You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku tace na roka mata. Nima Nace Allah Ya baki my sisto

20

A dinning suka tarar da Mamie

Abinci yaci sosai kafin ya sha maganinsa Daddy yace

Jeka ka kwanta

Barci yayi har magrib sannan ya farka Alhmdllh jikin da sauki

Da kyar baffa ya yarda su kwana da aranar yaso su tafi Su mama dai a Ranar suka tafi tareda Salim.

Washegari da wuri suka tafi

Sai dai kafin su tafi daddy sai da ya kara dubashi. Suna isa Kano suka sami motar Sarina

Su k'asimu duk suna gida Jajantawa aka yi tayi.

Farouk kuwa gaba daya jikinshi tsami yayi mishi Don haka bokiti ya d'auka domin wanka. Inna hadiza tace

Ga ruwa can me dumi kayi amfani dashi

Indo ce ta amsa ta sirka mishi Ta Kai mishi bayi. Makota da abokan arziki.haka suka yita zuwa Kasancewar labari A K'auye beda Wuyar yaduwa. Da safe bayan ya karya ya Kalli Audu yace

Audu ya kamata nadan taka Baffa yace

Ka bari sai da yamma saboda yanzu Rana zaka ga ta D'aga Kaga kan nan ma Ya dawo daga kasuwa

(kasancewar Idan rani yayi sukan koma kasuwa ne) Hakan ne ya faru bayan ya dawo

Suka Fita

Inda suka Saba zama suka nufa sai dai Yau wajen babu laifi a cike yake Sani Ya Kalli magaji yace

Duba can ka gani Dariya magaji yayi yace

A'a kaga yan Boko an dawo kenan. Ko kallonshi farouk beyiba.

Magaji ya kuma cewa

Allah Ya kyauta gaba

Abu ce ta k'araso Tana dariya Kallon farouk tayi tace

Umar Andawo ahe abinda Ya faru Kenan D'aga Kai yayi Alamar eh

To Allah ya Kyauta gaba.

Ameen Ya furta Wanda kawai lebenshine Ya motsa. Murmushi tayi tace

Wlh hankalina ya tashi sosai Magaji yace

Ke Meye haka wuce ki Bamu Waje Harararshi tayi

Sani Ya Mike Cikin zare idanu yace Zaki bar nan ko sai na makeki.

Cikin sauri ta juya

Farouk kuwa Kauda kanshi yayi

Ganin zaman bazai masa bane yasa yace Su Mike su zagaya gari.

** *** *** *** ** Cikin huci Faisal yace

Wlh bazai yiwu ba

Ammar ya zuba masa idanu yace

Ka zauna ka kashe kanka Akan wata yarinya k'arama. Harara Faisal ya galla masa yace

Eh ai gwara ni ma tasan ina sonta bayan Kai har yanzu ka kasa gayawa Yusra kana sonta Murmushi ammar yayi kawai.

Faisal ya zuki taba yace

Wai kasan waccar matar muna fika ce har ta tura d'an ta. Kallonshi kawai ammar yayi be ce komai ba

Harara Faisal ya galla mishi yace

Kai Wlh wannan izzar taka naga inda zai kaika. Dariya ammar yayi yace

Ba wannan yafi bani haushi ba shine Sakin wancan yaron da Abban Zaria yasa akayi Tabe baki Faisal yayi yace

Dama wa'innan son ya'yansa ai Ya mishi yawa Ammar yace

Na rasa meyasa Wlh be sona. Oho matsalarshi ce wannan K'ara zukar tabar yayi yace Yaushe zamu tafi adamawa Ammar yace

Nan da two weeks

Kallon rainin wayo yayi masa yace

Kama isa Wlh ban yarda ba Ammar yace

To zan biya wajen abbana kafin na wuce

Aikuwa sai dai ka biyo ni Dan ni nan da one week zan tafi. Ammar yace

Kai bikin fa sai nan da three weeks D'aga Kai yayi yace

Nasani amma bazan yarda wancan ya kayar Dani ba Dafa kafadarshi yayi yace

Kada ka damu Dan uwa amra zan baka Dariya yayi yace

To daddy hamma (Al'ameen modibbo kenan) Hakadai suka Cigaba da firarsu.

Haj Zainab tace

Kada ki damu yaya Idan kin zo zamu koma wajensa domin ya kadasu su shiga duniya Haj halima tace

Bari sai nazo din amma kada ki Bari su zo adamawa Dariya Hajiya Zainab tayi tace

Me zai kawosu adamawa Ki kwantar da hankalinki To sai nazo d'in ki gaida baban Faisal d'in.

Insha Allah zai ji.

Dakyar ammar yayi convincing Faisal ya yarda suka kai sati biyu Abuja suka wuce Don suyi sati daya

Bangaren Salim ma yau suke ta shirye shiryen tafiya Harda angon

Salim ke Waya da haidar suna shirya yadda tafiyar tasu zata kama Haidar yace

Kada ka damu zamu taho on Wednesday Tabe baki yayi yace

Haba wane Kalar Ranar laraba kafin nan ai ankusa Gama events d'in Murmushi haidar yayi yace

Amma kasan dole na jira su Mamie ko da Nawan Dan kasan tanan zamu wuce Ko Hade rai Salim yayi yace

Gaskiya jibi zaku taho Dariya yayi yace

To ubana bani umarni ne.

Tun Ranar litinin har laraba Salim Waya yake babu sauki Ganin Abin nashi bazai k'are bane yasa ya hadashi da Mamie Kwantar Mai da hankali tayi tace

Ranar alhamis zasu biya su d'auki farouk sai su wuce

Haka ya hakura amma duk Wani Abu dayake faruwa sai Ya sanar dasu Idan kuma na d'auka ne yakan d'auka Ya tura musu su gani.

Yau alhamis Ranar da su haidar zasu wuce adamawa.

Salim ne ke Waya da haidar Haidar yayi dariya yace

Gamu nan yanzu zamu taho and kada ka kuma kira pls Dan ni zanyi driving. Dariya Salim yayi yace

Yara duk na rigaku

Murmushi kawai haidar yayi yace Sai mun iso

Salim yace

To Allah ya kawo ku yanzu muma zamu tafi taro Wani uncle dinmu ne dake South Africa yanzu zasu sauka

To

Kashe Wayar yayi

Mamie da sumayya ne zasu tafi

Dan surayya Tana makaranta su kuma yaya Adnan da yaya Abbas da daddy zasu zo daurin aure Ranar Jumu'a

Jan kunnenshi daddy yayi Akan ya tafi dasu a hankali kasancewar yau ne zai Fara driving me

nisa .

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

21

Sai wajen azahar suka isa.

Duk da Garin k'auye ne amma yanayin Garin ya birge su Mamie Haidar yayi mata jagora har Cikin gidan

Yayinda daddy Ya tsaya a waje Inna hadiza ke alwala

Da murna take musu sannu da zuwa har dakin Inna Mari ta kaisu ita kuma ta Riga ta tada sallah

Haidar yace

Inna ina farouk ne Ya tafi masallaci

Inna hadiza ta bashi amsa

To muma Bari Muje Masallacin

Indoce ta shigo da ruwa akwanon sha. Zama tayi ta gaishesu

Mamie tayi murmushi tace

Ashe ma humaira d'in ba babbace Hannu tasa ta Rufe fuskarta Sumayya ta jata suna ta fira

Inna Mari Tana idar da sallah suka gaisa

D'an wake ne yaji Mai da yaji me dadi ga salad da tumatir Sallama su haidar sukayi suka shigo

Tabbas Idan suka jero ba lallai Ka ganesu ba saboda Kamar da sukeyi Farouk ya Matsa Kusa da Mamie yace

Mamie anzo Lafiya Shafa kanshi tayi tace Lafiya lau my son Ya jikin Yayi sauki

Ya bata amsa

Kallon haidar tayi tace

Da gaskiyarka Babyn momma kamata yayi Akoma cewa d'an wake d'an filawa( Mamie tayi santi)

Dariya akayi gaba daya

Haidar ya Tabe fuska yace

Haba Mamie agaban yaran nan aisai su rainani Dariya akayi gabadaya

Sumayya tace

Yaya farouk kaga mamie itama tayi santi Ko Inna Mari tace

Farouk ka tashi ka shirya domin da tafiya agabanku. Kallon Indo yayi yace

Zubo mana abinci muci tukunna Dan nasan halin wannan. Dariya aka kuma yi

Farouk kuwa Kauda Kai yayi Kamar bashi ya fad'a ba Sai da sukaci suka koshi sannan ya mik'e Ya tafi wanka Indo tace

Aunty sumayya zo Muje kiga gari kafin su shirya Inna hadiza tace

Daga nan ku biya Dandali ku kira baffanku kice bakin sun iso Ita kanta sumayya yanayin Garin yayi mata dad'i

Baffan ma Ya rigasu isowa gida Dan sai da suka biya ta bingi. Suna isowa ma har sun fito

Sumayya ta Kalli farouk da haidar tace

Haba yaya meyasa kuka saka kaya kala d'aya. Haidar yace

Ke Matsa ki bawa mutane Waje Farouk yayi murmushi yace Bama so a ganemu ne.

Haidar yace

To ai ko ita bazata ganemu ba. Turo baki tayi tace

Mamie Wai bazan gane su ba

Mamie tace

Kyaleshi kawai auta Ko nima ba ganesu zanyi ba Duka akayi dariya

Gefen me zaman banza haidar ya bude ya shiga

Farouk shi ke driving kasancewar zamansu a kaduna Anan suka koya dukansu. Sai bayan isha sannan suka shiga Garin adamawa ahakan ma Sunyi gudu Haidar ya kira Salim

Da haka yana musu kwantance har suka iso Tab rigiji gabji

Duk iya tunaninka gidan sarautar ya wuce haka Babu Kowa saboda sun tafi Kamu

Wani yaro ne yayi musu jagora har Cikin gidan Wata dattijuwace zaune ga kuyangu suna kaikawo. Cikin fara'a ta tarbesu

Abin ci kala Kala aka kawo musu Kallonsu farouk tayi ta musu filatanci Kallon juna sukayi sukayi murmushi

Murmushin Mamie tayi kan tace ai basa ji ma. Da mamaki tace

Amma duk Wanda ya ganku yaga Fulani Sallama Salim yayi yashigo

Wajen Mamie ya Fara zuwa Cikin murna yace Barka da zuwa Mamie

Had'e rai haidar yayi

Kallon farouk Salim yayi yace Barka da zuwa Dan uwa Sumayya tace

Ai fa yaya Salim ga yaya farouk d'in nan Kallonta ya yi yace

Waye Ya gaya miki haka ai ni duk inda naga mummuna ina ganeshi Duka haidar ya Kai mishi yace

Wlh zan koma inda na fito yanzu. Yana dariya yace

Sai ka dawo.

Mikewa sukayi Salim ya kira Khairat Wanda take Yar uwarsu ce Yace Mata.

Kinga su mama suna wajen kamu ga Mamie nan Idan su mama sun dawo ki hadasu mu zamu fitane.

D'aga Kai tayi tace To

Wani Bangare na gidan suka nufa Wanda yake can gefe Wani kofar suka bud'e suka shiga

Garden ne me kyau ta gefenshi suka bi

Wani wajene Kai kace haddadden hotel ne Suna bud'e kofar suka shiga

Lifter

Hawa na biyar suka tsaya

Dakine reras gasunan Wani daki ya bude Wanda ya hadu sosai komai na d'akin milk and brown ne.

Salim yace

Wannan shine d'akina Haidar ya tambayeshi Bangane ba

Dan murmushi yayi yace

Duk Wani family na gidan nan to Yanada d'aki Anan Bangaren mata kuma yana ta gefen fada

Koda Kai ba mazaunin Garin bane Ko kasar amma sai an maka naka d'akin Murmushi farouk kawai yayi yace

Nuna mini bayi nayi wanka Yana fitowa haidar ya shiga Wasu kananan kaya ya saka

Bakar Riga da Blue Jeans haka ma haidar.

Salim kuwa Manyan kayane ajikinsa wato shadda Riga da Wanda sky blue. Masallacin fadar suka shiga sukayi sallah

Suna fitowa daidai lokacin da motoci ke parking gasunan bila adadin Cikin mamaki haidar yace

Wannan family tab kiyashi kenan Hararshi yayi yace

Mune kiyashin? Dariya yayi kawai

Farouk kuwa Dan karamin tsaki ya ja kafin yace Ai ni wannan ko hayaniyar su ciwon Kai zata sani Haidar yace

Muje Ko

D'akin Salim d'in suka koma sunata fira Washegari da safe busa ta tada su Tsaki farouk ya ja yace

Kai Wlh dama banzo ba Cikin gida kuwa

Mamie na zaune suna fira wata mata ta shigo Da fara'a ta k'arasa kusada mama tace Halima an tashi Lpy

Itama Cikin fara'a tace

Lafiya lau rumaisa kin iso muna can muna Kamu Murmushi tayi tace

Wlh matsala aka samu amma da tun shekaranjiya zamu iso

Kallon Mamie tayi tace Sannu baiwar Allah

Gaisawa sukayi Kamar sunsan juna kafin tace

Su farida basu farka ba tun jiya suke damuna da tambayarki Dariya kawai mama tayi .

Karfe biyu fadar ta cika taf Kamar zata tsage saboda mutane Hada hada akayi

Farouk ne zaune a d'aki Salim ya harareshi yace

Wlh ka tashi Muje Ko kuma na gayawa yaya Mubarak baka je daurin aurenshi ba Banza yayi dasu hakan yasa haidar yayi dariya yace

Ashe dai kuna fada

Harara ya galla mishi kafin ya mik'e Ya Kalli Salim yace Muje Ko A lifter suka had'u da Faisal da ammar da yaya Muhammad Gaishe da yaya Muhammad sukayi Cikin murna

Yace

Yan biyun Mamie saukar yaushe Dariya Salim yayi yace

Jiya fa suka zo

Faisal da ammar kuwa haushi kamar ya kashe su ganin Ko su nuna sun San dasu.

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

22

Daurin aure ne akayi sun Kai guda bakwai Kai wannan family da girma yake

Farouk ganin kanshi na neman Ya fara ciwo yasa shi barin wajen Wajen wasu bishiyoyi yaje ya zauna

Sun Kai su shida suka jero Tundaga nesa amra ta ce Waye wancan ne?

Yusra tace

D'aya daga Ciki tace Wake nan

Da hannu amra ta nuna shi

Ganin wa aka nuna yasa Yusra yin murmushi tace Abokin yaya Salim ne

Da mamaki tace

A haka daya juya Kamar daddy hamma Murmushi Yusra tayi tace

Zo Muje ki tabbatar bashi bane

Jan hannunta tayi yayinda sauran suka wuce Suna karasawa Yusra da murmushi tace Yaya FAROUK Ko yaya HAIDAR

Da sauri Ya juyo ganin Yusra ce yasa yayi tsaki yace

Ke bakida hankali Ko haka ake Idan aka zo Waje babu sallama babu komai sai surutu Sunkuyadda Kai tayi tace

Yi hakuri na manta ne Ina sumayya

Ya tambayeta Tana tareda husna

Amra kuwa Sakin baki da hanci tayi Tana Kallonshi Tabbas wannan shine Wanda ya dace ta aura

Gyaran murya tayi Wanda yayi daidai da karasowar su haidar Salim yace

Barka da hutawa aunty na

Dan murmushi Tayi kawai ta Kauda Kai gefe Dariya haidar yayi yace

Tsiyar ka zamo yaro kenan Ko Wacce karamar yarinya ka dinga ce mata aunty. Had'e rai yayi Ya ce

Oya kaima gaida ita

Dan kallon gefen ido yayi mata yace Tab Allah Ya kyauta wannan yarinyar.

Amra kuwa mamaki ne ya cikata sai ta Kalli haidar sai ta Kalli farouk Wa'innan identical twins d'in irin haka

Magana take shirin yi su Faisal suka karaso Kallon up and down yayi musu kafin yace Ammar kasan talaka be iya samun wajeba. Dan murmushi ammar yayi yace

Kuda kuma wajen kwadayi yake mutuwa. Cikin zafin rai haidar yace

Kai Kama kanka wallahi nafi karfin nazo kwadayi ku kanku kun sani Dariyar mugunta Faisal yayi yace

A hakan Ban gani akasa ba

Amra da sai yanzu tayi magana tace Kai brother Wai Meye Hakane

Farouk kuwa yadda kasan ba'a halliccesu Awajen ba . Banza Ya bawa ajiyarsu.

Haniya wajen ya tashi dashi Wanda takai ga ammar ya D'aga hannu ya Mari haidar

Cikin bacin rai farouk shima Ya wankeshi da tafi Wanda yayi daidai da isowar sarki Al'ameen

tareda modibbo sai abba da karamin su daddyn Abuja. Kowa Tsayawa yayi.

Abba Ya ce Meye haka

Daga hannu sarki yayi yace

Gobe Idan Allah Ya kaimu ina bukatarsa ganinku gaba daya a fada Naji me yasa kuke fad'a a Ranar da aka daurawa yan uwanku aure har takai ga Mari.

Wucewa sukayi Wanda jikin su gaba d'aya yayi sanyi Faisal yace

Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun yanzu Mai martaba yasan ni na Fara hada wannan fadan ai da matsala.

Ammar yace

Kai Allah Ya kyauta da nasan Hakane da bangaren Fulani na wuce Ko yafindo Hari Kowa watsewa yayi

A lifter Salim ya kallesu ganin Kowa harkarshi yakeyi babu Wanda ya damu yasa yace Ku bakusan me kuke bako?

Cikin halin ko in kula haidar yace da akayi me? Jinjina Kai kawai yayi Ya Cigaba da harkarshi.

Da yamma aka Fara tafiya hall d'in da za'ayi dinner Salim ya kira mama a Waya

Tace

Yaya kun taho Gamu tareda mamien taku Cikin jin haushi yace

Mama Wai farouk ne bazai zo ba Jim tayi kafin tace

Lafiyarsa kalau kuwa Eh mama

Ya bata amsa Tace

To Kai Idan zaka zo ka taho mana.

Yana kashe Wayar ko kallonshi be yi ba ya juya ya fita. Haidar na fitowa daga bathroom Cikin sauri Ya Fara shirinshi Kallon farouk yayi yace

Kai Nawan ina Salim

Kamar bazai yi magana ba sai kuma yace Ya tafi

Tsayawa yayi yana kallonshi

Can ya dau wayarshi Ya Kira Salim d'in Koda ya D'aga masifa Ya Fara yi mishi Salim yace

To Idan ka Gama sai ka taho ai Harara yayi Kamar yana ganinshi yace

Waye zai kawoni

Akwai wa'inda basu Gama tahowa ba ai. OK

Ya gaya Yana kashe Wayar Agogonshi yake daurawa yana tafiya Jirani mu tafi

Juyowa yayi Ya Kalli shi yace Oh dama zakaje

Be yi mishi magana ba har ya Gama shiryawa

Ankon dinner ne ajikinsu yadi ne Kamar silk me Kalar blue and sky blue. Bakin harabar gidan mutane ne tsiraru wa'inda basu Gama tafiya ba Tunawa yayi da key d'in motor da suka zo da ita Dan haka

Juyawa yayi domin yaje ya dauko Yana tsaye har ya dawo

Bude motor yayi suka shiga

Har ya ja zai tada ta k'araso da sauri Glass d'in ta kwankwasa

Zugewa yayi

Koda suka had'a idanu sai da gabansu Ya fadi Farouk dai wayarshi kawai yake dannawa Ganin shirun yayi yawa yasa yace

Ba wajen dinner zakije ba

Sai a lokacin Ta sami damar D'aga Kai Alamar eh To shigo

Suna gaba Tana baya

Sai dai duk da haka gabanta be daina faduwa ba

Motor shiru sai haidar lokaci zuwa lokaci dayake magana Abinda ta Lura dashi Na gefen surutu be dameshi ba Juyowa haidar yayi Ya ce

Ko kinsan hanyar Eh na sani

Kallon farouk yayi yace Nawan koma baya ko?

Sai da yayi Jim sannan ya bude ya fita

Kallonshi take Wanda ya hassada mata sake rudewa Sai da ta zauna sannan tayi Ajiyar zuciya

Bata sake tabbatar wa ba sai da ta kuma kallonsu Ya ilahi

Ita ke nuna hanyar har suka iso A bakin harabar hall d'in

Haj salma da haj Zainab ne tsaye suna Magana

Dayan gefen kuma abbane da daddy sai daddy hamma suma suna magana

Motor na Tsayawa duka kallo ya koma kanta

Fitowarsu yayi daidai da bugawar zuciyar yawancinsu. Daddy hamma a ranshi fadi yake

Meye hadin rumaisa da wa'innan yaran

Haj Zainab kuwa da haj Salma zufa ce ke zubo musu Cikin tashin hankali haj Salma tace

Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun na shiga uku ni Salma Me zan gani

Cikin rudewa haj Zainab tace Kiyi hakuri Wlh bansan zasu zo Ba

Sudai ciki suka shiga

Neman Salim sukayi dakyar suka ganoshi Cikin sauri Ya juyar da Kai Haidar yace

Dalla ni da ka tafi Ka barni banji haushi ba sai kai Hararar farouk yayi yace

Da wannan nake fa Au Wai Dani Kake

Banza Salim yayi dashi

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

23

Sai wajen Karfe sha d'aya sannan aka tashi Suna isowa gida kwanciya kawai sukayi

Bangaren rumaisa kuwa bangaren yafindo Hari ta nufa Wata matace da bazata wuce shekaru Hamsin da biyar ba Zaune hannunta rike da casbaha Tana ja

Cikin sauri ta fad'a jikin ta Tana fadin Yafindo yau na gansu

A kidime yafindo Hari tace

A ina kika gansu kuma su waye 'Ya'yana yafindo kuma a wajen dinner Dan murmushi tayi tace

Watakila yaran da suka zo ta bangaren halima kike magana Wai'nnan ma ai ba yan biyu bane kawai kamace da suke. Kallon mamaki take binta dashi kafin tace

Dama kin gansu D'aga Kai tayi tace

Kwarai kuwa jiya suka zo

Jinjina Kai tayi tace

To yafindo wai'nnan 'Ya'yana ne jikina ya bani

Kallo kawai ta bita dashi domin Abin Nata sai da addu'a Shiyasa batason abinda zai kawota najeriya domin duk zuwanta sai ta rakito ya'yan wasu tace natane

Nisawa yafindo Hari tayi kafin tace

To yanzu Jeki kwanta Idan Allah Ya kaimu gobe ayi Maganar. Mik'ewa tayi ta tafi

Da kallon tausayi yafindo ta bita.

Daddy hamma ne bayan sun Gama fira dasu abba Kamar bazai yi magana ba sai kuma yace Ahmad su waye wa'inda suka kawo rumaisa d'azu

Dan murmushi yayi yace

Hamma abokan Salim ne kaga baban daya daga Ciki Ya nuna daddy

Shi kuma Dayan fa ? Ya kuma tambaya Yana Kano

Ya bashi amsa

Be kuma cewa komai ba Hajiya Salma tace

Na shiga uku wallahi duk Wanda ya Kalli wai'nnan yaran yasan jinin modibbo ne Idan me Martaba ya gane haka na shiga uku

Dan murmushi hajiya Zainab tayi tace

Kin manta dama mun shirya zuwan wannan Ranar Kedai ki kwantar da hankalinki da bakinta zakiji ta amsa ita ta yardar da yaranta

Share zufa tayi tayi Murmushin mugunta tace Hakane fa Kin fini saurin gane Abu

A Ranar mutane dayawa awannan familyn basuyi barci ba Ciki kuwa harda Salim

Ganin yawan motsin da yake yasa Haidar yace Lafiya kuwa

Dan karamin tsaki ya ja kafin yace

Ina tunanin hukuncin da me martaba zai yanke mana Gobe ne Idan Faisal ya nuna cewa nafi sonku sama dashi.

Shiru na Dan Wani lokaci sukayi kafin haidar yace Tab wato dai halin Fulani yana nan

Salim yace

Ai Al Adar Nan ba'a auren bare Dan murmushi yayi yace

Kace kaima auren zumunci zakayi Tsaki ya ja kafin yace

Auren soyayya dai.

Suna fira a haka har barci ya d'aukesu Washegari da safe

Bayan sunyi breakfast Kowa Ya tafi fada

Anan suka Ga ainihin yawan familyn su Salim Wai ma a hakan wasu sun wuce tun jiya Shidai haidar gaba d'aya kanshi ma Juyawa yakeyi.

Daddyn yola(wanda shine d'an sarki na farko ) Ya bude taron da addu'a

Kallon ammar yayi yace Kaine babba meya had'aku

Labari Ya bayar na karya da gaskiya Jinjina Kai me martaba yayi

Daddyn yola ya dubi Salim yace Saura Kai Tashi ya yi Ya bada labarin abinda Ya sani Shima Jinjina Kai yayi

Faisal shine Wanda ya bada labarin abinda Ya faru a karshe Daddyn yola Ya dubi su haidar yace

Waye zai yi magana a Cikin ku Daddyn Abuja Ya Mike yace

Amma hamma jabiru kasan dai bakine ba yan family bane Me martaba yace

Halliru zauna

Dole tasa yabi umarnin mahaifinsa Mik'ewa haidar yayi Ya bada nashi labarin

Me martaba ya Kalli haj Zainab ya girgiza Kai Daddyn yola yace

Amma meyasa Kai zaka fifita baki Akan yan uwanka Sunkuyadda Kai Salim yayi

Daddyn yola yace

Yanzu za'a hukunta Wanda ya Mari ammar a Cikin ku. Mik'ewa farouk yayi yace

Ina da magana

Da idanu me martaba ya bishi Wajen tsayin minti uku kafin yace Anbaka dama

Kallon me martaba yayi yace Hukuncinku babu adalci a ciki Kowa taso mishi yayi

Da sauri me martaba ya D'aga musu hannu hakan yasa sukayi shiru Kallon farouk yayi yace

Me yasa kace haka

Babu tsoro Ko fargaba yace

Saboda ai ni baku tsaya kunji nawa labarin ba sannan kuma kun tambayi shedun dake wajen kafin na mareshi me yafaru Ai sumayy na wajen da ita da wata yarinya.

Dan mu Bamu a family naku sai ku mana zalinci

Dan murmushi me martaba yayi yace

To me yayi maka ka mareshi

Basu labarin abinda Ya faru yayi sannan ya Dora da cewa

Ai da shedu domin mahaifinsa shine Ya tura sojoji suka kamani Akan danshi ya mareni Me martaba ya juya ya Kalli modibbo

Shi kuma sunkuyadda Kai yayi kawai Juyowa yayi yace

Cigaba

Farouk ya Dora da cewa

Sannan a labarin da Dan uwana ya bada ai madam zainab tasa an koreshi Daga makaranta saboda kawai ta zageshi ya mata magana.

Ko duk wai'nnan ba laifi bane?

Dan murmushi me martaba ya kuma yi kafin yace To Kai Marin da kayi mishi fa?

Saboda ya mareni a Zaria ne bansami damar ramawa ba. Jinjina sarki yayi mishi yace

An gaida namiji inaso naga iyayenka. Farouk yace

Me zakayi musu

Mik'ewa me martaba yayi yace

Zan shiga daga ciki zuwa anjima da yamma za'a kuma zama sai dai inaso zaman yafi wannan zama na sirri abinda Ya shafi iyalai ne na jiki

Juyawa yayi Ya Kalli daddyn yola yace Jabir kazo mini da iyayen su duka Su biyun. D'aga Kai yayi yace

Angama Allah Ya ja kwananka. Dan murmushi yayi ya shige Ciki

Yana tafiya daddyn yola ya Kalli abba yace Kaji abinda me martaba yace

Dan haka ina iyayensu suke? Abba yace

Iyayen Haidar suna nan Cikin gida Dan sunzo biki Sai dai iyayen farouk suna Kano su.

Daddyn yola yace

To zamu booking flight mu tafi sai mu taho dasu. Modibbo ya Mike yace

Nima ina neman alfarmar binku Idan yaso sai nayi magana akawo mini jet Dina. Jinjina Kai daddyn yola yayi yace

An baka dama

daga haka daddyn Abuja ya Rufe taro da addu'a sannan Kowa Ya Mike

Magan gani kanana suka Fara tashi kan cewa yaro k'arami yaja da me martaba Mamie na zaune labari yazo mata

Cikin tashin hankali ta kirasu

Kallonsu tayi bayan sun zo tace

Kunsan me kuka aikata kuwa to inaso anjima Idan an kuma zama kada Wanda ya kuma ja da Mai martaba

Fad'a sosai tayi musu sannan tace Su tafi

Ada yau zasu tafi amma kasancewar wannan abinda Ya faru yasa Daddy Ya Kira Mamie yace dole su Bari sai gobe.

Ammar yace

Mom ni Wlh hakan ya mini Allah Ya sa a tura shi shida iyayenshi gidan kurkuku Yayar me martaba Wacce ita bata taba haihuwa ba suna kiranta da hajiya yaya tace

Hmm yaro yaro ne kana gani yaja da me martaba Da zai hukuntashi ai daya hukuntashin Kai acikin yayanshi da jikoki ban da modibbo akwai me ja da Maganar me martaba ne ya barshi Shiru sukayi kafin suce Hakane kuma fa

Can ammar yace

To anjima dai zamu ga wane hukunci aka yanke masa. Karfe sha biyu suka sauka a Kano

Motoci aka turo daga masarautar Kano domin su daukesu

Sai da suka Fara Mik'a gaisuwa sannan suka wuce Garin Sarina Salim ya musu jagora har kofar gidan

Mutane an firfito ana leke Kowa da abinda yake cewa

Salim ne ya shiga yayi sallama da baffa Don Sunyi sa'a yana nan Bayan ya fito suka gaisa kallon su yayi yace

Ku shigo ciki Daddyn yola yace

Ba zama mukazo yi ba so muke kashiga ka fito da mahaifiyar farouk Sarkin adamawa na nemanku

Duk da dakiya irin ta baffa amma sai da gabanshi ya fadi Lafiya dai ko?

Ya tambaya

Murmushi abba yayi yace Ka dai zo Muje Kaji acan

Shiga yayi babu dadewa ya fito tare da Inna Mari

Please Login or Register in order to submit comment