You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gayawa

kowa abinda ke damunta akan hakan ba.

"Ta danne dariyarta, ta ce ""In kwankwasa masu kofa Hajiya, ince me?"" To a nan itama Hajiyar sai"

"ta yi shiru, don bata san abin cewa ba."

"Amma ta kudire a ranta Saifuddeen da ita ya ke zancen, bazai kuma shiga dakin Rukayyah ba"

daga yau.

Suka ci gaba da hirarsu sama-sama amma ba kamar da ba. Don hankalin Hajiya kwata-kwata ba

ya jikinta. Allah ne ya kawo Alhaji tun kamin ya zauna ta ce

"""Maza Asi kirawo Saifuddeen ki ce ya zo inji Alhaji""."

Asi ta mike wannan karon ba ta yi musu ba. Ta hau steps uku da zasu sadaka da dakunan barcin

"daga falo, zuwa dakin su Rukayyah, tasa hannu ta kwankwasa ba a amsa mata ba, ta yi sallama ba a amsa ba."

"Sai ba ta shiga ba, ta kafar dan mukulli ta sanya bakinta, ta ce ""Saifuddeen Alhaji na kira"". Ya ce"

ta ce da Hajiya yana zuwa.

"Alhaji ya ce ""Yaya aka yi Saifuddeen ya dawo yau? Na ga motarshi a waje""."

"Hajiya ta ce ""Shiriritarshi mana"". Asi ta gyara mata da cewa"

"""A'ah Hajiya, matarshi ce ta dawo da shi. Idan gaskiya kike so ki baiwa Saifuddeen matarshi da"

"zarar mun dawo, ta warke ko bata warke ba, amma duk inda ya ke hankalinshi bazai kwanta ba, bai san halin da take ciki ba""."

Hajiya ta ce

"""Kada ya kwanta din, ita kadai ce matarshi? Ke ce bakisan sanabe irin na Babangida ba& ""."

"Alhaji ya katsesu da cewa ""Ince ko kin gaya mishi karfe goman dare zamu tashi?"" Don baya son"

zancen da Hajiyar ke yi. Ta ce

"""Aa'ah ban fada ba, kai nake jira ka zo ka fada mishi da bakinka""."

"Suna haka Saifuddeen da Rukayyah suka fito, sunyi fes sai shekin amarci suke, shi da ya shigo a jigace."

"Hajiya ta kama baki tana mamakin rashin kunya irin ta Saifuddeen, sai dai ba ta ce komi ba, don ta lura"

"ba abin da ya samu Rukayyar. Shi ma da ganinshi ka ga maras gaskiya, sai sunkuye-sunkuyen kai ya ke. Tuni Asi ta dagosu."

"Rukayyah kuwa, ko a jikinta, sai kara shige ma angonta ta ke, shi kuma duk kunya ta isheshi, sai"

"angijeta ya ke kadan-kadan a haka suka zauna, ta ce"

"""Alhaji ina kwana?"" Ya ce,"

"""Ina wuni dai Rukayyah, ince ko kin gama shiri?"""

Cikin rashin fahimta Saifuddeen ya dago ya dubi Alhaji. Amma bai ce komi ba. Alhajin ya ce

"""Yanzu nake tambayar Umaima, ko ta gaya maka yau zamu tafi kai Rukayyah asibiti, ta ce ba ta"

"fada maka ba""."

"Gumi ya yanko mishi tun daga tsakar kanshi, har yatsar kafarshi. Daga can kasan makoshinsa da"

"kyar ya ce ""Wane asibiti ne? Kuma a ina ne?"" Ya ce"

"""Wani private hospital ne a Delhi"". Kamar zai yi kuka ya ce ""Amma Alhaji da ni za a yi tafiyar ko?"""

"Alhaji ya yi murmushi ya ce ""Na so hakan. To amma akwai kayayyakin jama'a da yawa da zaku"

dauko daga Spain cikin wannan satin.

"Zuwa next week in komi ya daidaita duk kayan ka badasu ga masu su, sai ka bi mu. Ni kuma sai"

"in dawo"". Ya ji dan sanyi, ya ce ""To Allah ya sa a dace"". Su duka suka ce ""Amin""."

"Har karfe goma na dare yana cikin gidan, tare suka ci abinci da Alhaji. Salima tana ta kiranshi a waya ya ki"

"dagawa, sai da Hajiya ta gaji da karar wayar ta ce da shi"

"""Ba ka ji ne, ana ta kiranka?"" Yayi tsaki ya amsa."

"Daga Alhaji har Hajiya sauraronshi suke, amma basu nuna hakan ba. Me suka ce, me suka ce?"

Oho! Ya sake jan tsaki ya ce

"""To Allah ya baki lafiya"". Daga haka ya kashe wayar ya tura aljihu."

"Hajiya ta kudire a ranta a yau kam bayan su Rukayyah sun tafi, zata yi mishi fada akan irin"

cuzgunawar da yake yiwa matarshi.

"Har da shi aka rakasu Rukayyah da ba tasan wainar da ake toyawa ba, filin jirgi. To anan fa ake"

"yinta, lokacin da Rukayyah ta fuskanci bada Saifuddeen za a tafi ba."

"Har ta soma hawa matattakalar jirgi, da ta juyo ta ga Saifuddeen bai taho ba ai saita dawo da"

"gudu ta kankameshi, tana kuka yana lallashinta da tattausar murya. A haka Asi ta jata suka shiga jirgin ya daga."

"Shi da Hajiya suka nufo gida, duk abin duniya ya dameshi, ya rasa inda zai sa kansa. Idanunshi"

sun kada sun yi jawur.

"Ganin halin da yake ciki ne yana tuki, amma tana ta magana ba ya jinta, kin san UWA. Nan da"

nan ta ji tausayinsa ya kamata. Ta kai hannu ta aza bisa kafadunsa.

"Ya yi ajiyar zuciya ya dan juyo ya dubeta, kana ya maida hankalinshi a tukin da yake yi. Ranta ya"

"sosu, ta ce cikin muryar lallashi"

"""Ni ko da zan baka shawara ka dauka, da ma shawarceka da ka daure zuciyarka da bacin ranka"

ka yi afuwa ga matarka. Ka yi sulhu da ita.

"Idan horaswa ce kake yi mata, idan ita din wata mai hankali ce, zuwa yanzu kam ta gane"

"kuskurenta. Ban san yaushe ka koyi riko ba. Abin zai zamo da daukar hakki""."

Ya sake kawo ajiyar zuciya mai nauyi ya ce

"""Shi kenan Hajiya""."

"Ta ji dadi, ta yi murmushi. Saukin kansa na daga abubuwan da ke kara mata kaunarsa."

Sai ta koma ga zancen da yake so. Ta ce

"""Sati mai zuwan in zaka bisu, ko tare zamu tafi ne?"""

"Ya saki fuska nan da nan ya ce ""Haba, ke ma da kike fama da kanki Hajiya? Ki dai ci gaba da"

"sanyamu cikin addu'arki, ko baki bimu ba zata bimu."

A gaskiya matsalar Rukayyah ta dameni. Wallahi-wallahi Hajiya al'amarina da Rukayyah wani

hukunci ne na Ubangiji.

"Ban taba tsammanin dai-dai da rana daya zan tsinci kaina da so da kaunar Rukayyah ba, tunda"

aka haifeta. Sai sanda Ubangiji ya hadata da lalura ba cikin tunaninta ba.

To idan kin duba wannan zaki san akwai abin da Allah (Subhana) ke nufi da wannan. Son da nike

wa Rukayyah ya fi gaban duk wani kokarin da zanyi in kwatantashi.

Kuma so ne tsan-tsa mara algus na fisabilillahi. To amma Hajiya ban san me yasa kika yi min

"wata mummunar fassara ba, tun ranar da aka daura aurenmu da Rukayyah."

"Na dade ina neman irin wannan damar, wato sanda kike cikin sanyin zuciya, inyi miki bayanin"

"kaina na rasa, sai yau."

"Ban san laifin da na yi miki akan Rukayyah ba, kiri-kiri da bakinki kika nuna min baki so na aureta"

ba.

"A kullum na yi wannan tunanin hankalina kan tashi, jikina ya yi sanyi. Tunanina na gaya min duk"

"ranar da Rukayyah ta dawo cikin hayyacinta da tunaninta, idan ta ce ba ta so na, za ki mara mata baya. !"""

"Sai ga hawaye sharrr-sharrrr, wasu na korar wasu."

"Maganar ta dunkule a makoshinsa ya hadiyeta gaba daya, mukut! Sitiyarin ya kufce, motar ta"

"kwace ta gicciye. Ya yi hamzarin kamo sitiyarin ya saisaita ta akan titi. Hajiya ta kidime ta yi kira da karfi,"

"""Saifuddeen! Sauka gefen titi& .""."

"Bai yi musu ba, ya bi umarninta. Ya sunkuyar da kai bai dago ba. Idanuwanshi sun kada sunyi jazur,"

"hawayen sun ki daina zuba. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, cikin kankanuwar murya,"

"""Saifuddeen, dube ni""."

"Ya dago sannu a hankali ya dubeta. Ta kai hannunta na dama bisa kirjinta, ta ce ""Ni wace ce a gareka?"""

"Ya ce ""Uwa, mahaifiya"". Ta ce"

"""Ka tabbatar da hakan, amma kake haufi?"

Ka ke haufi a bisa kaunar Uwa ga danta? Duk son da zanyi wa Rukayyah zai kai rabin-rabin

"wanda nake maka ne? Sai dai ni din Allah ya yi ni wata irin mutum ce. Mai maida nata ba nata ba ne, kuma mai matukar kaunar dan uwanta."

Ba ni da kowa a duniya sai Usman (Uban Rukayyah). Tun muna kankana iyayenmu suka mutu

"suka barmu. Tare muka yi fafutukar rayuwa har Allah ya rayamu. Don haka Usman da 'ya'yanshi su kadai nake da su a duniya, su ma ni kadai garesu."

"Don haka bazan taba yarda da duk abin da zai wulakantasu ba, don basu da shi."

"Na dade da burin inga cewa ka so Rukayyah, ka aureta da farko, ka maida ita uwar 'ya'yanka."

"Ka ga na hada jinina wuri guda, na dunkule ko mutuwa na yi bani da fargaba. Nasan ko ba don ni"

"ba zaka ci gaba da kula min da dan uwana da iyalinshi, domin matarka."

"Sannan Rukayyah ba zata tagayyara ba a gidan aure, in dai tana surukar Alhaji."

"To amma a tasowarka, sai na ga sabani ga tunanina, ka nuna min mafarkina bazai taba zama"

"gaskiya ba. Karewa ma, baka da wanda ka tsana a duniya, sai Rukayyah."

Ban sani ba ko hakan na da nasaba da ajin rayuwarku da kake ganin ba daya ba ne?

"Ni dai nasan kai mutum ne mai ALHERI ga kowaa, bansan dalilin ka na zama mara ALHERI ga"

talon  yar uwar ka ba!!!

"Tun daga wannan lokacin na ja wancan mafarkin nawa gefe, na shiga yiwa Rukayyah addu'ar"

"Allah ya kawo mata miji dai-dai ita, talaka dan uwanta, wanda zai kaunaceta fisabilillahi, ya darajjata, ya martabata don bazan taba bari ta je inda zata wulakanta ba."

"To kuma kwatsam, ina zaune, sai na ji cikin lasifika wai ka amince ka auri Rukayyah, a lokacin da"

ta ke cikin wani hali na rashin sanin inda kanta ya ke.

"Abin da ban gane ba shi ne, Alhaji ne ya rokeka ka yiwa 'yar uwarka (auren-huce-haushi), ko ko"

"wata manufa ce daban kake da ita na yin hakan? Yarinyar da ko kwakkwarar gaisuwa baka yi da ita, mene ne dalilinka na aurenta a sanda ta ke cikin shafewar tunaninta? Bata san kai ko wane ne a gareta ba? Anya kana nufin ALHERI, cikin al'amarin nan?"""

"Ya bude baki zai yi magana, ya ma rasa abin da zai ce, sai ya mayar ya rufe. Hajiya wace irin"

philosopher ce? (Mai bin usilin ilmin abu). Bata san shi so sartse ne ba?

"A lokaci daya ya ke sarke mutum. Ba ruwanshi da yanayin LAFIYA, lokaci da dangogin su. Abu ne"

"da ke darsuwa a duk sanda ya so, ko ya ga dama. Shi kuwa me zai nufa akan Rukayyah, banda ALHERIN?"

"Da zai iya, da ya dauko gudar tsokar zuciyar kawai ya tsaga, ya nuna mata."

"Yana daga cikin irin mutanen da basa iya bayyana abin da ke zuciyarsu da fatar baki, sai dai"

action da emotion dinsu ya nuna.

"Akalla mintuna ashirin suka shude bai ce komi ba, sai sautin bugun zuciyarshi da nauyin"

"numfashinshi da ya karu, har tana iya ji cikin kunnuwanta tak! Tak!! Tak!!!"

"Ta san halin danta, ta fi kowa karantarshi, ta fi kowa sanin duk wani takun rayuwarshi, don haka"

tuni ta fahimceshi. Sai dai so ta ke ya furta. Ya furta mata da bakin shi cewa a halin yanzu yana son RUKAYYAH!

"Ta kuma tabbata bazai furta din ba, koda ace zasuyi shekara ne tsaye a wajennan kuwa. Idan yai"

"hakan, ai MAZA SUN FADI. Don haka da ta gaji, ita da kanta sai ta ce"

"""Ja mota ka kaini gidanka, in baka da abin cewa, in duba matarka, na ji tana gaya maka dazu"

bata da lafiya.

"Duk ranar da ka tanadi kwakkwarar amsa ga zargin da nake maka, ranar ne zaka gane, ina son"

"aurenka da Rukayyah ko bana so???"""

"Bai ce komi ba, ko shi yaso hukuncin da ta yanken, da watakila sai dai su kwana a wurin domin"

kuwa ba shi da amsar da zai bayar ga tambayarta.

A hankali yasa giya ya tada motar suka harba kan titi ba tare da sun kara ce da juna ko uffan ba.

"Mu karasa a littafi na uku, kuma na karshe insha-Allah, taku har abada;"

Sumayyah Abdulqadir (Takori).


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment