You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ farouk Ko haidar

Story and written

-by- deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar.

Bismillahir rahmanirrahim.

Wannan littafin kirkirarrene bawai ya

Faru da gaske bane.

Godiya gareki Dijency saboda da taimakonki na Gama littafina me suna MATA TA GARI.



"Rana ake yi me zafin nan Wanda har Tana makogoronka zakaji yana kokarin fashewa saboda azabar kishi,"

Dai dai sha biyu da Rabi yayinda

"Ya keto tsakiyar k'auyen su, tafiyace me tsayi yayi kafin ya k'araso Cikin garin."

"A gajiye yake ga zufa ga yunwa da kishirwa, kusan ya Saba da hakan tunda mutane daidaiku ne ke Karatu a k'auyen"

"Kasancewar mutanen ciki basu Wani damu da karatun ba hakan yasa ko primary babu a Garin. K'auyen Sarina kenan dake Wanda mutanen Garin suka fi bawa noma da kiwo mahimmanci, Garin Darki dake gabansu garine babba Wanda kan mutanen ciki yafi na Sarina wayewa Hakan yasa sukeda makarantu da sauransu."

To sai Ya kasance Idan kanaso kayi Karatu sai dai kaje can wannan Abin shi yafi bashi haushi. Duk da agajiye yake zaka iya shaida kyawunshi

Farine Wanda ba irin na tashin hankali ba.yanada tsayi Wanda ya dace da daidai jikinsa. Yatsun hannunsa Zara Zara Wanda yake sanye da Wani irin zoben azurfa Mai kyau irin na da d'innan. Idonshi Manya ne sosai yayinda suke a Fuskarsa me Dan tsayi.

Hancinsa dai dai Wanda ya dace da yanayin Fuskarsa Wanda bakinsa ya kasance karami dake zagaye da pink lips.yanada dimples Wanda duk lokacin daya motsa bakinshi zai lotsa.

Ba Wani babba bane a shekaru sosai tunda yanzu ne ya Kai shekaru goma sha takwas.

Dai dai Wani gida ya tsaya Wanda a haka zaka dauka karamin gidane amma sai ka shiga Ciki. Gidane me sa-sa da yawa

Tundaga zauruka zaka Fara shaida hakan dakuna ne jere inda nanne samarin gidan ke zama Daya daga Cikin dakuna nan samarin Ya bude ya shiga

Tsaki k'arami yayi kasancewar yadda ya bar d'akin haka ya dawo ya sameshi Tabbas iro be gyara dakin nan ba

Littattafansa dake baje a k'asa ya kalla Cikin takaici Hadawa Ya yi Ya maida su inda suke

Kafin ya Soma cire kayan makarantar murmushi yayi Tunawa da yayi yanzu fa Allah Ya

taimakesu shi kenan angama da secondary Dan yau suka Gama zana NECO Cikin gidan Ya shiga

Tun daga farkon gidan har k'arshe d'akuna ne. Yawancin matan suna zaune Kowacce

Da d'aurin k'irji.

"Wasu na sana'a wasu na aikin su. Bangaren baffa mudi kenan shine babba Wanda yakeda mata hudu babbar matarsa tanada Yara goma sha biyu, sai Mai bi mata Inna uwale tanada yara goma cif cif itakan masifaffiyace hakan yasa Kowa baya kulata."

Sai Inna saude Wanda take da yara goma sha d'aya itakan mata ce me kawaici da sanin Ya kamata

K'aramarsu Inna Hari fitinanniyar matace ta bugawa a jarida yaranta takwas. Sallama ya kuma yi kafin su amsa

Gaishe dasu yayi sannan ya wuce

Wani bangaren still ya kuma shiga Wani bangaren nan kuma bangaren baffa habu kenan shima matansa hudu yara ashirin da hudu.

Shima dai gaishesu yayi wasu sun amsa wasu Ko kallo be ishesu ba

Bangare na uku shine bangaren baffa Adamu bangarene tsaftatacce me kyau Daga gani na cikinshi Sunada tsafta

Shi kuma mata biyu gareshi kacal Matarsa Inna Mari da Inna hadiza

Inna Mari matace me ha'kuri da sanin Ya kamata itace matarsa ta farko ta dade bata haihu ba. Sai Inna hadiza matace me tsananin fad'a amma Idan ka tab'o ta kenan sai dai suna zaman Lafiya fiyeda sauran 'yan gidan.

K'ofar d'akin Inna Mari yayi sallama ya shiga Tana zaune Tana yanke farce D'agowa tayi tace

Wa'alaikumussalam sannu da dawowa. Murmushi yayi yace

Inna na gaji.

To zauna mana sai na amso maka abincinka Ta gaya Tana k'ok'arin mik'ewa.

Dakata Inna ki Bari zanje da kaina Cire rigar jikinsa yayi Ya fita

Bokiti ya dauka Ya Debi ruwa Ya shiga bayi yayi wanka . Yana fitowa ya shiga d'akin Inna hadiza akwance ya sameta.

Sai wata 'Yar budurwa zaune gefenta da tire da alamu talla zata tafi Had'e rai yayi yace

Ke humaira

Da sauri ta d'ago idanunta kasancewar tasan shi kad'ai yake kiranta da wannan sunan dariya tayi Wanda kyawunta ya k'ara bayyana.

Meye haka ina zakije ne?

Inna hadiza ta dago ta kalleshi tace Jarababbe ka dawone?

To talla zataje naga ta yadda zaka hanata Dan yau baka isa ba

Juyawa tayi kanta tace

Kin d'auka kin tafi ko sai na tashi na b'allaki. Da sauri Indo ta d'auki tiren ta fice.

Kai kuma Idan zaka shigo ka d'auki abincinka to Idan kuma Tsayawa zakayi Anan to kayita Tsayawa har mahadi ya bayyana

A zafafe ya saki labulen d'akin Ya juya Ko d'akin Inna Mari be koma ba ya fice.

Can wajen wata bishiyar mangoro yaje ya zauna kasancewar ranace duk sun tafi gona Ko kiwo ya sa shi kad'ai Ya zauna a wajen.

Rik'e kansa yayi dake barazanar fashewa.zuciyarsa Kamar zata Faso haka yakeji. A hankali ya dinga sauke numfashi har ya daidaita

Yafi minti ashirin a zaune sannan ya tashi ya yi hanyar Bayan gari Ya nufa Tafiya me nisa yayi Tsakanin gonaki wajen wata gona ya shiga.

Zaune a inuwa suke su shida wasu na cin abinci wasu na alwala. Daya daga ciki Wanda da alamu Ya girmeshi yace

Barka da dawowa 'yan makaranta.

Waje ya nema Ya zauna Gefensa Ya kalla yace Ina baba? Dayan daya Gama alwala yace

Lafiya kuwa Kake farouk? Kanaji musa na maka magana kayi banza dashi Yace

Ya mutsa fuska yayi yace babu komai

Musa ya Kalli Wanda ke zaune Yana cin abinci yace Audu kira baba kace ga Dan Gata Ya dawo.

Yanzu fa zai dawo ka bari yazo mana

Kallonsu yayi dukansu duk 'ya'yan baba Adamu ne duk da sun San baban yafi sonshi basu tab'a damuwa da hakan ba.

Musa yace

Ibro ku kyaleshi Dan Allah kunsan yaya lafiyar kura bare tayi Hauka. Ku Bari zaizo ne yanzu

Shidai farouk be ce musu komai ba

Kusan minti sha biyar sannan baffan ya bullo ta tsakiyar duhun Dawa Tsoho ne Dan ya Fara tsufa

'ya'yansa guda takwas ne. Bakwai maza d'aya mace

Babansu shine k'asimu sai Mai bi masa musa sai ibro Wanda wajen sa'an farouk ne sai bello sai Audu sai k'araminsu harisu maccer kuma Aisha Wanda suke ce mata Indo

Yarinyace 'Yar Gata a wajen yayyenta komai suka samo Nata ne.

Dukkansu Kansu a Had'e yake daga k'asimu sai musa su kad'ai ne sukayi aure Su bakwai yaran Inna hadiza ne farouk ne kawai d'an Inna Mari.

Tashi farouk yayi yaje wajensa yace Baffa sannu da aiki.

Yauwa sannu yarona.

Andawo an Gama kuma?

D'aga Kai kawai yayi Kallon 'ya'yansa yayi yace

Waye Ya b'atawa umar rai kuma daga dawowa. Ibro dake alwala Ya mik'o wa baban buta yace Gashi baba sai ka wanke masa.

Dariya sukayi duka

Farouk kuwa murmushi yayi yace Baba nifa Inna k'arama ce.

Dariya suka kuma yi kafin musa yace Fad'anku waye zai shiga ku bashi kunya. Ato dai ai kunfi Kusa yanzu kaci abincine? Baba Ya tambaya

Girgiza Kai yayi yace A'a

Juyawa baba yayi yace

Kai Audu zubawa Dan uwanka abinci.

Zuba masa yayi kad'an yaci Ya tashi shima yayi alwala sukayi sallah dukansu sannan suka Fara aiki.

Duk da kansa Kamar zai fashe amma haka ya daure yake yi domin iya kawaici da mutunci suna yi masa

Zaije makaranta tun yana k'arami su suna noma kuma Idan lokaci yayi na biya masa kud'in makaranta Haka za'a d'auki abincin da suka noma a biya masa ko siyan litattafai.

Yanzu haka tunda ya Fara jarabawa suka sauka barinsa yana aiki sai dai yayi karatu.

Tun sauran 'yan gidan na magana har sun gaji sun Dena ma.

farouk Ko haidar

Written by

Deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar



Suna isa gida yamma tayi matan Kowa Na hada hadar d'ora girki

A sasan su ma Hakane Inna Mari ce keta iza wuta Sannu da aiki sukayi mata

Yauwa sannunku Ya aiki

Alhmdllh Inna Bari na tayaki Farouk ya gaya yana tsugunnawa

Tabbas yasan daurewa kawai yake amma da wuya Idan ba ciwon kan sa bane zai tashi Gashi maganinsa ya k'are

Inna ta tab'ashi tace Lafiya Kake kuwa?

Eh Inna lafiyata lau Ina Indo. Inna tace

Ta d'auki gyad'a ta fita talla. Had'e rai yayi yace

Kina kallo kuma ta d'ora mata.

Toh ikon Allah sai kuma a k'i d'ora mata talla Wai Meke da munkane Abin fifita Wutar Ya ajiye Ya fice daga gidan

Jinjina Kai Inna Mari tayi tace Allah Ya kyauta

Yana fita Dandalin Garin ya nufa na yamma Maza da mata ne dank'am Kowa na harkarsa

Can ya hangota gefenta sani ne zaune sai faman fira sukeyi

Da sauri Ya koma da baya Ya jingina da itacen mangoro dake wajen Runtse idanu yayi zuciyarsa na masa zafi

Hannunsa ya hade Waje d'aya ya matse yana Jan numfashi da k'yar Dafashi akayi

Yana Juyowa yaga d'an uwansa Audu ne Lafiya Kake kuwa?

Audun ya tambaya

D'aga masa Kai kawai yayi Tsugunawa yayi a wajen ya dafe kansa A sanyaye Audu yace

Kan ne.?

Ido jajir ya d'ago yace

Audu banason tallan da Indo takeyi duba ka gani dariya takewa sani Idan nayi magana kuce Wai Na hanata neman kud'i

Na rasa meyasa bakwa fahimta. Dafashi Audu yayi yace

Kada ka damu muna sa ido sosai akanta kaga bazata fad'a wata hanyar ba. Kauda kansa gefe yayi kawai

Meyasa basa fahimta ne Oho?

Sun dad'e a nan suna fira kafin ayi kiran sallar magrib su tashi su tafi masallaci Suna dawowa gida suka nufa

Kowa yana d'aki suka shigo Farouk yacewa Audu

Ina zuwa Bari nayi wanka Dariya Audu yayi yace

Ai Ko agwagwa bazata nuna maka wanka ba.

Shidai be ce komai ba ya dau bokiti ya ja ruwa a rijiya Ya shiga wanka

Yana fitowa ya tarar da duk sun fito domin cin abinci Dan a tsarin gidan Idan akayi magrib to Akan shinfid'a k'atuwar tabarma ne domin cin abinci

Gaba d'aya 'ya'yan baffa Adamu ne zaune suna cin abinci Sallama baffa yayi Ya shigo

Da sauri farouk Ya mik'e ya amshi ledar hannunsa Wajen Inna Mari Ya ajiye sannan ya dawo ya zauna Fruits ne Wanda ya Saba siyowa.

Kasawa akayi Kowa Ya d'auka

Bello ne yasa hannu ya dauki na Indo Ihu ta saka Tana sai Ya bata

Audu Ya daka mata tsawa yace

Dalla rufewa mutane baki wawiya kawai Harara farouk ya aika masa yace

Kaga malam ka Barta tayi kayanta Kai bello bata kayanta kafin na tashi Da sauri Ya ajiye mata ya bar wajen Baffa yace

Ni Na rasa wannan soyayya dake Tsakanin farouk da Indo Inna hadiza tace

To ai kuma gashi ya shagwab'ata kuma gaba ina jiye masa ba. Dariya Inna Mari tayi tace

Sunfi Kusa dai

Tab'e baki Inna hadiza tayi tace

Hakane kam amma Aini a wajena zata sha wuya. Dariya sukayi kafin baffa yace

Ikon Allah ni na rasa meke faruwa kwana biyu Tsakaninki da d'an naki kwana biyu. Wai Dan na Fara d'orawa Indo talla

Murmushi farouk yayi Ya mik'e yace Humaira let's go

Harara Inna hadiza tayi tace

Kaga ka kiyayeni wace gulmar Kake mata. Shidai gaba yayi be ce komai ba

Da Dan D'aga murya tace

Ni nake maka magana kana tafiya Ko? Juyowa yayi Ya nuna mata kanshi.

Dan sauri suka Fara tambayar lafiyanshi

Har tausayi suka bashi wannan wace irin k'aunace? Inna hadiza tace

Allah Ya sauwake Audu ya siyo maka maganinka a wudil gobe Baffa yayi murmushi yace

Hadiza kenan kuyi fad'a da d'anki ku shirya Wanda ya shiga kuma yaji haushi. dariya tayi tace

Duk abinda Kake so muna tayaka sonshi

Allah dai ya muku albarka Ameen suka amsa gaba d'aya Bangaren farouk kuwa

D'akinu Ya shiga Indo na bayanshi Kallonta ya yi yace

Ya kin iya na jiya ? Eh

Ta bashi amsa To karanto

Thank you -na gode Where are you -kana ina How are you -ya Kake

Pls borrow me your ball -dan Allah ara mini k'wallonka. Murmushi yayi yace

Gud gal yayi yanzu ki Bari gobe na k'ara miki. to

Ta fada Tana wasa da yan yatsunta . kiran sunanta yayi yace

Humaira Meye d'azu sani yake gaya miki kike dariya Zaro idanu tayi tace

Yafa ce kada na gayawa Kowa Gabanshine ya fad'i yace Kamarya gaya mini.

ganin babu wasa a Fuskarsa yasa ta cewa Dama cewa yayi yana sona

Zaro idanu yayi yace Da gaske

D'aga Kai tayi Alamar Eh

Zuface ta Fara keto masa Ahankali Ya koma ta kwanta Shiru d'akin na wani lokaci kafin yace

kuma kema kina sonshi Daga Kai tayi Alamar Eh

ganin kallon dayake matane yasata saurin girgiza Kai A zafafe ya mik'e ya fincikota

Yatsunta guda biyu ya matse

Tsabar azaba hawaye kawai ke zuba daga idanunta.

Tabbas tasan ya farouk akwai mugunta amma Ta yau ta tsorata da ita.

farouk Ko haidar

Written by deeja

One love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar



Cikin hasala yace

Bana ce kada kiyi soyayya da Kowa ba? D'aga Kai tayi Cikin azaba tace

Bazan kuma. Ta saki kuka

Ahankali Ya saketa Ya koma ya kwanta. Hanyar Waje ya nuna mata

Da sauri ta fice Tana kuka

Bata shiga d'akin Inna hadiza ba Dan tasan halinta D'akin Inna Mari ta shige

Inna Mari na uwardaki tajiyo kuka Fitowa tayi Tana fadin

Indo keda waye? Cikin sheshsheka tace Ya farouk ne

Ikon Allah me kuma ya had'aku? Inna Mari ta tambayeta

Wai Dan sani yace Yana sona.

Shiru Inna Mari tayi Tana mamakin wannan Abu Janyota Jikinta tayi Tana rarrashin ta

Ki Bari da safe zan masa magana

Bangaren farouk kuwa Tana Fita ya mik'e Ya zauna

Tabbas babu aure a Tsakaninsu tunda mahaifinsu d'aya to amma Kamar yadda yayi alk'awarin shi zai Nemo mata miji to bazai Bari taso Wani ba (Kaji farouk da K'ok'ari )

Da safe yana tashi yaji Alhamdulillah kan ya Dena ciwo hakan yasa ya shirya da wuri suka

wuce gona

Suna zaune suna fira ta ratso hanyar

Kanta d'auke da kwano gefenta wata k'aramar yarinyace Tasha ado irin na garinsu.

Bello da Audu suka Kalli farouk suka Fara dariya Had'e rai yayi Ya juya fuska

Sallama tayi musu suka amsa Kallon farouk tayi tace Umaru gafa abinci

Ko kallonta beyi ba bare tasa ran zai amsa Audu yace

Ke Abu ki ajiye mana zaici ne

Harara ta balla masa tace ina ruwanka Dariya yayi yace

To daga gwaninta ai sai ki bada himma Kallon farouk tayi tace

Umaru kanaji ina magana kana banza Dani Mik'ewa yayi Ya bar wajen

Kallo ta bishi dashi

Duk iya daurewar da su Audu sukayi sai da sukayi dariya K'ara k'uluwa tayi ta tashi ta tafi Tana kuka

Audu mik'e yaje Kusa dashi yace

Haba farouk ka Dena mata wulak'anci mana Shiru yayi

Audu yace

Nifa wannan miskilancin naka haushi yake bani fa Still beyi magana yayi

Indo ce ta k'araso ta gaishesu ta ajiye musu abinci Farouk yace

Humaira

Da sauri ta k'araso Kusa dashi Yau ma kin d'auki tallan?

Hawaye ne ya zubo mata tace Eh amma Wlh ban kulashi ba

Kallonta yayi Kamar na minti biyu har ta cire Ran bazai yi magana ba D'aga Kai yayi Alamar yaji

Sannan yace

Jeki zubo mini abinci

Audu dai na tsaye Yana kallon ikon Allah Dariya yayi yace

Wlh matarka ta shiga uku da mulki Be ce komai ba

Domin yasan dama bazai yi magana Indo ce ta k'araso da abinci a hannunta Mik'a masa tayi

Amsa yayi Ya Kalli Audu yace Bismilla

Kad'a Kai yayi Ya saka hannu suka Fara cin abinci Da yamma suna zaune a Dandalin yamma

Sani yazo Ya zauna Ya Kalli farouk yace

Haba umaru Ya haka Dan Nace inason k'anwarka sai kuma ka hanata? Kamar bazaiyi magana ba sannan yace

Kanwata ce ina to zata auri Wanda na zab'a mata ne Baki bud'e Audu yake kallonshi

Sani be ce masa komai ba

Ya mik'e yace

Ina dai a matsayin wa Kake kawai amma Kake wannan tsarin Kamar ubanta to zaka gani kuwa

Murmushi farouk yayi yace OK zaka gani

Yana tafiya Audu ya kalleshi yace Meye Hakane Wai?

Kasan dai watarana aure zata yi Ko to kuma kana korar mata masoya. Tashi yayi Ya bar wajen.

Da dare suna zaune suna cin abinci Inna hadiza ta Kalli farouk daya fito wanka tace

Ka kyauta Wai wane irin yaro ne Kai ka hanata Tsayawa da samari ni wannan wane irin Abu ne?

Kallonta yayi yace

Ita ta gaya miki haka? Bansaniba

Murmushi yayi yace

Nifa cewa nayi kawai ni zan zab'a mata mijin aure Dukansu bud'e baki sukayi suna maamaki.

K'asimu yace

Cab Abin naka har yakai nan kuma

Shidai be kuma cewa komai ba ya shige d'akin Inna Mari

Indo kuwa matso hawaye take Dan tasan da wuya yau be daketa ba Suna gamawa ya kalleta yace Muje muyi Karatu

Babu inda zataje

Inna hadiza ta gaya Tana mik'o masa Leda Amsa yayi Ya duba

Maganinsa ne a ciki Kallonta yayi yace To Inna yau kuma rigima kike ji.

Had'e rai tayi tace

Aika rainani dole ka gaya mini haka Shiru yayi Ya zauna kawai

Baffa yayi murmushi kawai ya mik'e

Bayan wata biyu sakamakon su ya fito yaci nine credit. ABU Zaria Ya samu admission

Yana gayawa baffa yace

Anya farouku Zaria beyi nisa ba Shafa Kai yayi yace

Dama ai d'aki zan Kama To Allah ya taimaka Ameen

Ya amsa

Yana gayawa Inna Mari ma haka tace Inna hadiza kuwa cewa

Tayi

To dayaake Abin da zamani amma duk fad'in Kano ka rasa inda zakaje makaranta sai Zaria Murmushi yayi yace

Zan dinga dawowa Hutu ai To Allah ya taimaka Ameen

Haka sauran 'yan uwansa suma suka ce

Bayan kwana biyu yana zaune a Dandalin yamma Abu tazo wajen

Sanin halinta yasa Audu be mata magana ba

Ganin Idan ba ita tayi mishi magana ba bazai kulata ba yasa tace Umaru yanzu Zaria zaka tafi bazan kuma ganinka ba

Dukda yadda bayasonta amma sai da ta bashi tausayi Cikin sanyin jiki yace

Ai zan dinga zuwa Hutu. Dariya tayi tace

To amma yau Naji dad'i kayi mini magana me dad'i Kallonta yayi yace

Kinga Abu nifa burina nayi Karatu ba yanzu zanyi aure ba To ai zan jiraka

Kina ganin gidanku za'a barki?

Shiru tayi Dan tasan baza a tab'a barinta ba. Tashi yayi Ya tafi gida

Kamar yadda ya zata kuwa

Tallan da be k'auna ake kasawa Indo

Ko Kallon inda suke beyiba Ya Debi ruwa a rijiya ya shiga wanka. Audu ya shigo gidan

Ganin Inna hadiza yasa ya tambaye ta Ina farouk?

Ya shiga sana'artasa

Zama yayi yana jiran fitowarsa Kallon Indo yayi mata alamu da tazo Tsugunawa tayi gabansa.

A hankali yace Kinason sani?

Daga Kai tayi Alamar Eh

To kada ki damu zan shawo miki kanshi

"Farouk daya fito yana jinsu ,banza yayi dasu Kamar be jisu ba. Yan mata uku ne tafe zasu je d'iban ruwa"

Suna tafe suna fira Dayar tace

Nifa Idan nice ke bazan iya jure wulakanci da umaru ke miki Dagowa tayi tace

Wlh binta inasonshi ne bazan iya rabuwa dashi ba

Dayar ta kalleta tace Au to magaji fa?

Bana sonshi gaskiya Girgiza Kai tayi

Suna mamakin irin son da take masa

Suna isa suka tarar da farouk ya rako Indo d'ibar ruwa Binta ta taba Abu ta nuna mata

Murmushi tayi ta nufi wajen su Sallama tayi musu

Yana tsugunne yana d'ibar mata ruwan Indoce ta amsa

Dagowa yayi yace

Abu kema d'ibar ruwan kikazo. Dariya tayi tace

Eh

Mik'awa Indo Nata tulun yayi yace Kawo naki

Wayyo Kamar ansaka a aljanna Da sauri mik'a masa

Yana amsa daidai isowar magaji da sani da idi Da sauri sani Ya nunawa magaji yace Kalli can Cikin zafin zuciya ya nufi wajen

Cikin fushi yace

Kai umaru Meye Haka dama Wai amanata kuke ci Ko? Ko kallo be isheshi ba

Hakan ya k'ara kular dashi Sani yace

Sannu me zab'awa k'anwarshi mata to nima k'anwata mijin dana zab'a mata shi zata aura Kallon Abu yayi yace

To kinji me yayanki yace Dan haka kibi zabinshi Cikin sauri tace

Amma ni Kai nake so Murmushi yayi mata

Ya mik'a hannu ya amsa tulun hannun Indo yace Mata Muje Cikin kuka Abu ke kiranshi.

Tsabar haushi dukanta sani Ya Fara Da kyar su magaji suka kwaceta

Yau farouk ke shirya kayansa domin ya wuce Zaria registration Kudin dake hannun baffa Ya amsa

Yace

Baffa Idan na samu yadda nakeso yau gobe zan dawo Idan kuma ba haka ba to sai jibi Daga Kai baffa yayi yace

To Allah ya Tsare Ameen Ya amsa

A kafa Ya zo har darki kafin ya sami motor da zata kawoshi Kano wajen obasanjo bridge Anan ya sami mota direct har Zaria

Tunda ya shiga motor Gabanshi ke faduwa Dan wannan ne tafiyarshi ta farko da zai bar Cikin Kano.

A motor Ya hadu da wani me Dan banzan surutu. Tun yana shareshi har ya saki

Kallonshi yayi yace Kai Dan Zaria ne? Eh Kaifa?

Registration zanje Dariya yayi yace

Kanada Wanda zai nuna maka abubuwa ne A'a

Dariya ya kumayi yace To Idan munje na raka ka

Ka gannin nan suna na Salim haifaffen Zaria ne

Yanzu haka kan na taho akaje aka mini registration a pharmacy Murmushi yayi yace

Nima haka.

Wai ya sunanka ne? Umar farouk.

Farouk ya bashi amsa Suna zuwa aka sauke su Motor samaru suka nema

Sai da suka shiga ABU Zaria suka Gama komai

Farouk dai Sakin baki yayi yana kallon makarantar Tabbas ta hadu sosai fiyeda yadda Kake tunani

Salim yace

Zan nema mana accommodation sai mu zauna daki daya Daga Kai yayi kawai

Yanzu Muje gidanmu ka kwana Kallonshi farouk yayi yace

A'a kaje dai zan nemi wajen kwana Dariya Salim yayi yace

Tab Ai kafata kafarka

Ganin bazai kyaleshi bane yasa ya bishi.

farouk Ko haidar

Written by deeja

Love =ØŠÝ

Dedicated to Madina m umar



Gidan babu laifi Dan gidane na alfarma

Bayan sun gaisa da mamarshi suka wuce d'akinsa. Gadone makeke komai a d'akin Masha Allah Salim yace

Farouk nan ne gidanmu ga d'akina Murmushi yayi yace

Na gode wannan d'aki haka Kamar Wani me mata

Abin ya bashi mamaki sosai Dan be tab'a tunanin farouk d'in ya iya tsokana ba. Hmm kasan me?

Girgiza Kai yayi Alamar a'a

Muje mu ci abinci in Kai ka kaga gari

To yanzu dai Fara nuna mini bayi inyi wanka Nuna masa Salim yayi shi kuma ya shiga.

Bayan yayi wankan ya fito ya shirya sannan suka fito Mama na nan a inda suka Barta

Salim yace

Mama Kinata hutawa abinki Harara ta aika mishi dashi tace Ai ka dawo dole ka dameni

Wasu 'yan mata ne guda biyu suka shigo gidan da gudu. Dayar taje bayan mama ta boye.

Ihu suke suna zagaye falon

Daka musu tsawa Salim yayi yace Dallacan matsa ku bani Waje.

Cikin Zunboro baki Kowacce ta Kama hanyar d'akinsu Suna gama cin abincin suka fita

Yawo sukayi sosai yana nuna mishi Cikin garin Zaria.

Duk da Garin ba Wani kyau gareshi sosai ba amma Yanayin tsarin Garin ya birgesshi sosai. Sai bayan isha'i sannan suka dawo.

Yanzu dai harda wa'inda be gani d'azu ba yanzu duk sun dawo. Duka kallonshi sukeyi

Mama ta Kalli Salim tace

Talkative aika gabatar wa da 'yan uwanka abokin naka Ko? Kai mama!

Yanzu Daman zan aikata.

Brothers and sisters wannan shine abokina umar da muka had'u a mota d'azu dana dawo daga Kano.

Dariya Abin ya basu. Had'e rai yayi yace

Meye kuma na dariya?

Babban ciki yace

Kai ai Garin kwashe kwashenka sai ka kwaso Wanda zai siyar damu Mama ya kalla ganin batace komai ba yasashi cewa farouk

Buddy tashi mu tafi

Dayar da suka shigo d'azu tace Yi hakuri yaya

Harara ya galla mata yace Matsa kafin na mareki.

Suna shiga d'akinsa Ya Kalli farouk yace

Kada ka damu da abin da suka fad'a haka suke dama. Murmushi farouk yayi Ya zauna bakin gado.

Tab'e baki Salim yayi shima Ya zauna

Mu bakwai ne a wajen daddynmu ainihin mu 'yan adamawa ne aiki Ya kawo mu nan .

Wanda yayi magana shine d'a na biyu a wajen daddyn mu sunanshi Muhammad babban kuma sunanshi Mubarak yana UK ne yana Karatu.

Shi kuma Muhammad yana Cairo ne ya dawo Hutu ne Sai ni Salim Wanda zan shiga yanzu makaranta.

Murmushi farouk yayi yace Kai baza'a fitar dakai bane Dariya yayi yace

Tab daddy ya fitar Dani ai yasan me yayi.

Sai wa'innan 'yan matan daka gani su 'yan biyu ne d'aya yusra d'ayar husna

Sai wa'inda ke binsu suma 'yan biyu ne fahad da farida su suna wajen wan daddynmu ne a South Africa.

Acan yake zaune? Farouk ya tambaya. A'a yaje check up ne To Kai bani labarinka. Kwanciya yayi yace

Yanzu na gaji gaskiya sai dai zuwa anjima. Dariya Salim yayi yace

Zo Muje mu sayo abinci Farouk yace

Saboda me bazamu ci Anan ba?

Shiiiiiii Salim yasa hannunsa abakinsa alamun yayi shiru To Bari nayi wanka

Da kallo Salim ya bishi yace

Wai Kai kana gajiya da wanka kuwa Bece masa komai ba har ya shige. A jere suka fito

Yanzu Basu a zaune a falo suna kan dinning

Ganin suna k'ok'arin fitane yasa Muhammad cewa

Ku kuma ina zuwa? Husna ta bashi amsa da Siyan abinci zamuje

Ta fad'a Tana Had'e rai

Irin yadda yakeyi Idan an bashi haushi Dariya sukayi gaba daya kafin mama tace

Kaga farouk kyaleshi kazo ka zauna kaci abincinka. Da sauri Salim ya kalleta yace

Mama me hakan ke nufi. Ta canza d'a

Yusra ta bashi amsa Harara ya aika Mata yace Nayi magana dake ne Dariya suka kuma yi

Muhammad Ya mik'e Ya matso Kusa da su ya kama hannun farouk yace Muje kaci abinci ka manta da wannan rigimammen.

Binshi farouk yayi

Hakan yasa suka kuma dariya

Buga k'afa ya Fara yi k'ara dariya

Please Login or Register in order to submit comment