kallon daddy hamma yayi yace Daddy likita nasan ganinka

Har ya mike sai kuma ya koma ya zauna ya kalli baffa yace Kaje kai

Murmushi baffa yayi yace Babu komai kaje kai Tashi yayi ya tafi

Bayan ya dawo yace Likitan yace

Akwai wani babban doctor da zai zo daga India ranar laraba zai duba shi amma suna sa ran ko zuwa anjima ya farfado

Shiru dai har zuwa yamma Daddy ya kalli mamie yace

Tashi mu wuce kada dare yayi

Kallonshi mamie tayi tace To

Haidar hade rai yayi Murmushi daddy yayi yace

Dama bazance kazo muje ba ai ka wani hade rai Sai da ya bawa kowa dariya

Washegari da safe da salim da haidar suka tafi sarina

Sun hado komai sannan suka taho da inna Mari da inna hadiza sai indo Audu kuwa sai gobe idan baffa ya koma

Suna zuwa suka tarar da mai martaba sunzo domin gidan sarkin kano suka je da safe Anan suka zauna har zuwa yamma babu wani labari

Washegari laraba suka likitan yazo Bayan ya gama bincikensa yace

A gaskiya kwakwalwarsa lafiya lau take haka gangar jikinsa

Bashuda internal injuries haka ma external to mai yahanashi farkawa? Mai martaba yace

Inajin zamu wuce dashi can adamawa idan har abin. Yaci tura Likitan yace

Eh to amma bazaku sami wani bayani sama da wannan ba Girgiza kai kawai mai martaba yayi

Bayan bakon likitan ya tafi Suka zauna sukayi shiru Daddy hamma yace

Mai martaba kozan tafi dashi can India ko Allah zai sa adace Girgiza kai mai martaba yayi yace

Kada ka damu za ayi masa na musulunci anan Washegari daddy hamma da ammar suka koma India https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION

"D'We beare's of soo golden a pen,We writer's assiduously percieven No pain,so Magical Our"

"creative golden pen,Be hold our worlds,A product of our pen savour Our worlds for it will cause u no pain"

farouk ko haidar

Written by deeja one love=ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

44-45

"Mai martaba kuma sai washe gari,Da safe Abba da mama suka iso kowa yaga halin da ya ke ciki sai ya tausaya masa Humaira kuwa kullum batada aiki sai na kuka"

Su salim kuwa saida daddy ya tsaya ya nuna musu bacin ranshi sosai sannan suka koma wajen service dinsu Amma fa koda yaushe hankalinsu na kanshi Kwananshi goma sha biyar daddy yace Akwai wani malami abokonshi a kaduna mai zai hana a koma dashi can Haidar yaji dadin hakan sosai da sosai

Yau suka gama services dinsu kowa na murna amma su nasu da sauki Salim kuwa a ranar suka tafi kaduna shida haidar

Akan nanda two weeks zasu dawo domin graduation.

Saukar hajiya salma daga flight ta Kira mai martaba aka tura mata dogarai da driver suka daukota

Fada ta fara wucewa tayi gaisuwa sannan ta shiga wajen fulani

Bayan sun gaisa fulani tace Sai kukaji abu Mara dadi Hajiya salma ta marairaice fuska tace Uhum wallahi abu babu dadin ji kwata kwata allah ya kyauta gaba

Fulani tace Ameen dai

Haka ma data shiga wajen yafindo hari Itama sai da tayi Mata jaje

Sannan ta karasa wajen uwar gijiyarta Da murna ta karasa

Rungume juna sukayi cikin farin ciki

Bayan tayi wanka taci abinci ta kwanta barci sai bayan la'asar ta farka Hajiya salma ta kalli yafindo karima tace

Wai mama ya akayi hakane?

Yafindo karima tayi dariyar mugunta tace Zo ki Gani

Bedroom suka shiga

Wata karamar tukunyar kasa ta bude tasa hannu ta ciro wani abu kamar kwallo kuma transparent

Da mamaki hajiya salma tace Wannan menene?

Yafindo karima tace

Wannan shine rayuwar farouk matukar tana cikin nan to bazai taba Tashi ba Dariya hajiya salma tayi tace

Kai mama malam ne ya baki ko kuwa? Yafindo karima tace

Wane malam wani na sake

Tafawa sukayi da hajiya

Please Login or Register in order to submit comment