You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma dariya

Salim yace

Mutumina Dan Allah ji Kamar yau suka Fara ganin mota Dariya haidar yayi yace

Tab da aiki

Shidai farouk be ce komai ba

Daidai kofar gidansu driver yayi parking Mata har ta katanga leke akeyi

Ikon Allah sai kallo Indoce ta fito da gudu

Rungumeshi tayi Cikin murna Tana fadin Oyoyo yaya

Cikin bacin rai farouk yayi saurin janyeta yace Ke Meye Hakane bafa ni bane

Kallon mamaki Ta bisu dashi

Jan hannunta yayi Ya juya ya kallesu yace Amegbo Idan kun Gama gulmar sai ku shigo Dariya sukayi sannan suka shiga

Kamar yadda yan gidan suka Saba da kallo suka bisu

Duka Suna tsakar gida Dan labari Ya Riga da Ya iso Akan ga farouk can ya dawo Wajen Inna Mari ya Fara zuwa Cikin murna aka tare su

Sun sha Tarba irin ta kanawan Dabo Haidar ya d'auki Dan wake Ya saka a baki Ya Kalli Inna yace

Wai umma sunan da ake bawa Dan wake Ya kamata kuwa? Kamar ya fa?

Gani nayi yanzu zamani yazo anayin na filawa. Daga Kai Inna Mari tayi

Ya Cigaba da cewa

To ai kamata yayi a kuma ce masa Dan filawa (lol

)Hartana farouk sai da yayi dariya wannan karan Salim yace

Mutum kawai Dan wake na kai masa yana mana santin ga inda dad'i yake

Ai ni an bani labarin kanawa Ada can baya saboda basuda masara da yawa sai suka koma danbu da Dawa.

Zaro idanu farouk yayi yace

Me? Bansan karya ina aka taba dambu da Dawa Dariya Inna tayi tace

Tab to wannan labarin waye Ya baka ? Wani ya diba Ya kai baki yace

A radio mana ana bada tarihin danbu

Ance fa lokacin da ake mulkin mallaka turawan da sukazo Kano danbu aka musu Da suka Ci

Kawai sai suka Fara fadin Well-done matawalle

Wai mata ne basu iya fadi ba Dariya Kowa yayi

Farouk yace masa

To kalarshi Kake ci Ko

Ina! Wannan yafi nasu dad'i harda madara aka barbada mishi fa Wannan karan harda Inna hadiza a dariya

(Tab danbu na kai maka Salim ) Sai da suka Gama cin abincin sannan Haidar yace

Ni Wai baka kaini wajen Audu ba Tashi farouk yayi yace

Ku jira nayi wanka sai Muje d'aki mu ajiye kayan mu sai Muje inda suke

Sunyi murna da ganinsu sosai

Kamar su hadiye su haka suka dinga murna Audu ya kallesu yace

Amma fa da mamaki kana gaya mini kamarku amma ban d'auka Kamar ta Kai haka ba.

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Congratulations for the second tenure malam nasiru Ahmad El -rufa'i Allah Ya tayaka riko.

Ameen

12

Dariya haidar yayi yace To ai gani Ya Kori ji Audu ya kuma cewa

Hakane amma Kamar tayi yawa Farouk yace

Wai ina Salim ne?

Yana can yana barci Audu ya bashi amsa

Dariya haidar yayi yace

Allah Dan uwanka Ya cika lalaci Kamar wata mace. Harara farouk ya galla mishi yace

Ina ruwanka to gulma kawai

Daga audun har haidar d'in dariya suka Cigaba da yi Da yamma suna zaune a wajen wata bishiya suna fira Abu ce ta taho da sauri

Tsayawa tayi Tana Washe baki Cikin matukar farinciki tace

Kai umaru kaga yadda ka dawo Dan birni Haidar ya rike dariyarshi yace

Da gaske

D'aga Kai tayi tace

Yasin da gaske duk da dama Kai daban Kake ko a Da Shiyasa Nace babu Wanda zan aura sai Kai

Kara sunkuyadda Kai farouk yayi Dan kar ta gansa Wanda hakan yasa suka kasa rike dariyar Shagala tayi da kallon shi tace

Kasan me

Girgiza Kai haidar yayi

Idan munyi aure zaka dinga mini irin wannan dariyar Allah Tana birgeni sosai Abu ta fad'a da kallo suka bita

Tabbas wannan sai a hankali

Fari tayi da idanu Wanda hakan ya kuma basu dariya Indoce ta k'araso wajen

Ganin haidar yana dariya yasa ta daure fuska Dan itama ta d'auka farouk ne Cikin jin haushi ta kalleta tace

Wai Meye haka kika zo kika tasa su a gaba kina shirme su kuma suna dariya sun maidake wawiya

Tsayar da dariyar haidar yayi yace

Haba humaira Abin ne da ban dariya kuma kin San nima ina sonta Zaro idanu tayi tace

Da gaske yaya farouk Eh ko Da wani abun ne

A'a babu komai Juyawa tayi ta Fara tafiya.

Hararshi farouk yayi sannan ya mik'e Ya bita da sauri Abu kuwa tsabar shirme bata ma Lura dashi ba

Shikuma haidar dama abinda yakeso kenan Audu kuwa Dan abi yarima asha kida ne Wai danma oga Salim baya nan kenan ta Kusa gida sannan ta tsaya Tana share hawaye Tabbas abinda Ya gaya hakan yake nufi

Humaira

Ya kira sunanta

Juyowa tayi suna had'a idanu tayi saurin Cigaba da tafiya

Ganin ta Kusa shiga gida yasa yayi saurin janyota Runtse idanu tayi Dan ko ganinshi bataso

Haba humaira ke yanzu Idan aka ce miki zanso Abu sai ki yarda haidar ne ke Mata wasa Da sauri ta bud'e idanunta Tana kallonshi

Ke in banda abinki kin taba ganina ina dariya Kamar haka. Shiru tayi Tana tunani Tabbas Hakane kuma fa

Ita tunda take ma zata iya irga sau nawa yayi dariya a gabanta da yawonta Hannunshi yasa a fuskarta yace

Gaya mini me kike tunani? Babu komai yaya

OK to Muje na baki tsarabarki

Dariya tayi har hakoranta suka bayyana Rike hannunta yayi suka shiga gida tare

Rigar daya d'auka a shoprite a kaduna ita ya ciro Ya bata Amsa tayi Tana farinciki

Har Cikin sasansu Ya rakota d'akin Inna hadiza ta shiga shikuma ya d'auki bokiti ya shiga wanka

Rigar ta ciro Cikin farin ciki ta shafa Jikinta

Tabbas ta fahimci farouk yana son Abu me purple a jiki Dan duk kayan dayake bata da Kalar batasan meyasa yake son Kalar ba

Sai da ta nunawa Inna hadiza sannan ta ajiye Akan gobe zata saka Tabbas yanzu ta Fara zama Yar gayu

Kiran sallar da aka Fara ne yasa haidar dakawa Salim duka Cikin sauri farouk yace

Meye haka Wai kuna Abu Kamar yara Dariya haidar yayi yace

To babba Kai Wlh matarka zata Kalli sanabe. Salim yace

Nidai Allah Ya isa Wlh Haidar yace

Banza tunda ka mini dariya na ma fasa baka labarin budurwar Nawan Cikin sauri Salim yace

Da gaske yi hakuri ka bani

Ganin yadda farouk ya daure fuska yasa haidar kwashewa da dariya yace Mutumina Bari muyi sallah na baka story.

Harda yadda take fari

Ganin bazasu kyaleshi bane yasa shi Mikewa yace

Idan kun Gama childish din sai ku fito. Suna idar da sallah suka wuce bakin bingi Kallon ruwan suke suna fira

Acan gida kuwa

Indo ta Kalli Inna hadiza tace

Amma Inna kinsan yaya farouk yana gari kuma Wlh ni tsoro nakeji yazo Ya ganni tare da saurayi ballantana sani ma.

Harara Inna hadiza ta aika masa tace

Kaji mini mutuniyar banza Idan kin zauna shi farouk d'in ina kuna sane babu aure a tsakaninku sannan Idan bakije Kinyi zance ba ta yaya zaki sami Mai sonki har ya aureki zaki wuce Ko sai na tashi.

Cikin sauri ta Mike tace

To Inna Bari na cire kayan Kinga yaya farouk ya kawo mini Kallon da innan ta mata ne yasata yin shiru.

Mayafi ta d'auka kawai ta fita

Firar suke amma hankalinta baya wajen Waige waige kawai takeyi

Gabantane ya tsananta buga hango su da tayi sun taho Kallon dayake matane yasa Jikinta Fara rawa

Had'e rai yayi lokacin da suka iso

Sallamar da sani Ya musu ma sauran ne suka amsa banda shi

Tsabar bacin rai har jijiyoyin goshinsa sai da suka tashi kallo ya jefa mata Wanda ita kad'ai tasan me yake nufi kafin yace

I give you two minutes ki sallameshi kizo Idan kika wuce Murmushin bacin rai yayi Ya wuce

Jikinsu gaba d'aya yayi sanyi Indo kuwa kuka ta Fara

Tabbas tasan ba karamar wahala zatasha ba yau Sani yace

Wai shi wannan me yake takama dashi ne Haidar yace

Ina wanta shi? Eh

Sani Ya amsa Salim yace

To Ya bata umarni ne a matsayin na yayanta Audu kuwa da kyar Ya iya rike hannunta

Ai Kamar ya k'ara zigata ne kukan ta kuma fashewa dashi tace Yaya Audu ka bashi hakuri Dan Allah

Kema kinsan yana hakuri Akan komai amma banda wannan kawai ki shigo kada ki karawa kanki laifi.

Wucewa sukayi suka Barta a tsaye Kallonta sani yayi yace

Kiyi hakuri kinji Nidai fatana Dan Allah ko me zai miki kada ki Dena sona

Wannan ma ta sonshi yakeyi bata ni ba kenan. D'aga Kai tayi Alamar taji

Wucewa yayi Ya Barta

Ganin bata wa kanta lokaci take yasata nufar hanyar Cikin gidan Sai tayi Kamar zata shiga sai ta dawo

Tayi ya Kai biyar sannan tayi shahadar shiga Har ta Kusa shigewa Cikin gida

Ya fuzgota

Da bango Ya hadata

Ta baya Ya matse mata hannu Har Tana Iska dakyar take Shaka Ga wuyanta dayake Mata zafi Goshinta kuwa tasan Ya fashe Tsabar azaba yasa kukan yaki fita Cikin fushi yace Mata

Wannan zafin da kike ji bekai Wanda nakeji ba.ina alkawarin da kika yi mini. K'ara hadata da bango yayi yace

Ba magana nake miki ba

K'ara tayi sannan ta fashe da kuka Cikin sheshshekar kuka tace

Kayi hakuri bazan kuma ba

Su haidar da ihun datayi ya fito dasu Tsayawa sukayi suna mamaki Audu ne ya Matsa Kusa dashi ya sa hannu

Yana fadin

Meye haka farouk

Ko gezau beyiba haka be saketa ba Azaba yasa kuka ma dakyar yake fita Cikin sauri Audu yace

Ba Tsayawa kallo zakuyi ba kuzo ku taimaka mana Dakyar suka iya kwaceta

Ai Tana jin ta shaki Iska me dad'i ta arta ana Kare Kamashi Audu yayi Ya kaishi d'aki zaunar dashi yayi Ruwa Ya Debo Ya miko masa

Cikin zafin zuciya ya watsa masa ruwan a jiki Magana yakeso yayi amma ya kasa

Jikinshi har rawa yakeyi saboda bacin rai

Haidar kuwa da Salim jikinsu sanyi yayi Dan basu tab'a ganin ya zuciya Kalar wanna ba Inna hadiza ce ta shigo

Kallon su Salim tayi taga jikin su a sanyaye

Juyawa tayi ta Kalli Audu taga Ya tsaya tsaki tsamo da kaya a jike

farouk Ko haidar

Written by deeja one =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Kuyi hakuri kun Jini shiru yau abubuwa ne sai a hankali 13

Fita kawai tayi sai Gata ta dawo da kwanan sha cike da ruwa ta kawo mishi. Babu musu farouk ya amsa ya kafa Kai sai da ya shanye Tass

Sannan ya ajiye

Kwantawa yayi yana rawar jiki

Inna hadiza ta Kalli Salim da haidar tace

Ku kuma fa Kowa Ya tsaya Kamar Wani akuya a gaban kura Dukda a tsorace suke sai da Salim yayi dariya

Juyawa wajen Audu tayi tace

Kai kuma kaje ka canza kaya mana Ajiyar zuciya yayi yace

To Inna

Baffa ne ya shigo dakin Idanu ya zubawa farouk

Kusa dashi yaje ya zauna addu'a yayi Ya tofa masa Kallon Salim yayi yace

Meyakawo haka ? Cikin rawar murya yace Firar da Indo tayi ne

Jinjina Kai yayi kawai yace Ku tashi Muje

Duka sasan suka wuce acan suka tarar da Inna Mari da Indo a Kwance Allah sarki Inna Mari akwai kawaici

Waje suka samu suka zauna Kallonsu baffa yayi yace

Tunda har farouk baya son firar da Indo take fita to daga yau na soke shi kubarshi muga abinda yake nufi

Babu Wanda yace komai har ya Gama Tashi yayi Ya fita

Su Audu ma suma fita sukayi Salim ne ya Kalli kofar dakin yace

Mutumina kuje bakin bingin nan yau bazan je ba Haidar yace

Saboda me?

Inaso na zauna wajen Dan uwana ne

Dariya haidar da Audu suka yi kafin Audu yace

Kaga ba ma fa lallai bane ya farka yau watakila sai zuwa gobe kaga Muje kawai Yau dai zaman be musu dadi ba

Duk shiriritar Salim kasayi yayi Hakama haidar da Audu

Jungum Kowa Ya zauna

Haidar ne ya katse shirun yace Wai dama yana yin haka?

D'aga Kai yayi yace

Amma sai Idan ranshi ya bace ne Ajiyar zuciya yayi yace

Allah Ya kyauta kuma babu Rashin Lafiya Eh mana

Audu yace

Kawai zuciya ce tayi mishi yawa Dariya Salim yayi yace

Tab kasan me na tuna Girgiza Kai sukayi Alamar a'a

Dariya ya kuma yi sannan yace Lokacin da aka watsawa Audu ruwa Dariya suka yi dukan su

Hakadai har dare yayi suka bar wajen Washegari sai wajen Tara sannan ya farka Da addu'a a bakinshi

Duka idanu suka zuba masa suna kallonshi Shima dai su yake kallo

Shiru sukayi for some minutes sannan haidar yace Sannu Nawan ya jikin

D'aga Kai yayi Alamar yaji

Da hannu ya nuna mishi Alamar ya D'aga shi

Cikin sasan su ya nufa sai da yayi wanka sannan ya dauro alwala dakin Inna Mari ya shiga ya Rama sallolin da ake Binsa

Gaishe da Inna yayi kallonshi tayi tace Akawo maka abinci

Girgiza Kai yayi Alamar a'a Indoce tayi sallama ta shigo Ganin farouk a zaune yasata Fita da sauri

Inna hadiza ta shigo Tana fadin

Ina farouk d'in Indo tace Ya farka

Eh Gashinan a zaune Inna Mari ta bata amsa

Sauran yan uwansa ne suka dinga shigowa suna mishi sannu Har zuwa dare bai samu yaci komai ba

Dan ji yake Kamar ana hura wuta a jikinsa

Da zasu kwanta ruwan addu'a baffa ya bashi ya sha ya shafa a jiki sannan ya kwanta Cikin dare haidar ya farka da salati a bakinshi

Kallon farouk yayi

Tabbas yasha yin wannan mafarkin to amma me Be tab'a ganin fuskar mutumin ba sai yau Share zufar fuskarshi yayi a hankali

Wani mutum ne daure da sarkoki a jikin wata bishiya me feshin wuta Wasu irin halittu ne zagaye dashi suna azabtar dashi

Akodayaushe baya ganin fuskar mutumin Wani haske ke zuwa ya Rufe masa idanu Amma a yau Allah Ya taimakeshi Ya gani fuskar farouk ce

Kusa dashi ya Matsa ya taba shi

Jikin sa Wani irin zafi yayi Kamar garwashi Arude Ya Fara tashin Salim

Da sauri Salim yace Meke faruwa

Kuka haidar ya keyi yace Salim farouk mutuwa zaiyi

Cikin sauri Salim yakai hannu jikin sa

Ba Shiri Ya Janye domin kuwa zafin yayi yawa

Bude kofa yayi Ya shiga kwankwasawa su Audu kofa Abinda Ya bashi mamaki Shine

Bugawa daya Audu ya bud'e yace

Farouk Ko dama na zaci haka Jeka Bari na kira baffa Salim komawa dakin yayi yayinda Audu ya tafi taso baffa

Shima dai baffan barcin beyi nisa ba Dan yasan hakan zata faru Tareda su Inna Mari ya taho

Ruwa a cikin bokiti k'arami aka zubo Da tsaftataccen tsumma

Inna hadiza ke jikawa Tana shafa masa A hankali zafin jikin Ya Fara raguwa

Maganin da ta bayar aka siyo mishi tunkan Ya tafi Inna Mari ta dauko aka bashi ya sha Baffa ya Kalli su haidar yace

To sai da safe ko

Amsawa sukayi jiki a sanyaye

Kowa da abinda yake tunani har gari Ya waye Alhmdllh lafiyar Allah Ya tashi babu ko ciwon Kai Sai dai haidar daya tashi da ciwon idanu

Inna hadiza tace

Oh ni dije Daga wannan sai wannan

Su uku suka tafi wudil suka siyo masa magani Yadai yi sauki

Ganin sun damu yasa yace

Kada ku damu dama nakanyi lokaci zuwa lokaci Ana gobe zasu tafi

Da yamma suna zaune suna fira Indo tazo wucewa

Hango su da tayi yasa Jikinta har Bari yakeyi tazo ta wuce Farouk yayi murmushi yace

Ina zuwa

Da sauri Ya bita har ta Kusa zuwa gida Humaira

Cak ta tsaya Juyowa tayi

Idanunta har ya kawo ruwa tace Wlh ban tsaya da Kowa ba yau Murmushi yayi yace

Ba wannan na tambayeki ba gobe zamu tafi fa Ajiyar zuciya tayi tace

Allah Ya kaimu

Tare suka karasa gidan

Wanka Ya shiga yayinda ita kuma ta shige dakin Inna Mari

Washegari suka d'auki hanyar babban birnin ilimi Garin autan sambo balaraben sarki Garin zazzau ci Garin Hausa

Bayan su Inna Mari sun cikasu tsarabar K'auye irinsu kuka da kubewa da dadda.......

Farouk Ko haidar Nidai Nace farouk

Maryam khamis (one love) tace Wai haidar

To readers let see wayafi mutane

Idan kana bayana kace ni Idan kuma kana bayan haidar wato My one love ka D'aga hannu.

farouk Ko haidar

Written by deeja one love =ØŠÝ

Dedicated to madina m umar

Yeah munfita mutane Wlh 14

Sun tarar dasu duk suna gida

Kwanciya Salim yayi yana fadin Wayyo Allah na gaji

Dariya haidar yayi yace Wlh Kai kacika San jiki

Harara farouk ya galla mishi Ya shige bayi Salim yace

Kai Wlh ka kiyayeni fa Hararshi yayi yace

Anki a kiyaya d'in yi Abin da zakayi

Yana fitowa daga wanka Ya shirya

Kallonsu yayi Ya ce

Ku tashi kuyi alwala mana

Sai da sukayi sallah sannan suka Ci abinci Alhmdllh idanun haidar d'in ya Washe sosai Da yamma

Haidar na zaune kusada mama Salim kuma ya kwanta a kujera Kan shi na Saman kafar farouk

Shi kuma farouk d'in yana danna Waya

Yaya muhammad da yaya Mubarak ne sukayi sallama suka shigo Cikin matukar farin ciki yaya Muhammad yace

Lallai kace iyayen rigima sun iso gidan. Salim ya dago ya kalleshi yace

Yaya waye masu rigimar? Kai da farouk mana

Kallon juna sukayi shida haidar suka kama dariya Da mamaki yaya Muhammad d'in ya bisu da kallo Kallon Mubarak yayi yace

Yaya kaga wasu identical twins? Kallonsu duka yayi yace

Tab Kamar tayi yawa Salim yayi dariya yace

Yaya bafa yan biyu bane hasali ma d'aya na Kano d'aya na kaduna. Cikin mamaki suka dinga kallonsu.

Mubarak yace

Ni Wlh akwai Wanda suke mini Kama ma dasu Mama tace

Nima haka na ke gani

Tashi Salim yayi Ya matsa kusada yaya Mubarak yace Yaya Ashe ka dawo ina tsarabata

Hararshi yayi yace

Wato tsaraba ita ta dameka Ko to Tana wajen mama. Da dare suna gama cin abinci Salim yace

Mama har yanzu fa baki bani ba Yusra tace

Me za'a baka? Ina ruwanki ne Ya bata amsa

Mama ta Kalli husna tace

Jeki ki dauko mini jaka Akan besides cabinet Tafiya tayi

Mama tace

Amma ai nan da bikin yayanku zaku dawo Ko

Cikin farin ciki Salim yace Ansa ne?

Eh mana nanda three months Yaya Muhammad yace

Ai gwara yayi Ya wuce nima sai nayi Dariya sukayi gaba d'aya

Yusra mu kuma sai a had'a namu da naka Ko yaya Salim Tabe fuska yayi Cikin shagwaba yace

Mama Wai kinji ai ban isa aure ba ko Dariya suka kuma yi

Haidar yace

Kai Wlh akwai katon banza

Hararshi farouk yayi bece komai ba ya Cigaba da Danna wayarshi Dariya Salim yayi yace

Kai Wlh ka kasa gane nine na gaban goshin farouk indai kayi mini ba daidai ba sai Ya harareka Husna data dawo daga Aiken mama ta Mika mata jakar

Haidar yace

Ni ai hakan be dameni ba Murmushi mama tayi tace

To ai kuwa ka Dena nuna musu Haka Dan su masu tuya da ruwa ballantana sun sami Mai Abba yace

Nidai zan so naga aurenku Kallonshi Salim yayi yace

Abba yanzu Kai sai kayi mini aure Abba yace

Irinka mashirmanciya zan nema na had'aku Dariya suka kuma yi

Mama ta mik'awa Salim jakar hannunta tace Gashi

Amsa yayi

Laptop ne apple product sai turarruka da agogo Haidar ya dauke agogon yace

Wannan Nawane

Tab malam ka isa sai dai ka d'auki laptop d'in Ko turare amma ni agogon nake so Da sauri farouk yasa earphone a kunnenshi

Ja inja suka Fara wannan na cewa be so wannan ma haka Su kuwa duk zuba musu idanu suka yi

Ganin abun bazai kareba yasa Yaya Muhammad yace Abinda za'a yi shine

Farouk ya dau laptop Kai haidar ka d'auki agogo Salim kuma tunda kaine k'arami ka d'auki turare

Zunboro baki yayi yace

Dama Kai ai tun ba yau ba nasan Dan adawatane Yaya Mubarak yace

To Kai haidar ka Bar mishi agogon ka d'auki laptop d'in Mak'e kafada yayi Alamar a'a

Mama tayi dariya tace

Tab ikon Allah gaskiya farouk na Kokari

Ganin Abin bazai k'are bane yasa farouk cire headphones d'in yace Dalla kun damu mutane

Wlh mama ki kwace duka Ki hanasu Salim yace

To ai Ma ni Ya kamata ya barwa tunda nine k'arami Kallon haidar farouk yayi yace

Kaga ka bashi kawai ka dau turare ko laptop d'in Had'e rai yayi Ya ajiye yace

Dama nasan shi kafi so ai kuma bayanshi zaka goya banaso duka ma Girgiza Kai yayi Ya d'auki agogon Ya Matsa Kusa da shi yace

To amsa ka rike

Kin Karba yayi ajiye masa Kusa dashi yayi. Wajen Salim ya koma yace

Kai ka hada duka dakin laptop din da turaren Hararshi yayi yace

Sai da ka fifitashi akaina sannan zaka Wani ce na had'a duka biyun to banso ma duka Ikon Allah

Har suna hada baki wajen fadin hakan

Farouk kuwa kallonsu duka yayi Wai nan Sunyi zuciya Ajiyar zuciya yayi

Kafin ya d'auki wayarshi Ya bar wajen Mama ta janyo haidar Jikinta tace Haba yarona Meye haka Wai

Ka amshi agogon mana Murmushi yayi yace

To mama

Kallon Salim tayi tace

Kai kuma zo ka dau Wani Abin Anan

Bayan sai da kika rarrasheshi sannan zaki kula Dani Abba yace

Ni ina ganin maslaha kawai d'aya daga Cikin ku ta dau wannan d'in anjima sai biyu suje su siyo suma

Salim ya harari haidar yace Sai ka rike wannan d'in Shima hararshi yayi yace Sai dai Kai ka rike

Wata husumar ce ta tashi

Da yaya Muhammad da husna kuwa me zasuyi banda dariya Abba kuwa k'ok'arin shi d'aya daga Cikin su ya d'auka

Ganin Abin nasu da iskanci

Yasa yaya Mubarak ya daka musu tsawa yace

Dalla malamai Wani ya d'auka Ko na gaggaura muku Mari Abin kuma sai Ya koma duka Kowa Na k'ok'arin d'auka

Shi kanshi wannan karan yaya Mubarak din sai da yayi dariya Mama tace

Amma wallahi Allah Ya shiryeku.

Yaya Muhammad yace Kowa Ya dauki Abu daya gobe sai Ya siyo Cikon biyun sannan aka sami maslaha

Karshe ma dai farouk suka barwa agogon Dariya husna tayi tace

Mama gwara da yan autanki basu Nan da abin yayi miki yawa Dariya yaya Mubarak yayi yace

Tab aiko da suna nan sai dai su su hakura Ko kuma wa'innan katon banza su Dena ba Yusra tace

Ji Kamar ba yanzu suka Gama fada ba amma har sun Cigaba da firarsu Farouk ne ya fito daga daki

Kallon Salim yayi yace

Kai inaka sa mini wannan book d'in Yana Cikin Jakata

Hararshi yayi yace

Kamar Wani karatun yakeyi Da ido Ya nuna mishi abba Dariya haidar yayi yace

Mutumina kaga yadda kayi kuwa Kamar Akuya a gaban kura Dariya sukayi gaba d'aya

Harararsu farouk yayi yace Dalla ku tashi Muje mu kwanta.

Washegari ma wajen siyayyar haka suka dinga rigima

Yaya Muhammad ganin zasu bata mishi lokaci yasa shi daukar musu da kanshi Ana gobe zasu koma makaranta

Haidar ne Kwance jikin mama yana barci Salim da farouk suka shigo gidan

Salim ya daka mishi duka yace Dagata

Tsaki haidar yaja yace Allah Ya isa Wlh Dariya Salim yayi yace

To na fasa gaya maka abin da nayi niya

Mama ta Mike tace

Allah Ya shiryeku wallahi.

Shidai farouk d'aki Ya tafi ya barsu a wajen

farouk Ko haidar

Written by deeja one love

Dedicated to madina m umar

15

Suna shiga makaranta suka Fara Dagewa da karatu domin next semester suka shiga Yanzu har Salim da haidar sun rage shirmensu sai dai lokaci zuwa lokaci

Yau Cikin matukar gajiya Haidar ya shigo D'akinsu

Farouk yace Yadai

Kwantawa yayi a Gadon Salim yace

Na gaji since jiya nake library Yanzun ma wanka zanyi naci abinci sai na tafi ina da lectures Murmushi farouk yayi yace

Kafa rame kwana biyu

Gefen fuskarshi ya shafa yace Wlh ji nake Kamar na gudu.

Dariya Salim yayi yace Rago kawai

Da mamaki suka kalleshi

Wai yau Salim ne ke cewa Wani Rago Ikon Allah

Jan plate din haidar yayi yace Yaro banda lokacinka yanzu

Shaf shaf yaci abincin ya wuce block dinsu Sai four sannan suka tafi

Library

Karatu ne can ma sukayi Sai six suka fito

Direct school cateen suka nufa Cake da coke suka siya

Suna zama

Salim ya Kalli farouk yace

Wlh karatu da wuya Dan bakaji idona ba . Murmushi kawai farouk yayi.

Suna Cikin ci haidar ya karaso zama yayi sannan ya ciro Wayar shi

Yace

Meyasa ka kashe wayarka mama ta kira tanaso tayi magana da Kai Farouk yace

Wlh nama mantane ban bude ta ba yau gaba d'aya

Tace ma ta Kira ta Salim shima no answer Wai Lafiya Nace Wlh karatu ne ya samu gaba Haidar ya fada Yana mikowa farouk d'in wayarshi

Bayan sun gaisa tace

Dama Maganar kayan daurin auren yayanku ne za'aje siyowa to shine nakeso Naji measurements dinku

Murmushi yayi yace

Ai duk kawai Kai d'aya zai yi mana

OK to takalmi fa sannan waincan yan rigimar Kalar agogon da suka fi so Murmushi ya kuma yi sannan yace

Kada ki damu dasu Mama kawai kala d'aya zaki daukar mana To shikenan ayi karatu Lafiya

Insha Allah.

Kashe Wayar yayi Ya Mike yace Kuzo mu tafi.

Yau dai zasu wuce kaduna Su dubo mamie datayi Rashin Lafiya kwana biyu. Haidar yace

Dan Allah ku Bari sai next week kafin nan na Gama mu tafi tare Make kafada Salim yayi yace

Tab mun shirya ka tsayar damu Next zuwa kaje

Farouk ya Dafashi yace

Ka bari nanda next month zamuyi Hutu fa

Sai Muje duka. Kwana daya nefa gobe zamu dawo To shikenan sai kun dawo.

Har bus stop sai da ya kaisu sannan ya dawo .

*** **** ****

Zaune take Tana shan lemo da waya a hannun ta Cikin nishadi take

Sallama tayi tace

Ya akayi Zainab kin sallameshi Madam Zainab tace

Wlh yaya Salma nayi bincike bazai yiwu ba domin yayanshi babban lawyer ne babanshi kuma babban likitane.

Share zufar dake fuskarta tayi Cikin Tsakanin bacin rai tace

Zainab ki san yadda zakiyi ya

Please Login or Register in order to submit comment