You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

"Abin da nake so ka yarda da shi guda daya ne shi ne Rukayyah duk dabararta, kafiyarta da makircinta, ba"

ta isa ta yi wa kanta abin da Allah bai mata ba.

"Ka saurare mu ka ga hukuncin da Allah ya yi a kan Rukayyah, cikin wuni guda kacal za ka tabbatar mu"

"muna namu ne, Allah na nasa, kuma na shin shi ne gaskiya."

Don haka ka dakatar da daurin auren nan har sai mun iso. Shi ma yaron ya zo ya ganewa idon sa halin da

Rukayyah ke ciki.

"In ya ga zai iya zama da ita a haka, Falillahil hamdu, idan ba zai iya ba ya bar mana ita mu nema mata"

"magani ta samu lafiyarta, sannan duk hukuncin da za ka yi mata sai ka yi mata. Amma Rukayyah yanzu"

abin tausayi ce& .

Ya kashe wayar ba tare da ya saurari komai daga bakinsa ba. Ya bar Alhaji Usman da sanyayyan jiki yana

jujjuya ido. To me ya samu Rukayyah haka?

"Saifuddeen ya ga ana shirin tafiya ba wanda ya yi zancen Rukayyah ta yi wanka, as a bride as she"

"is& (amarya guda)!. Ya ce  Hajiya, a shigar da Rukayyah ta yi wanka mana? Amarya guda ba kwalliya? "

"Hajiya ta ce,  Kai ma dai Babangida da wani zance ka ke. Ta yaya za a fada mata cewa ta yi wankan? »"

"Ba tare da wata damuwa ba ya juya ga Asi ya ce,  Ki kama ta ku je bandaki, ki tube a kan idonta"

"ki ajiye ruwa, soso da sabulu a gabanta, kawai ki hau wanka, in kin gama sai ki mika mata soso da sabulun ki tsaya tare da ita har sai kin ga ta yi daidai, in ba ta yi daidai ba ki dinga gyara mata."""

"Asi ta yi dariya sosai cikin jinjina hikima irin ta Saifuddeen kamar wani Psychiatrist, ko ko wanda ya yi"

"karatu (Professionally), a kan matsala irin ta Rukayyah."

"Ta kama hannun Rukayya suka tafi tana tirjewa sai da ta ga Saifuddeen ya mike ya biyo su tukunna, ya yi"

zaman dirshan a kofar bandakin yana mata alama da girarsa da kansa ta je sannan ta yarda ta shiga.

Sai da Asi ta turo kofar sannan ya tashi ya fito ya dawo falo wurin su Hajiya suna magana a junansu

kasa-kasa amma da ya nufo su sai suka yi shiru.

"Shi ma bai tambaye su me suke cewa ba, yana zama a kujera kira ya shigo a wayarsa, don haka ya mike"

ya koma barandar falon Hajiya yana magana.

Yana gamawa kafin ya maida wayar aljihunsa kiran Nafisah ya shigo tana tambayar Rukayyah.

"Ya ce,  Idan mijinki ya barki ki tafi Jalingo mu hadu a can, Rukayyah ma can za mu tafi har ita yanzu. "

Ta nemi karin bayani ya ce sauri suke lokacin tashin jirgin su ya cika in sun sauka ya kira ta. Nafisah ta

"soma kuka ta ce,"

" Ni fa ban gane ba, idan Rukayyah mutuwa ta yi ku gaya min mana? Ai ni Musulma ce. In ba haka ba ku"

hada ni da ita mu yi magana mana? Kowa na kira na tambaya Rukayyah sai ya yi ta yi min hanya-hanya.

"Ya yi murmushi ya ce,  Wallahi wallahi, Nafisah, Rukayyah ba mutuwa ta yi ba. Karewa ma aure Babanta"

zai yi mata yau din nan.

Jikin Nafisah ya yi matukar sanyi. A take ta gano matsalar da take tunanin Rukayyah na ciki wato auren

dole.

"Daga can baranda inda yake tsaye, ya hango fitowar Asi da Rukayyah daga daki."

"Asi ta tsantsara mata kwalliya da shadda Ghalila, launin wadda ke jikinsa riga da zane mai aikin surfani"

mai kayatarwa.

"Rukayyah da ba ta son daurin kai yau Asi ta tsantsara mata, da ganinta dai ka ga amarya."

Ya samu kansa da saita Rukayyah da camerar wayarsa yana daukar kyakkyawar fuskarta a hoto.

"Ta juya gaba, ta juya baya, ta juya hagu da damanta duk yana daukanta ba tare da ta sani ba da alama ita"

"akwai abin da take nema ba ta gani ba, wanda kowa ya san ko mene ne."

Tana shirin fara kuka ya shigo falon yana yi mata dariya.

"Ta taho za ta rungume shi ya yi sauri ya kauce ya rike hannunta. Alhaji ya ce,"

 Mu je.

Kowa ya mike suka yo waje inda motoci suke. Masu kula da gidan cikin fararen kaya wadanda a zahiri

(securities) ne suka soma kukkule ko ina Rabi ta koma sashenta.

"A filin jirgin ma dai Saifuddeen na rike da Rukayyah, ita kuma ba ruwanta da kowa. Inda duk ya sanya"

kafa nan take mayar da tata ba ta kalle-kalle. Sai ka rantse da Allah (PREVIOUS RUKAYYAH) ce.

Jirgi ya daga ya dire su a Yola cikin awa daya inda suka samu mota fijo (Station wagon) mai tambarin

gidan talbijin na Taraba da direba da Alhaji Usman ya turo na tsimayen su. Ta kwashe su zuwa Jalingo.

******

A JALINGO

K

"arfe daya na rana suka isa kofar gidan su Rukayyah, ga (canopies) nan an sanya an kuma shimfida"

manyan tabarmi a kofar gidan. Alhaji Usman da wasu daga cikin amininansa abokan aiki suna dakin zaure falo ne guda na saukar bakin Alhajin suna tattaunawa.

Isowar Alhaji Dambatta ke da wuya duka suka fito suna yi masa barka da zuwa ana ta musabaha.

"Wannan na daga cikin halayyar Alhaji da ke burge kowa, ba shi da girman kai ko kadan ga son hira da karrama jama a."

"Shi da su suka nufi falon Alhaji Usman yayin da Hajiya, Asi da Mama Amina suka yi cikin gida suka bar"

"Saifuddeen da Rukayyah ana daru a zaure, shi ya dage sai ta bi su Asi har bata rai ya yi amma duk a banza ta kama shi ta kadandane ya rasa yadda zai yi da ita, don shi dai ba zai iya shiga cikin gidan ba."

A lokacin Hafiz da Munaya kannen Rukayya suka shigo za su wuce cikin gidan. Hafiz rike da huhun goro

"da alewa. Munaya ta kyallo ido ta ga Rukayyah ai da gudu ta saki hannun karamin kaninsu Lukman ta rungume Rukayyah tana murna ta ce,"

" Yaya Rukayayh shi ne ki ka tafi Legas ki ka bar ni, wallahi da gobe zan biki tunda an yi hutu kewar ki ta"

"ishe ni, gidan duk babu dadi idan ba kya nan? "

"Sakatoto! Rukayya ta yi tana kallon Munaya,  yar kimanin shekaru goma sha biyu, wadda ba su da"

maraba da Rukayyah ko a farce.

"Shi Hafiz da yake mai hankali ne tsugunnawa ya yi yana gaida Saifuddeen ya ce,"

" Yauwa Hafiz, kama hannun Rukayyah don Allah ko ba ta so ka shigar da ita cikin gida. "

"Hafiz ya juya idanunsa kan Rukayyah ya ga ko kallonsa ba ta yi ba, shi da yake na hannun damarta. Babu"

da Rukayyah ke dasawa da shi a cikin kannenta irin Hafiz. Wannan ya samo asali ne da shakuwar da suka yi da juna tun suna kankana a Gombe.

"Ya ce,  Hala ba ta gani ne?"""

"Abin ya baiwa Saifuddeen dariya, ya yi murmushi ya ce,  Lafiyar idanunta kalau, ku din ne ba ta san ku ba,"

sai a hankali.

"Munaya ta kama kugu, ta ja baya ta ce da karfi,  Ba ta san mu ba?! "

"Ya ce,  Ba ta san ku ba. Amma a hankali za ta gane ku. "

Ya juya ga Hafiz da yake yafi hankali wanda ya nutsu yana kallon Rukayyah da fuskar kauna ta  yan

uwantaka.

Ya yi masa takaitaccen bayani yadda zai gane. Idanun yaron suka kada suka yi jawur amma hawaye ba su

"zubo ba. Ya kama hannun Rukayyah yana yi mata murmushi, sannan ta yarda ta bi shi, amma fa bata kallon gabanta."

"Saifuddeen take waiwaye tana kallo idanunta cike da kwallah, har suka shige cikin gidan ba ta dauke"

idanunta daga kansa ba haka shi ma.

"Ya runtse ido ya yi wa bayansa makari da bango kada ya fadi. Ya harde hannuwansa a bayansa, wasu"

zafafan hawaye suka zubo.

Ya tabbata daga yanzu ya yi sallama da Rukayyah kenan har abada! Shi kadai ya san yadda al amarin ke

tafarfasa zuciyarsa.

"Ya mance shaf da  yar Munaya, wadda ke tsaye har yanzu cikin sanyin jikin jin cewa wai Yayarta"

"Rukayyah da suke kwana su tashi tare, ta manta ta. Ta matso gabansa cikin kankanuwar murya ta ce."

 Yaya Saifuddeen.

"Da sauri ya bude ido ya juya ya dauke hawayen idanunsa da yatsu biyu ya kakaro murmushin dole ya ce,"

" Munaya tafi gida mana?"""

"Ta noke kafada ta ce,  Kai ma ta manta ka ne shi ne ka ke kuka?"""

"Ya ce,  Ni ba ta manta ni ba, tausayinta nake ji Munaya shi yasa nake kuka. "

"Ta ce,  Yanzu sai yaushe za ta tuna mu? "

"Ya ce,  Babu lokaci. Ke dai duk san da ki ka yi sallah ki dinga yi mata addu a kan Allah ya maido mata da"

tunaninta.

"Ta yi dan tunani can ta ce,  To yanzu shi ma Uncle Aliyu wanda za ta aura mai kawo mana chocolate, shi"

"ma ta manta shi?"""

"Tamkar ta soke shi da mashi a kahon zuci. Cikin karfin hali ya ce,  Ban sani ba Munaya. "

"Ta ce,  Ka ce da Daddy ya fasa yi mata auren, tunda ba ta da lafiya. Ta yi ciki tana kuka sosai."

Ya ja jiki da kyar ya doshi falon Alhaji Usman. Nan kunnuwansa suka jiyo masa fafatawar da ake tsakanin

Alhaji Usman da mahaifinsa. Alhaji Usman na fadin.

"""Wannan kaidin Rukayyah ne. Bana ko tantana baki ta hada da likita suka yaudare ku, don kada ta auri"

Aliyu. Don dai ni ban taba jin wannan almarar ba a zahiri sai a finafinan karya (memory eradication).

"Da dai hauka take, ko kurumcewa ta yi sai in yarda da su, amma babu makawa sai na daura mata aure da"

"Aliyu yau din nan in ya so don bakin ciki ta kashe kanta ta mutu kafira ina ruwan wani."""

"Cikin danne bacin ran shi Alhaji Aliyu ya ce,"

"""Nima ban ce kada ka daura mata auren ba, karewa ma na zo ne don in halarci daurin auren kamar"

"yadda na gaya maka a waya, am not here to convince you! Kuma ni zan yi wa Rukayyah kayan aure da Uba ke yi wa  yarsa, abin da na ce shi ne ka kira shi yaron da za ka bawa auren ya ga halin da take ciki."

"In ya tabbatar maka yana son ta a haka kuma zai iya auren ta a haka, to babu laifi a daura. "

"Duk sauran mutanen da ke falon suka hada baki suka ce,  Haka ne, wannan shi ne daidai. "

"Alhaji Usman ya yi tsaki ya ce,"

" Me zai zo ya gani ban da karyarta? Makirar yarinya annamimiya mai hali irin na Jummai, don ba zan ce"

na Amina ba.

Rukayyah tun tana karama kawo girmanta take sa min ciwon kai. Ban taba sa ta abu ta yi min shi cikin

dadin rai ba.

Wallahi wani zubin har tunani nake anya ba musanye aka yi wa Amina da ita a asibiti ba?

To don dai na ga tana matukar kama da Yaya Umaimah ne amma ko kusa ba halin ta daya da uwarta

ba.

"Dariya Alhaji Aliyu ya yi ya ce,  Bakin ciki nake jiye maka Usman. Kada ka kai  yar a dawo mana da ita a"

ranar da ka kai ta. Don wallahi a halin da Rukayyah ke ciki yanzu ba karamin masoyinta ne zai iya jurar rayuwa da ita ba.

Ina mai tabbatar maka a yanzu Rukayyah ba ta da maraba da jaririn da aka haifa shekaran jiya. Ka fitar

da tunanin makirci ta yi kwata-kwata daga zuciyarka don a kan idona komai ya faru. Ita ko mi ya yi mata zafi za ta yi wa kanta wannan mugun alkaba i?

Ai ko kuturu ne za ka aura mata sai haka. Balle kuma mutumin da ta kawo maka da kanta ta ce tana so.

"Bai dai huce ba, haka bai gama yarda ba, amma don mutuncin Alhajin da yake gani ya fiddo waya yana"

kiran Aliyu Dukku. Ya ce  Kana ina ne?

"Ya ce,  Ina nan cikin Jalingo, wajen da za mu kama mu yi walima bayan daurin aure muke ciniki. "

"Ya ce,  To Alhamdulillahi, ka baro duk abin da ka ke yi ka zo yanzu ina son ganin ka. Bai jira amsa ba ya"

kashe wayar.

"Saifuddeen ya yi sallama ya shigo, ya russuna yana gayar da su. Alh. Usman ya ce,  Saifuddeen kenan,"

dan Dambatta mai kama da Jalingo.

"Yana mai kallon Alhaji cikin sigar tsokana, Alh. Aliyu ya yi murmushi. Ya rasa me yasa Usman ke son yi"

"masa wannan gorin kullum ya ga Saifuddeen. Idan kuma ya duba sai ya ga haka ne, komi na Saifuddeen na dangin Umaima ne."

Aliyu Dukku ya yi sallama suka shigo falon shi da babban amininsa. Saifuddeen ya daga manyan idanunsa

ya dube shi zuciyarsa na harbawa.

"Yana mai son tantance wane ne angon Rukayyah. Daya baki ne dogo, daya fari sol gajere dan dukul mai"

hanci. In dai da gaske Bafullatanin Gombe ne angon Rukayyah kamar yadda ya ji Hajiya na fadi he must be the short one.

"Ban da abun RAK, mene ne abin so a fuska cike da saje da gashin baki mara fasali."

Ba alamun wadatar ilimi a tare da shi. Da ganinsa ka ga  yan shago irin wadanda ba sa ragin ko

"kwandalar nan ko da cinikin dubu nawa za a yi musu, sai dai a fasa cinikin. Irin masu kashewa yarinya dubban nairori a waje kafin su aure ta da ta shigo ta zama nama."

"Ya shiga jan tsaki tsut-tsut yana faman kawar da kai, kada a ce su gaisa (A a ku ji min Malam Saifuddeeni"

da shiga sharo babu shanu. Takori).

"Suka zube cike da sarakuta suna gaida su Alhaji. Alhaji ya yi murmushi ya ce,  Wanne ne takwaran nawa"

ne? Gadanga kusar yakin Rukayyah?

"Aliyun nakara dukar da kai abokin ya nuna shi. Yana dariya ya ce,  Ga Aliyun nan. "

"Abin da Saifuddeen ke gudu shi ya faru. Alhaji ya ce,  To kai takwarana ga babban Yaya can sai ka matsa"

ka soma kamun kafa ka kwashi gaisuwa don yanzu shi ne na hannun damar Rukayyah.

"A liyu ya daga kai ya dubi sashen da Alhaji ya nuna Saifuddeen, kamar ya yi kuka da abin nan da"

"Alhaji ya yi masa yana ta jujjuyar da kai. Babu shakkah ya san wadannan fuskokin guda biyu a kafafen yada labarai, musamman jaridu game da duk wata harka ta shige da ficen jiragen ruwa."

"[12/17/2019, 19:16] Takori: Da na ga mafarkina ba zai taba zama gaskiya ba, na hakura na fawwalawa"

Allah na cire tunanin al amarin kwata-wata daga cikin raina. Amma ban daina addu ar kada Allah ya hada Saifuddeen da matar da ba ta nufin shi da ALHERI ba!! Ban daina addu ar kada Allah ya hada shi da

matar da za ta raba ni da shi ba!!!

"Sai ga shi yau ina zaune, ban zata ba ban tsammani ba, ijaba ta saukar min. Allah ya cika min burirrika na"

har guda biyu.

"Na farko dai kaunar da nake wa Rukayyah, ba zan taba iya rabuwa da ita ba. Ko da na zo daurin auren"

"nan karfin hali kawai nake yi, amma ban daina tunanin yaya zan yi in tafi in bar Rukayyah ba?"

"Ba ma a hannun ki ba, a hannun wasu jinsin mutane da ba su san ta ba, cikin irin wannan hali da take ciki."

"Na biyu hankalina ya kwanta, Saifuddeen ya yi auren da na yarda da shi. Auren da na san ana ganin"

"kimata, ana ganin darajata an kuma san ni na haife shi. Sannan ko ban gan shi ba ba ni da kaico, don na san yana a hannun da ba za a karkatar da zuciyarsa daga gare mu ba."

"Sai dai abin da ban sani ba shi ne, wannan auren hadin Alhaji ne ko ko bukatar Saifuddeen ne ta kashin"

kansa?

"Idan har hakan ne to Almadulillahi! Amma idan har hadin Allaji ne, dukkaninsu za su fukanci fushina."

Sannan ba zan bar shi tare da Rukayyah ba sai Allah ya ba ta lafiyarta.

A sannan ne za ta yi wa kanta  zabi na zama da shi ko a a? Don ni shaida ce kan cewa SAIFUDDEEN BA

IRIN MAZAN DA RUKAYYAH KE SON AURE BA NE! BA YA DAGA CIKIN LISSAFIN MAZAJEN DA RUKAYYAH

"KE BURIN AURE!!! Don haka ba zan kware ta ba, don ba ta da lafiya!!!"""

"Amina dai ba ta ce komai ba, tana jinjina rigima irin ta Hajiya cikin ranta. Ta mika hannu ta dauko"

"makullin dakin Rukayyah cikin lokar gadonta ta mikawa Hajiyar, sannan ta sa murya ta kira Munaya ta ce ta je ta taya Hajiya shirya kayan Rukayyah."

"Munaya ta bude dakin, Hajiya ta daga ido tana kallon dakin Rukayyah, komai tsaf-tsaf kamar tana ciki ba"

"ta je ko ina ba. Hotonta da ta zana kanta da hannunta kamar gaske, shi ta fara yin tozali da shi. A kasa ta rubuta RUJ, Wato (Rukayyah Usman Jalingo), Hajiya ta yi murmushi ta ce da Munaya."

"""Rukayyah gwanar zane, har yanzu tana nan ne da zane-zanen nata?'"

"Munaya ta ce,  Sosai ma. Har nima ta zana ni, ke ma ta zana ki, ta zana Rabi mai aikin ki da Mama. "

Ta daga katifar Rukayyah ta shiga zarowa Hajiya zane-zane kala-kala masu ban mamaki wadanda

Rukayya ke yi da hannunta.

"Abin da ya dauki hankalin Hajiya guda daya ne, wato wasu irin motoci na zamani da ta zana kamar gaske"

"har da yadda cikinsu da kujerunsu za su kasance idan an kera, da birki da sityari da komai har karin bayani ta yi a kasa cikin harshen Turanci, sai ka rantse da Allah Rukayya digiri ta yi a fannin zane-zane."

Ga wasu irin gidajen zamani flat ma abota tsari da ban sha awa ta zana. Ta yi wa kowanne sunan daya

"dace da shi& . Squared bungalow, rectangular bungalow, triangular, roundedda sauransu da kalar fentin"

"da zai dace da kowanne wani a kasansa tasa.. green house, pink house, wani inner milk, outisde brown da dai sauransu."

"Hajiya ta dade tana nazarin su, tana mamakin wannan abin al ajabi. Wato wata dunkulalliyar fasaha da"

"basira ce tsura cikin kwakwalwar Rukayyah, wadda babu wanda ya sani, babu wanda ya farga sai da Allah ya shafe tunanin nata da abin da ke cikinsa baki daya."

Sai a lokacin ta tuno hirarsu ta karshe da Rukayyah.

"""Ki ce da Munaya ta baki kayan zane na& . Hajiya baki san ni archititect ba ce ? "

"Tasa habar zaninta ta share wasu sababbin hawaye da suka cika mata ido. Ta ce,  Munaya hada min duka"

wadannan zane-zanen cikin babbar ledar can.

Munaya na hadawa ta jawo wata loka sai alkaluman zane da kalolin da take shafa musu kala-kala lodi

"guda. Hajiya mamakinta ya kai intaha, domin kayan zanene (Art-materials) masu tsada  yan waje. Sai a lokacin ta tuno inda ta samo su."

"Ta tuna rannan Rukayyah ta zo mata hutu kamar yadda ta saba, a lokacin tana aji hudu, da yammaci ta"

shirya ta ce da Hajiyan za ta shiga kasuwa neman kaloli da alkaluman zane an ce su dawo da su makaranta da zarar an koma hutu.

"Don haka Hajiyar ta hada ta da direbanta suka shiga kasuwa, kuma a daren ranar Alhaji ya ba ta kudi"

masu yawa har naira dubu hamsin Hajiyar ta ba ta shawara kan ta sayi dankunne da sarka na gwal ta sanya a kunnenta.

Da ta dawo ta ganta da wasu  yan mitsi-mitsin  yan kunnaye da akwati mai kyau cike da setin kayan zane

"da kaloli. Ta ce  Rukayyah ya ki ka sayo dankunne kawai, ina sarkar? "

"Ta ce,  Hajiya wa yake ta wata sarka na samu abin da na fi so a rayuwata? "

"Ta daga akwatun kayan zanen tana nuna mata, wanda yake na gilashi mai garai-garai.  Kayan zane ne"

"Hajiya!"""

Don haushi Hajiyar ba ta sake bi ta kanta ba. Rukayyah ta yi daki da su tana ta murna. Tun daga ranar

"Hajiyar ba ta sake ba ta kudi masu kauri ta ce ta sayo abu ba, sai dai ta sayo mata. Sai yanzu ta tuna tabbas wadannan kayan su ne a cikin akwatun."

"Kuma ita ce akwatun da ta ce da ita tasa Munaya ta dauko mata idan ta zo Jalingo, ta taho mata da su"

ana i gobe wannan mummunan al amarin zai faru da ita.

"Ta nisa ta ce,  Zuba su cikin akwatin ki jera su a ciki. "

"Munaya ta hau jere. Ta zauna sosai tana jera kowanne a muhallinsa, yayin da Hajiya ta maida hankali ga"

"jera sitturunta cikin troller katuwa. Munaya a marairaice ta ce,  Don Allah Hajiya ki tafi da ni, tunda mun yi hutu. "

Hajiya ta fahimci Munaya sarai ba karamar kauna take yi wa  yar uwarta ba.

Ta yi tunanin ita ma za ta taimaka mata wurin kula da Rukayyah. Don kuwa zama za su yi tare babu inda

Rukayyah za ta je (gidan Saifuddeen).

"Ta ce,  To maza dauko kayanki. Da gudu ta nufi inda nata kayan suke ta soma hadawa."

"Ta koma dakin Mama Amina tana gaya mata har da Munaya za ta tafi, ta bar mata  yan mazan."

"Su ma ba don ta koshi ba sai don tana tausayin ta bar ta ita kadai. Ta yi murmushin su na Fulani ta ce,  In"

kin so ma duk ki hade na bar miki. Ni mijina kadai ya ishe ni.

"Ta ce,  Ba wani nan. Fillanci ne irin naki. Amma na san ji ki ke yanzu kamar ki dora dukkan hannuwa aka"

"ki kwarma ihu kin aurar da rabin ran ki (Rukayyah)."""

"Mama Amina ta yi dariya ta ce, ""Tun da ehu ba ne ai da sauki, tunda ba hadiyar zuciya zan yi in mutu"

ba.

Saifuddeen ya shigo cikin takunnan nashi da baya canzawa. Asi ta biyo shi da gudu har kofar dakin Mama

"Amina,"

" Ango ka sha kamshi, ka ga yadda goshika ke wani kyalli kuwa? Na Rukayyah ALHERIN Allah ya kai maku"

"har  ya ya, jikoki da tattaba kunne. "

"Ya yi murmushi da ya kara bayyanar da kwarjininsa, cikar zati hadi da tsantsar farin cikin da ya tsinci"

"kansa a ciki a yau, irin na wanda Allah ya yi wa baiwa da kowa, da komai na rayuwa."

Ya ce Aunty Asi kin ci mota (Kare magana). Insha Allah da na koma gida zan aiko miki da ita. Na gode

kwarai da fatar ALHERIN ki.

"Asi ta sake zabga wata gudar kamar wata marokiya ta ce,  Insha Allahshekara mai zuwa war haka zan"

taho Legas yi wa Rukayyah wankan jego.

Anan kuma kunya ya ji. Ya kyale ta ya danna kai cikin dakin bakinsadauke da cikakkiyar sallama.

"Suka yi ido hudu da Hajiya, wani irin tattausan murmushi mai dauke da matsananciyar kaunar UWA ta"

"sakar masa, wanda bai taba gani a fatar bakinta ba. Babu shakkah bai taba ganin irin wannan bayyanannan farin ciki a fuskar Hajiya ba."

"Kamar yadda bai taba ganinta cikin nishadi irin na yau ba, duk da tana kokarin boyewa, kada ya gane."

"Shi ma ya mayar mata da martanin murmushinta, yana mai dauke kai daga kallon sashen da Rukayyah"

"take, tana ta sharar barci abinta cikin kwanciyar hankali."

"Ya karasa ciki ya tube takalmansa a bakin kofa, a hankali yake tambayar Hajiya,  Ina Maman ne? Ta yi"

mai nuni da kofar dakinta ba tare da ta ce uffan ba.

"Ya karasa bakin kofar ya tsugunna bisa gwiwoyinsa yana yi mata sallama, amma bai iya ya shiga dakin ba"

"kamar da, surkunta sosai yake nunawa yau, ita ma da kyar ta iya amsawa da Allah ya kiyaye hanya. Bayan wannan ba ta kara komai ba."

"Ita ma Hajiyar a zahiri kunyarta yake ji, ko ido ya kasa kuma hadawa da ita. Ya sadda kai yana fada mata"

"Alhaji ne ya ce ta fito su tafi. Ta koma cikin kujera tare da sake sabon zama ta ce,  Ga shi kuma Rukayyah barci take yi. Kuma ba zan tashe ta daga barci ba, domin tana daga cikin ka idar likita, kai da bakinka ka ke gaya mini. "

Ya zame ya zauna sosai a kan carfet bai ce komai ba. Domin kuwa bai ga fuska ba. Ta maida fuskarta ta

"dinke kamar ba ita ce mai annurin nan yanzu yanzun nan ba. Yana so ya ce da ita to ai lokacin tashin jirgin ya kusa, har yaushe za ta tashi daga barcin? To bai ga fuska ba, don haka ya ja bakinsa ya tsuke ya ci gaba da zaman tsammanin warabbuka."

"Munaya ta shigo cikin nutsuwa ta durkusa gabanta ta ce,  Hajiya duk kayan an shigar su mota, ku ake"

jira.

"Ta ce a takaice, ""To madallah Munaya, sannunki dai. "

"Ita ma ta bi layin Saifuddeen ta zauna shiru, suna jiran  yar lelen Hajiya ta tashi daga barci. Wadda

Please Login or Register in order to submit comment