You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure, haka ba zan kai ta kotu ba saboda darajar aure."

Amma magana ta karshe ita ce babu wani cikin dangina ko na mahaifiyarka da zai kara sanya kafa

cikin gidanka.

"Duk mai son ganin ka ya je ofis ya same ka, mu kuma in ka zo gaishe mu shi kenan falillahil hamdu,"

"in ma ba ka zo ba ba damuwa ka je can ta kashe ka kai kadai, amma wallahi ba dai  yan Dambatta ko  yan Jalingo su kara shiga wannan gidan ba& . "

Daidai lokacin da wancan jar fatar baturen likitan ya shigo rike da takardun sakamakon Rukayyah a

"hannunsa. Ya ja kujera mai fuskantar Alhaji ya zauna. Ya dubi Saifuddeen a nutse ya ce,  Are you her husband. (Kai mijinta ne)? "

"Ba tare da wani jinkiri ba ya amsa da  Yes. Alhaji ya galla masa harara cikin harshen Hausa ya ce,"

" Allah ya tsari Rukayyah mijin Salima dai, ba Rukayyah ba. Mijin gwal, mijin lu ulu u ai ya fi karfin"

Rukayyah.

"Dariya sosai Alhaji ya ba shi, duk da tension din da yake ciki. Likita ya nuna Alhaji ya ce,  And you&  "

 Her father. Alhaji ya amsa.

"Ya dube su duka cikin tausayawa ya girgiza kai ya ce,  Am sorry. "

"To kuma dukkaninsu sai jikinsu ya yi sanyi, ba ma ya Saifuddeen, wanda zuciyarsa ta soma harbawa"

da sauri da sauri saboda fargabar abin da zai fito daga bakin likitan.

Daga shi har Alhajin sun dauki dukkan hakalinsu sun mikawa likitan. Wanda ya maida hankalinsa ga

warware takardun result din Rukayyah. Ya dora ta a kan tebur ya ce su duka su matso su gani.

"A hanzarce Alhaji da Saifuddeen suka matso, har suna gwara kafada jikinsu na bari. Taswira ce mai"

dauke da zanen kwakwalwar Rukayyah gaba daya da gaba dayan jijiyoyin jikinta masu kai sako cikin

"kwakwalwa (neuron) sako-sako, lungu-lungu, kusufa-kusufa ga su nan (nerves)da biron hannunsa ya sa"

yana yi musu bayani dallah-dallah.

"Cewa sakamakon mugun buguwa na bazata da kan Rukayyah ya yi da karfe, Rukayyah ta gamu da"

"lalurar nan ta (Post traumatic-amnesia), wato (Shafewar tunani) na bazata. (Which occur through organic causes)."

"Mafi munin abun kuma shi ne nata lalurar cause complete damage to her brain, sakamakon wani"

"jini cikin kokon kanta da ya sauko ya toshe sashe mai tunawa dan adam abubuwa daban-daban da suka gabata, ya sani, kuma yake yi."

Maganar da yake yi yanzu shi ne Rukayyah ba za ta sake tuna kowa da komai da ya gabata a

rayuwarta ba!

"Alhaji jikinsa ya yi lakwas, ya mace murus. Ko danyatsansa ya kasa motsawa, balle ya janye jiki daga"

sunkuyon da ya yi. Shi kuwa Saifuddeen tafukansa biyu yasa ya rufe kyakkyawar fuskarsa da karfi. Babu

"shakka hawaye yake yi, masu zafi, masu radadi irin wadanda bai taba fitarwa ba. Yana mai tuna tambayar da ya ji tana yi wa kata da safe, bayan da suka gama gulmar sa ita da Nafisah."

" & . Wane ALHERI ne, Alhaji ke son kullawa a tsakaninmu? Wane ALHERI ne, ke tattare da"

tarayyarmu& . ?

"A fili ya ce,"

" Babu ALHERI Rukayyah, sai sharri ga rayuwarki, ina mai baki hakuri Rukayyah& Rukayyah Allah ya"

huci zuciyarki& ..

ALHERI 2 na daukeda karashen labarin.

"Taku,"

Takori

"December, 2015"







"[12/17/2019, 19:15] Takori: ALHERI 2"

S

ambatun shi ya ishi Alhaji da ke ci gaba da sauraron bayanin likita. Ya cira idanun shi da suka kada suka yi

"jajir ya ce,"

 Kai fita ba ni wuri tun ban yi zuciyar maka tsinanniyar matar ka a kotu ba. Yaran zamani da shegen

"kwashe-kwashe, ka je ka kwaso min abin da ya fi karfina."

Idan kun so abu kamar da ya so fitowa cikin mahaifiyarshi. Ba ruwan ku da neman zabin Allah balle

"albarkar iyaye ciki, a a ku dai kun gani kuna so, kuma dole a yi muku in ana son kwanciyar hankalinku."

"In ban da haka ni ban ga abin so a wannan zankaleliyar matar ba, kamar matan Samudawa, da ganinta"

babu birbishin imani balle fa zuciyar tsoron Allah& .

"Ya mike a sukwane ya fice don ganin yadda ran Gadangan ya gama baci. Amma bai tafi ba, bakin kofar"

ofishin ya koma ya labe ya kasa kunne abin tausayi. Ba zai iya tafiyar bai jiyewa kunnuwansa makomar rayuwar Rukayyah ba.

"Alhaji ya ce,  To yanzu me za ku iya yi mana a kai? Ku taimaki rayuwar Rukayyah, ko auren fari ba ta yi ba,"

yarinyar kirki ce mai kyakkyawan buri a zuciyarta& . Ya soma hawayen tausayin Rukayyah shi ma ba tare da ya shirya ba.

"Dr. Abayomi ya ce,  Irin wannan matsala ta shafewar tunani, ba a kanta aka fara ba. Karamin tsautsayi"

sai ya kawo shi.

"Kuma babu wani likita a duniya da zai ce ga abin da zai iya yi maka a kai. Sai dai ya ba ka shawarwari, na"

hanyoyin da za a bi a samu tunanin ya dawo da kansa.

"Rukayyah za ta iya dawowa cikin tunaninta a kowanne lokaci, be it today, tomorrow or even forever !"

"(Yau ne, gobe ne ko kuma har abada). A yanzu zata yi amfani da duk abin da aka koya mata, domin jin ta da ganinta garau suke."

Haka kwakwalwarta za ta dauki abubuwa through imitation wato (Ta hanyar kwaikwayon mai yi). Amma

"na baya has been completely eradicated from her memory (Gaba daya ya shafe daga cikin kanta), just the present!. "

"Alhaji yasa tafuka ya share hawayen da ke zarya a kumatunsa, ya ce cikin sarkewar murya,  Likita kana"

nufin& kana nufin ba za ta gane kowa nata ba?

"Likitocin duka biyu suka gyada masa kai,  Amma idan aka yi kokarin fahimtar da ita a hankali za ta gane"

"kowa, da sabon matsayin da kwakwalwarta ta ba shi. "

"Ya ce,  Likita, har yaushe Rukayyah za ta kai a cikin wannan halin? "

"Dr. Abayomi ya ce,  Na ce maka babu kayyadadden lokaci. "

"Dr. Kenny ya yi dan gajeren tunani ya ce,  Da zarar an samu jinin da ya sauko ya toshe bangaren tunanin"

nata na baya ya sauka.

"Hakan kuma zai faru ne a hankali there is no specific time. Sai dai ana bukatar ta samu kwanciyar hankali,"

"a kuma dinga nuna mata her past incidents (Abubuwan da take yawan yi a da) da wadanda za su yi jimirin koyar da ita abubuwa daban-daban na rayuwa. Kamar shi mijin ta da ya fi kowa kusanci da ita.  Alhaji ya katse shi a fusace,"

 Na ce maka ko auren fari ba ta yi ba. Karya yake yi shi ba mijin ta ba ne& .

"Kenny ya ce, ""Cool down Alhaji. Alhaji ya yi kwafa, cikin matsanancin takaicin Salima da Saifuddeen din"

da bai ji ba bai gani ba.

"Dr. Abayomi ya ce,  Advisably (ashawarce) Alhaji me zai hana ku aura mai ita? Na ga alama yana matukar"

sonta. Dubi halin da ya shiga saboda lalurar ta. Kuma zai iya taimakawa kwarai wurin samun kwanciyar

hankalinta da dawowar tunaninta& 

"Alhaji ya mike don haushi kamar ya dallawa Dr. Abayomi mari, ya soma fada kamar ya ari baki yana cewa."

 Amma ku likitoci in ce ko wani lokacin ba kwa ji sosai ne? Waye zai dauki  yar shi mai lafiya ma bare

mara lafiya ya hada ta da wannan azzalumar mahaukaciyar matar tasa ?

"Ita ce fa ta janyo mata, ta tankado ta daga bene. Da bakinsa ka ji yana fade ba matse mai baki na yi ba."

"Ba don Allah ya takaita da nisan kwana a gaba ba, da waya san iyakacin abin da zai faru? Amma za ka ce wai a aura masa."

"A hakan ma ba a aura masa ba tana neman ranta, ina ga an ce ga ta su zauna tare matsayin kishiyar ta?"

Ba wuka za ta dauko ta luma mata ba? Gidan Saifudden. Umh!! Ba  yan Dambatta ba& ba  yan Jalingo

ba&  Ya maimaita ya kara maimaitawa.

Ya doshi kofar fita kamar kububuwa yana cewa.

" Ka hada min takardunta yanzu Ingila zan kai t a a duba ta. Ban yarda wai Rukayyah ba za ta gane mu ba,"

"balle Hajiyarta& wannan tatsuniya ce, irin ta finafinan ku na karya. Ban yarda akwai cutar da bata da magani ba& .. "

"Abin da ya ce ya yi wa Kenny ciwo kwarai, ya yi murmushi ya ce, ""I m Irish. Wato shi (Ba ireshe ne)."

Amma (Harvard) na tsallaka na je na dauko kwalin likitancin kwakwalwa. Sanin makamar aiki sai dai in koyawa likitan Biritish.

Abin nan da na gaya maka shi duk wani likitan kwakwalwar duniya zai fada maka. So ina jiran ku in kun

dawo don in ga ci gaban da aka samu. Ga takardun nan zo tattara ka tafi da su.

Alhaji ya wawuro takardun ya dukunkune ya fito da su. Bayan ya rubuta masu cheque na billdin da suka

tura masa.

Nan ya yi karo da Saifuddeen a make jikin kofa ya juya baya ya make yana zukar magana. Ya kuwa

"daddage ya zuba masa duka a bayan nasa, ba shiri ya yi gefe yana sosa wurin."

Alhaji ya ci gaba da sauke kwandon bacin ransa a kansa da ruwan bala I iri-iri. Ya kara da cewa.

" Je ka kamo hannun ta mu tafi. In ba za ta iya tafiya ba ka dauko ta a bayan ka, ai ku ku ka jawo mata. "

Shi dai ya yi dakin da aka kwantar da Rukayyah a ran shi yana gode Allah da ba a sa masa suna Aliyu ba.

Da mai yiwuwa haka zai zama masifaffe kuma jarababbe kamar Aliyu Dambatta.

Tana kwance har yanzu idanunta a lumshe Sai ka rantse ba abin da ke damunta.

"Nurse din nan ta dazu na zura mata allura cikin jijiyar hannunta, amma kamar ba jikinta ake bulawa ba."

" Allah Sarki RAK! Ya fadi a hankali, wato shi dan adam lafiyar shi da ran shi gaba daya ba a bakin komai"

suke ba a wurin Ubangiji.

"Idan ya ga dama cikin minti daya sai ya dauke abinsa. Duk wannan rawar kan, kadafiri, da iyayin na"

"Rukayyah, yanzu sai yadda aka juya ta."

"Haka tunaninta na rashin daukar raini da wargi, yanzu shi ma sai yadda aka sarrafa mata shi. Allah abin"

tsoro!

Ya karasa gabansu ya ce da nurse din ta taimaka mai ta kama Rukayyah zuwa mota. Wannan karon kam

"shiru ta yi ba ta kwaikwayi abin da ya ce ba, watakila zafin allurar da aka yi mata ne ya shige ta."

Ta kama Rukayyah ta mike ta rungmo kugunta suka fito shi kuma yana biye da su. Ya bude motar ta

kwantar da ita a bayan motar ya rufe.

"Ya zaga ya shiga mazauninsa ya tada motar. Sai da Alhaji ya ga ya yi ribas ya juya ya yi gate din asibitin,"

sannan ya yi umarni ga direbansa ya bi bayansu.

Suna shiga harabar gidan direban da ya dauko Hajiya daga airport ita da Asi da Maman Rukayyah shi ma

ya sawo kan motar cikin gidan.

Allah Sarki Hajiya tana daddaburawa da kyar da kyar ta nufi motar Saifuddeen inda ta hango Rukayyah

shi kuma yana kokarin fito da ita.

"Asi ta zo ta taimaka masa suka fito da ita, amma Amina ba ta tsaya a harabar gidan ba ciki ta shige"

(Fullancin ya motsa).

"Asi ta shigar da Rukayyah har dakin Hajiya tana kokarin kwantar da ita a gado ta ce,  Sannu Rukayyah, oh!"

Mu muna can muna shirin auren ki ke kuma ashe ga kaddarar da ta afku.

Nan Rukayyah ta hau aikin nata na maimaici amma da yake Asi doguwar magana ta yi sai ta manta

ragowar ta tsaya a.

 Muna can muna shirin auren ki.

"Asi ta rankwashe ta a ka ta ce,  Au! Shakiyanci za ki yi min?"""

"Rukayyah ta ce,  Au! Shakiyanci za ki yi min? "

"Asi ta ce,  Shakiyiyar duniya au muryar tawa ki ka koma kwaikwayo?"""

Nan ma Rukayyah ta maimaita sak yadda Asi ta fada. Tsoro fa ya kama Asi da gudu ta yi falo tana kiran

sunan Hajiya da Mama Aminah.

"Nan ta tadda su sun yi jugum-jugum, Alhaji na mayar masu da bayani. Ita ma ta zauna tana sauraro nan"

take ta gano matsalar Rukayyah.

Haba! Biri ya yi kama da mutum. Rukayya ce za ta ga Asi duk irin ciwon da take ba ta tambaye ta  yar ta

Yasmin da ta ke matukar so ba?

Asi tasa kuka a hankali tana  Wayyo Rukayyah Allah Sarki! Yanzu a haka za a daura miki aure goben?

"Ba su ankara ba sai ganin Hajiya Umaimah sukai har ta kai bakin kofa, tana tafe tana dafa bango, da kyar"

"take iya daga kafafunta, tana yi tana share hawayen da ke shatata kumatunta."

"Alhaji ya sha gabanta a hanzarce, ya hana mata hanyar wucewa ya ce,  Umaimah ina za ki?"""

"Ta ce,  Ba ni hanya Alhaji, don Allah ka kauce in wuce. "

"Ya ce,  Sai kin gaya min inda za ki tukunnah. Ni da kaina zan tuka ki in kai ki. "

"Wasu hawayen suka zubo. Tasa gefen mayafinta ta share cikin muryar kuka ta ce,  Kotu za ni in shigar da"

"karar matar Babangida."""

"Ya ce,  To saurare ni minti biyu in sake kaya sai mu je. Ya kamo hannunta ya dawo da ita kujerar da ta"

tashi.

"Shi ma ya samu wuri ya zauna dab da ita. Cikin lallashi ya ce,  Yanzu Umaimah da girmanki ki shiga"

sha anin yara ai ba mutuncinki bane.

"Ta ce,  Mutum mai mutunci shi ake yi wa kawaici. Amma a inda babu mutunci, kawaicin ba shi da"

amfani.

"Ya ce,  Haka zuwa kotun ma ba shi da amfani. Da yana da shi da tun kan ki dawo na je miki. Yadda ki ka"

"dauki Rukayyah diyar cikinki, haka nima nake jin ta."

To amma ba girmanmu ba ne a ji sunan mu a kotu. Kuma babban abin kunyar da surukar mu. Ina ki ka

kai wannan akidar taki ta maida dan kowa naki? Naki ba naki bane?

Rukayyah ta riga ta nakasa. Haka Allah ya rubuta mata. Tun kan mu zo duniya kaddarorin rayuwarmu a

"rubuce suke, ba wanda zai iya canza kaddarar rayuwarshi. And that s Rukayyah s destiny, wato wannan ita ce kaddarar rayuwar Rukayyah."

"Me kotun za ta yi mata ta wanke miki wannan bakin cikin? Babu. Iyakaci a ce za a daure ta, ga jikan ki a"

"jikinta, ai hakan bai dace ba."

"Ko kuwa a ce za a bamu Diyyah, mu yi wa Rukayyah magani. Nawa za a baki wanda Allah bai baki ba?"

"Don haka ni Alhaji Uban Salimah, Saifuddeen da Rukayyah. Na dauki nauyin neman lafiyar Rukayyah a"

ko ina cikin duniya in har da gaske ne babu cutar da Allah ya saukar a doron kasa ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba.

"Za a nemawa Rukayyah magani, da yardar Allah Rukayyah za ta dawo cikin tunaninta a lokacin da"

dukkaninmu ba mu zata ba.

"Ta ci gaba da rayuwarta mai ban sha awa, kamar da, ta ci gaba da cika miki tumbi da daddadan girkinta,"

"ta ci gaba da shafa miki maganin ciwon kafa da ciwon baya, ta ci gaba da killace miki daki da tsaftace"

"bandakinki, ta cika miki gidan nan da jikoki maza da mata& .. "

"Sai ta yi murmushi, sannan aka koma kulla mai yiwuwa."

"Ta ce,  Yanzu a haka gobe zan kwashe ta mu koma Jalingo da sassafe, har tikitin na saya mana. "

"Alhaji ya ce,  Ke kuwa me ya yi zafi? "

"Ta yi kwafa ta ce,  Wannan kafaffen uban nata mana. Yanzu haka zancen nan da nake maka ya gama"

raba goro ya sanar a talabijin da rediyo gobe zai daura mata aure.

"Kai ma ga naka goron can buhu guda ya ba Asi ta kawo maka. Don ni na ce ba zan dauko ba."""

"Alhaji ya yi salati ya ce,  Usman! Usman, wai shi wane irin bahagon mutum ne? "

"Hajiya ta ce,  Bar shi dai, shi da abun sa? Nuna min zai yi ba ni na haifi  yar ba shi ya haifi abun shi."

Ni kuma na kyale shi ya yi mata auren dolen duk abin da ya biyo baya babu ruwana. Allah na tuba a

wannan zamanin auren soyayya ma yaushe ya tsira balle auren dole?

"Alhaji ya ce, ""A wannan halin kam bai dace a daurawa Rukayyah aure gobe ba. Ni nan niyyata da goben"

"zan tafi Abuja nema mata (Medical Visa) zuwa U.K, a duba ta sosai. "

"Ta ce, ""A a, gara dai in dauke ta a hakan in kai ta ya ga halin da ta ke ciki da idanunsa ko ya fasa daura"

mata auren. Don yanzu in aka aika masa cewa ba ta da lafiya ga abin da ya same ta cewa zai yi wata kutunguilar ce muka hada baki da ita muka shirya ni da Aminah har yau ba ka gama sanin Usman ba.

Ni na rasa dalilin shi na likewa auren yaron nan sai ka ce daga kan shi cewa aka yi da shi Rukayyah ba za

ta samu mijin aure ba.

"Asi ta ce, Haka zai bar shi ? Surkullen su na  yan Dukku zai yi masa, don in kin ga yadda yake tada"

hakarkari da jijiyar wuya a kan auren nan sai kin yi mamaki.

Ai ke Hajiya mai sauki ce ya yi miki saboda yana ganin girmanki da ya ce zai yafe miki Rukayyah.

"Tunda Rukayyah tasa kafa ta baro gidan nan Yaya Amina ba ta kurbi ruwa ya tsirga mata ba, kullum sai"

ya ce da ita macewar Rukayyah ce a ranar daurin auren kawai za ta hana shi daukanta zuwa gidan Aliyu.

Shi ma din sai an biya da gawarta gidan tukunna an zaunar ta a bakin gado in ya so a fito da ita kafin a

wuce da ita makabarta.

"Alhaji ya kai hannu ya toshe baki cikin kaduwa ya ce,  To Allah ya sauwake, kada Allah yasa hakan. Me ya"

yi zafi? Nima tafiyar ta kama ni kenan. Don ba zan so a ce ban halarci daurin auren  yata Rukayyah ba.

"Ya kuma yi dan tunani, can ya girgiza kai cikin jimami ya ce,  To amma, dai& . Oh& . A wannan halin za a yi"

wa Rukayyah aure?

Rukayyah fa a halin yanzu daidai take da jaririn da aka haifa yau din nan!

"Kowa ya yi jugum-jugum na lokaci mai tsawo. Ba ma ya mahaifiyar Rukayyah, wadda Allah kadai ya san"

halin da zuciyarta ke ciki.

"Alhaji ya daure ya ce,  To amma san da za mu isa ba za mu taras an daura auren ba? "

"Asi ta ce,  A a, don sai bayan saukowa masallaci. "

"Ya ce,  To Allah ya kai mu. "

"A sannan ne ya juya ga Saifuddeen, wanda tunda suka shigo kansa yake sunkuye a gefe daya, duk"

"maganganun nan da suke bai tofa masu ba. In ban da zufa ba abin da yake, duk da sanyin split mai girman gaske da ke bada raba a falon."

"Tausayin shi ya kama Alhaji, yana da tabbacin tun safe bai ci komai ba har zuwa yanzu karfe goma sha"

"biyun dare. Yini daya rak duk ya zabge, bai taba ganin shi ya yi wujiga-wujiga irin yau ba. Ga wata zufa da yake ta yankawa babu gaira babu dalili. Shi kadai ya san abin da ke damun zuciyarsa."

"Ya san inda abun da Saifuddeen ya tsana a duniya to bai wuce fadansa ba, ya fi so ko fadan ne a yi masa"

"cikin dadin rai da kwanciyar hankali, amma yau wane ta aziri ne bai masa ba a kan laifin da ba nashi ba?"

"Ya juya ga Asi ya ce,  Nemo Hajiya Rabi ta hado mana abinci. "

"Asi ta mike ta yi ciki. Alhaji ya ce da shi,  Dauko madara cikin firji ka kai wa Rukayyah ko za ta sha. "

Saifuddeen bai ji ba sai da Alhaji ya kara maimaitawa.

Ya yi firgigit ya mike ya nufi dakin Hajiya inda dan karamin firjinta na bakin gado yake kuma inda

Rukayyah ke kwance.

"A lokacin Hajiya da Amina suka mike suka shiga dakin da ke daura da na Hajiya, ita Aminar za ta yi alwala"

"ne ta yi sallah, kafin Rabi ta kammala hada abinci ko dakin da Rukayyah take ba ta kalla ba, ba yadda Hajiya ba ta yi da ita ba kan ta shiga dakin ta ganta, amma ta ce sai da safe."

"Don haka Hajiya ta fito ta kyale ta. Lokaci daya suka shiga dakin itada Saifuddeen, ya bude firjin ya dauko"

"madarar, sai suka ga har Rukayyah ta yi barci."

"Hajiya ta ajiye jakar hannunta shi da ita suka tsaya a kanta cirko-cirko, ta ce  tashinta zan yi, bai kamata a"

bar ta ta kwana da yunwa ba.

"Tasa hannu tana tashinta,  Rukayyah, Rukayyah. Ta bude blue idanunta cikin nauyin barci tana kallon"

Hajiya.

Saifuddeen ya karaso ya zauna a bakin gadon ya bincine hancin kwalin madarar shanu ta kwali

"(Oldenburger) ya tsiyaya a kofi duk Rukayyah na kallonsa, ya mika mata, amma ba ta karba ba, shi din dai take kallo. Ya yi murmushi ita ma sai ta yi irin murmushin da ya yi. Ya ce,  Karbi mana Rak! "

"Ita ma ta ce,  Karbi mana Rak! Hajiya ta juya fuska baya tana yarfe hawaye. Wai Rukayyan ta ce yau"

Allah ya maida haka?

"Ya kamo hannun Rukayyah yasa mata kofin a ciki ta karba ta rike, amma ba ta kai bakin ta ba, saboda"

"haka ya karba ya kai nasa bakin yana sha, sai da ya shanye tas duk tana kallonsa da murmushin da har zuwa lokacin bai har kyakkyawar fuskarta ba."

"Ya sake cika kofin ya mika mata, wannan karon ba musu ta karba ta kai bakinta ta soma sha, nan da nan"

ta shanye. Ya sake tsiyaya mata ta shanye jikinta har rawa yake.

"Rabi ta shigo da filet da cokali shake da abincin da Rukayyah ta fi so a rayuwarta, wato faten doya."

Ba ta san me ya samu Rukayyah ba. Asi dai ta ce da ita Rukayyah ba lafiya. Ta shigo da hanzarinta tana

fadin.

" Sannu Rukayyah, ciwo haka rana daya? Ni fa dazu Nafisa take bugo (land-line) wai in fadawa Hajiya ta"

kasa samun Rukayyah a waya. Na ce da ita Hajiya ta je Jalingo Rukayyah kuma tana can gidan Babangida.

Ta ce ta sani don da safen nan ma sun dade suna magana yanzun ne dai tana ta bugawa tana ringing fiye

da sau dari amma ba a dauka ba.

"Jikin ta ya ba ta ba lafiya ba, don shi ma Babangidan ta kasa samun shi. Na ce da ita watakila ta je"

"unguwa ne ta bar ta a gidan, ashe kuna asibiti. Me ya same ki ne? "

"Ga mamakin Rabi, Rukayyah ko gizau, kamar ba da ita take magana ba. Don ma dai yunwa ta haukatata"

ne tana ta shan madara da tuni ta fara yi mata maimaicin nata.

"Rukayyah ko kallon ta ba ta yi ba, ga ta a zaune daram da duwawunta da lafiyarta sumul-kalau. Ko daga"

ido ba ta yi ta kalle ta ba. Ba ta daddara ba dai ta sake cewa.

" A can gidan ki ka baro wayar kenan?"""

"Nan ma shiru. Ta sauke kofin daga bakinta, Saifuddeen ya karba. Ya cire tissue yana goge mata baki,"

"Hajiya ta mika mata hannu ta ce,  Ba ni abincin nan ki gani Rabi. "

A sanyaye Rabi ta mikawa Hajiya plate din hanunta da cokali mai yatsu. Hajiya tasa cokalin cikin doyar

"tana ci tana kallon Rukayyah, sannan ta mika mata."

"Rukayyah ta maida hannuwanta baya ta noke wato ba za ta karba ba. Saifuddeen ya ce,  Kawo Hajiya in"

gani ni ko za ta karba. Ba musu ta mika masa.

Ya tashi daga inda yake zaune ya matsa sosai kusa da ita ya soma dibar abincin da cokali ya kai bakinta.

"Kallon shi take amma ba ta bude bakin ba, sai ya bude nasa sannan ta kwaikwaye shi ta bude yasa mata."

"Nan da nan ta shiga ci, amma fa idanunta a kansa tana kallon yadda yake taunarsa a nutse, ita ma tana kwaikwaya."

"Ta kai loma ta biyar kenan ta kware, ji kake, mukut, ragowar da ba ta kai ga hadiyewa ba ya dawo jikinsa"

ya batamasa kaya.

"Rabi ta yi hanzarin zaro tishu ta mika masa ya soma gogewa ya ce,  Maza kawo ruwa. "

"Ta karasa ga firjin Hajiya, zuwa lokacin hawaye sun wanke mata fuska. Tana tambayar kanta to hauka ne"

wannan ya samu Rukayyah a dare daya ko ko kurumta ce?

"Ga mamakin Hajiya da Saifuddeen, Rukayyah sai ta kama hannun Saifuddeen mai rike da tishu yana goge"

"jikinsa da ta bata, ta kwakwale tishu daga hannunsa ta ci gaba da goge masa yadda ta ga yana yi."

"Fuskarta ta nuna ba ta ji dadin abin da ta yi ba. Ya yi mata murmushi, ita ma ta yi tana mai sunkuyar da"

kai kasa.

"Hajiya Umaimah sai ta samu kanta cikin wani tunani, wato Saifuddeen zai iya

Please Login or Register in order to submit comment