You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ"[12/17/2019, 19:14] Takori: SHIMFIDA"

"LAGOS, 25 WATAN ZULKIDAH"

R

"anar Talata ce, cikin watan Zul kidah, garin Lagos kamar koyaushe cike yake da cunkoson ababan"

"hawa, babu masaka tsinke ; musamman da yake a daidai lokacin kowa na kokarin kai wa gida domin tsira daga duhun dare da samun hutu."

"Ma aikata sun taso, suna son isa gida domin yada kafada, haka  yan kasuwa sun rurrufe shaguna an"

bar wa gobe cinikin in Allah ya kai mu. Da misalin karfe shida na yamma kenan.

"Daidai lokacin ne Rukayyah ta sauka a garin Legas cikin jirgin kasa, wanda ya dauko ta tun daga"

"Yola. A kalla kwanan su biyu cur cikin jirgin don haka Rukayyah ta gaji likis, ta yi fiyat irin na kowanne matafiyin da wahalar zaman jirgin kasa ya koda."

"Doguwar Bafillatana, santaleliya, mai dauke da kayatacciyar doguwar fuska ma abociyar zati da"

"kamala. Wadda Allah ya wadata da kayatattun idanu farare kal. Babban sirrin kyawun RUKAYYAH USMAN JALINGO, shi ne gassun girarta masu kauri, bakake sidik wadanda ke zane zirit kamar shatar siririn watan da bai fi kwana biyu da bayyana ba."

"Rukayyah ma abociyar kwalliya ce, don haka ne duk da gajiyar da ke tare da ita, da idanunta da"

"suka fada, in ka dube ta sosai za ka hango bayyanannen kyawun fatar ta da jambaki ruwan hoda mai sulbi da ta mulke siraran lebbanta, wanda ya dace da launin shaddar Ghalilahdark pink da ke jikinta."

"Dinkin jikin ta babbar riga ce Senegalese har kasa da zane, tana yafe da dan kankanin gyale, launin"

"kayan jikinta, amma mai haske wato light pink, wanda ya fi shaddar haske. Hannunta na dama sakale da babbar jakar mata ta hannu baka kirar Yue Jin  yar kasar China, mahadin bakin takalmi mara tsayin"

dunduniya da ke kafarta.

"Kasancewar ta yafa gyalen a kafadunta ne, yasa bakin gashin kanta mai santsi da sulbi ya bayyana"

"ta kasan dankwalinta, wanda ke kunshe cikin tafkeken ribbon ruwan hoda. Kai da ganin Rukayyah ka san ba ta fito daga kankanin gida ba, abin nufi, kanta a waye yake, idanunta a bude farare sol."

"Kai tsaye ta fito daga (rail-station)wato tashar jirgin kasa cikin takun nutsuwa, tana tura  yar jakar"

kayanta troller mai matsakaicin girma zuwa inda ta hangi tadi-tadi masu jiran mai daukar su drop (shata).

"Tun kafin ta karasa gare su wani direba ya taso ya karbe ta, yana mai tambayarta inda za ta je,"

"fuskarta babu walwala ta ce, ""BGC, Road 2, G134."""

"Cikin mintuna ashirin sun iso kofar tangameman gidan, mai dauke da irin girgijejen (gate) din nan"

"na zallar farin karfe, da akewa lakabi da (Mahdi-ka-ture). Ta bude kofar motar ta fito, shi ma ya fito ya bude (boot) din motar ya fiddo mata jakarta, ta kirgo kudin da ta tabbatar sun fi karfin abin da zai tambaya, ta mika masa. Hannu bibbiyu cikin rawar jiki Bayaraben ya sanya ya amsa, yana ta zuba mata godiya kamar ba zai daina ba."

"Ba ta kara bi ta kan shi ba, ta karasa jikin (gate) ta kwankwasa da  yan yatsunta zara-zara wadanda"

ta kawata da zobban zinare guda uku.

"Maigadin da ke kan aiki ya leko, ganin Rukayyah ce babu dogon turanci ya bude mata kofa, wani"

"yaron gidan Yohan da ke baiwa shukoki ruwa ya taho da hanzari ya karbi jakar hannunta, yana yi mata sannu da zuwa."

Sanya kafarta cikin harabar gidan ke da wuya wata ni ima da sanyi suka sauka a zuciyarta. Ni imar

"garin Legas, ma abociyar lumshi da sanyi, gami da kamshin furanni shuke-shuken da ke harabar gidan, su nesuka haifar mata da wannan jin dadi. At last she escape(auren da ba ta so). Ta kuma ji kamar ta rabu da kaya. Wato kafaffen Babanta, da tsohon masoyinta, Aliyu. Kai dama cakudadden gidan nasu baki daya"

"da ke cikin garin Jalingo, cikin jihar Taraba."

"Tana taku sannu a hankali, cike da rangajin gajiya da yunwa zuwa cikin gidan. Motoci ne da suka"

"amsa sunan motoci  yan uban-ubansu a fake cikin rumfar adana motoci biyar da ke harabar gidan, wannan na wane waccan."

"Furanni kala-kala masu dadin kamshi da sanya nisahdi, haka gaba dayan gidan shimfide yake da"

"koran (grass carpet) masu taushi tun daga farkon gidan har zuwa siririyar kofar shiga cikin gidan, wadda Rukayyah da Yohan suka bi zuwa kuryar gidan."

"Ta yi sallama a babban falo, cikin siririyar muryarta mai dauke da alamun matsananciyar gajiya. Rabi"

"mai aiki da ke goge-goge a tebirin cin abinci, ta amsa mata, lokaci guda ta juyo cike da fara a tana cewa."

 Marhabin da  yan hutu.

"Rukayyah ta ce,  Ki jiki da abin haushi, wane hutu kuma? Mun yada kwallon mangwaro baki daya,"

mun huta da kuda?

"Ta ce, ""Ba dai har kin kare makarantar ba?"""

"Ta soma taka steps a hankali tana cewa,  Zancen ki ke so. "

"Rabi ta rangada zazzakar guda ""Ayyururiiiiii& .. Kai ka ce marokiya ce, ta ce, ""Ashe aure ya zo, zan"

"sha shagali, zan cake in cancare, amma dai da mai sunan Alhaji ne in ce ko? Don ba zan taba mancewa da kyautar bajintar da ya yi min ba, tun a farkon ganina da shi, wadda har yau har gobe ba a kuma yi min"

"rabin-rabin ta ba."""

"Rukayyah ta ji kamar Rabi ta soka mata mashi a kahon zuci, don haka ba ta juyo ba, balle ta amsa"

"mata, ta ci gaba da tafiya sululu& . Can kuma ta kwabe baki tana mai ci gaba da hawa matattakalar"

"benen. Ta ce,  A ah da Malam Audu ne. (Wato mijinta mai rasuwa)."

"Rabi ta jujjuya kai cikin alhinin tunawa da masoyi ta ce,  Allah sarki ! Kyale bawan Allah a"

"makwancinsa, ya ci gaba da jirana, kafin in zo, Abdullahi sai Rabi, Rabi ce Hurul-Ininsa, don haka ki nemo"

"naki yarinya, tun da wurwuri, tun dare bai miki ba. Rabi da Audu sai gani sai hange& . "

"Ta karasa sama tana dariyar Rabi, a zuciyarta ko tausayi ne fal. Domin ita kanta shaida ce a kan"

"matsananciyar soyayyar da suka yi tun ba ta da wayo, wanda Allah ya yi wa rasuwa shekarun baya, bayan rayuwar aurensu ta shekaru ashirin ba tare da haihuwa ba. A da shi ne babban direban gidan."

"Haj. Umaimah,  yar kimanin shekaru hamsin a duniya, amma in ba gaya maka a kai ba, tsammani za"

"ka yi ba ta fi shekaru arba in ba, saboda kyawun jiki da hutun da take ciki, wadda ta kasance matar aure daya kwal cikin wannan tangamemen gida. Ta idar da sallar Magariba kenan ba ta kai ga tashi daga sallayarta ba, kamar yadda yake a al adarta, sai ta yi sallar Isha i take tashi, zama take ta yi ta lazumi da"

dogon carbi mai dubu har sai an kira sallar Isha i.

"Duk da nauyin shekaru masu yawa da suka hau kanta, idan ka dube ta ka ga kyakkyawar mace"

"Bafullatanar usli, wadda ta ci zamaninta a da can, aka dama da ita cikin gwagwarmayar rayuwar aure,"

"take kuma cikin jin dadi mara misaltuwa a yanzu. Ma abociyar riko da Addini, kuma a uwa ta kowanne fanni."

"Sannu a hankali Rukayyah ta bi jikinta ta kwanta, ta kwantar da kai a kafafunta, bayan ta cillar da"

jakar hannunta a kan kujera kai ka ce kankanuwar yarinya ce  yar shekaru uku. Tana mai furta.

"""Wash! Allah na, am very very tired. Wato ta gaji likis."

"Ba ta yi tsammanin ganinta a wannan lokacin ba, don haka ta kama baki, ta kai hannu ta shafa"

"kanta, farin ciki da mamakin ganinta a daidai wannan lokacin da ba ta yi tsammani ba, zane baro-baro a kyakkyawar fuskar manyantakarta ta ce,"

 Rukayyah! Ikon Allah!! Ke da wa ki ke tafe?

"Dan yatsanta daya (sabbab) ta daga mata, wato ita kadai  Ni kadai raina Hajiya, na taho a jirgin"

kasa.

"Hajiya ta yi salati ta sanar da Ubangiji ta ce,  Yanzu shi Usman da saninsa ya barki ki ka taho ke kadai?"

"Don me ba ki gaya min ko a waya ba in turo direba ko Yayanku su taho da ke? Kada ki sake wannan gangancin kin ji na gaya miki don Legas ba Jalingo ba ce, balle yanzu da ake rikicin nan na Addini da"

kabilanci.

"Ta ce a shagwabe kamar ta fashe da kuka,  Hajiya nima tafiyar ce ban shirya mata ba. "

"Ta ce,  Me ya faru? Zancen mai sunan Alhajin ne dai har yanzun ake ta yi kamar cin kwan"

"makauniya?"""

"Rukayyah ta yi narai-narai da ido fal da hawaye, kiris take jira, ta sako su ta ce, ""Shi ne Hajiya, bari"

"dai in yi sallolin da ke kaina, in ci abinci, sai in gaya miki komai."""

"Hajiya ta kwalawa Rbai kira ta taho da sauri, ta ce ""Ina can ne ina hadawa mutuniyar abinci."""

"Hajiya ta yi murmushi cikin yabawa ta ce,  Ya yi kyau, ai mantawa na yi ba sai na saki ba. To a gyara"

"mata dakin kwana ko, kuma ki hada mata da mutumin nata (faten doya). "

"Rabi ta ce,  Wallahi kamar na san tana tafe, dazu da na yi sharar falo na ce bari in share dakin don"

haka dakin a kintse yake.

"Hajiya ta ce,  Sannunki dai Rabi, Allah ya yi miki albarka. A lokacin Rukayya ta dade da shiga bayan"

gida.

"Saboda sanin da Hajiya ta yi wa Rukayyah, wanda ko uwar da ta haife ta ba za ta gaya mata wacece"

"Rukayyah ba, yasa kallo daya da ta yi mata ta tabbatar tana tare da matsananciyar damuwa."

"Rukayyah ma abociyar raha da kazar-kazar, duk ta saki ta yi lakwas kamar mai takaba. Don haka"

"kafin ta idar da sallar ba abin da Hajiyar ba ta kissima a ranta ba, kan abin da ke damun Rukayyar, ya kuma taso da ita haka gatsar takanas-ta-Kano tun daga Jalingo."

"A sanin ta dai auren Rukayyan ya kusa, don sati mai zuwa take shirin tafiya gida can Jalingo kai wa"

"Baban Rukayyan gudummuwarta ta furniture (kayan gado) data yo ordermusamman tun daga China,"

"duk da canje-canjen da Rukayyan ta dawo tana nunawa a kan al amarin, bai hana iyayenta da duk masoyansu fasa shirye-shiryensu na auren nata ba."

"Rabi ta gama shirya abinci bisa ledar cin abinci ta fita, domin Hajiya ba ta hawa tebur, saboda ciwon"

"kafafu da take fama da shi shekara da shekaru, an yi maganin an yi har an gaji, kasashen duniya daidai ne maigidanta bai kaita ba, domin neman magani ; amma in an samu ya lafa, bayan  yan watanni sai ya dawo. Irin ciwon nan ne mai matukar naci da baya jin magani, Allah ya hada ta da shi. Amma kullum"

cikin godiyarsa take.

Rukayyah ta kama hannun Hajiya ta mike suka karasa suka bararraje bisa ledar. Rukayyah ta ja

"tangaren din da ke dauke da farfesun kifi ragon ruwa, tana zarewa Hajiya kaya tana sanya mata cikin filet dinta suna hira jefi-jefi wadda cin abincin ya rinjaya."

Da sukakare Rabi ta zo ta kwashe kayan suka koma falo suka nutse cikin bakaken (leather) masu

tsananin taushi da suka yi wa falon kawanya. Rukayyah ta dauki remote ta canza tasha daga MBC3 zuwa

tashar CNN inda ake watso labaran duniya (World News) suna nuna zalunci da barnar da Yahudawan Isra eela ke yi wa Musulmin yankin Ghaza ne.

"Kai da ganin ta ka san cikin damuwa take, don dai yarinya ce (frank) mara sanya abu a ranta. Haka"

"take da faram-faram, ba ta da fushi ko kankani, sai dai wasu abubuwa da yawa wauta ce ziryan wadanda"

"idan tana yi za ka fahimci cewa  yar fari ce, wadda sangarta hadi da shagwaba suka gamewa jiki. Duk da haka Rukayyah yarinya ce mai hankali da nutsuwa matuka, tare da girmama duk na gaba da ita."

"Hajiyar ta dade tana kallon Rukayyah, cikin nazari wanda ita Rukayyan ba ta sani ba, hankalinta ya yi"

nisa a wani wajen daban. Tana mai nazarin manya-manyan sauyukan da ta gani a tare da yarinyar cikin watanni uku kacal da ta yi ba ta ganta ba.

"Ta rame, ta yi dan duhu, dogon hancin ya dada sirancewa, ya sanya dara-daran idanun cikin lungu,"

"duka jikinta ya saki. Rukayyah ma abociyar zafin nama, wadda da wuya ka ganta ta zauna tana kallon talbijin ko karance-karance, ita dai ta ganta tana kazarniya ta tsaftace wuri da jikinta tukunnah."

"Ga son aiki, musamman girki, don daga sanda ta zo Rabi ta yi sallama da girkin Hajiya da Alhaji (in"

"yana gari), duka aikin Rukayyah ne. Daga san da ta zo za ta fara kawar da datti, komai kankantarsa, amma yau ko dan wankan da take da zarar ta iso kafin ta yi komai ba ta yi ba. Haka yawan wasan da suke yi da Rabi, duk ta rage, ko Rabin ta tsokano ta ba ta kulawa. Da kuwa sai Hajiyar ta shiga tsakani ta"

raba su.

"Haj. Umaimah ta kare nazarinta kaf a kan Rukayyah, ta kawo gwauron numfashi cikin ranta ta ce,"

"""Allah ya jish-she mu ALHERI. A fili kuma cikin sanyin murya mai kwantar da hankali ta ce,"

"""Yaya aka yi ne, Rukayyan Daddy, ke nake sauraro?"""

"Rukayyah ta yi ajiyar zuciya, ta zuki iska ta fesar abin ta, ta ce, ""Wallahi Hajiya maganar Aliyu ce ta"

"tashi, yanzu ma Dady bai san na taho ba, ni da Mama muka tsara hakan. "

"Wayar Hajiya da ke gefe ta shiga kiran sallah alamar shigowar kira, ta mika hannu ta dauka ta yi"

"murmushi ta ce,"

"""Ga Maman nan, na san tana can ta kasa hadiyar loma, sai ta ji yadda ki ka iso. "

"Ta kai kunnenta ta ce, ""Salamu alaikum. Ta juya tana kallon Rukayyah tana dariya, ta ce,  Rukayyah"

 yar rigima ba gata nan ta iso lafiya. Suka yi  yar magana daga karshe suka yi sallama ta kashe.

" Amina ke tambayar yadda ki ka iso, ta ce tun fitowar ki hankalinta bai kwanta ba, sai daga baya ta"

"dinga ganin wautar kanta, da ta bari ki ka taho gari irin Legas ke kadai. "

"Rukayyah ta murmusa ta ce,  Mama kenan, ni wallahi har birnin Sin zan iya kai kaina, don kawai in"

gujewa auran Aliyu& ..

"Cikin matsanancin mamaki Hajiya ta ce,  Ke kuwa a kan me? Ya haka Rukayyah? Me ya yi zafi ke da"

Aliyun naki kuma?

"Ta turo baki ta bata fuska ta ce,  Da kenan Hajiya, amma yanzu na tsane shi bana ko san ganin shi,"

ni ki daina ma cewa Aliyu na kada  yan amin su amsa& .

"Dariya ta kama Hajiya, ta jawo ta jikinta tana dariya ta ce, ""Rukayyan Daddy, Rukayyah rigima, ba ke"

"ki ka kawo mana shi ba muna zaman zamanmu, kina ta wasa abin ki, muka karbe shi;"

"Domin da alama dan mutunci ne ga ilimi, ga rufin asiri, ga shi har kudin aurensa mun karbe mun"

"sanya rana, kada ki maida mu kananan mutane mana? Ko dai gaskiyar Usman ne kin fiya giggiwa da ruwan ido? "

"Rukayyah ta soma huci, ta janye jikinta a hankali daga jikin Hajiyar, ta koma can gefe guda, ta"

"takure. Ita kadai ta san yadda zuciyarta ke tafasa. Mintuna biyu kuma a tsakani sai hawaye sharr! Sharr!! Wasu na korar wasu bisa lallausar kumatunta. Gaba daya ta yi jawur, abin ki da farar mace sol."

"Hajiya ta kidime, ta taso da kyar ta dawo kusa da ita, ta kamo kanta ta rungume a kirjinta, tana"

"sauke zazzafan numfashinta a kirjin Hajiyar, sai da ta tabbatar zuciyarta ta yi sanyi ta ce a tausashe."

 Rukayyah!

"Ta dago rinannun idanunta ta dube ta, amma ba ta amsa ba. Ta nuna kanta ta ce,"

" Ni wace ce? Ta ce cikin rishin kuka,  Hajiyata! "

"Ta ce, ""Idan da gaske kin yarda ni Hajiyarki ce, wadda ba ki da wadda ta fita bayan uwar da ta haife"

"ki, ki gaya min damuwarki a kan auren Aliyu, ni kuma in na ji hujjar ki abar karba ce kin` sanni ai, ba zan bar Usman ya yi miki auren da ba kya so ba, wallahi sai in bana raye!"""

Tasa hannu biyu tana share hawayenta cikin gasgata furucin Hajiyar. Cikin sanyin murya ta soma yi

wa Hajiyar bayani.

****

T

"un da na dawo gida ranar da muka yi candy Daddy ya ce in ce da Aliyu ya fito, domin ya dade da yin"

"alkawarin da zarar na kare makaranta aure zai yi min, ba zai bar ni in ci gaba ba, ba don komai ba wai saboda na fiya rawar kai, taurin kai da kidifiri."

Ya sha gayawa Mama idan ya bar ni na shiga babbar makaranta ba zai iya tankwara ni ba. Ni kuma

sai a yanzu ne na san wasu abubuwa game da shi (Aliyun) wadanda a da ban sani ba. Ko ko in ce ya yi min karya ya boye mini ya yaudare ni. Wallahi Hajiya na tsani mutum MAKARYACI to shi kuma Aliyu

halinsa kenan.

"Kin san na sha gaya muku Hajiya ba zan taba auren MAI MATA ba, domin ba zan taba mance halin"

"da muka shiga ba a sanda Daddy ya auri Anty Jummai ba, mu da Mama da shi kan shi Daddyn, ke ma kuma kin sani. Wanda ya janyo muka yi rayuwa ta shekaru goma ba tare da mahaifinmu ba, wanda da ba don ke ba da ban san wane irin kuncin rayuwa za mu fuskanta ba. Wallahi ko a lahira Hajiya bana fatan"

"Allah ya hada ni da kishiya."""

"Ta yi shiru, tana hadiyar numfashi da kyar cikin matsanancin takaici, na tasowar wani miki da ya"

"dade yana kwance a zuciyar mutum. Hajiyar ba ta katse ta ba, domin ta san abin da take tunani, murmushi kawai ta yi. Sai da ta mula don kanta ta ci gaba."

"« Farkon haduwata da Aliyu, a Gombe ne na je hutu gidan Anty Asi kanwar Mama. Farat daya na ji"

"Aliyu ya shiga raina saboda wasu dalilai, muhimmi shi ne kasancewar shi dan GOMBE, ni kuma duk"

"wanda ya fito daga wannan gari abin so ne da girmamawa a gare ni. Ba don komai ba sai don cewa su ne suka rufa min asiri, ni da uwata, a sanda duniyar mahaifin mu ta juya mana baya!"

"Da farko na tambaye shi ko yana da mata? Don Aliyu ko a lokacin ba yaro ba ne, a kalla zai girmi"

Yayan Nafisah. Ya rantse min wallahi a kaina ya fara sha awar aure.

Don haka na sake da shi muke soyayya har zuwa sanda na kawo shi gare ku. Ya kuma ce min shi

"ma aikaci ne a Bankin Arewa, saboda ya raina min hankali."

"Don kudi kam da sittiru na kece raini yana da su, amma ni wannan ba shi ne a gabana ba, kawai na"

"san ina masa so na tsakani da Allah, kasancewata mace ta farko da za ta shigagidansa, ni dai burina a rayuwa kenan."

"In zauna ni kadai babu kishiya. In auri miji ni kadai mu shimfida rayuwa irin taku da Babansu Nafisa,"

"mai cike da aminci, nagarta da kaunar junada girmama juna tun daga kuruciya har girma, babu tashin hankali ba wulakanci, sai zama na soyayya da kauna mai dorewa ta Fisabilillahi. Hajiyar ta yi murmushi,"

Rukayyah ta ci gaba.

 To kwatsam a wannan hutun namu na karshe ya zo min (visiting) shi da kanwarshi Rufaida za ta yi

"sa ata. Akwai wata (room-mate) dina Nanah ita ma  yar Gombe ce, tana ganin Rufaida suka dafe juna suna murnar ganin juna. To bayan tafiyar su ne nake tambayar ta ina ta san Rufaida?"

"Wallahi Hajiya budar bakinta sai cewa ta yi ai matar Aliyu Yayan Rufaida, Aunty Aysha kanwar"

"Mamanta ce, su kan hadu in dukkaninsu sun je mata hutu."

"Ta ce  ya yan Anty Aysha uku da Aliyu kuma shagonsa da ke cikin babbar kasuwar Gombe, kusa da"

shagon yayanta ne abokinsa ne sosai.

"Wato dai Aliyu dan kasuwa ne, ba ma aikacin Bankin Arewa ba, (kamar yadda ya ce). Wallahi Hajiya"

"a lokacin ban yarda ba, saboda ban taba tsammanin cikakken mutum kamar Aliyu zai iya karkace kai ya kantara karya haka ba, wai don kawai a aure shi."

Me ya rasa da sai ya yi karya zai samu matar aure? Me ye abin yi min karya da aikin banki ina

ruwana da wani aikin banki?

"Wato ma makwadaiciya ya dauke ni ko diyar matsiyata? Na ce da Nanah kai ban yarda ba, karya"

"take, ina! Ba dai Aliyu na ba."

Ganin yadda na kidime ta tambayi abin da yasa na damu haka. Ban ji nauyi ba na gaya mata Aliyu

"yana a matsayin (fiance)dina ne, amma ya ce min baya da mata."

Nanah ta ce idan ba ki yarda ba ranar da za mu je dauko kayan (Practical) na yi miki alkawarin ki bi

ni zan kai ki har dakin matar Aliyu.

A gaba dayan kwanakin da suka biyo baya ban yi barci ba. Ita kuwa Nanah da biyu ta dage sai ta kai

ni ko don taya  yar uwarta kishi.

"Ranar dauko kayan (practical) na yi karyar gidan Aunty Asikanwar Mamana zan dauko nawa kayan,"

don haka aka bar ni na bi direbansu Nanah.

"Muna tafe tun daga Bajoga har Gombe ban san inda kaina yake ba, saboda tsoron abin da zan je in"

"tarar, kada furucin Nanah ya zan tabbatacce."

Gidan yana nan a (Commercial Area). Nanah ta danna kararrawa wata mace fara tas gajera irin

"Fulanin Kumo, ta bude kofa, kallo daya na yi mata na ga tsabar kamaninsu da Nanah."

Da kyar na iya daga kafa na shiga falon. Tangamemen hoton Aliyu da matar suna sanyawa junacake

"a baki ranar dinner dinsu shi na fara yin tozali da shi. Na koma gani dusu-dusu, a haka muka zauna cikin kujera tana lale da  yanmatan Bajoga."

"Ta tafi ta kawo mana ruwa da lemu, a lokacin yara guda biyu suka dawo daga makaranta. Kallo"

daya na yi masu na tabbatar na ga  ya yan Aliyu tun daga kai har yatsun kafa.

"Ga kuma daya yana rarrafe a tsakar daki. Tun da na ji kugin motar Aliyu cikina ya kulle,  ya yan"

"hanjina suka dunkule waje daya, yawun bakina ya bushe, na sunkuyar da kai ban kara dagowa ba."

Tun daga bakin kofa yake kira  Darling I m back. Daga can cikin kicin ta amsa  welcome daddy gani

nan zuwa .

"Ya shigo falon amma ni bai gane ni ba, saboda kaina a sunkuye yake. Don haka ya yi saurin sauke"

hannuwan cikin kunya ya ce a a su Nanah ne?

"Ta fito dauke da tray da ta daura lemon kwali da kofuna da ruwan (Ragolis) ta karaso, kafin ta aje"

sai da ta ba shi hot kiss a kunchi kana ta zo ta aje mana ta koma kujerar da yake ta zauna a masangalinta.

"Da na ga Nanah ta zame tana gayar da shi nima sai na yi yadda ta yi, na zamo daga cikin kujerar na"

ce ina wuni?

"A hanzarce ya juyo ya dube ni, nima na yi mai kyarr da ido. Ban kara cewa komai ba na mike na fito,"

"ya biyo bayana yana ta magiyar in tsaya in saurare sa, wallahi Hajiya a take na ji na tsane shi, duk wani so danake mai na neme shi na rasa. Me ake da makaryacin mutum don Allah?"

"A ganina aure ba abin wasa ba ne, da za a gina shi a kan karya, matsayinsa ya wuce nan kimar shi da"

"darajar shi sun fi karifn haka, tunda ba abu ne da ake tunanin yi na kayadaddan lokaci ba, abu ne wanda ake sa ran idan an yi shi ya yi karko har abada."

"Abin haushin ma ga da namiji magidanci kamar Aliyu, kafin ya ankara na tari mashin na haye na"

ce ya kai ni Jeka-da-fari unguwar da Anty Asi take. Na dauki duk abin da nake bukata na (Practical) washe gari na bi motar kasuwa na koma makaranta.

Amma saboda rashin kunya irin na namiji kafin in koma gida ya je ya kalallame Daddy ya tura kayan

sanya rana da na lefe duk ba tare da ya nemi izinina ba.

"Da na dawo ne nake gayawa Mama, ita ma ranta ya baci ta ce ai har ya turo lefe da kayan sanya"

rana. Nasa mata kuka na ce ni wallahi ko na rasa mijin aure ba zan aure shi ba.

"Ta je ta samu Daddy da zancen karyar da Aliyu ya yi, ta ce da shi wannan abin dubawa ne, ba"

"kishiyar ce abin damuwa ba, duk mutum makaryaci, ba namiji ba ne da ya cancanci a ba shi aure."

Budar bakin Daddy sai cewa ya yi mu gaya masa inda Allah ya ce kada a auri mai mata?Kuma maza

masu iyali sun fi rikon aure.

Kuma wai Aliyu ya gaya masa dalilin shi na kin sanar da ni yana da mata da wuri shi ne don ya lura

"ba zan yarda in aure shi ba, idan ya gaya mini, alhalin shi kuma yana matukar sona, niyyar shi sai bayan an yi auren, sannan ya gaya mini yadda

Please Login or Register in order to submit comment