You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka kuma yi. Mama tace Kaji kyalesu autan mama

Dariya yayi yace Yauwa mamana Muhammad yace

Jishi k'ato dashi Wai auta Kallon farouk yayi yace Kannensa hud'u fa

Murmushi farouk yayi yacigaba da cin abincin sa.

Har suka Gama cin abincin Kowa da drama da yake yi Abin birge farouk yayi

Washegari tun da wuri farouk ya shirya.

Babu yadda basuyi Akan ya hak'ura zuwa anjima sai Ya tafi K'in yarda yayi hakan yasa suka kyaleshi

Sun masa Sha Tara ta Arziki Salim yace

Kome ke tafiya zaka dinga ji ta wajena yanzu Bani number dinka. Ai ni banada Waya

Farouk ya fad'a Mama tace

To aikuwa bazai yiwu ka tafi ba'aji daga gareka. Kiran Muhammad tayi tace

Ka biya ta sahad ka siyo mini waya. Samsung Galaxy S5 ya siyo

Bashi tayi tace

Ya rike Dan su dinga ji daga gareshi

Haka ya tafi Yana mamakin mutuncin mutanen.

Yana isa Garin darki ya sami me mashin ya d'aukesa har Cikin garin Sarina. Be tarar da Kowa a gidan ba Kamar yadda ya zata

Wanka kawai yayi Ya shirya ya tafi gona. Suna ta aiki yaje ya samesu.

Bello yace

Ga 'yan makaranta sun dawo Murmushi farouk yayi yace Ina Audu

Bello yace

Yana wajen baffa suna girbi Murmushi yayi yace

Bari naje wajensu.

Da baffa da k'asimu ne a tsaye suna magana yayinda Audu da ibro suke girbin. Cikin fara'a suka tareshi suna tambayarsa Ya makarantar.

Labari ya basu gaba daya sannan ya ciro Wayar ya nuna musu. Cikin farin ciki Audu ya amsa yace

Tab Kai ka fara wannan Yar dangwalen kaf Garin Sarina. Shima cire Riga yayi Ya duk'a suka Cigaba tare

Indoce zaune da faranti a gabanta Abu ta k'araso ita da harira

Abu tace

Naji ance yayanki ya dawo Ko D'agowa tayi ta kalleta tace

Wlh ban saniba Kinga tun dazu Na baro gidan ban koma ba To shikenan inaji k'aryane

Abu ta gaya Tana k'ok'arin mik'ewa Indo tace

Wai ke Abu baki hak'ura da yaya umar ba kiga dukan da sani Ya miki Juyowa tayi tace

Tab Ko kasheni zaiyi bazan so magaji ba. To Allah ya taimaka

Ameen

Indo na dawowa ta sami farouk na wanke takalmi Da sauri ta k'araso Tana dariya tace

Yaya harka dawo.

D'aga mata Kai yayi yace Eh kin tafi talla Ko?

Daga masa Kai itama tayi Murmushi yayi yace

"Da kyau,Kin had'u da sani ko?"

Girgiza Kai tayi

Shigowarsu Inna Mari yasashi yin shiru. Da fara'a suka k'araso suna fad'in Barka da yan makaranta.

Murmushi kawai yake yi be ce komai ba.

farouk Ko haidar

Written by

Deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Wayyo 'yan Zaria zasu cinye ni Wai Nace garinsu babu kyau to ai nima 'Yar nan ne. Yanzu dai sai kuyi hakuri bazan kuma ba

Umar farouk hauwa'u da Aisha salisu ku Janye Allah Ya isanku kunji Zaria tafi Abuja kyau lols





Gaishesu yayi kafin ya basu labarin abinda Ya faru. Sunyi farinciki sosai da sosai

Salim yasha addu'a har mamaki Ya dinga yi

Yau dai Cikin farin ciki ya tashi Dan jiya Sunyi Waya da Salim Akan sun sami accommodation sannan kuma lectures zai Fara nan da sati biyu.

Kowa Ya fahimci yana Cikin farin ciki sosai Tafiya suke tareda Audu zasuje wajen

Da suka Saba zama

Magaji ne da sani suka tsayar dasu Magaji ya nuna farouk yace

Kai baka jin Magana Ko?

Nace maka ka rabu da Abu kak'i Ko to Wlh ni ba sa'an wasanka bane bar ganin kana zuwa makaranta Cikin birni dukan ban mamaki zan maka.

Murmushi farouk yayi yace

Kaje ka tambayi Abun Idan na tab'a cewa ina sonta da kazo kana wannan haukar. Audu yace

Haba magaji Meye Hakane na tareshi kana wai'nnan magan ganun Shiru yayi Shidai bai kuma cewa komai ba

Ganin abin na neman Ya zaman musu fad'a yasashi Janye audun domin su tafi Masifa audun yaketa yi

Shidai be kulashi har suka isa wajen

Zama sukayi sannan Audu ya harareshi yace Ka wani tsaya miskilanci Kamar Wani d'an sarki Murmushi yayi ya juya ya Kalli gefe

Tsaki Audu yaja yace

Wannan shegen miskilancin naka na Kusa rabuwa dashi ai Kallonshi yayi da sauri yace

Ka gaji danine? Halinka na gaji dashi Audu ya bashi amsa

Shiru dai yayi be kuma cewa komai ba Tab'e baki yayi yace

Ai bazaka Dena ba

To sai nayita zuba surutu babu ma'ana Dariya Audu yayi yace

Oh surutun da muke shine Mara ma'ana?

Be ce komai ba sai ma wayarshi daya ciro yana dannawa. Me Hali be fasa halinshi

Still bece masa komai ba

Bayan sun Gama cin abinci farouk yace Baffa zamu Fara lectures nan da sati biyu Baffa yace

To ikon Allah yanzu ya za'ayi? Sauke Kai k'asa yayi yace

Eh nan da kwana goma zan tafi Dan naje na shirya. To Allah ya kaimu

Farouk ya amsa da Ameen

Indoce tsaye Tana shanya ya shigo gidan Amsa sallamar da yayi tayi

Kusa da ita ya tsaya yace

Kina nan kina wanki kin manta da karatu Ko Sunkuyadda Kai tayi tace

a'a innace ta sani Tab'e baki yayi yace

Ki mini alfarma d'aya mana Wasa take da yatsun hannunta

Kinga gobe zan tafi makaranta inaso pls kada ki tsaya da kowanne saurayi Kallonshi tayi tace

To inasha Allah bazan tsaya da Kowa ba A sanyaye yace

Har sani fa

D'aga Kai tayi Alamar Eh Murmushi yayi yace Gud gal

Washegari da wuri Ya shirya domin tafiya Kaf gidan Kowa Allah Ya tsare yake masa

Audu da suke tafiya Don su fita titi ya kalleshi yace

Daba Dan kun had'a uba da Indo ba da sai nace Ko ita zaka aura Murmushi yayi yace

Nidai kawai ka tabbatar da bata saurari Kowa a Garin nan ba Jinjina Kai yayi yace

OK Babu Matsala

Har Sai da ya sami mota kafin Audu ya koma.

*** **** *** *** *** Kamal ya Kalli haidar yace

Yanzu duk makarantu kaduna ka rasa makarantar da zaka tafi sai Zaria Kallonshi haidar yayi yace

Nima haka kawai Naji can nakeso na tafi kuma ai makaranta ce me kyau. Kamal yace

Hakane

Yanzu dai zo Muje kaci abinci and kada ka manta gobe kazo da wuri Ka kaini. OK ba matsala

Washegari da wuri suka shirya suka tafi

Farouk na sauka a fly over Ya Kira Salim yazo Ya d'aukeshi Gidansu Salim d'in suka Fara zuwa

Sai da suka kwana d'aya kafin su wuce Kan su tafi daddy ya tarasu yace

To Sarkin rawar Kai bance kaje kana shiririta ba Dan zan sa masu duba mini me kukeyi a makarantar banda shirme Karatu kawai ya kunayi

Sannan ku rike juna Salim ga d'an uwanka nan farouk

Kaima farouk ga Dan uwanka nan Salim ka fishi nutsuwa Dan Allah Idan yayi Abu ba daidai ba ka tsawatar masa

Sunkuyadda Kai yayi yace Insha Allah daddy

Tashi kuje Allah Ya muku albarka Ya baku abinda kukaje nema. Ameen suka amsa duka

Daddy da kallo.ya bisu Tabbas yaron Yanada nutsuwa sosai kuma Yanada saurin shiga rai Da yamma suka shiga makarantar

Gyara dakin sukayi kafin suyi alwala su tafi sallah Suna fitowa Salim ya Kalli farouk yace

Yunwa fa nakeji

Daidai lokacin da motorsu haidar tayi parking Kamal yace

Wazamu tambayane kaga waincan d'in sun juya sun tafi Ka ajiyeni kawai ka tafi kaga olredy dare yayi

Suna zaune suna cin abinci Wayar farouk tayi k'ara Kallon Salim yayi yace

Ina zuwa

Waje ya fita domin amsa Wayar Yana dagawa Audu yace Farouk kanajina

Eh

Ya amsa

Dama Indo ce tace na kira ka Bata Wayar yayi

Cikin sauri tace

Yaya kana makarantar yanzu Eh

Ya bata amsa

Haidar ne ya karaso kusada Salim yace Pls ina so na tambayeka admin block ne Jin muryarsa yasa shi saurin d'agowa Dariya yayi yace

Haba farouk me zakaje yi admin block Cikin Rashin fahimta haidar yace

Bangane ba nifa tambayarka nazo yi kuma kanaso ka gaya mini wata magana daban Salim yace

Kai farouk Meye Hakane Wai?

Kai ba sunana farouk ba haidar nake inaji ka sami Matsalar kwakwalwa ne Wucewa yayi Ya barshi da mamaki.

Farouk ne ya k'araso yace Ka Gama mu wuce

Cikin mamaki yace

Kai dakata Yanzunan Wani me Kamada Kai Ya barnan Dariya farouk yayi yace

Me Kamada ni kuma Cikin maamaki yace Dama kana dariya?

Kai kabar shirme Dan Allah zo Muje kawai Cikin sauri yace

Wlh da gaske nake Dan da farko na d'auka kaine ma To sauke

Farouk ya bashi amsa

Duka ya Kai mishi daga nan suka Cigaba da harkarsu Yau Dai suka Fara daukar lectures

A gajiye suka dawo

Kwanciya Salim yayi shi kuma farouk daukar bokiti yayi Ya nufi tap Dan d'ibar ruwan wanka Har ya dawo yana nan yarda ya barshi

Tsaki yaja yace

Mtsew dallah tashi banza kalallab'a kawai Dariya Salim yayi yace

Wlh buddy bakasan me ba Ji nake Kamar na gudu

Be ce masa komai ba har ya Gama shiryawa

Hot plate ya jona Ya d'ora musu abinci

Har ya Gama Salim be tashi ba Zubawa yayi Yace

Ka tashi muci abinci Mikewa yayi Ya sauko

Dauke abincin farouk yayi yace

Wlh baka isaba kaje Ka wanke hannu

Yana mita ya mik'e Ya wanko hannun yazo Ya saka hannu suka Ci abincin Salim dai shi kad'ai yake firarsa.

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Kuyi hakuri na manta masu kananan Waya number din bazai fito ba amma yanzu na gyara Sannan ba lallai na dinga muku posting sau biyu ba amma Idan ya samu zan iya muku

Na gode

06

Haidar ne ya fito daga library hannunsa dauke da littafi. Gefensa Hafiz ne (room mate dinsa)

Wata shegiyar motace taho a rough driving

Cikin sauri Salim da yazo shiga Cikin library yayi saurin Kautar da haidar d'in Cikin ikon Allah motar tayi gefe

Parking tayi can gefe

Kusan minti uku kafin a bud'e motor a fito Irin crazy din nan ne sunsha swag

Duka Tsayawa kallonsu sukayi

Kallon up and down yayi musu kafin ya shafi lips dinsa yayi hanyar school cateen A Fili haidar yace ja tsaki kafin ya juyo Ya Kalli Salim yace

Na gode sosai Nunashi yayi yace Kamar na Sanka Ko?

Murmushi Salim yayi yace Admin block

Dariya haidar yayi yace

Hakane Ashe kanada hankali dai Harara Salim ya balla masa yace Da me ka maidani?

Dariya haidar ya kuma yace

To Naji yanzu ina abokinka me Kama Dani. Sosa Kai Salim yayi yace

Yana d'aki yana barci

Oh I see

Haidar ya gaya

Juyawa yayi Ya kalli Hafiz yace

Ka tuna Wanda nake baka labari akanshi to ka ganshi nan Dariya Hafiz yayi yace

Ai na tabbatar

To yanzu Bamu number dinka so that sai muna gaisawa Dariya suka yi duka kafin suyi exchanging numbers Salim yace

Am sure zaka yarda da maganata one day Tame fa

Haidar ya tambaya

Ta cewa kuna kama da Dan uwana Oh Ya fara kenan

Ya gaya Yana jan hannun Hafiz Ya Cigaba da cewa Salim let's call it a day

Murmushi yayi

Farouk ne ya k'araso yace Kai buddy ina kaje ne Dariya yayi yace

A ina ka ganni ne? D'aga Kai yayi Ya ce

Oh ka Fara hankali gaskiya zan gayawa daddy Dariya Salim yayi yace

Yanzu muka rabu da. Me Kamada Kai Murmushi farouk yayi yace

Ka Fara ko

Allah da gaske nake har muryarku iri d'aya sai dai shi yafika fara'a da surutu Murmushi kawai farouk yayi yace

Muje mu shirya kasan munada lecture Suna tafe suna fira

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tacewa driver Mu tafi.

A gajiye suka dawo Dan haka farouk wanka kawai yayi Ya kwanta Salim ya kalleshi yace

Kai buddy ka tashi ka d'ora mana abinci Wlh am hungry Juyawa yayi yace

Kai ma ai ka iya Dariya Salim yayi yace Tab shiririta ma kenan

Farouk na jinsa yayi banza dashi.

Ganin bazai tashi bane ya sashi mik'ewa Ya fito domin siyan Wani Abin da zai ci Haidar yayi dariya bayan Salim ya bashi labarin yunwa ta fito dashi daga daki To mu karasa nima ita nakeji

Dariya sukayi gaba daya kafin Salim yace Kasan Dan uwana akwai kafiya ne Tunda be so ba bazai Dafa ba

Karar Wayarsa ta katse shi

Ganin me kiran yasa yayi saurin dagawa To gani nan zuwa kawai ya fad'a

Kallon haidar yayi yace

Ba kana tunanin shirme nake gaya maka akan kuna Kama da Dan uwana ba To kazo Muje yanzu ka ganshi

Dariya haidar yayi yace

Wannan Dan uwan naka din jinsa yafi ganinsa Dariya Salim yayi yace

Muje daga nan kaci girkinsa Kallon d'akin yayi yace

Tab gaskiya ya tsaftatu sai kace da Mace Dariya kawai Salim yayi

Wayarsa ya ciro Ya Kira farouk Yana dagawa yace

Bro ina ka shiga ne gamu tareda haidar

Naje submitting assignment ne amma bazan dade ba zan dawo Farouk ya bashi amsa

Salim yaceda haidar to Kaji Ya tafi cafe

Daga kafada yayi Alamar babu damuwa Yace

Yanzu dai zubo mana girkinsa muci Dariya Salim yayi yace

Wlh da Dad'i Haidar yace

To Nace babu dad'i ne kawai ka bari bakina zai tantance Zuba musu abincin yayi suka Fara ci

Haidar dai harda santi Bayan sun gama yace

To ni zan wuce Dan zanje library yanzu Idan ya dawo ka gaishe dashi. To zaiji

Rakashi yayi kafin ya dawo ya kwanta Sallama farouk yayi Ya shigo

Tsaki yaja ganinshi a Kwance yace

Ni Wlh na gode wa daddy da be fitar da Kai kasar Waje Karatu ba Dariya Salim yayi yace

Eh naji babu komai haidar na gaisheka Kallo farouk ya bishi dashi kafin yace

Wa kaje ka jajibo mana ne?

Kanaso ka ce mini ka manta da Wanda na ce maka kuna Kama ne.

Tsaki ya kuma ja ya d'auki bokiti ya fita

*** *** *** *** *** Wani

Makeken gida motor ta shiga

Wata da bazata wuce 32yrs bace ta fito daga motar Cikin sauri take tafiyar tanayi Tana hadawa da gudu Falon ta fad'a Ko sallama babu

Bata kula da yaranta dake mata sannu ba Upstairs kawai ta nufa

Wani hadadden bedroom ta shiga. Jakarta da mayafi ta jefar Akan gado Zagaye d'akin ta Fara Cikin sauri Tace

Bazai yiwu ba

Da sauri ta janyo wayarta ta Danna kira Ana d'agawa tace

Aunty mun shiga uku sirrinmu dake boye shekara goma sha ashirin ya kusa Ya bayyana Daga can barin tace

Meya faru?

Yau naga d'aya daga Cikin 'Ya 'yan yaya idris A gigice tace

Me?

Karyane Wlh bayan boka yace sun mutu ki dai sake bincikawa . Huci tayi tace

Wlh Ko zanyi yawo tsirara bazan Bari su bayyana ba

Ni ina nan shekara goma sha shida na kasa Haifar yara . To bazai yiwu kisan yadda zakiyi dashi

Ajiyar zuciya tayi tace

Bakisan Meye tashin hankalin ba

Tareda Salim d'an wajen kareema na ganshi What ya akayi suka had'u

Wlh ban saniba na dai gansu kawai

Ki san yadda zakiyi ki rabasu ke Idan ta Kama kiyi sanadiyar barinshi makarantar To.

farouk Ko haidar

Story and written by

By deeja

One love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

07

Haidar Kalli Salim yace

Wai wannan Dan uwan naka Anya akwaishi kuwa duk lokacin da zan zo baya nan Harara Salim ya galla mishi yace

Ai koda nake Da surutu nasan me nake fad'a Dariya haidar yayi yace

Am sorry Kaji friendy yanzu dai zuba mana abinci muci. Salim yace

Sai dai na zuba maka Dan Ranar nan da mukaci tareda Kai daya zo sai da yayi magana Murmushi haidar yayi yace

Daga ji MA zai yi kishi Dariya suka yi gaba d'aya Abincin ya zuba masa yaci Yana gamawa yaceda Salim

Kalli zan tafi sbd inada lectures Karfe biyu sai gobe OK to jirani na raka ka mana

Tare suka jero har Waje

Sai da ya kaishi har bakin room dinsu kafin ya juyo A bakin kofa Ya taradda farouk

Harararshi yayi yace

Kai Wlh kanada matsala yanzu kuma daga ina Kake Kallonshi kawai farouk yayi yace

Daga ina Kake? Dariya Salim yayi yace Daga library daddy

Murmushi farouk yayi yace

Ai Nike taking responsibility dinshi Anan D'aga gira d'aya Salim yayi yace

Da gaske?

Kana tambaya ne Ni Muje Dan Allah

Shiryawa sukayi suka tafi lecture Sai hudu suka dawo

Tana office dinta Tana nazari Ya shigo Ciki Babu batun sallama kujera yaja ya zauna Cikin shagwaba yace

Mummy Don Allah account Dina yayi low kuma daddy tun jiya yace zai mini transfer har yanzu shiru

Tura masa Jakarta tayi

Yasan me take nufi hakan yasa ya zura hannu ya Debi yadda yakeso ya tashi ya Fita

Clash sukayi da farouk da Salim. Har ya wuce Ya dawo ya tsaya Nuna Salim yayi da hannu yace Kai zo nan

A hankali Salim ya Fara tafiya

Ganin da gaske zuwan zai yi yasa farouk saurin janyoshi baya Me Kake nufi ne ?

Ko kallonshi be yiba yaja hannun Salim Don su wuce Tare hanyar yayi yace

Kai bada Kai nake magana ba Kallon rainin wayo yayi masa yace

Kwakwalwarka bata ja ne ina nufin bazai zo ba. Zaro idanu yayi yace

Kai kasan koni waye?kasan waye babana? Kasan waye mamana a makarantar nan.

Kallon Salim yayi a zafafe yace Kai zo nan

Da sauri yaceda farouk Bro yi hakuri ka bari naje

Farouk be ce komai ba ganin hakan yasa ya taka yaje har gabansa Kallonshi yayi sama da k'asa yace

Daure mini igiyar takalmi na Tsugunawa yayi Ya daure masa Runtse idanu farouk yayi

Salim ya dago ya kalleshi yace Na Gama

Lips d'in sa ya shafa yace

Jeka ka dauko min wayata a office din mummyna A sanyaye ya juya ya tafi

Har ya Kai bakin kofa Ya D'aga murya yace Sorry boy Gata a jikina

Salim ya Kalli farouk

Watsar da takardun hannunshi yayi Ya juya ya bar wajen da sauri Dariya yayi yace

Gud boy ina ka samo wannan shi kuma

Faisal wannan abokina ne duk wulakancinka Ya tsaya kaina Kada ka kuskura kaje kanshi. Salim ya bashi amsa sannan ya tsugunna yafara tattara takardun da farouk ya zubar Take d'aya Faisal yayi yace

Me kace shin abokinka yafi Dan uwanka ne? Mikewa Salim yayi yace

Baka San Wani abokin yafi Wani Dan uwanba ballantana a yanda nakejin farouk yafi mini Kai sau dubu

Tureshi yayi sannan ya tsugunna Ya d'auki paper d'in ya tafiyarshi

A hanya suka had'u da haidar Dariya yayi yace

Mutumina sai ina

Dan karamin tsaki ya ja kafin yace Zanje wajen Dan uwanane

Muje to

Duk inda suke tunanin zasu ganshi babu shi Hankalin Salim ya tashi sosai da sosai Haidar ya kalleshi yace

Ka kwantar da hankalinka bazai bace ba Kallonshi yayi

Idanu Sunyi ja yace

Ranshi abace yake kuma be iya fushi ba Zama sukayi Akan Wani dakali haidar yace To amma na d'auka bakuyin fad'a ai

Shiru yayi for some seconds Sannan yace

Bani na bata masa rai ba To waye?

Haidar ya tambaya Labari Salim ya bashi

Murmushi Haidar yayi yace

To yanzu dai ka sake kiran wayarshi Kira yayi no answer

Haidar yace

Kawo number din na kira da wayata Kira yayi still be D'aga ba

Ajiyar zuciya haidar yayi yace To yanzu abinda za'ayi shine

Muje room dinku mu zauna may be zuwa anjima Ya dawo Tsayin one hour be dawo ba

Haidar yace

Friend zan tafi gaskiya Dan inaso naje Wani waje.anjima. D'aga masa Kai kawai yayi

Yana fita Salim ya koma ya kwanta

Tunani yakeyi Wai shi farouk wane Kalar mutum ne A haka har barci ya d'aukeshi

Motsin bude kofa Ya sashi farkawa

Kallonshi yayi kafin yace Wani Abu farouk yace Ka tashi kayi sallah kazo muci abinci

Kallo kawai Salim ya bishi dashi Be kuma cewa komai ba

Sai ma wajen zama daya nema Ya zauna yana karanatawa Waya a kunne

Daga yanayin yadda yake Wayar ya gane da Indo yakeyi Cire Wayar yayi yace

Malam Kaifa nake jira

Tashi Salim yayi yaje yayi sallar Har ya dawo Wayar yakeyi

A sanyaye yace

Za muci abinci yanzu sai anjima

Da sauri Salim ya amshe Wayar ya Kara a kunne Sallama yayi Ta amsa

Kai waye ? Ta tambaya

Kai baki sanniba ni sunana yaya Salim

Farouk najinsu suna shirmensu be ce komai ba har su Inna Mari sai da yasa ta basu suka gaisa Shidai farouk abuncinsa Ya Cigaba da ci

Sai da kud'in ciki ya k'are sannan suka hak'ura

Farouk na gamawa ya d'auki Wayarsa da papers d'in d'azu Ya fita D'aga kafada Salim yayi Ya Cigaba da cin abincin sa

Sallama sukayi suka shigo Dariya haidar yayi yace

Kana nan zaune ya dawo Ko? Daga Kai yayi kawai

Hannu haidar yasa acikin abincin Kallon Hafiz yayi yace

Bismillah sunaci

Suna fira har suka Gama Dariya Salim yayi yace

Wato Hafiz abokinka yacika kwadayi Dariya Haifz yayi yace

Eh mana

Hada fuska haidar yayi yace Dan ma ina taimaka muku Kana taimakawa cikinka dai Tashi yayi yace

Tunda Hakane bazan kuma cin abincin ku ba . Fita yayi

Hafiz yayi dariya yace

Kofa ruwan Lipton be iya dafawa ba Dariya Salim yayi yace

Allah sarki Kamar ni kenan

Farouk ne ya shigo kallonsu sau daya yayi Ya Kauda fuskarsa Hafiz yace

Ya ka dawo kuma har Ka je ka canza kaya gaskiya kayi sauri

Farouk dai da idanu ya bishi

Can yace

Kai bro ina ka samo wannan kuma? Dariya Salim yayi yace

Hafiz ga Dan uwana da nake baka Labari Sakin baki yayi yace

Wlh na d'auka wasa Kake Ashe da gaskene ikon Allah Wlh da zance haidar ne Murmushi Salim yayi yace

Bro ga friend d'in Wanda nake baka labarin kuna Kama haidar ka tuna shi

farouk Ko haidar

Story and written by Deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Dafatan anyi zabe Lafiya Allah Ya k'ara Had'e kanmu baki d'aya Ameen 08

Murmushi yayi yace

Wai Kai wane iri ne haka?

Ji ka yarda Wai muna Kama? Hafiz yace

Wlh bakuda banbanci Kamar Ku d'aya Dafa kanshi yayi yace

To Kai ma Ya saka maka virous d'in kenan Dariya Hafiz yayi

Had'e fuska Salim yayi yace Wane virous gareni

Daukar bokiti yayi Ya fita

Dariya Hafiz Ya kuma yi Wanda ta kular dashi Daukar pillow yayi Ya bishi da gudu

Sai da ya kaishi block dinsu sannan ya kyaleshi Wayarshi ce tayi k'ara

Ganin mamanshi yasa shi dagawa Cikin bashi umarni tace

Kaje office din Hajiya zainab Kan yace komai ta kashe Wayar

Iska ya furzar Ya nufi hanyar admin Sallama yayi

Sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga

Tana zaune Kan two seater shi kuma d'an mulkin yana kan Kujerar ta ta aiki Wayarsa yake daddannawa

Yafi minti talatin a tsaye kamar basu San dashi ba

Jikin dakiya ya kuma cewa

Aunty gani

Ai na san da Kai tunda ina gani Ta gaya Tana d'agowa ta kalleshi

Tafi minti biyar har ya Fara tsarguwa sannan tace Kaje ka Kira abokin naka Wanda yafi Dan uwanka Murmushin takaici yayi

Ya juya ya fita

Tabbas da matsala na kira farouk muzo nan Ya fad'a to yanzu yaya zanyi

Wata dabara ce ta fado masa arai Da sauri Ya nufi block dinsu Suna zaune suna fira ya samesu Zama yayi a gefe

Haidar ya juyar da Kai Hafiz yayi dariya

Harara Salim ya galla mishi Ya juya ya Kalli haidar yace Kai mutumina zo Muje Kaji Babu inda zan je

Haidar ya gaya Yana mik'ewa Hannunsa ya rike yace

Haba aboki kada kayi mini haka mana Kazo Kaji

Haidar yace

Ka kyaleni malam babu abinda zan ji Sakin hannunsa yayi yace

Ina Idan aboki yana Cikin matsala aboki na taimaka masa amma Ashe ba haka bane Kenan gaskiya ta fada

Da sauri haidar yace Wacece?

No babu damuwa kawai Juyawa yayi Ya fita

Da sauri haidar ya bishi

A hankali ya Dafa kafadarshi yace gaya mini gaskiya me ya faru? Ajiyar zuciya yayi yace

Muje wajen da yakeda sirri Garden suka je

Salim ya Kalli haidar yace

Ka tab'a jin ana masarautar modibbo Dariya yayi yace

Waye besan da zamanta ba kace mini masarautar adamawa Murmushi yayi yace

Sarki Al'ameen idris abdussamad

Sarki na talatin da uku

Sarki ne me adalci sosai ya haifi yara guda goma sha bakwai a ciki akwai mata akwai maza Babana shine d'a na hud'u yana da yaya Wanda yake bi Al'ameen suna kiransa da modibbo Yana India acan yake da zama bayan Wani Abu ya faru

Cikin kannen kakanmu akwai Wanda ya haifi Hajiya Zainab Kallonshi haidar yayi yace

Kana nufin Hajiya Zainab dana sani Ta nan makarantar D'aga Kai yayi yace

Bata da mutunci da babana da ita full cousin ne

To Tana da Ya Wacce ke auren wannan wan babana dana gaya maka Ta fita Rashin mutunci sosai

Da mamana da hajiya zainab babansu d'aya kuma Yarta ita ta raineta wato Hajiya Salma Mamana macece me ha'kuri dalilin dayasa take danne wasu abubuwan dake faruwa kenan Ita duk Wani Abu daya shafi Hajiya Salma to girmamashi take

Hakan yasa muke taka tsantsan da bacin ran Wanda ya danganceta

Jiya na baka labarin me ya faru tsakaninmu da Dan hajiya Zainab Wanda kanwa take ga hajiya Salma

To yanzu ta kira mamana tace naje Naje d'in tace sai naje da farouk Jinjina Kai haidar yayi yace

To yanzu meyasa ka bani labarin nan ?

Na baka ne saboda inaso kaje a matsayin kaine farouk Dan zuwa da farouk akwai matsala Salim ya bashi amsa

Na fahimta Haidar ya fada

Yauwa nasan kafi farouk sanyin zuciya Dan Allah Idan mukaje suka nemi da ka bada hakuri ka bayar Kaji

Salim yace da haidar. D'aga Kai yayi Alamar yaji

Yadda ya barsu haka ya dawo ya samesu Kallon haidar tayi

Har saida ya Fara gajiya da kallon

Ta bagaren ta kuwa gaban ke faduwa Tabbas wannan jinin modibbo ne Ya ilahi

Ta fada a hankali Tana dafe Kai Dan karamin tsaki haidar ya ja Cikin zafin rai Faisal yace

Kai karamin

Please Login or Register in order to submit comment