You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

turaren (Geo-Armani) ya

bakunci hancinnansu.

"Kafin ta jiyo takun shi na GIRMA akan marbles daga can wajen kujerun falo ya dakata, ya tube"

"takalamn shi cikin sallama, kana ya karaso."

"Rukayyah ba ta dago ba, kanta yana kasa, tana kallon irin wannan sullubebiyar kafa jawur kamar"

"ka taba jini ya yi tsartuwa, ma abociyar zara-zaran yatsu da tsaftatattun farata kai ka ce kurar duniya ba ta taba hawanta ba ko ko ba a taba takata a kasa ba."

"Ta yi hanzarin dubar kafarta mai dauke da bakin lalle a kowanne dan yatsa. Iri daya ce sak, da"

wannan kafar da take kallo babu bambanci sai fadi da tsayi da ta fi tata.

"Sai ta hau boye abarta cikin zaninta, kada shi ma ya ga kamannin kafafun nasu, ya ce wata alaka ta"

hada su.

"Har ya gama gaida su Hajiya suka ba shi umarnin zama a kujerar da ke kusa da ta Alhaji, kuma"

"wadda ke daura da wadda take zaune, kasancewar kujeru hudu ne kacal ke da tebirin cin abincin na tsurar bakin gilashi mai santsi."

"Rukayyah ba ta dago ba, ba don komai ba sai don tsoron irin kallon raini da kaskancin da zai yi mata,"

wanda ko kadan ba za ta jure ba.

"Hajiya ta ce,  Yaushe ku ka dawo ne? "

" Jiya-jiyan nan wallahi, amma yanzu zan koma Maidugurin ta jirgi da zarar na bar nan. "

"Alhaji ya kasa boye mamakinsa ya ce,  Me kuma za ka koma ka yi? "

"Cikin ladabi ya ce,  Ai yau din zan dawo Alhaji, in Allah ya yarda. Saliman ce ba ta jin dadi, ko mi ta ci"

"sai ta maido shi, kuma ba ta iya shiga kicin don wai ba ta son warin abinci, idan ya soma dahuwa."

"Shi ne ta ce in je in taho mata da kanwarta Yagana, ta dinga kula da gidan saboda Hajiya kin san ni"

bana iya cin abincin masu aiki.

"Hajiya ta ce,  Allah ya iganta. Cikin mamaki ya ce,  Hajiya me Allah zai inganta, ciwon?"""

Ta ce cikin halin ko in kula  Ba ciki ne da ita ba?

Ya kawar da kai cikin jin kunya ya ce ba mu je asibiti ba don haka ba mu tabbatar ba.

"Ta ce,  Ai gara ku je, a yi ta zama da ciwo?"""

"Alhaji ya kasa boye fushinsa da bacin ransa ya dago ya dube shi a hankali ya ce,"

" Yau satin ka guda rabon ka da ofis, ka raka mata biki, saboda kai ne bita-zaizai, ka bar muhimman"

"aiyukan da ke gabannmu, saboda ana bikin kawar matarka, yau kwana na bakwai bana barci, ina ta aiyukan da kai ka kasa, ina murna zan dan huta kwana biyu, shi ne za ka ce min komawa za ka yi?"""

"Ya dukar da kai a ladabce,  Wallahi Alhaji na ce a yau zan dawo, in ban dauko yarinyar nan ba Salima"

ba za ta bar ni in zauna lafiya ba.

"Alhaji dai don haushi sai ya rabu da shi bai sake tofawa ba, ya ci gaba da cin abincinsa."

"Hajiya ta tura masa foodflask gaban shi ya bude ya saka funkason biyar a faranti, ya fara cika kofi"

"da kunun gyada ya daddaka, ya sake cikawa ya shanye a hanzarce, duk Hajiyar na lura da shi."

"Yasa funkason nan a gaba da ci, kamar Allah ya aiko shi, sai da ya ga buzunsa, da alama irin"

"tsohuwar yunwar nan ya tara ta kwana da kwanaki. Rukayyah dai ta samu ta mike zata zille Hajiya ta ce,"

" Rukayyah ban ga fa kin ci wani abin kirki ba, kin mike?'"

"Rukayyah ta ce,  Wallai Hajiya am O.K, Nafisa nake so n kira a waya. "

"Abin dai da take gudu shi Hajiyar ta yi mata, ta ce  To baku gaisa da Yayan naki ba. "

"Ta zuki iska ta fesar, ta juya bangaren da yake zaune cikin rashin walwala da kasalalliyar murya ta ce,"

 Ina kwana?

"Da farko kamar ba zai amsa ba, ganin Hajiya ta zuba masa ido ya dan dube ta da wutsiyar ido, a"

"kaikaice ya ce,  Rak, yaya Jalingo?"""

"Ta yi gaba ba ta amsa masa ba, a ranta tana cewa ai ka san hanyar ta, ka je ka tambaye ta man. Ji"

"wani rainin hankali wai wani Rak, wato ban kai matsayin da za a kira ni da cikakken sunana Rukayyah ba."

"Alhaji ya ce,  In ka kammala sai ka je ofis bakin nan na Rasha yau za su gama da kai da karfe sha biyu"

na rana.

"Kamar ya saka kuka ya ce,  Amma Alhaji na riga fa na yi booking wallahi, kuma jirgin eleben zai tashi,"

"tunda muka dawo ban ci wani kwakkwaran abinci ba, sai lemu nake ta daddaka, gara in fara dauko wadda za ta dinga dafa min abincin tukunna sai a daga appointment din. "

"Hajiya ta bude baki kamar za ta yi magana, ta dai daure ta yi shiru, amma ranta ya gama baci da"

"wannan sabuwar halayya ta Saifuddeen, wai musu da Alhaji?"

"Amma ta san Alhajin ba kanwar lasa ba ne, baya daukar wargi ko kankani, zai yi maganin abun da"

kansa yanzu-yanzun nan.

Ba ta gama tunaninta ba ta ga Alhaji ya mike tsaye cikin kakkausar murya ya kwankwasa tebirin da

" yan yatsunsa da karfi ya ce,  Saifuddeen!. Ya ce,  Na am. Ya sake cewa  Saifuddeen!!"" Ya ce,  Na am. "

"Sai da suka yi haka har sau uku kafin ya ce,"

" Wato aikin matarka ya fi nawa ko? Tunda ka yi auren nan nake lura da kai, ka bar komai ya"

"sakwarkwace, ka zama mijin-tace, sahorami, sullutu, shashasha, idan haka aure yake lalata jarumin mutum, mu kan da ba mu yi ba. Da ba mu tara abinda yau muka tara ba."

"Bari in gaya maka mace da lokacinta aiki da lokacinsa. Ba haka ka ga ina nanikewa uwarka ba, ina"

"raka ta biki. Yanzu kamar kai Saifuddeen dube ka don Allah, a ce ka zama dan aiken mace, kaicon ka!"

Wallahi-wallahi ka ji na ratse ba za ka je Maidugurin nan ba. Idan mataimaki take so ga Rukayyah

"nan ba abin da ba ta iya ba, in ka dawo ofis ka biyo ka dauke ta ka kai mata ita."

"Duk  yan uwanka ba wanda ya isa ya je gidan ka ya wuni, saboda su ba a dauke su mutane ba. Idan"

"ba ka sani ba in gaya maka abin da aka yi wa Hajiyar Dambatta a gidan ka, a kofar falo aka sauke ta ko ruwa ba a ba ta ba."

Zaman awa daya ta yi a kan takalamnta tana zaman jiranka ta ba ka tsarabar da ta kawo maka na

"gireba da ka sa ta yi maka, aka aiko ta zo ga direba nan zai kai ta inda za ta matar gidan fita za ta yi."

"Wai uwar da ta haife ni ne wannan balle sauran dangina. Hajiya har kuka ta yi san da take gaya mini,"

"saboda wulakancin da matarka ta yi mata ba ta taba zato ba, na ba ta hakuri na hadiye wannan ban gaya maka ba, kada in zamo uban wofi mai hada husuma."

"Ba a fi kwana uku a tsakani ba Baffa Jibo shi ma ya je neman ka kan zancen gonakin Dambatta, shi"

"ma aka bar shi a bencin maigadi, ga motar ka yana gani a rumfa aka ce ba ka nan."

Duk na yi hakuri alhalin ina ganin irin dawainiyar da ka ke yi da nata  yan uwan. In ba ka sani ba ina

da (record) na duk motocin da ka ke dauka bada izinina ba kana bai wa kannenta da kawayewanta.

"Ubanka ne ya saya mini, ko ko uwarka ta ba ni jari?"

Wallahi in ba ka nutsu ka kama kanka kamar kowanne magidancin kwarai ba sai na kwace komai

"nawa daga hannunka, ka je ka nemo na kanka ka san zafin neman yadda za ka ji dadin bautawa mace. Ka gani idan ba ka da komai za ta zauna da kai ko a a?"

Tashi ka ba ni wuri don Allah tun bakin cikin ka bai haifar min da ciwon hawan jini ba.

"Magana ta da kai ta karshe ita ce idan ka kai Rukayyah ta koro ta, ta gani idan ban kore ta ba. Ai ba"

ubanta ya gina min gidan ba.

"Duk matar da ba za ta so ka da  yan uwanka ba, wallahi ba mai kaunar ka ba ce, shashasha. Dube"

"ka don Allah namiji har namiji, amma bai isa ya amsa sunan maza ba& . "

"Hajiya ta yi murmushi, cikin jin dadin yadda ya wanke mata shi tas, abin da ita ba za ta iya ba, kada"

a ce ta fiya sa ido kan al amarin surukar ta.

"Ta shigo dakin da Rukayyah take, tana kishingide bisa gado suna shan hira ita da Nafisah a waya"

"suna ta kwasar dariya abinsu, ba ta san wainar da ake toyawa a gidan ba. Ganin Hajiya ta shigo ta yi wa Nafisah sallama ta kashe wayar a cikin kallonta."

"Hajiya ta ce,  In kin kare abincin rana Rukayyah, ki shirya kayanki, anjima Yayanki zai zo ku tafi"

"gidansu. Saliman ce ba lafiya wai ba ta iya girki sai ki dinga taimaka mata, don Allah, na san ki Rukayyah ba daga nan ba. "

"Rukayyah ta bata fuska ta zumburi baki, ta cika fam ta soma hura hanci, ta ce,"

" Gaskiya Hajiya daina hada ni da wannan  yar ikon da ba ta san mutuncin mutane ba, ni kuma kin"

"san halina ba na son raini kuma ba na daukar wulakanci, don haka tafiyar mu ba za ta zo daya ba, me zai hana a tura masu Rabi? "

"Hajiya ta zauna a gefen gadon sosai ta kamo hannunta cikin lallashi ta ce,  Haba Rukikis, ta Aliyu mai"

komai dozen! Ba sai an kula kashi ya`ke doyi ba? Ko kin taba jin inda karfe daya ya yi amo?

"Ai ba don ita za ki ba, don dan uwanki za ki, kuma don shi za ki yi. Kin ga nima gobe Jalingo zan tafi"

"kan maganar ki, ba za ki ji dadin zaman gidan ba don na ji Rabi na cewa za ta bi ni ta gano gida."

"Sannan Alhaji shi ya zabe ki da kansa har amanarki ya ba shi, ya kuma san da Rabin, amma ya zabe"

"ki, saboda sanin dacewarki da cancantar ki. "

"Dariya Hajiya ta ba ta sosai ta ce,  Au! Matsayi da cancanta ne ma aikin matar Yayan? "

"Ta ce,  Matsayi ne mana, ita da ke shirin kawo maku da guda, ai a je mata ko ba don halinta ba. "

"Ta jinjina kai, ko me ta yi tunani ta ce, gaskiya kam. Ta mike ta soma shiri ba tare da tunanin komai"

ba.

"Sai wajejen karfe shida na yamma Saifuddeen ya dawo gidan, ya bi ya maka bakin (spaces) yadda ba"

"ka iya hango kwayar idanunshi. Allah kadai ya san halin da zuciyar shi ke ciki, na cewa da a kai sai ya dau Rukayyah, bacin rai ne, takaici, farin ciki, ko bakin ciki, oho! Shi ya bar wa kansa sani."

"Sun dade suna hira da Hajiya anan falo, shi bai ce Rukayyah ta fito su tafiba, Hajiyar ma ba ta kira ta"

"ba, sai kara zakulo sabuwar hira take duk hankalin shi ya yi kan uwargida Salima, da ya baro ba yadda take."

Daga can kicin Rukayyah ta bullo dauke da tray ta ci ubansu kwalliya da wani beig material mai

"yarari, dinkin babba ne, amma an matse shi sosai daga tsakiya yadda ya fiddo zahirin kirar jikinta da"

dukiyar su ta gado kamar an hura balan-balan. Tayi kananun kalba (BobMerly) akanta siri-siri ta makalkale su da (beads) kalar ruwa sai reto suke a kafadunta.

"Maimakon ta daura dankwali a kanta, sai ta yafa shi ya zagayo ta wuyanta, wannan al adar"

"Rukayyah ce, ba ta yin daurin kai sai dai ta yafa dan gyale."

"Ta taho da sassarfa cikin tafiyar nan tata kamar wadda ke kan gajimare, ta russuna ta ajiye masa"

"tiren. Yana iya shakar lallausan kamshin da ke tashi jikinta mai kwantar da hankali. Ya lumshe ido abin ki da (Womaniser), kare mata kallo yake a yau, daga gira har yatsun kafa ta cikin dark-spaces dinsa ba tare"

da dukkansu sun sani ba.

"She is indeed pretty, cute and sexy. Yawun bakinsa gaba daya bushewa ya yi, komai na yarinyar ya"

"yi masa, illa halayyan ta na girman kai da jiji-da-kai."

"A ran shi ya ce,"

" Wato wannan yarinyar ma  yar yi ce, yana ganinta haka wata (local-local) ashe ta yi kilin (clean). To"

shi kilin din a wurin  ya ya mata ba wuya ne?

"Rukayyan kam ba ta kan shi take ba, ba kuma don shi ta yi kwalliya ba, wannan abu ne da ya"

"zame mata al ada, (kullum cikin kwalliyarta take), saboda tsabar kama jikin ta da kwalliya ta yi ko ta yi ko ba ta yi ba, da abarta za ka ganta."

"Abinci kuma da ta kawowa Saifuddeen umarnin Hajiya ne, ba ta yi ne don ta burge ko don ya kula ta"

ba.

"Ta koma can cikin 3-seater ta harde kafafu, ta dauki daya ta dora a kan daya, ta dauki remote tana"

canja channels daga wannan zuwa waccan ba tare da ta kula da hirar su ba.

"Dankwalinta ya zame ta baya, wani irin lallausan gashi kanannade baki sidik, mai sheki da daukar"

"ido a cikin kananun kalba ya yi masa sallama, real,wanda babu algus a cikinsa, sabanin wanda ya saba gani na izgar doki."

"Allah ya taimake shi idanun shi cikin bakin gilashi suke, da Hajiya ta hango irin mayataccen kallon"

da yake bin Rukayyah da shi kamar bai taba ganin diya amce mai kyau ba sai yau a kanta.

"Hajiya ta lura Saifuddeen saitin da Rukayyah take kawai yake kallo, ko taba abincin da ta ajiye masa"

"bai yi ba, tana ta magana bai ji ta ba, hankalinsa ya tafi can ga matsananciyar sha awar Rukayyah, tunanin shi kwata-kwata baya tare da ita."

"Shi yasa Allahu Subhanahu wata ala ya ce  Ku boye kawarku, (ta hanyar sanya hijabi), illa ga"

"mazajen ku, ku iyayen ku, ko iyayen mazajenku, ko yayyanku, ko  yan uwan ku na jini (Muharramanku& .)"

har zuwa karshen ayar (Ahzab).

"Ita ma ta juya sashen da Rukayyan take, ta ga irin fitinannen kyan da ta yi sai ta tsorata. Ta zabura"

daga kujerarta ta ce cikin daga murya

" kai ! Ci abincin mana ku tafi dare yana yi, ke kuma Rukayyah je ki maza ki dauko hijabi ku tafi,"

bana son ki dinga fita da wannan dinkin banzan .

"Daga shi har Rukayyan firgigit suka yi, shi na rashin gaskiya ita na rashin zaton dalilin tsawar, ya yi"

"saurin sauke kai, ya nutsu, ya zama kintsatstse kamar ya nutse cikin kasa saboda kunya."

Ya san Hajiya kwarai da sa ido a kan al amarin  ya yan ta gami da fuskantar inda duk wani motion

"nasu yasa gaba, babu mamaki ta dago yadda ya shagaltu a kallon Rukayyah."

"Rukayyah ta ce a marairaice  Wallahi Hajiya kin tsorata ni, ai ba sai kin yi fada ba in kin ce in saka"

"zan saka ne, fadan ki kidima ni yake. "

"Hajiyar ta sassauto ta yi murmushi ta ce,  To maza ku yi azama ku tafi, na daina fadan. "

Ya mika hannu ya bude hadaddiyar soyayyiyar shinkafa (fried rice) wadda ta sha anta da kayan

"lambu da aka yayyanka gutsi-gutsi, wani lafiyayyen kamshi da bai taba jin wani abinci da shi ba, ya bakunci hancinsa (Mushroom curry). Yawun bakinsa ya tsinke tun kan ya kai bakinsa."

Ya nade hannun riga ya soma kwasar girkin Rukayyah mai dadin gaske. Ya kammala ya kora da

farfesun kayan ciki wanda ya dahu lugub.

"Idan kuwa har irin wannan daddadan girkin zai dinga kwasa kullum, ai kuwa ya rike  yar Hajiya, da"

amana.

"Ta fito tana tura jakarta da ta zo da ita, sanye da ruwan tokar (After dress) mai kauri, amma hakan"

"bai boye jelunan kitson ba. Hajiya ta daga ido ta kara duban Rukayyah, sai ta ga kamar wadannan din sun fi wadancan bayyana kyawun surarta."

Ta soma tunanin kar ta bar Rukayyah ta fita da Saifuddeen ba don komai ba sai don sanin halin

kayanta kamar yadda ta san yunwar cikinta.

"Sai ta hau fada na babu gaira babu dalili,  Ke kam Rukayyah na rasa wacce irin yarinya ce ne mai"

"kunnen kashi. Haka za ki fita duk jelar gashi a waje? Hijabi na ce ki sako ki ka je ki ka sako rigar gaye to ai sai a fasa tafiyar, ba dole. "

"Rukayyah ta tsaya kawai tana mamakin Hajiya, don dai ita ba ta dahijabai sai na sallah, to ko shi"

"Hajiyar ke nufi? To a fasa tafiyar mana, dama ba ita tasa ta ba. Ita ma ba son zuwan take ba."

"Hajiya ba ta taba yi mata fada irin haka ba, sai yau, don za ta fita da danta? To lalatacciya ta dauke"

ta ko me?

"Kawai sai ta ji ranta ya baci, Allah sarki rashin sani! Rukayyah ba ta san Hajiyar nata dan ne ba ta"

"yarda da shi ba, take son ta kare mata mutuncinta."

"Shi dai bai tofa masu ba, yasa kai ya fice ya koma cikin mota yana amsa kiran sweety Salima."

"Rukayyah taso ta ce da Hajiya na fasa zuwa, amma ta yi tunanin Hajiyar tafi karfin haka a gare ta."

"Ta koma ta dauko hijabin sallar ta baki wuluk, ta maka, ta hankada jakar keceeeee& .!!! Za ta fita,"

"kamar guguwa. Hajiya a sanyaye ta ce,"

 Rukayyah ! .

"Ta dakata, ba tare da ta juyo ba kuma ba ta amsa ba, ta ce  yanzu don na yi miki fada kan abin da"

"zai amfane ki, shi ne ki ke fushi? "

"Jikin Rukayyah ya yi sanyi, tausayin Hajiya ya kamata, ta dawo ta tsugunna a gabanta tana"

murmushi ta ce  wallahi Hajiya ba fushi na yi ba .

"Ta ce to je ki, ki kula da kanki, don Allah na san ki da karambani ban da sakarwa duk wani namiji"

"fuska Rukayyah, dukkansu wayo ne da su, wayon cuta da rashin ALHERI, wayon yaudara da ha inci."

Kullum ki zama cikin hijabinki a gaban maza wannan ita ce mace  yar mutunci da ta san daraja da

"martatabar kanta, kina ji na? Rukayya ta amsa  to Hajiya ta , ba tare da ta yi tunanin jirwaye ne take yi mata ba."

"Ta ci gaba da cewa kuma ki yi musu biyayya tunda sama suke da ke. Ki dinga hakuri da mutane, kad"

aki ce komai aka yi miki sai kin rama.

"Ki rage wannan giringidishin ki kama kanki, ki zama mai kawar da kai kan abin da bai shafe ki ba."

"Ke dai abin da ya kai ki kawai ki yi, wato girkin dan uwanki, ba ruwanki da kowa . Ta sake cewa  to ."

Ta daga kafa za ta fito Hajiya ta ce.

" Gobe in na dawo daga Jalingo zan yi waya in gaya miki yadda muka yi da Usman din, idan ta ji sauki"

ki dawo.

"A zuciyar Rukayyah ta ce har yaushe? Ai ni nan ba zan wuce sati ba, sai ka ce wata mara abin yi?"

"Cikin motarshi ta same shi a zaune kafafunshi duka biyu suna waje, yana magana da mai dakinsa"

cikin wata irin lallausar murya da ta kasa amincewa ta yardarwa kanta ta Saifuddeen ce.

"Jin irin kalaman soyayyar da ake yayyafawa, ba shiri, ta ja da baya, ta jingina da murfin motar tana"

mai duba agogon hannunta.

"A kalla mintuna talatin ta share a tsaye, kamar bai san da halittar mutum bil adama na jiransa ba."

Wayarsa kawai yake yi cikin nishadi(looking so classy and gentle).

"Tana shirin komawa ciki don haushi ya rufe wayar ya dauke kafafunsa ya mayar cikin motar, ba"

kuma tare da ya dube ta ba ya ce  kina iya shigowa . To anan fa ake yin ta.

"Ya yi kicin-kicin da fuska, yana shirin ganin inda za ta zaba don zama. A ganinsa ba karamin ci-baya"

"ba ne ya jera da Rukayyah a gaban mota, ga wani zurmemen hijabi bakikkirin kamar tsumma ta zurma. Sannan ba karamin faduwa ba ne ta kame a baya ya tuka ta, to yaya kenan?"

"Rukayyah sai ta katse mai tunani ta hanyar bude gaban mota ta kame abinta, ita ma huci take na"

"shanyatan da a kai a tsaye minti talatin kamar wata mai neman aikin lebura a DAMBATTA SHIPPING? Shi ma a fusacen ya fisgi motar, kamar wanda ya dauko tulin kashi, yana Allah-Allah ya sauke shi, ko ya samu sa aida."

Ba ta taba shiga mota mai dadi da ni imar wannan ba. Wato dai wannan ita ce Opel-Astra da take

"jin labari a Magazine, websites da sauran kafafen tallace-tallacen motocin  General Motors din Amurka. Tana da yakinin, wanda ya zabi motar gwani ne wurin iya zaben abubuwanjin dadin rayuwa masu burgewa, sai dai kam a ganin ta bai iya zaben abokiyar rayuwa ba."

"Wata irin mace salalab, siririya kamar bulala, ba gaba, ba baya, irin matannan zokala-zokala da ta ke"

"gani suna (fashion parade) a talbijin masu kama da zangarniyar dabino, sai dai fa fuskar nan mai shegen kyau ce, da ta ji hanci da ido, gami da tsararren bakin sumba (kissable lips). A wurin MANYAN MAZA irin SAIFUDDEEN ALEEYU DAMBATTA, wadannan su ne mata na sanyawa a gaban mota, na fita tsara, na"

"shiga taro. Wadanda a tsaye za ku goga kafada-da-kafada da su, har wani lokaci su kere ka a tsawo."

"Ta taho da gudu ta kama mijinta a falon, suna wasu irin abubuwa da Rukayyah ba ta taba gani ba"

har da su tande-tande da lashe-lashe kamar wasu mayunwatan mayu.

"Ko da yake ta kan gani jefi-jefi a fina-finan India da na Turawa, wai sunan shi soyayyah (Romance)."

"Saidai bata taba gani a zahiri ba. Sai da suka nutsu, Salima ta kyalla ido ta bayan mijinta ta hango Balarabiyar budurwar, santaleliya jawur da ita, maimakon Yagana, baka-kirin."

"Wannan yarinya ba ta da maraba da SAIFUDDEEN ALIYU DAMBATTA a fuska, yatsu da santala-"

santalan kafafunnan nasa.

"Ta zare zurmemen hijabinta, wanda ya addabe ta da zafi, hakan ne ya bawa Salimar damar hango"

zahirin kirar yarinyar sosai kamar tarwada. Ga wasu yala-yalan real gashi na reto.

Tana linke hijabin tana sakar mata lallausan murmushi. Ta daga mata fararen hannuwanta da suka

"sha adon bakin lalle a kan kowanne dan yatsa, gami da zobban farin zinare (white gold) a yatsunta uku, sai walkiya suke ta ce cikin wata irin sassanyar murya."

" Hi, matar Yaya!. "

"Ko kifta ido ta kasa, tana kokarin tuno inda ta taba ganinta. La shakkah ta taba ganin fuskar ko da"

sau daya ne. Sai dai ta manta a inda ta gantan.

"Wanda tun a lokacin ba ta kwanta mata ba, ba ta yarda da ita ba, kuma ba za ta ce ga dalili ba. Sai"

dai can a karkashin zuciyarta ta san tsabagen kyawun yarinyar da kamannin ta da Saifuddeen ne ya mintsini zuciyarta.

"Ba tare da jiran umarni ba (Rukayyah - Akarambana), aka tura jaka ji ka ke keceeey& & . Har tsakiyar"

"hadadden falon da ya fi mata kama da fadar marigayiya Stella Obasanjo, ko ko falon Titin Atiku. Kai wuce nan. Ta ce a ranta."

Ya fi kama da falon Turai  Yar Adua. Irin fulullukan nan da take gani tasoshin (Interior decoration) na

tallan su cikin talbijin daga kasar Italiya.

"Shi dai maigidan duk ya dabar-barce, na irin mazannan masu tsananin gudun bacin ran matansu."

Ya karasa ga  yan mitsi-mitsin (leather seats) gajejjeru farare sol masu numfashi da suka taimaka

"sosai wurin kawata (black and white) falon, tare da daukar (remote) yana karo karfin (split), domin ta"

"kawar mai da dan gumi-gumin da yake yi na tsoron hukuncin da Madam, za ta yanke masu, shi da Rukayyan, wanda ya tabbata daidai yake da fuskantar fushin, Alhaji Dambatta."

"Madam Salima dai na nan tsaye inda suka bar ta, tun bayan da mijin ya yi kokari ya zame jikinsa"

"saboda kunyar idanun  yar kanwallen da ke tsananin ganin GIRMAN sa, ya yi ta maza (in ji mata) ko ko ya yi kundumbalar cewa."

 Baki gane ta ba ne? Rukayyah ce diyar Kawu Usman kanin Hajiya.

"Ta dan yi yake, amma idanun nan farare kal, sun kada sun yi jawur, kana ta daure ta iso kusa da shi"

"ta zauna, tanakokarin yin matashi da cinyoyinsa cikin alamu na maras lafiya ta ce,"

" Ai fa ga kama nan.  Bata kuma kara juyawa ta kalli Rukayyan ba, haka ba ta ce da ita ga wuri ki"

zauna ba.

"Rukayyah dai ko a jikinta, karewa ma ba ta san suna yi ba; domin san da suke maganganun su waya"

take yi da Rabi.

Da ta kammala ta karasa daya daga cikin kujerun falon nesa da su ta harde kamar yadda take yin

"zaman kujerarta, wato sai ta debi kafafunta biyu ta mikar da su a kan kujera, ta dauki daya ta dora bisa daya, tana fuskantar talbijin. Ba ta kara kallon su ba haka suma ba su

Please Login or Register in order to submit comment